*A GARIN MU* WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 1: Jihar Zamfara, jiha ce mai tarin albarka, jiha ce mai cike da arziqi, na noma, na ma'adanai, da kiwo, Allah ya azurta Zamfara da mutanen kirki tun kafuwar ta, ya sanya ta zama qasa mai tarin albarka, da ruqo da addinin musulunci, jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Nigeria da suka yi tashe a tsaida shari'ar Musulunci shekaru masu yawa da suka gabata. An san mutanen jihar Zamfara da son zaman lafiya, gaskiya, amana, juriya, jarumta,ilimi, kasuwanci, sana'o'i, sarauta, da dik wani abu na jin dadin rayuwa. Zamfara gari ne na zaman lafiya a baya, gari ne da aka yanke shi daga jihar Sokoto,a zamanin General Sani Abacha, a 1st October 1996, shine shugaban qasar da ya ba ta 'yancin ta, ta zama jaha kamar sauran jahohi a qasar nan ta Nigeria. Jihar Zamfara ta tara sarakuna, da shuwagabannin gwamnati masu adalci a baya, ta yanda qasar ta zamanto a koda yaushe cikin aminci take, kowanne dan jahar kuma kowanne yare, da addini ya ke zaune cikin kwanciyar hankali, ba fargaba, ba tashin hankali, balle tsoro. Wannan ita ce jihar Zamfara a shekarun da suka gabata. Garin Gusau shi ne babban birnin jihar zamfara, gari ne da ya qunshi al'umma kala kala, mabanbanta, yaruka daban_daban, da addinai daban-daban. Gwamna Halliru Murtala Gusau, shi ne Gwamna mai ci, ya na zaune da iyalan shi a unguwar GRA, Gwamna Halliru ba shi da abin so a duniya sama da iyalin shi, dan haka komai ya ke yi a duniyar siyasa domin su ne, Hajiya Ikilima wadda aka fi kira da Hajiya Ikee, ita ce matar shi, sai yaran su biyu Sultan me shakara Ashirin da tara, da Sultana Mai shekara Ashirin da biyar,dikkan su sun yi karatu ne a University of Westminster London, in da Sultan na da BSc a Architectural Technology, Sultana Kuma na da BA a Arabic and linguistics. Dikkanin su sun samu gata, kalar wanda in da za a hada su da sauran yaran gwamnonin Nigeria, za a yi wahala a samu ya su, kama daga dukiya,da tsaro, saboda tsaron da suke samu in Sun samu amincewar iyayen su har su ka fita, to sai mutum ya rantse Gwamna ne da kan shi ke yawo, motocin sojoji da 'yan sanda ne kawai mutum zai hango su na biye da su dik inda suka dosa. Yau kusan sati biyu kenan, Sultana na roqar mahaifiyar ta da su bata dama ta fara aiki itama, dan kasar ta ta mori ilimin da Allah ya hore mata, yau ma kamar kullum, Hajiya Ikee shiru ta mata ta ci gaba da ɗaukan inibin ta ta na jefawa a baki, hankali kwance, qafar ta kuwa mai aikin su ce Me Buruji ke matsa mata, kan ta a qasa, saboda tsoron had'a ido da uwar gidan nata. Cikin tausaya wa Sultana ta ce, " Baaba je ki kitchen za mu yi magana da Hajiya" "To ran ki shi dade" A duqe ta miqe kamar wadda take a fadar matar sarki. Da sauri Hajiya Ikee ta kalli Sultana ta ce, "Na hwa san mi kike yi Sultana ,wato Ina Sanya Me Buruji wahala ko? Shi na kin ka kore ta, tau ki kiyaye ni, kar ki koma yi min haka nan, and da ki ke damu na akan ki hwara aiki,Ni misshamin kai da aikin ki? Daddyn ku ya ce ba za ku yi aiki ba, kuma na goyi da bayan shi, % saboda ku ba diyan talaka kuke ba, albashin ga dai in shi ki ka bida ana baki duk wata, dangi ma aka basu albashi ba tare da sun tai aikin komi ba balle ke? Daga yau kar ke ko dan uwan ki ku sake tunkara ta da wanga batu, kin ishen da d'umin banza, haba" Cikin fushi ta tashi za ta bar tafkeke kuma qayataccen parlourn na su, wanda tsayawa ma fadin had'uwar shi, bata lokacin mai karatu ne. Da sauri Sultana ta rungume Mahaifiyar tata ta baya, tare da dora kan ta a saman bayan ta, cikin kalamai masu sauqi Sultana ke magana. "Mum Dan Allah ki hakuri, indai ni ta, ban koma yin magana akan aiki, zan hakura, ba zan sake maganar ba, ki dena hushi pls" Juyawa ta Yi ta na Dan murmishi, sannan ta zauna a kujerar da ta tashi, sannan ta ce, "Ni wallah mamaki kuke ban diyan ga, kamar ba kuyi karatu qasar waje ba, kamar wadan da sun ka yi cudanya da talakawa, Allah ya daukaka ku, amma kullum burin ku bai wuce ku ga kun wulaqanta kanun ku ba," Murmushin takaici Sultana ta yi, dan ta san in tai magana, yanzu ran mahaifiyar ta zai qara ɓaci. Amma tabbas ko a dangi ana mamakin yanayin tarbiyyar su, wadda ta sha bam_bam da ta iyayen su. Su kuwa ba su ga abun mamaki ba, dan sun san yanda akai suka samu tarbiyyar nan, sannan sun sani Ubangiji Allah ya na yin yadda ya so, a sanda ya so ba tare da neman izinin kowa ba, sun sani da izinin shi, da ikon shi ne suka zamo yara na gari, tarbiyyar da suke da ita ta sha banban da halayyar iyayen su. Lokacin da aka kai su Sultana makaranta a qasar waje, sun kammala primary a nan Nigeria a Abuja, makarantar hade take da islamiyya, mai matuqar tsada ce, dan haka yara suna samun ilimi na kowane fanni, sun haddace qur'ani tun su na Nigeria, wanda iyayen su ma basu wani damu da hakan ba, fatan su su samu kyakkyawan result da zai kai yaran babbar makarantar gaba da primary, dake qasar turawa. Kuma sun samu nasarar hakan, an kai su makarantar gaba da Sakandire a London,ba su samu damar ci gaba da karatun Islama ba, sai bayan da suka shiga jami'a lokacin hankali ya shige su, Sultan ya ga haddar su na zubewa, shi ne ya sama masu wani malami Bature ne,amma Musulmi masanin addini sosai, ya ke koyar da su addinin su, ba tare da mahaifan sun wani damu ba, su dai abinda suka fi damuwa da shi shine, yaran su su zama masu ilimin boko, ta yanda daraja da qima, tare da ajin su zai dagu a cikin sa'annin su. Hira suka ci gaba da yi, amma ran Sultana ba bu dadi, ta so matuqa ta yi lecturing shi ne babban burin ta a rayuwa. ********************** Me Buruji na komawa bangaren masu aiki,ta ja hannun kishiyar ta me suna Lamishi, suka koma gefe,nan ta labarta mata me ya faru a ciki, kama baki Lamishi ta yi, sannan t ce, "Ohhh diyan ga na Gwauna ba su samu iyayen kwarai ba wallah, wadda ki ka san ba su na sun ka haihe su ba, Allah shi kyauta, mu je ki isuwa aikin ki, da kin ka tai kin ka bari, walle ban qarasa maki,Nima nawwa ya isan" "Lamishi hoo, yanzu dan goge kici (kitchen) din shi abbaki iya isuwa mini?" "Ke walle ban iyawa, tai dai ki isuwa, yanzu ki na gamawa mu tai gida,wancan dan mutuwar zuciyan da yaran shi na can na jiran mu samo mu kai musu su lasa, bada aniya ki isuwa (kammala,gamawa) mu ta tahiya gida" Ba bu bata lokaci kuwa Me Buruji ta kammala aikin ta, suka yi wa sauran ma'aikatan sallama, dauke da ledojin da suka cika da abincin da aka ci aka rage, sai masu aiki su tattara su raba a tsakanin su, saboda yawan abincin da kuma kala kalan wanda ake dafawa, shi ya sa yake isar masu aikin, watarana ko sun dafa nasu, na masu aiki, se dai su tafi da shi, gidajen su. Sai da suka tsaya a gate aka duba kayan su, sannan suka fita. Dan sahu suka tsayar suka dauki hanyar unguwar su da ke a TUDUN FAILA. A qofar gida suka tadda mijin su, zaune da abokan shi, suna manne da gini, sanye da wasu jemammun tufafi, mijin su na hango su ya washe baki, ya dago daga jikin katangar ya na lashe busassun labban shi. Lamishi ce ta saki guntun tsaki ta ce, "Kalli mijin ki,mai matacciyar zuciya, sai wani lashe baki shi kai awaw-wani baqin maye, sun bi sun wani maqale ga gina awwad-dangin qadangaru....kaiii Allah shi wadaran wanga mutuwar zucciya walle" "Ameen ke dai" Ko gaishe da abokan mijin nasu ba su yi ba suka fada gidan, su na jin su na gaishe su, tare da yi masu sanu amma ko kallo ba su ishe su ba, bata rai Dan Talo ya yi, ya tattare qasan rigar shi ya afka cikin gidan nasu ya na fadin. "Ina zuwa na iskamma wadan can lalatatun, ba dan na amince ba ko titin gidan Gwauna ba ku bi wallah, dan tsabar raini, abukkai na za ku walaqantawa haka? To ba wata sheeee....." Maganar shi ce ta maqale, ganin wata sharbebiyar kaza na maiqo, Lamishi na aje wa a farantin silver. Kallon shi suka yi a tare cikin daure fuska, Lamishi ta ce, "Ba wata sheee me?" Cikin inda inda Dan Talo ya ce, "Ba wata 'yar shimi na sauya? Zahi ni ka ji yau" "Ahayyyeeeeee, ayyuuuriiiriiiii, Dan Talo amanar Lamishi da Me Buruji " Tafawa suka yi, shi kuma ya hau yaqe, dan ya san sun fahimci kwana ya sha....... Ku dakace Ni a shafi na gaba, dan jin yanda zata kaya... Comment Vote Share. A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 2: Babu zuciya haka Dan Talo ya durqusa a gaban matan shi ,yawu na qoqarin zuba masa, sai surutu ya ke zubawa, mara ma'ana. "Koni dun Allah Yi ki sallame shi, shi ta tahiya,ya cika min kunne da d'umin banza" a cewar Mai Buruji da ta ke wurga wa Dan Talo harara. (Ni dak dan Allah ki yi ki sallame shi ya cika ni da surutun banza) "Wa ka d'umin banza? Walle matar ga kin rammin, (raina Ni) tauu ya yi, in ta qamar iskanci da rashin kunya kka ji, na dame ki na shanye, ke sani ko?" "Ahayyyee, Ni ko nissani,tunda ga qarshen rashin kunya, ka tsaya mata su bido su kawo, ka canye, ka sude hannu,da ka qare ka ishe mu da jininin yohi" Miqa masa kwano Lamishi ta yi da abinci, tini ya rufe bakin shi, ya karbi kwanon ya yi waje, ya na fadin, "Ina zuwa, bari na isuwa cin abinci za ki maimaita abinda ki ka hwada" "Haka nan aka iya,namijin hotiho" Lamishi da ta dawo daga ajiye abincin yaran su ne, ta dangwara kwanon nasu abincin a gaban Mai Buruji ,ta zauna, tare da fadin , "Ke dai ba ki gajiya da jayo mana wancan dan na gaji jininin (mita) shi zo shi aza mana cin mutunci, se rai ya yi ta ɓaci" Dariya kawai Mai Buruji ta fara, ta na kai lomar shinkafa bakin ta, sallama aka rangada, tare da fadin, "Mutanen gidan na nan kuwa?" "'Yakkwadai(kwad'ayayyiya) , ke duk san muna nan daidai wanga lokaci, shigo mu ci" "Ba ka qi ta mutum ba ai, abinci abokin kowa na wallah" Ba Bismillah ba komai,haka matar da ake kira da 'Yabbuga ta danna hannun ta a kwano, ta fara kai lomar shinkafa bakin ta, ta na ci ta na qoqarin basu labari . "Dan Allah dai ki bar d'umin ga, ki na maisuwa mana na baki," "Akwai labari" "Ai mun san ba a rasa nono a riga" Fatali ya yi da butar da ke saman hanyar shiga cikin gidan , cikin maye da kirari, da kuranta kan shi ya ke magana, daga qarshe ya zabga wani ihun da ya sanya 'Yabbuga kwarewa da shinkafa,tsabar tsoro, sai tari ta ke son ta maqale ya qi maqaluwa, "Lawwali yanzu tsakanin ka da Allah hwashe min buta zakai ka tafi ka barni da sayen sabuwa? Ka..." "Ina abinci naaa...yunwa nake ji...ciki na ba komai kamar tekun da ta qafe haka nake ji na" "Shi na kici tai ka dauka, lalataccen banza" Wata zabura ya yi, kamar ba shi ne ya shiga a bige ba, ya zaro wata sharbebiyar wuqa,ya goga a qasa, tare da zuba wani uban ihu, 'Yabbuga ta zabura ta runtuma dakin Lamishi a guje ta na fadin, "Tsautsayi ya kawo ni gidan ga, Lawwali na gari, da na san ya na gari da ban zo kwadan banza ba, yau bone ya ci ni, Allah ka taimake ni na hita gidan ga lahiya," Jikin ta sai rawa ya ke, zufa na karyo mata, a rayuwar ta ko Allahn da ya halicce ta bata tsoro kamar yanda take tsoron Lawwali,tunda ko salloli biyar basu dame ta ta tsaida su ba, yanda take tsaida gulma da munafurci a unguwar, Lawwali ya farke mutum ya bace a neme shi sama ko qasa a rasa ba wani abu bane a wajen shi , ko da an kama shi, ba ya kwana a cell , a ranar ze fito, kuma wanda ya sa aka kama shi, ya jawa kan shi masifa. Shi ya sa ma, mutane suka hakura da kai shi qara wajen hukuma. Abincin shi ya dauka, ya fita zuwa dakin shi da ke zauren gidan, ya na fito,wata ajiyar zuciya 'Yabbuga ta sauke, tare da qarasa sude hannun ta da ta ci abinci, leqe ta ke ta window dan ganin shin ya tafi ko yana nan? Ta na ganin fitar shi ta yi wuf ta fito itama, takalman ta a hannu, ta bar gidan, cikin sanda kar ya fita su gamu, Lamishi na mata magana, akan ta tsaya ta fesa masu me ya faru a shiyya da basu nan, ta ce su same ta a gida. Kwata-kwata bata son dik wani abu da zai hada ta da Lawwali, saboda Lawwali na da daurin gindi matuqa a wajen manyan mutane sosai,saboda rashin tsoron shi, da cika masu duk wani aiki da suka saka shi. Sun dauke shi a matsayin wata kadara tasu mai amfani da mahimmanci,da suke kula da ita da dukiya, da qarfin mulki da ikon su, dan kar wani abu ya same shi. Lawwali shi ne babban d'an Lamishi wadda ita ce uwar gidan Dan Talo, masu bi mashi mata ne guda uku, Rakiya, Ashibi, da Lami, dikkanin su suna dakin mazan su, sai autar Lamishi mai suna Mubaraka. Mai Buruji na da yara biyu maza, Kamilu da Jamilu. Dik yaran gidan ba wanda ya yi makarantar islamiyya balle ta boko, in ba Mubaraka ba, ita kadai ce ta ke zuwa islamiyya da kuma boko, da kyar ta samu Lamishi ta amince, tare da sanya bakin Lawwali, dan ya na mutuwar son qanwar shi, ba ya son dik wani abu da zai taba ta. Duk abinda ta ke so,sai ta bi ta hannun shi ta ke samu, ba dan komai ba sai dan ban-bancin ra'ayi da d'abi'a da ta ke da shi da mutanen gidan. Shekarar ta sha shida, amma ta matsu ta yi aure itama kamar sauran yayun ta, ta bar ma su Lamishi gidan, su yi ta jahilcin su. Kusan kowanne gida ana samun irin wannan, yaron da ya fi biyayya, ya fi sanin ya kamata, da ciwon kan shi, ya fi shan wahala, tsangwama wajen iyaye da 'yan uwa, ya fi shan aiki, da kuma rashin samun kulawa, balle a kai ga gode masa. Haka ce ke faruwa da Mubaraka a cikin gidan su, wajen Lawwali kawai take samun yabo, da soyayya ,har ma da kyauta, lokuta da dama, har mamaki take, anya Lamishi ce mahaifiyar ta? Amma kamannin su kad'ai sun tabbatar da hakan,Mubaraka, irin yaran nan ne, baqaqe masu madaidaicin kyau, ba ta da wani shahararren kyau, amma saboda kyaun hali da d'abi'un ta, mutum ba zai gaji da zama da ita ba. Sallama ta yi, tare da murmushi mai annuri, ta shiga gidan, ba komai ya sa ta murmushi ba, sai ganin yayan ta a gida. Har sun gaisa, ya bata tsarabar da ya kawo mata,ta littattafai da biskit, da alawowi, ya na bata, ya rufe dakin na shi da ke soron gidan ya yi gaba, dama ita ya ke jira. Ba tare da sun amsa sallamar ta ba, Lamishi ta kalli sabuwar ledar da ke hannun ta ta ce, "Ke mi nana wannan ga hannun ki?" Cikin doki da murna Mubaraka ta ce, "Tsaraba ta ce da Yah Auwal ya kawo min" "Kawo ta nan,Lawwali ka bata yarinyar ga wallah, bashi da aiki sai bannar kudi nai a harikar banza, ai ta siyan takardun da ba su da anhwani" Da fari ko kadan Mubaraka ranta bai ɓaci ba da Lamishi ta ce ta kai tsarabar, dan dama ko bata ce ba, ba zata ci komai ita daya ba, amma zagar mata takardu da karatun ta, anan ake samun matsala da ita, nan da nan kuwa ta tura baki, alamar ran ta ya baci. "Kina barin turo shegen goshi awad-diyar jakka, bani nan" Amshe ledar ta yi, ta wurga mata littafan ta a qasa, ita kuma ta na bi ta na kwashe wa, cikin qunar rai, ko biskit din bata tsaya amsa ba t shige dakin su. A nan take suka rabe har da qawayen su da suke nunawa kalar azziqin da suke da shi a unguwa, yamma kawai suke jira ta qarasa yi, kafin nan,kowacce daki ta shiga babu sallah babu salati, suka kwanta,suna jiran la'asar ta yi........... *A GARIN MU* WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 3: Allah ya halicci duniyar nan kusan komai guda biyu ne, misali,da ya yi duniya sai kuma ya yi lahira,mace da namiji, mutum da aljan, mai kyau da mara kyau. Unguwar TUDUN FAILA itama ta qunshi mutane kashi-kashi, akwai mutanen kirki, akwai na banza, a kuma kwai 'yan ba ruwan mu da kowa. Mutanen kirkin da ke unguwar TUDUN FAILA sun fi na banza yawa, amma ya na daga d'abi'ar dan Adam, bayyana mummuna, ya boye kyakkyawa, wannan dalili ne ya sanya mutanen kirkin unguwar suka ware kan su daga cikin irin su Dan Talo, da matan shi. Bahaushe ya ce, wake d'aya ke bata gari. Lamishi ce ta fito, cikin wata atampa, mai kyau, da hijabi kalar kayan ta, takalmin ta baqi, sai 'yar wayar ta a hannu, ta kalli qofar dakin Mai Buruji ta yi tsaki, sannan ta ce, "Kedai akwai malalaciyar mata, komai saurin da ake sai kin bata wa mutane lokaci, Allah shi cece ki kar a tashi tahiya Makka ki makara, walle jirgi tahiyasshi zai shi barki, ba ruwa nai, dan ba ya jiran kowa" Cikin dariya Mai Buruji ta fito sanye da ta ta shigar kamar wadan da za su biki, ko suna. Kallon ta Lamishi ta yi, ta miqa mata hannu suka tafa, sannan suka sanya dariya kamar wasu yara. "Mika saki dariya halan?" "Idon mutuniyar nih-hango, dut ta walqita taga tuwahin (kaya) ga sai hankalin ta ya tashi" Sake sanya dariya suka yi, suka sa kai za su fita, Kamalu dan Mai Buruji ne ya dawo, ya yi fururu da shi, dika dika ba zai wuce sha uku ba, shegen yawo ne da shi,baya son zaman gida sam, dan Uwan shi Jameelu mai shekara sha biyar tun tuni ya koma ya ci abinci, ya kwanta, har wannan lokacin ya na ciki ya na bacci, amma Kamalu zai iya kaiwa sha daya na dare a waje, watarana shi ke rufe gidan. "Ja'iri,yunwa taddawo da kai gida, da ka samu inda kacci abinci ma na san sai dare aka ganin ka," Duqar da kan shi yayi, ya kauce wa dukan da Lamishi ta kai masa, ya na dariya. Ciki ya shige su kuma suka fita, tun daga nesa suke hango wasu mata guda biyu zaune qasan wata bishiyar darbejiya mai yalwar ganye, da ni'ima, zazzaune suke saman duwatsun da ke wajen. Daga nesa 'Yabbuga ke wara ido dan ganin sunan atampar da su Lamishi suka sanya,bata samu nasarar ganin qasan ba, saboda an kalmashe an dinke, su na zama kuwa ta kai hannu jikin Mai Buruji da tafi kusa da ita, cikin dabara ta shafi atampar ta na masu sannu da zuwa. "Sa'idawa, shahwa da kyau wallah, super ta ba komi ba, sabuwar ta mun ka sanya ba kwance ba, ko ita ma ki na saye ne?" "Yo in da kudin kuturu alkaki ai sai na qasan kwano ko?" cewar 'Yabbuga da ta qule saboda gano ta da suka yi. "Ahayyyyeee,Allah gani inji gurguwa, watarana kau kuturu zai hadiyi yawu da quda,dan wani alkakin na sarakai ne,ba na siyan gama gari bane...keni rabu dani da d'umin banza, bamu labari mi na na ki ka son hwada mana dazu ki ka ga dodon ki,ki ka gudu" Wadda ake kira da Ta Yahai (Yahya kenan) ita ce cikin dariya ta ce, "'Dana ya shigo gari kenan, dan albarka me maganin munahukan shiyya" Dariya suka sanya, Yabbuga kuwa rai ta bata, dan ta san ci mata fuska suke, sun san yanda take tsoron Lawwali. "Ke rabu da Ta Yahai, bamu musha" In ji Lamishi da ta qagu ta ji me' Yabbugan zata fada masu. Zama ta gyara dan jin an sosa mata inda ya dame ta da qaiqayi. "Hummm na taba ku da alheri, kishiya ta taɓa kishiya da bakin wuta....jiya akai dirama a kwarkwadar mu, tsakar dare nijji ana ihu, ana bada hankuri, nittashi zaune ni da Dan Jumma, ko da mun ka saurara, ashe mutuniyar aka liqa wa mugun kashi," "Kaiii wanga mutuni ba dan Sunnah bane, mi tai Mai halan?" Cewar Mai Buruji da ta matsa daf da Yabbuga tsabar son jin gulma . "Yo ai abun ba sabo bane, sun yini ba bu ko kwayar hatsi,dare ya yi,ya tai amsar haqqi nai ta hana, shi ko yabbuge banza, ya amshi abi nai, ya barta nan ta na kuwwar banza" "Ohhhh wanga shi aka kira qarfin hali, a dake ka kuma a hana ka kuka, gaskiya mutunin ga azzalumi na" Lamishi da ta qi jinin ta ji ana wulaqanta mace ta fadi hakan, lokuta da dama ji take da ace su na magana da Hansatun Isa da sai ta mata magana, ta koya mata yanda zata kwaci 'yancin ta wajen Isa, ko ya hakura da mugun halin shi su zauna lafiya. To amma Hansatu ta kame kan ta, mace ce mai kame wa matuqa, da kiyaye dik wani abu da zai hada ta hulda da su Yabbuga, tunda ta san halin su. Su na nan su na gulmar ta, ta na gida ta na fama da matsanancin ciwon qirji, ba komai ne ya kawo mata shi ba, illa rashin cin abinci, yaran ta ta kalla guda uku, biyu mata ,daya namiji, suna ta kai loma, hannu baka, hannu kwarya, akan qanzon da ta masu fate da shi. Lallabawa ta yi ta dan debi loma daya ta kai bakin ta, wani irin zafi da murdawa qirjin nata ya yi, sai da ta durqusa,tare da rintse ido, hawaye ne suka sauka mata, da sauri ta share,dan kar yaran su gani,bata samu nasara ba kuwa, qaramin yaron ta mai shekara hudu ya ga sanda ta ke share hawayen,dakatar da cin abincin ya yi, ya ce, "Umma sannu, qirjin ki na ka ciyo?" Cikin murmushin yaqe ta ce, "Eh shi na ka ciyo Ahmad, amma yayi sauqi, kaga Ni ma har na tashi ? Maza ka ci abincin ka yaron kirkin Ummaa,ku ta tahiya makarantar Allah" "To Umma" Amina da Bilkisu ma sannu suka mata, sannan suka dauki dan sauran faten da suka rage, suka aje a gaban ta, suka ce sun qoshi. "Abincin da ba shi da yawa, ku canye shi maza, kahin ku dawo,inshaa Allahu zan sama mana wani abun, ku canye ku tafi makarantar Allah maza" Qin ci suka yi, tare da barin kwanon a gaban ta suka tafi da gudu wanke hannu, suna gama wankewa, Amina mai shekara goma,ta shirya Ahmad cikin wasu yagaggun uniform din da sun dage masa, ita kuma hijabi kawai ta saka tamiqawa Bilkisu mai shekaru takwas nata hijabin, su na kammala sakawa suka yi wa umman su sallama suka fita, bakin su dauke da addu'a . Ta gaban su Mai Buruji yaran suka wuce, sai da suka gaishe su sannan suka tafi,amsawa sukai su na bin su da kallo. "Dazu fa Baban su har da shi a garkar mu, wajen cin abinci" "Ai wadda kika san dan shi d'ai muka zuwa aiki,kullum shi na garkar mu, da ya qare cin abinci shi tai yawo" Yabbuga ce ta karkace zata yanko wata gulmar Isa ya taho zai shige gida,cikin izza da isa da taqama ya ke tafiya , wanda be san shi ba zai rantse wani namijin azziqin ne. Har su na rige rigen gaida shi ,juyawa ya yi, ya amsa tare da tsokanar su Lamishi . "Ah ah matan Dan Talo kenan, irin wanga gayu haka awaz-zaku biki? Ko dake masu hidima gidan Gwauna ai dole ku wataya " Murmushi suka yi, su na irin abun nan na mata in an yabe su, Yabbuga kuwa tsaki ta ja, sannan ta ce, "Haramun dai, ka tsaya yabon matan wani, ka baro ta gida ba yabo" "Yabbuga kishi takai da ku wallah, kun San bata iya ganin wani ya yi abu, batai ba" Dariya suka sanya har da shewa, ya shige gida,ya bar Yabbuga da mita. Kafin ya qarasa shiga ya daure fuska tamau kamar ba shi ne ya gama hira da matan wasu a waje ba....... A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 4: Jin motsin shi ne ya san ya ta miqe wa da kyar, hankalin ta tashe, domin shi din kamar wani dan aiken mutuwa n ne a gare ta, rashin fitar ta tsakar gida zai iya ja mata masifa a wajen mijin nata da take tsananin so da qauna. Murmushin yaqe ta sanya a labban ta, tare da yi masa sannu da zuwa, bai amsa ba, sai shura buta da ya yi da qafar shi ta hagu, cikin wani irin mummunan yanayi ya juya ya kalle ta, yawu ta hadiya da kyar, cike da tsoro, bakin ta na rawa ta ce, "Ka yi hankuri, su Amina na sun ka wanke hannu, Na....naaa manta ban zuba ruwa ba" "Zaki debo min ruwa ko surutun banza za ki tsaya yi min?" Da sauri ta tafi daukan butar, kafin ta sa hannu ta dauka ya tura mata da qafa, dan baya ta ja saboda kar ta bige ta, sannan ta duqa ta dauki butar, wajen diban ruwan daidai inda yake a tsaye ne, ya diba kawai, amma sai ya wahalar da ita. Ta na gama zubawa ta duqa ta fara zuba masa, qamshin miya ta ji a hannayen shi a lokacin da ya tara su gaban ta dan ta zuba masa ruwa. Murmushi mai ciwo ta yi, ta tabbata yau ma ya ci abinci a waje, ba tare da ya damu da ita ko yara sun ci ko basu ci ba. "Baban Amina, nicce akwai dan kuddi wajen ka na dahwa muna abinci?  Yau kwana uku ba mu ci abincin kirki ba, dazu ma qanzo na nissamo gidan Yabbuga niddahwa mun ka ci, kuma da alama yaran nan basu qoshi ba" Hannayen shi ya sanya a qugun shi ya na kallon ta, irin kallon nan mai kidimar da wanda ake kallo, ta gigice matuqa, dan bata san me zai je ya zo ba, amma koma mene ne, bata da zabi, dole shi ne zai kula da su, shi ne zai yi mata duk wani abu da take buqata ita da yaran su . "Kin raina Ni ko? Na ce kin raina Ni ko? Kin fara min tambayar titsiye ko? To ina da kudi,kin gan su, ba zan bayar ba" Hannu ya sanya a aljihun shi ya zaro dari bakwai, ya nuna mata, sannan ya miqa su daidai fuskar ta, "Ko zaki kwata ne? Tunda na ga kin yi qarfin halin yi min magana yanzu, ban sani ba ko kin yi qarfin duka na ki amshi abu a hannu na ne" Kada kai take ta yi, tare da fadin, "Ah ah, ka yi hankuri, ba haka nika nuhi ba" "Hansatu , Hansatu, Hansatu ki kiyayen, kar ki bari na juyo kan ki ba zaki ji dadi ba" Duqar da kan ta tayi, tare da share majinar da ke diga daga hancin ta, saboda kukan zuci da take, Daki ya shige, ran shi a matuqar bace. Babban abinda ya ban mamaki, haushi, da tausai shi ne, kwano ne ajiye a wata shimfida, abinci ne a ciki, kalar wanda ta bawa yaran ta da rana, duk yunwar da take ji, bata iya ci ba, sai da ta aje masa. Dan mugunta irin ta Isa dauka ya yi, ya fara ci, sai da ya cinye tass ya sude kwanon ya yi fatali da shi ya bar gidan. Qarfe biyar da rabi, ta rasa ya zata yi, dan haka mayafi ta dauka, ta yafa a saman kan ta, sannan ta saka takalmin ta silifa da ya sude, ya ke qoqarin bulewa. Jan qofar gidan ta yi, ta nufi dandalin gulmar su Lamishi, duk wanda ya kalle ta da kyau zai tabbata ta sha kuka, amma ya zatai, ba zata iya boye yanayin da take ciki ba, tunda mai rufa mata asirin ya tone shi kowa ya san halin da suke ciki,  (ba mai rufa asiri sai Allah). Ta na zuwa ta Gaishe su, dikkan su amsa wa sukai, cikin zumudin son jin me ya faru, ba wai dan su taimaka mata ba. Shiru ta yi, can suka ci gaba da hirar su, amma hankalin su na kan ta, gani ta yi lokaci na tafiya, cikin sanyin murya ta ce, "Uhmmm... Nicce ko akwai wadda ke da wanki cikin ku? Ku kawo na hwara na kuddi, amma za a hada da kuddin wanki da klin da toka(sabulu) " Kusan a tare suka hada baki suka ce babu, ji ta yi kamar an daki zuciyar ta, da me za su ci abinci dare? "Ko wani aiki ba ku da shi? Wanda zan yi ku biya Ni?" Lamishi ce ta ja ta  gefe, ta ce, "Ina da wankau, amma fa na yau ne kawai zan baki, ba wai kullum zaki zanka(dinga) yi min wanki ba" Kamar ta durqusa a qasa ta gode mata, haka Hansatu ta hau godiya. Gidan Dan Talo suka koma , Lamishi ta bata wankin, ta bata kudin omo da sabulu, ta biya ta ladan wanki dari uku, godiya ta dinga yi har da kwallar ta. Ɗaukan wankin ta yi a ka ta yi shago, ta auni wake, dan ya fi arha, kuma in ta dafa za su jima suna shan ruwa in an ci, ta sai man ja ta sai  maggi, ta sai omo da sabulu, sanan ta yi gida. A hanyar ta ta komawa gida, ta ga dandalin su Lamishi suna nan suna hira, kafin ta qarasa ta ji Lamishi na basu labari  taimakon da ta mata, ran ta ya baci, amma ba yanda ta iya, wanda ya ajiye ta shi ya ja mata komai, ta na yin kusa da su sukai shiru, kamar ba su ke magana ba. Gidan ta ta shige, ta ɗora tukunya ta wanke wake ta jiqa tokar murhu kadan ta zuba dan ya dahu da wuri, itacen ba yawa, fatan ta Allah ya sa ya dahu da wuri, ba dan yaran sun kusan dawowa ba da jiqa waken zata fara, ta rage asarar ice. Bokiti ta dauka ta je ta roqi Yabbuga akan za ta debi ruwa a rijiyar gidan ta, cikin daure fuska ta ce ta je ta diba, godiya ta yi, ta shiga ta dinga jidar ruwa, qirjin ta na matsanancin ciwo, amma ba yanda za ta yi, dole hakuri za ta yi, ta nemawa yaran ta abin da za su ci. Ta na fitowa daga gidan Yabbuga ta ji ta na fadin. "Kuuu ban baku labari ba, kun kuwa san an yi baquwa a shiyyar ga tamu? Humm in kun gane(in kun ganta) ta baqa awab-baqar talle (kamar baqar tukunyar miya) , mijin ta ko kyakkyawa, nicce wanga mi yaggani da ya kwaso mace hakan ga awak-kuddi (kamar kudin shi basu cika ba) nai basu cika ba" Dariya suka sanya da shewa , suka tafa, "Yabbuga idon duniya, ta wanne bangare gidan yake gobe in su Lamishi sun taso aiki mu tai ganin gida ?" "Can bayan gidan su Lamishin ne ai, sai kun ga gidan , wayyooo aljannar duniya kenan, gidan da nika mahwalkin samu Allah yabbatar, babu komi, su ci anan, mu ci a can" "Ke haba na gane gidan, gidan nan me dan banzan kyau, ashe an tare" "Shi hwa ni ka batu" Lamishi na qoqarin magana Yabbuga ta jiyo qarar machine din Dan Jumma, da wata iriyar alkafura ta hantsila ta fada gidan ta, dariya suka fara yi, suna fadin , "Shegiyar za ta yi tsiya kenan,duk ka ga Yabbuga ta shiga gida bata son Dan Jumma ya gan ta nan, to akwai tsiya" "Ina yini Dan Jumma ?" Cikin daure fuska ya amsa ya shige, bai jira jin me za su fada ba, cikin qunar rai, dan ya san dole Yabbuga ma na wajen, sai dai guduwa ta yi da ta ji shi. Sallama ya rangada, tare da jingine machine din shi, ya cire yar ledar da ke jikin hannun machine din, ya taka zuwa bakin qofar dakin nasu, kwance take abun ta, ta na jin shi ya na sallama ta qi amsawa. Murmushi ya Yi, dan kuwa ya san halin kayan shi, ajiye ledar ya yi, ya zauna tare da bude kwanon abincin da ke gaban shi, shinkafar ce dai da miya, kullum abincin kenan, in an sauya kuwa to tuwo ne, in ya kawo taliya ko wani kalar abincin sai ta dafe lokaci daya ta raba wa qawaye ta nuna masu itama ana cin dadi gidan ta, ba wai dan ta samu lada ba. Budewa ya yi ya fara ci bayan ya yi Bismillah, "Au ka na gani ina hushi ba za ka kula Ni ba ko? Tauu ya yi, ci abincin ka ka qoshi da kyau, ya yi" ta juya baya ta na zumbura baki, ita a dole fushi take. Dan Jumma bai kula ta ba, sai da ya ci abincin shi sanan ya tattara hankalin shi zuwa gare ta...... A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 5: "Ina sauraron ki sarauniyar mata, mi am-matsalar ki yau Kuma?" "Auuu ni ce matsalar ma ko? Tau ya yi" "Kin dai san ba haka nika nuhi ba ko? Ina so na San damuwar ki, da har zan sallama ki qi amsa min ki na musulma" "Suhwa nika so"(super na ke so.. Atampa) "Me ne ne haka nan? (Me ne ne hakan)" "Atanhwa suhwa nika so," (atampa super nake so) "Ai ko aiki ya gane ki wallah, ni da nike qaramin ma'aikacin da rabo na da albashi yau wata biyu, haka d'ai sai ni kama sai maki wata super Dan dai ban da hankali ko?  To mi za mu ci in kin Sanya super?" Kuka Yabbuga ta saka, har da Kiran ta shiga uku, tsiyar auren talaka kenan, bata rai Dan Jumma ya yi sosai ya kalle ta, "Ni ki ke kira da talaka yau Kuma Yabbuga? Lallai mace akwai ta da mance alkhairi, ke manta sanda nike da walwala, ke mance sanda nike da azziqin da kk Shan gatan da ba bu ya ke a cikin tsarar ki? Ke fa ba qaramar yarinya bace, karki manta bara waccan anka kai Kareema d'aki, yanzu haka ciki gare ta, kin kusa kai wa ga jika, shi na ki ke Wagga baqar tabi'a" "Ni ke baqar  d'abi'a ko kai? Yanzu ace yar super ga ba ka iya sai min? Shin ta Ina ka bi ka shigo gidan ga? Ba ka ga su Lamishi a waje bane?ko ba ka ga irin tuwahin da ke jikin su ba ne? Nan Nan Isa da yaggane su sai da ya tsaya ya yabe su, ni matar ka Kuma maqotan shi kallo ban ishe shi ba" Wani irin zabura Dan Jumma ya yi, tare da kallon Yabbuga a yanayi na tashin hankali. "Mi na na ki ka ce, Isa ya gane  ku bai yaba tuwahin ki ba ,shi ka banna maki rayuwa hakan ga?(Isa ya gan ku be yaba kayan ki ba shi ke bata maki rai?) Ashe dama Isa ki ka aure ba Dan Jumma ba? To ki tai Isa shi sai maki super Yabbuga na Yi masallaci" "Walle ba ka Isa ka juyan magana ka tafi ba, ka San ba haka nika nuhi ba, super ko sai ka siye ta gidan ga, kahin ka ga hwari na," "Irin wanga halin da ki ke shi Kareema ta koya, daga yin aure mijin ta ya kawo qara ya hi sau bakwai, kwanaki ba koro ta ya yi ba da ya gaji da bani bani da sai min? Da girman ki amma ki na wanga mummunan hali, ba lehin ki na ba, lehi na na, da a baya niyyi zamanin sai maki duk wani abu da aka yayi, maimakon yanzu da Banda shi ki hakura ki San na kyautata maki a baya, shi na kk hango na sama da ke, se ki fada min, da su Lamishin Basu aiki gidan Gwauna Ina na zasu samu kwancen tsohuwar super ma balle sabuwa? Sannan  da ki ke gasa da Lamishi, ai Lamishi ta ciri tuta tunda ta iya zama da kishiya, me ya sa baki gasa da ita ta nan ba? Gashi can su na zaune lahiya kamar Yaya da qauna" "Babbar batasin Nan, ni ka ke kalla ka yi min batun kishiya Dan Jumma? Ashe ka daina so na? Ka San ya akai Suka hwara zaman lahiyar ne ? Ai na dole ne, tunda Mai Buruji ta hwara rashin nasihwa(rashin mutunci) , ta ga bata diban komai jikin Lamishi, shi na aka zauna lahiya, Kuma indai batun suhwa ne Dan Jumma yassa ka min batun kishiya riqe suhwar ka, banni so, amma ka sani kai da ka samu kwaciyar hankali gidan ga sai na huce haushi na" "Ga leda nan na shigo maki da ita, huce haushin ki saman ta" Alwala ya fita waje ya yi, ya wuce masallaci, qofar gidan ba kowa dik su Lamishi sun tafi,bayan sun gama jin drama da akai a gidan, ko a gida ma labarin da sukai ta yi kenan. Hansatu kuwa bayan ta gama dafa wake,ta soya man ba ko albasa, ta zuba ita da yaran, ta aje ma Isa na shi, da ruwan sha, a shimfidar shi da yake zama, a tare Suka ci da yaran ta, suka qoshi, kowa ya Sha ruwa, cikin hamdala, sai annashuwa da murna suke, ga wani Nan ta Dan rage da safe ta zafafa (dumama) musu su ci. Ta na idar da sallah ta hau wankin Lamishi, bata tashi ba sai da ta gama shi tsaf. Ta shanya, lokaci ne na iska, bata kwanta ba sai da ta ninke su ninkin guga ta daure ta ajiye, qarfe Sha d'aya saura, hamma ta ke ta dokawa, ta gaji matuqa, ga shi har wannn lokacin qirjin ta bai daina ciwo ba, ya dai rage ne kawai. Dan kishingid'a ta yi a tsakiyar yaran ta da ke kwance a parlour , Nan da Nan kuwa bacci Mai dadi ya share ta. Bata sani ba, shin ta jima ta na baccin ko kuwa? Kawai dai taji an take qafar ta ne, har sau biyu, tsabar mugunta, ba zai durqusa ya tashe ta ba, sai dai ya take qafar ta. Da sauri ta janye qafar tare da miqewa ta na masa sannu da zuwa. Amsawa ya yi ciki ciki, ya qaqalo murmushin dole, Wanda ya Sanya gaban Hansatu faduwa da qarfi, Dan ta San ma'anar shi, taba wuyan ta tayi, ta ji shi zafi rau, ta San ba komai ya ja ba sai aikin da ta Sha, ga ciwon qirji na damun ta, gashi ta yi aiki cikin iskar da ke kadawa me sanyi. Kwallar ta ta mayar, ta raka shi waje tare da zuba masa ruwa ya wanke hannu, kamar wani qaramin yaro, abinci ya ci, ya qoshi, tare da zabga wata gyatsa me Dan banzan wari. Kauda kai Hansatu ta Yi, Isa kuwa ko a jikin shi, ya na tashi ta tattare komai, sannan ta je ta wanke bakin ta da ruwa da dan gishiri, ta bi shi daki, (ita ta iya ta wanke bakin ta, saboda Kar a ji warin shi, Amma shi ya wuni zubur da baki bawanki, sannan ya ci abinci, ko kurkurewa bai ba, ya tafi ya kwanta a haka) Ga Isa da Dan banzan son yin kiss, ga baki na wari, Kuma Hansatu bata Isa ta nuna hakan ba, duk wani qoqarin ta na Sanya shi ya dinga wanke bakin,abun ya gagari tunanin baya ta fara, ta gwada aje masa hodar wanke baki da suke amfani da shi, ya yi fatali da ita, qarshe sai da yajibge ta, ya ce ta raina shi, shi zata kalla ta ce bakin shi na wari? Ta gwada Yi masa magana direct, ya jibge ta, Kuma ya mata kiss ta qarfi, ya ce in mutuwa zatai sai dai ta mutu, Amma yanzu ya fara. Gani ta Yi tunani ba zai kai ta ba, ya na iya fizgar ta da qarfi, da kan ta ta cire kayan ta ta kwanta a saman qaton gadon nasu, Wanda ya yi matuqar bani mamaki, ace kamar Hansatu masu ci da kyar ta na da irin wanna gadon. Addu'a kawai take a ran ta har ya gama abinda zai ya tashi, fatan ta Allah ya raba ta da daukan wani cikin, ya Kuma bashi ikon dinga wanke bakin shi, tunda ta Yi dik wani qoqari ya qi farawa, Allah ne kawai zai sauya masa ra'ayi ya fara. Cikin daren Isa na barci,jikin Hansatu ya dau zafi Mai tsanani, ga wani irin sanyi da take ji, bargon ta ta ja ta lullube jikin ta da kyau, Amma dik da haka sanyi take ji, Isa bai ma San tana Yi ba, Kuma in ta tashe shi ta San sauran, tunda naquda ma ya yi fada da ta tashe shi ballantana zazzabi. Haka ta kwana da mummunan zazzabi, da zafin jikin ta ya dame shi ma sauka ya yi daga gadon, ya sa pillow a qasa ya kwanta, ya na ta surutai qasa qasa. Hawayen baqin ciki ne suke kwaranya a idanun ta, har aka Kira asuba,ta na Nan kwance, takasa tashi. Ba ta samu damar tashi ba kuwa sai da safiya ta fara Yi, da kyar ta iya hura wuta ta sa musu ruwan wanka, Amina da Bilkisu ne Suka shiga gidan Yabbuga duka samo ruwa, sai masifa ta ke masu, ta na fadin wata Rana ta ga alamar sai sun qafar mata da rijiya. Ta na gama wanka ta Yi sallah, Isa ya fita tun tini, ya na can wajen Mai soya masa, ya ce a bashi ta dari biyu abin shi. Kayan da ta daure jiya, ta kunce ta raba, ta Dora ma yaran ta ce, "Maza ku kai wa mama Lamishi, ki ce mata Ina godiya,in ta na da ra'ayi ta na iya kawon wani wankin Nan gaba, ku Yi sauri kafin su fita, sun kusan tahiya gidan Gwauna , maza" Da sauri kuwa Suka je, suka isar da saqon Mahaifiyar su, aiko wanki ya yi wa Lamishi kyau, ta ce zata kawo wani in ya taru,Mai Buruji ma ta ce za ta kai nata. A hanyar su ta komawa ne Bilkisu ta ce, "Amina mu je ta wajen Mai masa, na San baba na can," "Kin San dik ya kammana muna leqen shi Kashi zai liqa Muna ga banza ko?" "Dun Allah mu tai, ni ko yawu na hadiya, mu dawo" Da sauri ta kama hannun yayar ta da ke son guduwa gida, suka nufi rumfar me Masa. Isa akwai jarabar wanke hannu, an zuba masa ya ja gefe shi kad'ai ya aje masar shi, ya tafi wanke hannu. Bilkisu kuwa lallabawa ta Yi ta dauke kwanon Masa, ta ja hannun Amina Suka gudu gida. Su na zuwa suka miqawa Maman su, Suka ce "Gashi baba na yacce a kawo maki" Cikin matsanancin jin dadi Hansatu ta amsa, ta sa yara a gaba Suka fara dukan waina da ci, su na ci ta na murmushin jin dadi. A can rumfar me Masa, wasu matasa da Suka San isan da yaran shi,sun ga sanda Suka dauka, Dan haka dariya kawai Suka dinga Yi. Isa na zuwa bega Masa ba, ya hau matasa da duka, ya na fadin sai sun biya shi masar shi, da kyar aka raba fadan, Nan suke sanar da Isa su ba su bane, diyoyin shi ne mata Suka dauke. Wani irin ashar ya Danna, sannan ya Sanya takalmin shi guda da ya fadi wajen dambe ya nufi gida......... A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 6: Da qafar shi ya daki qofar gidan, gaba dayan su zabura Suka Yi a tsorace, Hansatu ce ta Dan Yi murmushi da ta ga shi ne, godiya ta ke da niyyar Yi ta ji ya hada yatsun shi biyar da fuskar ta. A kidime ta kalle shi, domin sanin laifin da ta aikata, Amina da Bilkisu ne suka shiga tsakanin su, ya ja hannun Amina ya kife ta da mari, zai qara mata Bilkisu ta riqe shi ta na kuka, "Baba ka bar dukan su, ni ta nid-d'akko, ni zaka daka, Kuma ni nicce Kai ka bayar mu zo gida mu ci" Wurga ta ya yi gefe, ta fadi ta dauje guiwar hannu, kuka ta Sanya Mai qarfi, tuni Hansatu ta durqusa ta na duba hannun nata, cikin sanyin murya da mamakin halin mijin nata ta ce "Yanzu akan wainar jikka biyu ka fiddawa diyar ka jini? Ka daki matar ka ? Wadda ta sadaukar da millions saboda Kai, anya Isa Kai ne Wanda na fada son shi shekaru Sha uku da Suka wuce kuwa? Anya Isa Kai ne Wanda ka min alqawurran kyautatawa kala kala? Haqqin ka ne fa ciyar da mu, Amma ba ka Yi, da na san ba Kai ka Basu ba dakkowa suka Yi,da bamu cin ta wallah, ka Yi hankuri inshaa Allahu ba mu koma tambayar ka kuddin abinci, ko Kuma mu dau abun ka, tashi Mu je na wanke maki, sannu" Kalaman ta Basu ratsa  fatar shi ba ma, balle tsokar jikin shi, hasalima wata fassarar ya Yi ta daban. "Auu abun gori Kuma ya koma Hansatu? To da ni da ke wa ya fara furta ya na son wani? Sannan wa ye ya kafe ya guji kowa na shi saboda masoyi? Kar ki dakko maganar baya akan haramun din da ki ka ci ke da yaran ki, duk Wanda ya sake min wannan gangacin zai ga ganganci" Kamar ta sanar da shi ba su ci haram ba, sai ta kama bakin ta, saboda ta San dukan banza za ta sha, har ya shiga daki ba Wanda ya sake motsawa a cikin su, sai sautin shassheqar kuka kawai ke tashi. Ya na shiga daki ya laluba ko Ina bai samu ko sisi ba, fitowa ya Yi sannan ya ce, "Ba kuci banza ba, ki tabbata kin nemo min dari ta biyu" Daga Kai ta yi ta na bin shi da wani irin kallon mamaki. Tunanin baya ta fara Yi, shekara goma Sha uku da Suka wuce, shi din yaron mahaifin ta ne,mutumin kano ne shi, ita Kuma mutuniyar zamfara, ya na ma mahaifin ta tuqin mota, ta haka suka fara soyayya, mahaifin ta na da lalurar hawan jini, kafin ya rasu soyayyar su batai qarfi ba, Amma dik da haka ya fuskanta, Dan haka ya ce ya bawa Isa ita, Yan Uwan ta da dangin ta kaf aka dinga surutu, Dan me zai dauki gudan Yar shi mace tilo ya aura mata yaron shi, budar bakin ta ta ce wa Mahaifiyar ta da Yayan ta ta na son shi. An saka ranar biki da ta gama candy, mahaifin ta a satin ya rasu, sun shiga damuwa sosai a zuri'ar baki daya, saboda shi din mutumin kirki ne, me son dangi ne da taimakon su, mutan unguwa da abokan aikin shi sun koka rashin shi, balle Kuma iyalan shi, Hansatu kuwa har ruwa sai da aka sanya mata a asibiti, saboda yawan suman da ta dinga Yi. Bayan rasuwar mahaifin su da wata bakwai, Yan Uwan ta Suka yanke shawarar a raba gado, sannan a aura mata Dan abokin mahaifin ta, Wanda ke riqe da kampanin Baban su, Dan ya ci gaba da kula da ita, da dukiyar ta, Amma ta dage, ta nace ta ce sai Isa ,a lokacin nan Isa kan shi ji yake in aka raba su zai iya shiga mawuyacin hali. Rashin lafiyar da ta dinga Yi bai bawa dangin ta tausayin komai ba, su dai qoqarin su su raba ta da Isa, har korar shi akai daga wajen aiki. Wata Rana da daddare ta tattare kayan ta tsaf, ta gudu wajen shi, a dakin da ya kama, ta roqe shi da su je ko masallaci ne a Daura masu aure, in yaso sun koma a matsayin mata da miji, ba mai raba su. A wannan daren haka suka kwana daki daya, rungume da junan su, dik da ba abinda suka aikata na masha'a amma hakan ba daidai bane. Washegari suka samu aka aura masu junan su a masallaci ,a ranar suka koma dangin Hansatu a matsayin ma'aurata,mahaifiyar ta ta ji takaicin hakan matuqa, Yayan ta babba ya ce ba za su bata ko sisi ba, a gaban mahaifiyar ta, kuma bata sanya baki ba, Hansatu kuwa yarinta ce? Giyar soyayya ce? Ko kuma rashin tarbiyya ne ya sanya ta shigewa dakin ta dake gidan ,har sun fara murna ta ji maganar su, kawai sai suka ganta dauke da akwati, ta kama hannun Isa suka bar gidan. Da kudin sarqoqin ta suka sayi gidan da suke ciki, aka sanya sunan Isa a takardar,gadon ta da komai na gidan duk da kudin da ta gudu da shi ne suka siya. Lokacin da kudi suka qare ne, Isa ya fara fito wa da Hansatu asalin kalar shi, rashin mutuncin yau daban na gobe daban, da ciki ko ba ciki in ya ga damar dukan ta, zai daka, da ya ji kawai ta bata masa rai, zai mata abinda kamar bai taba furta mata kalmar so ba. Wani irin kuka ne mai tsanani ya turniqe Hansatu, Bilkisu ce ta fada jikin ta ta na kuka, ta ce, "Mama dan Allah ki dena kukan haka nan, lehi na na, bazan sake ba,ki yahe min," Dan shafa bayan yarinyar kawai ta yi, ta ya za ta budi baki ta sanar da yaran ta me ta aikata? Sakayya ce ta qin yin biyayya ga mahaifiyar ta ke bin ta? Shin a wani bangaren ba umarnin mahaifin ta ta cika ba? Tunda dama ya so a yi auren? Ta ya zata sanar da yaran ta mahaifin su azzalumi ne? Shin wadannan abubuwan da suke faruwa da ita silar waye? A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 7: Lawwali ne da yaran shi zaune a wani tsohon kamfani na gwamnati,waje ne da ya qunshi sashe sashe, da dikkan alamu ofishin ma'aikatan wajenne, Lawwali kuwa ya maida wajen a matsayin ma'aikatar shi ta yin garkuwa da dik Wanda aka bashi umarni, ko Kuma ra'ayin kan shi ya bashi da ya Yi hakan,waje ne da ya ke a cikin wani surquqin daji, da dikkan alamu gina shi aka fara yi domin wani aikin na gwamnati kuma aka bari ba tare da an kammala ba, ko an waiwaye shi, Lawwali da yaran shi na ta qoqarin Neman network dan yin waya amma sun rasa. Ya fi awa uku ya na abu d'aya, cikin nasara kuwa ya samu wayar da ya ke son Yi ta shiga, da hanzari ya fara magana. "Hello Excellency  ba waku, yunwa ta addabe ni da yara na, ga shi ba ruwan sha, mu na buqatar kayan caji,...hello...hello" Wayar ce ta sake katsewa, cikin fushi ya buga ta da qasa, ya daki jikin ginin wajen, wani dattijo ne daure a jikin ginshiqin da ke a tsakiyar faffadan wajen da suke, bakin shi ya bushe, da alama yunwa da qishirwa suna damun shi, idanun shi a rufe suke, ba ya ganin kowa, amma ya na sauraren su. Cikin wahalalliyar murya ya ke magana, "Yanzu Lawwali duk irin amanar ka da na dauka, na riqe, haka zaka saka min da shi? Ba irin taimakon da ban maka ba a rayuwa, amma saboda wancan dan adawar ya biya ku kudi qalilan kuke wulaqanta ni haka" Cikin fushi Lawwali ya kalli mutumin da ya haife shi, ya shure shi da qafa, sannan ya naushe shi sau ba adadi, har sai da wani daga yaran shi ya riqe shi. "Oga ka Yi hakuri,Kar ya mutu, in ya mutu Excellency ba ze Mana da kyau ba, ajiya kawai ya ce muyi, ba kisa ba, ya jaddada Mana hakan, sai bayan zabe mu sake shi" Bangaje yaron nashi ya Yi ya duqa gaban bawan Allah n da ya gama duka, cikin qunci yake magana. "Ka riqe ni amana? Wace iriyar amana ka riqe? Amanar shaye-shaye? Ko ta Neman mata da kisan kan mutane? Ko kuma amanar fyade da garkuwa da mutane Dan neman kudin fansa? Kai Bari ka ji, ka ga da ace Excellency ze sauka, Wanda ya sake Hawa ya ban irin wannan umarnin, shi ma qaddamar Masa zan, taimako d'aya ka min a duniya, shi ne Iyaye na Dake aiki a gidan gwamnati har yanzu, dik da ka sauka su na Nan suna ci gaba da Yi, da wannan aikin gidan mu suke ci su qoshi, su Yi sutura, Dan haka iyakar godiyar da zan maka kenan, in ma zan Yi maka godiya" "Oga Lawwali ya suma fa,gashi ba ruwan yayyafa Masa" Murmushin mugunta Lawwali ya Yi, babu bata lokaci ya kunce wandon shi ya fara tsiyaya ma wannan mutumin fitsari akai, sai kuwa gashi ya farfado. Kula da abinda Lawwali ke Yi ne ya Sanya wannan bawan Allahn qoqarin kaucewa, Amma dake ya na a daddaure ne, sai ya kasa matsawa. Dariya Lawwali da yaran shi Suka dinga Yi. Har magariba ba wani bayani daga wajen gwamna, yunwa dik ta cinye su da qishirwa, ga wayoyi sun mace ba caji, sai torch lights suka kukkuna, su na Nan zaune, har isha'i ta Yi, Lawwali ne ya tada mutane uku ya ce su dau mota su shiga gari,su sama masu abinda za su ci,Dan ya na ta jiyo kukan yaran da ke killace a wasu sashen da ke gidan da ko rufin kwano babu a wasu sashen, ya kuwa tabbata yunwa ke damun su,kudi ya Basu akan su siyo Dan wani abu ko ba yawa a fara da shi, Kuma su tabbata sun samu ganin Gwamna a daren ko Kuma su Yi magana da shi ta waya, a Kai masu abinci da ruwa. Har za su tafi Lawwali ya dakatar da su, "Yauwa ga waya ta ku tafi da ita, a sama min caji" "To Oga," Mota suka tada Suka dauki hanyar shiga gari. Sun samu sabani da mutanen gwamna, Dan kuwa Basu jima da tafiya ba aka kawo qatuwar mota lode da abinci da dik abinda suke buqata. Ba bata lokaci yaran Lawwali da za su Kai su goma suka dirar wa abincin suka dinga shigar wa wani daki ana lodewa, bayan sun kammala shigar da duk wani abu da ya kamata suka zauna cin biscuits da juice dan kawar da yunwa kafin matan da ke cikin wajen su dafa abincin, drivern da ya kawo saqon ne ya tsaya ya na bawa Lawwali saqon gwamna. "Oga Lawwali gwauna ya ce na hwada maka, kudin fansa da za a ce dangin Lamido su bayar ace su basuwa  milliyon dari biyar, kar a rage masu ko sisi, dan ya San ya saci ya hi haka nan, da zarar sun kawo kun amshe ku qarasa shi, ya gama Yi wa qasa banna" Daga Kai kawai Lawwali ya Yi cikin Isa, da nuna shi ne oga a wajen,dik qoqarin cin binci da kowa ya ke, shi bai  je ba ya na gefe, ya na son ya ga kowa ya qoshi har da yara da matan da suka kwamushe, Dan haka yaron shi Mai kula da wajen in baya Nan ya aika, ya kwaso Mata uku su raba abinci, haka kuwa aka Yi, kowa ya ci ya qoshi, daga qarshe Lawwali shi ma ya samu ya ci a nitse. A wajen ba a Kiran kowa da sunan shi saboda tsaro, Lawwali Oga suke ce Masa direct, daga Mai bi Masa zuwa mutum.biyar da ke qarqashin shi, da Number ake Kiran su. No 1 shi ne Mai bi ma Lawwali, sai No 2 Mai bi Masa, haka haka, har No 5. A cikin mutanen da aka kwamushe akwai wadan da iyayen su ko 'yan Uwan su sun zaci sun rasu, domin an amshi kudin fansar su, Kuma an qi maida su gida, sun fi shekara a wajen, sun Saba ma da wajen, wasu Kuma har yanzu ba su Saba ba, Neman duk wata hanya da zata fidda su ta maida su wajen ahalin su suke, musamman manya masu hankali. Wasu Kuma sabbin zuwa ne, bangaren sabbi daban na tsoffin zuwa ma daban, wasu daga yaran Lawwali sun Yi 'yan Mata a wajen, su na dik wani abu da suka so da su, cikin sauqi, ba tare da sun takura su ba, Lawwali ya San da hakan, Kuma bai Hana ba. Wajen ya zama kamar prison ga wasu, wasu Kuma kamar unguwa suka je, su na saka ran komawa gida watarana, wasu Kuma kamar gida Suka dauki wajen, kowa da yanda yake ganin wajen. In ba an samu akasi kamar na yau ba, a wadace suke Koda yaushe da abinci, ruwa da dik abinda suke buqata, wutar lantarki ce kawai babu a wajen. ********************** Watarana Mubaraka ta dawo daga makaranta, ta gama cire Kaya ta Yi wanka, ta shirya, ta dau abincin ta, ta fara ci, Lawwali  ya shiga kamar kullum ba sallama. Sanye yake da qananan Kaya kamar ko da yaushe, sun Yi matuqar Masa kyau, zama ya Yi a kusa da ita, suna ma juna murmushi, hannu ya sa ya amshi spoon din ta, ya Yi Loma daya, sannan ya Bata a baki. "Yah Auwal ni fa ba yarinya bace" "A waje na ke jaririya ce har yanzu" Murmushi suka Yi a tare, ledar da ya shiga da ita ya janyo, ya dudduba, wata Yar madaidaiciya ya dakko, ya bude masu, sannan ya ja kujera qarama ya zauna da kyau. Nama ne gasasshe a ciki, zuba masu ya yi. Saman abincin ya ce su ci, "Na Yi kewar cin abinci da Kai Yayana" "Nima haka qanwa ta" "Amma za mu ragewa su Umma ko?" "Ga nasu can, wannan namu ne, Ina sane na zo yanzu, na San kin dawo, ko Zaki ci abinci, ko ki na wanka, " "Sai Kuma gani Ina ma cin abincin, da na qoshi ka kawo da na Yi fushi" "Ai Ina aiki da lokaci, na san ma baki ci ba" Sama akai da kwanon, ana masifa. "Lawwali zaka ci uban ka Wallah ita d'ai ta a gidan da ka bata nama hakan ga Mai yawa?" Cikin Bata rai Lawwali ya ja ledar gefen shi ya cire wata Leda ya miqawa Lamishi, "Aje Mana abincin mu, ga naku Nan, Dan mugun kwadai ya maki yawa Lamishi wanga nama da bai da yawa shi na ki ka wa baqin ciki mu ci, Wanda kuka ci gidan Gwauna in an hada da wanga ko rabi be ba," "Uban ka ke bamu nama a gidan Gwauna?" "Lamishi na fada maki ki dena zagi na ko," "Mi zaka min Dan uban ka? Waje ka ke Zaki, gida mussa ka ke wallah" Dariya Mubaraka ta Yi, Dan ita dariya suke Bata, cikin dariya ta ce "Yah Auwal tsaya biyewa Umma na canye" Da dariya Shima ya Debi biyu a tare ya sa a bakin shi, Lamishi da ta ga ta na ta masifa Basu kula ta ba, sai kawai ta tafi, ta na tafe ta na laluba ledar, ta na diban naman ta na watsawa a baki, kafin ta raba masu ta ci da yawa. Bayan Lawwali ya gama cin abinci da Mubaraka, sai ya Kira ta dakin shi, ta zauna bakin gadon shi, Mai kyau kamar na wata amaryar. Waya ya zaro ya miqa Mata. "Ga taki, kin huta da aron ta Lamishi ana zagin ki, za ki iya Kira na duk sanda kk so, zan dinga saka maki Kati akai akai" Murna a wajen Mubaraka ba a magana, sai dai can qasan ran ta, ta San ba kudin halal bane, har ta gaji da Yi ma Yayan nata nasiha, yanzu Addu'a ta koma Yi masa, ta na fatan watarana Allah ya amsa ya daina aikata dik wani abu Mara kyau....... Shin ku na ganin wata Rana Lawwali zai daina halayyar shi kuwa????? A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 8: Da yamma liss su Yabbuga suka Yi qungiya guda, zuwa gidan sabuwar maqociyar su Lamishi, Yabbuga ita ce a gaba, ita a dole ta San matar gidan. Sun jima su na buga gidan, har Lamishi ta fara jin haushi ta ce su tafi, amma dake Yabbuga na tsananin son Shiga gidan sai ta ce, "Ke wataqila kwana takai, ko ta zaga boli, mu jira kadan, ke dus-san ba ta hitowa lokaci guda daga bugun da be hi uku ba," Suna tsaka da jayayyar ko su koma ne matar gidan ta bude qofa, Yabbuga washe baki ta Yi, sannan ta kutsa Kai ciki, su Lamishi suka bi bayan ta, sai da Mai gidan ta fara zama sannan Suka zauna. Gaisawa Suka Yi,Yabbuga ta gabatar da su baki dayan su, matar ta Yi murmushi sannan ta ce, "Allah sarki ni ko suna na Asshibi, ai na so na shiga wajen ku, sai dai nicce Bari har na idasa gyara waje, har yanzu wajen bai kammalu ba, gashi kin rige ni zuwa, to na gode sosai" Budar bakin Mai Buruji da ta kalli matar ta ga Yar babba ce, Dan ko za ta girme ta to da kadan ne, sai ta ce. "Ina Yan yara," Cikin jin nauyi matar ta ce, "Ba yara, ai ni din amarya Nike" "Amaryaaa" Suka fadi a tare, sai Kuma Suka yi shiru, abin Sha da Dan motsa baki ta je ta kawo musu, kan ta kawo har sun fara gulmar ta, ta na dawowa Suka Yi shiru. Lamishi ce ta fara daukan cincin ta Kai bakin ta, Wasa Wasa sai da suka cinye komai suka shanye lemo tass sannan suka Yi hamdala, Suka mata sallama, sannan Suka fita. Tun daga qofar gidan Suka hau gulmar ta, "Kee ni na ga duniya, ke gane ta kuwa? Gudan gudan tulluqa, ga ta baqa qirin awar bayan tallen miya,Wai amarya take," Yabbuga ta fada cikin al'ajabi. "Kee Yabbuga Ina kyautata zaton zaura ta, wallah" "Lamishi baki da dama wallah, Wai zaura , yo baku gane min hoton mijin ta ba ga giina ta rataye, kyawu nai da gani ya hada dangi da hillani" "Ohhh wanga Hadi nasu Kam shi ah-hadin Allah, in ba Allah ba wa'iisa yin wanga hadi" Dariya Suka dinga Yi kamar wasu qananan yara, a qasan bishiyar su suka zauna Suka dora da hirar su. Hansatu na jin sun fara hira ta San an kafa dandalin munafurcin kenan, tagumin ta ta gyara domin ba ta da lokacin ma saurarar su, tunani ta hau yi game da abinda za ta quqqulla ta dafa ko ta kwadanta masu su ci da daren. Ta duba kaff gidan ba wani abu, sai wani tsakin masara da ya Yi qwari, tunani take ta Yi, akan yanda zata sarrafa shi kafin yaran su dawo, ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce, "Mara shi ba ya hushi, dole ni tai nemo abinda nika ciyar da diya na" Mayafi ta zara ta duba qafarta, takalmin ta da ke ihun gajiya da taka shi ta kalla, murmushi ta Yi, lokacin da ta tuna sai takalmin da ta so na qasashen turawa shi take sawa qafar, amma yanzu ita ke saka wannan takalmin da ko mai aikin gidan su ya fi qarfin shi. Tun daga zaure sukai ido hudu da Yabbuga, cikin magana qasa qasa ta sanar da su Lamishi ga Hansatu Nan zuwa, shiru Suka Yi kamar ba su ke gulmar Yahai ba, kasancewar Ta Yahai din Bata samu zuwa dandalin gulmar ba, Yahai na gida ba lafiya. "Assalamu alaikum, mun wuni lahiya? Ya yarori," A tare suka ce, "Lahiya lumui, ya su Amina," "Lahiya lumui suke,....na ji ku na hira na nicce Bari in taho don Allah taimakon Nan dai da kun ka Saba, shi nika bid'a, 'Dan Mai nika so da d'an gishiri ku sammin in dahwa muna abinci kahin su dawo, da swahe ma Basu ci komi ba, Rana ma ta wuce ga dare ya Shiga," "Tauuuu, Isa bai gari halan? Irin wanga horon yunwa? Gaskiya bashi kyautawa, wanga zalumci ne wallah, ka bar diya har ukku da mace ba abinci, wanga zalumci na" "Ke Lamishi Ina ruwan ki? Ba ita tagga tana iyawa ba? Duk wacce ta maishe da namiji uba ai ko ta na macewa marainiya, gashi Nan ta na dandanar azabar namiji, biyayyar da ta ka wa mijin ta, walle ni bani Yi ma nawa, gashi lahiya lau Nike da miji na, ci da Sha da, sutura kuwa wadda manya za su sawa haka nika sa ta,yanzu haka jiya yakkawon naman sanuwa, saboda bani son aiki nan nibbar mai abu nai, shi yayyi muna abinci mun ka ci dazu, komi ya aje muna, duk da qaramin ma'aikaci na, ai maza Zuma na, sai da wuta, wa ka ragawa namiji yanzu?" "Keee Yabbugaaa raba kan ki da bawa matar mutane irin Wagga shawarar, tauuu, in ki na Bata abinda taka bid'a ki Bata, in baki Yi tau, Dan mu mun Yi nesa da gida" Bata rai Yabbuga ta Yi, Dan ita ma kayan abincin sun Yi qasa, gashi ta gama yabon miji komai akwai, tashi ta Yi Rai ba dadi, tace wa Hansatu ta bita ciki. Ko da suka je, wata tsohuwar jarkar manja ta Bata, in an narka be fi a samu dan kadan ba, ta debar Mata uban gishiri kamar auna shi tai Dan yawa, ta debar Mata barkonon da ba a daka ba, ta Bata Maggi biyu. "Tauu ga su Nan, ki boye dai ba sai sun ga mi nibbaki ba su Yi ta tsintse, tunda ke San dai abin magana bashi musu kadan" Durqusawa Hansatu ta Yi ta na ta godiya, saboda hakan ai babban taimako ne a wajen ta. Zata fita ta ga zogale ya Yi fala fala,gwanin sha'awa, roqar shi ta yi, cikin bacin rai Yabbuga ta tsinkar mata kadan ta bata, tare suka fita, Hansatu na boye bubuwan da ta samo a mayafi, Yabbuga na qara kare wa har sai da ta shige gidan ta, sannan ta koma wajen zaman su. Ta na zama ta dinga lissafin qarya na abinda ta bawa Hansatu, harda cewa ta bata busasshen kihi yara sun ji galmi galmi. Nan dai sukai ta mata jinjina, ta na basarwa. Tuno Asshibi ta yi, ta kece da dariya , sannan ta kalli Lamishi ta ce, "Hummm walle dun-nittina matar can sai dariya ta kammin,( duk na tuna matar nan se dariya ta kama ni) kun ga shegiya baki awat-ta'adin yuqa? (Baki kamar ta'adin Wuqa)" Dariya sosai su Lamishi suke ta yi. Hansatu kuwa na can na sarrafa tsakin masara domin yaran ta. Cikin ikon Allah kuwa sai ga faten tsaki ya samu, wanda za su ci su dan maida yunwar su, cikin murnar samuwar wannan abincin Hansatu ke komai,ta na hamdala ga Allah,ta na kammalawa ta zubawa kowa na shi,ta shiga wanka, ta so ci kafin su dawo,sai ta tuna su da suke yara ma suka hakura da yunwa balle ita? Da misalin shida na yamma su Amina suka koma gida, murna a wajen Ahmad ba ta faduwa, tun da ya ga murhu ya ga toka,ga guntun icce jiqe ya san an yi dahuwa. Cike da so da qauna, tare da kulawa ta zuba masu ruwa suka wanke hannayen su, sannan suka fara cin abincin, suna yabawa qoqarin ta. Bayan sun gama sun sha ruwa, Hansatu ta fara koya masu karatun boko, Amina ta iya rubuta Hausa, turanci kuma ta na ji amma bata iya mayarwa dika, Hansatu ta ga tunda ita ta iya, yaran ta basu samu damar zuwa boko ba, mai zai hana ta koyawa yaran ta a gida? Su na nan su na bacci Isa ya koma gida a zafafe kamar kullum ya shiga, bai amsa gaisuwar yaran ba balle ta uwar su. Abincin shi ya jawo, ya zura hannu a aljihun shi ya zaro ledar kifi, dan dari biyu. Ya juye ciki ya cinye. Bai tambayi komai game da girkin ba, ya samu ne kawai,kuma ya ci,ya qoshi ya bar kwanon a wajen. Ahmad ne ya je wajen shi, cikin tsoro, da kuma murnar nuna masa sabuwar kalmar da ya koya, ta Father, wato Baba, Cikin Bata Rai Isa ya ce, "Wato Hansatu kin rantse da Allah ke sai raina ya baci ko? Ban hana Maki koyawa yarana karatun nasara ba? Ni da na yi zuwa Sakandire uwar me ya tsinana min,in ba tuqin motar uban ki ba? Ke da ki ka yi zuwa Sakandire yanzu ta amfana da shi ne? Kawo littafin nan" Amsa ya yi,ji kike kyyyaaaat ya yaga, yaro kuwa ya buga kuka. Korar shi waje Isa ya yi, sannan ya zauna abinshi ya na hango su,suna jimami, dan sun ji komai,shi kuwa Isa kallon yaran ya yi ya kalli mahaifiyar su, wani irin shu'umin murmushi ya yi, sannan ya furta, "Allah ya kaimu....." Me ye a ran ka Isa???? A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 9: Yau Lamishi ta tashi ba ta jin dadin jikin ta, zazzaɓi ya dame ta, dan haka da Mai Buruji za ta tafi aiki, sai ta ce Mubaraka ba inda zata sai dai ta raka Mai Buruji ta yi mata aikin ta. Mubaraka bata so ba, domin har ta shirya, ta saka uniform, zata makaranta, duk magiyar da take akan a barta ta je makaranta, Lamishi ta qi, qarshe ma zagi ne da qoqarin kai mata duka ne ya biyo baya, bata da zabin da ya wuce ta bi Mai Buruji, a ranta ta na ta jin haushi rashin Auwal a gida. Dan Talo ma tirsasa ta ya yi, ya ce sai ta je, wa ya sani ko ita ma a ɗauke ta aiki, hanyar samun su ta qaru. Sun isa gidan da misalin takwas na safiya, sai da suka sha tambayoyi da kuma neman izinin barin Mubaraka shiga gidan wajen Hajiya Ikee, bayan bayani da Mai Buruji ta mata, dai ta amince, aka bar su su shiga, Mubaraka zuwan ta na farko kenan, dan haka sai kalle kalle take, irin na qauyawan da suka je binni, direct dakin Sultana Mai Buruji ta kai ta, suna tafe ta na sanar da ita duk binda ya kamata ta yi. A zaune ta tarar da Sultana ta na karanta qur'ani, sai ta ji wani irin dad'i ya kama ta, durqusa wa ta yi ta gaishe ta cikin girmamawa ,itama ta amsa, bayani ta sake mata, cikin murmushi Sultana ta ce, "Ai kuwa ga kamannin ku nan sun fito ke da Umman naki, Bismillah in kin wanke toilete zaki gyaran nan, sannan ki dan wanken wadannan kayan" "To inshaa Allahu," Bayi ta je ta wanke tass, ta na yi ta na mamakin irin haduwar wajen,kayan bayin da ta gani a wata roba ta dauka ta duba an aje komai, amma ita da za a barta da hannu za ta wanke su, ba sai an wani sanya a washing machine ba. Ko da ta fita gani ta yi Sultana ta koma saman sallaya ta bar mata gadon ta gyara, ai kuwa cikin azama ta fara gyarawa. Karatun da Sultana take Yi itama ta fara bi, dan shiru Sultana ta Yi, cikin murmushi mai sauti,take bin Mubaraka da kallo, sai ta ji yarinyar ta shiga ran ta, "Masha Allah, Mubaraka ko? Ashe ke din hafiza ce,masha Allah Muryar ki na da dadin karatu, izun ki nawa?" "Na sauke Aunty sultana ,Amma ba a Mana bikin sauka ba, na gode da yaba min," Har ran ta ta ji dadin yabawar da Sultana ta Mata, ta so samun wannan yabon wajen iyayen ta, amma ina, ba su san mahimmancin karatun qur'ani ba su, balle su yaba. A haka ta gama gyara dakin suna karatu ita da Sultana, cikin nishadi, sai Sultana ta ji kamar ta jima da sanin Mubaraka, yarinyar ta shiga ranta cikin lokaci qanqani, sai take jin ta kamar a mkaranta take, da ta gama aikin ta ma, hira suka dan yi, anan Sultana ta ke jin wasu labaran da bata ji dad'in su ba, game da rayuwar Mubaraka, ta na son karatu, iyayen ba su damu ba, a nan ne ta ji kwadayin son shiga cikin gari,ta na son ta je ta ga yanda mutane suke rayuwa a cikin unguwanni, da kewaye, amma ta san zai wahala ta samu hakan. Daga baya Mubaraka Neman izinin zuwa wankin ta yi, sai da ta sake zuwa wajen Mai Buruji ta nuna mata wajen, dan yanayin kyaun gidan na ruda ta, ta manta hanyar zuwa wajen da ake wankin, har tunanin yanda za ta koma wajen Sultana ma take. Yawo take a gidan Dan ganin ya gidan ya ke,ta na tafe ta na qarewa qayataccen gidan kallo, ta na jinjina lamari irin na masu kud'i, cikin murmushi ta ayyana a ran ta 'Dole gida ya had'u ya tsaru, gidan gwamna guda' Tunanin ta ya tsaya cak a daidai sanda ta shiga wata farfajiya, a hankali take jiyo kukan qaramin yaro, ta na tafe, har ta kai saitin inda kukan ke fitowa, ta na saurarawa sai ta ji ya na fad'in, " Dan Allah ku kyale ni da zafi, wayyoo na Shiga uku" Wani gini ta gani, an dan kebance shi daga jikin ginin babban gidan, dan haka can ta nufa, rasa ta inda za ta leqa ta Yi, saboda ya nayin gidan ba qaramin gini aka Masa ba ta yanda zata samu damar leqawa ta ga me ke faruwa. Wankin da ta je shanyawa ta maida hankali wajen shanyawa , ta shanya biyu ta samu gefe ta zauna zaman jira riqe da bokoti, da kuma sabuwar wayar ta da earpiece da Lawwali ya siya mata, ta tabbata koma su wane za su fito, to kuwa zata jira,hannun ta ta sanya qasan rigar ta ta zaro wayar ta da earpiece din ta, ta danna a kunnen ta ta rage qirar'ar da ta kunna sosai, hankalin ta tashe, ta rasa me akewa yaron da ta ji ya na ihu, ji take kamar ta fada dakin ko da za a kashe ta sai dai a kashe ta, amma ta na so ta ga agajin me yaro qarami yake nema a wannan babban gidan, da alama gidan nan na dauke da wani sirri... Bata gama tunanin ba ta ji ana son bude qofar qara volume din wayar ta tayi, ta ci gaba da shanya, ba tare da ta nuna alamar ta San komai ba, da gefen Ido Kuma cikin dabara ta ke kallon wajen, qaramin yaro almajiri aka fitar qafafun shi a ware yake takawa, dik inda ya wuce jini ke diga, Yayan ta Lawwali ta gani da wani amintaccen yaron shi riqe da yaron, kukan da take riqewa ne ya ke qoqarin tona asirin ta. Su na wucewa Excellency ya fito, ya na qarasa gyara rigar shi ,tare da yarfe zufa,wata takarda ce a hannun shi ya na tafe ya na nannade wa, ya zagaya bayan ginin wajen, ya bude wani Dan Rami a wajen suck away ya wulla takardar da in ba qarya Mubaraka zatai ba rubutun larabci ne a jiki, domin ma'abociyar karatun irin takardun ce ita a kullum, dan haka ta san me idon ta ya hango. Wata iriyar zufa ta ji ta karyo Mata, shin meye wannan? 'ya Allah ka Sa ba abinda nake zargi bane' shi ne abinda ta ayyana a ran ta. Cikin tashin hankali ta shanya rigar Sultana ta bacci ta qarshe. Ta durqusa ta dau bokiti za ta tafi ta ji an ce "Keee" Ta so ta nuna ta ji Amma sai ta Dake, ta fara rera karatun qur'ani ta na bin na wayarta. Kula da abinda ke kunnen ta ne ya Sanya Excellency jinkirtawa,ya daina motsi, ya na son tabbatar da shin ta gan shi ko bata gan shi ba, har ta dau bokin ta za ta tafi zuciyar ta ta hau ayyana mata ta juya, kwakwalwar ta Kuma ta bata shawarar ta ci gaba da tafiya, shawarar kwakwalwarta ta dauka ta ci gaba da tafiya, kamar bata ga komai ba, kuma bata ji komai ba. Bata tsaya ba kuwa se da ta kai qaramar qofar da zata sada ta da cikin babban gidan, hannun ta mai rawar tsoron da ya mamaye zuciyar ta ta sanya ta bude qofar, tai wuf ta shige. Ta na Isa dakin da washing machine din ya ke ta ajiye bokitin ta dinga kuka, kamar zuciyar ta ta Fado bakin ta. Ta na tsaka da kuka ta ji dawowar su Lawwali, lallabawa ta Yi ta bi su a hankali, a daidai wani lungu ta tsaya, ta ji suna magana qasa qasa ba ta ji me ake fadi ba dai, Amma tabbas har da Gwauna, ta najin motsin komawar su ta gudu ta koma ciki itama, mayafin ta ta Sanya, ta fita gate, su Lawwali na fita Suka gan ta, ta na tafiya a qasa, tsaida abun hawan ya sa aka Yi. Sannan ya ce ta Shiga Gani ya Yi ta na kuka, cikin damuwa ya ce, "Barakana ya akai? Kukan me ki ke?" Kafe shi ta Yi da jajayen idanun ta, kamar ta amsa shi ta fasa. "Kai na ke ciwo" "Subhanallahi....Kai mu wuce chemist" Can kuwa Suka je, a ka hado Mata magani kala kala, ya sai Mata yagot da lemun roba ya sai Mata gasasshen nama, ya ce su tafi. Har gida Suka Kai ta, ya kama hannun ta suka shige, yaran shi na mota su na jiran shi, Lawwali na shiga ya Bata Rai, "Uban wa ya aike ta aiki gidan can ? Na ce waye ya aike ta aiki can gidan yau?" "Uban ka na, ishasshe,nicce uban ka na, Dan uban ka ba ka Yi min hwadin banza, (baka yi min fad'in banza) ni uban ka zan CI ni kwana lahiya" "Ni ba fad'a nake nema ba Lamishi, kin San yarinyar Nan Bata Saba da aikin wahala ba, wacce a aike ta aiki can gidan?ta je makaranta ta dawo ta je aiki? Habaa" "To na tashi masassara ta damen, Shina nicce ta tai ta taya ni, yo wankin sultana nawa ne? Diyar da kamar yanzu ta Sanya ta cire haka tuwahin ta suke, Kai ka daure ma yarinyar ga gin**take Mana iskanci wallah" Mubaraka ce ta ja hannun Lawwali Suka je dakin ta, ta ce "Yah ni fa qarya na Yi Amma ba ciwon Kai nake ba" Cikin mamaki ya kalle ta, Mubaraka da qarya? "Ke ko me ya faru haka?" "Yah Auwal ka fadan gaskiyar abinda kuka wa almajirin nan, na ji kukan shi, ya dawo ya na zubar da jini ta qafar shi, shin..... Innalillahi....wayyooo Allah na....Yah Auwal ka rantse min da Allah Kai baka.....wayyooo Allah na" Jikin Mubaraka ne ya hau rawa ta ma kasa kukan. "Ba bu ni Mubaraka ba na aikata luwadi, na Yi maki alqawari ba bu ni, yaro kawai muka samo saboda umarnin me gida ne" Kukan da take riqewa ne ya kwace Mata, ta dinga Yi kamar zata shide,tausayin yaron ne ya Mata yawa, hango girman Gwauna ta Yi, ta hango yaron, wani kukan ta fara tare da tari Mai qarfi, ta na shessheqa,ruwa ya bude ya fara bata, ta Yi wurgi da ruwan, cikin kuka ta ce, "Yah Auwal ka bar aiki da shi, zai Kai ka wuta, yah Auwal ko ba abinci za mu rayu ba zamu iya second daya cikin wutar Allah ba, yah Auwal ka min alqawarin baka taba aikata wanan abun da kowa ba, ba kuma za ka bari a yi da Kai ba," "Na maki alqawari na tsani luwadi,qazanta ne, ban taba ba, ba a taba Yi min ba, Dan Allah ki dena kuka, zuciya ta zafi take in Ina jin kukan ki, yanzu Lamishi sai ta zo," Muryar ta kuwa Suka jiyo, "Shegiya 'yar bid'ar a Yi, wato kuka ki ke masa shi Kuma uban mu ya zo ya Dake mu ko? To ki suma,na hada ku dika na ci uban ku" Ta kasa daina kuka, to me ya Yi da takarda Mai rubutun Arabic? Tashin hankali ne ya sake shigar ta, ta kama hannun Lawwali da qarfi ta ce, "Yah Auwal ka bar aiki gidan Nan, bana so, in ka ci gaba zan mutu" Wani Mari ya sakar Mata, cikin tsananin bacin rai,sai da ta ga gilmawar walqiya, nan take nadamar saurin fushin shi ta shige shi, amma ai laifin ta ne, dan ta san ya na son ta shi ya sa take maganar mutuwa,da sauri ya rungume ta, ya na lallashin ta, "Yi hakuri baraka na, Kar ki qara furta mutuwa akan ki, ba Zaki mutu ba, inshaa Allahu zan bar aikin Amma sai da dabara Inna Bari yanzu ku na cikin matsala, kinji?" "Ka Yi alqawari?" "Na Yi alqawari Barakana " Share Mata hawaye ya Yi, sannan ya ce, "Kinga yanzu dole ki Sha maganin da muka siyo Dan yanzu kan ya fara ciwo da gaske." Nama ya miqa Mata gaban ta da komai, ya ce ta ci, ta Sha maganin sannan ya tafi, kasa ci tai ta koma aikin kuka. Shi kuwa har suka tafi maboyar su bai daina jiyo kukan qanwar tashi da ya ke so sama da kowa da komai a duniya ba. Dakin shi ya shige ,ya kwanta, kamar ko da yaushe, ba ya shiga shirgin yaran da aka sa su kamawa, indai ba 'yan siyasa ba, kusan a ce ma duk wanda suka kama ba su san shi ba, No 1 zuwa No 5 kawai suka sani. Sai juya kalman ta yake a ran shi, 'Za mu iya jure rashin abinci, ba za mu iya jure wutar Allah ba' ********************** Da misalin takwas na safiyar asabar, Isa ne ke zaune a majalisar su ta masu zaman banza, labarai ake ta bayarwa da suka ja ra'ayin shi matuqa, shiruuu ya yi, ya na sauraron su, bai tanka ba, matashin da ake kira da Idi ne ya ce, "Yau Malam Isa ya shiga tunanin uwar gida, ko dai gida za ka koma ne, kar ka yi laifi" "Habaa Allah ya kiyaye, ai mata bayin mu ne, sai yanda muka yi da su, da sassafen nan me zan mata a gida inna koma? Zaman gida ai sai matan" Miqewa Idi ya yi zai tafi, Isa ma tashi ya yi, ya bi bayan shi, sun yi tafiya mai nisa Isa ya ce, "Ka na ta sauri Ni fa biyo ka na yi game da maganar da kai a majalisa, da gaske ka ke sana'ar saida goro a Makka indai an samu ta shiga akwai riba ? "Kwarai da gaske, kai baka taba ji ba?" "To a ina zan ji? Ni ba wasu yan uwa masu maiqo nake da ba" "To da gaske ne, yanda ka ji din nan, haka abun yake" "To na gode, zan neme ka inshaa Allahu" Dariya Idi ya yi, ya kalli Isa sama da qasa, sannan ya tafi ya na dariyar ina Isa zai samu kudin siyan goro ya kai Makka, balle ya samu na kujerar tafiya makkan ? Isa gari ya shiga, ya dinga yawo, domin neman qarin bayani akan sana'ar saida goro, abun ya kidimar da shi ,yanda ya ji ana samun kuɗi, ai kuwa ya qudiri aniyar fara saida goro, shi ma ya fita layin su Dan Talo , wato masu mutuwar zuciyaaaa...... A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 10: Tissue ce a qasa jiqaqqu an wurgar a tsakiyar parlour'n, ba abinda ke tashi sai sautin kukan Sultana ,jikin ta sai rawa ya ke, idanun ta  da fuskar ta sun yi jajawur, abinka da farar fata, kallon wayar ta sake yi a karo na ba adadi, ta na kallon wani video ne a YouTube, mata ne da yara tare da mazaje na wani qauye da ke a cikin garin Zamfara aka yi wa barna, an karkashe mata da qananan yara, mazajen su an masu yankan rago,gidaje na ci da wuta, wasu daga cikin iyayen na ta rusa kuka, an dauke masu 'yan matan yaran su, wata mata ta na kuka ta na fadin, 'A gabana yakkashe ta, yabbi ta ya taushe-a gabana ya kashe ta, ta bi ta ya taushe... Fyade) , mahaifin ta ya tai  wajen, kar a ci ma diyatai mutunci, sun ka yanka shi, ina gwaunati take? Shin ba mu da masu taimakon mu ne? Ana kashe mu, da diyoyin mu, ana halaka dukiyoyin mu, yanzu ki duba gidajen can da an ka bankawa wuta, ina na zamu koma? Wa zai karbe mu? A dangi wa muka ajiye da zai amshe mu da lalurorin mu? Kowa ya na fama da kai nai a wanga yanayi na matsin rayuwa' Kuka ne ya ci qarfin matar da ke magana, da dukkan alamu ita kan ta 'yar jaridar kuka take, Sultana kuwa kamar ta sume saboda tausayi,Lamishi na tattare tissue da Sultana ta ke zubarwa ta na hawaye. "Uwar daki na ki yi hankuri, masu aikata wadan ga muggayen laihukka(laifuka) ba mutane na ba, domin shi mutum ba shi kisan dan uwa nai, kuma su ba dabbobi na ba, domin ko zaki bauna da barewa suna cin abinci kusa da shi bai tabe su ba, saboda a qoshe yake, duk kin ka ga dabba ta kashi 'yar uwar ta, to yunwa taka ji, wadan ga mutane ba aljanu na ba, domin aljani ma sai an masa wani abu yake daukan fansa, ko kuma wasu daga azzalumai suna aiki da su, suna sanya su aikata mugunta, wadan ga mutane Allah dai yassan su, kuma shi zai muna maganin su, uwar daki na kukan ya isa haka nan, zaki zazzaɓi" Cikin tsananin kuka Sultana ta ce, "Baba Lamishi Ina za su tafi? Wandancan gidajen su ne gidajen su, an qone su, an yanka wasun su, kuma an sace matan su, ya zuqatan su suke a yanzu? Baba Lamishi what if su ma aka tunzura su, tunda ba mai taimakon su, suka fara irin abinda aka musu? Shin laifin waye ? Waye silar samar da ta'addanci a qasar nan ne? Ya Allah ka kawowa bayin ka agaji a cikin wannan musibar rayuwar da suke fuskanta," Kukan ta ne ya qaru da ta ga wata mata ta fita da gudu, ana tare tare, ashe a gaban ta aka yanka mijin ta da matashin yaron ta, aka tafi da yan matan yaran ta uku. "Ke Lamishi,amshe wayar nan ki kashe, sanan ki tashi ki tafi,"in ji cewar Hajiya Ikee da ke isowa cikin parlour'n cikin b'acin rai. "To Hajiya, Allah ya huci zuciyar ki, ran ki shi dade," Wayar ta karba cikin ladabi, ta kashe, sannan ta ajiye a gefen Sultana, ta qarasa tattare tissue din zata fita, Sultana ta miqe dan komawa dakin ta, wani jiri ne ya ɗebe ta, ta kuwa tafi luuu za ta fadi, Hajiya Ikee da Lamishi suka tare ta, Hajiya sakin ta tayi, Lamishi ta kai ta har dakin ta, ta taya ta ta kwanta, ta rufe ta, soyayyar Sultana na huda duk wata gaba ta jikin Lamishi, domin tausayin ta ga talakawa, da da hali ita aka damqawa shugabancin ba mahaifin ta ba. Ko da Lamishi ta koma parlour kafin ta Isa ta ji Hajiya na bayanin dalilin zubar tissue Mai datti a qasa, "Sultana ce fa, daga ganin abinda ya faru a wannan qauyen da ake ta haskawa a gidajen talabijin da kafafen sada zumunta shi na duk ta daga hankalin ta, yanzu haka ta na daki kwance" "Wai me ya sa ba ki jin magana, shin ban hana ki barin ta kallon irin wadannan shiraruwa ba? yanzu da ta ji sauqi zata yi ta tambaya ta kamar ni na kashe su" Da qarfi ya ke tafiya cikin bacin rai, wanda bai boyu wa, cikin zuciyar Lamishi kuwa cewa ta yi, 'Dan buta uba mai suhhwar tumakin Dan Talo, wanga mutuni mara tausayi Allah ka yi muna magani nai,'(Dan buta uba mai siffar tumakin Dan Talo, wannan mutumi mara tausayi Allah ya mana maganin shi) Lamishi bata fita daga qofar dakin Sultana ba, sai da ta ji qarar rufe qofar shi ,Hajiya ta bi shi ta na ta bashi hakuri, ya na ci gaba da zazzaga masifa, kwashe komai ta yi ta je ta zubar, jikin ta duk a sake. Har suka gama aikin su bata sake walwala ba, lokaci zuwa lokaci ta na leqawa dakin Sultana ta ga ya take, kukan dai shi take yi, kamar a lokacin ta ke ganin abinda ya faru. Lokacin da Lamishi ta yi shigar qarshe dakin Sultana ta gan ta zaune ta na tunani mai zurfi. "Uwar daki na lafiya? Ko na kawo maki abinci ne ki dan taba kadan? Saboda ke ne kawai ban tahi gida ba," "Lamishi, Ni kam na tambaye ki mana," Da sauri Lamishi ta zauna a gefen Sultana ta Bata dikkan hankalin ta, "Dan Allah gidan ku ya yake?.. Amm... Ina nufin akwai sirri? Wani zai iya zama ba tare da an sani ba?" "Tab gidan mu yanda ki ka san bakin kassuwa haka yake ,kowa shiga yake, maza na qofar gida, mata na ciki, dan dai a ci abincin da muke tahiya da shi, da an gama ne dai baki koma ganin wasu sai wanshegari" "Ok, ba komai jeki kawai,....kuma ba ki san ko ina ba da mutum zai iya zuwa na sirri haka?" "Gaskiya ban sani ba..... uwar daki na, in hasashe na ya Yi daidai, ke ce ke son fita daga gidan ga ko?" Shiru Sultana ta yi, ta juyar da kan ta, hawaye na tsiyaya a idanun ta, jin ta take kamar a gidan kurkuku "In haka kike tunani ran ki shi dade ki bari, domin zaman ki anan shi ne ruhin asirin ki da kariyar ki, kinga duniyar da ke a wajen gidan nan? Duniya ce ta azzalumai, duniya  ce ta daukan rai ,duniya ce ta shan jini, da kwace muhalli, duniya ce azzaluma,duniya ce cike da miyagu masu raba Mata da maza da mutuncin su, zaman ki a inda iyayen ki sun ka killace ki shi kad'ai ne kwanciyar hankalin ki da kariya a  gare ki" Cikin kuka Sultana ta ce, "Su kuma bayin Allah da ake kashewa fa? Haka za su ci gaba da rayuwa?" Tashi ta yi da gudu ta fita daga dakin, Lamishi kuwa komawa ta yi wajen Mai Buruji, ta ce su tafi kawai, dan bata ga alamar Sultana za ta ci wani abu ba. Dakin mahaifan ta ta nufa ta dinga buga qofar da qarfi, Hajiya Ikee ce ta fito ita da Sultan ,Sultan na ganin yanayin Sultana ya san ba lafiya, cikin hanzari ya nufe ta, tare da qoqarin kama ta ta kwace ta yi gefe, "Ina daddy? " "Yanzun Nan ya fita, za su fita government house me ne ne sulty na?" Da gudu ta fita, ba ko takalmi a qafar ta, Gwamna ya shiga motar da zata kai shi gidan gwamnati kenan, bayan shi da gaban shi kuwa motoci ne masu bashi kariya, duk sun yi shirin tafiya, ganin Sultana ta fito a birkice cikin kuka, da hargowar kiran sunan shi ne ya sa ya dakatar da su, ya fita, "Sulty baby me ke faruwa? Ina za ki haka?" "Daddy, Ina zaka je? Za ka je wajen mutanen can ne da aka qonawa garin su? Daddy pls help them, they really need ur help, daddy su ma fa mutane ne, Kuma a qarqashin kulawar ka suke, me ya sa haka take faruwa da su ne?" Dan kallon gefe da gefen shi ya yi, ya ga kan mutanen da ke wajen a dan duqe, wasu kuma sun qura musu ido, dan jin amsar da zai bayar, dan kama kafadun ta ya yi, ya goge mata hawayen idan ta, wanda ba su daina zuba ba duk da gogewar da yake ta yi, "Sulty baby, yanzu haka can zani,ki koma ciki, guards ku tsananta tsaro, kar a bar kowa ya shiga ko ya fita," Ya kalli idanun Sultana a lokacin da yake fadin hakan, saboda ba yau ta saba satar jiki ta fice ba,sai dai ya ji labarin ta kai taimako wajen Wanda ibtila'i ya fadawa. ".....ina nufin kar a bar kowa ya fita, a tsananta tsaro" Ture hannun shi ta yi daga kafadun ta, cikin hawaye ta ce, "Me ya sa ba za a ba wa mutanen can tsaro ba kamar yanda ake ba wa wannan gidan? Shin masu gadin mu a gidannan nawa ne? Yawan su bai isa ya kare wani qaramin garin ba? Me ya sa ba za a kai taimako wajen da ya dace ba?.." "Keep quiet sultana and go inside kafin na saba maki," Mota ya bude cikin fushi ya shige, nan da nan kuwa aka kunna jiniya, motocin da ke bashi kariya na biye da ta shi. Qoqarin durqusawa take a wajen ta na kuka, Sultan ya tallabe ta, sai wutsil wutsil take tana son kwacewa, motar su Lawwali ce ta shiga gidan , Lawwali ne a gaba gefen mai zaman banza, yau ce rana ta farko da ya fara dora idanun shi a kan Sultana, yau ce rana ta farko da ya taba jin wani abu mai nauyin gaske, wanda bai taba jin kalar shi ba a gaba daya rayuwar shi ya soki zuciyar shi, wani irin yanayi ne mai dad'i cike da shauki, da wani dandano wanda bai san yanda zai fassara shi ba, har motar ta tsaya,yaran shi suka fara fitar da wasu buhuna da aka nannade aka ma wani irin dauri, wanda komai kwakkwafin ka ba ka Isa gane me ye a cikin daurin ba, Lawwali na zaune a mota, har Sultan ya yi nasarar dauke Sultana wajen Lawwali bai ma sani ba, ganin ta kawai yake a cikin kwayar idon shi, kamar a mafarki ta na zuwa gaban shi,shi kuwa sai zabga murmushi yake. "Oga an gama," A dan daburce ya kalli No 1, "Tau tau, ya Yi, shiga mu  tahi, kun aje dai inda Excellency yacce ko?" "Eh oga," "Tau ya yi, muje" Kallon inda ya ga Sultana a duqe ana fama da ita ya sake yi, ya dan saki murmushi, 'shege Excellency, dole ya dinga kaffa kaffa da zuwan mu, ashe ya aje kadara mai tsada a gidan shi,' Cikin zuciyar shi ya ke wannan tunani, har suka fita daga gidan suka dauki hanyar dajin su bai magana ba, No 1 na Masa magana gaba daya hankalin shi ya tafi wajen tunanin sultana. ********************* "Ki na nufin har yanzu ba su dawo ba? Kuma ki ke zaune a gida ki ke kukan banza ba ki tafi Nemo su ba? In wani abu ya samu yara na Hansatu sai na maki abinda ya fi qarfin mutuwa azaba, ..ba Zaki tashi ki tafi makarantar tasu ba?" A tsawace ya Yi maganar, cikin rashin kwarin jiki, da ciwon da qirjin ta ke Mata ta miqe ta nabin bango, duhu ya fara, ko yar touch light dinnan ba ta da shi, ga shi ba wuta a unguwar, cikin duhun da ya fara Shiga, ta nemi takalmin ta, ta dauki mayafin ta, ta fita. Ko Bai Mata fada ba, ta na da niyyar in ta idar da sallah ta fita Neman su, amma me ya sa ba zai Taya ta ba, zai aika ta? Ko su tafi tare, yaran ai Shima na shi ne, zuciyar ta ce ta sanar da ita cewar, 'Hansatu yau ne kike tare da Isa ? Yau ko ke Kika Bata ai ba zai je Nemo ki ba, ballantana yaran da ya tsana, ya ke ganin su na daga cikin silar talaucin ku' Hawaye ne masu tsananin zafi ke sauka a fuskar ta, a zuciyar ta kuwa wani irin quna ta ke  ji, qirjin ta ne ya sake Yi Mata suka, sai da ta damqi saitin zuciyar ta, ta durqusa a tsakiyar hanyar, da mazajen kirki na unguwar na ta fitowa daga masallaci Dan komawa gidajen su. A hanyar Isa ya same ta, "Tsayuwar me kike anan?" Daga Kai ta Yi a wahale ta ce "Gaba (qirji)na ka Yi min ciyo, Amma yanzu zan tafi" "Hummmm" Shi ne kawai abinda ya fadi ya wuce ta ya na kwafa, da kyar take tafiya, ko da ta Isa makarantar sai ta gan ta a rufe, tun daga gate din ma alamu sun nuna ba kowa ciki, Mai gadin wajen ta tambaya, ta Masa kwatancen yaran, ya ce Bai gan su ba yau, ya gane su, yara ne nutsattsu masu hankali, ga qoqari, malaman kan su na yaba qoqarin su. "Hajiya jiya dai sun taho, Amma yau ban gane su ba,mu na gaisawa da abokina Amadu ai kullum, Amma yau ban gane su ba" Idanun ta sun fara bushewa, Ina yaran ta Suka tafi to? Su ba masu yawo bane, "To ko gidan mu Suka tafi?....kaii inaa, tun da suka je sau uku na Hana su ba su sake zuwa ba, yau shekara biyu, to Ina suka tafi?" Yawo Hansatu ta fara, lungu da saqo na unguwar nan, Bata ga ko ji Wanda ya ga yaran ba. Hankalin ta ya tashi ya Kai qololuwa, yara har uku, ace sun Yi batan dabo? Ina Suka shiga? A wanne hali suke? A hannun wa suke? Wa ya sace su? Tunani ne ya Mata yawa, ta yanke jiki ta fadi a qofar gidan Asshibi......... A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 11: Ta jima kwance a wajen, mutane ba su kula da ita ba, saboda duhun dare da ya shiga , da misalin takwas da wasu 'yan mintinan mijin Asshibi ya dawo, hasken fitilar motar shi ne ya haska ta, dan haka a tsorace ya fito daga motar, ya na gudun mugayen mutane, masu kwanciya da niyyar neman taimako, daga nan su cutar da mutum. A hankali ya fita daga motar, sannan ya tsaya daga nesa,inda da an ce kyat ya zura a guje, ko da ya yi ta magana ya ji shiru, wayar shi ya dakko ya haska Hansatu ,ganin alamar gajiya, da wahala a tare da ita, ya tabbata wannan ta na buqatar taimako, da wayar shi ya yi amfani ya kira Asshibi, amsawa ta yi tare da sanya babban hijabi, saman qananan kayan ta, bata fi mintuna biyar ba ta fito. Bayani ya mata, suka isa gaban Hansatu a tare, Asshibi ta ce, "Boyar Allah, boyar Allah ko ni tashi dannan, ba ki ganin wajen akwai datti," A wahalce murya can qasa, Hansatu ta ce, "'ya'ya na,....ban gan su ba...tun da suka tafi makaranta ban gan su ba....." Mijin Asshibi na jin haka ya miqe da ga tsugunon da ya yi, gefe can ya koma ya lalubi wayar shi, ya danna kira, cikin qasa qasa da murya ya ce, "Kai taho garka ta(qofar gida na) ka dauki matar ka, ga ta nan ta hwadi," Komawa ya yi wajen su Hansatu ya na jimami, cikin tausaya wa Asshibi ta tallafe ta suka shiga ciki, kamar kar ta bi Asshibi , amma ba ta da kwarin yin musu da ita. Ko da suka shiga, kunun da ta dama take sirki da shi, shi ta sakawa Hansatu a babban cup, ta saka sigar da madara ta juya sosai, ta kafa mata a baki, Hansatu na jin abu da sigar, ga qamshin kayan yaji, sai yunwar ta ta murda, cikin ta ya bada wani irin sauti da qara. Ba bata lokaci ta kurba sau biyu, za tai na ukun ta tuno da yaran ta, shin a wanne hali suke ciki, sun ci abinci kuwa, a wanne muhalli suke, su na raye kuwa? Wani irin kuka ne da tunda aka haife ta bata taɓa yin irin shi ba, ya kwace mata, Asshibi kuwa hawaye ne kawai na tausayi ke saukar mata,ganin hawayen ta kuwa tashin hankalin mijin tane, dan haka dakin shi ya shiga, wayar Isa ya sake kira, cikin fada ya ce ya je ya dauke matar shi, ko ya sanar da ita ina yaran suke. "To dan tonanniya, gani nan garkar ka, ku turo ta mu tafi," Komawa parlour ya Yi, ya ya na Basu hakuri, sai suka ji ana buga qofar,da sauri mijin Asshibi ya fita dan ganin wane. Sun dan jima da Isa suna tattaunawa kafin ya koma, "Wani mutum na ya taho, ya na neman Mata tai, yanda ya yi min bayani, ina kyautata zaton ita ce wagga, raka ta can garka" Da kyar Hansatu ta miqe, cikin dan saka ran wataqila yaran sun koma gida. Ko da ta ga isa, ta ga yanda ya bata rai, ta san ba nasara, wani malolon baqin ciki ne ya tokare mata maqoshin ta, cikin murya mai rauni ta ce, "An gane su?" "Ba ke ce ki ka tafi  nemo su ba? Ke zan tambaya an gan su ko ba a gan su ba" Kafe shi ta yi da jajayen idanun ta, sannan ta ce, "Yanzu tsakanin ka da Allah Baban Amina ba ka tafi neman diyan ga ba? Ni kad'ai zan ta neman su? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibatee wa aklifnee  khairan min ha, ya Allah ka bayyana min yara na cikin qoshin lafiya da aminci da salama" Ta na taka qafarta wajen gate din ana kawo wutar lantarki, ihun yara har da wasu manyan ne ya karade kunnuwan su, hasken da ya bayyana ne ya sanya Hansatu jin kwarin guiwar ci gaba da neman su. Gida gida haka ta dinga shiga neman su, wasu su tausaya mata, wasu su dinga ganin sakacin ta. Har sha dayan dare Hansatu na yawo, ita da wasu daga matan unguwar da suke da mutunci, wanda ta zaci sun san ta za su taimaka mata wajen neman yaran ko leqe zuwa qofar gida ba su yi ba. Hankalin ta ya tashi ainun, isa kuwa wajen mazajen unguwar ya tafi ya na cigiya, duk wani lungu da saqo na unguwar an duba ba yaran,shawara aka tsayar akan washegari a je akai cigiya gidan talabijin da rediyo, masu wayar cikin su tun a daren suka bi ta gida, ta na da wasu hotunan yaran da aka taba daukan su a Makarantar boko,nan akai zooming fuskar su aka dauka, aka watsa social network. Hansatu ji take me za ta zauna a gida ta yi? Bata san a wanne hali yaran ta suke ba? Tashi ta yi, ta yi alwala ta yi ta nafila, ga yunwa na cin ta, cikin ta se qara yake, qarshe da tsayuwar ta gagare ta, a zaune ta qarasa sallar ta. Isa kuwa banda minshari ba abinda ya ke ja, daga farkon gado, ya koma qarshe, daga qarshe ya koma tsakiyar gadon har asuba ya na baccin asara. Asshibi kuwa tunani da tausayin Hansatu ya gama nuqurqusar ta, ta sha kuka ta gode Allah, wannan tausayi nata ne ya jawo masu barin unguwar da suke a baya, da an rasa yara ko kuma ta ji an sace Wani ta dinga damuwa kenan, wasu sun danganta hakan da rashin haihuwar ta, wasu sun danganta hakan da ganin ido, duba da cewar bata da halin kirki itama, amma mutane na manta cewa dan Adam tara yake, bai cika goma ba, dik yanda ka kai da mugun hali, ba za a rasa mai kyau ba a tare da kai, haka duk yanda ka kai da kyakkyawan hali, ba za a rasa mummuna ba ko yaya yake a tare da kai. *********************** Abu kamar wasa qaramar magana na neman zama babba, yau sati Daya da kwana uku, ba labarin su Amina ba motsin su, Hansatu ta fita daga hayyacin ta, mutane ko ta ina zuwa ake masu jaje, labari ya kai har wajen Hajiyan Hansatu, abin d'a da mahaifi, sai ga ta ita da yayan ta sun je, cikin wata rantsattsiyar mota mai numfashi, duk wanda ya ga Hajiyan Hansatu zai mamakin ta na da diya amma ta bar ta take a wulaqance haka, dukiya sai kuka take a jikin ta, duk da ba ta wani ci ado ba, a ganin ta, amma a ganin idon talaka ta ci ado ne sosai . Hansatu ta dake, ko kuka bata yi, sai tasbihi a zuciyar ta, ganin Hajiyan ta ne ya sanya bakin ta rawa, a hankali kwallar da ta cika ta tumbatsa a idon ta ta fara kwaranya, zama Hajiya ta yi a kusa da ita, ta kama hannun ta, itama kwantar da kan ta tayi a cinyar Hajiyan nata, jaje Hajiya ta mata,ta amsa da kyar, cikin kuka ta ce, "Hajiya yara na duka fa aka ɗebe man, ba guda ba, ba biyu ba, dika ukun, Hajiya ina ji a jiki na, mutuwa zan yi, hankali na ya fara barin gangar jiki na, zuciya ta tafi ciwon da aka sanyawa gishiri zafi, tafi gulandon da aka fama ciwo Hajiya, na rasa inda zan saka raina Hajiya ," Kwalla Hajiya ta mayar, domin ba wanda bai tausaya wa Hansatu ba a wajen, hatta da su Lamishi da suka shiga yi mata jaje sai da zuqatan su suka raunana. "........dan girman Allah kar ku cutar da yaran nan, ku taimake Ni ku dawo mana da su, mahaifiyar su ba ta da isasshiyar lafiya, shin wai ku ba ku da imani ne?" A guje Hansatu ta qarasa waje, dan jin me mijin ta ke fadi, ta zaqu ta ji me ke faruwa, a handsfree Isa ya Sanya wayar, kowa da ke wajen ya kasa kunne, Hajiyan Hansatu kuwa kamar ta amshe wayar take ji. Daga wayar ne mai magana ya ce, 'Taurin kan ka ne zai sa na kashe daya daga yaran yanzun nan, tun shekaran jiya na ce ka aiko milliyon goma, ka tsaya neman ragi, Ina ruwana da talaucin ka da ka ke fada? Bani da lokacin jiran ka, in baka kawon milliyon goma ba nan da kwana uku, gawar yaran ka za ka gani a titi' 'Dil Dil Dil Dil' Shi ne qarar da wayar ta yi, sai a sannan ne mutanen wajen suka kula Hansatu ta suma. Ruwa aka yayyafa mata sannan aka kaita daki,ta na tashi ta dinga kuka, "Yanzu baban Amina tun da jimawa aka ce akai kudi ba ka fadan ba? Me gadon nan yake ko gidan nan da muke ciki suke? Da ba za mu siyar ba? Yara na sun fi min komai na duniyar nan, ka nemo mai saida gidan a siyar dan Allah ka amso min yara na" Kuka take sosai, isa na share hawayen qarya. "Hansatu kaina ya kulle ne, kwata kwata na manta a gidan kan mu muke ma, bari na je na siyar da gidan na aika musu kudin" Miqewa ya yi zai fita, Yayan Hansatu ya ce, "Dakata, in kun saida gidan yaran sun dawo ku zauna a ina? Muje na rubuta maka cheque ka karba ka fidda kudin ka basu" Isa zubewa ya yi gaban qanin bayan shi ya na godiya, kamar wani soko, Hansatu kuwa kukan farin ciki take tayi, ko ba komai yaran ta za su dawo gida lafiya da yardar Allah, kuma gashi ta shirya da iyayen ta. Ana bama isa cheque ya wuce banki ya cire kudin , ya nufi maboyar su shi da mijin Asshibi, tun a hanya ya sanar da shi ya na tafe. Kamar yanda suka tsara kuwa Isa ya bashi kaso daya cikin kaso uku na dukiyar nan, sannan ya tafi ya boye nashi kason a banki. Sai da ya gama komai sannan ya koma ya debi yara suka nufi gida. Yara fess da su, Ahmad har dan kumatu ya yi, saboda kullum sau uku suke cin abinci a rana, Amina kuwa dake ita ta na da wayo, ta rame ta yi duhu, saboda kewar Umman su. Ko da suka isa gida ranar ba wanda bai kukan farin ciki ba, yanda Hansatu ta kidime da murna da sujjada ba adadi dan godewa Allah, abun ya sanya mutane hawaye. Qanqame su ta yi tsam a jikin ta kamar za ta maida su cikin ta. Labari kan labari haka su Bilkisu ke bawa Hansatu da mutane, Amina kuwa ta lafe jikin Umman  ta, can kamar daga sama suka ji ta ce. "Umma kin ci abinci kuwa? In baki ci abinci ba umma ki ci abinci, Ni ma na kasa cin abinci saboda ina tunanin ki, umma ina ta tausayin ki, ina ta tunanin irin halin da za ki shiga idan ki ka rasa mu" Kuka mai maqaqi a wuya ne ya taso ma Hansatu , "Amina ban ci abinci ba, ruwa da koko kawai nake iya sha,shi ma ba ko yaushe ba,Amina inna rasa ku mutuwa zan yi, ba zan iya jure rashin ku ba" Ai kuwa ba bata lokaci Hajiya ta zaro kudi, ta bawa Isa ta ce a siyo kayan abinci, a siyo risho da kananzir a zo a dora abinci, su ci su qoshi,ita za ta wuce gida, tunda an ga yara. Mutane daya bayan daya ake shiga taya su murna, wasu da suka ji labarin mahaifiyar Hansatu ce ta biya milliyon goma sun sha mamaki,dama su din masu azziqi ne amma take a wahale? Isa ya samu kan gaba, ya dinga zagin iyayen Hansatu , ya na nuna wa mutane ai ba su da tausayi, dan ta auri talaka suka guje ta.... Anyaaa kuwa Isa ....... A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 12: Mubaraka na ta sauri Dan ta kammala wanke-wanken da take yi, ta wuce islamiyya, Lamishi da Mai Buruji Suka koma gida daga gidan Isa. Sannu da zuwa ta musu, sannan ta shigar da kwanukan ta kitchen, "Hummm ke ga ikon Allah ko? Ashe iyayen Hansatu attajirai na, sun ka barta ta na cin azabar Isa ko? Rayuwar duniyar ga na ban mamaki, Wai mutane su dinga wahal da yaran su da kan su" Murmushi Mubaraka ta Yi, Wai Lamishi ke ganin laifin wasu iyayen, ita ya take mata? kenan a ganin ta duk kyara, tsangwama, da kyamar da take nuna Mata Abu ne Mara illa,ta manta ita ma haka take mata azaba, take wahal da ita kamar ba ita ta haife ta ba. Daki ta Shiga ta bar su,su na ta jajen abinda ya faru. Shiri ta Yi tsaf, ta Yi kyau abin ta, uniform din ta fes kamar ba ta zama saboda tsafta. "Umma na tafi makaranta" "To sannu Uwa ta, ke yanzu baki raba kan ki da Wagga wahala ko? Makarantar nan dai ban ga mi ta ke Yi maki ba gidan duniya , Dan kawai ki tai wajen qawaye ne ai ta d'umin banza da yohi" "Umma ba haka bane, shi karatu ko ba Kai aikin gwamnati ba zaka Yi na sa Kai, sannan ba zaka zauna da duhun jahilci ba, Umma inshaa Allahu Zaki alfaharin da ilimi na a gaba" "Ke ruhe min baki, yanneman me shegen iyayin tsiya, wahala dai ke ta aura ba Lamishi ba, Kuma wanga karatu da ki ke ta faman wahal da kan ki walle nasan ba albarka zai ba, to ki ta yi, Kar ki fasa hita, ki tai ki debo min ruwa na Sha kahin ki fita yawon, ko a makarantar taku an Hana Yi ma Iyaye bauta?" Hawaye ne ke gudu sosai a fuskar Mubaraka, a fakaice fa Lamishi ta debewa karatun ta albarka ne, miqewa ta Yi daga tsugunnon da ta Yi a gaban su, ta kalle su ta ga hirar su suke kamar ba abinda ya dame su, hirar gaba dayan ta gulmar mutanen unguwa ne. Jug Mai kyau ta samu, ta dauraye ta debo ruwan sha, ta Kai musu, amshewa Lamishi ta Yi,ba sannu balle Allah ya sawaqe, sai wata mummunar kalma da kullum ta ke hada Mubaraka da ita, wato , "GANTALALLA" Da baqin cikin Lamishi Mubaraka ta bar gidan, a makaranta ta Yi tambaya akan yanda za ta ci gaba da Yi ma mahaifan ta biyayya ba tare da ta gaji ba. Da misalin qarfe shida da rabi Mubaraka ta dawo gida, kaca-kaca, kamar ba sai da ta gyara ko Ina ba ta fita,hijabin ta ta cire ta ninke,ta dora asaman wani Dan farin bokitin Lamishi da takan dama kunu, sannan ta dau buta ta zaga bayi, ko da ta fito gani ta yi an Yi wurgi da hijabin a qasa, bokitin ba ya nan, murmushi ta Yi, da ta fahimci Lamishi ce ta dauke bokitin ta, ta Kuma Yar Mata da hijabin a qasa, kamar bokitin ta ya fi hijabin mahimmaci. Dauka tayi ta Kade, ta shiga daki, ta cire Kaya, sannan ta nufi dakin Mai Buruji ta Gaishe su, qoqarin fita take Lamishi ta ce "To GANTALALLA an dawo Kuma sai a dau tsintsiya, in kin qare shara ki Tai zuwa Dora abincin dare, wancan uban naku Mara zucciya, ya je ya canye abincin da mu ka rage na dare shi kad'ai" "To Umma " Kitchen ta fara sharewa, ta dora ruwan tuwo, da ya kusan tafasa ta wanke shinkafar tuwo ta zuba,sannan ta tafi tsakar gida ta fara shara. Sai da shinkafa ta dahu lubus, ta tuqa, gani ta yi ya Yi ruwa,sai ta debo gari zata zuba Lamishi ta fita, ganin Mubaraka na shirin yin talge a tunanin ta kenan, hakan sai ya sa ta zabga uban ashar, sai da Mubaraka ta saki muciyar da ta dakko dan sake tuqa tuwon a qasa Dan tsoro,garin ya Dan zuba a qasa kadan. "Tuwon wahalar naki Zaki tuqa muna? To walle bamu cin tuwon wahala miyar bala'i gidan ga, bakki da aiki sai tuqa Muna tuwon gari, ga gumi (shinkafa)Allah ya hore Muna, ga sure da alanyahu,(yakuwa da alayyahu) Amma ki Yi Muna tuwon gari, ke San dai ba son shi muke ba" Da alamar gajiya da halin Lamishi, cikin yanayi na rashin mataimaki Mubarakah ta ce, "Ni fa ba tuwon gari bane, shinkafar tuwon ce bata isa ba tuwon ya yi ruwa shine zan daure da gari," Dik da hakan Bata tsira ba, sai da Lamishi ta bude tukunyar miya, zata fara masifa, ta ga miya na zabalbala, Mubaraka Bata ce komai ba, komai na cikin miyar na hadin miyar sure ne, ganyayyakin ne Bata samu yankawa ba, saboda aikin ya Mata yawa. Bata samu kammala girkin Nan ba sai gab Isha'i, ruwan wanka ta dora, sannan ta je ta zauna, ta na hutawa, a wajen gyangyadi ya fara daukan ta. "Mubaraka, mi kikai a Nan zaune?" "Ba komai Baba, wanka zan shiga, ruwan nika jira shi tafasa," "Tau ya Yi, a bada himma" Kitchen ya fara leqawa, be bayar da ko sisi ba Amma ya na Neman abinci, Lamishi kuwa ta sa kowa ya dauki na shi, an kai Masa nashi dakin shi. Ko da ya ga alamar an Yi girki murmushi ya Yi, ya shige dakin shi. Mubaraka na fitowa daga wanka aka dauke wuta, alwala ta Yi, ta nufi dakin ta, sabo da zaman duhu, harta San inda komai yake a dakin ta, a haka ta shirya, sannan ta tada sallah. Ta na tsaka da sallah ta ji qarar Gen, ihu su Jameelu suka saka, su na rawar murna, ta na sallame sallar ta itama ta saki murmushi Mai qayatarwa, murmushi ne da ke Nuna tsantsar farin ciki, da shauqin son ganin abin qauna. Ta na tafe ta na azkar a bakin ta, ganin su Jameelu ta Yi da Leda sun nufi dakin Lamishi suna murna. Da damar wasu gidajen ana tsoron yayu maza, wasu saboda suna son qannen su, ba su son su ga a abinda zai Bata rayuwar su, wannan dalilin ke sa su tsare gida, har qannen su dinga tsoron su. Wasu saboda Basu da gaskiya, ba su aikata abin kirki da qannen wasu, shi ya sa suke matsawa na su, tare da Hana su zuwa ko Ina, a Yi ta musu tsawa, sai su Saba da tsoron yayun nasu. Lawwali da qannen shi duk babu kalmar tsoro a tsakanin su, sai girmamawa, domin kuwa ya ja su a jiki, Jan da iyayen su ma ba su masu irin shi,ya na son qannen shi sama da yanda yake son kan shi, da mutum ya taba qannen shi, gwanda ya rungumi tiransuhoma da damuna,Dan zai iya kawar da ko ma waye akan qannen shi, musamman Mubaraka . Sai da ta kwankwasa sannan ta jira neman izinin shiga, Dan murmushi ne Mai sautu ya fita daga bakin Lawwali ,izinin shiga ya Bata, ta samu waje kusa da shi ta zauna, cikin murna sosai. Hannu ya sa ya dafa kan ta, ta na jin hannun shi akan ta ta rintse idanun ta, da suka cika da hawaye, Nan da Nan kuwa ya fuskanci damuwar da ke cikin ran ta, miqewa ya Yi tsaye, da alamar a bige yake ma, dan tsayuwar tashi ba wani sosai ya Yi ta ba. "Wane Mai qarar kwanan ne ya Bata ran ki? Waye lahira ke son Tai bago yanzun ga, wa ya taba ki? Hwada min ko wane ne, rayuwa tai ta baci"(ran shi ya baci) Dan tura baki gaba ta Yi, cikin shagwaba ta kama hannun shi, ta ji yanda ya ke rawa, "Yah Auwal ni fa ba Wanda ya taba ni, na Yi kewar ka ne kawai, Kuma ka min alqawarin daina irin wagga rayuwa, Amma ka kasa cika min, ba ka taba daukar min alqawari ba ka cika ba, Yah Auwal Anya kuwa zaka sauya?" Sai a wannan lokacin ne ya ji kwamciyar hankali, zaro Mata ledar kayan kwalama dangin su sweets yayi,ajiyewa ta yi a gefe ta na kallon shi, shi kuwa shiru ya yi, ya na tunani, gaba daya tunanin da yake a zuciyar shi ya tattara ne akan cika Mata burin ta. "Yah Auwalll" "Na'am sarauniya Baraka ta, Baraka Ina so na daina wadannan abubuwa, musamman yau, min fita operation an kusan yin nasara akan mu,kin ga Nan, harsashi ne ya gogi naman wajen,abubuwan rashin nasara na ta bin mu" Kukan Mubaraka ne ya katse Masa labarin shi , cikin kulawa ya kalle ta, gani ya Yi, ta na kallon ciwon,da Bata kula da shi ba, sai daga baya. "Kwantar da hankalin ki, kin manta Yayan ki jarumi ne? Ba fa yau na Saba karbar harsashi ba." "Yah Auwal ka cika min alqawari na ka bar aikin Nan" "Zan bari, Amma da sharadi" "Sharadin me???"........ *Zan so jin wannan sharadi Nima* A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 13: Idanun shi ne Suka fara rufewa, cikin mayen bacci, da mayen shaye-shaye ya ce, "Diyar Gwauna ni ka so Baraka" Dafe qirji Mubaraka ta Yi, tare da zaro idanun ta farare waje, "Diyar Gwauna ?" Kallon shi ta Yi daga sama har qasa, da ace baya harkar shaye-shaye, da mugayen laifuka irin Wanda yake, da ace shi din mutumin kirki ne, Mai ilimi, Mai Neman halal ko da ba yawa, da ace shi din ba Mai kashe mutane bane, ba tare da haqqin su ba, tabbas da ta San in dai kyau zai sa a so mutum Yah Auwal din ta zai zama zabin sultana, amma a yanda yake dinnan inaa, ba ta hango komai da zai hada su ba, sai ma raba su, hanyar ba ta da mabulla. Tsugunnawa ta Yi, ta cire Masa manyan takalman shi, Wanda suka kusan Sanya ta amai, domin kuwa jini ne a jikin su, idanun ta hasko Mata abinda Bata gani ba suka dinga Yi game da jinin, sai ta ke ganin kamar wani ya kashe ya fadi a qafar tashi. Kuka take sosai, zuciyar ta na radadin halayyar da Yayan ta ke ciki. Tunawa ta Yi da hukuncin Wanda ya kashe Rai, kashe shi za ai, Kuma zai dawwama a wuta, wani sabon kukan ne ya kwace Mata, zama ta yi a qasan wajen, ba zata iya daukan wannan baqin cikin ba. Ta na gama cire Masa takalmin ta wurga su bakin qofa, ta miqe, ta fita waje cikin sauri, ruwa da tsumma ta dakko, ta goge takalman, sannan ta debo ruwan dumi Mai kyau da dankwalin ta wankakke, ta dinga jiqawa ta na goge Masa ciwon shi da ke fidda  jini. Ta na Yi ta na kuka, kukan ta ne ya tada shi, idanun shi kamar ba za su bude ba, saboda baccin da ya ke ji, amma ganin hawaye idanun ta sai ya tada hankalin shi, da hanzari ya miqe, "Barakana mii na na?" Fadawa ta yi jikin shi ta na kuka, sake rikicewa ya yi, ba ya son kukan ta kuma ta sani, amma ta ke yi. "Amma dai ke san bani son kukan ki ko?" Daga kai ta yi,sannan ta fara qoqarin share hawayen ta, taya ta sharewa ya yi, sannan ya kalle ta da alamar ya na son sanin meye ya sanya ta kuka, shiru ta yi, cikin Muryar lallashi ya ce, "Haba likita na, ko dan kin  ga wanga dan ciwon ne kk kuka? Ke da kk Saba ganin ciwon da ya hi wanga a jiki na? Me ne na  kuka, ashe da nake  hwadin zaki karatu ki kai matakin likita dan ki na kula da ni ba zaki iya ba" "Yah Auwal da zafi ?" "Me? Au wanga? Babu zahi,bari kuka barakan Yah Lawwali" Dan murmushi tayi, cikin hawaye ta ce, "Ni dai Auwal sunan ka, ba Lawwali ba" "Tau na jiya, Auwal suna na ba Lawwali ba, mi na na ka saki kuka?" "Sai yaushe na za ka dena kashe bayin Allah?" Shiru ya yi kamar ba zai amsa ba, can ya nisa ya ce, "Sai sanda wadda nika so ta hwara so na" "Yah Auwal ka bar wannan maganar , kayi tuba domin Allah, mutanen hwa da kuke kashewa bayin Allah ne, Allah ne ya halicce su, ya sanya musu rai, ya basu 'yancin su yi rayuwa, amma ku ke kashe su, ku ke hana su 'yancin da suka samu a wajen Allah na rayuwa, Yah Auwal in watarana aka zo har gida aka kashe wani a gidannan fa? Ko kuma su ka sace ni, ya z...." Maruka kyawawa guda biyu ya ɗebe ta da su, a fusace ya daga pillow ya dakko qaramar bindigar shi, ya dora ta a saman kan shi, ya maida ta kan ta, daga baya ya daga ya harbi sama, sai da ya bula soron dakin, cikin tsananin fushi, idanun shi sun koma jajawur, ya kalli Mubaraka wadda ta ke durqushe kuma a takure a qasa tsabar tsoro,daga ta ya yi ya na son ta kalle shi, amma ta gama tsora ta da shi,cikin murya mai razanar wa ya ce, "Duk wanda ya yi karambanin taba ki, ko wani nawa, se na kashe shi, sai na kashe dangin shi kafff, da mutanen garin su, duk wanda ya yi kuskuren taba koda tsilin gashin kan ki na, sai na ga bayan shi da dangin shi kafff, ke din rayuwa ta ce, ina son ki, sama da yanda nika son uwayen da sunka haifan, Barakan zan aurar da ke da hannu na, da hannu na da kai na zan kai ki dakin auren ki, barakana ke rayuwa ta ce, duk wanda ya tab'a ki ni ya taba, ko hararar ki mijin ki ya yi sai na ɗebe mai ijiya, (ido)" Rungume junan su sukai, cikin kuka ta ce, "Yah Auwal indai ka na so na kamar yanda ka ce, to ka dena abinda ka ke" Rintse idanun shi ya yi, saboda abinda ke masa yawo a kan shi, zama ya yi, ya dafe kan shi, ita kuma ta na tsaye ta na kallon shi. Kashe mutane a jinin shi yake, an horar da shi hakan tun da quruciyar shi, ya shiga gari ya tada masu zaune tsaye ba wani abu bane a wajen shi,su shiga gari su kashe kowa su kwashe dukiyar su da mata, da hatsin su ba komai bane, su yi ma 'yan mata fyade su kashe su ko su tafi dasu ba komai bane,amma duk da haka, akwai zuciya a qirjin shi, wadda bai san ta na aiki ba sai an tabo Mubarakan shi, a yanzu ya qara tabbatar da akwai zuciya a qirjin shi tunda ya fara son sultana, Mubaraka zuciyar shi ce, Sultana kuwa jinin da ke gudana a cikin zuciyar shi ne, in ba daya a cikin su, ba zai iya ci gaba da rayuwa ba. Shi ya sani shi mugu ne, shi wata iriyar halitta ce, wadda ba ta da suna ,saboda sharrin ta, amma dik da haka ya fada so, shi so baya shawara da kowa in zai shiga zuciya, da ya na neman shawara da bai shiga zuciyar mutum kamar shi ba, da ko qanwar shi Mubaraka ba zai so ba. Da ba zai damu da dangin shi ba har ya dinga zuwa gare su, duk da ya san hatsari da hakan zai iya haifar wa, a rayuwar su, soyayyar da yake masu ke kawo shi wajen su, duk da cewa tunda ya fara wannan harka bai taba sama da awa uku a gida ba, kuma ya kan jima bai zo ba. Miqewa ya yi, ya dafa kafadun ta ya ce, "Barakana ki tai zuwa dakin ki, zan dan je wani waje, na kuma miki alqawarin daina wannan harka, amma fa ba yanzu ba, akwai abinda nika son yi,sai kuma na samu sauyin aiki" Murna ta fara sosai, duk da ta so ya ce ya bari a take a wajen, amma akwai hope watarana zai bari, kamar yanda ya ce. Ciki ta shiga da murna, Lamishi na zaune tsaki ta ja mai qarfi sannan ta ce, "Gantalalliya in kin gama kai qarar mu wajen uban mu Lawwali sai ki je ki bidi makashin wuta ki kashe muna wuta,  dan kuwa b uban ki DanTalo ka biyan kuddin wuta ba ni ka biyan su" Mubaraka bata ce komai ba ta wuce dakin ta, ta kashe fitila kamar yanda aka ce ta yi, tsabar masifa Lamishi ta manta cewar Gen ne ma aka kunna ba wutar nepa ba. Lawwali kuwa takalmin shi da ta cire masa ya dauka zai saka ,ya na ganin shi fess ya saki murmushi, ya San aikin barakan shi ne. Bindigar shi ya dauka ya soke ya fice. ************************ "No 1akwai wata yarinya na yi tambaya cikin gida an ce mun qaunar Lawwali ta, ina so a dauke ta ba tare da sanin shi Lawwali ba, a adana ta, domin da alama ranar da kuka kawo almajiri dan yin aikin nan ta gani" A tsorace No1 ya kalli uban gidan nashi. "Ranka shi dade Excellency sir akan yarinyar nan, Lawwali na iya tada jihar Zamfara kafff, ina ganin a jarraba ta a gani, in ta san sirin ka, sai a dau mataki, in bata sani ba, a barta kawai, in oga ya birkice sai zaman garin nan ya gagare mu" "Me ya hwaru?" Ba No 1 ba, hatta da gwamna Halliru,sai da ya tsorata, cikin kidima, da in ina suka juya maganar, da yabon shi akan aikin da suka cika ma wani kauye. Bata rai ya yi, ya nemi waje ya zauna . "Excellency sir zuwa na yi a sauyan wajen aiki, na gaji da shiga tafasa, cikin dokar daji kullum, ka aje ni kusa da kai, ina so ko yaushe qaunata ta so gani na, ta gane ni, kar ka damu, daji ne ba zan sake zuwa ba, amma in wani aiki ya taso, zani , ba tare da ta sani ba" 'Tabbas yarinyar ta san wani abun' "Ok to na ji me kace, kuma na amince, za ka na bi na duk inda na ke, amma sai ka sauya shigar ka, da askin ka," No 1 na son magana gwamna ya katse shi , "Kai kuma daga yau, kai za ka dinga kula da maboya, kai ne incharge ," "Seeee ka yiiiii excellency, se ka maimaita ko su na so, ko ba sa so, ko mu kashe kowa a zauna ba kowa" Kirari sosai Lawwali ya wa gwamna,kafin ya tafi ya nufi gida dan ya na son ya bawa Mubaraka labari. Gwamna na wa Lawwali  kallon biri, shi kuma Lawwali  ya na masa kallon ayaba...... A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 14: Lawwali ya tattare ya koma sabon gidan da gwamna Halliru ya siya masa, ya na matuqar ji da Lawwali saboda shi din babbar kadarar shi ce, abokan siyasan shi na ja da baya da shi sosai saboda Lawwali , da ace ya inganta rayuwar Lawwali ne ya sanya shi a wata harkar halal da zai more shi, da matsalolin da za su shiga a gaba da basu faru ba. Gida ne madaidaici mai kyau, dakuna biyu kowanne da bayi, sai tsakar gida da madafi irin na zamani, an zuba komai na more rayuwa, Lawwali ya yaba da wajen, gida ne da ke cikin unguwar da gwamna Halliru da iyalan shi suke ciki, a son Lawwali ma shi a kai shi cikin gidan, komai zai fi masa sauqi. Har gida ya sa No 1 ya kai shi, ya dakko Mubaraka suka je ta ga wajen, Ita dai bin wajen take da kallo, shi kuwa kallon ta yake ya ga farin cikin da za ta nuna, amma ya ga shiru , "Barakana ba ki ga sabon gida na ba ne?" "Yah Auwal na gani , a ina ka samu kuddin sayen wanga gida mai kyawu hakan ga," "Ohh baraka ki sa albarka kawai, ba ke ce ki ka ce na sauya sana'a ba? Tau wanga shi na matakin hwarko, duk wani laihi da na ke aikatawa na bari, yanzu diyar gwamna zan dinga tuqawa ke ga uniform Dina can? Ke gane su? Ina zuwa bari na saka ki gani ko suna yi min kyawu" Daki d'aya daga cikin d'akunan ya fada, hannun ta da ta daga dan dakatar da shi, ta mayar ta na murmushin zumudin da yake, ta fara zaga wajen, No 1 na tsaye a waje ya na hango su tare da sauraren su, y na nad'e komai. Lawwali ne ya dawo sanye da uniform kalar fari da baqi, wanda suka yi matuqar yi masa kyau, matsala daya, jikin shi ka na gani za ka san riqaqqen dan daba ne, hakan bai boye kyaun da ya gada wajen mahaifin shi ba, Dan Talo, domin kuwa da ace Dan Talo zai gyara da kyau, wata budurwar ma sai ta ce ta na son shi. Murmushi ne mai kyau ya kwace wa Mubaraka ,ko ba komai ta kan yi farin ciki duk sanda ta ga yayan ta ya sanya manyan kaya, in suka fito da shi ya yi tsaf sai ya yi kyau gwanin sha'awa. "Ka gan ka kuwa Yah Auwal , shin ka diba yanda kayan  ga sun ka yi ma kyawu? A gaskiya ba da ban ba dan ba sai na ce Aunty Sultana..." "Shiiii," Shi ne abinda Lawwali ya ce, sannan ya wayance,ba ya son No 1 ya San shirin shi, ya jima da sanin No 1 na neman matsayi na musamman wajen Gwamna, so ba zai bari ya ji qudirin shi akan Sultana ba. Daki suka shiga ya zaunar da ita bakin gado ya ce, "Barakana ki fada min me ne ne a ran ki, gaba daya bakya farin ciki, murmushi kawai ki ke, amma ba har zuciyar ki ba" "Yah Auwal ni dai gaskiya ina jin tsoro, in Aunty Sultana bata ji wani abu ba game da yanda ka ke ji fa?" Da wani ne ya fadi haka ba Mubaraka ba, da ya d'and'ani azabar Lawwali, d'an had'iye bacin ran shi ya yi, ya ce, "Baraka na ki min addu'a ke baiwar Allah ce, ba ki da laifuka a wajen Allah kamar Ni, ki roqe shi y sanya mata so na, kamar yanda nake son ta,....Baraka kin san matsalar da za a samu ma kuwa?" Girgiza kai ta yi, zama ya yi a gefen ta, ya ce, "A binciken da na yi kwanakin baya na gano cewa ba fa wani fita ma take sosai ba,sai ta bushi iska ne ta ce zata siyayya, to yau she zamu zanka haduwa?" "Inshaa Allahu kar ka damu, ka riqe Allah, ka maida hankali Yah Auwal ka yi tuba na tsakani da Allah, Allah zai taimake ka" "Amma baraka.." "Yah Auwal kamar yanda ka yarda in ka  loda harsashi a bindigar ka, ka harba ba abinda zai hana harsashin huda abinda ka harba, to amsa addu'ar Allah a wajen bawan shi da ya yi imani da shi, ya amince Allah ne me yi tafi harsashin bindigar ka" "To baraka zan dage da roqon Allah" "Yah Auwal ni na san rabon ka da sallah yanzu an jima, domin sallah na sanya fuskar mumini haske da kyalli, babu wannan a tare da kai, to ta ya ka ke ganin za ta gan ka ta ji ta kamu da son ka? A yanda na ji labari kai din masanin qur'ani ne kafin Lamishi ta kashe maka guiwa ka fara harkar nan, me zai sa ba za ka koma ma abinda ka bari ba?" Shiru Lawwali ya yi, tunanin baya ya yi, a da kaf makarantar allon Malam Hadi ba ya shi, gashi yanzu ko a hanya in ya je unguwar ba ya gaishe da malam Hadi. "Baraka dare na yi, muje Mu aje ki gida ko?" Tashi ta yi, suka fita parlour, tunawa ya yi ko dan ruwa bai ba ta ba, leda ya samu ya cika mata da juices kala kala, da kayan marmari, da dangin biscuits, ya bawa No 1 ya riqe, suka fita . Har gida suka aje ta za su koma, ta ce, "Yah Auwal ba za ka sanar da su Baba ci gaban da aka samu ba?" "Bassu kawai, kuddi kawai suke so ko? To ana kawo masu, ba su damu da me na ke ba, ke kad'ai ce ki ka damu da rayuwa ta, shi ya sa na bawa rayuwar ki mahimmanci kema" Ya na gama fadi ya daga wa No 1 hannu, ya bashi umarni suka ja suka tafi. Ta na shiga kuwa ta tadda masifar Lamishi na jiran ta, "Sannu tinkiya, uwar tinbele, ke san gidan ku amma sai an nemo ki, ina ki ka tafi tun azzufur ba ki gidan ga sai yanzu zaki dawo?" "Umma Yah Auwal ne fa ya dauken mun ka tai gidan da an ka sai mai, ya nuna min" "Ga ki uwar shi ko? Shi yasa  nake qara tsanar yarinyar nan fa, d'an nawa guda tilo kin zame mai kamar  uwar shi, ni be kai Ni ba, se ke, bani nan" Amshe ledar hannun Mubaraka ta yi, ta bubbude, ta ga lemuka da kayan marmari. "Uhumm uwar kwad'ayi, wanga lemon wahala da ya had'o ki da shi fa? Ina lehin yar kaza ko balangu, ah ah, an hada mu da kayan ruwa mu sha mu yi ta hitsarin wahala ko?" Dariya Jameelu ya kece da ita, dan shi a duniya fadan Lamishi na bashi dariya, "Jameelu ka kiyaye ni, ina fada kana dariya zan yanka maka mari se kayi hitsarin wahala" Haba me Jameelu zai yi ba dariya ba, a guje ya bar gidan, dan ta na iya yan ka masa marin wahalar da ta furta . Juyawa ta yi kan Mubaraka ta ɗora daga inda ta tsaya ta ga wayam. Ci gaba tai da masifa, ta na bude robar lemukan ta na kurba, ta na ware masu tsami a gefe, masu zaqin a gefe. *********************** Mota ce madaidaiciya a qofar gidan Isa, driver na zaune ya na jira, Hansatu kuwa na ciki ta rikice, ta rasa ma kayan da za ta sanyawa yaran ta, kowanne ta dakko ya na da matsala ,ba ta san kayan yaran ta sun lalace ba haka sai yau, ita kan ta atampar da ke jikin ta ta ji jiki, wata baiwar Allah ce a nan layin nasu take bata tsofaffin kayan ta da na yaran ta, ita ta bata atampar ta kusan shekara biyu ta na dirzar ta. Cire tunanin komai ta yi aran ta, ta saka masu jemammun kayan suka fita, kallon Isa ta yi, cike da mamaki, tun da Isan na da kaya masu kyau,amma ya saka wasu tsofaffin kayan shi sun kode kwarai, musamman ta saman bayan shi , "Kun shirya? Mu je mun bar bawan Allah na ta jira" Kalaman shi ma na yau abun mamaki ne, A gaban mota Isa ya zauna, Hansatu da yara suka shiga baya. Driver tuqa mota ya yi, suka fara tafiya . Yabbuga na zaune a qasan bishiyar su ita da matar Yahai, sun ga wucewar su Hansatu. "Ke ji Isa wani kaya da ya saka" Dariya suka kece da ita, Matar Yahai ta ce, "Ina za su haka?" "Jiya da dare na ji Isa na fadin sai sun je, ko ta na so ko bata so, ita ko ta na ta magiya akan kar su tai, tau qarshe sai da ya buga ke san jakki ba shi jin dumi sai bugu"(kin san jaki baya jin magana se an dake shi) Dariya suka sake sanyawa, Dan jumma ne ya fita daga gida za shi masallaci, ran nan baqiqqirin, ya na gida ta fita zaman gulma, ko abinci da kan shi ya diba a tukunya, tsabar gulma na cin ta, ta gama girkin bata kwashe ba ta bari a tukunya, dik ya danqare. "In kin gama dumin sai a tai zuwa sallah ko?" Gaba ya yi bai jira ta cewar ta ba. ********************** A gaban kantamemen gate din na gidan su Hansatu motar ta tsaya,wani irin kuka ne mai tuquqi ya tasowa Hansatu ,rabon ta da gidan tun wani zuwa da su Amina suka yi, ta je dakko su, lokacin Ahmad na qarami sosai,ba kalar wulaqancin da masu gadi ba su mata ba, saboda sabbi ne ba su san ta ba, kuma yayan ta da ya fita a wulaqance ya kora yaran, ko ciki ba a bari ta shiga ba. "Ah ah hito mana" Fita ta yi, ta na share hawaye, an sauya fentin gidan, gidan ya sauya kamar ba shi ba, kalle kalle ta fara, qofar shiga gidan ta kalla, hawaye ne suka zuba mata tunawa da mahaifin ta da ta yi. A kunne ya rada mata, "Ki na barin wannan  iskancin ko sai na ci maki mutunci" Da sauri ta hau goge idanun ta, yayan ta da ya fito kuwa a zaton shi wata kalma mai dadi aka fada mata, ta daina kuka. Ciki suka shiga............ A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 15 Masha Allah, shi ne kawai abinda Musulmin kwarai zai ce in ya ga abinda ya masa kyau, ko ba mutum bane, ko da waje ne, ko tufafi, ko abun hawa, indai ya maka kyau ,to ka ce masha Allah, shi ne abinda Hansatu ta fadi a qasan ran ta, an gyara gidan su sosai ,ya yi kyau kamar ba shi ba. Mahaifiyar ta na zaune a daya daga cikin kujeru na alfarma, ganin su Hansatu ne ya sanya ta miqewa tsaye, ta na murmishi, hannu ta bude mata, Hansatu kuwa ta na isa sai ta durqusa a qasa ta hau kuka, kuka ne da duk mai raunin zuciya ya kalla sai ya koka, mahaifiyar ta ma kan ta hawaye ta ke, "Hajiya ku yafe min, na aikata babban kuskure akan so, na qi bin umarnin ku, Hajiya dan Allah ki yafe min, daga yanzu ba zan sake tsallake maganar ku ba" "Hafsat ta shi kin ga yaran ki na kuka, tashi na yafe maku , da ke da mijin ki, qaddarar samun wadannan kyawawan yaran ne ta raba ki da mu, mun godewa Allah da ya sanya ta hanyar aure kuka same su, ba ta hanyar banza ba, mu ma muna da laifi, da mun hakura mun bi me kuke so da haka bata faru ba, da ace ke din baki samu kyakkyawar tarbiyya ba, da lalacewa zaki, tunda ki ka tafi ban qara yin lafiya ba, hawan jini ya kama Ni, saboda yawan tunani, amma alhamdu lilLAAH daga ranar da na je na gan ki, zuwa yanzu n fara samun lafiya a jiki na, dan haka daga yanzu ke da iyalin ki, ba mu yi muku shamaki da ko ina ba na gidan nan" Isa ne ya zube guiwa bibbiyu ya na godiya, tare da matso kwallar dole, "Hajiya mun gode da yafe mana da kuka yi, Allah ya qara girma da daukaka, Allah ya qara arziki, mun gode" Murmushi Hajiya ta yi, Yayah'n Hansatu ne ya daga Isa daga durquson da ya yi, shi kuma ya na ta wani sunne kai, kamar na Allah, yaran shi na ta bin shi da kallon mamaki. "Mun zama daya yanzu, ka daina godiyar nan haka" Kwalawa matar shi kira ya yi, mai suna Aziza, ta kuwa taho cikin izza da mulki, kamar wata sarauniyar gaske, sai buda hanci take, ta na rufewa, ita a dole ga matar mai kuddi. "Haba Baby wanga wane irin kira na? Me ne ne?" "Qauna ta Hafsat da na ke fada maki? Ita ce ta zo," Wani kallo ta bi Hansatu da shi daga sama har qasa, tabbas ga kamanni nan, amma wannan wacce irin shiga ce a jikin ta? " "Wagga d'in ita ce qaunar ka?" "Eh ita ce, tai ki sa a kawo masu abincii da an ka tanada domin su" "Ni fa na mance ban ce a yi wani abinci na musamman ba, amma dai an yi na dare, a wajen su kuwa na san zai zama kamar na ranar sallah, ina zuwa" Daga Hajiya har Yayahn ba wanda ya tanka, kunya ce ma ta kama su, suka hau yi ma su Amina wasa, murmushin yaqe Hansatu kawai take yi, lallai matar yayan ta batta da mutunci da dukkan alamu. Kafin wani lokaci qanqani an cika dinning table da abinci kala kala, qamshin shi ya sanya yunwar cikin su motsawa, ta yanda har ana iya jiyo kukan yunwar ta na neman agaji, cikin wasa Hajiya ta ce, "Wayyyooo wayyoo ni yunwa taa, yi hakuri bari kuka haka nan, yanzun ga zan baki abinci ki tafi" Dariya su Ahmad sukai ta yi, ta na riqe da hannun Bilkisu da Ahmad Amina na biye da ita suka zauna a kan kujerun table din, plates ta sawa kowa a gaban shi, ta na tambayar su me za su ci, da sauri Hansatu ta isa ta karba ta na zuba masu hawaye na zubar mata, mahaifin ta ta tuna, a baya in ta na zuba masa abinci, ya na mata wasa, tare da sanya mata albarka. Dafa kan ta Hajiya ta yi ta ce, "Allah ya miki albarka, ki kasance cikin farin ciki har qarshen rayuwar ki" "Ameeen Hajiya ta" Isa ya gama qulewa, sun tafi sun bar shi, yunwa sai narkar masa da tumbi take, ko ta ma waiga ta kalle shi, balle ya mata alama, kwafa ya yi a hankali, sannan ya furta, "Za mu je gida ne" Yayah ne ya kama hannun shi, ya ce, "Suruki na mu je mu ci abinci," A zaqe Isa ya miqe, ya na zama kuwa, kazar da ke gaban Hansatu ce ta tsone masa ido, to ta riga ta san halin gogan nata, dauka ta yi ta mayar plate din gaban shi, da murmushin yaqe, "Ah ah, Hafsat ci naki mana, ga wani nan zuba masa," Isa maida hannun shi baya ya yi, da har zai kaiwa kazar damqa, hansatu da ta san halin mijin ta, cika masa plate ta yi d kyau, kusan duk abinda ke kan table din sai da ta sa masa,ba kunya ba tsoro, ba godiya haka ya fara ci, su Amina sun jima da fara cin abincin su. Shiru ka ke ji, banda qarar cokula da taunar Isa ba ka jin komai, hakan kuwa ba qaramin bata ran Aziza ya yi ba, cin abinci kamar wani akuya, dan tsaki ta ja, sannan ta ce, "Haka ka ke cin abinci?" Kafe Isa ta yi da ido, ta na yatsina fuska, cike da nuna kyankyamin shi, dan murmushin yaqe ya sakar mata, ya ci gaba da cin abincin shi, da qarfi ta daki table din, sai da yaran suka razana, ta ja kujera baya, ta bar wajen. Ta na tafe ta na masifa da harshen turanci. "Ku yi hakuri da halin Azizah, in baki manta ba, akwai wanda muka zaba Maki ki aura a baya, qanwar shi ce, yanzu haka su na da hannun jari mafi yawa a kamfanin mu, yayan nata ke riqe da kamfanin, mutumin kirki ne matuqa, amma Aziza dake renon qasar waje ce, tarbiyyar ta da tamu ta bambamta, a haka ta fara barin wasu munanan halayen mutanen can, ku ci abincin ku, ku rabu da ita, a qasan ran ta, mutuniyar kirki ce, ba ko da yaushe take haka ba" "Ba bu komai Hajiya,Allah ya sa ta gyara halayen ta gaba daya, domin ku ci gaba da jin dadin zama da ita" "Ameeen" shi ne abinda yayan ta ya riga kowa fadi, ya na mutuwar son Aziza, amma halayen ta na baqanta ran shi. Bayan kammala cin abincin su ne, Bilkisu ta ga Hajiya ta goge bakin ta da tissue ta ɗora a kan ragowar abincin ta, ga qashin da ta ci ta tauna duk ta zuba a sauran abincin, tashi ta yi tsam ta dauke, sannan ta kalli Hansatu ta ce, "Umma ai dai ba kyau wulakanta abinci ko? Hajiya ki dena bata abincin da kika rage, kar watarana ki rasa abinda za ki ci, Umma bari na samo leda mu qulle sauran mun dumama gobe" Kunya ce ta kama Hansatu matuqa, Hajiya kuwa da Yayah yi sukai kamar ba su ji me Bilkisu ta ce ba, kwashe wanda suka zuba a saman plate din suka yi kawai, suka tara a wani empty mazubi dake wajen, "In Allah ya yarda daga yau ba zaku sake zama da yunwa ba kunji?" Daga kai yaran sukai suna kallon Uncle din nasu cikin farin ciki. Basu suka fara shirin komawa gidan su ba, sai bayan isha'i,Hajiya ta haɗa masu ashirin ta arziki,dan kuwa sai da bayan mota ya qi rufuwa. Kayan sawa ne, na Hansatu da yaran, da na Isa kan shi, Isa kuwa bayan sabbi shi da Hansatu har da kwance na Yayah da Aziza da Hajiya suka samu, yaran ne kawai aka sai masu sabbi tun kan su je. Har qofar gida motar ta tsaya, Yabbuga na jin qarar mota ta diba da gudu ta labe a zaure, ta na leqen su, Dan Jumma kuwa mamaki ya gama kashe shi,gulmar ta ta har ta kai, su na tsaka da hirar su ta zabura ta yi waje haka? Sai da ta gama ganin kayan da Isa ya shigar shi da Hansatu sannan ta koma ta labe a katanga, daidai inda ta kan ji maganar su, ta na tsaye ta ji maganar Isa, "Bubbude mu ga meye a ciki, dan iskanci shi ne dazu ku ka tafi cin abinci kuka bar ni zaune ga dan iska, na je gidan su Mata ta cin azziqi ko?" "Ka yi hakuri ba haka bane" "Dalla Malama bude naga me aka saka a ciki," Ganin abun azziqin ne ya yi yawa, nan da nan ya fara washe baki, ya na zuba, har zama ya samu waje ya yi, ya na ma Hansatu hira, mamaki ya gama kashe ta. Ranar Isa sai da ya gwada mata soyayyar da suka dade ba su yi irin ta ba. Ta ji dadin hakan matuqa, addu'a ta dinga yi Allah ya tabbatar da su cikin azziqi mai albarka. Yabbuga kuwa ta nade komai jira take washe gari ta yi ta guntsawa qawayen ta na gulma, duk yanda ta so ta yi maganar abu da Dan jumma ya qi bata hadin kai, tai ta Masifa ita daya, har bacci ya dauke ta......... Sai mu jira uwar gulma ta tashi daga kwana😅 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 16: Da misalin 8:12am, Yabbuga na tsaye a qofar dakin Hansatu, riqe da jug din da ta ciko shi da wani tsinkakken kunun da ta tsulawa ruwan zafi, sai sallama take wage baki ta na dokawa, Isah ne ya fito ya na miqa, rigar shi a kafada, ko kauda ido Yabbuga ba ta yi ba, ta fara gaida shi , "Ango na Hansatu, an kwan lahiya?" "Lahiya lau, qaqa an kayi yau kittaho gidan ga da swahiya haka?" "Ohhh ni Yabbugan Dan jumma abin arziqi dai be amshi kare ba, wagga tambaya awab-ba a son zuwa na?" "Ni ban ce ba, na ga dai ba ki saba taho wa da sahe ba, Ni rabo na ma da na gane ki gidan ga na mance" Sai a sannan kunya ta kama Yabbuga. "Yo jiya ina zaune na kunna gidan redio nijji Mallam na wa'azi akan zama da maqwacci lhiya, shi na nicce bari mu gyara, rayuwar ga ba tabbas" Isah dai kurkure bakin shi ya yi, ya fice. Hansatu ce ta qarasa fita tsakar gidan, dan dama ta na tsaye, ta nutsu ta yi shiru ne kar a ce kuma ta yi laifi. "Barka da sahiya Yabbuga," "Barka dai Hansuwa, shin ina 'yan yara ban gane su ba" "Su na ciki, karatu Ni ka masu, ke san abinda ya hwaru, ina tsoron barin su sake hita,kuma dama basu zuwa boko, to mu na karatu a gida " "Allah Sarki, tauu ga wanga nikkawo musu, a gasa hanji, ko da dai na ga jiya kun tai gari a mota," Cikin dariyar son jin gulma ta yi maganar, Hansatu murmushi ta yi ya karba, ta na godiya, a zaton ta Yabbuga tafiya za ta yi, sai ta ga ta na qoqarin binta ciki, kasa hana ta shiga ta yi, suka shiga ciki, kayan da Yabbuga ta gani jibge sun so tsorata ta, amma ta dake, "Ah ahhh wanga abin arziqi hwa, daga ina?" Murmushi kawai Hansatu ta yi, ta nemi tsohuwar tabarmar ta ta shimfidawa Yabbuga, tunda suke a unguwar wannan shi ne zuwan Yabbuga na Shida har ta zauna a dakin ta. Tun ta na farko farkon zuwa, lokacin ta na da abubuwa,sai kuma yau. Abu kamar a mafarki kawai Hansatu gani ta yi yabbuga na bude buhuna ta na leqawa, mamaki ma ya hana Hansatu magana, Ita kuwa ta na budewa ta na Suratu, tare da yaba abubuwan da ta gani. Isah ne ya shigo, tare da fadin, "Ku jira Ni ina zuwa," Dakin ya fada ba ko sallama, Yabbuga kuwa qamewa ta yi a gefe, dan tun da ta ji Muryar Isah ta daina leqen buhunan. "Ke miqon wannan buhun da na ware jiya," "To" Shi ne kawai abinda Hansatu ta ce,gashi ga buhun ya dauka amma ba zai dauka ba sai ya sata aiki. Da kyar ta ke jan buhun, ta kai waje, kayan abinci ne danqare a ciki, da suturu masu tsada, ya tattare, a cewar shi ba ya so su saba da abin duniya ,shi kuwa ba shi gare shi ba, kuma da iyayen ta suka tula musu kayan abinci ba na cefane da shekarun shi zai sai kayan miya? Maza ne a tsakar gidan guda uku, daya mai gwanjo ne, daya mai shago ne, daya mai sai da kayan abinci ne na awo. Sai da Hansatu ta fitar da buhu uku, sanan ta koma ta na maida numfashin baqin ciki, da gajiya. Ta na tsaye ya gama siyar da komai, aka bashi kudin ya kalmasa a aljihu. Ya kalli Hansatu da ke tsaye , "An jima ki dafa taliya, mun kwana biyu ba mu ci ta ba, kwai ragowar manjan nan ko? Ki soya, ga hamsin a siyo yaji, wannan ashirin din ki sai Maggi, kin San taliya da manja akwai dad'i,se na dawo" Miqa mata saba'in ya yi, ya fice, amsa ta yi ta na masa addu'a har bakin qofa, ta koma ciki, a zuciyar ta ta ji dadin kudin da ya bayar, a qalla an samu sauyi, tunda da ko kwandala baya bayarwa (to kudin da ya saida abincin fa?) Mamaki ya gama kashe Yabbuga, amma cikin ran ta fari kwal, domin yau ta guntsi gulma me dumi a bakin ta, jira take su Lamishi su dawo daga aiki a zauna majalisa ta guntsa musu suma. Sallama ta wa Hansatu ta tafi, ta na shiga Dan Jumma ya fara tambayar daga ina take. "Gidan makwatta nittai, ko an hana ziyara ne a hadissan da kk karanta min kullum?" "Ah ahhh ni ban ce ba, amma ziyara ba halin ki bane sai kin so gulma" "Dan Jummaa Ni ka ka kira magulmaciya?" Bai amsa ta ba ya fita, tare da sanar da ita ga dari uku nan a sai kayan miya, shi ya tafi. Masifa ta dinga yi, kamar akwai me sauraron ta, ta yi ta kuma ,ita a dole an fada mata sunan da ba halin ta bane. *********************** Yamma ce liss, garin na fitar da hucin zafin ranar da ya kwankwada da rana,wanda ke waje, kuma a unguwa irin ta yaku bayi, shi ya ke dandana kudar shi, dan kuwa ba shi da abubuwan more rayuwar da zai sanyaya jikin shi, balle ya samu ruwa mai sanyi ya sawa tumbin shi ya ji dadi. A gidan gwamna Halliru kuwa Hajiya Ikee ce ta shiga dakin Sultana, Wanda ta kashe fitilu tsaf, ta ke kwance cikin duhu, idanun ta da suka kumbura na kulle, ta takure waje guda hawaye na zuba a cikin su. Sanyin da ke ratsa dikkan wani sashe na jikin ta ya sa ta rawar dari, Hajiya Ikee ce ta dau remote din AC ta rage sosai tare da fadin, "Haba Sultana, wagga wace rayuwa kin ka ɗorawa kan ki ta jidali? Ke zauna ke dai a daki, awar wata mayya, ke ware kan ki, rayuwa kuwa za ta yu a haka?" Juyar da fuskar ta gefe ta yi, sannan ta goge hawayen ta a hankali, fitilun dakin Hajiya Ikee ta kunna, da sauri Sultana ta kulle idon ta, saboda hasken da ya gauraye dakin ta. "Tashi mu je, Daddyn ku ka kiran ki," Kamar ba za ta tashi ba, amma ta miqe da kyar, cikin tsananin gajiya da zaman da ta ke a daki, bude wardrobe din ta ta yi, ta dauki wata riga jallabiya mai kyau, kalar ja, ta sanya a kan qananan kayan nata. Mayafin ta yafa, ta fita, ba tare da ta jira Hajiya ba. Su na isa katafaren parlour'n da ke dauke da manya kuma fararen kujeru,sai manyan hotunan shugaban qasa, mataimakin shi, gwamna da mataimakin shi, sai daya gefen hoton ahalin gidan ne, su na dauke da farin ciki, da nishadi ,sultana na rungume a jikin Sultan su na dariya, iyayen su ma na rungume da junan su. Parlour'n komai fari ne, sai carpet mai kalar green da ratsin baqi, glass table babba a tsakiya da gefe da gefe, sai suka qayata kwalliyar wajen. Sultan na ganin qanwar shi ya miqe, ya tarbe ta, kanta a qasa ta gaida shi, y amsa, duba fuskar ta ya yi, ya ga ta na murmushin yaqe. "Sulty baby me ke damun ki ne haka?" "Me zai dame ta kuwa? Banda tunanin talakawa da tassa ga rayuwar ta, ka san diyar Daddy akwai tausayi, taho nan wajen daddy kin ji Sultyn Daddy" Cike da shagwaba ta zube a kujerar da yake zaune, shi kuwa ya rungume ta ta gefen shi na dama. Cikin kulawa, da lallashi ya fara magana, kamar wani na Allah. "Sulty na, ina so ki sani, ita rayuwa ta na zuwa ma kowanne bawa ne ta yanda Allah yasso, sannan shi wanga abu da kin ka ga shi na hwaruwa iko ne na Allah, ba lehin mu na ba shuwagabanni, lehin talakawa na, domin kuwa da damar talakawa da ki ke gani sun hi masu kuddi iskanci, sun ji masu kuddi sabon Allah, shi nassa Allah ke jarabtar su, ba komi na ba, amma masu mulki na da lehi suma, wajen qin tallafawa talakawa, ta yanda za su samu abin yi har su taimakawa wasu, to wanga tunani da niyyi yassa nacce, daga yanzu zan bude maki gidauniya, da zaki zanka taimakon talakawa, ki na shiga duk inda kk so, dan ki tallafawa talakawa, na amince maki na yarje maki, Amma da sharadi " Hamdala kawai take jarawa, tare da share kwallar farin ciki, cikin sauri da azama tace, "Daddy fadi sharadin ka, in Allah ya so ina cika shi" "Sharadin shi na, office zan bude mi ki, ba na son yawan yawo, ki nemi ma'aikata da kan ki, shi ma shi na cikin taimakon da zaki hwara, Sannan akwai driver da na samo maki, ban yarda ki hita ko da da bakin gate na , ba tare da shi ba,ya zame maki tamkar inuwa, duk inda kin ka sa qawahun ki shi aje na shi nan, har office ina so in kittai, shi zam shi na tsaye bakin gambu, ba driver bane kadai, yanda zai kula da rayuwa ta haka zai kula da taki, ina ji da shi cikin masu yi min aiki gaba daya, ki yarda da shi ba zaki wahala ba" Maganganun shi duk sun shige ta, kuma ta riqe su kaff a kwanyar ta, dan haka tace, "Daddy na yi ma alqawarin kula da dukkan sharudan ka, na gode na gode na gode Daddy na" Sultan ma farin ciki ya kama shi, ganin farin ciki a fuskar qanwar shi. Hajiya Ikee ce ta ce, "Tau yau dai ki na hitowa cin abinci damu ko?" "Eh, yau da Ni za a ci abinci, Ni zan serving kowa, na hutar da masu aiki" "Hhhhh sai ka ce ke ki ka dahwa, dan dai serving abinci, ai ba aiki na ba" Cike da shagwaba ta kalli Daddyn su da ke danne dannen remote dan sauya tasha, hankalin su na kan hirar shi kuma ya ga ana nuna wani mummunan ta'addanci da aka yi ma wata rugar Fulani, wanda abun ya bashi mamaki, dan ba shi da hannu a lamarin, to waye ya aikata hakan? Ya na sauya tashar ya ji Sultana na fadin, "Daddy ka ga Yah Sultan kooo" Murmushi ya ɗan yi a takaice, sannan ya ce, "Sultan za ka sha mamaki duk sanda Sulty Baby ta maka abinci mai dadi ,sai ka bani ajiyar kunnen ka guda" Dariya sukai ta yi, cike da nishadi suka ci gaba da hira. *********************** Gwamna ya sanar da Lawwali duk wani tsare tsare da shirin shi, ya kuma damqa amanar sultana a hannun shi, ya nuna masa mahimmancin kula da lafiyar ta, da bata kariya, ya yabe shi akan irin jarumtar shi, da ganin zai iya kula masa da gudan jinin shi. Lawwali kuwa ya sanar da gwamna zai kula da Sultana da rayuwar shi,kafin wani abu ya same ta sai ya fara samun shi,gwamna ya yarda da Lawwali matuqa. Lawwali ya koma gida cike da murna da farin ciki, wayar Lamishi ya kira dan a hada shi da farin cikin ran shi wato Mubaraka. Ko da ya dauka sai ya ji haniya,tsaki ya ja, dan ya san ta na can majalisar tasu ta gulma ne. "Lamishi ya da ai a hada Ni da Mubaraka ne? Na san ki na can majalisar ku ta gulma," "Lawwali za ka ci uban ka, Ni ka ka hwadi ma magana haka ba ladabi? Tau dan uban ka Ɗan Talo, ko shi be isa hwada min ba sukari ba" "Shi kin ka ce, dama tsoron ki shike" Cikin dariya ya yi maganar, dan kuwa hango ta yake ta karkace ta qanqance idon nan zata fara zabga masa masifa, tunawa ya yi ashe ya sai ma Mubaraka waya,kit ya kashe wayar, Lamishi kuwa dai zuba ruwan masifa take, tare da yi masa alqawurran rashin mutunci duk sanda ya je gidan. Ko da ta kula ya kashe wayar ma bata dena wayar qarya ba, dan kuwa Yabbuga ta hanga ta ga yanda tai shiruuu ta nutsu, kamar ba ita ke zuba masu gulmar gidan Hansatu ba, tsoron da Yabbuga ke wa Lawwali ya shahara, ba tun yau ba ko waya ya kira Lamishi in su na tare, tari wannan bata so ya kwace mata,wani ashar Lamishi ta danna kamar ta na yi da Lawwali, ware ido Yabbuga ta yi, ta na kada yatsa, alamar Lamishi ta bari. Sai da Lamishi ta gama wayar qaryan ta sannan ta ce, "Dan babbar butar me gari kai, aza shi kai dan shi na tantiri a waje, Ni ma za ze gagare ni, to ni na ci uwar dan iska na yaga zani, Allah shi maido shi gidan lahiya, zan nuna masa Ni na haihe shi,Ni uwar shi ce a dabanci" "Um ummm Lamishi, ki dena Jan Lawwali da hwada, in kai nai ya juye walle shi na manta ke uwatai ta shi yanka maki dukan wahala" "Ke arrr, matsoraciyar banza, nan nan ko tari Lawwali ya yi gudu kike, sai ka ce ke ba qawar uwatai ta ba" Yabbuga da ko dogon labarin Lawwali ba ta so a yi ce ta kalli hanyar da mijin ta ke dawowa ta ce, "Ohhh yau Dan jumma ko ina ya tsaya, bari in shiga gida in zuba mai ruwan arwalla ga buta" Habaa me su Mai Buruji za su yi, banda dariya,yau Yabbuga ke son zubawa miji ruwan alwala, saboda tsabar an kirayi sunan dodon ta, bata kula su ba ta fada gida, ta na shiga ta rufe gambu ,(qofa). Hijabin ta ta cire ta hau mita, "Bahaushe ya ce hanyar lahiya, a bita kullum kullum (a bita da shekara ) ina nika yarda uwa tai ta je ta ambaci suna na gaban wannan me danyen kan shi biyo ni har gida shi yi min aikin ganganci? Ban wallah daukan kasada," Butar ta dauka zata zuba ruwan, me ta yi tunani kuma oho, ta fasa ta fada dakin ta. *********************** Yau mutan gidan Gwamna Halliru sun tashi da bayyanannan farin ciki, dan kuwa Sultana farin cikin su ce, a duk sanda take walwala, to suma su na walwala, sanda kuwa take cikin qunci, suma fa ba za su zama cikin farin ciki ba, har sai ta koma normal. Hakan ce ta sa gwamna yi mata abinda zai sanya ta farin ciki. Cikin doguwar riga baqa mai fadi mai stones kalar blue da farare su na ta walqiya kamar fuskar ta, ta fito, riqe da jaka, da wayar ta a hannu. Sultan ma cikin shiri, ya fito, dan su na son su je su ga inda Foundation din nata yake. Hajiya Ikee an sha ado na alfarma ita da gwamna , sai qamshin turare masu tsada ke tashi, Sultana ta yi mamakin ganin irin motar da aka ware domin kai ta da komowa da ita daga duk inda za ta, tsohuwar motar ta ta kalla, ta ga batai komai ba, last year aka sai mata, ta so yin magana, amma bata son ta bata moment din, ba komai, zata san ya da ta yi da waccan din. Qamewa ta yi a lokacin da ya bude mata qofar shiga mazaunin da ya dace da mace mai aji da kima kamar ta,qamshin turaren shi ta shaqa cikin salo mai burgewa, ta kuwa burge Lawwali,idanu suka qurawa juna. Wata iriyar faduwar gaba ce ta kama Sultana, abinda tunda take a rayuwar ta ta duniya bata taɓa ji ba game da kowa, idanun ta ta lumshe a daidai lokacin da ya furta, "Ran ki shi dade, Bismillah" Tsigar jikin ta ce ta kowanne kusurwa da kafa ta jikin ta ta miqe, 'Waye wannan?' Shi ne abinda zuciyar ta ta furta a hankali, uniform din shi ta kalla,ta rasa gane a wanne bangaren tsaron yake, bayan ta zauna ne ya shiga mazaunin driver ya zauna shima ,motocin su Gwamna ne a gaba, sannan ta su, sai ta masu tsaron lafiyar su na take masu baya. "Wane ne kai?".......... *Wane ne shi ? In ji Sulty Babu* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 17: "LAWWALI DAN TALO" "What?" "Eh suna na kenan, Ni ne sabon drivern ki, kuma guard din ki," "Ok, kuma sunan ka kenan? LAWWALI DAN TALO?" Murmushi Lawwali ya yi, ya ce, "Eh sunan kenan Ranki shi dade, ko akwai matsala na?" "Ah ah , tambaya d'ai Ni kai, amma zan iya kiran ka da Auwal?" Wani irin murmushi ya yi, mai sauti, wanda ya narkar masa da duk wata gaba ta jikin shi, nan da nan ya ji ran shi ya haskaka, Mubarakan shi na kiran shi Auwal, ga Sultana...na neman izinin kiran shi da Auwal, cikin sauri da alamar bada hakuri Sultana ta ce, "I am so sorry pls, ba niyya ta na sauya maka suna ba, na ga kamar Auwal da Lawwali daya ne, shi ya sa, i can call u with whatever u want me to," (zan iya kiran ka, da duk abinda ka ke so na kira ka da shi) Shi ma cikin hanzarin da zaquwa ya ce, "Ran ki shi dade, ki kira Ni da Auwal, sunan da nih-hi so na wallah, qauna ta dai ka kira na da wanga suna ,shi nas-sa kin ka ji na yi shiru" Sultana ta ji dadi da ba ta bata masa rai ba, dan haka sai ta daga kai kawai, ba ta son ta yi maganar da zata sa ta yi dana sani, ta rasa dalilin da ya sa ta ke ta surutu da mutumin da ta fara gani yau, har da qoqarin sauya masa suna. Tafiyar awa daya da wasu 'yan mintuna ce ta kai su unguwar da Foundation din yake, motoci sun tsaitsaya, Gwamna da Hajiya Ikee da Sultan suna tsaye su na jiran ta fito, ta tsaya mamakin ganin motocin 'yan jarida da police su zagaye wajen, ga mutane mabuqata an tara su a wajen, dama Daddyn nata ya yi wannan shirin ne? Lallai da gaske yake yi, amma abinda bai mata dadi ba shi ne, yan jarida da ta ga suna tsaitsaye su na jiran fitar ta, ba haka ta ke son gudanar da qungiyar ba, ba ta buqatar sanar da duniya abinda take yi, ta na son yi ne domin Allah. Kamar Sultan ya karanci tunanin ta, kurdawa ya yi cikin mutanen, ya ɗan taba kafadar Lawwali da ya bude mata mota ya na jiran ta fita, matsa wa ya yi, ya tsaya a gaban ta, cikin murya mai taushi ya ce, "Sulty baby fito mana, kar ki damu da mutanen nan, ki fito kawai abin ki ki ga waje, sannan ki bawa wadannan mabuqatan abincin,da ke a can wajen, an yi haka ne dan wasu mabuqatan su ga wajen su zo gare ki neman taimako ke gane?" Daga kai ta yi, amma a qasan ran ta, da an barta, shi mai neman taimako ai ba ya buya, a duk inda suke za ta nemo su. Cike da jin kunya ta fita, dan bata saba da irin wannan abubuwan ba, shi kan shi Sultan bai ji dadin yanda mahaifin nasu ya tallata abun ba, da ya san za ai haka da bai zo ba, yanzu hotunan su da video din su zai ta zaga gari. Yanka dan kyallen da aka Saka a bakin qofar shiga building din ta yi da almkashin da ya sha ado da kyalle, addu'a ta yi a zuciyar ta, ta neman sa'a, da nasara akan abinda ta sa gaba, tare da kariya daga dukkan sharri, sannan ta sanya qafata ta dama ta shiga, har cikin offices din guda bakwai, sai manyan store rooms guda hudu, wajen kamar dan irin buqatar ta aka riga aka gina shi,tabbas abinda take buri kenan n biyu a rayuwar ta bayan koyarwa, to ga dama ta samu. Hawayen farin ciki ne ke son saukar mata, ta maqale su, Hajiya ta rungume, itama ta rungume ta, nan da na kuwa aka hau daukan su hotuna, ji ka ke kyas kyas kyas, Gwamna Halliru ne ya dafa kan ta, sannan ya rada mata wani abu, da hanzari ta daga kan ta, suka fita zuwa farfajiyar wajen, Lawwali na can daga nesa ya yi zooming din ta a wayar shi ya na mata video ,fuskar ta cike da annashuwa da annuri ta ke rabawa mabuqata abinci. Buhun shinkafa ,qaramin buhun sugar, sai omo, sabulu, mangyada, man ja, indomie da gishiri, su ne abubuwan da sultana ta dauki awa biyu ta na rabawa. Shiri na musamman aka dauka live ana yaɗawa a gidan talabijin n garin Zamfara ,nan da nan kuwa wasu mutanen suka ji qaunar sultana ta shige su, wasu kuma banda zagi da tsinuwa ba abinda suke mata, wasu zagin ta suke da mahaifan ta har su na fadin. 'Dubi kayan jikin su, shi kadai ya isa wani talakan ya ci da kan shi na wata uku, a haka suke son taimakawa' Kowa da abinda ya ke fadi, domin shi ɗan Adam kayan Allah ne, ba mai iya masa, ba tare da sun san me ne ne a zuciyar ta ba, sun yanke mata hukunci. Yanda Sultana bata gaji ba haka ma Lawwali bai gaji da ɗaukan ta ba, domin kuwa gwamna da Hajiya Ikee da suka ga abun ba na qare bane, tafiya suka yi, suka bar ta, Sultan ya so zama, Hajiya ta tisa shi a gaba suka koma gida tare. Mutane kuwa kamar ingizo su ake, qara zuwa wasu suke, su na layi, Ita kuwa miqawa take, cike da farin ciki, da murmushi, da za a bude qirjin ta wataqila hasken dake ciki sai ya kashe na wani ido, saboda tsabar haske, da farin cikin da ke ciki, tabbas dukkan mai bayarwa domin Allah farin ciki ya tabbata a zuciyar shi . Sun bar wajen da azahar, ba dan sultana  ta so ba, sai dan komai ya qare ne, har da kudin dake jakar ta sai da ta bayar. Mutane na ta mata addu'a, wasu har ran su, wasu kuma yi kawai suke, a gefe su na zagin ta, da iyayen ta, su na fadin na munafurci ne, dan an kusa zabe ne, ya ke son ya yi amfani da ita, dan ya zarce. Sultana na ta daga ma wata dattijuwa hannu ta fada motar ta, Lawwali ya mayar ya rufe. "Ran ki shi dade ina muka nufa?" "Gida" Shi ne abinda ta fadi, ta kwantar da kanta a jikin motar, fuskar ta dauke da murmushin da ya kasa gushewa, ko gajiya bata ji a jikin ta, saboda jin dadi. Lokaci zuwa lokaci Lawwali na satar kallon ta, a duk lokacin da zai dora ido akan fuskar ta, sai ya ji jinin jikin shi ya tsinke, ya qara gudu, ba qaramin kamu son ta ya masa ba. Har suka isa gida bata daina fara'a ba. Bude mata motar ya yi, ya tsaya dan ta fita ya rufe, bata san ya na yi ba, dan durqusa wa ya yi daidai kunnen ta kadan ya ce, "Ran ki shi dade mun iso," A firgice ta kalle shi, fuskar shi ta kalla, ta ga ba wani alamar wasa, ko murmushi, sanar da ita kawai ya yi, ya kalli gefe, ajiyar zuciya ta sauke mai qarfi, ta masa godiya zata fita, har ta fara taku za ta shige ta dawo baya, ta kalle shi, shi ma ita ya kalla, idanun su cikin na juna ta ce, "Sultana,...ka kira Ni da sultana" Cikin hanzari ta bar wajen, bin ta ya yi da kallo, cikin wani irin yanayi, domin kuwa ta gama kashe masa duk wata laka ta jikin shi . Jiki ba kwari ya rufe motar ya gyara parking , sannan ya kashe ya tafi gidan shi ,tun a hanya ya kira Mubaraka ya na bata labarin yanda komai ya kasance, ta na ta taya shi farin ciki, ashar din Lamishi ne ya katse mata wayar da take da Yah Auwal din ta. Komawar su kenan, ta hangi tukunyar tuwon su na zubewa, rude ya tafasa ya malale a qasa. "Dan uwar ki bani wayar nan, dama Lawwali ya d'ai sai wayar ga ne, amma na san watarana sai ke yi min ba daidai ba, garin uban ki ka samo shi ko muwa? Mu ka tahiya da zahi, da rani, da damina mu nema, mu kawo a ci ba Dan Talo ba, yanzu da kin ka bari ya tude ki na da abinda zaki dahwa muna? Bani...bani wayar nan, yau sai na liqa Maki kashin wahala (sai ta mata dukan wahala)" Mubaraka miqa wayar ta yi, ta hau qoqarin guduwa, Mai Buruji na fadin, "Du Allah dai ki kyale diyar ga Lamishi, dubi fa wanga aiki da tayyi Ita dai, ko ina qal qal qal, dan dai ta tussuwa talge? Ana iya yin wani, ballantana ma ga abinci mun zo da shi" "To radio uwar zance, tunda niyyi niyyar liqa mata kashin wahala sai na buga in ji dadi, da ki ka hwadin abinci, nan nan wannan mijin naki me mutuwar zuciya mun ka wuce da abukkai nai waje, su na jiran mu kunce su canye" Wata zabura ta yi da ta sa kajin gidan da Mubaraka, da Mai Buruji tsere, shigar Yabbuga kenan ta ga ana tsere, Mubaraka na ta ihu ta na bada hakuri, Mai Buruji ta maqale qofar dakin ta su na dariya ita da Kameelu, Yabbuga ce ta sheqe da dariya ta ce, "Yau na ga ikon Allah ma daki kusa, mace ci nesa" Ai ta na fadin haka zuciyar ta ta tuno mata Lawwali, wani irin tsoro ne ya kama ta, in ya shigo ya ga ana dukan Mubaraka, gaba dayan su sun shiga uku. Cacima ta kai wa Lamishi ta na son kare Mubaraka daga dukan ta, cikin rashin sa'a Lamishi ta fadi qasa, qafa ta gurde, salati ta zabga, tare da rusa ihu, Dan Talo ne ya keta cikin gidan a guje ya na fadin, "Mi an kai, wam-mutu? Shin mi na na yah-hwaru wanga salati har garka ana ji" Ya na cikin maganar ya lura da Lamishi uwar gidan shi a qasa, ga Yabbuga da Mai Buruji na qoqarin daga ta, bayani Yabbuga ta masa daga qarshe ta ce, "Walle Dan Talo da ta ba Mubaraka kashin wahala Lawwali ya yi ajalin mu har lahira gwanda ta qalle qawahu na baro qohwata na yi jinyar ta, ina nika iyawa da bala'in Lawwali ?" Har daki suka kai Lamishi ta na ta rusa kuka, mai gyara aka kira ya je ya duba qafar, aka yi addu'o'i aka shafa man shanu da kade, mai gyara ya ce, "Lamishi ki kula da qahwar ki turmushe na kin kai, kar ki zan ka aikin da zaki wahal da ita, nan da sati kina warkewa, Allah shi bi da lahiya" (Turmushe, targade) Lamishi baccin wahala ne ya dauke ta, Mubaraka kuwa ta san ta ja wa kan ta dukan da ita ma in ba ai sa'a ba sai ta kwanta, dan haka kuka ta fara, ta na addu'ar Allah ya mantar da ita me ya faru ya ba wa zuciyar ta hakuri. Haka Lamishi ta kwana qafa ta yi haushi, ta kumbura,miqo min dakkon kuwa har Dan Talo ranar bata bar shi fita ko ina ba. Washegari...... *Cassss ga washegari mutuniyar ku 😅* A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 18: Washegari da sassafe bayan Mubaraka ta yi sallah, ta ɗora abin karya wa, ta share gidan tsaf, ta wanke bayi, zuwa bakwai da arba'in 7:40am, ta gama komai, wanka ta shiga a gurguje, da niyyar ta shirya ta gudu zuwa makaranta , ba tare da sanin kowa ba. Sai da ta tabbata ta aje ma Lamishi komai na buqata, sannan ta tafi ta sanya uniform ,ta rataya jakar ta, ta na saka takalmin ta ta ji kiran Lamishi, cikin faduwar gaba, tare da saddaqar wa akan ba zata makaranta ba yau ma ta tafi amsa kiran Lamishin, "Na'am Umma gani" "Dan uban ki Dan Talo ina kk Shirin tafiya? Kin nakasa ni sannan ki tafi zuwa makaranta? Baki wallah zuwa ko ina, je ki shirya ki bi Mai Buruji," Wani irin kuka Mubaraka ta fashe da shi ,a rayuwar ta ta tsani duk abinda zai hada ta da gidan gwamna, kuma ta na hango alamun Lamishi na son ta maida aikin gidan kamar na gado, tunda suna yi itama se ta yi shi. "Dan soyayyar ki da Annabin rahama Umma kar ki aika ni gidan can, ki barni na tai zuwa makaranta, na kwana biyu ban tai ba, Umma..." "Ki na ruhwa min baki ko se na fashe shi? ....Mai Buruji...ke Mai Buruji...in ke qare ku tai da wannan lalatacciyar, ta maye gurbi na, kin san sultana ta fara zuwa aiki," Mai Buruji da aka kwalawa kira ce ta shiga dakin sannan ta ce, "Na ko ga Sultana na son Mubaraka, ya kamata mu tafi lokaci na wucewa" Cikin kuka Mubaraka ta shige gaba, ko uniform din ma qin cirewa ta yi, suka tafi. Sun isa gidan tara da rabi ta yi, Lawwali na tsaye jikin motar Sultana ya na jiran ta, uniform din nan sun sha guga sai sheqi suke, ga qamshi na tashi a jikin shi, waya yake da No 3 ya na sanar da shi duk abubuwan da suke faruwa, tare da neman sani akan wasu abubuwan da ya kamata su yi, rashin shi a wajen ba shi ke nufin tsayawar ta'addancin su ba, ta waya ya ke sanar da su duk wasu dabaru da makirce makircen nakasa mutane bayin Allah. Tsayawa ya yi da maganar da yake, a daidai lokacin da mata guda biyu masu matuqar mahimmanci a rayuwar shi suka tsaya a gaban idanun shi. Sultana ce ta fito cikin simple shigar ta mai kyau, da ɗaukan hankalin mai kallo, a daya gefen Mubaraka ce saye da uniform idanun ta sun yi jawur saboda kuka. Wayar shi ya soke a aljihu ya nufi Mubaraka, cikin tsananin damuwar da ta bayyana a fuskar shi, jijiyar gefen goshin shi ta fito, cikin Muryar shi ta asalin dan daba ya ce, "Wane ne? Wane me qarar kwanan ne ya sa ki kuka?" Hawaye ne suka gangaro mata, Mai Buruji ce ta sakada za ta wuce ya mata wani mugun kallo ta koma ta tsaya cak, tare da fadin, "Lawwali ina ni ina tabin Mubaraka? Ai ba karen maguzawa na yaccijen ba, walle ba ni ta ba, Lamishi ce ta hana ta zuwa makaranta, tace nan za ta taho, ta yi wa Sultana aiki, jiya ta samu turmushe"(targad'e) Rintse idon shi ya yi, cikin baqin ciki ya kama hannun Mubaraka, sannan ya kalli Mai Buruji ya ce, "Ke ki yi wa Sultana aiki, makaranta take so, makaranta zata je, so kuke ta zauna ta zama jahila kamar ni?" Sultana na tsaye ta na mamakin abubuwan da ta ji kuma ta gani, dama Lawwali dan su Lamishi ne? Sai yanzu da ake magana ta ga kamannin shi da Mubaraka, duk da ba sosai bane, amma akwai kama ta jini, har yanayi ya mata da Lamishin ma. Waje ya nufa dan sama mata adaidaita sahu duk da ya san hakan zai wahala a irin wannan unguwar, amma ba zai damu da nisan inda zai je ba, dan farin cikin qanwar shi. Sun dan yi nisa Sultana ta daga murya ta ce, "Auwal..ku shiga Mota mu aje ta makaranta ,sai mu wuce daga can" Hanyar mota Sultana ta nufa, su ma suka juya suka koma wajen motar, durqusawa Mubaraka ta yi, ta gaida sultana ta amsa cikin kulawa, bude ma Mubaraka Lawwali ya fara yi, sannan ya zaga zai budewa Sultana, ta daga masa hannu, ta bude da kan ta ta shige . Sai da ya dauki hanyar makarantar su Mubaraka sanan fushin shi ya fara tafiya, ba zai bari a tauye ta ba, ba zai bari a lalata rayuwar ta a tagayyarar da rayuwar ta kamar yanda aka yi wa tashi ba. Sultana na kula da yanayin shi, tare da jinjina irin qaunar da yake ma qanwar tashi, ya kuma yi matuqar burge ta, sai ta ga qimar shi da darajar shi a idon ta. Cikin murya mai taushi Sultana ta ce, "Ashe Auwal Dan uwan ki ne? ...Auwal ashe ita ce qanwar ka da ka ke fadin ita kadai ke kiran ka da Auwal?" Wata ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi, tare da sakin murmushin da ya bayyanar da irin son da yake ma qanwar tashi. "Eh Ran ki shi dade, ita ta qauna ta da nika batu akai jiya" "Allah Sarki, ashe ku din yaran Lamishi ne, na ji ki na fadin ta samu turmushe, ya yi tsanani ne sosai ?" Dan bata rai Lawwali ya yi, dan ya qudirta da ya aje Sultana zai je gidan ya tada ma Lamishi da duk wani ragowar hankali da ya rage a jikin ta. "Eh jiya ta fadi amma da sauqi an gyara mata, an dai ce ta bari har ya warke ne kar qafar ta samu matsala ," "Allah Sarki in kin je, ki ce ina diba ta, Allah shi bi da lahiya" "Ameen, zan hwadi mata" Burki ya ci a gaban makarantar su Mubaraka, goma har ta yi, ana qoqarin fita break, Mubaraka ta san me yake shirin yi, dan haka da sauri ta fita ta tare shi, "Yah Auwal kar ka shiga dan Allah, in ma bulala ce za a min, na cancanta, kwana na biyu ban zo ba, yau na je late bai kamata ba, su nada 'yancin yi min komai, malamai na ne, ballantana ma ba zan shiga yanzu ba, saura yan mintuna a tashi break sai na hade da sauran ɗalibai kawai" Kallon gate din ya yi, ya ga a bude yake, ya kalle ta ya ga ta na murmushi, bai san sanda shi ma murmushi ya kwace masa ba, sai ya nemi baqin cikin da yake ciki ya rasa,ya rasa kalar qaunar da yake ma qanwar shi, niyyar shi ya shiga ya buga masu warning akan kar a taba masa qanwa, amma ta hana. Dafa kan ta ya yi, sannan ya rungume ta kadan, Sultana da ke kallon su cikin sha'awa da burgewa ce tai saurin daukan su a hoto ta na murmushi, hannu Lawwali ya zira aljihu ya bata dari biyar,sannan ya koma mota, ta na ta daga nasa hannu shi da Sultana ,sultana ma hannu ta daga mata, dauke da murmushi, zai tada motar kenan aka fita break, dan tsayawa ya so yi ya ga shigar Mubaraka, sai kuma ya fasa, ya bata ma Sultana lokaci matuqa ba tare da ya yi tunani Ba, sai a wannan lokacin ya ga tsaurin idon shi . Hakuri ya dinga bawa Sultana, har sai da ta masa shiru, tunda ta ce ba komai, amma yaqi ya dena bata hakuri. "Ran ki shi dade kin yi shiru, ko dai ba a yafe min laifi na bane?" "Wa ya ce maka ka yi lehi? Ai kai lambar yabo ya kamata a baka, a matsayin ka na yayan da ya fi kowanne yaya so da qauna tare da kulawa ga qauna tai, ina ganin soyayya da kusanci na da Sultan amma naku, ya burge ni sosai" "Koh Ran ki shi dade?ina godiya da yabawa, yabon ki ya fi duk wata lambar yabo ko girma da za a bani, " Murmushi ta samu kan ta da yi, ba ta sake magana ba har suka isa, shi kuwa leqen ta ta madubi, shi ne ya zama aikin shi . Bude mata qofar yayi, sannan ya take mata baya har office din ta, akwai mutanen da ta kula da su a jiya da ta ke bada taimakon nan, yau ma sun zo, su na ganin ta suka taso, fess da su,da alama mutane ne masu ilimi. Har office suka je, Lawwali ne ya gabatar mata da su, domin ya san su, suma 'yan gwagwarmayar siyasar mahaifin ta ne, amma su mutane ne masu gaskiya da amana, gwamna na amfani da su in ya na son isar da saqon addini, ko kuma saqo wajen mutanen kirki, dan ya siye zuciyar mutane a ce shi din na Allah ne. Ya rasa dama aikin da zai basu tun kafuwar gwamnatin shi, kullum suka je neman aiki hakuri yake basu, bude wannan NGO ya taimake shi sosai, dan haka ya ce su zo su taya sultana aikin. Sultana ta ji dadin ganin su sosai , dan haka ba bata lokaci ta tattauna da su, ta kuma zabawa kowa bangaren da ya dace da shi . Da taimakon su ta fara kasafin yanda zata gudanar da qungiyar, aiki ya sha kanta, da wannan damar Lawwali ya samu, ya tafi gida ba tare da sanin ta ba. Ko da ya isa ya wuce Yabbuga a qofar gidan Asshibi, ta qurawa motar shi ido ta na son tai gulma dan bata gane motar waye ba,idon su karaf ya fada a na junan su, rakubewa ta yi a jikin ginin gidan Asshibi ta na salatin da ko iyawa ba ta gama yi ba, Lawwali da ya san yanda Yabbuga ke mugun tsoron shi ne ya ci wani wawan burki dan nesa da su, ta na ganin haka, sai ta yi zaton baya ze yi ya je wajen su, bangaje Asshibi ta yi, ta afka gidan ta, ta na salati, ko ina na jikin ta rawa yake, Lawwali kuwa me zai banda dariya,qarasa wa ya yi gidan su,ya bude ya shige . Lamishi na ta baccin ta hankali kwance. A tsaye ya tsaya mata, ya ce "Lamishi...Lamishi, shin kwana ki kai ko mi?" Bude ido ta yi, tare da qanqance su, tsaki ta doka sannan ta ce, "Sannu uba na, nicce sannu ubana, lalatacce tambadadde fado min a kai za ka yi? Ka tsaya min a ka kamar za ka hwado?" "Ba wannan ya kawo ni ba, Barakana ba zata yi bautar gidan Gwauna ba,in ki na bari har ki ji sauqi tau, in baki bari ki hakura da aikin, ai dama kun tsufa barin ku kawai sun kai dan an saba, amma me kuke in kun tai?" Kofin da ke gefen ta ta dauka ta maka masa a guiwa, ko gezau be ba, yo wace wahala ce shi be sha ba, "Ka hwa rammin Lawwali, (ka fa raina ni Lawwali) in ce ga abinda za ai ka ce ah ah? Za ta dawo ta samen tunda ta kai qarata wajen ubana" "Ni dai na fada maki, bata koma zuwa aiki wani gida, sai da son ran ta" "Ka san bana jin magana, se ka buga zan gane me ka ke cewa ubana...kuma wane irin kaya ne na gani jikin ka? Jahili dai ka ke balle in ce ko aiki ka samu na taimakon qasa" Ran shi ya yi mummunan baci da kalmar Jahili data jefe shi da ita, ba dan ya na musun shi din jahili bane, amma su waye silar zaman shi Jahilin? Wani mugun kallo ya wurga mata, sannan ya sa kai ya bar gidan. Zagin dai da ta saba, wanda shi ne ya dauki kaso saba'in na lalacewar shi, shi ta dinga qunduma masa, ta na maimaitawa, tare da fadin Mubaraka za ta same ta, su a dole qungiyar 'yan hadin kai, to duk abin su ita ta haife su, sai ta so kowa ya zauna lafiya, da sauran kalamai munana marasa dad'in saurara. Da misalin qarfe uku na rana suka koma gida, Sultana ta so lokacin tashin su Mubaraka bai wuce ba su dauko ta, haka nan take jin son yarinyar, ta alaqanta hakan da ilimin da ta kula Mubaraka na da shi. Sun isa gida sun tarar da Mubaraka ta kwaso wankin kayan sultana daga ɓangaren wanki na gidan, za ta mayar cikin gida. Ko a fuska ran Lawwali bai ɓaci ba, tunda Mubaraka ma bata da damuwa akan hakan, shi dai ko ma mene zatai ya zama ta na son abun, da kuma dukkan alama ta na jin dadin aikin, ba bacin rai a fuskar ta, sai ma walwala. Da hanzari ta aje kayan ta nufe shi, tare da yi musu sannu da zuwa baki dayan su, jakar Sultana ta amsa, sai sultana ta riqe, cikin murmushi ta ce, "Na gode, na hutar da ke, kar gatan ya min yawa, ga wanki kin debo, a ina za ki riqe jaka? In yau kin kai min gobe wa zai kai min?" "Ko Ni Kin kai wa izini har ciki sai in kai miki, ballantana Mubaraka," Kallon Lawwali Sultana ta yi, tare da sakin murmushi mai kyau, ta wuce ciki, ta na shiga suka tafa, "Yah Auwal da alama Aunty Sultana na yin ka hwa, ka ga wani murmushi da tayyi maka?" "Allah ya sa, wannan murmushi halayyar ta ne, kowa ma yi mishi ta kai, Allah shi nuna min ta yi min irin wanda ni kai mata,....ke ci abinci?" "Ameeen Yah Auwal, eh na ci abinci ,kafin Mama(Mai Buruji) ta tafi gida ta ban abinci, nima na kusan gamawa, wankin sultana kawai zan je in isuwa" "Tau ya yi, In ke qare ki yi min magana, zan jira ki can garka, mu tai gidana, da kai na zan maishe ki gida, dazu na tai gida ai" Nan ya bata labarin me ya faru tsakanin shi da Lamishi, idanun ta ne suka kawo ruwa ta ce, "Ni dai dama baka tai ba wallah, yanzu ta na iya gwada min bone kan haka da kai, ya kamata ka rage kulawa da ni, tunda bata son haka nan" Wani kallon baki da hankali ya mata, sannan ya duqa ya dauki kwandon wankin, ya dora Mata akai, ya tallabe qeyar ta cikin wasa, yar qara ta saki, ya mata gwalo ya tafi, tare da sanar da ita yana jiran ta, sultana da ke tsaye jikin window'n dakin ta ne,ta saki labule, ta na murmushi, su na burge ta sosai. Har dakin sultana Mubaraka ta shiga, bayan ta yi sallama, ta bata izinin shiga, ita ta jera mata kayan inda ya dace ,sannan ta tambaye ta ko da abinda zata mata? "Babu komai, amma ina so na tambaye ki," "Allah ya sa na sani" "Inshaa Allah, kin ma sani, Ni kuwa na ce, ke da Auwal maman ku daya Abban ku daya?" Da kallo Mubaraka ta bi Sultana........ Kallon da ya gajiyar da ni burutu😂😂 A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 19: "Yaya na ne, uwar mu guda uban mu guda da shi, amma ya girme ni sosai, mu na da wasu qannen maza ne su, guda biyu," Ajiyar zuciya sulatana ta sauke, sannan ta yi murmushin ta da ke qawata kyaun fuskar ta ta ce, "Masha Allah, makarantar ku guda da qannen naki?" "Ai su Jameelu ba su zuwa makaranta,yawon su kawai suke a unguwa, duk gidan mu ni kadai ta ka zuwa makaranta" Gyara zama Sultana ta yi, cikin rashin fahimta ta ke kallon Mubaraka da ke mata bayani, "Yah Auwal ya yi karatun allo, har ya kai ga sauke qur'ani, kamar yanda na ji labari, amma ban taba jin labarin ya yi boko ba, zama da masu ilimi na ya sanya shi koyon karatu da rubutu, sannan ya iya turanci kad'an, amma bai je makaranta ba, ni kuma kin ga wadda karatun nawa shi ke, yau in an bar ni na tai, gobe ba zani ba,su Jameelu kuwa ba su ko son zuwa makarantar Allah balle ta bature" "Ikon Allah, zan so zuwa shiyyar ku niga wadda take, watarana" "Kai ka kaiii, lallai ko da mun ji dad'i mara misali, ace ke da kan ki kin tai shiyyar mu,ko ba dan matsayin da ki ke da shi ba ma, domin kyawun halin ki da kullum Umman mu ke fad'a a shiyyar mu" "Mubaraka kenan, to ni din wata ce daban? Ni ma mutum ce kamar kowa na duniya, a duniya babu wanda ya fi wani, sai wanda ya fi tsoron Allah, yawan dukiya, matsayi, muqami duk ba su na mutum ba, tsoron Allahn da bawa shike da shi, da kuma kyakkyawar mu'amala su ka yin mutum, ke gane?" Daga kai Mubaraka ta yi, sannan ta ce, "Aunty in tambaye ki? Dan Allah kar ran ki ya ɓaci da tambaya ta" Kada kai Sultana ta yi, sannan ta bada hankalin ta ga kallon Mubaraka. "Aunty yaushe na zaki aure?" Dariya ce ta kwacewa sultana , ta ce, "Mubaraka kenan, ni da ko saurayi ban da wa zan aura?" Zaro ido Mubaraka ta yi cike da mamaki, sannan ta ce, "Aunty ko dai ke ta baki kula su? Ko ni din nan, maza na cewa su na qauna ta, balle ke, aunty Sultana ke gane ki kuwa? Wa zai ce ba shi son mace kamar ki?" Murmushi kawai sultana ta yi, domin ita maganar ma saurayi ko miji bata gaban ta tun da can, a kullum damuwar ta be wuce ta ga yanda zata fara aiki dan ta koyar da al'umma abinda Allah ya sanar da ita ba, sannan ta bude gidauniya ta na taimakon mutane, to yanzu ta samu buri d'aya ya cika, wataqila za ta duba maganar aure a nan gaba, domin maganar lecturing da take son yi da alama ba zai samu ba. Lokaci Mubaraka ta kalla, ta ga ya tafi sosai, har hudu da rabi,da sauri ta miqe tsaye, "Subhanallahi, na manta Yah Auwal na waje ya na jira na, na tsaya surutu" "Jiran ki kuma? Yanzu ki na nufin sai mutum kamar Auwal ya tsaya jiran ki? Namiji ne fa, ba su son jira" Murmushi mai dauke da tsantsar so da qauna Mubaraka ta yi, sannan ta ce, "Aunty Sultana, ina so ki sa ido akan Yayana da kyau, a hankali za ki san wane ne wannan Auwal din, Yah Auwal daban shike cikin maza" A bakin qofa Sultana ta tsaya, dan sauraron Mubaraka ba ta san ma ta na bin ta ba. "Zan sa ido na biyu akan Yah Auwal din ki Mubaraka, sai gobe, ki gaishe da Lamishi da jiki" "za ta ji" A gurguje ta fita daga katafaren gidan, a zaune ta tadda shi a saman kujera ya na bacci, tsinke ta samu ta saka masa a hankali a qofar hanci, ai kuwa atishawa ya saki mai qarfi, miqewa ta yi ta na dariya, daga baya ta kama kunnen ta ta na bashi hakuri, kama ta ya yi, ya daga hannu kamar zai mare ta, cikin wasa ya san daki kuncin ta kadan, suka yi wa masu gadin qofar gidan da ke kallon su cikin sha'awa sallama, suka fita. Sultana bata bar jikin window ba har sai da ta daina hango su, fuskar ta dauke da annuri ta fada wanka. A hanya kuwa Mubaraka ta kwashe duk yanda sukai da Sultana ta sanar da Lawwali, murna a wajen shi kamar har ta ce masa ta na son shi. Ko da suka isa gidan shi, sai da suka ci suka sha, ta yi wanka, ta maida kayan da ta cire, suka dauki yar qarama kuma tsadaddar motar shi da gwamna ya sai masa, tunda yanzu ba ya cikin tawagar su ta daji,ya na buqatar mota, ko da fitar gaggawa ta kama. A motar suka isa gida, kafin su shiga Mubaraka ta lallaba shi ya sai balangu mutumin Lamishi, har da kaza da madara, suka isa. Ko da suka shiga gidan shiruuu, ba kowa, ajiye ledojin hannun ta tayi, ta lelleqa, ba kowa da gaske, to ina suka je? Ina ita Lamishi me jinya? Tsaki ya ja, sannan ya zauna su ka hau hira, ita kuma ta duba ko akwai abincin dare, ko se ta ɗora, gani ta yi akwai a flask, da zai ishe su, na gidan gwamna ne, dan haka ajiye naman ta yi, ta ce in sun dawo daga duk inda suka je an ci. "Ke da kissani? Ta na can yawon gulma" "Yah Auwal ina fada maka ka dinga tausasa harshen ka ga uwayen ka, umma ka ke fadin ta tai gulma" Irin abun nan ya yi na 'yan mata masu yanga,  ya murguda baki, ya yi fari, shi a dole an masa fada. Dariya ta yi, ta ce, "Dama Aunty sultana ta gan ka" "Ki na ganin duk mun ka hadu in yi mata haka nan? Za ta so ni?", "Walle ba ruwa na, in tayi shiri shiri kwancin kwana ta shere ka mari, ka gan ka kuwa? Awab-budurwa wallah"(ba ruwa na in ta yi kwance kwance ta kwad'a ma mari, ka ganka kuwa kamar budurwa) Dariya sukai ta yi, har Dan Talo ya shiga gidan a gaggauce, buta ya dauka dan zagawa, Lawwali na ganin shi,ya miqe ya daure fuska, "Lawwali, ai na hango motar ka ne, muna dawowa daga garkar Yahai, nicce bari na zo, ko zan samu wani abu, bari na hito daga yauce, (bayan gida)" Ya na fadawa bayi, Lawwali ya zaro dubu biyar ya ba Mubaraka Ya ce, "Amshi ki ba uban nan nawa me kwadayi, in ya hito daga tutun wahala, ban jira nai wallah, na tafi nemo yaki halal yaki haram din da suka so" Magana ya ke kamar da wasa, amma cikin zuciyar shi zafi take, a ce iyayen ka basu damu da inda ka ke samo kudi ba, kuma da ganin Lawwali sun san dai ba aikin jima  yake ba ko kafinta, ko dako, balle aikin office, Amma kullum nema suke a wajen shi, kuma basu yake, manyan kudi ma kuwa, se kace wani babban ma'aikaci, ko babban ma'aikaci watarana ya na zama bai da shi. Mubaraka da ke tsaye cikin tausayin Yayan nata ne ta amshi kudin, ta na so ta bashi ko da hakuri ne, dan ta san ya yake ji, amma ya fice, tun kan ta ce komai. Dan Talo da ya fito ya ga ba Lawwali, a zaton shi ya tafi ne, nan da nan kuwa ya hau ashar, ya na kiran lawwali da sunaye marasa dadin ji. "Gashi hwa, ya bar maka kuddin, ya dai tafi ne an kira shi ga waya" Baki Dan Talo ya washe, ya na kuma godiya, soke su ya yi, a sassan aljihun jikin shi, sannan ya fita. Girgiza kai Mubaraka ta yi kawai, ta na nema ma ahalin ta shiriya. *********************** Su Lamishi kuwa su na gidan Isah, Yabbuga nan ta tattare su suka fada, har da Asshibi, yau ta samu leqa gidajen shiyya, duk gidajen mutuncin unguwar ba d'aya da Yabbuga ta raka ta, sai nasu ya nasu. Qarshe da suka shiga gidan Lamishi suka gaisa shi ne suka rankaya gidan Hansatu gaba dayan su. Sun tadda Isah na gida, sun gaisa su na ta wani hira kamar sun samu abokin su, kafin daga baya ya fada daki, da fita zai amma ya fasa,Hansatu kuwa ta gama dafa shinkafa da wake, ya ji yaji mai dadi, ga man ya samu matsayi har albasa aka saka masa. Nan dai Yabbuga uwar kwadai ta hau yaba qamshin girkin, Ita kuwa Hansatu jin haka ya sa dole ta debar musu, haqqin su ne sun ji qamshi tunda akwai ta zuba musu. (Da damar mutane rowa ta saka ba su damuwa da haqqin maqoci, a yi girki mai dadi, me qamshi a lashe a sude hannu, wasu ma maqotan su talakawa ne, amma ba za su sammusu ba, duk da dai yanzu duniya ta sauya, ka na iya bawa mutum dan Allah da haqqin maqotaka, ya ce dan a san ka na cin dadi ka bayar, amma ka tsarkake zuciyar ka ka bayar, mutum shi ya sani da ya maka sharri, sannan wasu in suka ga ana basu, sai su fara zaqewa da roqo, har mutum ya koma boye abu ya na rowa, da ace kowa zai gyara da an zauna lafiya) Su na kai loma su na zuba hira, rabi da kwatan hirar bata wuce ta auratayya ba, Isah na daki ya na jin su, ya na kuma jin dadin hirar saduwar auren da suke ta yi, Hansatu kuwa sai fada masu take, su yi a hankali mijin ta na ciki, Matar Yahai na bude baki kuwa, sai da ta fadi maganar da ta sa Hansatu shiga wani irin hali na matsananciyar kunya, su kuwa suka sheqe da dariya, Asshibi kuwa sai ta ji matan sun kwanta mata a rai,dan kuwa wajen hirar banza ta fi kauri dama. Hansatu ta gaji da jin maganganun su, masu sanya ta kunya, cikin tattausan lafazi ta ce, "Wai ku in tambaye ku? Me ne ne jigo a rayuwar aure ne?" "Saduwa mana heeeeee casssss" Suka yi shewa tare da tafawa, Isah kuwa dake daki, har sake gyara kwanciya ya yi, ya na sauraron su. Zama Hansatu ta gyara ta ce, "Tabbas saduwa daya ce daga jigon da ka sa a yi aure, amma ba ita kad'ai ba ce  jigo a gidan aure  ba, abubuwan na da yawa, su din ginshiqai na da ka riqon aure, in babu su da tuni aurarraki da dama sun watse. Na farko akwai yin auren ma shi kan shi domin Allah, sannan Yarda, riqon amana, saduwa, ladabi, biyayyah, soyayya, qauna, tausayi, ciyarwa,tufatarwa, wajen zama,girmama juna, qimanta juna, mutunta juna, tausayawa juna,iya girki,da wasu mahimmai dai. Wa'yanga abubuwa in suka hadu, aure ya ginu, ya zauna kenan sai dai in ajali nai na ya yi. Na fahimci me ya sa kuke ganin kamar saduwa ita ce kad'ai abinda ka riqe aure, ba komai na yasa ba saboda fadi da ankai cewar,Aure shike hada wata alaqa, tsakanin mace da namiji, wannan shi na  nufin hade rayuwarsu ta zama daya haka nan kuma makomarsu ta kasance guda daya. Kowacce irin al'ummah akwai irin matsayin da ta ba wa aure, Aure a musulinci wani daurine da shike halatta wa ma'aurata mace da namiji jin dad'i da junansu, ta hanyar saduwa  irin ta jima'i,da sauran mu'amaloli na jin dadin saduwa, Allah (subbahanawu wa ta'ala) ya halicci mace daga hakarkarin namiji ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu. Wannan babban dalili ne da zai sa ku ga kamar saduwa tahi komai a aure, amma duk wadda bata iya kula da miji ba, ta hanyoyi da dama, musamman iya girki, tsafta, kwalliya, ladabi da biyayya, bata iya magana ba, komi yattaho bakin ta hwadi takai, to wallahi mace na da saura a gidan aure ba ta iya komi ba" Gaba dayan su har Isah da ke kwance, hansatu ta basu mamaki, ba mace ba ce me yawan Suratu, amma sai gashi yau ta yi magana cikin ilimi da nutsuwa da fasaha. Mai Buruji ce ta fara yunqurawa ta miqe ta na sude hannu, "Tauuuu, Mallamar gidan aure mun gode da wanga ilimi da munka samu, bari mu tai mu dora a gidan mu mu ma ko mun zam matan so ga mazajen mu kamar ke, mun gode da wake da shinkahwa ke iya girki, shi yasa Isah ba shi iya cin abinci ko ina, sai gida " Dariya suka kwashe da ita, da shewa, dan kuwa magana Mai Buruji ta gaya wa Hansatu, ita da ake jibga kuma ake zagi kowa na ji, ita ke musu bayani haka. Murmushi mai ciwo Hansatu ta yi, sannan ta ce, "Ai duk abinda na fad'a  maku ba qarya ciki, ballantana ki fad'a  min magana, kuma ko da na fad'a ban ce ni ina aikata su ba,sannan ban ce ina da wani cikakken matsayi a wajen miji na ba, ballantana ya zama abin yi min arashi," Yabbuga ce ta taimaka wa Lamishi ta miqe, sannan ta kalli Hansatu ta ce, "Keee wagga kwantas kin ga gida munkai yanzu, shiga daki ki lallaba Isah dan kuwa duk ya walqita ya ga ba shinkahwar ga se ke mance da kin taba sanin mi na na ma'anar aure a musulunci" Dariya suka fita su na mata, kafin su rabu sai da suka yi ta gulmar ta, Yabbuga na basu labarin yanda yake dukan ta da zagin ta, akan abu qalilan. *Shin a maganganun Hansatu akwai gyara ne mutanen kwarai? In akwai gyara ko qarin haske akan zamantakewar aure a qaro mana ilimi* A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 20: Mata kala kala ne a duniya, musamman ta bangaren kwalliya, da gyaran jiki, kowacce mace da hanyar da take bi dan ganin ta yi kyau. Akwai wacce za ta yi gyaran jiki da kaya irin namu na gida da muke amfani da shi yau da kullum, kamar su lalle, dankalin turawa, sugar ,kwai, cucumber, tumatur, gwanda, Madara, lemo, zuma da sauran su, wadannan kadai sun ishe ta ba tare da ta yi kwalliya ba. Wata ta kuma kayan wanka na Bature kawai sun ishe ta, ba tare da kwalliya ba. Wata kuma ta na haɗawa duka , ta kuma qara da kwalliya. Sultana na daga cikin matan da basu damu da gyaran jiki da kayan amfanin yau da kullum ba, ta fi amfani da kayan gyaran jiki na Bature, masu gyara asalin fatar mutum ba tare da ta sanya shi fari ba, (wannan shi ne aji da waye wa, bleaching qauyanci ne da zubar da kuma da mutunci ga mai hankali amma tare da nuna wa Allah be iya ba, ya tauye ki, ke bari ki wa kan ki abinda ya gaza wa'iyadhubillah). Yau tun da Sultana ta fito daga wanka,ta ke tunanin wanne kaya za ta saka dan ta yi kyau, me za ta yi wa fuskar ta dan ta qayata ta? Ta jima zaune a dan qaramin table din, ta na shafe shafen mayuka da turaruka masu sanyin qamshi, yau ce rana ta farko da ta fara shafa kwalli, tare da shafa powder har dikin wuyan ta, jan baki ta jera a gaban ta ta na tunanin wanne za ta shafa, kalar purple mai haske ne idon ta ya sauka akai, dauka ta yi ta goga kadan, sannan ta hade kyawawan labban ta, kallon kan ta tayi a madubi, ganin yanda ta yi kyau ne ya sanya ta sakin murmushi mai laushi. Maskara ta shafa ma gashin idon ta mai yalwa, ta gyara girar ta, abun shafa powder ta sake dauka ta gyara ko ina na fuskar ta. Kallon wayar ta ta yi, ta ga ta na ringing, Sultan ne ke kiran ta, amsawa ta yi cikin sallama, da gaisuwa. "Ok ina nan tafe ,bani minti biyar," Kashe wayar ta yi, cikin sauri da zare ido, ashe ta dauki lokaci mai tsawo haka? Lallai masu yin kwalliya su na cin lokaci, anyaa za ta dore kuwa? Kayan ta ta nema wanda ta saba sawa ko da yaushe, wato doguwar riga irin ta larabawa, in ta saka irin su su na amsar ta sosai, duk da ita din ba wata fara bace sosai, amma ba za a kira ta baqa ba, fatar ta na da haske sosai . Ta na kammala shirya wa ta dauki jakar ta, ta sanya takalmin da ya zo da jakar ta ta, wayar ta riqe a hannun ta, ta na sake duba time din da ta bata. Ta na daf da sauka daga yar matattakalar benen ne ta tsaya cak, Lawwali ta gani tsaye da Daddyn ta su na magana qasa qasa. Daddyn ta da alama ya shiga damuwa sosai . Da dan hanzari ta isa gare su, takun takalmin ta, da qamshin turaren ta ne ya sanar da su zuwan ta, Lawwali na dora idon shi a kan ta, ya ji kamar an zare masa dukkan wata damuwar shi,da lakar  jikin shi, har wani lumshe ido ya ke. Shi abinda ka ke so, Indai ka gan shi, komai munin shi kyakkyawa ne a wajen ka, ballan tana kyakkyawa ji za ka yi kamar ba abinda ya kai shi kyau a duniya. Sultana kallon Lawwali ta yi, ta ga yanda yake kallon ta, kunya ce ta ji ta kama ta, sai ta ɗan sunkuyar da kan ta qasa, ta na murmushi, bai san sanda na shi ya bayyana ba, gaishe da Dad din ta tayi, sannan ta gaishe da Lawwali, da hanzari cikin girmamawa Lawwali ya mayar mata da gaisuwar. "Daddy lafiya? Na ga hankalin ka a tashe?" A dan daburce ya kalle ta, ya hau yaqe, ya na dafa kafadar ta, tare da shafa kuncin ta ya ce, "Sulty baby ba abinda ke damu na, dama ina tsaye ne ina jiran ki fito, kowa yunwa yake ji, amma ba ki fito ba, sai kuma gashi masha Allah, na ga yau kin yi wata iriyar kwalliyar da ban taba gani kin yi ba" Dan kwabe fuska ta yi, cikin shagwaba, wanda ya sanya Lawwali dan jingina da jikin ginin da ya ke tsaye a jiki ,tare da hard'e hannun shi a qirji,ya lumshe idanun shi a hankali ya sauke su akan ta. "Daddyyy ban yi kyau ba ko? Let me go and clean my face, yanzu zan dawo" Da sauri Lawwali ya ce, "Wacce baki kyawu ba? Ke gane ki kuwa? Tunda ni ke duniya ban taba ganin mace kyakkyawa awakke ba" Wani irin farin ciki ne ya lullube Sultana, har gwamna Halliru zai fassara maganar Lawwali, sai suka ji Muryar Sultan na fadin. "Ba ka yi qarya ba Lawwali,bayan budurwa ta ban taba ganin kyakkyawar macen da ta hiki kyau ba Sulty Baby" Dan tura baki ta yi kadan sannan ta ce, "Wace budurwa ka ke da? Bayan tsoron mata ka kai" Dariya aka sa a wajen, suka nufi dinning table, aka bar Sultan da son kare kan shi, shi ba tsoron mata yake ba, kawai dai tausayin su yake ji. Hajiya Ikee ma zama ta yi ta na dariya, tare da taya Sultan kare kan shi. "Sultan ai jarumi na wallah ,matar shi sai diyar sarki ko shugaban qasa" Lawwali na gaishe ta ta yi kamar bata ji ba, ita ta qi jinin talaka, masu aikin ta kaf ba dadin ta suke ji ba, Lawwali da ya ga ta qi amsawa hanyar fita ya kama abin shi,dan  ya basu waje, sai ya ji Muryar Sultana na fadin "Auwal ka ci abinci kuwa?" Cikin jin dadi, ya juya ya kalle ta, a ranshi ya na ayyana ta na bashi abinci a baki, da sauri ya kawar da tunanin ya amsa da . "Eh na ci,in ke qare ki dai yi min magana mu tai" "Tau ya yi" Fita ya yi,ya nufi can baya inda suke shanya a gidan ,waya ya dauka ya kira No 2, bata wani jima ta na ringing ba ya dauka, cike da damuwa da tsoron Ogan nasu. "Hello, No 2 garin ya kuka bari ya gudu? Wanne irin daqiqanci ka damun ku? Dazu 1 ya kire Ni yacce min wai tsohon gwamna ya gudu, ka sani, duk kun ka bari ya hita dajin nan baku nemo shi ba, da hannu na zan halbe ku, dukan ku, umarni na ne, ku hita har da su Sa'adatu a nemo shi duk inda ya shiga, bai isa hita wajen nan ba yanzu, ku bazama da motoci a nemo shi, da kun ganai ku halbe shi, kar ku jira komai, kuma ku sani, zan bincika, duk wanda nikkama shi na da hannu a taimaka masa ya hita,.....duk wanda ya taimaka masa.....hummm sai na zo dai kawai," 'Oga....' Kafin No 2 ya yi magana Lawwali ya kashe wayar, cikin fushi ya tafi, ko daya je ya tarar Sultana na ta neman shi, dan sake fuskar shi ya yi,sannan ya je da sauri ya bude mata qofa, wayar shi ce ta yi qara ya duba 'Excellency' shi ne a jikin wayar, daga wa ya yi, tare da yin qasa da Muryar shi, "Kar ka damu ranka shi dade, na bada umarnin a nemo shi, da na aje ta za ni nima" 'Ah Ah kar ka kuskura ka bar min yarinya ita daya, ka tsaya a wajen ta, ban yarda ka matsa ko ina ba,' "Amma ranka ya dade..." 'Umarni nake baka ba shawara ba Lawwali' "To ran ka shi dade," Kashe wayar ya yi, ya shige motar ya ja su suka bar gidan,ya kasa sake fuskar shi saboda bacin ran da yake ciki, rashin zaman da ba ya yi sosai a wajen yanzu ya sa su na sakaci da abubuwan da ya kamata su na bawa mahimmanci. Sultana ta dan damu da  ba ta ga ya kalle taba, sai ta samu kan ta da jin ba dad'in rashin kallon ta da ba ya yi a yau. "Tsayar da motar," Ta madubi ya kalle ta, cike da mamaki, kauda kai ta yi kamar ba ita ta yi magana ba, "Ran ki shi dade mi kicce?" Dora idanun ta tayi a nashi sannan ta ce, "Dan koma baya kadan, ka tsayar da motar daidai waccan matar mai suya qosai" Komawa baya ya yi, ya tsayar da motar, tunda ya dora idon shi akan ta ya manta da tunanin da ke a zuciyar shi ,fita ta yi, matar na ta soya qosai, ba mutane sosai a wajen, saboda hantsi ya fara. "Assalamu alaikum, baba a bani qosai na nera dari," "Wa'alaikumussalam, to yarinya ki dan jira ke ga ni dai akwai wasu gaban ki" "To Baba" Lawwali ne cikin hade fuska ya nufi wajen zai magana, Sultana ta marairaice ido, ta masa alamar ya bari, yanayin yanda ta yi ya shige shi, amma sai ya koma ya tsaya a gefen ta, Ita kuwa kallon unguwar take, ta na kuma wa, da alamar su na buqatar taimako,yara baja baja ba masu zuwa makaranta, ita fa ta na son makaranta ,ta na bawa makaranta mahimmanci, ta na son ganin yara na zuwa makaranta, ba ta son ta ga yaran da ya kamata ace su na aji, ta gan su su na wasa a unguwannin su. Wani yaro ne da zai kai shekara goma sha daya, ya keto a guje ya tada qura, saura kadan ya fadi, cikin qiftawar ido Lawwali ya tare shi, sultana kuwa har ta rufe ido, dan kuwa ta saddaqar zai fadin, shiru ta ji, dan haka sai ta bude ido a hankali, "Ke gani bai fadi ba? Yara irin wannan sun hi ki son jikin su," Cikin murmushi ya fadi hakan, Itan ma murmushi ta mayar masa, tare da maida hankalin ta kan yaron da ke raba ido a tsakanin su. "Me ya sa ka ke wargi ba ka tai makaranta ba?" (Wargi wasa kenan) "Ba a biya min kuddin makaranta ba" "Ina ne gidan ku?" "Shi na can bayan shiyyar ga" "Me ya kawo ka shiyyar nan?" "Wargi nittaho wajen diyoyin innata  (wasa na taho wajen yaran innata)" "Ohh su ma ba su tai makaranta ba kenan" "Uhm" "Ok to mu tai na ga gidan ku, za ka kai ni?" "Mi za ki yi gidan mu?" Dariya ta yi sannan ta ce, "Zan gaishe da maman ka ne, na ce ta na da yaro mai hankali" Shiru yaron ya yi, tare da saurin amshe hannun shi zai gudu, Lawwali ya riqe shi, ya daga fuskar shi, ya na kallon dan baqi kyakkyawan yaron, "Ina za ka tai,ka rake mu gidan ku mana," "Mama ta ta mutu masu halbi na sunka halbe ta, baba na shi na inda likita da Goggo ta, an halbe shi a qafar  shi guda,likita ya ce za a yanke,ba kowa gidan mu" Sultana na jin wannan labari sai hawaye ya fara gangarowa saman kuncin ta, Lawwali kuwa ji ya yi kamar an dora masa wani abu mai nauyi a qirjin shi,tun da ya ke bai taba jin haka ba, ko dan bai taba tsayawa ya yi magana da wanda suke illatawa bane? Gani ya yi Sultana ta ja  yaron ta rungume a jikin ta, ko kula da dattin jikin shi ba ta yi ba. Mutanen da ke wajen kallon ta suke da mamaki, da kuma birgewa, hankalin mutane ya fara yawa kan su Dan haka mota ta ja yaron suka nufa, ta zauna ya na tsaye gaban ta, ta kira Lawwali, ta bude jakar ta ta debi dubu goma ta ce ya bawa mai qosai, ta qara jari. Sai ga Mai qosai ta debo qosai me yawa ta kawo ma Sultana ta na ta godiya kamar za ta kwanta mata, ita kuma tana nuna ba komai. Amsar qosan ta yi, itama ta yi godiya, matar ta tafi, ta na ma Sultana addu'a. "Ina ne makarantar ku? " "Makarantar mu na can shiyyar mu, yawancin yaran shiyyar mu da na nan shiyyar ita suka zuwa" "Za ka raka ni a mota ne ko da qafa?" "Mu dai tai da qafa," Ya na dan dariya ya fadi hakan, Sultana ta fahimta ya na tsoro ne, ba ta ga laifin shi ba, zamani ya sauya, jakarta ta dauka da wayar ta, Lawwali ya kulle mota, suka taka. Har zuwa makarantar yaran, ana ta karatu, makarantar ga ta nan ne dai kawai, kuma a haka ta kudi ce, sallama ta yi, ta nemi ofishin shugaban makaranta aka kai ta, bata fito ba sai da aka lissafa mata adadin yaran da ba su biya kudi ba, ta yi alqawarin biya, suka bata account No,ta tura musu, sannan ta ce a sanar da yaran su ci gaba da zuwa makaranta, za ta dawo ta duba ko sun dawo,sallama ta musu ta tafi Lawwali mamaki ya hana shi ma bin ta su tafi, anya Sultana jinin Halliru da Ikeelima ce kuwa? Tsayawa ta yi a gaban shi ta ce, "In ka qare kallon nawa mu je ko?" Murmushin gefen baki ya mata, sannan ya ce, "Ai ke din ce Ran ki shi dade, bayan kyau da ki ke da shi,har da kyauwun zucciya, " Kunya ce ta kama ta, ta sunkuyar da idanun ta daga kallon shi, su na tafe su na dan yin hira, ta na jin dad'i in ya yabi kyawun ta, bata sani ba ko dan bata saba jin haka bane oho, kawai dai ta san ta na jin dad'i. Har suka isa mota, yaron na riqe da hannun Sultana, "To yanzu ina ne asibitin da Baban ka yake?" "Babban asibiti ne, amma ban san waje ba, Inna Rabi ta tassan waje,Ga gidan ta can, wancan me buhun" Bata gaji ba, sallama ta yi suka gaisa da matan gidan, gida ne na haya, mai dakuna da yawa ciki, Har qofar Innar shi Rabi ya kai ta, suka gaisa, ta mata bayanin haduwar ta da yaron, sai a sannan ne ta tuna bata san sunan yaron ba, Innar shi ce ta sanar da ita sunan shi Huzaifah, sultana sanar da ita tayi ta na son ta je duba mahaifin yaron a asibiti, ya za a yi? "Dama an jima kadan zanna kai musu abinci, mu tai na rake ki" Nan da nan ta shiga ta saka hijabi, ta kulle qofar ta, suka fita, motar da ta gani su na nufa ce ta dan tsorata ta, Sultana ta ce, "In ki na ganin akwai matsala ki min kwatance, zan bide su" Kunya ce ta kama Rabi ganin Sultana ta gano ta. Nan dai ta shiga suka tafi har asibitin, ta ga mahaifin Huzaifah, ta biya duk wani abu da ake buqata, bayan nashi ma har da na wasu mutum shida. Alqawarin sake komawa ta yi, watarana asibitin dan taimakawa masu jinyar. Sai da suka isa office din su, Sultana ta ke nazarin abubuwan da suka faru, tabbas masu neman taimako na asibiti, da irin unguwannin su Huzaifah, unguwannin talakawa, lallai yau ta samu wata babbar nasara a abinda ta ke da buri, alqawarin taimakawa mabuqata da ta dauka da yardar Allah za ta yi qoqarin cika shi duk da ta sani ba zata iya taimakon kaff mutanen garin Zamfara ba, amma zata qoqarta taimakawa wanda ya samu. (Shin irin su Sultana ne kawai ya kamata su dinga taimakawa talakawa? Ke me kike aikatawa na taimakon wasu? Kai fa? Mu tambayi kammu, a rayuwa kar mutum ya ce sai ya ci ya tada kai sannan zai bawa wasu, da kadan din da muke da shi da shi za mu taimaki wasu, masu kidnapping har gida wasu masu qarfin halin suke zuwa su yi su tafi, masu asiri da maita har gida suke bi su cutar da mutane, me ya sa masu taimakawa mutane ba su bi gida gida? Ba riya bane dan ka yi abu wasu sun gan ka sanda ka ke yi, niyyar ka ita ce ladan ka, baka sani ba da loma daya da zaka bawa wani ya ci Allah ya maka rahama ,mu kyautata niyya yayin yin aikin alkhairi, in dai mugaye za su bi gida gida su kashe, su sace, su cinye,to kuwa kai mai aikin alkhairi kai ka fi cancanta da ka bi gida gida dan kyautatawa, zamanin magabata na gari har gida suke bin wanda za su taimakawa, me ya sa muka daina? Ladan ne Bama so?) *Tambaya a gare mu baki daya* A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 21: Tafiya ya ke a cikin duhun dajin da suka yi wa hanyar mota da kan su, saboda yawan shiga da fita, babu hasken komai, sai hasken futilun motar, qarar tsuntsaye, da wasu dabbobin kawai ke tashi, bai tsaya a ko ina ba sai ginin da yake maboyar su, cikin hanzari ya fita daga motar ya shiga wajen, tun daga bakin qofa har ciki masu gadi ne riqe da muggan makamai, gaisuwa kawai suke miqawa wajen Ogan su da suka yi kewar gani kwana biyu, ya so ko da murmushi ne ya musu, amma bacin ran da ya ke ji ya hana shi sake musu fuska, sun kuma fahimci hakan. Qofar da za ta sada shi da inda aka ajiye Tsohon Gwamana No 5 ya bude masa, bayan ya gaida shi, daga masa kai ya yi kawai ya shige, a wata kujera da aka tanadar masa ya zauna, tare da harde qafar shi daya saman daya, kallo ya kafe mutanen dakin da shi, ya jima ya na kallon su,daga baya ya ce, "Wab-bud'e shi?" (Waye ya bude shi) Shiru wajen ya dauka, cikin bacin rai Lawwali ya zari bindigar qugun No 3 ya harbi qafar Tsohon Gwamna, wata iriyar qara ya saki, tin qarfin shi, jijiyoyin kan shi da na wuyan shi sun fita rudu-rudu, ya na so ya riqe qafar amma ba hali, saboda an daure hannayen shi, cikin rawar murya ya ce, "Wata yarinya ce, ......na mata ...alqawarin....million goma....in ta kunce ni.." Wata dariya Lawwali ya saki sannan ya ce, "Ku je ku kawo min su Sa'adatu, na ji a cikin su wacce mai qarar kwanan ce tab-bude shi" No 2 ne ya fita cikin sauri, Lawwali kuwa fada ya fara yi, "Meye amfanin ka a nan Inuwa( No1) kai ne fa babba yanzu, ka na mi da an ka bude shi, ko ka san hitar shi daga nan, daidai yake da tonuwar asirin mu! " 'Yan mata ne guda uku suka shiga kowaccen su sanye take da kaya kamar mai shirin fita yaqi,a cikin matan da ke wajen, su aka bawa horon fita da mazan in za a je cikin gari sato mutane ko wani fada ko wata hatsaniya dai. Daya daga cikin su sai rawar jiki take, hankalin ta a tashe, lokaci zuwa lokaci ta na daga kai ta kalli No 1, da alama ta na neman agaji ne a wajen shi, shi kuwa kauda kai ya yi kamar bai taba ganin ta ba. Su na qarasa shiga Lawwali ya yi ido hudu da budurwar da ke rawar jiki, ya ce, "Yaseerah kin bata wayon ki, shin kin manta million nawa Excellency ya ce mu karba wajen mutenen ga? Kudi na hwa masu yawa, me ya sa zaki zagaya ki aikata haka?" "Oga.... Dama...." Cikin sauri No 1 ya kalle ta, ya ce, "Oga butulci ne irin na mata, bai kamata a barta ba, ya kamata a hukunta ta saboda  ya zama izina ga na baya" Kafin Lawwali ya bada umarni, ko ya yi magana, No 1 ya harbi Yaseerah, qarar bindigar da qarar ta kusan a tare suka karade wajen, gaba daya kallo kan No 1 ya koma, shi kuma ya fara wani murmushin jin dadi ya ce, "Oga a min afuwa, irin haka ba za ta qara faruwa ba, zan sa ido sosai, ba a koma samun maci amana wajen ga na yi ma alqawari" "Wa ya ba ka izinin yin halbi?" "Oga a min afuwa, na zaci za ka yi hwarin ciki na kawar da maci amana, duk da ina son Yaseerah  ba zan taba bari ta ci amanar mu ba," Yanda ya yi maganar ya sa Lawwali zaton ko No 1 na jin haushin cin amanar da Yaseerah ta yi ne, shi ya sa ya harbe ta. Umarni ya bada akan a ɗauke ta, a binne ta a daren, sannan ya miqe kamar zai tafi ya saita Tsohon Gwamna ya saki kunamar bindigar a qirjin shi, sannan ya fice, No 2 na biye da shi a baya, "Oga ka sani fa dangin shi ba su aiko kudin nan ba, sun ce su na nan suna haɗawa ne, yanzu da aka kashe shi ya za a yi?" "Ko sun kawo, ko basu kawo ba dama ba komawa wajen su zai yi ba," Motar shi ya fada, sannan ya wurga ma No2 bindigar shi, ya ja motar shi ya bar wajen. Ko da ya isa gida wanka ya yi, ya nemi abinci ya ci, ya kwanta, nan da nan bacci mai dadi ya dauke shi. *********************** Sultana ta kasa rintsawa, tunanin fuskar Lawwali ta hana ta sukuni, duk wani motsi da za ta yi ganin shi take, har a yanayin ma da bai taba zuwa mata ba, fuskar shi ta ke gani daf da ta ta in ta rufe ido, da ta bude se ta ga kamar da gaske shi ne a tsaye . Miqewa ta yi ta shiga bayi, ta daura alwala, ta tada sallah, raka'a biyu ta yi, ta hau addu'a. "Ya Allah ina roqon ka, dan kyawawan sunayen ka tsarkaka, ya rabbi, ka tausaya min a cikin halin da zuciya ta ke ciki, ban san me ne ne hakan ba, Allah ka bayyanar min da ma'anar abinda nake ji,ya Allah ka sanya ya zama alkhairi ne, Allah ka kawar da sharrin abinda ke cikin rai na" Salatin Annabi ta yi, daga qarshe ta miqe, ta nade carpet din sallah ta kwanta, addu'ar bacci ta yi, ta shafe jikin ta, sannan ta kwanta da bangaren hannun ta na dama bakin ta dauke da tasbihi. Lumshe ido ta fara yi, cikin ikon Allah kuwa bacci mai dadi ya dauke ta. (Wannan shi ne amfanin addu'a, ka roki Allah mai duka, sannan ka yi imani, da yaqin cewa Allah ya ji, kuma ya amsa, lokaci kawai kk jira komai ya daidaita. Ba wai ka yi addu'a ba kuma ka ci gaba da damuwa, ya zama da kai da wanda bai yi addu'a ba baku da maraba) *********************** Washe gari da safe mutanen Tsohon gwamna suka aika da 300m cash, suka aika Zuby ta karba, No 2 da   No 3 na can nesa sun yi ready ko da an zo da 'yan sanda, Zuby kuwa sanye take da hijabi da niqabi, ta yanda ba mai iya gane ko ita wace ce, ta na karba motar su No 2 mai baqin gilashi ta tsaya a gaban ta, ta fada suka wuce a guje suka tada qura. Dan Tsohon Gwamna da qanin Tsohon gwamna na ganin an wuce ba a fiddo masu da shi ba suka bi motar da gudu su na ihun kiran su, motar tini ta bace kamar walqiya, yaron durqusawa ya yi ya fashe da matsanancin kuka, baffan shi ne ya dafa shi shima idanun shi na zubar da hawaye, kusan wata daya kenan rabon su da yayan na shi,suna cikin wanan mummunan halin wayar Qanin Gwamnan tai qara ya duba kiran. Hannu na rawa ya dauka, cike da jimami da tsoro, "Ka duba bayan dutsen nan za ku ga dan uwan ku" Ai be gama jin me za a ce ba ya yar da wayar ya kwasa da gudu bayan dutsen, gawar tsohon gwamna ce ta masa maraba, salati ya saka da qarfi y fadi a wajen, da gudu dan gidan tsohon gwamna ya isa dan tare shi amma inaa, kafin ya isa ya fadi qasa, gawar mahaifin shi da ya gani cikin jini ta kidimar da shi, ihu kawai ya fara, ya na kiran a taimaka musu, ga shi wajen daji ne ba mutane, in ya diba a guje dama, sai ya koma hagu da gudu, da kyar y samu natsuwa ta zo masa ya yi inda suka aje motar su, domin sun hana su shiga da mota, a guje ya ke keta dajin har ya isa wajen motar su, kunnawa ya yi ya koma wajen gawar da baffan shi, ya ɗebe su ya mayar motar sai gida. Ranar wannan ahali sun shiga cikin matsanancin tashin hankali, masu kuka nayi, masu suma na yi, masu addu'a na yi, masu ihu da kururuwa na yi, nan da nan kuwa labari ya baza garin Zamfara da kewaye ,mutane sun shiga tashin hankali da firgici, Indai manyan qasa ba su tsira ba su kuma gama gari fa? Direct gidan Lawwali suka nufa da qatuwar jakar kudin, ya shirya tsaf dan tafiya gidan gwamna Halliru, sai qamshi ya ke bugawa, zuciyar shi fess kamar ba abinda ya aikata mummuna, fatan shi ya cimma burin shi na sace zuciyar baiwar Allah Sultana. Bugun gate din gidan sukai ta yi, shi kuma ya na tsaki da ihun fadin "Wane na ya ka son balle min gambu?"(wane ne ke son karyan qofa) "Oga" Shi ne kawai abinda suka fadi, ya gane su waye, ya na bude qofa suka miqa masa jakar suka koma motar su suka wuce, shi kuma a motar shi ya saka jakar ya bude gate ya shiga mota, bayan ya fidda motar ne ya rufe gidan ya nufi gidan Gwamna Halliru. Ko da ya isa time din 7:12am ne, ya sanar da gwamna zuwan shi, ya na isa ya tarar da gate bude, motar shi ya shigar ya aje ta a parking lot, ya bude ya dauki jakar, ya zaga ta baya, dakin da suke zama su tattauna mugayen abubuwan su, shi da gwamna, da sauran miyagun mutanen da suke harkokin banza tare. Sultana ta yi mamakin ganin Lawwali da sassafe haka kuma ya zaga ta baya inda mahaifin su ne kaɗai ke zuwa da baqin shi,gashi dauke da qatuwar jaka, to ko gidan aka ce ya dawo da zama ne? Wataqila ya dawo gidan da zama ne. Murmushi ta yi mai kyau, dan jin dadin hakan, tare da fatan Allah ya sa hasashen ta ya zama gaskiya. Ta na mamakin yanda yanzu ta koyi leqe ta window, hakan ba halin ta bane, a baya ba ta tuna sanda ta taɓa bude labule ta kalli qasa ba, amma a yanzu kullum sai ta kalli qasa, musamman kafin ta fita, da kuma in sun dawo. Fitowa ta yi daga wanka, daure da towel, ta shirya, cikin kwalliyar da ta fi ta jiya daukan hankali, ta sauka qasa, a gurguje ta ci abinci, sannan ta fita, tsaye ta gan shi jikin mota ya na waya, ya na ganin ta ya kashe wayar ya bude mata mota, idanun shi akan ta, bakin shi dauke da murmushi, Itan ma haka, tsayawa ya yi kafin ya rufe qofar su na kallon juna "Shin ki na sane ki ke kwalliyar ga dan ki gusar da hankali na ga jiki na ko kuma ki na sane ki ke satar zuciya ta ba tare da jin tsoron zan rasa ta ba gaba daya?" Cike da jin kunya Sultana ta kauda kai ta na jizar lips din ta na qasa, bai tsaya jiran amsar ta ba dama, Ita kuwa a zaton ta ya na nan tsaye ya na jiran ta amsa masa, sai kawai ji ta yi mota ta fara tafiya,kallon shi ta yi ta madubi, su na hada ido kuwa ya kashe mata ido daya, tare da d'aga gira daya, kunya ce ta kama ta sosai sai da ta rufe fuskar ta da tafukan hannun ta. Sallama suka yi da mai gadi, mai gadi na gaishe da sultana ba ta ji ba ma, har suka hau kan babban titi ba ta dawo normal ba, tabbas ta gama yarda a yau ta kamu da matsanancin son Lawwali, ita da take kwalliya dan ta ja ra'ayin shi, shi ya ja ra'ayin ta da kallon shi da kalaman shi. Har suka isa ba su sake magana da juna ba, sai da ya je bude mata mota zata fita ne ya ce, "Ran sarauniyar kyawawan matan Africa gaba daya shi dade, ina neman izinin ki zanna, gida wajen qauna ta," "Dan Allah Auwal ka dena sani jin kunyar ka,...and zaka iya zuwa, in ka je ka ce ina gaishe ta, ina gaishe da....(shiru ta yi, dan ta na jin nauyin ce wa Lamishi kuma a gaban shi, daga baya ta ce,) ina gaishe da Umman Mubaraka" Wata iriyar siririyar dariya mai sauti ya saki, tare da duqar da kan shi, hakan ba karamin kyau ya yi wa sultana ba, zuciyar ta ta ji ta tafi wajen shi gaba daya, kafe shi ta yi da idanu, cikin yin qasa da murya yace, "Ko ran Ran ta ya dade za ta iya sammin Lambar wayar ta, saboda in ta na buqata ta se na dawo?" Miqa masa hannu ta yi, ta na nufin ya bata wayar shi, hannun shi ya miqa, sauran kadan hannayen su su hadu,da sauri ta janye hannun ta cike da shagwaba ta ce, "Wayar ka fa za ka bani" Shi kuma 'yar dariyar da ke tafiya da ita ya yi, ya ce, "Ohh na zaci gaisawa za mu yi" Hannu ya sa ya zari wayar a aljihun shi, ta bi qirjin shi da kallo, yanda rigar ta zauna a jikin shi, kamar a jiki aka dinka ya mata kyau, yawo ya yi da wayar a gaban idanun ta ya na murmushi, tare da lumshe idanun shi. "A gaskiya ran ki shi dade in ki na yi min irin wanga kallo, sai ke gano muni na da ni ke ta boyewa kar ki gani" Sultana ta gama kamuwa da matsananciyar kunya ,kasa amsar wayar ta yi, sai shi ya zare tata a hannun ta ya sanya lambobin shi ya danna kira, ta ta No ya yi saving, sannan ya miqa mata wayar ta, ya kulle motar ya raka ta har office, sannan ya tafi. Bai tsaya a ko ina ba sai bakin titi, tun kan ya isa ya yi waya ya sanar da su inda za su dauke shi, ya ɗan jira su kadan kafin suka isa, mota ya shiga suka ja Sai gidan Gwamna Halliru...... *Dan Allah ku dan min hakuri da wannan, ban sani ba ko za a samu ci gaba nan kusa na yi baqi na yi busy sosai, ko wanan ma da kyar na samu nayi* A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 22: A mota ya bar su, zai shiga No 1 ya yunqura zai bi shi, kallon shi Lawwali ya yi, cikin hade girar shi,ya ce, "Ina zaka je?" Dan yaqe ya yi, sannan ya koma ya zauna, qasan zuciyar shi baqqiqirin a ganin shi ai ko ba a shiga da kowa ba, an shiga da shi, tunda shi ne wanda ke bi ma Ogan nasu, kuma shi ke kula da can daji yanzu. Lawwali bai saki fuskar shi ba har ya shige gidan, bai jima ba sosai ya dawo dauke da jaka, ya ajiye suka tada mota, sai gidan shi, ya so ya leqa dajin ya ga ya abubuwa ke tafiya, dan yanzu ba ya so a maimaita sakin wani da suka kwamushe, asiri ya tonu,duk da ba wai tsoro yake ji dan an san da zaman su ba, ya sani yayi gagarar da zai iya ji da dik wata tarzomar mahukunta, a shirye yake a yi uwar watsi ko a mutu ko ai rai kawai. Zaune suke a parlour'n shi, su na kasafta kudin, kamata ya yi a ce in sun raba kudin daidai su shiddan kowa zai samu kusan miliyan 42,amma sai suka yi kasafin kamar kashin dankali, na sama ya danne na qasa, Gwamna shi ne ya fi kwasar kaso mai tsoka, sannan Lawwali, sai kuma suka ware kudin kula da maboyar su, abinci,ruwa, man da za a saka a mota, da abubuwan yau da kullum, kudin shigo da makamai dama a wuyan gwamna yake, ,No 1 na ta jira ya ji kason shi shima ya dara na qasa da shi, sai ya ga an bashi miliyon ashirin, yaqe ya yi ya karba, ya na ta godiya, kamar babu komai a qasan zuciyar shi . Sauran yaran Lawwali kuwa murna kamar za su shide, ba su taba kama kudi masu kauri haka ba, babban abin takaicin shi ne, su na samun kuɗi dan samu, amma cin su na musu wahala, saboda idanun mutane, kuma sun fi yin rayuwa a daji, duk da cewar wasun su na da iyalai, har da iyaye, amma su na tsoron fitar da dukiyar su ci, (meye amfanin dukiyar da ba za ka ci ba? An kashe mutane a banza, ba a samu rayuwar jin dadi ba, an sace mutane a banza ba a yi ninqaya da dukiyar ba cikin kwanciyar hankali, ga tsoro, ga fargaba, ga zunubin wanda ya kashe mumini akan su, mu yawaita tuna cewar Allah yace duk wanda ya kashe munini kamar ya kashe duka duniya ne, kuma wanda ya raya mumini daya kamar ya raya duka duniya ne,sannan wanda ya kashe mumini da gangan, sakamakon shi jahannama ne,zai dawwama a cikin ta,ba fita, Allah ka tsare mu ka kare mu, ya ilahi me ne jin dadi a kashe kiyashi ma balle mutum? In ya mutu kai me za ka zauna ka yi a duniyar?  Ba ku tunanin yanzu ku na gama kashe mutum kuma ku bingire ku mace? Me ka/ki ka tanada a ranar lahira da zai kare ki/ka daga shiga jahannama? Me za ku ce wa Allah a ranar qiyama? Shin wutar ita kuka fi so a inda za a dawwama ba fita, ko kuma talauci da quncin rayuwa a duniya, lahira a samu aljannah madawwamiya, ba fita, ba wahala, ba qunci, ba azaba, sai zallar ni'imar Allah, da jin dadi? Zabi ya na gare mu, tare da yawaita addu'a, Allah ya sa qaddarar mutuwar kowa ba ta hannun mu, domin wasu Allah ya rubuta su ne ajalin wasu, shi yasa suke kashe kashen nan, Allah ya nesan ta mu da ga aikata kisan kai, ameen) Su na tsaka da murna Lawwali ya ji wayar shi na qara, dubawa ya yi ya ga sunan Sultana da ya yi Saving da 'Ran ki shi dade' da sauri ya dauka, tare da yi masu alamar su yi shiru, ko motsi wajen bai sake yi ba, sallama ya yi, ya ce, "Ran ki shi dade na neman Lawwali ne?" Cikin dakewa ya yi maganar saboda idon yaran shi, daga can Sultana sai ta ji ba dadi, domin ba haka ta so ba, ba ta san me ta zata zai fara fadi ba, amma ta sa a ran ta he is going to say something sweet to her ,musamman tunda shi ya iya tsara kalamai, ita ma dakewa ta yi, ta fito masa a oganniyar shi, ta ce, "Ina ka shiga tun dazu na gama ina jiran ka?" Miqewa ya yi, tare da dan duwaqa ya na bata hakuri, har cikin ran shi bai so ta gama bai koma ba, cikin sauri ya mu su alama, nan da nan kuwa kowa ya kwashe kudin shi, da shirin su suka zo, kowa ya zo da inda zai saka na shi, su na gama kwashewa suka fita, ya rufe gidan shi, suka tafi. Nesa da NGO din suka aje shi ya dau adaidata sahu, dubu guda ya damqa masa ya sauka a hanzarce ya shiga ciki. Ko da ya isa a zaton shi zai gan ta a bakin mota, sai ya ga ba kowa, mota na nan yanda ya barta, sai zafi da ta dauka, ciki ya shiga ya ga duk mutanen wajen sun tafi, sai ita kadai, ta kwantar da kan ta a jikin kujera. Kallon ta ya ci gaba da yi har da sanya hannun shi a qirji, ya na murmushi, wai fa gajiya ta yi a hakan, office dik AC, kujera kamar an yi ta da soson katifa, amma ta nuna ta gaji saboda ba a saba da wahala ba, sai ya tuna farkon zuwan su wajen, har suka koma da fara'a a fuskar ta, 'to ko dai dadewa ta ce musabbabin bata ran ta?' "In ka gama kallon nawa za ka iya kai ni gida?" A dan firgice ya ce, "Na'am?" Miqewa ta yi ta zagaye shi, tana dan tura baki, tare da ɗaukan jakar ta da wayar ta, ta fara tafiya, wurga masa key din offices din ta yi, ta ce, "Ka rurrufe ko ina, this will serve as ur punishment, na tafiya ka dade ba tare da ka kira Ni ba," Shan gaban ta ya yi, ya tsaya, tare da kama kunnuwan ta duka biyun da hannayen shi, cikin murya irin ta jaruman maza da ware idanun shi fess akan ta ya ce, "Habaa Sultyn Daddy, ki yahe ma wanga yaron na ki, mai gadin ki, kuma drivern ki, indai hukunci ne ki ban kowanne iri na Zan dauka, amma ba zan dauki hushin ki ba, murmushin ki kamar hasken da ke haska min hanya ne, fushin ki duhu ne a gare ni, so ki ke in ta tahiya cikin duhu mu fada rami? Ko..." Muryar ta can qasan maqoshi ta ce, "Shiiiiii, ya isa haka, ni ba fushi nake ba,da na ga baka dawo bane sai na ji...." Shiru ta yi, tare da cizon leben ta na qasa, wanda hakan dabi'ar ta ne, da sauri ta bar wajen, Lawwali kuwa ji ya yi wadannan kalaman nata sun fi maqudan kudin da ya samu a yau mahimmanci, duk da ba ta qarasa kalaman taba, ya kula da cewar ba ta son ya yi nesa da ita ne, cikin sauri ya rurrufe ko ina, ya bi bayan ta, juyawa ta yi, ta qi yarda su hada ido, har ya je gaban ta ya bude mata mota bata kalle shi ba, kuma bata dena cizar leben ta ba, sannan murmushin ta bai gushe ba. Ko a mota ma ta kasa daga ido ta kalle shi ta madubi, shi kuwa idanun shi ya kasa barin fusakar ta da ta kawar gefe, mamakin irin kunyar ta yake yi, kamar ba wayayyiya ba, kamar bata yi karatu a qasar waje ba, kamar shekarun ta ba su haura ashirin da biyar ba. (Kunya halittace, ta wani ta fi ta wani, kunya ado ce, wanda ba shi da ita ya yi hasara, kunya ni'ima ce, wanda aka azurta da ita ya dace) Ko da suka isa gida kafin ya fita ya bude mata, ta fara qoqarin budewa, ji ta yi qofar a kulle, daga ido ta yi ta kalle shi, su na hada ido ya kashe mata ido daya, dariya ta saki mai sanyi, shi ma haka, "Yanzu dai an dena fushi da ni ko?" "Ehhh" "Tau na gode, sai da sahe," "Allah shi kai mu sahiyar lafiya," "Ameen" Fita ya yi, ya bude mata kamar yanda suka saba. Mubaraka ce ta tafi da gudu wajen su, kafin Lawwali ya yi magana ta rungume shi tare da fadin, "Yah Auwal dina na yi kewar ka sosai sosai sosai" Cikin dan hade fuska Sultana ta kalle shi, ina ya je dazu? Wayance wa ya yi, ya juyar da Mubaraka ya na zaro mata ido, sannan ya ce, "Baraka na hoo, dazu dazu mun ka rabu, amma har ke yi kewar Yah Auwal, ni ma na yi kewar ki Baraka naa" Ya dan ja kunci ta ya na mata alama da ido ta yi shiru, shiru ta yi cikin tunanin me yake faruwa. Sultana kuwa mamakin ta ne ya kau, sha'awar soyayyar da ke tsakanin yaya da qanwar ya kama ta. Jakar sultana Mubaraka ta amsa, suka shiga ciki, "Ina jiran ki a gate" Juyawa Mubaraka ta yi, ta ce, "Tau gani nan zuwa, yanzun ga," Su na isa ta ajiye jakar Sultana inda jakunkunan ta suke, sannan ta kalli dakin da ta gyara ya yi tass ta ce, "Aunty Sultana jiya baku dawo da wuri ba, shi ya sa yau na ce ni ma zan jira ku har ku dawo," "Allah sarki, aiki ne ya yi yawa shi yasa akwai damuwa ne?" "Babu komi, haka kawai Ni ka son ganin ki, bari na tai, yah Auwal na jira na" "Na gode Mubaraka, Ni ma ina son ganin ki ko da yaushe, ki na da hankali, da nutsuwa" Miqewa ta yi, ta bude wardrobe din ta, ta debar wa Mubaraka wasu kayan ta da ta ware za ta bayar, har da 'yan kunnaye da sarqoqi, guda uku uku, sai kayan kwalliya, da turare biyu, takalmi biyu sannan takalle ta tace, "Ni kuwa Mubaraka cikin jakkunan ga wacce ta hi kyawu?" Mubaraka kallon su ta yi, ita bata damu da kayan kyale kyale ba, burin ta a rayuwa kadan ne, ta ga ta saka sutura ta mata kyau kawai, bata damu da kyawun suturar ba ko tsadar ta, amma ta na da kalar da ta fi so, fari da ja, sune kalolin ta, dan haka wasu jakunkuna masu kalar fari da ja ta nuna tace, "Wagga da wagga sun yi kyawu kwarai," Hannu Sultana ta sa ta dakko su, ta na fara'a, in zata yi kyauta wani irin dadi take ji a zuciyar ta, wanda baya boyuwa, har wanda zata wa kyautar sai ya ji abun da aka bashin kamar dama nashi ne dawo masa da abin shi akai. "Tauuu Mubaraka 'yammata kema ga kayan 'yammata ki zanka sawa ki kyawu, maza ki tai Auwal na jiran ki" Baki Mubaraka ta bude cikin mamaki, da tsoron yawan kayan da aka bata, da gani babu tambaya kaya ne masu tsada, ita kam da ta san Sultana za ta mata wannan kyauta mai yawa da bata jira su ba, kar sultana ta ga fa kamar dan abin duniya take son ta, ita kam sam ba haka bane, domin Allah take son ta, cikin hanzari Mubaraka ta ce, "Haba Aunty, wanga kyauta ta yi yawa, ban tsaya ku dawo dan ki yi min kyauta haka ba, na tsaya ne domin ina son ki domin Allah" Mubaraka ta qara shiga zuciyar Sultana kwarai kwarai, halayen su kusan daya ne, cikin fara'a sosai ta nemi babbar jaka a dakin,  ta zuba mata komai, ta saka mayafi ta riqo hannun Mubaraka, suka fito zuwa parlour ,Hajiya Ikee na zaune ita da Sultan su na hira, ta ga su kamar wasu 'yan uwan juna, "Ke Sultana meye haka ni ke gani? Me aikin ki ke riqewa haka? Ko dake ba zan mamaki ba a halayen ki na shegen son cudanya da tallaka, kee! Kama hanya ki tai, ba ke qare aikin ki ba?" Cikin rawar jiki Mubaraka ta nufi hanyar fita, Sultan ne ya kira ta, tsayawa ta yi cak tare da juyawa, "Yarinya taho nan" Hajiya sake baki ta yi, ta na kallon yanda yaran nata ke nuna wa mai aiki mahimmanci, kamar ba yaran Gwamna ba, Cikin magana mai taushi Sultan ya ce, "Ya sunan ki?" "Mubaraka suna na" "Ok, ke ce diyar Lamishi ko?" Daga kai ta yi, bata amsa ba, "Me ya hana mata zuwa kwana biyu?" "Ta yi turmushe na ,(tayi targade ne) amma ta ji dama, gobe ta na tahowa" "Ok, in kin tai ki gaishe ta" "Ta na amsawa" Hajiya Ikee kallon su kawai take da mamaki, duk masu aikin gidan ba wanda basu sani ba, ita da take tare da su shekara da shekaru ma ba kowa ta sani ba, amma su har sun kula da wata bata zuwa. Ledar kayan Sultana ta miqa mata, sannan suka yi sai da safe, a gurguje ta fita ta bar gidan. Ko da Mubaraka ta fita Lawwali ya ga fuskar ta ba walwala, sai ya hade girar shi waje daya, ya Qura mata ido, kula da yanayin shi ne ya sa ta sakin fuskar ta. Ta sani kadan da aikin shi ya koma ya musu ba dadi. "Mi ya hwaru?" "Babu komi, kalli abinda Aunty Sultana ta bani, duk sai nij-ji ba dadi, kar ta ga kamar ina son ta ne domin azziqin su" "Shi daya ke  sa ki bata fuska? Ko wani abu aka maki?" "Ba wanda ya min komi, Yah Auwal mu tai zuwa gida yunwa nika ji" Dan zare ido ya yi, sannan ya kama hannun ta, suka tafi gidan shi, Wanka ta yi,ta samu wata riga mai kyau, da mayafin ta, a cikin kayan da Sultana ta bata, ta saka, ta sanya takalmi kalar kayan, Lawwali tsayawa ya yi ya na kallon ta, kamar ba Barakan shi ba, Lallai Indai haka kayan 'yan gayu ke mata kyau, zai maida ita sarauniya a cikin mata, ba shi da wanda zai kashewa dukiyar da ya tara sama da ita. Shopping ya fara kai ta duk da kukan yunwar da take ta yi, ya sai mata jaka kalar da za ta shiga da kayan da ta saka, ya qirga dubu goma ya saka mata a ciki, dan ya san wannan din ma sai ta tambayi ina ya same su, ko ba yanzu ba, daure fuska ya yi saboda ba ya so ta hau shi da wa'azin ta da bata gajiya. Wani qayataccen wajen cin abinci ya kai ta, aka Kawo Mata abinci kalar wanda bata taɓa mafarkin gani ba ballantana ci. Nan da nan kuwa ta yi Bismillah ta fara ci tana ta murna, zuciyar shi cike da so da qaunar ta ya ke kallon yanda farin ciki ke bayyane akan fuskar ta, sai ya samu kan shi cikin nishadi da walwala. Bai maida ta gida ba sai bayan magariba, ta sha yawo, duk ta gaji, ga kaya niqi niqi da suka shiga da su, har su Jameelu sai da su ka musu siyayyar suturun sawa da abubuwan buqatu na yau da kullum, kamar yanda ya bata dubu goma suma haka ya basu, su Lamishi kuwa dubu ashirin ashirin ya basu, ya so basu sama da haka, amma shegen surutun su ya ja musu. Kafin ya tafi se da ya buga warning kar wanda ya karbewa Mubaraka kayan ta, tunda ya na cikin kudi sosai yau, ko musu ba wanda ya masa. *********************** Tun safe har dare Mai unguwar Tudun Faila, da manyan unguwar ke ta kai kawo su na neman dan mai unguwar, mai suna Isyaka, babu inda ba su duba ba sama ko qasa a unguwar nan babu shi babu bayanin shi, mahaifiyar Isyaka ta yi kuka har ta gaji, har da aljanu se da ta tayar, Isyaka yaro ne dan shekara tara, yaro ne mai shiga rai, ba shi da qiwa, ba shi da rikici, in mutum ya zauna da Isiyaka sai ya ji kamar kar su rabu, duk cikin yaran Mai unguwa ya fi qaunar shi, duk da cewa ya na da manyan yara. Mai unguwa ne ya zauna cikin gajiya da yawon da ya sha, ya kalli matar shi da ke ta turje turje irin na masu aljanu ta na kiran sunan dan ta, duk dauriyar da mai unguwa ke yi, sai da ya karaya, hannun shi ya sanya a idanun shi ya fashe da kuka, "Dan Mutum? Dan Mutum za a nema a rasa awat-taguwa? Kaiii Allah shi yi muna maganin wanga hali da muke ciki" *AMEEEN* A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAEH PAGE 23: Washe gari ma haka aka tashi da neman Isyaka, ba a gan shi ba, kusan duk wanda ya san yaron da wanda ma bai san shi ba, ya taimaka wajen neman shi, shiru kamar an shuka dusa. A da ne in ana neman mutum ake zuwa gidajen rediyo, talabijin da jaridu neman shi, amma yanzu saboda yawan batan yara da manya da ake, a filin cigiya da sanarwa kadai in aka saka awa biyar ya yi kadan a fadi yara da manyan dake bata, a wannan qasa tamu. Roqon Allah aka durfafa domin shi kadai ne zai taimake su, su ga yaron su cikin koshin lafiya. Mijin Asshibi ne ya ja Isah daga cikin mutane, suka koma nesa sosai suka tsaya, "Isah ban taba zaton za ka min haka ba, ni ne na koya  ma wagga harka, amma ka zagaye ta bayan ido na ka dauki kaya, baka sanar da ni ba," "Wanne kaya? Ni ban dau kowanne kaya ba, to in ma na dauka ka san ban da wajen ajewa, dole kai din dai zan kawo wa" Mamaki ne fall zuqatan su, tabbas sun sani ba su dauki Isyaka ba, to waye ya dauke shi? ********************** Yau kwana biyar kenan Gwamna Halliru bai kwana a gida ba, sakamakon qaratowar zabe ba zama, daga wannan qauye zuwa wannan unguwa, haka za a dinga nuna shi gidan talabijin yana ayyukan alkhairi, kamar su gina masallatai, noma, samar da ruwan sha da sauran ababen more rayuwa, tallafa wa gajiyayyu da marasa lafiya, sune suka zama ayyukan da ya sa a gaba, ana yi ana dauka a hoto da video ana yad'awa jama'a. A wannan lokaci ne na qaratowar zabe,lamura ka yi ma wasu daga cikin mutanen qasa wahala da tsanani, tare da qunci , wasu kuma lokacin ne suke cikin walwala, da nutsuwa da yalwa, harkokin samun su ta bude, rayuwar su ta yalwatu da dukkan abinda suke burin samu. Gidan gwamnati Hajiya Ikee ta koma da zama, mutane na zuwa, wannan ya shiga wancan ya fita, watarana har fita take da muqarraban ta unguwanni dan kai masu taimako, mutanen mu kuwa dake a hannu suke, ana buqatar abincin da wasu kayan masarufin duk sun manta da wahalhalun da suka sha abaya, da rashin kula su da gwamnatin bata yi ba a baya, ta na da manyan mata a unguwanni daban daban, da ke rabon kayyaki da abinci, tare da kudi wa mata a gidaje, domin a sai quri'un su, ko me ya sa da ba a tallafi matan ba sai zabe ya zo a bi su da dubu ko dari biyar da atampa oho. Motoci ne masu numfashi, da qoshi ke yawo a saman hanyar  qauyen da duk titin ya farfashe, mutanen qaramin kauyen kuwa, sun yi babban shirin tarbar Gwamna da muqarraban shi. Motocin na tsayawa, securities suka zagaye motar Gwamna, 'yan jarida na tsaye na jiran fitowar shi su fara daukan rahoto, manyan motocin abinci da suka zo da su ne suka qaraso, qatti na ta sauke buhunan abincin, mutanen qauyen natsaye su na kallon su, sai da suka bari Gwamna Halliru ya fito an fara daukan shi,tare da fadin rahotanni na son rai da zuciya, sukai  ta fitowa da gorori, da bulalai, tare da duwatsu, dukan motocin suka fara, tare da jifan su da duwatsu su na fadin "Ba ma yi ! Ba ma yi !" A gurguje Gwamna ya fara qoqarin komawa motar shi, cikin rashin sa'a wani matashi ya maka masa gora a goshi, babu bata lokaci kuwa daya daga cikin masu tsaron gwamna ya zari bindiga ya harbe matashin, qarar bindigar ne ya sanya mutane rudewa, wajen ya kacame da hatsaniya, wasu na qoqarin guduwa, wasu na ganin ko za su rasa ran su sai sun cimma abinda suka yi niyya. A guje motocin gwamnatin ke guduwa, wasu daga matasan kuwa sun hana a dauki manyan motocin abincin, sun kakkare ko ina. Haka wasu daga muqarraban gwamna suka gudu da qafafun su. Sultana ba ta jima da komawa gida ba, ta idar da Sallah ta kwanta, ta na hutawa ta ji qarar motoci, dan tsaki ta ja ta daki pillow ta toshe kunnen ta, tare da yin goho a gadon, ta na dukan gadon, cikin dan kukan shagwaba ta dauke pillown daga kan ta ta miqe, idanun ta lumshe take tafiya, kafin ta isa motocin sun shiga gidan, labule ta daga ta leqa qasa, ta na hamma, tare da murza idanun ta, ba shiri ta wattsake  daga baccin da ya taru a idon ta. Mahaifin ta ta gani cikin jini, farar babbar rigar shi ta gaba tayi faca faca da jini, da sauri ta bar jikin window ta zari rigar ta ta saka, ta manta gaba daya kanta ba dankwali ta fita parlour ,securities na waje, gwamna ya shigo, ciki, cike da bacin rai, wani daga securities din ne ya shiga ya sanar da zuwan doctor, Dr zama ya yi a kujera ya na fidda kayan aiki, Gwamna Halliru na tsaye ya na bada mummunan Umarnin da ya sanya Sultana kusan suma a tsaye, da wa mahaifin ta yake waya haka? Wanne azzalumin ke taya mahaifin ta aikata mummunan aiki irin wannan? Zama ya yi ya na fitar da wani irin hucin bacin rai da baqin ciki, Dr ya fara gyara masa ciwon shi, ko zafi bai nuna alamar ya na ji ba, tsabar yanda ran shi ya kai qololuwa wajen ɓaci, tsoro ne ya kama Sultana, har ta kasa qarasawa wajen shi . Hawaye ne kawai ke zuba a idanun ta, bakin ta na rawa, zuciyar ta na bugawa da qarfi, hannu ta sa ta shafi kan ta, ta juya sama da gudu, wayar ta ta dauka, ta na kallon ta, shin Hajiya za ta kira? Ko Sultan? Ko kuma...... Lawwali ne ya fado mata a rai, lokuta da dama in mutum na cikin damuwa, ba wanda ke fado masa a rai sai masoyin shi, wannan dalilin ne ya sanya Sultana tunawa da mahaifiyar ta, da d'an uwan ta, qarshe ta dire akan lawwali, (hakan na nufin Sultana ta kamu da son Lawwali?) cikin hanzari ta kira shi, ta jima ta na ringing bai daga ba har ta katse, sake kira ta yi, ya na fara ringing ya dauka, a gaggauce ya ke magana, daga baya ya tsaya cak, saboda jin kukan Sultana da ya yi. "Ran ki shi dade lahiya? Me ya hwaru ki ke kuka?" Ta kasa magana sai kuka take, da kyar ya samu ta nutsu. "Daddy ne...Daddy ne na ji ya na waya....wai za a je wani qauye a tashi garin,....ya na so a kashe kowa...har mata da qananan yara...ba ya so a bar kowa ya rayu, saboda sun zubar masa da jini...ya bada umarnin a sa wa garin wuta..Auwal ya zan yi? I need your help pls" Kuka ne sosai ya kwace mata, fita ta ɗan yi waje ta tsaya jikin bene, ta na hango Gwamna Halliru ya na bada umarni ga 'yan jarida kar su kuskura su saka abinda ya faru a zuwan su qauyen a kowacce kafa ta yada labarai, har kuma abinda zai faru washegari. Sultana sanar da Lawwali tayi abinda taji ya na faruwa, Lawwali kuwa ya jima da dauke wuta, ya na cikin tsaka mai wuya, shin wa zai bi? Gwamna ko Sultana? Ta na neman taimako a wajen shi,ba tare da sanin shi ne wanda aka bawa Umarni ya je da yaran shi su tashi qauyen ba. Amma zai jira ya ji wanne irin taimako take nema a wajen shi. "Ran ki shi dade sanar da ni irin taimakon da ki ke nema a waje na" Cikin kuka sultana ta ce, "Ban sani ba...Ni ma ban sani ba...just stay with me on the phone, har sai Sultan ya dawo, ina jin tsoro, ba na son kasancewa ni kadai, ina jin tsoro" Takure take a jikin matattakalar benen, a gaban idon ta mahaifin nata ke ta abubuwan da ba ta taɓa zaton zai aikata ba, Lawwali na sauraron kukan ta, har cikin qoqon zuciyar shi, yaran shi na tsaitsaye su na jiran umarnin shi. Jin zuciyar shi yake kamar wuta, kiran Gwamna ne ke shiga wayar shi, cikin sanyin murya ya ce, "Ran ki shi dade, ina da wani kira mai mahimmanci na shigowa, ki yi min hankuri na daga, zan sake kiran ki" Shiru ta yi, bata amsa ba, banda kuka ba binda take yi, kashewa ya yi ya dauki wayar Gwamna, cikin tsawa da fada yake magana. "Shin kun tahi ko kuwa?" "Mun shirya yanzu za mu tai" "Ku kashe kowa, kar ku bar kowa da rai," "Tau ranka shi dade" Ya na gama magana da gwamna ya sake kiran Sultana, bata dauka ba, ta na zaune a wajen ta na kuka, komai ya tsaya mata cak, tsoro da mamaki duk sun kau daga zuciyar ta, gata nan ne dai kawai. Jin bata dauka bane, ya sa Lawwali bawa yaran shi umarnin tafiya, nan da nan kuwa suka fita, suka shisshiga motocin su, dauke da muggan makamai, da bindigogi, da bama bamai,basu shiga kauyen ba sai da suka  je dajin su suka tsara komai, sanan suka qara mayaqa, cikin dare suka shiga garin, mutanen garin sun sakankance, su na ta murna, da jin dadin samun kayan abincin da suka yi, tare da korar azzalumin gwamnan nasu. Kwatsam suka fara jin harbi ko ta ina, da tashin qananan bama bamai. Gari fa ya rude, da tashin hankali da iface iface, duk wanda ya san Lawwali a zahiri ba zai gane shi ba a yanzu, gaba daya wannan mutumin ba shi da digon imani, ba tausayi a zuciyar shi. Kashe mutane kawai yake kamar ya na kisan kiyashi. Basu suka bar garin nan ba sai da suka maida shi kamar toka, daidaikun mutane ne suka samu guduwa, suka bazama daji, da wasu qauyukan da ke kusa da su. Qarfe sha biyu na dare, suka bar qauyen, direct gida Lawwali ya nufa a motar shi,ya na zuwa ya yi wanka ya ci abinci, ya kwanta, juyi ya dinga yi, wanda ya rasa dalilin yin shi,a hankali tunanin Sultana ya fara mamaye zuciyar shi mai kama da dutse, soyayyar ta da soyayyar mubaraka ne kadai ke raya zuciyar shi, banda su ba shi da wani abu da ke narkar da zuciyar shi. Wayar shi ya dauka ya dinga kallon hotunan su, ya na sakewa, ya rasa yanayin da yake ciki, ko kuma abinda yake ji a zuciyar shi . Bai san sanda ya danna kiran Sultana ba, ya kara a kunnen shi, cikin shaqaqqiyar Muryar  da ta ci kuka ta gode Allah ta dauka. "Ran ki shi dade, baki bacci ba?" Kallon qur'anin da ta gama karantawa ta yi, ta lumshe idon ta hawaye suka zuba, ta ce, "Eh ban yi bacci ba, kai me ya hana ka bacci?" Shiru ya yi, tare da gyara kwanciyar shi, ya lumshe idanun shi ,sanan ya ce, "Na kasa bacci, ban san me ke damu na ba, Sultana ina da wani babban al'amari a tattare da ni, wanda ni ka jin matuqar tsoro akai" "Me ne ne wannan al'amarin? Ko zan iya sanin shi?" Da sauri ya kawar da maganar ta hanyar tashi zaune ya ce, "Ran ki shi dade, ya kamata ki kwanta ki bacci, akwai gajiya a tattare da ke sosai " "Humm Auwal kenan, kai a ganin ka zan iya rintsawa? Bayan zuciya ta da ƙwaƙwalwa ta su na hango min abinda ban gani ba? Zuciya ta na hango min kukan yara ƙanana, da mata,da mazaje, zuciya ta na hasko min yanda jini ke malala na dan Adam ba dabba ba,ba tare da haqqin su ba, anya mahaifi na mutum ne kuwa? Anya wadan da suke aikata kashe kashe da zubar da jinin al'umma mutane ne kuwa?anya akwai zuciya a qirazan su kuwa?anya suna tunawa da cewa kamar yanda suke daukan rayukan bayin Allah suma watarana ran su za a dauka? Anya su na sane da cewa akwai wuta akwai aljannah? Anya su na tunawa da cewa su na da mahalicci wato Allah, mai yawan rahama, da kuma yawan azaba? Anyaa????" *Makaranta Sultana na neman amsa* A GARIN MU WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 24: Wata iriyar zufa ce ke karyo mishi, wadda ta sanya shi tunanin anya ya kunna AC ma kuwa, kallon saitin AC din ya yi, ya ga a kunne take, tashi ya yi ya kunna fan, sannan ya koma ya zauna, ya na sauraron yanda Sultana ke karanta masa abubuwan da ko Mubaraka mai yi masa nasiha da wa'azi kullum, bata taɓa fada masa wadannan kalaman masu matuqar taba zuciya ba. Cikin tsagaita wa da kuka sultana ta ce, "Allah shi ne mafi sani game da mutanen nan da Daddy ke aiki da su,su ke lahanta mutane, suke kassara su, suke illata su,in masu shiryuwa ne, Allah ya shirye su, in ba masu shiryuwa bane Allah ya musu abinda suke wa bayin shi, " Shiru Lawwali ya yi, dan bai isa amsa wa da ameen ba, tunda ya san mene ne suke wa yaran wasu, jijiyoyin kan shi ne suka tashi rudu rudu, qit ya kashe wayar,gaba daya ya kashe ta. Yawo ya fara yi a dakin, me zai sa Sultana ta musu wannan addu'ar , in wani abu ya samu ahalin shi fa? (Na wani bnza na ka dukiya kenan). Ranar Lawwali bai samu bacci ba sai gaf da suba, bacci kuwa ya sha me kyau, bai tashi ba sai qarfe goma na safiyar ranar. Sultana kuwa dama ta yi waya NGO akan ba zata je ba, bata jin dad'i, su kula da wajen, da duk wanda ya je neman taimako, abinda ya fi qarfin su su sanar da ita. Lawwali ma sai da ya tashi ya ga message din ta, ji yayi hankalin shi ya tashi, me ke damun ta? Dole ne ya je ya duba ta. Wanka ya dauka, ya sanya wasu riga da wando,na shadda sun yi mishi kyau sosai, ba hula, wayar shi da yan kudi, sai makullin mota ya dauka, ya fita, kafin ya je wajen ta, sai da ya shiga gari, ya siyo mata kayan kwalama na Bature, duk ya ma rikice ya rasa me ya kamata ya siya, haka dai ya siyi banza ya siyi wofi ya ja mota sai gidan Gwamna. Ko da ya isa ya tarar da securities da yawa, sanin ko shi waye a wajen gwamna ne ya bashi damar shiga ba tare da wani bincike ba, gwamna Halliru da Hajiya Ikee ba su gida, Sultan ne da Sultana sai masu aiki, ranar Mai buruji da Lamishi duk sun samu zuwa, har a sannan qafar Lamishi bata qarasa warkewa ba, dan haka Sultan ya hana ta yin komai, sai godiya take, ya ce ta ci gaba da turo Mubaraka, ba se ta zo ba, tunda ba lafiya. Sultana na zaune kusa da Sultan, ya yi tambayar duniya ta qi sanar da shi abinda ke ran ta, saboda ba ta son ya tsani Daddyn su kamar yanda ta tsani ganin shi,ba ta so ta b'ata kowa a rayuwar ta, ta fi so ta fadi alkhairin mutum, in ba ya zama dole se ta fad'i sharrin mutum ba, wannan ba yanda zata yi,balle mahaifin su, bata fatan Sultan ya sani, zuciyar shi zata karye sosai, saboda yanda yake son mahaifin nasu sosai. Hawaye ta share sannan ta yi murmushin yaqe ta ce, "Yah Sultan ba abinda ke damu na, ciwon kai ne kawai, in ina da matsala ka sani kai ne mutum na farko a duniya da ke fara ji" "Haka ne, amma Ni ma kin san na fi kowa sanin ki, ba ciwon kai bane kadai damuwar ki, akwai wani abu da ya ke faruwa, wanda ki ke boye min" Bude baki ta yi dan yin magana wayar ta ta dau qara, ko da ta ga sunan Auwal, sai ta samu kan ta da jin dad'in hakan,domin a daran jiyan ta yi ta sake gwada kiran shi bai shiga ba, har da safen nan ma ta kira bai shiga ba. "Assalamu alaikum," "Wa'alaikumussalam, Ran ki shi dade ya ki ke? Ya jiki? Ina hwata dai kin samu lahiya ko? Na taho na duba jikin ki, tunda kin ce baki da lahiya" Miqewa ta yi da sauri ,ta isa gaban window'n da ake hango farfajiyar gidan, ganin shi tayi tsaye da ledar shopping a hannun shi, murmushi ne mai kyau ya kwace mata, ta jingina da ginin wajen, sannan ta ce, "Lallai ka iya zuwa dubiya, haka ake zuwa dubiya an sha gayu? What if mara lafiyar ta rikice fa?" Waige waige ya fara ya ga ta ina zai hange ta, bai gani ba,  cikin sa'a ta sake leqa shi suka hada ido, dariyar shi da ke rikita mata kwanya ya saki, sannan ya shafa kan shi, tare da lumshe ido ya sauke su fess akan ta, Sultan ne ya isa gaban ta, ya harde hannayen shi a qirjin shi, ya na kallon ta da mamaki, dazu fa kuka take. Su na hada ido, ta bar wajen za ta hau sama, ya riqe hannun ta, a hankali ta ce, " ka shiga parlour na baqi gani nan zuwa" Kashewa Lawwali ya yi, ya shiga gidan ya shige har inda aka ce masa, ya zauna zaman jiran ta. Ita kuwa qoqarin gudu take Sultan ya riqe ta, "Ina zaki je baki min bayanin sauyawar ki ba a lokaci qanqani? Na fi qarfin awa biyu ina tare da ke, kina ta hawaye, kin kasa fadan komai, yanzu daga amsa waya sai ki fara dariya?" Shiru Sultana ta yi, dan ko me zai faru ba zata sanar da shi mummunan sirrin mahaifin su ba, gwanda ta tonawa kan ta asiri, akan ta fada masa gaskiya. "Yah Sultan, i am in love, ....i am in love with my driver, amma ban sanar da shi ba, shi ma kuma da alama ya na so na, bai sanar da ni bane kawai, Yah Sultan ina cikin damuwa ne saboda na san ba wanda zai goyan baya a gidan nan,labarin soyayya ta ina hango qarewar shi tun kafin ya fara" Bilhaqqi yanzu kuma kukan hasashen da ta yi take yi, "Sultana tabbas zabin ki ba mai karɓuwa bane a wajen su Hajiya da Daddy, amma a waje na karbabbe ne, in dai ki na son shi, ya na son ki, zan tsaya a gefen ki, har sai kun cimma burin ku" Qanqame hannun shi ta yi cikin nata, tare da fadin, "Na gode," Shafa kan ta ya yi, sanan ya ce, "Wannan shi ne abinda zan miki, duba da yanda iyayen mu suka maida ni mara mamora a cikin al'umma, ba na aikin komai, ana kulle na kamar mace, ba na baki wata gudunmawa a matsayi na na yayan ki" "Yah Sultan kar ka ce haka, soyayyar ka a matsayin dan uwana ta wadatar da ni komai," Cikin ran ta kuwa cewa ta yi, 'Dole iyayen mu su yi kullen mu, domin sun san me suke aikatawa, su na tsoron kar wani abu ya same mu,' Sai da ta ɗan gyara fuskar ta ta sanya sutura mai kyau da ta rufe jikin ta sosai, sannan ta isa wajen Lawwali, sassanyan qamshin ta ne ya fara yi masa maraba, kafin kyakkyawar fuskar ta  ta masa sallama. Sake baki ya yi ya na kallon ta, anya da gaske bata da lafiya? Shi be ga alama ba, "Kallon nan na ka na neman ya yi min yawa wallah" "Anya kuwa? Ke taba jin inda wata ya ce wa mutane kallon da suke mishi ya yi yawa?" "To ai Ni ba wata bace" "Kin fi kama da wata mai haske shi ya sa na yi misali da wata, sanyin ki kuwa ya fi kama da ruwan qorama, shi ne ba shi cutar da kowa sai amfanarwa" Kunya ce ta kama ta, tabbas ta gama yarda da cewar, abinda ke zuciyar ta shi ne a zuciyar shi, "To dubiya kacce ka taho, amma ba ka yi min ya jiki ba" "Ban ga alamar ciwo a tattare da ke ba, sai ma alamun cikakkiyar lahiya, amma, ya jikin ki? Ina hwatan da sauqi ko?" "Na ji dama, ciwon da ke jiki na ba a zahiri yake ba, a badini ne, domin kuwa zuciya ta na quna matuqa akan abinda zai iya koma ya  faru da mutanen can, da kuma abinda ka hwaruwa a garin nan, da ma Nigeria baki daya" "Hummmm" Shi ne kawai abinda Lawwali ya iya cewa, nan da nan ya tuna addu'ar da ta musu, cikin sauri kar a zurfafa magana ta sake yanko wata addu'ar ta cimmusu baki daya ya ce, "Ran ki shi dade, ina fatan ban yi karambani ba, na je zan siyo ma mara lahiya kayan dibiya, na rasa mi zan kawowa, na kwaso wadannan" "Na gode sosai, amma da baka wahal da kan ka ba" "Babu komi, indai ke ji dad'in kyauta ta, farin ciki na zai qaru" "Lallai ka yi farin ciki domin kuwa na ji dadin kyautar ka" Yar dariya suka yi a tare, Lawwali ya shagala da kallon ta suka ji an rangada salati, da sauri sultana ta miqe ta na zare ido, cikin in ina ta hau yi wa Hajiya Ikee Barka da zuwa, wani mugun kallo take bin Lawwali da shi, daga sama har qasa, babban abinda zai ba mai karatu mamaki shi ne, Lawwali dai ba a talauce ya je ba, kayan jikin shi kawai sun tasamma dubu dari,ga tsarabar daya kawo ma Sultana ya kashe 50k, wayar hannun shi abar kallo ce,  ga motar shi can a waje, ko wani dan attajirin sai haka, amma Hajiya Ikee ke masa maqasqancin kallo, "Ran ki shi dade Barka da War haka," Cikin tsawa ta ce "Dakata min diyan tallaka! Me ya kawo ka har parlourn manyan baqi? Ke Sultana wacce wanga diyan tallakan ya shigo min har nan?" Cikin kame kame da tura baki Sultana ta ce, "Hajiya ke san hwa mai tsaron lahiya ta shike, Daddy ne yacce duk inda ni aje qawahu na shi sa na shi, tau yau na ce masa ban zuwa ko ina ban da lahiya, shi ne yazo diba ni, in baki yarda ba ki tambayi daddy shi ne yacce duk inda niyyi shi ma shi yi" "Akan wanne dalili za a hada ki da wanga gola golan qato? Tau ban yarda ba, ke da gani nai ke san shi na shan wani abu, kuma...." Cikin jin kunyar kalaman Hajiya Ikee Sultana ta katse ta, dan cin fuska ba shi da dad'i ,tsabar kunyar Lawwali Sultana ta kasa kallon shi. Lawwali kuwa kawai ayyana irin azabar da zai ganawa Hajiya Ikee yake a duk ranar da tsautsayi ya had'a su, a fuskar shi kuwa murmushi ne bayyane, wanda ba me gane ma'anar shi in ba yaran shi ba, da ace a daji ne yake wannan murmushin to fa tabbas sai ya kai harbi, kad'a kai ya yi, ya ajiye ma Sultana tsarabar ta a gaban ta da kyau da kyau,ya kalle ta ya ga yanda take jin kunyar hada ido da shi, qoqari ya yi suka kalli juna, kashe mata ido daya ya yi, ta kuwa sanya murmushi, tare da rufe fuska, Hajiya Ikee salati ta saki, ta na tafa hannaye, Lawwali kuwa wucewa ya yi tare da fadin, "Na bar ku Lahiya, Ran ki shi dade " Ya na fita Hajiya Ikee ta ja Sultana, ta na masifa, tare da fadin, dole a sauya mata driver, bari Daddyn ta ya dawo, kuka kawai Sultana take, ta na bada hakuri, amma haka Hajiya Ikee ta murje idon ta, ta ce sai an sauya mata Lawwali. ************************ Da asuba Mai unguwa ya fita Masallaci, an yi sallah, aka hadu da mutanen unguwa aka sauke qur'ani, aka roqi Allah, akan Allah ya kawo qarshen wannan tashin hankulan da ake ta yi, sannan aka roqi Allah akan ya bayyana Isyaka, Mai Unguwa fadi yake, ya na kumawa, "Ya Allah ko gawar shi ne Allah ka gwadi mana, mu san ya mutu ne, ya Allah ka bayyana muna da shi lahiya" Bayan kammala addu'a kowa na tafiya gida ne, wasu da basu samu zuwa har gida jajanta masa ba, suka jajanta masa a nan. Sai da gari ya dan fara wayewa ya yi sallama da mutane ya dau hanyar gida, a hanya ya gamu da wani daga cikin yaran shi ya na ta gudu, ya na haki, tare da murna, ya na hango baban nasu yaci burki a gaban shi, ya ce, "Baba ! Baba !! an ga Isyaka, ga shi can gida, kwance jikin Baabaa" "Alhamdu lilLAAH, Hamdan katheeran, Allah na gode maka," 'Dan dandamalin wani gida ya hau a gefen hanyar, ya yi sujjadar godiya ga Allah, sannan suka kama hanya, suka nufi gida. Ko da suka je, ga Isyaka nan, ya yi fururu, kayan shi duqun duqun, jikin shi alamar ya ci duka ya gaji. Ya na ganin Mahaifin nasu kawai sai ya fashe da kuka, a da kuwa ko kukan ma ya kasa. Mai Unguwa ma kukan ya fara yi, ya na sake godewa Allah tare da fadin, "Ba abinda ya fi qarfin Allah, duk abinda Allah ya yi daidai ne, Allah mun gode maka, Allah ka qarawa Annabi daraja da wasila da fadhila, Allah mun gode maka, d'an baba, ya aka yi?" Ya na cikin kukan ya saki murmushi, hawaye na zuba. Kishiyar Baabaar Isyaka ce ta zo, ta ce, "Tau ga ruwan wanka can na sauke taso ki je ki  wanke shi ya  ji dad'in jiki shi" Godiya Baabaar Isyaka ta mata, ta kinkime shi ko nauyin shi bata ji,su ka nufi bayi, riga ta fara cire masa, ta fara qoqarin cire masa wando, ihu ya sanya, ya na fizge fizge, kamar mai jinnu, tare da fadin "Ba na sooo, kar ka taba ni, ba na sooo wayyooo Allah na da zahi, zahi nika ji wallah, wayyoooo a taimaka min...." Kuka sosai Baabaar shi ke yi, ta fita da gudu, zata kira taimako, ta tadda Mai unguwa da kishiyar ta da wasu daga yaran gidan a bakin qofar bayin, da kyar a ka samu ta nutsu, ta yi bayani, dakko shi akai waje, aka cire wandon, juya bayan shi Mai unguwa ya yi, wani wari ya ji ya na fita daga bayan yaron nashi, su na daga shi aka duba sosai, an fafake ma yaro baya, jini da wani ruwa mai danqo danqo ke zuba, ga wari, ihu da kururwar mata da yaran gidan ne ya cika ko ina na gidan, Mai unguwa kuwa suman tsaye ya yi, hawaye na bin kuncin shi, zuciyar shi ta yi mugun qunci, ta yi baqiqqirin, "Wa ya yi maka wannan mummunan al'amari Isyaka? Wa ye ya bata maka rayuwa Isyaka? Wa ye ya zalunce mu? Ya aikata abinda Allah da Manzon shi ya yi hani da shi, ya tsine wa masu yi, da wanda aka musu, Allah ya na fushi da masu wannan mummunar dabi'ar da ko dabbobi ba sa aikata wannan alfashar,wa ye ya ci amanar mu? Waye shi ? Waye ya ci amanar mu?" Babban dan Mai unguwa ne ya kama Isyaka daga hannun mahaifin nasu, ya aje saman tabarma, sannan ya ja hannun baban nasu suka koma gefe, ya zaunar da shi saman kujerar shi ta tsakar gida, ya na jin ya zauna, ya dafe goshin shi, ya fashe da wani irin kuka, mai ciwo. Gaba daya gidan ya rikice, da sassafiyar har maqota sun ji koke koken sun shigo, kafin ka ce kwabo, labari ya baza unguwa. Wasu da ke a social media kuwa har sun fara yadawa, tare da ɗaukan hoton Isyaka ba da izinin iyayen shi ba, ba da sanin shi ba. Gani suka yi kukan ba zai kai su ba, uwar gidan Mai unguwa ce ta dauke shi, ta na kuka ya na kuka, ta wanke shi tass, ya suma ya kai sau uku kan a gama, saboda ciwon da ke jikin shi. Ranar ahalin Mai unguwa ba mai maganar karyawar safe ma balle na rana, kowa hankalin shi a tashe yake, bayan sun gama shirya yaron, Liman ya yi sallama da Mai Unguwa. Ko da ya je, suka gaisa ya jajanta abinda matan shi suka je suka bashi labari,  sai ya bada shawara akai yaro asibiti, sannan a kai ma yan sanda rahoto. Haka kuwa akayi ,a police station an yi ma Isyaka tambayar duniya bai san su waye suka dauke shi ba, bai ma san sanda aka dauke shi ba,sannan  aka maida shi, (sharrin asiri,wasu masu aikata hakan su na sihiri,domin in b asihiri ba ba yanda za a yi wasu abubuwan su faru, se kuma son zuciya da rashin tsoron Allah, Allah ya ma na tsari da mugun ji mugun gani, mugun aiki) Ba yanda suka iya, daga qarshe dai aka ce za a yi bincike, wanda zai wahala ayi din,cases irin wannan sun fi dari a wajen yan sandan,ba kan shi farau ba,an dad'e ana yi ba a bi ma mutane haqqin su, domin wasu masu bin haqqin ma suke kwace haqqin, asibitin aka wuce da shi, nan ma sai da aka sha fama kafin a samu bashi gado. ********************** Lawwali na fita daga gidan su Sultana unguwar iyayen shi ya nufa, domin yanda ran shi ke tafasa da kalaman Hajiya Ikee, in bai dora sanyin idaniyar shi a idon shi ba ba zai ji salama ba, bai san me zai iya aikatawa ba. Ko da ya isa gida kuwa, ya yi sallama Mai buruji da Kameelu ne suka amsa shi, Kameelu ya tafi da sauri ya na ma yayan nasu sannu da zuwa, ya ga ba walwala a tattare dashi, nan take ya ce, "Yah Lawwali Mubaraka kuwa bata nan, tun da ta tafi makarantar boko bata dawo ba, wataqila ta wuce islamiyya daga can" Idanun shi ne suka kada suka yi jawur, cikin d'aga murya yace, "Miii ! Mi ka ce? Ina ta tai? Yanzu hwa mangariba ake kira, ina ta tsaya?" Lamishi ce ta fito daga dakin ta, ta tsartar da yawu, ta na saka takalmi ta na daura zani ta ce, "Ina ko ta tafi banda gantali, na ce kar ta tai makarantar wahalar ga amma sai da tassa qafa ta hita, in ma sace ta ank....." Wani duka Lawwali ya kai wa randar da ke tsakiyar gidan, sai da ta tarwatse, ruwan cikin ta ya baje a wajen, ba Mai Buruji ba da ta riga ta fara tsorata da yanayin da ya shigo da shi ba, hatta ita 'yar taurin wato Lamishi sai da ta shiga taitayin ta, kameelu kuwa a guje ya bar gidan, cikin hargowa ya kalli Lamishi yace, "Ina raga maki ne saboda Baraka na, duk wani abu ya same ta, sai na yi ajalin ki" Yanayin yanda ya yi maganar ya kad'awa Lamishi hanji, a rayuwar ta kafff yau ce rana ta farko da ta ji tsoron d'an nata, ashe kyale ta yake saboda Mubaraka na hana shi, Dan Talo da ya  so shiga gidan dan ganin motar Lawwali ne, ya ji ana tashin hankalin nan, ya koma cikin sanda ba tare da kowa ya ga shigar shi ba, balle fitar shi. Dakin shi ya shige ya dinga wurgi da duk wani abu da hannun shi ya kai wajen,  tunawa ya yi da ya sai mata waya, kiran wayar ya fara, amma ta na ringing ba a daga ba, wata qara ya saki, sannan ya daki qofar dakin da qafar shi, sai da ta balle tai qasa. Mai Buruji ta gama shiga tashin hankali ,mayafin ta a hannu ta fice a gidan cikin sanda, ta afka gidan Yabbuga. Lawwali ne ya sake kiran No Mubaraka aka ce, a kashe take, ihu ya saka, tare da zabura ya fita ya bar dakin , a guje ya ja motar shi ya bar gidan........... *Mubaraka Allah ya sa ba gidan qawaye ki ka fara bi ba, tunda an fara sa manyan kaya, Lols* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 WRITTEN BY HAERMEEBRAERH PAGE 25: Ko da ta farfaɗo,kwance ta gan ta a wani gado madaidaici, wanda da alama sabo ne dan katifar shi ma ko leda ba a cire ba, haka aka saka ta, mirror da komai na dakin sabo ne, hatta da fentin dakin, sabo ne, kamar irin dakin sabuwar amaryar nan. Gefen ta ta kalla, a yayin da ta ji kafar ta ta yi nauyi, Murjanatu ce a hannun ta na hagu, ta danne mata qafa da jikin ta, dayan hannun ta na dama kuwa Saliha ce. Tunanin baya ta fara yi. Ta kammala duk wani aikin ta na ranar, ta shirya dan tafiya makarantar boko, Lamishi ta hana ta, ta ce ba inda zata ta zauna ta jire gida, ta yi magiya, ta yi roqo amma inaaa, fafur Lamishi ta ce ta zauna ta jire gida, in ba yawon tazubar zata ba, karatu dai an jima ba aje ba mi za ta gane yanzu? Bayan sun tafi, Mubaraka na zaune gidan shiru, kawai sai dabara ta fado mata, ta kuwa sake shirin makaranta, ta dura hijab da niqab din islamiyya, ta dauki kudi cikin wanda Yah Auwal din ta ya bata, shago ta je, ta sai kwado, aka bata mai kyau, me kwari. Ta na zuwa ta samu ko ina ta rufe, ta sa kwado ta garqame qidan, ta kai wa Yabbuga ajiyar key, ta ce ta yi makaranta . Da azahar an tashi boko, ta tsaya a makarantar har lokacin islamiyya ya yi, dan ta san bata isa zuwa gidan gwamna ba, Lamishi na can, Auwal na can za su yi rikici a gaban mutane. Saliha da Murjanatu yaran mutum guda ne, jinin su ya hadu da Mubaraka, kasancewar ta mai qoqari, su kuma su na son mutum me qoqari da kamun kai, (Sai hali ya zo daya ake abota), dan haka suke qawance, boko da islamiyya, su na zaune da iyayen su anan unguwar Tudun Faila. Sun roqi Mubraka da su tafi gidan su, in za su islamiyya sai su tafi tare . Haka kuwa aka yi, da misalin qarfe uku, na rana, sun ci abinci sun yi wanka, sun shirya cikin kayan makarantar su, sun sanya niqabin su. Tafe suke su na hira, suka ji an taka wani wawan birki, a gaban su, kafin su gama tunanin me ya faru, an dauke su cak kamar wasu leda an watsa a mota Bus, ihun su ya qare ne a lokacin da No 4 ya zira hannun shi cikin niqabin su ya shaqa masu wani abu, suka hau bacci. Tun daga nan suke bacci ba su san a inda suke ba, sai a wannan lokacin da ta farka . Tashin su Saliha ta yi, ta na qoqarin yin kuka, su na farkawa suka hau ihu, No 4 ne ya bude qofar ya shiga hannun shi dauke da wata qatuwar bindiga ya na muzurai, tare da fadin. "Ko ku mana shiru ko na tarwatsa kan yarinya," Kamar an yi ruwa an dauke, haka suka yi shiru, sun qanqame junan su, su na rawar jiki, No 1 ne ya shiga, fuskar shi a rufe, idanun shi ne kawai a waje, hatta da hannun shi da qafa duk a rufe suke, cikin kakkausar murya ya ce, "Ke ! Zo nan" Cikin rashin fahimta Saliha ta miqe ta je, wani mummunan duka ya kai mata sai da ta juya, ta kidime, "Da ke nake? Ke kuma inna sake kiran ki ba ki zo ba, za ki ga yanda zan lahantar da ke," Cikin rawar jiki, Mubaraka ta miqe,dan kuwa ya nuna ta da yatsa, ta san da ita yake tabbas, amma gudun kar ya dake ta ta tsaya daga nesa. "Ba zaki zo ba kenan?" Da sauri ta isa gaban shi, ko ina na jikin ta rawa yake, tsabar tsoro,hijabin ta ya cire ya yi wurgi da shi,sannan ya tuge dankwalin ta, gashin ta irin na hausawa mai cika ya kalla, cikar shi da tashon shi sun burge shi,hannu ya kai zai taba, ta yi baya da sauri tare da fadin, "A'uzu billahi,meye haka ka ke yi, ko baka san haram bane ka taba ni" Wata iriyar dariya ya kwashe da ita, sannan ya nuna ta da hannun shi manuni, ya ce, "Ke, ke ce ke fad'in an tabi haramun? Qaunar Lawwali ka batun haramun?" Hannun shi ya sa gaba daya ya fizgeta ta fada jikin shi da qarfi, qara ta saka, ya kuwa wanke ta da mari se da bakin ta ya fashe, jini ya dinga diga, kuka ta fashe da shi ta na kiran sunan Allah, akan ya kawo masu agaji, Lawwali ne ya fado mata a rai, nan da nan ta kalli bawan Allahn da ya mare ta, kallo ta bishi da shi daga sama har qasa, tabbas shi ne, abokin Yah Auwal, wanda ta ji ya na kira da No 1, cikin rawar murya, ta furta, "No 1?" Da sauri No 4 ya fita daga dakin hankalin shi a tashe, zufa na tsattsafowa daga kowacce kafa ta jikin shi,cikin tashin hankali ya kira wayar No 1, shi kuwa ya na ciki ya na ganawa Mubaraka azaba, bai so ta gane shi ba, ya na ganin kiran No 4 ya sake ta ta fad'a cikin su Murjanatu,nan da nan kuwa suka rungume ta, su na lallashi. Ya na fita No 4 ya ce, "Dama ka san da qaunar Oga a cikin su? Garin ya ankai muka dakko da qaunar Oga? Ba cewa ka yi wata qaunar abokin ka za mu dauka ba? walle ba ruwa na in oga Lawwali ya gano kai ka ɗauke ta, kar ka kira suna na, ina da iyali, ina da mahaifiya da tai yi min saura, ban shirya mutuwa ba ni da dangi na" Wata tsawa No 1 ya sake ma No 4, "Wai kai me ye haka? Kana wani tsoron shi kamar  ba namiji ba? Yanda ya ke jin shi shege ne mu ma muna jin kan mu, kuma ka na ganin da mun tsaya diba wadda nika batu ka na ganin ba za a kama mu ba? Dallah be a man, yanzu ka tai zuwa samo musu abinci mu kulle gida mu koma daji, kahin a kula bamu nan" No 4 dai bai gama daukan wannan maganganun ba, a mugun tsorace yake, gani yake kamar zai ga Lawwali a gaban shi, cikin rawar jiki ya tafi ya samo masu binci, da ruwa, da duk wani abu da ya kamata su yi amfani da shi, dayan dakin dake can lungun gidan suka maida su, dakin na dauke da bayi, da babban gado, su na wurga su suka rufe gidan, sannan suka tsorata su da fadin akwai masu gadi, in suka ji kwakkwaran motsin su, sun bada umarnin a shiga a harbe su. Ko da suka fita daga gidan, ina dubawa sai na ga wajen sabuwar unguwa ce,ba gidaje sosai, Bus suka shige suka dauki hanyar da zata sada su da maboyar su. *********************** Lawwali ya firgice ya haukace wajen neman Mubaraka, tsakanin makarantar su ta boko da islamiyya da unguwar su ya yi zuwa ba iyaka, daga baya gida gidan yan makarantar su ya dinga bi ya na tambayar sanda suka gan ta na qarshe, jikin Lamishi kan ta sai da ya fara sanyi, Dan Talo kuwa ya na can yawon bin abokai, bai san me ke faruwa ba, sai wajejen sha daya da ya dawo ya ji Muryar Lawwali cikin maye ya na ta ashar tare da alwashin in ba a gan ta ba a gobe sai ya yi ajalin Lamishi, mugun bakin ta ne da tsanar da take wa Mubaraka ya ja ta bar gida. Lamishi fa yanzu tsoron d'an nata ya gama shiga kowacce kafa ta jikin ta, basu taba ganin shi cikin matsanancin hali irin wannan ba, ya farfasa musu abubuwan amfani, ya jiwa kan shi rauni kala kala, ga shi ya kasa kokawa, banda huci ba abinda ya ke fitar wa kamar wani damisa. Dan Talo qin shiga gidan ya yi, ya labe a waje, (uban banza kenan) jira yake ya samu Lawwali ya shiga dakin shi ya afka gidan, in ya so a nutse ya tambaya ya ji ina Mubarakar ta tafi. Da misalin sha daya da rabi  na dare Lawwali ya gama yanke shawara, makullin motar shi ya dauka,ya ja qofar shi zai fice, Dan Talo na maqale ya ji motsi, kwanar gidan ya sha a guje, Mai Buruji da Yabbuga na tafe su na tattauna tashin hankalin yau da Lawwali ke ta yi a unguwar, Yabbuga na fadin, da an sha kwana za ta koma, bata fatan had'uwa da shi ya na lafiya ma balle yanzu da yake a fusace. A guje suka ga Dan Talo, su ma diba suka yi a guje Yabbuga ta yarda yar kwabirar wayar ta rakani kashi, sai ihu take ta na kiran Dan Jumma tare da zagin shi ta na fadin ya na sane ya qi raka su. Dan Talo ya riga su fad'awa gidan su Yabbuga, dafe da qirji suka same shi ya na maida numfashi, Dan Jumma ne ya fito a tsorace ya na tambayar waye. "Mi na na kun ka shigon gida haka  a guje kamar wad'anda aka biyo? Yaqi akai halan?" "Yaqi ake amma a gida na, wannan shegiyar yarinyar ce ta tafi yawo, bata dawo ba, ta ja muna bala'i, hatta da gambun gidan nan bai tsira ba, sai da Yaron nan ya ɗebe shi yau, komi ya hwashe ya lalata, na jiyo ya na fadawa Lamishi gobe in ba a ga Mubaraka ba sai ya yi jalin ta, ban ko wallah shiga shi gama da ni" "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, anya Dan Talo kun yi addu'a kuwa? Yaro awa diyan shedannu? Bashi jin maganar kowa sai dai a ji tashi?" "Ke Yabbuga shige ciki, kai kuma, dan Allah ka kama matar ka ku tafi gida, kuma da ka ke fad'in Mubaraka ta tahi yawo, ka hini sanin halin ta, iya sani na da ita ba za ai mata shaidar yawo ba, yarinya ce me hankali ,ko tunanin wani abun ne ya same ta baku yi, ku kam Allah ya yi muku sauqi, (gyara tsayuwar shi Ɗan jumma ya yi, ya na kada hannu, ya ce) zan ruhe gida" Cikin sanyin jiki Mai buruji ta bi Dan Talo da jiki ya wa sanyi, sai yanzu maganar batan Mubarakan ya fara shigar shi, tabbas ita ba me yawo bace, kawai dai yawan fad'a da Lamishi ke yi ne ya sa shi ma yake fada. Su na shan kwana suka tsaya cak, sai da suka tabbatar motar Lawwali bata nan, suka qarasa. Su na shiga suka ga Lamishi na hada kayan ta, cikin tashin hankali, Dan Talo na tsaye a bakin qofar shiga dakin ya ce, "Ke kuma mi na na ki ka yi haka? Ina zaki da wanga tsohon dare?" "Gidan iyaye na zan tafi, tunda d'an da na haifa da ciki na ya ce  sai ya yi ajali na akan qaunar shi, diyar da ni na haihe ta da ciki na, wanga wanne irin bala'i na? Ka dai san yadda Yaron nan shike ko?" "Tau in kin tai can an ce maki barin ki zai? Kin ga kin ja musu musiba, gwanda ki zauna, gobe mu tai bid'ar ta gaba dayan mu, ki yi tunani dai" Shiru ta yi, ta na nazari,to ina Mubaraka ta tai? Ita din ba me yawo ba ce, (sai yanzu ta san ba me yawo bace, duk sunayen da take kiran ta da su). *********************** A hargitse ya shiga dajin, kowa ya san Oga ba lafiya a daren,dan haka kowa ya nutsu, No 1 da sauran yaran shi na kusa ne suka bi shi a baya, dakin da suke ajiye mutanen da suka sato, 'yan uwan su sun kasa biyan kudin fansa ya shiga ,firfito da su ya sa aka dinga yi, sai da ya fidda wajen mutum biyar sannan ya jera su a filin wajen, idanun shi kadai abin tsoro ne, bindigar da aka cika da harsashi ya karba ya dinga kai musu harbi, sai da ya harbe su tass, sannan ya koma dakin shi da ke wajen, ma'ajiyar giyar shi ya je ya bude,ya jima kwarai  rabon shi da shan giya ,dakko kwalba ɗaya ya yi, ya kafa kai, bai aje ba sai da ya sha ta kusan rabi, wata iriyar razananniyar qara ya saki, ya buga kwalbar a qasa, wannan qarar ta firgita No 4 ba kadan ba, hankalin shi ya yi bala'in tashi, tsoro ya hana shi tunanin mafita. In ya ce ze sanar da gaskiya,ya san bai tsira ba, in ya bari har Lawwali ya gano da kan shi nan ma bai tsira ba, ya zai yi?????? *Ina nissani?* [6/21, 5:15 PM] HAERMEEBRAERH ❤️: 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 27: Sati biyu ya wuce ba Lawwali ba bayanin shi, ba Sultana kadai ba, hatta da Gwamna Halliru ya fara shiga tashin hankali akan lamarin Lawwali. Duk wata barna da ta'asa da Lawwali ke aikatawa ta na komawa kunnen Gwamna Halliru, ga zabe ya gabato sauran kwana goma sha uku, lamarin ya tabarbare fiye da tunanin Gwamna, domin kuwa a yanzu Lawwali ko cikin gari bai cika shiga ba, sai jefi jefi dan ya ji halin da ake ciki game da neman qanwar shi da ya sa a yi. Lawwali ya koma kamar mahauci, akan neman Mubaraka, ya yi kuka har ba iyaka, ya zama kamar wanda ya rasa iyayen shi da dangin shi a dare daya. Duk wata motar da ta yi tsautsayin bi ta kusa da dajin su, to sunan su matattu, ko kuma ya sa a kame su, ayi ta azabtar wa, ko ya sa a yi ta amsar kudi wajen dangin su, madadin batan Mubraka ya risinar da shi,sai ya sake ruruta masa wutar rashin imani a zuciyar shi. Sultana kuwa duk ta fige ta rame saboda rashin Lawwali, ko ta je Foundation din ma watarana da kuka take komawa gida, rashin ganin shi a idanun ta ba karamin azabtar da zuciyar ta yake ba. Duk ta dora laifin akan Hajiya, domin a tunanin ta maganar da Hajiya ta yi ne ya sanya shi yin fushi ya tafi. Ta gwada No shi ya fi sau shurin masaqi amma ta qi shiga, kullum sanar da ita ake a kashe wayar take, ta yi kuka ta godewa Allah, ta yi sallah ta yi addu'a akan Allah ya dawo mata da shi in da alkhairi, in babu Allah ya sa mata hakuri da dangana, hakan da ta yi ne ya sa ta ɗan samu sauqi kadan a ran ta, har ta ci gaba da aikin alkhairin da ta sa wa ran ta. Shiru shirun ta, da rashin shiga mutane da take ya bawa Gwamna damar yada abubuwan da take na alkhairi a gidajen talabijin da rediyo, da duk wata kafar sadarwa, mutane kuwa na ta yabawa, wasu na qara neman taimako a wajen ta, ita kuwa hakan na mata dadi, ganin aikin da take ya na ta bunqasa. In ta na aikin ta na samun nutsuwa da kwanciyar hankali,da ta dawo gida komai sai ya kwance mata ,ba abinda take gani a idon ta in ba Lawwali ba, tsayuwar shi a jikin mota, da murmushin shi mai sauti, yanayin yanda yake kafe ta da ido, ya na kallon ta, sai ta ji kamar a wannan lokacin ya ke kallon nata, har lumshe ido take, watarana ta yi murmushi in ta tuna, watarana ta fashe da kuka. An shiga sati na Uku Lawwali be bayyana ba, sai wata safiyar Lahadi, ya shiga gari, direct wajen aski ya nufa,a ka yi masa aski me kyau, aka masa gyaran qafafu da hannuwa, sannan ya sayi turaruka, da kayan abinci ya nufi gidan shi,ko da ya shiga gidan duk ya yi qura, kallon ko ina ya yi, cikin sanyin jiki ya ajiye ledojin hannun shi ya kalli ko ina, wasu irin zaratan hawaye ne masu zafi suka dinga zubar masa. Mubaraka ce ke masha shara, in ta biyo shi, ta yi wanka ya maida ta gida, ko gyaran da akai wa gidan na qarshe ita ta masa, har ta dinga mishi fadan ta ajiye wani flower vase a tsakiyar table, ta koma ta gan shi a qasa, ya kama kunnen shi ya na bata hakuri, ta na ta tura baki ta na shagwaba, ta ce ta hakura kar ya sake, ta mayar ta gyara komai, ta yi wanka ya maida ta gida, ya na gama tunawa ya sanya wani irin kuka mai ban tausayi, sannan ya ce, "Barakana ina kin ka tai na? Wanne hali ki ke ciki? Kin ci abinci? Kin yi wanka kuwa? A wanne irin waje ki ke kwana? Barakana, ki yafe wa yayan ki, na kasa kare ki, na kasa nemo ki, baraka na ki dawo gare Ni, ke ce sanyin idaniya ta, na rabu da Sultana duk da son da nake mata, na kasa cire ta a zuciya ta, dan Allah ki dawo ki taya Ni neman soyayyar ta, ba zan iya ba Ni dai,ke Ni ka jira ki sa Sultana ta so ni, Barakaaaa" Kuka ya dunqule a waje guda ya na yi, kamar qaramin yaro, ya na son dika qannen shi, amma mubaraka ta daban ce, ita kadai ce ke son shi, ita ke kula da shi, ita kadai ta damu da rayuwar shi, tun ya na da burin ya dawo na gari, har ya kangare, ba wanda ya damu da wace iriyar rayuwa yake ciki, kudi kawai iyayen shi suka sanya a gaba, yau kuwa zai kai musu kudin da zai haukata su, amma sai suma sun bayyana masa Barakan shi, ko ya sawa kudin fetur a gaban su ya qona, hakan sai ya fi masu ciwo sama da yanda yake ji a ran shi. A haukace ya debi kudin da ya koma da su, masu dimbin yawa a jaka, ya zari makullin motar shi, da wayar shi da ya bari a gidan, bai je ko ina da ita ba, motar shi duk ta yi qura. Ya na shiga ya fitar da ita, ya koma ya kulle gidan, ya na qoqarin fita daga layin, motoci guda biyu da ke kai Sultana Foundation a yanzu su ka shiga unguwar suma,kamar an ce ta daga kai, Lawwali ta gani fuskar shi ba walwala, idanun shi jawur kamar ba shi ba, ya na tsula gudu,gashi duk ya yi duhu, "Auwal? Dama Auwal na nan? Shi ne ya daina zuwa? Driver bi motar Auwal duk inda ya yi," "Tau Ran ki shi dade" Dayar motar masu tsaron lafiyar ta na ganin an juya suma suka bi su, ta waya ta sanar da su me ke faruwa, kwantar da hankalin su suka yi suka bi su a baya. Saboda damuwar da Lawwali ke ciki, be ma kula ana bin shi ba, har sai da ya shiga unguwar su, ya tsaya a qofar gidan su, sannan ya kula da motocin Sultana. Wani irin yanayi ne mara fassaruwa ya shige shi, kewa ne, tsantsar soyayya ce, da kuma neman taimakon ta, duk sun had'u sun game masa waje daya. Ita kuwa bata san sanda hawaye ke gudu a fuskar ta ba, ga alama nan, Lawwali na shaye shaye, amma bata duban wannan, domin dama dan Adam tara yake, be cika goma ba, ita dai a kowanne hali yake ta na son shi, ita kadai ta san ya take ji. A hankali suke takawa zuwa ga junan su, Sultana ji ta yi kamar ta kwantar da kan ta a faffadan qirjin shi, ko abinda take ji zai ragu, Lawwali ji ya ke kamar ya isa ya rungume ta, ta shafa kan shi da siraran yatsun ta, tare da fada masa cewar 'Komai zai wuce, zai yi daidai' a cikin kunnen shi. Sun jima su na kallon juna kafin Sultana ta yi qarfin halin cewa, "Why? Me yasa? Me ya sa za ka tafi a lokacin da zuciya ta, ta amince, ta yarda, ta kuma gamsu da ta kamu da matsanancin ciwon son ka? Me ya sa ka tafi, a lokacin da nake tsananin buqatar ka, ka kuwa san ya nake ji a nan dina? (Ta sanya hannu, ta nuna saitin zuciyar ta, cikin kuka,) ba zaka gane ba, saboda baka san me ne ne soyayya ba ga dukkan alamu," Cikin sauri ya dakatar da ita, dan kalaman ta na sake harzuqa zuciyar shi, ta na hango masa mugunta kala kala. Cikin cije lebunan shi a cikin bakin shi ya shafa kan shi, da hannu daya, sannan ya ce, "Sultana, ba ke dai ka jin duk abinda kin ka lissahwa ba, ni ma ina ji dika, wataqila har da dori ma, amma sultana ba ke d'aya zuciya ta ke so ba, qauna ta ita ce rayuwa ta, ban da komai banda kowa sama da ita,ita kad'ai ce gata na a duk qasar ga, ba mai so na tsakani da Allah, sama da ita, a yanzu haka ji na nake kamar duk duniya sun juyan baya, ni kadai ne, ban da kowa banda komai," "Wait a minute,me ya samu Mubaraka?" A cikin tashin hankali Sultana ta masa wannan tambayar, a cikin qasa da minti bakwai ya bayyana mata me ya faru dangane da batan ta,da kuma irin neman da yake mata, bai samu ba. Cikin kuka Sultana ta juya ta rufe bakin ta, ta jima a haka ta na kuka, Lawwali ma ji ya ke kamar ya yi kukan, sai daga baya  ta juya gare shi, ta na share hawayen ta, motar ta ta fara budewa zata shiga,sannan ta ce, "Mu je gida Daddy na nan yau, mu sanar da shi,a sanya neman ta, duk inda ta shiga, i love her, she is a gud gurl, I can't let anything happen to her, she is like a sister to me, mu je gida Auwal, maza shiga mota mu je," Kallon gidan su ya yi, cikin takaici, ya na jiyo muryoyin mata ana ta zabga hira, ya ji haushi da be shiga ya tarwatsa su ba, qanwar shi ta bata amma suke hira haka ana dariya har waje ana ji, ya so ya shiga ya gan su, da duk sai ya musu rashin mutunci d'aya bayan d'ayan su, amma ba komai next time. Kwafa ya yi, ya shige motar shi, ya bi ta su Sultana. ************************* Gwamna Halliru na ganawa da su No 1 da 4, su na tattaunawa akan yanda Lawwali ya haukace. Sultana ta je za ta shiga parlour wasu masu tsaron wajen ne suka dakatar da ita, tare da sanar da ita cewar Gwamna ya ce kar a bawa Kowa damar shiga, sai da izinin shi, d'aya daga cikin su ta kalla tace, "Ka je ka sanar da shi ni ce, na ke son magana da shi, ya na da mahimmanci na gan shi yanzu" Har security din zai tafi, Lawwali ya qarasa shiga wajen, su na hada ido, security ya ja baya, tare da fadin, "Ran ka ya dade Oga, Barka da zuwa" "Gwauna hwa? " "Shi na ciki Oga" Mamaki ne danqare a cikin Sultana, an hana ta shiga amma an budewa Lawwali  ya shige,me kenan? Lawwali ya fi ta matsayi a gidan Uban ta kenan? Ko da suka shiga shiru wajen ya dauka, ba No 4 da ake tausa ba, ana nuna masa ba abinda Lawwali zai yi, as long as bai gane ina qanwar shi take ba, har Gwamnan kan shi sai da hankalin shi ya tashi ainun. Cikin rawar murya, No 4 ya ce, "O....ogaa, kai ne da rana haka?" Lawwali ko kallon No 4 be ba, ya samu kujera ya zauna, tare da harde qafa,No 1 ne ya je ya tsaya a daf da shi,hakan kamar girmamawa ne a gare shi, No1 na ta hararar No 4 tare da yi masa nunin ya nutsu, Sultana kuwa mamakin abinda take gani ya fi qarfin ta, waje ta samu ta tsaya, ta na kallon yanda mahaifin ta ya yi lakwas a gaban Lawwali, bai magana ba akan zaman da Lawwali ya yi a gaban shi . "Oga har yanzu fa shiru,yanzu haka mun kawo maganar ne wajen Excelency saboda a bamu taimako" "Mu ma abinda ya kawo mu kenan,na yi iya qoqari na na kasa, ina neman taimako a hukumance, a bido min qauna ta, in ba haka ba,....." Shiru ya yi, ya taune leben bakin shi na qasa, tare da dukan tafin qafar shi da ya dora a saman dayar qafar tashi. "Ah ah Sultana, mik-kawo ki nan?" "Tare muke," "Ban gane tare kuke ba, qaqa an kai kuke tare?" "Dad Mubaraka ce ba a gani ba, kusan sati Uku yanzu, shi ne na rako shi neman taimako wajen ka, amma yanzu na kula is like, ni anka rako, ko wani zai iya min bayani akan abubuwan da nake gani a yanzu?" Da sauri gwamna ya zari wayar shi, ya kira Head quarter na yan sanda, ya fara bada report din batan Mubaraka, Sultana tuni ta manta da tambayar da take yi, ita da Lawwali sun bawa Gwamna hankulan su. Wayar aka bawa Lawwali ya yi kwatancen ta,da bayanin ranar da suka nemeta suka rasa, tare da alqawarin ze tura hotunan ta. Godiya ya miqe sosai ya na wa gwamna, Sultana ma haka. Gwamna na son bin su ya ji dalilin da ya sa suke a tare, kuma ya na son magana da su No 1, dan haka sai da ya bari su Lawwali sun fita, sannan ya qara jaddada musu su yi taka tsantsan ta yanda asirin su ba zai tonu ba, domin in Lawwali ya san sun sace qanwar shi, har shi kan shi ba zai tsira ba, ballantana su. Wannan kalamai sun sake birkita No 4, da kyar yake hadiyar yawu, zufa sai karyo masa take, a sati ukun nan, duk 'yar qibar ma da ya yi, saboda kudin da suke samu, duk ta zabge, ya fita hayyacin shi, ba wani kwanciyar hankali a tattare da shi. Su Sultana kuwa a jikin motar shi, suka tsaya, su na magana, hira ce mai dadi,ta yaushe gamo suke yi, kusan kaso saba'in na hirar dukkan su akan Mubaraka su ke yi, Sultana na son mubaraka, ba wai dan ta na qanwar Lawwali ba,ah ah, yarinyar abar so ce ga duk mai hankali. Shi kuwa a wajen shi Mubaraka ita ce rayuwar shi, a ganin shi ma ba zai taba samun kan Sultana ba in bata nan. Bayan sun yi sallama za su tafi ne Sultana ta ce, "Haka ake sallama da masoyi? " Kallon yanda ta maida kai gefe ta yi, sai ta masa kyau, murmushi ya yi, kadan, wanda rabon shi da murmushi na gaskiya, ba na mugunta ba, tun kafin batan Mubarakan. "Ya ya kamata masoyi ya yi sallama ?" Dan rufe fuskar ta tayi da hannun ta kadan ta ce, "Kamata ya yi ka ce, Sultana na tafi, zan dawo anjima, ina son ki" Bude baki Lawwali ya yi, ya na dariya mai sassanyan sauti, ya ce, "Kaiii ka kaiii ka kaiii, Baraka na ta ce man ke ustaziya ta wallah, ashe ke iya soyayya haka?" Mayafin ta ta ja sosai ta rufe fuska sannan ta ce, "To ai soyayya kowa na yi" "Ok, to sultana Ina son ki," Wani irin dad'i ne ya ziyarce ta, musamman da ta kalle shi ta ga babu wasa a kalaman shi, iyakar gaskiyar shi yake fada, ta ji sautin Muryar shi, ba alamar gatse ko wasa, amayar da ta ta zuciyar ta ce, "Auwal ina son ka, In na ce ina son ka, ba ina nufin ina son ka fiye da yanda kk so na bane, ina nufin ina son ka a kowanne hali, ina son ka ko da wani sabani ya haɗa mu, ina son ka ko da ka na cikin damuwar da ta sa ka nesanta da ni, ina son ka sama da nisan nan da ke tsakanin mu,ina son ka sama da yanda na ke jin zafin rashin ka a rai na, ina son ka sama da dukkan wani abu da zai qoqarin shiga tsakanin mu, ina nufin nafi son ka Auwal" Ya Salam, Lawwali ya gama narkewa,kalaman sultana sun wanke masa wani kaso na baqin cikin da ke ran shi,dama haka take fata, shi ne dalilin da ya sanya ta cire kunya ta furta abinda ke ran ta, sai bayan ta gama kashe masa gabban jikin shi, ta juya da gudu gudu ta shige gida,dan kuwa kunyar shi ba zata bar ta ta tsaya jin me zai ce ba again. Lawwali ya jima a wajen, kafin ya shiga motar shi, ya tada ya bar gidan. Su No 1 kuwa ya na fita suma suka bar gidan, dan zuwa sauyawa  su Mubaraka maboya kamar yanda Gwamna ya bada shawara, da kuma wajen zama. Lawwali har ya isa gida bai dena murmushi ba, ya jima ya na dirzar dattin jikin shi,kafin ya samu abinci ya ci rabon shi da abinci sosai kamar na ranar ba zai iya fadin ga lokacin ba. Ya na kammalawa ya kwanta, dan hutawa. ********************** Vissa ta samu, na tafiyar Isah Saudiya, ana sauran kwana biyu tafiyar Isa,  Hajiya ta sa Isan ya kai mata su Hansatu su gaisa, Hansatu ta sha mamakin jin duk abinda ke faruwa a bakin mahaifiyar ta, ace duk wadannan abubuwan na faruwa bata sani ba? Haka ta dinga yaqe ta na yabawa Isah ,tare da yanka qarya kala kala, dan ta kare shi, yaran ta na ta mamakin qaryar da take ta shinfidawa. Ba daban ta basu tarbiyya mai kyau ba, tabbas da sun tona mata asiri, dan kuwa ba su so ta rufa masa asiri ba. Isah kuwa sai murmushi yake ya na fadin, "In ban muku ba wa zan wa?" Yayan Hansatu ya qara masa dubu hamsin ya qara a kan jarin shi, sai godiya suke ta zabgawa. Da yamma Hajiya ta sa mota ta maida su gida. Tafiyar Isah Makka daiiii sauran kwana biyu, wace zata yi rakiya?????😂 [6/21, 5:15 PM] HAERMEEBRAERH ❤️: 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 26: Da misalin tara na safe,Isah ne tsaye a qofar katafaren gate din gidan su Hansatu, mai gadi ya hana shi shiga, sai bala'i suke, hargowar su ta ratsa har cikin gida,Hajiya na zaune ta na kallon Sunnah TV ana gabatar da maimaicin wani shiri akan kiwon lafiya, rage volume ta yi, ta saurari rikicin da ake tsakanin Isah da mai gadi, tashi ta yi, ta leqa window , magana ta ke amma ba sa jin ta, gashi Yayah'n Hansatu baya nan,matar shi ma tun jiya ba ta nan, daga an mata fad'a akan rashin iya kalami, ta yi fushi ta tafi gida. Hijabin ta ta sanya, ta fita, Isah na ganin ta ya saka fuskar tausayi, kiran shi ta yi, mai gadi ya bar shi ya shiga, zai wuce ciki ya yi qasa da murya, ya ce ma mai gadin. "Tallakan banza da wofi, haka za ka qare a gate Dan walaha kawai," Wangale baki ya yi ya qarasa gaban Hajiya tare da zubewa a qasa, cikin sauri ta ja baya sannan ta ce, "Habaa Isah tashi, tashi mu shiga daga ciki," Tashi ya yi, amma ya coge ya qi shiga, cikin raunin murya ya ce, "Hajiya na zo ne a taimaka mana, ba da ban ba yanda zan ba, nan ne waje na qarshe da zan zo, domin ku din surukai na ne, bai kamata Ku saida akuya ba ta dawo ta na ci muku danga, ina cikin wani hali Hajiya, kasuwanci ya tsaya cak saboda rashin jari, da can ina dan zuwa makka ne na kai goro, ina samu sosai, muna cikin walwala, da wadata, da iyali na, amma yanzu har kunyar shiga gida nake, saboda babu, inna shiga yara na na kukan yunwa na kan ji kamar na kashe kai na dan baqin ciki, babbar damuwar yau mun tashi ba ko silin hatsi, ga Hansatu na fama da zazzabi , shi ne na ce bari na zo ko dubu daya ne na samu na kai ta asibiti" Hajiya ta shiga matsanancin tashin hankali, 'yar cikin ta ke zaune cikin uqubar rayuwa haka?  Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. Cikin sauri ta shige ciki, tare da bashi umarnin ya bi ta ciki. A parlour'n su ta bar shi ta shige ciki, kudi masu yawa ta dakko, har bata san adadin su ba, hawaye na zuba a idanun ta, tsabar yanda take jin ran ta na quna, ta tafka babban kuskure, su na da dukiya haka yar ta ke fama da rayuwa ,abu daya ne ya ba zuciyar ta hakuri, da ta tuna kowa a rayuwar shi iya arzikin da Allah ya yanke masa zai ci, to ita ma haka ne. Isa kuwa kafin ta fita ba inda bai leqa ba a gurguje, ya tabbatar dukiya ta ji a gidan, ko ta ina akwai arziqi. Komawa ya yi ya zauna ya na jinjina kai, Hajiya kuwa ta goge hawayen ta tas, ta zauna ta miqa masa maqudan kudin hannun ta, sanan ta ce, "Isah daga yau kar ka qara kiran kan ka da suruki na, kai d'a na ne, ba suruki na ba, duk abinda ka ke so ka same ni kai tsaye,ga wannan, ka na da passport?" "Eh ina da shi a da, amma yayi espaya yanzu, na jima ban je can Makkan ba, saboda rashin jari" "To ga wannan, ka je ka yi, sannan ka min magana, sauran kuma ka kai ta asibiti, ka sai maku kayan abinci, in komai ya daidaita passport ya samu za muyi magana, ka na da waya?" Dan sosa kai ya yi ya ce, "Ehhh ina dai da sim, Amma ba waya, ta lalace da jimawa, a na ta abinci Hajiya wa ya ke ta waya?" Wani abu ta ji ya maqale mata a wuya, mai d'aci, murmushin yaqe ta yi, ta miqe ta shiga dakin ta ta dawo, riqe da waya, wayar ta ce, ta cire sim din ta da komai, ta zauna ta yi formating wayar sannan ta miqa masa, waya ce mai matuqar kyau da tsada, ta tasamma dubu d'ari biyar da wani abu. "Ga wannan, ka yi amfani da ita, last 3weeks Wannan yaron ya siyo min ita, in kaje ka gaishe ta, ita ma zan sai mata wayar dan mu na gaisawa" "Hajiya ban san da wanne kalami zan maki godiya ba, amma ina fatan Allah ya jiqan Alhaji, Allah ya masa rahama, Allah ya sa kiyi kyakkyawan qarshe na gode na gode " "Ameeen Isah, ka dena godiya, yi wa kai ne ai" Haka ya tattare yan kudaden shi ya na godiya ya fita, sai da ya kai gate ya juya ya ga ba me kallon shi, ya fiddo kudin ya na tafiyar fad'i. A gaban me gadi ya tsaya, ya dinga juya su, ya na masa kallon raini. "Kai mai gadi, ka shiga hankalin ka, in ba haka ba, se na sa an kore ka, masu gadi uku na fitar a gidan nan tun sanda ina zama a gidannan, ka tambaya ka ji wane ne Isah direba, tsohon dan iska ne ni, kuma surukin gidannan ne, daga yau na sake zuwa ka min iskanci se ka bar gidan nan, tunda ba gadon tsoho a ciki wajen gina shi" Me gadi baki ya sake ya na kallon ikon Allah, se da Isah ya maida kudi aljihu, ya gyara tsaf sannan ya bar gidan. Ko daya isa gidan shi, ya tadda Hansatu na ma yara wanka,ta share gidan fess ko ina qalqal, ta yi wankan ta shar da ita, da kayan da aka bata daga gida, ramar da ta yi ne da baqin da ta yi ne kawai ze nuna halin rayuwar da take ciki. Murmushi ta mi shi, wanda bata gajiya da yi masa a duk sanda ze fita ya koma gida, dauke kai ya yi, kamar kullum. Ba sallama ya shige, za ta bi shi ta masa sannu da zuwa ya dakatar da ita cikin daure fuska, komawa ta yi ta ci gaba da yi wa Ahmad wanka, ta na yaqe, abun ya mata zafi sosai, amma ba halin magana. Se da ya boye kudin shi tass sannan ya dauki dubu talatin ya bar gidan, ta na fada masa ga abinci amma bai kula ba. Direct wajen yin passport ya je, aka ce gobe ya koma, bai ji dadi ba, haka ya tafi, ya na saman machine suka wuce wani mai saida gasasshiyar kaza,yawun shi ne ya yanko, ai kuwa ba bata lokaci ya ce ma me machine ya juya, Isah kamar abun wasa, ya ce a bashi kaza daya, qosasshiya aka yanka masa ita aka bade ta da yaji, sannan ya ce a bashi rabin kaza again , aka yanka aka sa yaji, ya amsa, shagon kusa da wajen ya je, ya sayi drinks, ya samu wani mai machine din ya nufi gida. Ya na zuwa ya tadda su a tsakar gida Hansatu na musu karatu, miqa mata ledar kaza ya yi, ya wuce daki, Hansatu da yara na ta murna, su na ta zuba godiya. Ya na shiga dakin ya bude tashi, sai a lokacin na kula da qatuwar kazar nan ya aje wa kan shi, ya basu rabi, kamar abun wasa, Isah ya sa kazar nan a gaba da ci, bai tashi ba se da ya ci ya taune qashi ya kora da lemo me sanyi, sannan ya saki muguwar gyatsa, ya ce, "Yauwaaa Allah na gode maka,me ake da talauci? Allah ka nuna min buri na ya cika, kullum se na ci wannan" Hansatu da yara kuwa na can sun saka barin kaza a gaba, su na ci, su na hamdala ga Ubangijin da ya azurta su da kaza ba tare da sun roqa ba. Dan sauran lemon Isah ya fito ya miqawa Ahmad ya ce, "Gashi nan, ba yawa ne da shi ba,...ke kuma in kin gama ki zo ina neman ki" "To mun gode Allah shi qara budi, Allah shi ruhwa maka asiri duniya da lahira, mun gode," "Ameen, ina abinci na? Ko dan kun ci kaza se aka ce miki ba zan ci abinci ba?" Da sauri ta miqe ta na bashi hakuri, abincin dama da ya rage taliya ce da manja, da dan yaji, har ta na murna in be ci ba da dare ta bawa yaran, tunda komai ya qare, ya siyar. Ta na bashi kuwa ya zauna a tabarmar da suka tashi, ya cinye tass, ya kora da ruwa. Daki ya kira ta, da yammar, ana gab da magariba, Hansatu na ta bashi hakuri akan ya bari a mayi sallah haka Isah ya qi, sai da komai ya yi daidai a tsakanin su sannan ya sa ta hura wuta ta ɗora masa ruwan wanka, dan a cewar shi yin wanka da ruwan sanyi da magariba mura ze saka shi. Da kyar iccen ya kama, ta samu ta ɗora ruwan ya yi,ta kai masa, itama tayi, ta yi sallah. Shi kuwa ya na gamawa waje ya yi, ganin shi kuma se sanda Allah ya yi musamman ma da yake jin aljihun shi da nauyi. Hansatu na shara, ta ji sallamar Yabbuga, watso sharar dakin ta qarasa yi, ledar da Isah yaci kaza ta baje a qasa, ido Yabbuga ta zare waje, tare da sake baki, ta na salati. "Keeeee waggaa, yanzu kaza kun ka ci shi na ko a qunshe fuffuke a kai min, tau wanda ya ci shi dai, shi dai zai mace, walle a dena rauwwa, yanzu ba daban Allah ya sa na ga kin kunna wuta ba, na zo diban rushi, da ban ko sanin kun ci kaza" Hansatu mamaki ne ma ya gama qamar da ita a wajen, yanda Yabbuga ta dage ta na magana cikin fad'a ne ya fi bata mamaki, kuma gashi tabbas yawu ya cika mata baki, murmushi ta yi, ta ce, "Allah shi baki hankuri, dake ba a gidan anka soya ba, balle na ce qamshi ya dame ki, nima yanda kiggane ta haka niggane ta, ya taho mana da ita, amma ki yi hankuri, in ya sake kawowa ina kawo maku" "Tun da kwadayayya ni ke ko? Yo ce miki niyyi bamu da azziqin cin kaza? Yau na ji zancen yohi" Yabbuga na diban garwashi ta na Masifa ba a sammata kaza ba. Hansatu kuwa abun ma ya dena bata mamaki, dariya ta dinga yi, ita da yaran. *********************** A bangaren Lawwali kuwa............ *Sai gobeeeeee*😅 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 27: Sati biyu ya wuce ba Lawwali ba bayanin shi, ba Sultana kadai ba, hatta da Gwamna Halliru ya fara shiga tashin hankali akan lamarin Lawwali. Duk wata barna da ta'asa da Lawwali ke aikatawa ta na komawa kunnen Gwamna Halliru, ga zabe ya gabato sauran kwana goma sha uku, lamarin ya tabarbare fiye da tunanin Gwamna, domin kuwa a yanzu Lawwali ko cikin gari bai cika shiga ba, sai jefi jefi dan ya ji halin da ake ciki game da neman qanwar shi da ya sa a yi. Lawwali ya koma kamar mahauci, akan neman Mubaraka, ya yi kuka har ba iyaka, ya zama kamar wanda ya rasa iyayen shi da dangin shi a dare daya. Duk wata motar da ta yi tsautsayin bi ta kusa da dajin su, to sunan su matattu, ko kuma ya sa a kame su, ayi ta azabtar wa, ko ya sa a yi ta amsar kudi wajen dangin su, madadin batan Mubraka ya risinar da shi,sai ya sake ruruta masa wutar rashin imani a zuciyar shi. Sultana kuwa duk ta fige ta rame saboda rashin Lawwali, ko ta je Foundation din ma watarana da kuka take komawa gida, rashin ganin shi a idanun ta ba karamin azabtar da zuciyar ta yake ba. Duk ta dora laifin akan Hajiya, domin a tunanin ta maganar da Hajiya ta yi ne ya sanya shi yin fushi ya tafi. Ta gwada No shi ya fi sau shurin masaqi amma ta qi shiga, kullum sanar da ita ake a kashe wayar take, ta yi kuka ta godewa Allah, ta yi sallah ta yi addu'a akan Allah ya dawo mata da shi in da alkhairi, in babu Allah ya sa mata hakuri da dangana, hakan da ta yi ne ya sa ta ɗan samu sauqi kadan a ran ta, har ta ci gaba da aikin alkhairin da ta sa wa ran ta. Shiru shirun ta, da rashin shiga mutane da take ya bawa Gwamna damar yada abubuwan da take na alkhairi a gidajen talabijin da rediyo, da duk wata kafar sadarwa, mutane kuwa na ta yabawa, wasu na qara neman taimako a wajen ta, ita kuwa hakan na mata dadi, ganin aikin da take ya na ta bunqasa. In ta na aikin ta na samun nutsuwa da kwanciyar hankali,da ta dawo gida komai sai ya kwance mata ,ba abinda take gani a idon ta in ba Lawwali ba, tsayuwar shi a jikin mota, da murmushin shi mai sauti, yanayin yanda yake kafe ta da ido, ya na kallon ta, sai ta ji kamar a wannan lokacin ya ke kallon nata, har lumshe ido take, watarana ta yi murmushi in ta tuna, watarana ta fashe da kuka. An shiga sati na Uku Lawwali be bayyana ba, sai wata safiyar Lahadi, ya shiga gari, direct wajen aski ya nufa,a ka yi masa aski me kyau, aka masa gyaran qafafu da hannuwa, sannan ya sayi turaruka, da kayan abinci ya nufi gidan shi,ko da ya shiga gidan duk ya yi qura, kallon ko ina ya yi, cikin sanyin jiki ya ajiye ledojin hannun shi ya kalli ko ina, wasu irin zaratan hawaye ne masu zafi suka dinga zubar masa. Mubaraka ce ke masha shara, in ta biyo shi, ta yi wanka ya maida ta gida, ko gyaran da akai wa gidan na qarshe ita ta masa, har ta dinga mishi fadan ta ajiye wani flower vase a tsakiyar table, ta koma ta gan shi a qasa, ya kama kunnen shi ya na bata hakuri, ta na ta tura baki ta na shagwaba, ta ce ta hakura kar ya sake, ta mayar ta gyara komai, ta yi wanka ya maida ta gida, ya na gama tunawa ya sanya wani irin kuka mai ban tausayi, sannan ya ce, "Barakana ina kin ka tai na? Wanne hali ki ke ciki? Kin ci abinci? Kin yi wanka kuwa? A wanne irin waje ki ke kwana? Barakana, ki yafe wa yayan ki, na kasa kare ki, na kasa nemo ki, baraka na ki dawo gare Ni, ke ce sanyin idaniya ta, na rabu da Sultana duk da son da nake mata, na kasa cire ta a zuciya ta, dan Allah ki dawo ki taya Ni neman soyayyar ta, ba zan iya ba Ni dai,ke Ni ka jira ki sa Sultana ta so ni, Barakaaaa" Kuka ya dunqule a waje guda ya na yi, kamar qaramin yaro, ya na son dika qannen shi, amma mubaraka ta daban ce, ita kadai ce ke son shi, ita ke kula da shi, ita kadai ta damu da rayuwar shi, tun ya na da burin ya dawo na gari, har ya kangare, ba wanda ya damu da wace iriyar rayuwa yake ciki, kudi kawai iyayen shi suka sanya a gaba, yau kuwa zai kai musu kudin da zai haukata su, amma sai suma sun bayyana masa Barakan shi, ko ya sawa kudin fetur a gaban su ya qona, hakan sai ya fi masu ciwo sama da yanda yake ji a ran shi. A haukace ya debi kudin da ya koma da su, masu dimbin yawa a jaka, ya zari makullin motar shi, da wayar shi da ya bari a gidan, bai je ko ina da ita ba, motar shi duk ta yi qura. Ya na shiga ya fitar da ita, ya koma ya kulle gidan, ya na qoqarin fita daga layin, motoci guda biyu da ke kai Sultana Foundation a yanzu su ka shiga unguwar suma,kamar an ce ta daga kai, Lawwali ta gani fuskar shi ba walwala, idanun shi jawur kamar ba shi ba, ya na tsula gudu,gashi duk ya yi duhu, "Auwal? Dama Auwal na nan? Shi ne ya daina zuwa? Driver bi motar Auwal duk inda ya yi," "Tau Ran ki shi dade" Dayar motar masu tsaron lafiyar ta na ganin an juya suma suka bi su, ta waya ta sanar da su me ke faruwa, kwantar da hankalin su suka yi suka bi su a baya. Saboda damuwar da Lawwali ke ciki, be ma kula ana bin shi ba, har sai da ya shiga unguwar su, ya tsaya a qofar gidan su, sannan ya kula da motocin Sultana. Wani irin yanayi ne mara fassaruwa ya shige shi, kewa ne, tsantsar soyayya ce, da kuma neman taimakon ta, duk sun had'u sun game masa waje daya. Ita kuwa bata san sanda hawaye ke gudu a fuskar ta ba, ga alama nan, Lawwali na shaye shaye, amma bata duban wannan, domin dama dan Adam tara yake, be cika goma ba, ita dai a kowanne hali yake ta na son shi, ita kadai ta san ya take ji. A hankali suke takawa zuwa ga junan su, Sultana ji ta yi kamar ta kwantar da kan ta a faffadan qirjin shi, ko abinda take ji zai ragu, Lawwali ji ya ke kamar ya isa ya rungume ta, ta shafa kan shi da siraran yatsun ta, tare da fada masa cewar 'Komai zai wuce, zai yi daidai' a cikin kunnen shi. Sun jima su na kallon juna kafin Sultana ta yi qarfin halin cewa, "Why? Me yasa? Me ya sa za ka tafi a lokacin da zuciya ta, ta amince, ta yarda, ta kuma gamsu da ta kamu da matsanancin ciwon son ka? Me ya sa ka tafi, a lokacin da nake tsananin buqatar ka, ka kuwa san ya nake ji a nan dina? (Ta sanya hannu, ta nuna saitin zuciyar ta, cikin kuka,) ba zaka gane ba, saboda baka san me ne ne soyayya ba ga dukkan alamu," Cikin sauri ya dakatar da ita, dan kalaman ta na sake harzuqa zuciyar shi, ta na hango masa mugunta kala kala. Cikin cije lebunan shi a cikin bakin shi ya shafa kan shi, da hannu daya, sannan ya ce, "Sultana, ba ke dai ka jin duk abinda kin ka lissahwa ba, ni ma ina ji dika, wataqila har da dori ma, amma sultana ba ke d'aya zuciya ta ke so ba, qauna ta ita ce rayuwa ta, ban da komai banda kowa sama da ita,ita kad'ai ce gata na a duk qasar ga, ba mai so na tsakani da Allah, sama da ita, a yanzu haka ji na nake kamar duk duniya sun juyan baya, ni kadai ne, ban da kowa banda komai," "Wait a minute,me ya samu Mubaraka?" A cikin tashin hankali Sultana ta masa wannan tambayar, a cikin qasa da minti bakwai ya bayyana mata me ya faru dangane da batan ta,da kuma irin neman da yake mata, bai samu ba. Cikin kuka Sultana ta juya ta rufe bakin ta, ta jima a haka ta na kuka, Lawwali ma ji ya ke kamar ya yi kukan, sai daga baya  ta juya gare shi, ta na share hawayen ta, motar ta ta fara budewa zata shiga,sannan ta ce, "Mu je gida Daddy na nan yau, mu sanar da shi,a sanya neman ta, duk inda ta shiga, i love her, she is a gud gurl, I can't let anything happen to her, she is like a sister to me, mu je gida Auwal, maza shiga mota mu je," Kallon gidan su ya yi, cikin takaici, ya na jiyo muryoyin mata ana ta zabga hira, ya ji haushi da be shiga ya tarwatsa su ba, qanwar shi ta bata amma suke hira haka ana dariya har waje ana ji, ya so ya shiga ya gan su, da duk sai ya musu rashin mutunci d'aya bayan d'ayan su, amma ba komai next time. Kwafa ya yi, ya shige motar shi, ya bi ta su Sultana. ************************* Gwamna Halliru na ganawa da su No 1 da 4, su na tattaunawa akan yanda Lawwali ya haukace. Sultana ta je za ta shiga parlour wasu masu tsaron wajen ne suka dakatar da ita, tare da sanar da ita cewar Gwamna ya ce kar a bawa Kowa damar shiga, sai da izinin shi, d'aya daga cikin su ta kalla tace, "Ka je ka sanar da shi ni ce, na ke son magana da shi, ya na da mahimmanci na gan shi yanzu" Har security din zai tafi, Lawwali ya qarasa shiga wajen, su na hada ido, security ya ja baya, tare da fadin, "Ran ka ya dade Oga, Barka da zuwa" "Gwauna hwa? " "Shi na ciki Oga" Mamaki ne danqare a cikin Sultana, an hana ta shiga amma an budewa Lawwali  ya shige,me kenan? Lawwali ya fi ta matsayi a gidan Uban ta kenan? Ko da suka shiga shiru wajen ya dauka, ba No 4 da ake tausa ba, ana nuna masa ba abinda Lawwali zai yi, as long as bai gane ina qanwar shi take ba, har Gwamnan kan shi sai da hankalin shi ya tashi ainun. Cikin rawar murya, No 4 ya ce, "O....ogaa, kai ne da rana haka?" Lawwali ko kallon No 4 be ba, ya samu kujera ya zauna, tare da harde qafa,No 1 ne ya je ya tsaya a daf da shi,hakan kamar girmamawa ne a gare shi, No1 na ta hararar No 4 tare da yi masa nunin ya nutsu, Sultana kuwa mamakin abinda take gani ya fi qarfin ta, waje ta samu ta tsaya, ta na kallon yanda mahaifin ta ya yi lakwas a gaban Lawwali, bai magana ba akan zaman da Lawwali ya yi a gaban shi . "Oga har yanzu fa shiru,yanzu haka mun kawo maganar ne wajen Excelency saboda a bamu taimako" "Mu ma abinda ya kawo mu kenan,na yi iya qoqari na na kasa, ina neman taimako a hukumance, a bido min qauna ta, in ba haka ba,....." Shiru ya yi, ya taune leben bakin shi na qasa, tare da dukan tafin qafar shi da ya dora a saman dayar qafar tashi. "Ah ah Sultana, mik-kawo ki nan?" "Tare muke," "Ban gane tare kuke ba, qaqa an kai kuke tare?" "Dad Mubaraka ce ba a gani ba, kusan sati Uku yanzu, shi ne na rako shi neman taimako wajen ka, amma yanzu na kula is like, ni anka rako, ko wani zai iya min bayani akan abubuwan da nake gani a yanzu?" Da sauri gwamna ya zari wayar shi, ya kira Head quarter na yan sanda, ya fara bada report din batan Mubaraka, Sultana tuni ta manta da tambayar da take yi, ita da Lawwali sun bawa Gwamna hankulan su. Wayar aka bawa Lawwali ya yi kwatancen ta,da bayanin ranar da suka nemeta suka rasa, tare da alqawarin ze tura hotunan ta. Godiya ya miqe sosai ya na wa gwamna, Sultana ma haka. Gwamna na son bin su ya ji dalilin da ya sa suke a tare, kuma ya na son magana da su No 1, dan haka sai da ya bari su Lawwali sun fita, sannan ya qara jaddada musu su yi taka tsantsan ta yanda asirin su ba zai tonu ba, domin in Lawwali ya san sun sace qanwar shi, har shi kan shi ba zai tsira ba, ballantana su. Wannan kalamai sun sake birkita No 4, da kyar yake hadiyar yawu, zufa sai karyo masa take, a sati ukun nan, duk 'yar qibar ma da ya yi, saboda kudin da suke samu, duk ta zabge, ya fita hayyacin shi, ba wani kwanciyar hankali a tattare da shi. Su Sultana kuwa a jikin motar shi, suka tsaya, su na magana, hira ce mai dadi,ta yaushe gamo suke yi, kusan kaso saba'in na hirar dukkan su akan Mubaraka su ke yi, Sultana na son mubaraka, ba wai dan ta na qanwar Lawwali ba,ah ah, yarinyar abar so ce ga duk mai hankali. Shi kuwa a wajen shi Mubaraka ita ce rayuwar shi, a ganin shi ma ba zai taba samun kan Sultana ba in bata nan. Bayan sun yi sallama za su tafi ne Sultana ta ce, "Haka ake sallama da masoyi? " Kallon yanda ta maida kai gefe ta yi, sai ta masa kyau, murmushi ya yi, kadan, wanda rabon shi da murmushi na gaskiya, ba na mugunta ba, tun kafin batan Mubarakan. "Ya ya kamata masoyi ya yi sallama ?" Dan rufe fuskar ta tayi da hannun ta kadan ta ce, "Kamata ya yi ka ce, Sultana na tafi, zan dawo anjima, ina son ki" Bude baki Lawwali ya yi, ya na dariya mai sassanyan sauti, ya ce, "Kaiii ka kaiii ka kaiii, Baraka na ta ce man ke ustaziya ta wallah, ashe ke iya soyayya haka?" Mayafin ta ta ja sosai ta rufe fuska sannan ta ce, "To ai soyayya kowa na yi" "Ok, to sultana Ina son ki," Wani irin dad'i ne ya ziyarce ta, musamman da ta kalle shi ta ga babu wasa a kalaman shi, iyakar gaskiyar shi yake fada, ta ji sautin Muryar shi, ba alamar gatse ko wasa, amayar da ta ta zuciyar ta ce, "Auwal ina son ka, In na ce ina son ka, ba ina nufin ina son ka fiye da yanda kk so na bane, ina nufin ina son ka a kowanne hali, ina son ka ko da wani sabani ya haɗa mu, ina son ka ko da ka na cikin damuwar da ta sa ka nesanta da ni, ina son ka sama da nisan nan da ke tsakanin mu,ina son ka sama da yanda na ke jin zafin rashin ka a rai na, ina son ka sama da dukkan wani abu da zai qoqarin shiga tsakanin mu, ina nufin nafi son ka Auwal" Ya Salam, Lawwali ya gama narkewa,kalaman sultana sun wanke masa wani kaso na baqin cikin da ke ran shi,dama haka take fata, shi ne dalilin da ya sanya ta cire kunya ta furta abinda ke ran ta, sai bayan ta gama kashe masa gabban jikin shi, ta juya da gudu gudu ta shige gida,dan kuwa kunyar shi ba zata bar ta ta tsaya jin me zai ce ba again. Lawwali ya jima a wajen, kafin ya shiga motar shi, ya tada ya bar gidan. Su No 1 kuwa ya na fita suma suka bar gidan, dan zuwa sauyawa  su Mubaraka maboya kamar yanda Gwamna ya bada shawara, da kuma wajen zama. Lawwali har ya isa gida bai dena murmushi ba, ya jima ya na dirzar dattin jikin shi,kafin ya samu abinci ya ci rabon shi da abinci sosai kamar na ranar ba zai iya fadin ga lokacin ba. Ya na kammalawa ya kwanta, dan hutawa. ********************** Vissa ta samu, na tafiyar Isah Saudiya, ana sauran kwana biyu tafiyar Isa,  Hajiya ta sa Isan ya kai mata su Hansatu su gaisa, Hansatu ta sha mamakin jin duk abinda ke faruwa a bakin mahaifiyar ta, ace duk wadannan abubuwan na faruwa bata sani ba? Haka ta dinga yaqe ta na yabawa Isah ,tare da yanka qarya kala kala, dan ta kare shi, yaran ta na ta mamakin qaryar da take ta shinfidawa. Ba daban ta basu tarbiyya mai kyau ba, tabbas da sun tona mata asiri, dan kuwa ba su so ta rufa masa asiri ba. Isah kuwa sai murmushi yake ya na fadin, "In ban muku ba wa zan wa?" Yayan Hansatu ya qara masa dubu hamsin ya qara a kan jarin shi, sai godiya suke ta zabgawa. Da yamma Hajiya ta sa mota ta maida su gida. Tafiyar Isah Makka daiiii sauran kwana biyu, wace zata yi rakiya?????😂 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 28: Kafin tafiyar Isah ya yi qoqarin ajiye musu buhun shinkafa, ya aje musu galan din man gyada da manja, galan daya daya, ya sai masu maggi, wake,barkono, da gishiri, ya sai musu taliya, su omo da sabulun wanka da wanki, rabon Hansatu da ta ga irin wannan kayan a hade waje daya, tun sanda suka yi aure, sai yau, kuka take ta yi, saboda rabuwa da masoyin ta. Hajiya ta mata alqawarin zuwa da ita da yaran da Hajiyan kan ta,ta bata hakuri tare da lallashin ta akan ta bar shi ya tafi domin kasuwancin shi. Yaran Isah kuwa murna suke da tafiyar tashi, har abun ya kasa boyuwa, garin murnar su da surutun da suke ne ya ja hankalin Yabbuga, da ta kasa kunne a cikin gidan, tun sanda ta ga ana shigar da kayan abinci. Dan Jummaa ne ya wurge ta da dan qaramin dutse, ya ce, "Ke hwasa zuwa gidan Kareema? Ina ta magana ke yi shiru" "Bar tahiyar nan, zuwa gobe zan tai, wai shin dole na sai ka kaini? Mu na tahe saman mashin kamar 'yan bangar siyasa, ka yi tahiyar ka na yi tawwa" "In baki hau bayan nawa ba, ai ke hau na wani qato, tau ki sani, walle baki zuwa ko ina in ba ni na zan kai ki ba, zancen banza zancen yohi" Cikin fushi y fice ya bar gidan, Ita kuwa ko a jikin ta, kunnen ta na gidan Isah, so take ta ji kalmar da zata gama da wadda ta qunsa ta haɗa su bata ma'ana amma ta kasa. Tsaki ta ja, ta zari mayafin ta, ta shuri takalman ta ta fice daga gidan ,ko jan qofa bata yi ba. Ko sallama bata yi ba, haka ta afka gidan, karaf kuwa kunnen ta ya ji maganar Ahmad, ya na fadin, in baban su ya tafi Saudiya gobe a gado zai kwana. Wani irin salati ta zabga, tare da tafa hannaye, Hansatu ce ta fito daga daki da gudu, ido ya mata jawur da alama kuka take. "Lahiya? Mi ya hwaru halan? ", "Yanzu ke Hansatu ina ganin ki shiru shiru ashe munahika ta? Ashe ke dauke ni maqiyyiyar ki da baki hwadi min mijin ki zai tahiya Makka, yau Allah ya sa ina da kunnuwan jin dumi, na jiyo daga wajen diyan ki, se qaqa?", Cikin fushin da Hansatu bata san ta na da kalar shi ba ta kalli 'yabbuga ta ce, "To sai qaqa kuwa? Ko ki na hana mai tahiyar na? Yo Ni na ji ikon Allah, komi na se na hwada miki? Tunda muke a matsayin ki na makwacciya ta ke taba zuwa ki tambayen shin na ci abinci Ni da diya na? Ko ke taba zuwa ki tambayen wane na abba lahiya cikin d'iya na ko niya? Haka d'ai ki dora min jidali? Don Allah dai ki barni na ji da abinda ka damu na" Daga 'Yabbuga har yaran sai da mamakin Hansatu ya aure su, budar bakin Amina kuwa sai cewa ta yi, "Kaiiii Umma ke burgeni wallah, dama haka nan zaki zanka yi wa Baba" Wani kallo Hansatu ta mata, wanda ya sanya ta hadiye dariyar ta, suka shige ciki dukan su, "In kin qare jin Isah zai tahiya Makka, sai a tai shiyya a baza" Habaaa nan da nan kuwa 'Yabbuga ta hau bala'i ta na fadin yarinya qanwar bayan ta na kiran ta da munahika, a haka dai ta zare ta bar gidan, cike da borin kunya Hansatu kuwa ta gama hada wa Isah kayan shi kafff a jaka, sabbin dinkunan da yayi, da takalma da duk wani abu da zai buqata su na akwati. Shi kuwa ya gama hada goron shi da duk wani abu da zai buqata, ya daure ya aje, gobe kawai ya ke jira ta yi. Daren ranar Isah ya mori jikin Hansatu kamar ba zai barta ba, Ita kuwa ta ci kuka kamar ba zata bar idanun ta su huta ba, zuciyar ta na matuqar zafi da quna, a duk sanda ta tuna gobe zai tafi, duk ta bi ta qular da Isah, amma ya danne, waya ya dauko aljihun rigar shi, yar qarama, me kyaun fasali, ya miqa mata. Da a da ne ya bata da tayi murna, amma yau ji take kamar ya na bata takardar saki, ji take kamar ta na bankwana da shi na har abada ne, rabon Isah ya lallabata haka tun ta na amarya. Ran Isah fa ya gama ɓaci yanzu, ya na bata waya ta na gani ta qi amsa ta na kuka, tsawa ya daka mata, sai da zanin da take ta share hawayen idanun ta ya kusan subucewa, "Keeee ! Ki na barin kukan iskancin nan ko baki bari? Ban son shashancin banza da wofi za ki karba ko na ajiye aba ta?" Hannu na rawa ta karba, tsabar kuka duhu duhu take gani, amma dole ta shanye shi, da alama ya gama kai wa maqura a hasala, kar kuma ya kai hannu. ************************ Da rana  Hajiya ta aika mota, aka kwashi Isah da su Hansatu sai Sokoto, ta can za su tashi zuwa qasa me tsarki, Hansatu ta sha warning wajen Isah akan kukan da take, ya kuma shiga jikin ta da kyau ya zauna, dan haka ta kama bakin ta ta tsuke, ba abinda take da ya wuce addu'a. Hansatu da yara basu koma gida ba, sai da Isah ya ga magariba ta kusa, shi ne ya ce a maida su, ai kuwa Hansatu me za ta yi in ba kuka ba, cikin jin haushin ta Isah ya ja hanun ta ya tura ta mota, duk ya matse mata hannun dan mugunta, amma bata kula ba. Kudi ya debo a aljihun shi ya qirga dubu goma ya wurga mata, ya wuce abin shi, ba sallamar azziqi. Hansatu kuwa tunda suka dau hanya take kuka, har suka isa gidan ta, Yaran kuwa farin ciki ne danqare a zukatan su, amma ba halin bayyanawa. *********************** Bincike ya tsananta akan neman Mubaraka, hakan ya yi wa Lawwali dad'i, ya kuma kwantar masa da hankali, a qalla dai hukuma ta shiga lamarin, ya na saka ran za a gan ta. Shi ma bai zauna ba, duk inda ya san ya dace ya je dan neman ta, bai gajiya ba, neman ta ya zama masa ibadar shi, tunda dama bai damu da ibadar ba. Kwanan su uku basu hadu da Sultana ba, Ita kuwa ta na son ta dan ja aji ta ga ko zai neme ta, tunda ta gama bayyana masa me ke ran ta game da shi, amma shiru, ba waya ba saqo, ba kuma zuwa da kai. Yau Lawwali a daji ya wuni, idanun shi na kan kowa da komai, ya kula da wani abu guda, wanda ya sanya shi zargin ko dai No 4 ba shi da lafiya, ko kuma ya na boye masa wani sirri, dan haka kiran shi ya sa a je a yi. Lokacin da saqon kiran Lawwali ya riski No 4 ,ya shiga gingimemen tashin hankali, bai san sanda ya furta, "Niiii? Mi an ka ce na yi???" Da qarfi ya fadi hakan, Da mamaki 'yar Aiken ta kalle shi, ta yi tafiyar ta. Jikin shi na rawa zufa na digar masa ya tafi amsa kiran Oga. Ko da ya shiga ya tadda Lawwali na qoqarin neman Network ya na son magana da Sultana. Lawwali bai ko kalle shi ba ballantana ya san halin da yake ciki, cikin Muryar shi ta Oga Lawwali ya ce, "Akwai matsala ne Taheer? Ina nufin gida lafiya suke ba bu matsala? Kwana biyu na ga baka cikin nutsuwar ka" Wani qololo ne ya tokare wuyan No 4, da kyar ya furta, "Ran ka shi dade Oga, diya ta ta ba lahiya, ina buqatar zuwa gida amma ba hali, Kuma kuddin waje na basu isa yin jinya" Lawwali sai a lokacin ya kalle shi , akwai mamaki, wanne irin ciwo ke damun diyar shi da kudin da suke samu a kwanakin nan kamar hauka ba su isar shi? Lawwali bai tsananta bincike ba, ya miqe, ya bude inda yake aje kudi, ya ga babu, ya kai su can gidan shi na cikin gari. "Baka da matsala, in dai kudi na Taheer, kar ka manta, tun ranar da mun ka hwara haduwa, na hwadi maka damuwar ka tauwa ta, ka zanka sanar da ni,mi zan yi da kuddi in ku baku wadata ba? Ka biyo ni gida na anjima mu tai ka amsa, kuma ka zauna wajen iyalin ka har sai sun samu lahiya" Daga kai kawai No 4 ya yi, hawaye na zuba masa,tabbas in ya riqe wannan magana bai sanar da Lawwali ba, ya ci amanar Lawwali, domin shi ne ya jawo shi wannan harkar da suke samu, ya taimaka masa sanda mahaifiyar shi ba lafiya har aka mata dashen qoda,kuma shi ke temaka masa a duk sanda matsala ta iyali ta taso, amma ace a hada baki da shi a na cutar da shi? Gashi in ya sanar da Lawwali sunan shi matacce, in ya bari Lawwali ya gano da kanshi su nan shi matacce, ya zai yi? Jiki ba kwari ya fita, dukkanin abokan aikin shi sun kula da sauyin da ya koma da shi, ciki har da No 1 Dan haka waje ya ja shi, suka bar sansanin nasu gaba daya, su na zuwa qasan wata bishiya No 1 ya finciki No 4 su na fuskantar juna, ya ce, "Ka sanar da oga komai ko?" "Shi ne kai na da naka suke a jikin mu? Kai sake min taguwa ni, in ji da abinda ka damu na," Fizge kan shi ya yi, ya koma baya ya na shafa kan shi, cikin damuwa, da kyar ya furta, "Na yi wa Oga qarya,...Oga ya min taimakon da ba wanda ya taba yi min shi a rayuwa, amma ina ha'intar shi, Oga ya min abinda ku ba ku min ba, yanzu ina cikin tsaka me wuya, in sanar da gaskiya in mutu, in yi shiru ya gano da kan shi in mutu, wa zai kula da ahali na?" "Kai banza na wallah, ka manta kuddin da Excellency yayyi muna alqawari,sun ninka wanda Oga ya taba bamu a rayuwa," "Amma wanda ya taimake ka lokacin da ka ka buqatar taimako ba ya shi a rayuwa" Wata dariyar mugunta No 1 ya yi, sannan ya daki kafadar No 4, ya ce, "In ka na ganin rayuwar ka bata da anhwani dan Allah tai ka sanar da Oga inda qauna tai take" Ya na gama fadar haka ya bar wajen, No 4 kuwa qara ya yi ta saki, ya na kuka, ya rasa ina zai saka ran shi, me ne ne makomar shi in ya sanar da Lawwali? *Ku ba wa No 4 shawara mutan group ya na cikin tsaka mai wuya* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 29: Lamishi ce zaune ta buga uban tagumi, hankalin ta ya fara tashi a 'yan kwana biyun nan, wai a ce dan mutum a neme shi a rasa kamar kwabo a tsakanin barayi? Sallamar qawa kuma aminiyar ta ta ji, wato 'Yabbuga, nisawa ta yi kafin ta amsa, cikin jimami, 'Yabbuga ta ce, "Ohhh ki na nan zaune in da na barki? Hummm Allah dai shi kyauta muna wanga lamari,...dazu ina ta so na tambaye ki, wai an ce jiya da bani nan na tai gidan su Dan jumma, wai diyar gwauna ta zaka? Mi ta zo yi halan?" Cikin sanyin murya Lamishi ta ce, "Ta zo ta ji ko an samu wani labari akan wannan yarinyar, ke san da shike sun saba,ta na son Mubaraka kwarai aran ta, ko jiyan ma sai da tayyi kuka da ni ce har yanzu shiru" "Allahu akbar, rayuwa kenan, za a  gan ta,ni da zuwa nayi ki taimaki wagga farar qahwa tawa ki sa min lalle, amma fa a gida na, dan ka na zaune baka san wa zai fado ba, se de ka ji ana gahwara kayya kayya" (Lawwali) "Mi ki ka nuhi? Gidan namu gidan qauraye na?" Kama bakin ta 'yabbuga ta yi ta ce, "Uhmm uhmmm, ba ki ji wanga batu daga gare ni ba, ki na samin ko ah ah?" "Ban wallah bin ki gida sa lalle, in ki na zama nan na sa miki Lalle tauuu, in baki zama yi ta tahiyar ki" Kyabe baki 'Yabbuga ta yi ta zauna, lokacin azahar ya yi, madadin su bari su fara sallah, sai suka yi kamar basu ji ma kiran sallah da ake ba,kwaba lallen Lamishi ta yi, Yabbuga na ta uban surutu, rabin surutun zagin Mai Buruji ne, dan ma Lamishi na taka mata burki, ta kan ce, ta tsani me zagin kishiyar ta, domin watarana zai zage ta ita ma. "Ni hwa ban ga lallen ga na kamu ba" inji Lamishi, Yabbuga tace, "Ke dai bari shi yi awa guda ki na ganin yanda zai yi kyawu kwarai" Su na tsaka da saka lalle Mai Buruji ta dawo daga aiki, ga lalle an qunshe wa 'Yabbuga hannu da qafa da shi, ko da Mai Buruji ta dakko kwanukan cin abinci yawu ya fara ambaliya a bakin 'yabbuga, ta ji haushi saka lallan nan a hannu, da ta sani da a qafa kawai aka saka mata. Ko da aka raba aka zo cin abinci sau biyu Mai Buruji ta bawa 'yabbuga a baki, suka yi ta cin abin su suna hira, Lamishi ta ce Allah shi kiyashe ta bawa qatuwa abinci a baki. Ran 'Yabbuga in ya yi dubu ya ɓaci, ta kame bakin nan ta gume shi gum, a haka gyangyadi ya dinga dibar ta. ************************ Shigar su gidan Lawwali ke da wuya, ya qirga kudi dubu dari biyar ya bawa No 4, No 4 kuwa cikin dakiya, da danne abinda ke ran shi,ya dinga murnar dole ya amsa ya na godiya. Lawwali na ta kallon shi, kallon da Lawwali ke masa ne ya fara shiga kowanne lungu da saqo na jikin shi,cikin hanzari ya fara qoqarin tafiya, Lawwali kuwa zama ya yi a daya daga kujerun da suka zagaye madaidaicin parlourn , ya dora qafar shi daya saman daya,No 4 na kallon zaman da Lawwali ya yi, ya tabbatar ba lafiya, cikin sarqewar murya ya ce, "Oga na tafi..se..se..see da swahe," Hannu kawai Lawwali ya daga masa, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, qafafun No 4 na rawa ya nufi bakin qofar, ko da ya murda ya ji ta a rufe, juyawa ya yi ya ga Lawwali na kallon yatsun hannun shi, sake jan qofar ya yi, ya ji ta gam, cikin tsananin tashin hankali ya juya tare da zubewa a wajen,ya sake jakar kud'in a qasa ya na kuka, zufa da hawayen shi duk sun hade waje daya. "Oga don Allah ka yi min rai, ka rufa min asiri ina da iyali, ka sani, ka san mahaifiya ta, ka ɗauke ta awat-taka,Oga ina da niyyar sanar da kai tsoro nika ji kar ka kashe ni, ina da qananan yara ka sani, har takwara na yi ma oga" Har gaban Lawwali ya isa ya kama qafar shi ya na kuka ya na bashi hakuri, wani irin naushi Lawwali ya kai mishi sai da jini ya yi tsartuwa a qasa, bakin No 4 ya fashe. Kasa ihun ma ya yi, dan ya san ya cancanci sama da haka ma, idanun Lawwali ba bu mai fatan ya gan su a wannan lokacin. "Taheer ni zaka ci wa amana? aza ka ke bani ganewa? To na ji duk abinda kun ka ce kai da wancan qaramin dan iskan, ina kun ka kai min qauna ta?" "Oga na san inda suke zan kai ka da kai na, Oga ka yahe min, ba da son rai na ba an ka ɗauke ta, ba ita mun ka tai dauka ba, qawar ta mun ka tai dauka, sun ruhe fuska bamu san da ita ciki ba" "Yi min shuuu ! Munahikin banza, ka na jin har akwai wata sauran yarda a tsakanin mu? Ba bu yarda tsakani na da kai, maza ka gaggauta kai ni ga qauna ta, sai dai zai zama siri tsakanin mu, kamar yanda gwauna da wancan shegen basu son na sani, ban yarda ka sanar da kowa ba,in kuma ka sake cin amana ta a karo na biyu, zan kashe ka, zan kashe uwar ka, dan ba uwa ta ta ba, zan kashe matar ka da diyan ka," "Oga ko na hwarko ma tsautsayi na wallah ban koma cin amanar ka, Nagode  oga na go..." "Dalla miqe ka je ka kai ni ga qauna ta" Jiki na rawa No 4 ya miqe, a bakin kofa ya tsaya ya na jiran Lawwali ya bude qofar shi, sai da ya dauki makullin mota, ya lodawa bindigar shi harsashi sannan suka fita suka bar gidan. Kafin su isa magriba ta gabata sosai, bai fi awa daya a kira ba, su na zuwa No 4 ya bawa Lawwali shawara su aje mota a nesa su qarasa da qafa, haka kuwa aka yi, sun isa qofar gidan, suka tarar an kulle da kwado, No 4 ne ya zari makulli a aljihun shi zai bude qofar, bai ankara ba ya ji an dafe qeyar shi da duka, "Dan iska, makullin ruhe qauna ta na hannun ka, amma kullum muke haduwa baka taba hwadi min ba" Su na shiga su ka ji gidan shiru kamar ba kowa, dakin da aka ajiye yaran suka shiga, ko da suka je sai ba su ga Mubaraka ba, sai su Murjanatu, tambayar su Lawwali ya yi ina take, cikin kuka Saliha ta ce, "Wannan d'ayan mugun ya dauke ta, kullum in ya zo sai ya dauke ta ya hita da ita, daga baya sai ya dawo da ita, ta na kuka" Wani irin ashar Lawwali ya saki,lallai in abinda yake zargi No 1 ya yi da Barakan shi,tabbas a yau dinnan zai kashe shi. A guje Lawwali ya kama hanya zai fita daga gidan, No 4 ya yi maza ya kulle ko ina ya bi bayan shi da mugun gudu,shan gaban shi ya yi ya na haki, wani naushi Lawwali ya kai mishi a ciki, sai da ya duqa "Oga ka san mutanen ga basu da dad'i, na sani Gwauna da kai ya ke taqama a duniyar siyasa,amma ba a cin munahuki da yaqin gaba da gaba, shi ma ka hito mai ta inda bai zata ba, babbar nasarar da an ka samu shi na ka san wanda ya dau qanwar ka," Tabbas maganar No4 gaskiya ce, to ta yaya zai rama abinda gwamna ya masa? Kan shi cike da tunani ya shige mota, ya bar No4 a wajen, No4 komawa ya yi, ya gargad'i su Murjanatu, akan kar su kuskura su sanar da zuwan su, da yayan Mubaraka, su na sanar wa za a kashe su nan take. Tsoro ya kama su, dan haka sun yi alqawarin ba za su fad'a wa kowa ba, har ita kan ta mubaraka din. ************************ 'Yabbuga bata farka daga baccin da ya kwashe ta ba sai da ta ji qarar bude qofar gidan da qarfi, a kidime ta farka ta na fadin, "Wayyoo Allah mun shiga uku, mi ya hwaru, ake bude gambu kamar ana girgizar qasa?" "Me ki ke yi a gidan nan a wanan lokacin," Bude baki 'yabbuga ta yi iya qarfin ta takurma ihu, marin kan ta tayi, wai ko za ta tashi, wataqila a baccin wahalar da ya dauke ta ne ta ke ganin shi a idanun ta. Qafa ya sa ya kwashe kujerar da ta dora qafafun ta ya yi wurgi da kujerar, kafin ya qara kaiwa d'aya kujerar duka 'yabbuga ta miqe, ta taka qafafun ta biyu a qasa, ta diba waje a guje, tsantsin ledar na diban ta, kai ba ko dan kwali, gashi duk ya tuttuje haka ta isa gida. Dan jumma na ta gyara ma'ajiyar abincin su da awaki suka shiga suka yi wa barna, gani ya yi ta afka gidan ba ko sallama, zani qanqame a hannun ta, kai ba dankwali, duk Leda a qafar ta, tsoro da tashin hankali ne suka rufe Dan Jumma, dan a tunanin shi ko masu kidnapping ne suka dauke ta ta gudo, tunda yanzu abun qara yawa yake. "Daga ina ki ke? Wa ya biyo ki? Masu kidnapping na halan?" "Wanga ya ci uwar masu kilnapim, ni da gidan Dan Talo har abada,tunda ba aljanna aka rabo a gidan ba," Wani irin tsaki Dan jumma ya saki, sannan ya kalle ta ya ce, "Dama can ki ka tahi na shigo na tadda bisashe (awaki) sun canye min kayan abinci? Ni da na gan ki a hirgice ma aza nikai ko sace ki an kai ki ka gudo, tunda na san ki da gudun ceton rai" Kar kacewa ta yi rai bace ta ce, "To mi ka ka nuhi? Wanga ba gudun ceton rai na ba halan, ka ga wadda Yaron nan ya shigo? Ka ga wadda ya dinga fatali da kujeru? Da na tsaya mi ka ka tunanin ze min? Dan Jumma na kula baka san hatsarin yaron can ba ne, Allah shi gama ku watarana" Cikin sauri Dan Jumma ya ce, "Ba Amin ba 'yanneman me mugun hwata," Haka sukai ta kace nace a tsakanin su, har ya gaji da hayaniya da ita ya bar gidan. Can gidan su Dan Talo kuwa Lawwali na can na musu ta'adin da ya saba, daki guda su Mai Buruji suka shige, su na ta bashi hakuri, amma bai kula su ba, sai da ya gama musu ta'adin da ya so, sannan ya shiga dakin Mubaraka ya kwanta a katifar ta, hawaye ne ke bin gefen fuskar shi masu dumin gaske, da a so samun shi ne yanzu ya samu ya ɗan hahharbe ko da mutum biyar ne, amma dole zai yi hakuri ya bi shawarar Taheer, zai dauki fansa ta inda gwamna bai zata ba. Ya na nan kwance har daya na dare, can dakin kuwa sun san bai fita ba, dan basu ji motsin shi ba, ga fitsari ya matsi Lamishi, Mai buruji ce ta ce, "Yaya kar ki yi min boli (fitsari) ga daki, ke hwa uwar shi ta, ki tai ki bolin ki ki dawo,ko ki tai dakin ki" Wani mugun kallo Lamishi ta sakarwa Mai Buruji, bata ce komai ba, se kwafa da ta yi, tare da sake leqawa, cikin ran ta ta na fadin, 'Ya jima da yin niyyar ajali na, ina hita a wannan halin da yake ciki, sai ya cika alqwani nai wallah' Lawwali na nan kwance wani tunani ya fado masa, kamar wanda aka mintsina haka ya miqe, ya na murmushi, cikin wata iriyar murya Lawwali ya furta, "RAN KI SHI DADE MASOYIYA SULTANA, MASOYIN KI AUWAL NA TAHE" *HUMMMM LAWWALI KAR KA DAU FANSA AKAN SOYAYYAR GASKIYA PLSS😭😭😭😭* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 30: "Alhamdu lilLAAH, a qallah Yah Auwal ya san inda nike da ma shi d'ai na damuwa ta, na san shi d'ai na zai shiga matsanancin tashin hankali akan rashi na, a wajen iyaye na kamar dashen iccen juji ni ke, wanda ya fito ga jeji a kuskure, zai gama rayuwa tai ya mace ba tare da sanin kowa ba," Idanun ta abushe take wannan maganar babu digon hawaye cikin su, sai tsantsar quna da suya da zuciyar ta ke yi, gaskiya ta fad'i, ko ta na raye ko bata raye ta san iyayen ta ba damuwa za su yi ba, wataqiila qannen ta su Jameelu su damu da rashin ta, amma mahaifin ta da in ya fice ma ba ganin shi ake ba sai zai ci abinci, be bawa Kowa abinci ba, amma ya na tsammanin komawa shi a ciyar da shi,babban aikin shi bai wuce zaman majalisa, da bin bangon gidajen abokan da suka ci abinci qofar gidan shi, shi ma ya ci nasu ya kade riga y koma majalisa. Lamishi kuwa jin gulmar ta da zuwa aikin ta, sun fi mata komai mahimmanci, ta na iya fita daga gidan da safe ta je aiki, ta dawo ta yi baccin awa daya ta fice gulma sai magariba ta dawo, duk abinda Mubaraka ta yi mai kyau ko mara kyau a matsayin fad'a ne, har nemo laifin ta take. Mai Buruji kuwa sama sama ne, to iyayen da suka haife ka ma sun yar da kai balle wani? Sai wanda Allah ya taimaka ne yake samun masu yi masa kara su kula da shi . Yah Auwal, Yah Auwal shi ne rayuwar Mubaraka, shi ne ruhi da numfashin ta, tun da aka sace ta ba ranar da za ta zo ta wuce bata wuni ta kwana kuka ba sai ranar da ta samu labarin zuwan shi, kullum a cikin damuwa da tashin hankali take, ta yi zazzabin ta yi ciwon, amma a banza, bata taɓa sanin ta na da jinnu ba sai a wannan wajen, ta tada su, har sun gaji sun lafa da kan su. Murjanatu ce ta kalli Saliha ta ce, "Yanzu daga tahiya ta yauce (toilet) har kin hwadi mata? Sai da an kace kar mu hwadi mata, yanzu ki na ganin rage damuwar da za ta yi ba zai sa su fahimci wani abu ba? Mun rusawa Yayan ta shirin da ya ke son yi kenan hwa, ke wai mis-sa ba ki iya riqe siri ne a ga rayuwar ki? Mtwss" Murmushi mai ciwo mubaraka ta yi, sannan ta dauke idanun ta daga kallon waje dayan da ta yi ta zuba su akan Murjanatu ta ce, "Kwantar da hankalin ki,ni a yanda nake dinnan ba zan taba komawa gida ba, ba zan bari Yah Auwal ya maida ni gida ba, abun kunya ne na koma gida a haka, amma ku? Ku za ku iya komawa gida, ina me baku hakuri, domin na san ni ta suka son dauka sun ka haɗa da ku,amma na sani, na san yayana ba zai taba hutawa ba sai ya his-she mu daga nan, inshaa Allahu ku na barin wajen ga" Cikin kuka Suhaila ta ce, "Mi ki ke nuhi? Ke dai san ba mu barin wajen ga in ba ke ko? Ko yayan ki ba na jin zai yarda ya his-she mu nan wajen ba bu ke a cikin mu," Shiru Mubaraka ta yi bata sake magana ba, amma ta san abu d'aya dole ya faru, za su tafi ba tare da ita ba, bata ga amfanin komawa gida ba, dama can ita GANTALALLIYA ce kamar yanda MAHAIFIYAR TA ke fadi kullum ba fashi . ************************ Da misalin takwas na safiyar litinin, Auwal ne ke tsaye a jikin motar Sultana, ya gama goge ta tass, sai sheqi take, gyara hannun rigar shi ya ke yi, ya na nannade shi sama, Sultana ce ta fito sanye da gilashi a idanun ta, fuskar nan kamar hadari, ta hade ta gam gam, ba alamar walwala, ko fara'ar nan ta ta, ba wani alamar nishadi, ko farin ciki, ga rama  ta yi ainun har ba ta boyuwa, hatta da doguwar rigar da ta saka sai da ta nuna alamar ta mata yawa. Kanta a qasa ta fito, Sultan na biye da ita da mug din tea a hannu, roqon ta ya ke ta sha ko da tea din ne amma taqi, qarshe ma fad'a ta fara yi, kwata kwata hakan ba halin ta bane, Sultan bai ji zafin fad'an ta ba, sai ma tausayi, kama ta ya yi ya rungume, jin ta a jikin shi ne ya sanya ta jin wani abu a maqoshin ta mai ciwo, ya tokare ta, ta na son fidda abun, amma ta gaji da fitar da shi kullum, meye laifin ta? Meye laifi dan ka so driver din ka? Hajiya ta tsaya tsayin daka akan ba ita ba Auwal, kar ta sake ganin wani abu mai kama da soyayya a tsakanin su, daina zuwan shi ba qaramin dad'i ya wa Hajiya ba, Daddy ne kaɗai ya damu, saboda tsaron lafiyar ta, sai Sultan, jin ta take ita da watan da ke sama ba su da bam-bamci, domin kuwa shi ya na kewaye da taurari ko ta ina, amma still shi kadai ne, ita ma ta na tare da su Sultan da Daddyn ta, amma jin ta take kamar bata da kowa a duniya, mutum d'aya da ya mallaki zuciyar ta ya mata nisa. Da sauri ta d'ago kan ta a lokacin da ta ji Dadyn ta da wanda ta ke tsananin kewa da son gani su na magana, kamar jiri ze debe ta, Sultan ya yi sauri ya tare ta. Leqa bayan Sultan ta yi, dan tabbatar da abinda kunnen ta ya ke jiyo mata, "....DPO ni ma ya kiren jiya, ya min bayanin da ya yi min dad'i, ya ce ana ta bincike, kuma su na ganin akwai alamun nasara, ana samun ta inshaa Allahu, shi na ma ya sa na ji hankali na ya ɗan kwanta" "Da kyau, na yi ma alqawarin ana ganin ta, nan ba da jimawa ba, ka d'ai kwantar da hankalin ka" Wani kallo ya wa Gwamna, wanda duk sa idon mutum ba zai iya fassara shi ba, murmushi ya saki mai sauti, irin wanda ya san ya na rikita sultana ,tabbas kuwa ya samu nasarar tarwatsa zuciyar ta in to thousad pieces, wasu hawayen farin cikin ganin shi ne ke gudu a kuncin ta, tabbas shi ne ba mafarki bane, ta na jingina jikin Sultan Daddyn su ya daga mata hannu, ya shige ciki, Lawwali kuwa cikin tafiyar shi mai dauke hankalin duk wani mai kallon shi,ya ke takawa zuwa inda suke,rigar Sultan sultana ta qanqame ta baya, hannun ta na rawa, wannan wanne irin so take wa Auwal? Ko da ya isa gaban su, dan duqar da kai ya yi, ya sanya hannun shi daya a qirji, daya a bayan shi, ya ce, "Barkan ku da swahiya ran ku shi dade" A hankali ya d'aga idanun shi cikin salon sace zuciya ya kalli Sultana, kashe mata ido d'aya ya yi, kamar yanda ya saba, wani numfashi ta ja, sannan ta hau qiqqifta idanun ta, dariya ta sake mai sauti, tare da hawaye,hannayen ta duka biyun ta d'ora a saman bakin ta, a hankali ta zare gilashin ta ta na goge hawayen idon ta,cikin dakiya ta ce, "Ka gama naka saura nawa, mu je ka kai ni office ina da abun yi" Cikin murmushi mai sauti Lawwali ya ce, "Dan Allah in za a hukunta ni a duba halin da nake ciki a min adalci, ina mai bada hakuri akan duk abinda na aikata, ni ma ba da so na bane, a duk inda na shiga ruhi na, hankali na, zuciya ta, su na tunanin ki, su na jin zogin rashin ki, amma qauna ta ban san halin da take ciki ba har yanzu, yanzu ma na kasa jure rashin ki na yas-sa na dawo gare ki Ran ki shi dade" Gaba dayan su ya basu tausayi, Sultan ne ya taka ya isa gaban shi, cikin jimanta rashin mubaraka ya ce, "Tabbas dole ka shiga tashin hankali da damuwa, mu kam mu hankalin mu ba a kwance yake ba da batan kamilar yarinya kamar Mubaraka, ballantana kai, Allah ya bayyana ta cikin aminci, kuma na san sultana ma ta yahe maka," Har zai tafi ya juya ya sanya fuskar Babban yaya, ya ce, "Ga amanar qauna ta nan, kar na ji kar na gani, duk ta sake kuka akan ka, za ka gamu da ni" Dan duqar da kai Lawwali ya yi cikin girmamawa ya na murmushi ya ce, "Ran ka shi dade ba ko ka sake ganin hawaye a wannan kyakkyawan idanun mai haske kamar hasken rana idan ta hito" Wata iriyar kunya ce ta kama sultana, ta yi matuqar kewar wadannan kyawawa kuma dad'ad'an kalaman daga wajen kyakkyawan masoyi Auwal. A tare suke takawa wajen motar, banda murmushi ba abinda suke yi. Bude mata motar ya yi ya ɗan duqar da kai, dan tura baki ta yi, sannan ta ce, "Na kula da wani sabon salo ka dawo, na ce ka dai na ce min 'Ran ki shi dad'e' ka kira ni da Sultana, ka qi, yanzu kuma wani sabon salo ka zo da shi na duqawa ko?" Cikin murmushin shi mai sauti ya ce, "Duk inda mai girma da daraja shike dole na a bashi girma nai, duk inda kyakkyawa take dole ne a girmama kyaun ta" 'Wayyooo zuciya ta, Auwal na so ya hwashe ki da kalaman shi' abinda sultana ta fada kenan a ran ta. A zahiri kuwa kad'a kai kawai ta yi, ta maida qafafun ta cikin motar ya rufe, bayan ya zauna ya daidaita komai, ya kunna motar, d'aga kai ya yi, ya kalle ta ta madubi, shi kawai ta zubawa ido, kamar wanda zai gudu ta dena ganin shi. "Ran ki shi dade Lawwali ne dai ba wani ba, in ki na min irin kallon ga za ki sa mu hwada rami," Kashe mata ido daya ya yi, tare da murmusawa ta gefen baki, Sultana ji ta yi kamar ta narke daga cikin jiki, da zuciyar ta,amma a zahiri dauke kai kawai ta yi ta maida gilashin ta sannan ta ce, "In kai ma ka gama kallon nawa zamu iya tahiya yanzu" Dariya ya yi sosai, sannan ya ja motar suka bar gidan. Labulen dakin ta saki, tare da kallon Gwamna Halliru ta ce, "Daddyn Sultan ka ga abinda nake ta hwada maka ka qi yarda ko? In baka d'auke yaron ga daga gidan nan ba, to ina mai tabbatar maka da sai an kawo maka shi a matsayin suruki watarana" "Ke hwa in ki ka tsani mutum ruwa in ya taka sai ki ce ya tada qura, yanzu mi na na ki ka hwadi hakan ga? Ke San dai Sultana yarinya ce mai son mutane, halin ta ne kunya da fara'a, ko dan ki na nan huska awat-ta tamacen alade ba a gane dariya ko hushin ki, shi kenan yarinya ba zata yi hwara'a ba, a waje ma yi wa wasu takai ballantana yaron da ka tuqa ta" Har cikin ran shi ya fi aminta da Lawwali Ya kusanci Sultana sama da kowa, amma shi ya rusa amincin da Lawwali ya bashi, da martabar da yake ganin shi da ita a ran shi. Tsaki ya ja ya bar jikin windown da tun da lawwali ya budewa Sultana mota suke tsaye su na kallon su. Hajiya Ikee ta qulu ta kai bango, alwashi ta ci a cikin ran ta, ba wanda ya isa ya hana ta korar Lawwali a gidan nan, dan kuwa bata haifar wa driver diya ba, Sultana matar manya ce, manyan ma na qololuwa,sabon shugaban qasa da suke saka ran ya ci zabe ta ke wa tanadin Sultana, Dan haka bata ga dalilin da zai sa driver ya shiga tsakanin burin ta ba, last week ta gama tallata sultana a wajen dan takarar shugaban qasar tasu, a lokacin da suka kai masa ziyara garin su, gaba daya ahalin, shi ne ake so a mata sagegeduwa, to ba zai yu ba. ************************ A wajen aiki ma, yau sun shaida sultana na cike da farin ciki, dan haka wajen ya zama a raye da farin ciki da nishadi, ba tare da sanin Sultana ba, Lawwali ya zari jiki, ya bar wajen, bai zame ko ina ba, sai maboyar da aka kai su Mubaraka, copy din makullin gidan da Taheer ya bashi ya dauka,duk wani abu da ya kamata ya sani Taheer ya sanar da shi, a daidai wannan lokacin su na can sansanin su, sai da rana d'aya daga cikin su ke zuwa a basu abinci. Sai kuma da dare nan ma wanin su ko su duka za su kai masu abinci, da sassafe kuma No 4 aikin shi ne zuwa ya kai masu na safe, ya kuma tabbatar da ba abinda suke buqata. A tsakiyar parlour ya tsaya ya na jiyo karatun qur'anin Mubaraka, zuciyar shi ta yi matuqar karyewa, musamman da ya ji ta na kuka dan bai san ma'anar abinda take karantawa ba, ballantana ya san ayar ce ta sanya ta kuka, saboda kwadayin rahamar Allah. A tunanin shi kuka take saboda ta na cikin matsala. Takawa ya yi cikin sanda,ya leqa ta bulin key din, zaune ya hango ta saman carpet din sallah, sai qawayen ta a saman gado, su na sauraran karatun ta. Dan kuwa ba bacci suke ba, idanun su biyu. Hannu ya sanya zai murda qofar,sai ya tuna bai karbi key din dakin ba, saboda ba ya so su san ya na zuwa duba su, har lokacin da ya daukar wa kan shi kubutar da su, ba dan an fi qarfin shi ba, sai dan shi ma ya na son ya rama abinda aka masa. Yanda Lawwali ke jin kan shi, ba kusa bane, ji yake duk qasar nan ba mai iya karawa da shi, ya na jin ba abinda ya ke son yi wanda ba zai iya shi ba, sai dai in be so ba. Cikin sanda ya bar gidan ,garin ya fita ya yar da gorar ruwa, wadda aka sha aka rage, ba a rufe bakin ba sosai . Da sauri ya qarasa fita ya bar gidan, ya kulle, inda ya aje motar shi ya nufa, ya shiga, har zai tada ta, ya ga No 1 ya tunkari gidan daga can nesa, a motar shi, kallon agogo ya yi, ya ga ai yanzu ba lokacin ba su abinci bane, me ya kawo shi? Dube dube ya ga No 1 na yi, sannan ya bude gidan ya fada. Lawwali ne ya bude qofar cikin tsananin fushi, ya sanya hannun shi a bayan rigar shi ya zaro 'yar qaramar bindigar shi, ya riqe, idon shi ya rufe, tsabar fushi da tashin hankalin da ya ke ciki, gidan ya nufa a fusace....................... *Hummmm Ni kuma anan na ji naaaaa gaji zan huuuutaaa😅😉😝😝* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 31: A guje Lawwali ya ke bin hanyar da za ta sada shi da gidan, kafin ya isa No 1 ya rufe qofar, har zai saka key ya bude wani tinani ya zo masa, cikin ran shi ya ke fadin. 'Haba Lawwali, ai bai kamata ka kashe wannan qaramin dan iska cikin sauqi ba, ka yi mishi kisan nan dai da ka yi niyya tun da can, ka bawa zuciyar ka hankuri, komai na da lokaci nai' Da sauri ya bar wajen, ya nufi motar shi, dan ba ya son ya ga me No 1 ze aikata a gaba, gashi lokacin tashin Sultana na ta gabatowa, wataqila ma ya na isa time ya yi, a dayan bangaren ma ba zai so rusa plan din shi ba na wajen Sultanan, dole ya na ji ya na gani ya hakura. Ya na tafe ya na sauke wani irin numfashi,kamar wani mayunwacin zaki, duk wanda ya san wane ne asalin Lawwali, a wannan lokacin is not a good idea ka bata masa rai, dan yanzu zai ma lahira sabon baqo da mutum. Gudun da yake zubawa har ya wuce misali, wataqila da a qasashen turawa ne da tuni an tsaida shi . Birkin da ya ci ne ya janyo hankalin mutanen da ke wajen, cikin su har da sultana, da ke saka hannu a wata takardar da za a fitar da buhunan shinkafa domin mabuqata. Ta na kallon idon shi ta ji wani irin yanayi da bata taba ji ba game da Lawwali, wato tsoro,sai dai ta bangaren Lawwali, su na hada ido sai ya ji bacin rai da baqin cikin shi ya ɗan ragu, har murmushi ya ɗan yi mata. Ganin murmushin shi ne ya sanya ta sakin nata, ta kawar da tsoron da ke ran ta, amma tabbas fuskar da Lawwali ya sanya a baya, bata fatan sake ganin irin ta har gaban abada. Kafin ta zo ya bude mata qofar,ta na shiga ya mayar ya rufe da qarfi,sai da ta ɗan razana, shi din ma da qarfi ya shiga ,ya kuma rufe da qarfin, cikin sauri ya tada motar dan ya na buqatar leqa sansanin su, ya ɗan huce haushin shin shi a can. Ba tare da ta yi wani tunani ba ta miqa hannun ta zuwa kafadar shi, a hankali ta shafa saman rigar tashi kafin ta matsa kafadar tashi sannu a hankali, wata iriyar ajiyar zuciya lawwali ya sauke mai qarfin gaske, tare da gangarawa gefen hanyar ya tsaida motar, kifa kan shi ya yi a jikin sitiyarin motar, ya na sauke numfashi, quncin da ke cikin zuciyar shi ba shi da misali, ya na ji ya na gani qanwar shi take a wulaqance, kafin ya gano ta ya zaci ba tashin hankalin da ya fi rasa ta da ya yi, amma yanzu ji yake wannan tashin hankalin ya fi na rasa ta da ya yi, shi ba qarfin shi aka fi ba, ba komai ba, amma ya ke azabtuwa. Bai san sanda ta zauna a gefen shi ba, sai jin hannun ta ya yi a saman qeyar shi ta na shafawa a hankali, idanun ta na zubar da hawayen tausayin masoyin nata, ta san duk damuwar shi ba ta wuce ta rashin Mubaraka ba. A hankali ya daga kai suka kalli juna, gaban ta ne ya yi wani mummunan faduwa, Lawwali kamar ba shi ba, fuskar shi ta yi jawur, idanun shi ma haka, ga wani dagawa da komawa da qirjin shi ke yi, cikin sauri ta zame hannun ta, ta sunkuyar da kan ta qasa, ba za ta iya jurar kallon shi ba. Muryar shi na rawa, ya ce, "Sultana....qauna ta a duk inda take ta na buqata ta, ina ji a jiki na, ta na cikin matsala," Tsigar jikin ta gaba daya ta miqe, sakamakon kiran sunan ta da ya yi, bata taɓa zaton bayan iyayen ta da suka saka mata suna sultana ba, akwai wanda ya iya fadin sunan ya yi daɗin saurara kamar Lawwali ba, ga wani matsanancin tausayin shi da ke addabar zuciyar ta, cike da raunin murya ta ce, "Allah na tare da ita ko ba ka nan, zai kula da lamarin ta, baka cutar da d'an kowa ba, kai ma ba za a cutar da taka qaunar ba" Da sauri ya kalle ta, sannan ya ce, "In kuma na cutar da wani fa? Sai a cutar da tawa qaunar ki ka nuhi?" Yanayin yanda ya yi maganar ya sa ta jin kalaman ta ba su yi dadin saurara ba a kunnuwan shi, cikin sauri ta ce, "Nooo ba haka ni ka nuhi ba, mu je gida mu sake wa Daddy magana, Ni kai na na damu da rashin Mubaraka," Cikin kauda maganar, dan gujewa bacin ran da ta hango kwance a fuskar shi, ita abun ma ya fara bata tsoro, ba ta taba ganin wanan Auwal din ba. Ba tare da ta koma baya ba suka tafi, har suka isa ba wanda ya sake magana, ta so kunna ko da rediyo ne dan kawar da shirun amma gaba daya bata ga fuska ba, ita da motar ta, ta najin tsoron driver,zuciyar ta ce ta mata tuni da cewar, 'Shi din ba wai drivern ki bane kadai,ya riqi babban matsayi a zuciyar ki Sultana, matsayin da babu wani mahaluki da ya taba riqe irin shi, a kaff tarihin rayuwar ki, shi ne namiji na farko da ki ka fara yi wa so irin na soyayya, kuma shi ne namijin da ki ke ganin za ki qarasa rayuwar ki da shi, har abada' Ji ta yi motar ta daina tafiya, ko da ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga sai ta gan su a cikin gidan su, baya ta leqa dan ta tabbata ma'aikatan gidan na ta gaishe ta ma bata kula ba. A tsaye yake a jikin qofar ya bude mata, ita kawai yake jira ta fita ya kama gaban shi, da yau har ita din ma haushi take bashi,in ba ganin shi ya yi a daji ya na ragargazar mutane ba ba zai ji dadi ba. "Ran ki shi dade, mun iso" Cikin yanayi na jin kunyar ya kama ta ta na kallon shi, ta fita, ya rufe, baya ta bude ta dau jakar ta, da wayar ta, duk ya na tsaye, "Dan Allah ka kwantar da hankalin ka, duk da na san abu ne mai wahala, amma ka jaraba karanta hasbunallahu, wa ni'imal wakeel, inshaa Allahu komai zai yi daidai, za a gan ta," Daga mata kai kawai ya yi da fake murmushi, Wanda ta san fake ne, amma ita sai ta mayar masa da kyakkyawa kuma mai kwantar da hankalin,amma ba irin hankalin Lawwali ba, dan kuwa ya dai ji dad'in ganin murmushin nata, amma bai rage masa rad'ad'in da yake ji ba a ran shi. Ya na qoqarin tafiya Mai Buruji na qoqarin fita itama, su na hada ido ta gigice ta yi baya a guje, ta koma bangaren masu aiki,ba ita ta bar gidan ba sai ana kiran la'asar. ************************ Gidan ya yi wa Lamishi shiru yau, ba wanda ya je mata jajen ma da ake dan yi, ga qawar ta tun jiya da ta keta da gudu, har yau bata dawo ba, ga Mai Buruji bata koma ba, shi kuma wannan lalataccen mijin nasu dan wahala sai zarya da sintiri yake kamar dan agaji, da aikin agajin ma yake da al'umma ta amfana da shi. Shigowar shi ta biyar kenan, cikin dan had'e fuska ya ce, "Ke ga wannan lalatacciyar bata dawo ba ko? Tunda kin ka bar zuwa ta samu wajen tafiya yawon shashancin ta, sai ta ga dama ta ka dawowa gidan ga" "Kar ka kuskura ka zage ta, yo akwai lalatacce da ya wuce ka? Baka nema ba, ba ka bada jallin nema ba, amma ka ishi mutane da dumin banza, kai ba ka damu da jimawar da tayyi ba, amma ka damu da rashin dawowar ta dan ka ci abinci kai da lalatattun abukkan ka, Ni ka ga tahiya ta ma gidan 'Yabbuga, in ta zaka kace ina can" Yaqe baki ya fara ya na mata kirari na uwar gida, ita kuma ta tsuke fuska gam, ta yafa mayafi ta bar gidan. Zaune ta tarar da 'Yabbuga a saman turmi, ta kasa kunnuwan ta gidan Isah ta ji me suke ciki, Lamishi na ganin haka, ta kwashe da dariya ta rafka gud'a, sannan ta ce, "Ahayyyeeee, Allah gani, in ji gurmuwa (gurguwa) gulma ajali, in ba ai ba a mutu,ki na nan zaune ke d'ai ga gida ba ki hitowa a sha hira? Ke tsaya kasa kunne shigifar (katanga) maqota," Hannu 'Yabbuga ta sa a baki ta na ma Lamishi nuni da ta yi shiru, jan hannun ta tayi, suka bar wajen, suka zauna a bakin qofar parlourn 'Yabbugan, Lamishi ce ta kalli 'Yabbuga hannu da qafa, ta ga bata ga komai ba, cikin rashin fahimta ta ce, "Shin ina lallen da nis-sa miki jiya?" Tsaki 'Yabbuga ta ja mai qarfi, sannan ta tura dankwalin ta gaban goshi ta na sosa cinyayyar qeyar ta, "Ina ko kigganai? Lalle dai ba lalle na ba, miyak-kad'i ta wallah (kuka)" (Lalle dai ba lalle bane kuka ce wallah) "Miiii? Wanne irin miyak-kad'i?" Fari 'Yabbuga ta yi, kamar wata 'yar daudu ta ce, "Miyak-kadi dai da kis-sani, ita mun ka kwaba, mun ka daura, niyyi awa da wanni zaune ina sharar bacci wahala, nic-ci gudun wahalar banza akan lallen ga na banza, dan da ban kai wannan lokacin gidan ku ba da ban hadu da qanin shedan din can ba, ya hirgita ni, duba, duba, nace duba nan ki gani" Wani shafcecen yanka ne a sharabar ta, kamar ta ji shi da icce ko langa langa, "Ke ga yanda na here qahwa, ban ci lalle ba na ci gudu, dake jikin tallaka na ko jin yankan ban ba sai dazu da zan wanka da rana nijji zahi, nicce too Allah gani gare ka missamen? Ina dibawa nigga qahwa ta here," Lamishi na son yin dariya ba hali, dan yanzu sai su raba hali, ga dariya ta mata yawa, "Yi dariyar ki, yanzu wannan dan rainin hankalin ya hita shi na yi min dariya," Ai kuwa kafin 'Yabbuga ta rufe baki,Lamishi ta fara keta dariya, tunano irin zaman da 'Yabbugan ta ci akan lallen da irin gudun da ta sha kawai take. Tun 'yabbuga na bata rai, har ita ma ta sake sukai ta dariya. Daga baya suka jajantawa juna rashin mubaraka, wanda har a wannan lokacin abun ba wai ya shiga jikin Lamishi bane, kamar yanda kowacce uwar kirki ya kamata ya shige ta ba. ************************ Lawwali na isa sansanin nasu, ya kira No 2 da No 3 suka tara masa mutanen da suka kama last 2days ,aka fitar masa da su tsakiyar daji,  No 4 na ganin haka ya san tabbas Lawwali ya ga wani abun da bai ganshe shi ba, ya na son zuwa ya bada hakuri ya na tsoro, kar laifin ya koma kan shi,dan ya tabbatar wadannan mutane goma da aka fidda ba daya da zai dawo a raye........... 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 32: Kukan bayin Allah kawai ke tashi a dokar daji, ba gida gaba ba gida baya, daga su sai Lawwali da yaran shi, kowannen su dauke da bindigogi, an gama loda wa Lawwali alburushi a bindigar shi, ya na tsaye cikin qunar rai da baqin ciki, ya na karba ya saki alburushi a kan mutum na farko da ke a gaban shi, haka ma ya yi wa na biyun shi, ya saita bindigar akan mutum na uku da ke gaban shi, kalaman Sultana suka bijiro a ƙwaƙwalwa da zuciyar shi, 'Allah na tare da ita, ko ba ka nan, zai kula da lamarin ta, baka cutar da d'an kowa ba, kai ma ba za a cutar da taka qaunar ba' Hannun shi na rawa, kamar zai ajiye bindigar,amma dake zuciyar shi ta riga ta bushe, bai samu sauqin baqin cikin da yake ciki ba sai da ya kashe mutum biyar a cikin su, ya sa aka maida saura, a wajen aka haqa rami, ba sallah, ba addu'a aka binne bayin Allah. Ko da suka koma sansanin su No 1 ya hango cikin 'yanmatan da ke wajen, ya na hira da su,ya na wani karairaya kamar tsohuwar karuwa, wani malolon baqin ciki ne ya taso masa, kujera ya bada umarni a saka masa a filin wajen, kamar qiftawar ido kuwa aka ajiye masa kujerar shi, ya zauna cikin isa da mulkin da yake ji kamar an bashi mulkin qasar baki d'aya ya kalli mutanen dake wajen,wanda gaba d'aya a qarqashin shi suke, matasa ne da magidanta, wanda adadin su ba zai wuce  sha uku zuwa sha biyar ba, mata da maza,dattijai da matasa, sai yara wanda shekarun su na haihuwa  ba zasu wuce sha uku zuwa sha biyar ba, akan yaudari mutane da su, dan a yi garkuwa da mutanen. Kiran su ya yi gaba d'aya, nan da nan kuwa suka isa kowa ya riqe bindigar shi, suka tsaitsaya kamar wasu horarrun sojoji,hakan ya yi matuqar birge shi, ya kuma sanya ya ji ya na da ikon da a yanzu in ya ce a kama masa No 1 a harbe wata kafa a jikin shi ba zata yi saura ba, ba tare da alburushi ya huda ta ba, amma bari ya yi playing game d'in su na cin amana shima. Murmushi kawai ya musu, saboda duk a tsorace suke, sun san labarin batan qanwar shi, sun san shi ne dalilin fushin shi, wasun su har fata suke ya gan ta da wuri saboda Ogan su ya dawo kamar da, mai fara'a, walwala, da basu nishadi. "Mun jima ba mu yi wasanni ba a wajen nan, yau ina so a yi wasan dambe,amma banda cuta, kowa ya yi da wanda yake bi,misali, kai...(ya kira wani matashi da ba zai wuce ashirin da biyar ba, sannan ya kira wani da yake sa'an shi) kai ma zo nan, kunga shekarun ku kusan daya ne, kuma muqamin ku ma  anan wajen, kusan d'aya ne, to ina so a yi dambe, sai d'aya ya gaji ya ce ya isa haka, amma in ku na ganin ku ragwaye ne, duk zan halbe ku na sake sabon zubi" Kafin Lawwali ya gama rufe baki har sun fara kasa kan su, kowa da wanda zai kara da shi. "Habaa ba kowa ne zai yi ba, in an ka ce kowa ne zai yi tau su waye 'yan kallo?" Mutum hudu kawai ya zaba, wato No 2 da No 3,sai No 4 da No 5. "Wadanga, su ne manya wajen ga ko?" Cikin d'aga murya da ihu suka amsa, da "Ehhhh su na Oga" "Tauuu su na zasu nishadantar da mu yau,...kaii Yakubu, taho kai na alqalin wasa, kai zaka bada damar farawa, sharadi daya ne, banda halbi, amma komi ana iyawa, a yi dambe har sai d'aya ya buga qasa so uku, sannan za a qare" Habaa mana waje fa ya dau harami, sai ihu da murna ake, su kan su wanda za su yi damben ba alamar bacin rai a tattare da su, nan da nan kuwa suka shirya, No 2 da No 3 suka shiga tsakiyar fili, Lawwali na zaune ya na taune cikin bakin shi, idan plan din shi ya tafi daidai, daga yau No 1 ze fara cin qaniyar shi a hannun shi. Mai kula da wasa tini ya harba bindiga bayan ya sanar da wasan ba wani doka, ana iya amfani da komai dan kare kai, amma banda bindiga. Kokawa kuwa da naushi, tare da harbi da qafa kamar 'ya'yan jakkai tuni ya kaure a tsakanin su,sun jima suna fafatawa kafin No 3 ya buga qasa ya na haki da fidda numfashi da kyau, Ihu da murna tare da tafi ne ya kaure a wajen, No 2 ne ya je gaban Lawwali ya duqa ,shi kuma ya daki kafadar shi cikin jinjina, da karrama wa, ihu wajen ya sake dauka, a fuskar No 3 babu alamar jin haushi ko hassada dan an samu nasara akan shi, tabbas har cikin ran su wasa suka dauki abun. No 4 da No 5 ne suka shiga fili, aka fad'a masu sharadin wasa, tare da harba bindiga, nan da nan suma suka kaure, ana yin nasu ne, wani  matashin da Lawwali ya radawa abinda yake so ya yi, ya fara bi d'aya bayan d'aya ya na fada wa mutane magana a kunnuwan su. Cikin rabin awa No 4 da No 5 sun jigata, ba wanda ya samu nasara akan dan uwan shi,amma fa kowanne a cikin su ya daku, banda jini ba abinda ke fita a jikin su su dikan. Cikin hargowa wajen ya dauki sunan, Oga da No 1, cike da mummunan tashin hankali No 1 ya fara kada kai, ya na ja da baya, kamar wani tsumma haka wani gabjeje a wajen ya wurga shi tsakiyar fili, No 1 ji ya yi kamar zai fitsari a wando tsabar tsoro, kowa ya san Lawwali a wajen, ba shi da na biyu a qarfi, ba shi da Mahadi a qarfi a wajen, to akan me za su hada su? Indai ba so suke a kashe shi ba. Wani irin fushi ne ya bayyana a saman fuskar Lawwali na irin quncin da ke cikin ran shi, cikin qanqanin lokaci ya kawar da fushin ya fara nuna kawai a bar wasan, kar ya cutar da No 1, dariyar yaqe No 1 ya fara, tare da fadin, "Oga ya ce a bar wasa haka nan, sai wani lokaci" A gaggauce Lawwali ya kalli matashin da ya yi wa rad'a, ai kuwa matashin ya yi tsagal ya ce, "Bamu jiya ba mu dai, mu na so mu ga hwadan manya, zai fi dadin kallo," "Muna so, mu ma mu na so, mu na son ganin fadan manya!!!!" Shi ne abinda mutanen wajen ke ta ihu su na maimaita wa, har suka jawo hankalin mutanen da ke rufe a wajen, ta window da duk wata kafa da za su samu damar kallon me ke faruwa suke leqe, ai kuwa cikin daga hannu d'aya wajen ya yi tsit. Lawwali ne ya isa gaban No 1 ya ce, "Kar ka damu aboki na, kawai ka dage, wataqila ka samu nasara akai na, ka ga ba ni da wani qarhi Mubaraka ita ta qarhi na ka sani, gashi ban gane ta ba, za ka iya nasara akai na cikin sauqi" Wata iriyar zufar saman hanci da saman lebe No 1 ke yi, gashi ya na jin wani ruwa na gangarar masa ta qafafun shi, be gama tantance shin fitsari yake a tsaye ba ko kuma zufa ce, ya ji ana karanta sharadin damben,kafin ya ja baya an harba bindiga, zare ido ya yi, ya na kallon Lawwali, wanda fuskar shi ta sauya, daga fara'a zuwa tsantsar bacin rai, hankalin shi ne ya sake tashi. Kwasa ya yi a guje zai gudu, Lawwali ya cafke shi, wani irin naushi ya kai ma No 1 sai da ya juya, tare da kifewa a qasa, qoqarin buga hannun shi yake a tashi wasan dan ya san ba zai debi komai a jikin Lawwali ba, Lawwali ya bi hannayen ya taushe, ya hana shi buga su. Dambe ya yi dambe, No 1 ya daku iya duka, duk wani haushin shi da Lawwali ke ji, sai da kaso mai tsoka ya ragu, sai da ya zamana hatta da tsayuwa No 1 ya kasa, baya iya d'aga yatsan shi ko d'aya, ballantana ya buga qasa, idanun shi sun kada sun yi jawur kamar ya yi taruwar jini a cikin su. Lawwali da kan shi ya d'aga hannayen shi biyu, ya miqe daga saman No 1, ya tabbata dukan da ya masa sai ya sanya shi jinya ta aqalla sati daya,ya ga ta fita yawon cin amana. Umarni ya bawa No 4 da ya yi jinyar No 1, cikin azama, No 4 da shi ma yake a jikkace, ya fara qoqarin daga No 1, wata qara ya saki mai qarfin gaske, da sauri no 4 ya sake shi, ko da ya duba sai ya ga ashe No 1 ya samu karaya ne, har hannun ya kumbure, da damar matasan wajen sun ji dad'in dukan da aka yi wa No 1 dama ya addabe su, ya ishe su, tunda Lawwali ya koma kwana da zama a cikin gari No 1 ke musu mulkin kama karya, yanzu gashi an yi musu maganin shi. Lawwali bai kwana a wajen ba, gida ya tafi, ko da ya isa wanka ya fara yi, sannan ya ci abinci ya zauna a kujera, ya na kallon hotunan Mubaraka, da video da ya dauke ta. Ya na kalla ya na murmushi, tare da jin dad'in sanin inda take, da kuma halin da take ciki,kulawa ta musamman No 4 yake basu,da taimakon Lawwalin. Duba time ya yi, ya ga sha d'aya saura, bai wani dogon tunani ba kawai ya danna number'n ta, ta yi ringing sau biyu kamar jira take ya kira, ta dauka, "Hello" "Assalamualaikum" Maida ido sama ya yi, kafin ya amsa sallamar da, "Wa'alaikumussalam, ran ki shi dade baki kwana ba?" "Ban yi kwana ba, kai mi ka kai da ba ka yi kwana ba har yanzu? Gobe akwai aiki fa, in muka tashi har wata unguwa za mu tai, last 3days an shiga an yi musu barna, ba kadan ba, mutan garin har wasun su sun yi hijira, qalilan ne ke zaune a garin, saboda basu da wajen zuwa" Sarai ya san ko ina ne, duk da ba su suka yi aikin ba, amma dai abokan aiki, ai ba sa buya. "Allah shi kai mu," "Ameen, me ya sa ka kire ni yanzu? Akwai wani abu ne?" Shiru ya ɗan yi na wasu seconds kafin ya ce, "Babu komi, kawai dai na yi kewar ki ne" Kwanciyar ta ta gyara, tare da sake manna wayar a kunnen ta, ta na jin yanda Muryar shi ta cikakkun mazaje ke dukan dodon kunnen ta, "Mun fa hadu d'azu" "Ehh sanin haka ne ma ya sa na ji duk na yi kewar murmushin ki mai tsadar nan, yau baki yi min shi ba sai sau biyu kacal, gaskiya ban qoshi ba, a qara min," Wata iriyar siririyar dariya ta dinga yi, har zuciyar shi bai jin komai game da dariyar ta a yau d'in ,soyayyar da ya fara mata kafin ya san me mahaifin ta ya masa, yanzu ta fara sauya salo, ta koma soyayyar daukan fansa. "Kaiiii ran ki shi dad'e gaskiya sai da sahe, wagga dariya zata hana min kwana" "Me ya sa za ta hana ma kwana?" "Saboda in na kwanta zan dinga tunanin ta, kuma zan ji ina son saurarar wata makamanciyar ta daga gare ki, gashi na sani har abada ba aure a tsakanin mu" Da sauri ta gimtse fuska, tare da mamakin dalilin da zai sa ya ce ba aure a tsakanin su "Mi ka ka nuhi? An haramta aure a tsakani na da kai ne ko mi?" "Ba a haramta ba a musulunci, amma iyayen ki sun haramta shi, sanin kan ki na ba mai barin ki auren driver ko? Ban taba baqin cikin rashin ilimin boko ba da na arabiyya sai yanzu, da ina da ilimi da iyayen ki sun bani ke,......ina son ki sultana" Tsigar jikin ta ce ta tsaya ta mimmiqe, ji ta yi bugun zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri. "Da gaske ka na so na?" "Kwarai da gaske, ina son ki Sultana" Rintse idon ta tayi, tare da cizon leben ta na qasa,cikin lallausan murmushi ta ce, "Dan Allah maimaita in ji" "Inda son ki sultana" "Ka same ni kuwa, ba abinda zai hana ka aure na," "Akwai shi," "Me ne ne shi?" "Iyayen ki, iyayen ki musamman Hajiya bata bari ki auri jahili, kuma driver," "Auwal ka dena kiran kan ka da wannan mummunan suna, in baka fad'a cewar baka je makaranta ba, babu wanda zai ce baka je ba, and na ji labarin har saukar qur'ani  ka yi, kuma ka fara Makarantar boko itama, to ka ga kenan kai ba jahili bane," "Hummm ba zaki gane ba, bari na bar ki ki yi kwana, amma fa ki sani iyayen ki ba za su bar ki aure na ba, ni dai abu guda nis-sani, ke kadai ni ke so, ke kadai nit-taba burin mallaka a matsayin matar da zan aura, bayan ke ban taba son kowa ba, .....Ina son ki Sultana" Idanun ta a rufe hawaye na kwaranya a idon ta, ya gama zuba kalaman shi masu zafi da kuma dad'i a gare ta, ya kashe wayar shi  ya barta cikin yanayin da ta kasa fassarawa. Shin da gaske yake iyayen ta ba za su bari ya aure ta ba? Me ye dalili? A duniya mutum na iya auren duk wanda yake so, se wanda musulunci ya hana, misali mace ta auri mace, ko namiji ya auri namiji, ko mutum ya auri wata dabba ko wata halitta, ko musulmi ya auri kafuri,ko muharramai su auri junan su, amma Indai akwai so da qauna kowanne namiji zai iya auren macen da yake so, haka ma mace za ta iya auren namijin da take so, to me ya sa ita zata zama daban a cikin mutane? Saboda kawai shi din driver ne? Da wannan tunanin bacci mai cike da rudanin tunani ya dauke ta. ************************* Duk abinda aka sanyawa rana, wannan ranar zata zagayo, ko ayi abun, ko kuma a fasa shi . Yau ce ranar zabe, gwamna da iyalin shi tun asuba suka shirya suka je wajen yin zaɓe, sun dangwala nasu sun koma government house, yau har da sultana aka tafi, ta na can ne kawai, amma hankalin ta baya tare da ita, rashin ganin Auwal na damun ta, tun randa suka yi waya, yau kwana hudu, ta ji shi shiru, shin ko dai ya rabu da ita ne saboda tunanin Hajiya ba zata yarda ba, daddy ma ba zai amince ba? Amma ai bai ce zai rabu da ita ba. Wannan tunanin sun ma ƙwaƙwalwar ta yawa, har ya fara sanya ta zance a fili, cikin rashin fahimtar me ta fada Sultan ya ce, "Mi kin ka ce? Wa ye zai bar ki?" Da sauri ta hau yaqe ta na barin wajen, tare da sanar da shi , "Ba kowa, ba komai, kar ka damu, ina zuwa" Tafiya kawai take a tankamemen gidan da ya cika da mutane kala kala, duk ta gama ratsa su ta wuce wani building, ba abinda ke tashi a hanyar wajen se karar takalmin ta, wayar ta ta tsaya cak ta na latsawa, sama sama ta ke jin muryoyin su, "......ka tabbata dai ka saka a kawo takardun zaben da aka dangwala ko? Na hwadi maka in banda aikin da Sultana ka yi a gari, sai d'an wanda munka hwara shekarar ga, walle ba mai zabar mu," "Ki kwantar da hankalin ki Hajiya, na gama komai, akwai taqadarin yaro na da ka yi min aiki ko wanne iri na, shi da yara nai, ke ko batar da mutum nicce ayi, ba shi koma second d'aya raye indai yaron nan na saka, ke duk wasu abubuwa da ki kaga ina yi da shi ni ka taqama, dan haka zabe kamar na ci na gama ne," Wata iriyar dariya suka sanya a tare, suka ci gaba da hira, Gwamna na bawa Hajiya Ikee labarin Lawwali, ba tare da ya sanar da ita sunan shi ba, sai jin dad'i take ta na addu'a Allah ya sa su zarce. Qoqarin komawa cikin mutane suke, cikin sauri Sultana da ta daskare a wajen ta cire takalmin ta a hannu, ta fad'a wata qofa da ta gani a dan bude ta b'uya, Hajiya Ikee ce da Gwamna Halliru suka fito, cikin farin ciki, sun sha ado na alfarma, sai walqiya suke, da qamshi. Su na wuce wa sultana ta sanya wani irin kuka mai ban tausayi, mahaifan ta ashe basu da imani? Kuma a haka suke neman su ci gaba da jagorantar al'umma?........... *Ni Ko nace iya abinda ki ka sani ma kenan 'yannan, ba ki san kalar tsafin da gyatumi ke yi ba* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 33: Lokuta da dama idan farin ciki, ko baqin ciki ya dami mutum, akwai mutum na farko dake zuwa zuciyar wannan mutumin, walau wanda ya yarda da shi ko da ba 'yan uwantaka ta jini a tsakanin su,ko kuma wanda ke da alhaki akan halin da mutum ya shiga, masoyi shine mutum na farko da ke fara zuwar wa mutum a rai, mace ko namiji, qawa ko saurayi, miji ko mata, ko kuma iyaye. A baya Sultana ba ta da wanda ya wuce Sultan a wajen ta, saboda shaquwa irin ta yaya da qanwa da ke a tsakanin su, komai nata shi take sanarwa, to amma tunda shi Allah bai sa har yanzu ya gano asalin mummunanan dabi'un mahaifan nasu ba, ba ta so ya sani, kamar yanda suka so ya yi rayuwa haka yake yi, ba ya saba umarnin su, ya kai a ce ya ajiye iyali, amma rayuwar shi abar juyawa ce a hannayen su, gwanda ita sun bata 'yanci, wanda a wajen ta ba 'yanci bane, sun yi amfani da abinda suke kira 'yancin su na biyan buqatar su ta son zuciya da shi. Lawwali ne babban wanda za ta iya wannan maganar sirrin da shi, (to wai ma makaranta mu dan tattauna wani abu mana, shin daidai ne kawai daga yin saurayi, dan ki na jin kin yarda dashi, dari bisa dari, sai ki ta fada masa sirrin ki? Musamman wannan babban sirrin? 'yan mata da dama su na shirme, da yarinta, kawai yanda ke ki ke jin ki na son namiji, To haka ki ke dauka shima haka yake son ki, kuma yanda kk yarda da shi shima haka ya yarda da ke, wallahi ba haka bane, maza kala kala ne,kashi kashi ne,akwai wanda zai so ki kamar ran shi, amma ba sirri, nashi sirrin ma be riqe ba balle na wani, kuma zai iya rufe ido ya manta da son da yake maki, ya kafta maki uba uban rashin mutunci, daga baya in kun shirya ya baki hakuri, ke kuma ya wuce, anjima ma in wani abu ya taso se kin fada masa. Akwai namijin da zai so ki, kuma zai saurare ki, zai taya ki warware matsalar ki da damuwar ki,zai shiga lamarin ki kamar nashi, kuma ze riqe miki sirrin ki,amma ki sani 'yar uwa irin su basu da yawa a wannan zamanin, wani ma Allah Allah yake yaji maganar ki ya fadawa yan uwan shi da abokan shi, ki na nan tanyare bude a faranti kowa ya san sirrin ki da na 'yan gidan ku, a kiyaye, a dena makahon so) Wayar shi take ta nema, ana fada mata busy, cikin bacin rai, da sharar hawaye ta bar taron, iyayen nata basu son video ko camera su hau kan ta, ganin yanayin da take ciki, dan haka suka basar sukai ta harkokin su, direct motar ta ta nufa,ta na qoqarin shiga, wani murdadden namiji da baqaqen kaya, da baqin gilashi ya tsaya a gefen ta ya ce, "Ran ki shi dade, Excellency ya ce kar a bar ki ki hita yanzu,sai an fadi sakamakon zabe gari ya lafa,sannan za ku fita,yanzu ki tai zuwa sashen ku," "Saqo ka ke bani ko umarni?" "Ran ki shi dade, ba umarni bane, dan Allah ki taimake mu ki koma, abincin mu na nan, ke mai tausayi ce, kar ki fita ya zama sanadin barin mu aiki" Kallon shi tayi, ta gan shi rusheshe, ko a ka aka ce ya maida ta sashen, cikin qiftawar ido ya na iyawa, amma ya gwammaci ya yi amfani da kalamai masu taushi a gare ta, cike da baqin cikin ci gaba da zama a gidan Gwamnatin ta shiga gaba, ya na take mata baya, har bangaren su, ta na shiga ta rufe da qarfi ta saki wani irin kuka, mai matuqar kuna. "Anya su Daddy za su hadu da rahamar Allah kuwa? Ashe duk abinda Daddy ke aikatawa, Hajiya ta yi kamar bata sani ba ita ka zuga shi aikata wasu munanan aikin? Anya iyayen ga namu su na da imani kuwa? Sun san Allah kuwa?" Kuka take ta na surutai ita kadai,ga wayar Lawwali ta qi samuwa, se gwadawa take. Har aka yi azahar ta yi itama, ta kwanta Lawwali bai kira taba, ta fara hasala yanzu kam, amma ba yanda zata yi, gashi ba zata iya fushi da shi ba, saboda kalar son da take masa ma, ba zai bata damar fushi da shi ba. Wayar ta ta sake laluba, ta shiga wajen rubuta saqo,ta hau rubutu kamar haka. ~Auwal dan Allah ka dauki kira na, zan iya rasa raina in har ban ji Muryar ka ba a yau, kai ne maganin quncin da zuciya ta ke ciki,kai ne farin ciki na,kasancewar ka tare da ni, shi ne cikar farin ciki na, pls ka kira ni, in ka ga saqo na, Ina son ka Auwal, and I really need u now, pls~ Abinci aka shigar mata da shi, ko daga kai ta kalla ma bata yi ba, ballantana su sanya ran za ta ci, duk magiya da roqo da mai aikin ta dinga yi, qarshe itama magiya da roqo, tare da kuka ta sanya wa matar, dole ta hakura ta barta. Ita kadai ta san ya zuciyar ta take a yanzu, wani irin qunci da ciwo take mata, wace iriyar rayuwa take ciki? Ai da wannan azziqin gwanda talaucin da ba ze raba ka da imanin ka ba, akwai abubuwa da dama da suke zamewa bawa musiba, to ta tabbata wannan azziqin musiba ne a gare su, sai dai za ta yi ta addu'a Allah ya kare su daga fadawa halaka, duniya da lahira. Abu kamar wasa, Lawwali bai kira Sultana ba, dik da cewa ya ga kiran ta, ya ga saqon ta, aiki ne ya mishi yawa, ga wajen da suke ba network sosai, yau kuwa tun cikin dare suka fita, suna ta kai takardun da aka riga aka dangwala wa yatsan zabe, mazabu kala kala. A gajiye yake matuqa, ko ya kira ta be san me zai ce ba, ya san dole ta fuskanci gajiyar a Muryar shi, ba shi da abin kare kan shi, dan haka ya qi kiran ta, ya ci gaba da harkokin shi. Wani sashe na zuciyar shi ya na jin ba dad'i , da bai kira ba, tunda ya san kalar yanda take son shi, ko Muryar shi taji ta na jin dadi a ran ta, kawar da tunanin ya yi, a fili ya furta, "Gwanda ta ji zafin rashin kiran nawa ma ai, hakan ma wani punishment ne" Kafin duhun dare ya shiga Sultana ta ji jiki,zazzaɓi mai mugun zafi ne ya kama ta, ba abinda take banda rawar sanyi, Hajiya Ikee ta shiga bangaren nasu ta tarar da Sultana kwance ta lullubu, sai rawar sanyi take, cikin tsananin damuwa ta isa gaban ta, ta na taba goshin ta, dan ture hannun ta sultana tayi, sanan ta juya baya, Hajiya Ikee, waya ta fara yi, akan a kira likita yanzun nan, cikin rawar murya sultana ta ce, "Ko ya zo ba abinda zai iya min, ...ba na so ya zo,... ki barshi kawai, .....ki je ku ji sakamakon zaben da kuka riga kuka san ku ne ma zaku yi nasara" Cikin washe baki, da rashin gane mai Sultana ta ce, ta miqe, "Bari in tai, nahi son a hwadi komai a gabana gashi can ana ta hwadi, har yanzu akwai mazabun da ba su kai sakamakon su ba, da alama za mu samu nasara, mun godewa Allah, bari na tai, in likitan ya zaka sai mu taho a baki magani ke jiya? Allah shi yi miki albarka," A hankali ta amsa da "Ameen" Shin addu'ar irin su Hajiya ma na cin mutum ne? Ni Ko na ce uwa dai uwa ce, komai lalacewar ta, in ta yi addu'a inshaa Allah, Allah zai amsa, zunubin ta daban, addu'ar ta daban, da ace mummunan kalami zata yi ga dan ta zai same shi,kamar yanda Lamishi bata da burin da ya wuce ta zagi yaran ta, ta musu baki. Likita ya zo da misalin tara na dare, ya bata magunguna, tare da bata shawarwarin rage tunani,domin jinin ta ya hau kadan, murmushi kawai ta yi masa ta yi godiya, Hajiya Ikee ta raka shi, ta koma wajen ta, dan dai ta san zabe kamar sun ci shi sun gama, amma me ke damun gudan jinin ta har jinin ta ya hau? Cike da damuwa ta koma dakin, hawaye ta gani daga idon sultana ya na gangarewa a saman pillow duk da cewa  idanun nata na rufe ne. Zama ta yi a gefen kan ta, tare da sanya hannu ta jaye gashin ta da ke gefen fuskar ta, ta shafa kan nata cikin kulawa da soyayya, irin ta uwa, cike da tausaya wa ta ce, "Sulty Baby mi ka damun ki? Hawan jini? Mi ya maki zahi, da uwar ki da uban ki, ga dan uwan ki masu son ki? In akwai abinda ki ka so duniyar ga ki hwadi min ki na samun shi ko menene shi kuwa" A wahalce Sultana ta daga ido ta kalli mahaifiyar ta, wadda take bata tsoro, tsoron gaske ma kuwa, dan bata san wanne ne halayen ta boyayyu ba kuma bayan wanda ta ji ta sani, cikin qunar rai ta ce, "Kar ki damu,Wataqila wannan ciwon shi ne ajali na, wataqila kuma a hankali Allah ya yaye min, amma ku ba za ku iya min abinda nake so ba" Cikin tsananin damuwa Hajiya Ikee ta sake mannewa a jikin Sultana, ta na jan ta jikin ta, da sigar lallashi, tausayi, soyayya, da tsantsar qauna, "Habaaa Baby Sulty, wace irin magana ta wagga ki ke yi? Kin San dai ba abinda ki ke nema a duniyar nan ki rasa daga wajen mu, akan su wa muke fadi tashi dan mu tara abin duniya? Duk ba dan ku muke yi ba? Ki sanar da ni abinda ki ke so, yanzun nan zan sa a kawo maki shi" "Hajiya kar ki damu, na fara lura da kuma sanin abinda za ki iya da wanda ba zaki iya ba, amma wannan kam na san ba zan same shi ba, Dan Allah ki bar wannan maganar ki tai an kusa sanar da sakamakon zabe" "Rayuwar ki is more important to me, than anything else in the world my dear just tell me what you want and I will get it done for you yanzun ga" Idanun sultana zafi suke kamar an zuba mata yaji, a hankali ta ware su a fuskar Hajiya Ikee wadda ta nuna tsantsar damuwa da gaskiyar maganar ta, na bawa sultana duk abinda take so. "Auwal....Auwal shi ne abinda zuciya ta ka so, Auwal na ke so ku aura min, indai har da gaske ki ke za ki yi min duk abinda nake so, shi ne rayuwa ta, in ku ka hana ni auren shi Hajiya zan mutu" Miqewa tsaye Hajiya Ikee ta yi tana kallon Sultana da wani irin kallon kan ki daya kuwa? "Wane Auwal ki ke nufi? Lawwali driver? Ki na da hankali kuwa? Na haifi yarinya kamar ki, kyakkyawa, mai ilimin arabiyya da boko sannan ta b'ige da auren jahilin driver? Ki na hauka ne?" "Hajiya ba fa jahili bane masanin qur'ani ne sosai, masanin qur'ani kuwa ai ba mai kira nai Jahili" "Sai ni, ni zan kire shi jahili tunda banga alamar shi na aiki da shi ba, qur'ani ya hana neman ilimin boko ne? Namiji har namiji ace driving shikai? Ba da ni ba, kar ki bata min rai, ki nemi komai a waje na, amma banda wanga, yau ga zancen banza zancen yohi, to bari ki ji, kar ma ki kuskura ki wa mahaifin ku maganar ga, dan rai nai sai yahi nawa ɓaci, ba abinda ya tsana sama da talauci ga rayuwa tai, ba zai so ya miqa ki gidan wahala ba, na hwada maki tanadin da nake a kan ki, shi na ki ke debo min wahala? Sam ba zai yu ba," Ta na ta Masifa ta bar dakin, a qasan ran ta bata so suka rabu ta haka da diyar ta ta ba, musamman yanzu da bata da lafiya. Sultana kuwa ko kukan ta kasa, tabbas sai yanzu ta fahimci me Auwal ke nufi,abinda babba ya hango dama an ce yaro ko ya hau rimi ba zai hango ba, ya riga ya fahimci ba za a bashi ita ba, ita kuma ta zaci son da iyayen ta ke mata zai taimake ta a bata wanda take so. Ta na nan kwance ido biyu ta ji ana taken Nigeria, ana iface iface, a cikin gidan, rintse idanun ta tayi cikin qunar zuciya ta ce, "Ban san sanda tallakan Nigeria zai bude ido nai ba, ban san sanda tallakan Nigeria zai fara addu'ar samun shugabanni wanda suka cancanta managarta ba, ba wanda suka so ba, ban san sanda tallakan Nigeria zai gyara tsakani nai da Allah ba, har Allah ya ji tausayin shi ya raba shi da shugabanni kamar su Daddy, ya Allah ka kawo mana qarshen wannan rayuwa mara aminci da muke ciki, ya Allah ka sa qasar mu Nigeria da duniya baki daya ta zama waje mai aminci ga bayin ka," "Ameeen Sulty Baby, ya jikin naki? Hajiya ta je ta na ta hwada, ban san akan mi take magana ba dai, amma na ji ta na akwai tanadin da ta yi akan ki, ko kin san akan mi taka magana?" Murmushin da be kai ko ina ba ta yi wa Sultan da Ke bin ta da kallo, sannan ta ce, "Ka manta mun je gidan dan takarar shugaban qasa?  To tun daga can ta fara ciniki na, ka shirya kaima za a yi naka kwanan nan, da ta samu wadda ta hito gidan kuddi za a saishe ka, Yah Sultan ina da wanda nika so, ta ce kar ma na bude baki na sanar da Daddy, sun gama maganar wanda za su bawa ni" Hawaye ne suka fara tsartuwa daga idanun ta, ran Sultan ya ɓaci matuqa, zai d'auki komai akan shi, amma ba zai taba jure ganin Sultana cikin mummunan hali haka ba, nawa take har da za a ce hawan jini ya kama ta? Cikin fushi ya bar d'akin, ta na ta kiran shi bai juya ba. Ya na fita wayar ta na daukan ringing, da kyar ta janyo ta, ta na ganin sunan Auwal,  hannun ta ya d'au rawa, bakin ta na rawa saboda kukan da ya taso mata, ta na dauka kuwa ta fashe da kuka, Lawwali na jin kukan ta, ya ji wani abu mai qarfi ya daki zuciyar shi, ba ya son jin haka saboda ita, ba ya son jin damuwa da damuwar ta, amma ya kasa jurewa sai da ya tausasa murya ya ce, "Ran ki shi dade ki yi min afuwa,na shiga matuqar busy ne, inda na tai ba network ,shi yasa ban dauka ba,amma ki yi hankuri, gani na dawo gida,dan Allah ki dena kukan" Cikin shagwaba ta ce, "In ka sake tafiya inda ba Network zan yi fushi da kai mai tsanani, ba zan sake kula ka ba" Siririyar dariya ya yi, Sannan ya ce, "A min ahuwa, in ki ka dena kula ni, ashe qarshen rayuwa ta ne ya zo, ba ke ba Mubaraka, lallai da zan zama kamar gunki, domin zan zam ba rayuwa a tare da ni" Itan ma dariya ta saka, wadda ba zata iya tuna sanda ta yi dariya ba a ranar gaba daya. "Na maka alqawarin sai ka mallake ni a matsayin matar ka, kuma sai mubaraka ta dawo gare mu lahiya" Kalaman ta na qarshe ba karamin faranta ran shi suka yi ba,har ya ji sabon lamari game da ita............... *Tambaya ta anan shi ne, Sultana da ke yi wa Lawwali alqawari, ta manta maganganun Hajiya ne?* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 34: "Dakata min Sultan, kai har ka isa ka taho ka yi min titsiye? To bari ka ji, kai kan ka, ina nan na tanadar maka wadda za ka aura, lokaci nika jira, ta na kammala digirin ta ta dawo qasar ga za a daura muku aure, diya ce ga minister'n tsaro, kuma babbar diyar shi, na duba wayar ka tass na ga duk matan da ka ke mu'amala da su, duk ba ya wuce gaisuwa, Ita dai nigga ku na hira jefi jefi, tunda Allah ya sa hankalin ku ya gamu waje guda, Daddyn ku ya ma iyayen ta magana, kuma sun yi na'am, ka shirya, ana gama auren Sultana naka za a yi" Baki Sultan ya sake kawai ya na mamaki, ya na namiji amma ana so a masa auren dole, to ba ma wannan ba, in an masa auren dole ya hakura tunda dama baida budurwar da ta kwanta masa ga rai, to ita sultana da ke son Lawwali fa? "Hajiya na amince ku aura min duk wadda kuka so, amma fa ba zan amince ku aura wa sultana mutunin da bata qauna ba" "To Uban mu, mun jiya, in an tashi auren sai ka hana,...dalla fita ka ban waje, yau so kuke sai kun batan duk wani farin ciki da nake ciki na ga alama" Daddy ne ya shiga dakin bakin nan kamar gonar audiga, cikin, farin ciki ya ce ma Sultan, "Ku shirya kai da qaunar ka gobe akwai party, around 1am, kwana za a yi ana murnar samun nasara, diyoyin gwamnoni ne suka partyn a Abuja, na san za ku buqaci kudi sosai, dan kusan kowa a wajen ya na taqama da uba nai, ga wannan, ku dauki duk nawa ya muku" Wani dan kati ya miqa masa,wanda yake a matsayin makullin ma'ajiyar kudin Gwamnan, kallo kawai Sultan ya bisu da shi,ya kasa cewa komai, da kyar ya bude baki ya ce, "Yaushe ku ka zama haka? Yaushe kuka dena damuwa da abinda muke so sai wanda kuke so? Yaushe za ku saki duniya, ku kama qiyama?" Daddy bai fahimci ina Sultan ya dosa ba, ita da ta san akan me yake magana, tuni ta miqe, ta na son kawar da zancen Sultan ya sa kai ya bar dakin. "Kwantar da hankalin ka ka jiya diyan ga in ka ce kabi nasu to fa ruwa ma sai an tauna musu an hadiye musu tsabar gata" "Amma mi an kai mai ? Ban taba ganin Sultan ya yi hushi haka ba,mi kin kai mai? Ki hwadi min gaskiya ko inna bincika  na gano kin masa wani abu ran ki zai ɓaci, ban hada d'iya na  da kowa ba" "Ni kuma ni na haihe su , har da ka ke hwadi min baka hada d'iyan ka da kowa ba, maganar wannan yaron driver ne taqi qarewa gidan ga, ya zo ya na wani hwadin magana yanda ya ga dama, to shi kan shi na sanar masa magana diyar Minister , shi na yake hushi " Shiru ya yi bai ce komai ba, ya fita ya bar dakin, bai tsaya a ko ina ba sai dakin Sultana, ta na bathroom, ta na alwala, sai da ta gama ta fito taga wayar ta a hannun shi, ya na duddubawa, har ta isa gaban shi bai aje wayar ba sai da ya gama abinda yake. "Sultana da dukkan alamu ki na son Lawwali, amma Sultana ki sani, ke baki san waye Lawwali ba, ni na san waye shi, ina mai baki shawara da ki hakura da shi, tun da wuri, tun lokaci bai qure miki ba" "Daddy kenan, indai Hajiya ta ji ta gani, ta ke zaune da kai, banga dalilin da zai sa ni na kasa auren driver na ba" Cikin rashin fahimta ya ce, "Me ki ke nufi? Sultana yaushe kin ka hwara magana irin wannan? Me ki ke nufi da abinda kin ka hwadi yanzu?" "Never mind Daddy, ina so nayi sallah, pls" "Sultana ina son sanin damuwar ki, talk to ur Daddy Sulty Baby, ki sanar da ni mi ki ka so" Cikin kuka ta ce, "Daddy ka tambayi Hajiya, ta san komai, dan Allah ka barni na gana da Ubangiji na, shi ne kaɗai zai min maganin damuwa ta, Hajiya ta tabbatar min da ba zan samu me nake so wajen ku ba, yanzu ka tabbatar min da na hakura da farin ciki na, saboda bai muku ba, bai yi daidai da abinda kuke so ba, ni Auwal nike so, ba wani shugaban qasa ba," Daddyn su ne ya ja ta jikin shi ya na lallashi, a zuciyar shi kuwa ya na mamakin sanda ya yi sake Lawwali ya yi nasarar dasa soyayyar shi a zuciyar sultana haka, sai yanzu yake tunawa da alamomin da Hajiya ke sanar da shi, lallai ya yi sake, Lawwali na shirin yi masa babbar illa, indai har ta nan ya biyo. "Ya isa kukan haka nan, zan yi tunani akan maganar, ki daina kuka" Da sauri ta kalle shi, ta na son tabbtar da gaskiyar maganar shi, dan yanzu gaba daya ta cire yarda a tsakanin su, gani take komai nasu qarya ne. Sai da ya ga ta daina kukan ya bar dakin, wajen Hajiya Ikee ya koma, ta na zaune ta zabga uban tagumi ta na tunanin yanda za ta raba tsakanin Lawwali da sultana. "Ki na da gaskiya ashe da kin ka ce  na kori yaron nan daga gidan nan naqi ji, ashe ya min babbar illa ina zaune ba tare da na sani ba?" Kamar an sosa mata inda ke mata qaiqayi haka ta miqe, kallon lokaci ta yi, ta ga ya tafi sosai, ta gaji tilis, kuma maganar nan na buqatar dogon nazari, ko kadan ba ta son batawa Sultana, amma dole ne ta raba tsakanin su da Lawwali. "Wannan magana ta riga ta wuce, yanzu mafita za ka nemo mana, dan kuwa ba zan taba yarda diyar ciki na ta auri driver ba, yau ko min muqamin da za ka damqa masa a gwamnati walle ba ya hanawa a kire shi da driver, ba zan zama abin dariya cikin abukkai ba,dole ka dau mataki" "Ba zaki gane ba, yanzu raba tsakanin sultana da Lawwali babbar musiba ce wallah, duk yanda zan miki bayanin yaron nan ba zaki gane ba, ni na san wane ne Lawwali," "Driver din? Me ye ba zan gane ba? Yau muke tare, ka kore shi kawai, shi bar gidan" Bai ce mata komai ba ya fada bathroom. Mita ta dunga yi tare da fadin ya sa yaron shi din nan da ke masa aiki, a sace Lawwalin ya bar doron qasa baki daya, Indai ze zame musu fitina akan dukkan tsarin su. ************************* Sai guje guje suke abin su a katafaren tsakar gidan kakannin nasu, cike da nishad'i da jin dadi, ita kan ta Hajiyar Hansatu rabon ta da fitowa farfajiyar gidan haka ta manta, Hansatu na ta tuna yarintar ta, zaune suke a saman kujeru na qarfe masu matuqar kyau, gaban su table ne an aje fruits da abin sha, su na ta hira a tsakanin su, wanda ya san Hansatu sati Uku da suka wuce ya gan ta yanzu ba zai gane ta ba, ta ciko ta murmure, ga wani haske da ta yi, in ta saka riga da skirt sai ta cike su famm, ban taba zaton hansatu na da shape haka ba sai yanzu. Hajiya ce ta kalle ta ta ce, "Gaskiya ya kamata a sauya maki waya, yanzu da yar wayar nan ta zamani ake hira da miji, sai ku yi chatting din ku kamar ku na tare, haka naga Yayan ki na yi da waccan maras kunyar da ta qi dawowa, amma fa soyayya a waya kamar Juliet," "Hajiya wai mi an kai mata ne haka?" "Wannan fa baki gane alqiblar ta, dan yanzu ko an ce mi yayi mata bata hwadi, ta na can qasar waje, da alama can taka so su koma da zama, tunda can ta yi rayuwar ta, ni kuwa ba me d'auke min yaro shi tai wata uwa duniya" "Ohhh amma ko bata kyauta ba gaskiya, ai mace hankuri aka santa da shi a gidan miji, ba irin wanga hali ba" "Haka ne, ita kam sam bata san wannan ba, komi so takai ayi yanda taka so, ba ko shi yiwa," "Allah to ya shirya ta, ya sa ta dawo su ci gaba da zaman su lahiya," "Ameen dai" Su na tsaka da hira Hajiya ta dauki waya, ta kira Yayan Hansatu, tace ya aiko mata da waya mai kyau, kafin Hansatu ta wuce, amsawa ya yi, da toh, sanan suka yi sallama. Hansatu bata koma gida ba kuwa sai da dalleliyar waya mai kyau, ba ta wani murna da wayar kawai dai ta nuna ta na murna ne, domin kuwa wanda ake mata kwadayin su yi hirar da shi, tunda ya tafi sai dai taji labari wajen Hajiya sun yi waya, amma baya kiran ta, balle ta samu No shi, kuma ita ba zata iya tambayar hajiyar ta No isah ba. Ko a mota ajiye kwalin wayar kawai ta yi a cinyar ta ta na tunani, ga dai shi ya tafi, kuma ya fadawa Hajiya kasuwancin goro yayi albarka, amma ko sisi bai masu aike ba, bata san ranar dawowar shi ba. A qofar gidan su motar ta tsaya, fitowa suka yi ita da yaran, kowa ya gan su ya ga jikokin masu azziqi, hatta da takalmin su yanzu mai tsada suke sakawa. Ko kallon majalisar su 'yabbuga bata yi ba, ballantana ta ga yanda suka sanya mata ido su na gulmar ta. Sallama ta yi da driver suka shige gida. Can majalisar su Lamishi kuwa banda gulmar su ba abinda suka ke. "Hummmm wagga ai ni zan baki labarin Hansatu ta sauya, bari dai, ai za su koma yar gidan jiya ne, ta na zuwa roqon abu zan mata kaca-kaca, yanzu ta koyi walaqanci,ko kallo bamu ishe ta ba,dan ta hwara daura suhwa, da holan, walle ta na barin shi" "Ohhh ke kuwa me ya sa kin ka ce haka? Ai ba kin mata hwatan komawa gidan jiya ba, indai ta sha wahala yanda kun ka ce" 'Yabbuga ce ta kalli Asshibi a sheqe ta ce, "Na hwadi, na ce na hwadi baki ganin wani kallon walaqanci da takai wa mutane?" "Ai kuwa ko kallon wajen ga ma bata yi ba" "Tauuu PA din Hansatu, ko zuwa zaki ki hwadi mata mi nicce?" Lamishi da ta zabga tagumi ta na tunanin shin duniya ina Mubaraka ta shiga ne, ta ce, "Dan Allah ku bar yi mana hayaniyar ga, wadda ku ka yi domin ita bata san ku na yi ba, ni abinda ya ishe ni ya dameni" "In baki so ki ji mi muka hwadi tai garkar ki, nan garka ta ta wallah" (in bakya so ki ji me muke cewa je ki gidan ki, nan gida na ne) Ran Lamishi ya baci, nan da nan kuwa magana ta girmama, aka hau fada, sai ga tone tonen asiri ana ta yi, akan gulmammakin da akai ta kitsawa anan ne matar Yahai taji maganar da daga ita sai 'Yabbuga suka yi ta, ya akai Lamishi da baquwar da bata fi watanni hudu da su ba ta sani? Ai kuwa sai fad'a ya koma kan 'Yabbuga da Matar Yahai, nan fa suma suka hau nasu maganganun, abu fa ya qi ci ya qi cinyewa, har da dambe. Asshibi naso ta raba amma abu ya fi qarfin ta, cikin sa'a kuwa Matar Yahai ta samu d'aga 'yabbuga ta maka da qasa, ta haye cikin ta, ta dinga kirba,sai da ta farfashewa 'Yabbuga baki sannan Asshibi da Mai buruji suka samu d'aga ta a jikin 'Yabbuga, Lamishi ta ji dadin hakan, dan kuwa ko ba komai an koya ma 'Yabbuga hankali, ta na miqewa ta hau kade jikin ta ta na fadin, "Baki daki banza ba, zaki gani, har gida se hukuma ta kama min ke, bari dan Jummaa ya dawo" "Baku da wanan azziqin da alfamar a Nigeria," "Haka kin ka ce ko?" "Na hwadi," Haka nan suka yi ta sa'in sa har aka kirayi magariba suka tafi gidajen su, Asshibi kuwa gidan su Lamishi ta nufa suka yi ta gulmar sauran. ************************** "Excellency gamu asibiti da shi, ba shi da halin magana shi yassa" "Mi ya same shi halan?" "Allah shi taimake ka wasa ta an ka yi, shi na ya samu rauni" "Allah ya bashi lahiya, ka na ji na ba, wannan ajiyar ina so a qara bata tsaro, gaf nake nai amfani da ita, ba na so Ogan ku ya san me ke faruwa, ka gane?" "Na gane Excellency," "Tau ya yi, ka gaishe shi in ya hwalka" "Zai ji ranka shi dade " Bayan sun gama wayar ne, ya sanar da No 1 duk yadda suka yi da gwamna, cikin jin jiki ya ke d'aga kai, alamar ya ji. Cikin ran shi kuwa ya na tunanin kalar azabar da zai ganawa Mubaraka, duk abinda ya tunano sai ya ga ya yi kadan, qarshe saboda tsananin ciwon kan da yake ji, dole sai hakura ya yi da tunanin zuwa wani lokacin. *Hummm anya ka daku kuwa No 1???* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 35: Satin su Sultana biyu kafin Gwamna ya bata izin fita daga gidan gwamnati, a wannan satikan kuwa duk ta rame, ta yi zuru-zuru rashin ganin Lawwali da bata yi ya fitar da ita daga hayyacin ta, ita kan ta, ta na mamakin kalar soyayyar da take masa, anya wannan soyayyar ba zata zama ajalin ta ba kuwa? Masu tsaron lafiyar ta ta dinga kallo daya bayan daya, sanda ta fito tafiya,dukkan su kamar sabbi ne, bata taba ganin wasun su ba. Juyawa ta yi, ta kalli Hajiya Ikee da ta ke zuba mata murmushi, ta kalli Sultan wanda ke kallon ta da tsantsar kulawa da tausaya wa, ta ce, "Ina driver na?" Hade fuska Hajiya Ikee ta yi, sannan ta bude baki zata yi magana, al'ajabi ya sanya ta hadiye maganar ta. Lawwali ne cikin uniform din shi, wanda da gani ka san sabbi ne, sai dai wadannan ba fari bane, ash color ne, da ratsin baqi a jikin riga da wandon kayan, duk yanda zan fasalta maku kalar kyaun da ya yi ba zai yu ba, sai ido ya gan shi kawai. Hawaye ne kawai ke tsartuwa daga idon Sultana, a lokaci daya kuma ta na dariyar farin ciki, da murnar ganin jarumin maza Auwal din ta. Ita kan ta Hajiya Ikee kasa magana ta yi tsabar kwarjinin da ya yi mata, Sultan kuwa zuwa ya yi ya daki kafadar Lawwali, tare da matsa ta, ya na zuba murmushi, "Me na fada maka game da sa min qauna kuka?" Lawwali dan duqawa ya yi, sannan ya ce, "A min ahuwa ran ka shi dade, an min iyaka da shigowa gidan nan ,yau ma Umarni uwar daki na tabban, ta ce na taho na maishe ta gida, in ban taho ba zata taka daga nan zuwa can gidan da qafa, shi yasa na dawo bakin aiki na, ina fatan za a karbi uziri na" Cikin share hawaye Sultana ta ce, "Mu je" "Ku tai ina? Sulty baby yaushe ki ka hwara kafiya da taurin kai, akan wannan qasqantaccen drivern ne ki ka hwara rashin kunya ko? Mu na hwadi ki na hwadi?....kaiii malam ji nan, bar ganin ka na da qirar majiya qarhi, qarhin mulki ba qarya ne ba, zan iya sanyawa a batar da kai, da kai da kaff dangin ku, ba Lamishi ba ce uwar ka? Ko ba ita ta ba? To zan ci mata mutunci gaban ka, in sa a dauren ku har igiya ta yi saura,in ga uban da ya tsaya maka kafff garin Zamfara, ka rabu da diya ta, tun kana gane hanyar komawa gida,ka karya asirin da ka mata kafin na haukata ka, ka na ji na? Ke kuma wuce mota ta mu tai" Hannu ta sanya ta fizgi Sultana da tun da ta fara zagi da ci wa Lawwali mutunci take kuka ta na bata hakuri, Lawwali kuwa tsaye yake ya na murmushi, babu mai iya karantar yanayin da yake ciki a fuskar shi. A cikin zuciyar shi kuwa, kawai tunanin yanda zai yagalgala naman Hajiya Ikee a dajin su yake, manyan mata masu ji da kan su ma sun nuna su na son Lawwali yaran manya da attajirai sun qaunace shi, a duk sanda Gwamna ya dauke shi suka fita babban taron manya, ya na wahala ya bar wajen bai samu wadan da suka maqale masa ba, to ita sultana daban ce da ba zata ta so shi ba? Tunda jini na tsargawa a jijiyoyin jiki da tsokar ta. Hajiya Ikee ce ta danna Sultana a motar ta, ta zagaya zata zauna, kafin ta zauna Sultana ta fita da gudu ta nufi Lawwali, "Sultan kar ka bari ta tabi wannan dan talakawan, ta janyo mana tsiya a zuri'a, kar ka kuskura ka bari ta tabe shi zan saba maka" Yanayin Sultan ya nuna ba ya son riqe sultana, Amma dole ya riqe ta, dan bai saba sab'a Umarnin iyayen nasu ba, rungume ta ya yi, ita kuma ta na tirjewa ta na kuka, tare da miqawa Lawwali hannun ta, shi dai ya na nan tsaye bai motsa ba, bai kuma b'ata rai ba, hasali ma murmushin nan ne a fuskar shi, Hajiya Ikee na kewaya wa ta daga hannu zata wanke Sultana da mari taji an mata wani irin riqon da sai da ta ji fatar hannun ta na tabo qashin ta. Sultana kuwa ta rintse idanun ta, ta qanqame Sultan, ma'aikatan wajen da dama sun riga sun san Lawwali, tini suka sha jinin jikin su, dan kuwa bacin ran da yake ta boyewa sai da ya bayyana a saman fuskar shi, wanda basu san shi ba kuma a ma'aikatan gidan sun zabura za su kai masa hari, akan me zai riqe hannun matar gwamna haka? Shugaban masu kula da securities ne ya dakatar da su cike da tsoro, kar su ja musu bala'i, Lawwali ya huce akan su. Yan kanzagi da 'yan maula da 'yan siyasan da ke giggilmawa ma sun tsaya ganin ikon Allah, a hankali murmushin fuskar Lawwali ya dawo, sannan ya saki hannun Hajiya Ikee, wadda ta ji kamar jijiyoyin wajen sun tsaya da aiki, wani yammmm, zummmm hannun ke mata, a hankali Lawwali ya furta . "Ran ki shi dad'e,shiga Mota na kai ki gida,daga nan ina da wajen zuwa" Da sauri kuwa Sultana ta bar wajen, har ta na haɗawa da gudu gudu, ta shige motar ta, ta zauna a gaba. Shima shigewa ya yi, ya zauna, ya ja motar, Sultan ma take musu baya ya yi, cikin tsananin fushi da jin nauyin mutanen da suka zuba mata ido, Hajiya Ikee ta fada motar ta ta zauna, jan ta akai motocin da ke take ma nata baya suka bi su. Lallai idan Gwamna ya dawo daga tafiyar da ya yi, za a yi ta ta qare, maganar Lawwali ta zo qarshe a shafin rayuwar su. ************************ A ranar da No 1 ya ji sauqi a ranar ya shirya dan zuwa maboyar da aka ajiye su Mubaraka, duk abinda yake No 4 na kai wa Oga bayani ta message, Oga ya gama shirya duk yanda za a yi, jiran zuwan No 1 kawai yake. Agogon shi ne last abinda ya daura, sannan ya kalli No 4 ya ce, "Mu tai, ka kai ni, da ina iya tuqa motar ma da kai na zan je, ba ni buqatar rakiya, amma ba zan iya ba saboda yanayin da nake jin kaina a ciki" "Kar ka damu, zan iya kai ka duk inda ka ke buqata, kai dan uwa na ne" "Na gode, mu tai ko" "To Oga" Sun fita daga dajin No 4 ya koma wajen No 1 dan zuwa maboyar su Mubaraka. No 1 na gaba a mota, No 4 ya aikawa Lawwali saqon gasu nan sun bar gidan. Shi kuwa waya ya yi ma sabbin yaran da ya horar, guda bakwai, su ma suka tabbatar masa da a shirye suke. Cikin duhun magariba suke tafe, kafin su isa har an yi sallah, wanda su ba ta gaban su, sunan musulmai ne kawai da su, amma duk wani abu da Musulmin kirki yake su ba sa yi. A qofar gidan su ka kashe motar, su ka fita, No 1 ne a gaba, ya na dingisa qafa, ya sanya key ya bude qofar, ya na fito. Kafin ya kunna fitilar ya ji fito a bayan shi,cikin sauri da faduwar gaba ya lalibi makunnin fitilar dan kunnawa, hasken ta bai gama haskaka ko ina ba wani daga matasan ya sa bindiga ya harbe kwan fitilar, qara da ihun 'yan matan ne ya cika gidan,tun da suke a gidan basu taba jin an yi dambe ba ma, ballantana harbin bindiga, yau tasu ta qare. No 1 kuwa asalin matsoraci ne dama shi, makircin shi da iya hada tuggun yaqi ne ya sanya aka bashi muqamin da yake da, amma ba jarumta ba, hankalin shi in ya yi dubu ya tashi, wani irin duka aka sakar mishi a qirjin shi, da bakin bindiga, sai da ya fara jin jiri, daya daga matasan ne ya wuce su, ya bude dakin , ya fidda yan matan, sannan ya kai su mota, tayar da motar ya yi, ya shiga gari da su,sai kuka suke, su na bashi hakuri, sun fara bashi haushi, ta madubi ya ga yarinya daya ko a jikin ta, kallon waje kawai take, ta na lumshe idanu, ita bata damu ba kenan ko sace ta za ai? "Kaiii dalla kun cika min kunne, Oga ne ya aiko mu, wace ce Mubaraka cikin ku?" Da sauri suka nuna ta, cikin ran shi ya ce, 'Dole ki taurin rai yarinya,' Sai da suka shiga garin sosai,ya tsaida mota ya wurgawa su Murjanatu kudi, ya ce su bace masa da gani, in sun je gida kome aka tambaye su, su ce basu sani ba, idan qaiqayin baki ya sa suka fadi wani abu, Oga da kanshi zai sa a kashe ahalin su gaba daya . Sai kada kai suke, su na tabbatar masa sun gane, ba wanda zai ji komai, sun yi alqawari,godiya suka dinga musu, sannan suka fita daga motar a guje, yanzu tsoron yarda da mutane ma suke, tunda kusa da unguwar su ne, ko abun hawa ba su nema ba, da qafa suka nufi gidan su. Mubaraka kuwa gidan Oga aka yi da ita, Lawwali na can ya yi order din abinci a best restaurant na cikin garin Zamfara, ya haɗa mata ruwan wanka da kan shi,ya gyara ko ina da kan shi,yaran shi na ta so su taya shi yaqi amincewa, so yake ya burge Mubarakan shi,so yake ya mata tarba ta musamman. Ya na da qarfin kawar da duk wanda ya so, ba tsoro bane ya sa shi jinkirtawa har wannan lokacin, ba kuma gudun tashin hankali bane, kawai komai da lokacin sa, yanzu ne lokacin da ya debar wa Gwamna da iyalan shi,duk da a tsarin shi sai gwamna ya dawo, amma inaaaa ba zai iya jira ba, dan wannan karon bai neme shi ba, bai bashi wani aiki ba, ya tabbata akwai wani shiri mara kyau da yake akan shi,gashi yau Hajiya Ikee ta tsokane shi iya tsokana. Ya na tsaka da kallon yanda ya gyara wajen, ya ji horn din mota,da sauri ya fita ya tsaya,yaran da ya debo guda uku, daya daga cikin su ne ya bude gate suka shiga. Zuciyar Lawwali ta karye da ganin qanwar shi, idanun shi ne suka cika tafff da hawaye, cikin azama ya nufe ta ya rungume ta, sai da ya raba ta da qasa. Jin ta a faffadan qirjin shi ne ya sanya ta sakin kukan da ya taho da wani irin qarfi da ciccira, da kuma daukewar numfashi, qoqari yake ya kwantar mata da hankali , ta nutsu ta dena kukan amma inaa, sai yi take, ta na qarawa, duk ta gigita shi,  ta kidima shi,rabon shi da shiga irin tashin hankalin yau tun sanda ya tabbatar da batan ta. Daukan ta yayi cak ya shiga da ita ciki, daga shi har ita hawaye suke, gashi yanayin yanda take kuka da ciccira yaqi tsayawa. Zaunar da ita ya yi a saman cinyar shi ya na lallashi sun jima a haka daga baya ya ji ta yi shiru,ta na ta sauke ajiyar zuciya mai qarfi, ya na dago ta ya ga ta yi baccin wahala. Ba datti a tattare da ita, ba yunwa a tattare da ita, hasali ma gani ya yi kamar ta yi qiba ta yi haske. Dakin da ya tanada domin ta, ya nufa da ita, dauke a kafadar shi, ya kwantar da ita, zama ya yi a bakin gadon ya na kallon ta, cike da tausaya wa, shi ne Silar shigar ta wannan mawuyacin halin, amma daga gobe komai yazo qarshe . Cikin fushi ya miqe, ya sanya rigar shi a saman vest din jikin shi, ya dau bindigogin shi, sannan ya dau key din motar shi, basu zame ko ina ba sai gidan da aka ajiye su Mubaraka. Ya na shiga ya tadda su a tsakar gida, No 1 cikin jini, No 4 na zaune a kujera, sai sauran yaran a tsaye sun yi shirin ko ta kwana. Lawwali na shiga kowa ya miqe da kyau, direct wajen No 1 ya nufa, ya daga shi, ya dinga naushi, sai da ya sumar da shi sannan ya ce a sheqa masa ruwa a dakko shi. Ba musu haka suka ja shi a qasa kamar buhu, suka wurga a bayan mota, suka rufe gidan suka tafi. Kowa dai ya san mutum kamar Lawwali zai wahala ace maboya daya gare shi,dan haka daya daga cikin maboyar shi suka nufa, waje ne kamar daji, ba gida gaba ba gida baya, ihun ka banza. Su na shiga Lawwali ya bada umarnin a daure masa No 1 sama a qasa, sannan a banqara hannayen shi baya a daure. Cikin abinda bai fi minti goma ba har sun gama. A wahalce No 1 ke magana, duk qoqarin su na su ji kasawa suka yi, sai da wani a cikin yaran Lawwali ya kasa kunne a bakin shi sannan ya ji me ya ce, dan murmusawa ya yi sannan ya ce, "Oga ya ce ka kashe shi dan Allah" Banza Lawwali ya yi da su, ya kammala hada abinda yake haɗawa, ya sa suka juya masa bayan No 1 ya sa a kunna Camera a dauki abinda yake yi. Ana juya masa bayan nashi ya debi ruwan acid ya kwara masa a bayan, wata iriyar qara da ihu No 1 ya saki, daga baya ya yi shiru, jikin shi ya saki, suma na biyu kenan, jikin No 4 sai rawa yake, tsabar tashin hankali, wannan azabar ya gudar wa kan shi tun asali. Kamar Lawwali ba zai magana ba, ya duqa ya kama fuskar No 1 ya ce, "Amma dai ka hi kowa sanin ba aikin Allah muke ba ko? Da aikin Allah muke da masallaci za a same mu, dan haka in ka na ganin ka hwara bautar Allah da gaskiya, daga yanzu tau ka hwara addu'a tsakanin ka da Allah'n shi dau rayuwar ka ka huta,amma da kai, da duk wani mai hannu cikin sace qauna ta, ko wane ne shi,ko uba na na sai na ga bayan shi, ko shi anka bawa mulkin qasa baki daya ba gwamna ba, sai na ga bayan shi , wannan alqawarin Awwal yayan Mubarakaa ne" Da qarfi ya saki fuskar No 1, jikin shi ya hau lilo a wajen. Kashe Video akai, ya amshi wayar shi, ya bar wajen, No 4 ya bi shi, cikin matsanancin tsoro, "Ka shirya komai akan abinda muka yi magana ?" "Eh...oga...na kammala komi" "Good, gobe da qarhe shidda na sahe zan same ku a tasha" "To Oga" "Kafi kowa sanin hali na in aka ci min amana, kar ka yi wasa da amana ta, rayuwa ta zan dauka na baka, kar ka ci amana ta, Taheer in ka bari quda ya sauka akan Barakana, hummm" Iya abinda Lawwali ya fada kenan,ya fada mota ya bar wajen. ************************** Mubaraka bata tashi farkawa ba, sai ukun dare, ko da ta farka a tsaye taga Lawwali ya na kallon ta, hannu ta miqa masa cike da shagwaba, shi kuwa da sauri ya kama, ya zauna a gefen qafar ta, ya kai hannun ta bakin shi ya sumbata. Murmushi ta yi, sannan ta ce, "Yah Auwal ina so na ga Ummaana" Wata tsawa ya daka mata sai da dakin ya amsa, Ita kuwa ta manne da jikin gado tsabar tsoratar da ta yi, nan da nan ta hau kuka, jikin shi ne ya yi sanyi, a hankali ya daidaita nutsuwar  shi,ya zauna gefen ta, ta yi baya, ta na zubar da hawaye, "Barakana duk irin kewar ki da na yi, ki rasa me zaki fara magana akai, sai mutanen da basu damu da batan ki ba? Mutanen da ba su daina duk wata harkar su ta yau da gobe ba akan batan ki? Barkana Ni kadai ne na damu, Ni kadai ne na ke kasa bacci saboda rashin ki, basu damu dake ba, gobe zaki bar garin nan, ki yi nesa da kowa, ban damu da abinda zai same su ba, ke ce rayuwa ta, kowa ya san da haka,abokan gaba za su iya amfani da ke dan cutar dani, dan Allah kar ki min musu, ki bi duk abinda na ce ki yi, kin sani ba zan cutar da ke ba ko?" D'aga kai ta yi a hankali, maganganun shi sun qona ran ta sama da yanda wuta ke qona leda, ta yaya za a ce iyayen ta basu damu da batan ta ba, iyayen ta fa na cikin ta, amma ba abun mamaki bane, ga duk wanda ya san halayyar su. "Yah Auwal na ji na amince, amma ina neman alfarma" "Kar ki ce mun zaki je ganin su" Shiru ta yi ta na kuka a hankali,sautin kukan ta kamar ruwan dalma ake diga masa a tsohon ciwo, "Ok tau ya isa haka nan, ina kai ki gobe" "Yah Auwal ina so na ga Aunty Sultana, na yi kewar ta, na san ta damu da bata nako? Har mafalkin ta ni kai" Murmushi mai sanyi ya yi, wanda shi kan shi bai san ya yi ba, Mubaraka na ganin haka ta tabbata har yanzu akwai soyayya a tsakanin su . "Tayi kewar ki fiye da yanda baki tsammani, amma lokaci ba zai bari ba, na san yanzu haka ta na sallah, bari na kira na hada ku,gobe da asuba zan kai ki gida, daga nan mu wuce tasha, duk wanda kin ka gani a matsayin wanda zan hada ku, ki yarda da shi, na san ko waye shi,ki yarda da shi,ba zai cutar da ke ba, na sai Maki waya da komai da zaki buqata, na sai gida duk da sunan ki, na sai motar da za a dinga hidima dake makaranta da duk wani abu da zai inganta rayuwar ki Baraka na na yi miki, hankalin ki kawai ni ka so ki kwantar,duk sanda ki ke da buqatar gani na ki hwada min ko a waya ne zaki ganni ke ji?" Ba abinda take in ba kuka ba, ba ta jin za ta iya jure zama ba shi, amma ba za ta iya masa musu ba. Da misalin hudu da rabi na asuba ya kira sultana, kamar ya sani kuwa sallah take, sai da ta idar ta kira shi, jin Muryar Mubaraka ba qaramin dad'i abin ya mata ba, ajiye wayar ta yi ta yi sujjadar godiya ga Allah sannan suka hau hira, duk kalar tambayar da Lawwali ya hana ta amsawa bata amsa ba, sai dai ta ce bata sani ba itama. Biyar saura minti goma suka yi sallama Mubaraka ma ta yi alwala ta yi nafila. Ta na idarwa Lawwali ya sa ta yi wanka ta ci abinci, sai gidan Alhaji Dan Talo....... *Ai na manta ashe bai je Makka ba😂😂🤭* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 36: Tun sanda Lawwali ya girgide musu qofar ya jingine, har yanzu ba a samu mai zuciyar da ya tsakura daga kudin da Lawwalin ya ke basu ba aka gyara qofar, dan haka yau ma da qafa ya daki qofar ta bude, ta na kaiwa qasa hankulan mutanen gidan da maqotan su duk sai da ya tashi, domin qarar ta yi matuqar tsorata su. Mubaraka ce ta kalle shi ta kada kai, dan ta gama fuskantar a fusace yake, ba dan ta matsa masa ba ba za su je ba. A tsaitsaye suka tadda mutan gidan, cikin sallallami da jimamin me ke faruwa, idanun su na sauka akan Mubaraka, murna ta kama su, musamman su Jameelu, wanda sai da suka runtuma a guje wajen ta, za su taba ta Lawwali ya dakatar da su, ba musu suka ci birki. "To kin gan su mu tafi?" "Yah Auwal ka bani minti goma dan Allah" "Whatt? Minti goma? Mi za ki yi halan?" Takawa ta yi gaban Lamishi da ke ta wangale baki, har cikin tsokar zuciyar ta ta ji dadin ganin 'yar ta ta, haka ma Mai buruji da Dan Talo, amma su na jin tsoron zuwa gare ta ɗan tijarar nasu ya musu rashin mutunci. "Umma na, na dawo, Alhamdu lilLAAH, Yah Auwal ya kwato mu daga hannun azzaluman da sun ka sace mu ni da su Murjanatu, Ummana na yi kewar ku sosai, duk sanda na tuna ku ina can, sai na ji hankali na ya tashi, sai in dinga hango wa zai dinga miki girki in ba abinci? Wa zai gyara miki daki? Wa zai zanka kai miki ruwan wanka ke da Baba, wa zai zanka shara da wanke-wanke? Ummaa na sai in dinga tuna wa zaki dinga yi wa hwada in ya yi ba daidai ba? Hankali na na tashi inna tuna duk sanda ki ka tashi baki ganni ba wane irin qunci zuciyar ki za ta shiga,.......ashe.....ashe ni damuwar banza nikai, hankalin ku kwance shike da bata na, na so matuqa na ci gaba da zama da ku, domin ko zuciyar ku ba ta so na, ni tawa zuciyar na son ku da qaunar ku, amma a halin yanzu zan bi yaya na, duk inda ya sanya qafa nan zan aje tawa, na gode da zama iyaye da kuka yi a gare ni na tsawon shekaru,za ku ci gaba da kasancewa iyaye na har abada, sai watarana" Cikin hawayen da ke ta zuba mata ta juya za ta koma wajen Lawwali da zuciyar shi ke ta tafasa, ya na jin zafi da takaicin abinda suke wa Mubaraka duk da ta kasance yarinya mai biyayya, Lamishi kuka take sosai na nadamar abubuwan da ta aikata, amma ba yanda zata yi ta hana Mubaraka bin Lawwali, dan bama ta isa ba, d'an zagi da fadan ma da yake d'aga mata qafa ta na masa yanzu babu dama, ya toshe hanyar su, dan yanzu zai hargitsa musu lissafin gida, juyawa Mubaraka ta yi ta kalli Lamishi da ke kuka qasa qasa, ita da Mai Buruji, sannan ta tsaya ta ce, "Yauwaa wane suna ma ki ke yawan kira na da shi ? GANTALALLIYA yar iska, da sauran su ko? To ina mai maki bushara da ni din nan, da kike kira da gantalalliya na godewa Allah da ya sa bani na dauki qafafu na na tafi gantali ba, daukata an kai aka kai ni wajen gantalin, me ki ke fata na aikata a wajen Gantali?...." "Baraka, mu je" Ba ta yi shiru ba, so take ta bawa Lamishi labarin abinda ya same ta a wajen, amma ba zai iya jure sauraran abinda aka mata ba, jikin shi har rawa yake saboda bacin rai, Lamishi kuwa kuka take bil haqqi, a rayuwar su kaff Mubaraka bata taɓa maidawa wani magana haka ba, me aka mata a can din? Me ya same ta, Lawwali ne ya daka mata tsawa a qoqarin ta na son sai ta qarasa labarin ta, jan hannun ta ya yi ta fuskance shi, su na hada idanu ta sanya kuka sosai, da qarfi ya rungume ta a jikin shi ya na numfashi sosai, dan kuwa shi ma kukan yake ji. Maida Mubaraka gefe ya yi, ya kalli iyayen nashi ya ce, "Wannan kukan munafurci  na ku kai wallah, ai murna za kuyi ku taka rawa, abinda kuke so, ya samu diyar ku, kullum fatan ki ta yi yawo ko? Ta yi gantali, ke kin san ma'anar Gantali kuwa? Ki ke hada d'iyar ki ta cikin ki da wannan mummunar kalma? Kin yi kuskure matuqa, ga gangali nan ki na gani, ko da shi ke ke rayuwar da muke ciki bata dame ki ba, ba a maganar mijin ku (subhallah mahaifin shi ya ke kira da mijin su) shi dai gashi nan ne d'ai, a dahwa a bashi ya ci shi kwanta da ku, ku haihwa, ya shiga gari ya yi hira da abukkai shi dawo, shi ci abinci, shi tai yawo, shin baka gajiya da aiki guda yau da gobe ba wani sabon abu da zaka qirqira da zai amfane ka da iyalin ka? Ko ni da nike wannan harka watarana gajiya nikai, to yanzu burin ku ya cika, kun haifi kalar diyan da kuka so, sai ku yi ta kuri a unguwa, mu tai, lokaci na tahiya" Har sun kai soro ya koma ciki, a fusace ya debi dika kudin aljihun shi ya watsa musu, ya daki bokitin da ake dama kunu a gidan, ya ce, "Gashi nan, ga abinda kun ka fifita sama da jini da tsokar ku,...ohh yi hankuri na hwashe muku bokiti, ku sai wani" A tsaye a bakin mota ya tadda Mubaraka ta na rizgar kuka, al'ajabin iyaye kamar su Dan Talo take yi, wai wasu mutanen a duniya me suka dauki aure ne? Mai suka dauki samar da zuri'a ne, shin sun cancanta ma su zama iyaye? Ba su bar wajen ba sai da Lawwali ya lallashe ta, ya bata baki sosai, da yi mata nuni da rayuwar da yake mata fata a gaban rayuwar ta. Cikin gidan Dan Talo kuwa bayan tafiyar su Mubaraka, Lamishi d'aki ta shiga ta ci gaba da kuka, tare da danasanin abubuwan da ta dinga aikatawa, ba abinda ke mata gizo sama da kalaman Mubaraka na qarshe, shin me ya same ta? Mai Buruji kuwa tattare kudaden ta yi tsaf, ta na gamawa Dan Talo ya je gaban ta, ya ce, "Bakkani su nan (bani su nan)" Wani kallon tara saura kwata ta masa, sannan ta ce, "Me ya sa da ina tattarawa baka taya ni ba, sai da niqqare, zaka ce na baka? Tau ban basuwa, yaya zan bawa" Cikin kad'a kai, da kyacci (qwafa)ya bar gidan, domin kuwa haske ya bayyana sosai, kowa na ganin kowa, gari ya washe. A tasha kuwa Mubaraka kuka ta sanya ta na tirjewa akan ba zata bi su No 4 ba, tun Lawwali na lallashi har ta suqurar da shi ya hau fada, "Gidan uban wa za ki zauna in baki bi su ba? Waje na? Rayuwar ki ta zauna cikin hatsari? Na rasa nutsuwa ta? Ko na kasa aiwatar da ayyuka na na yau da gobe, ko kuma wajen wadancan mutanen ki ke son komawa(iyayen su ya ke nufi). Ita dai ta yi dif hawaye na zuba, ganin yanda take a tsorace ne ya sanya shi jan ta gefe ya daga kan ta, ya na share mata hawaye, sannan ya rungume ta, kukan ta ne ya qaru, ita dai da zai taimake ta, da ya barta a duk inda ya ke, bata son barin garin, musamman da No 4. "Baraka na ki saurare ni da kyau ki ji, Taheer ba zai taba cin amana ta ba, na san inda zaku zauna, na san komai game da rayuwar shi, ba zai cutar da ke a kan sanin shi ba, ko wancan bai san ke za a dauka ba , sanda ya sani lokaci ya qure, na yarda da Taheer kamar yanda na yarda da kai na, dan Allah kar ki qi binai, hankali na zai hi kwanci in ki na can,ke ga shi na da iyali, ba shi d'ai na ba, ga mahaifiya tai, ga mata tai,ga diya nai, ba ke dai ta ba hwa" Ita dai jin shi kawai take, ta hakura zata bi su,amma ba dan zuciyar ta na so ba. Lawwali na tsaye ya na ganin yanda Mubaraka ke share hawaye, daga musu hannu ya yi sanda motar su ta tashi. Cikin tsananin hawaye ya juya ya nufi motar shi, tunda yake a rayuwar shi yau ce rana ta farko da ya yi addu'a ya roqi Allah wani abu da kyakkyawar zuciya. "Ya Allah ka kare min qauna ta, Allah ka san wad-da ni ka son ta, Allah duk inda take ka zama gatan ta ba na kusa balle na bata kariya, Allah ka kare min ita, kai na mai kare bayin ka a duk inda suke, Mubaraka bata da lehin komi, Allah ka sani komai ke faruwa laihi na ne, kar ka hukunta qauna ta da lehi na" Ya jima zaune a motar idanun shi sun yi jawur saboda kuka, time ya kalla ya ga bakwai da rabi, cikin sauri ya nufi gida kafin ya isa takwas ta wuce, wanka ya fada, ya yi a gaggauce, ya na shiryawa wayar shi na ringing bai dauka ba dan ya san ko waye. Sai da ya gama shiri tsaf, ya ci abinci sannan ya fesa turarukan shi masu qamshi mai dad'i, sannan ya samu yaran shi da ke gidan ya sallame su, tare da basu umarnin komawa can sansanin su. Ya na tafiya kan ya isa gidan Gwamna ya yi waya da wanda ya bawa tsaron No 1 ya ji ya suke, sun sanar da shi duk irin abinda ya ce su yi ba wanda ba su aikata ba, ya na nan ya na jin jiki, murmushin jin dadi ya yi, sannan ya kashe wayar shi. Ran shi fess ya shiga gidan, a qalla ya sauke manyan nauyin da suke kan shi, saura na gaba. A tsaye ya gan ta, ta na ta safa da marwa, hankalin ta a tashe, siririyar dariya ya saki, dan kuwa ya san sai ta masa shagwabar ta, akan dad'ewar da ya yi, ta bayan ta ya ja ya tsaya, tare da kama kunnuwan shi, qamshin shi ne ya sanya ta tsayawa cak dan kuwa ta san ya iso kenan. Cike da shawagabar kuwa ta juya, ta langwabe kan ta gefe daya, ta na kallon shi da wani irin sassanyan kallon da ya sa jikin shi mutuwa. "Me ya sa ka ke min haka? Ka na so zuciya ta ta buga ko?" "Tabdi, ashe dama zuciyar ki bata bugawa? To da inji ne a jikin ki ki ke amfani da shi?" Cikin kama haba da kallon ta a karkace yake maganar, hakan da ya yi ba karamin dariya ya sanya ta ba,ai kuwa dariya ta dinga yi, shi ma ya na taya ta,  kallon yanda fuskar ta ke sheqi da walqiya yake ta yi, a hankali ya furta, "Sultana ke kyakkyawa ce, fuskar ki na sheqi kamar hasken farin wata, zan so ki kasace cikin hwarin ciki har qarshen rayuwar ki" A hankali ta daina dariyar ta ɗan sunkuyar da kan ta, ta na murmushi, "Ameeen Allah ya sa, amma ka dena zuga kyau na, duk yadda  ka ke ganin kyau na, naka ya wuce nawa," Kama baki ya sake yi, sanan ya ce, "Ran ki shi dade mu bar wagga magana, namiji ina yaga kyawu? Namiji iri na dan talakawa taya zai zama mai kyau?kyau ai shi na wajen ku diyan masu kuddi, mai da sabulu da komi da kuka amfani da shi daban ne da namu," Ran Sultana ya baci da kalaman shi, ya kuma kula da hakan, dan haka sassanyar dariya ya yi, ya ce "Yi hankuri wasa ta nikai, dama dan in ga kin turo dan karamin bakin nan na ki" Murguda masa bakin ta yi, ta wuce jikin mota ta na murmushi. Hajiya Ikee na tsaye a jikin window ta na kallon su, Lawwali ne ya daga kai ya kashe mata ido daya tare da dora yatsun shi biyu a gefen goshin shi, ya yi saluting din ta ya bi sultana, da sauri ta saki labulen ta yi baya. "Dan banzan Yaron nan dama ya na gani na?" Hannun ta ta kalla da ya kumbura ta inda ya matsa mata jiyan, ta saka qanqara ta saka ruwan dumi ta gasa har yanzu ciwo yake mata. Bari zai ci qaniyar shi duk sanda Gwamna Halliru ya dawo daga tafiya, yaron shi zai ara mata a je har gida a kashe mata shi, in ba ya duniyar gaba daya ta ga yanda zai auri sultana. Bari ma zata yi maganin shi da kan ta ba sai ta jira gwamna ba. ************************* Sun isa cikin garin Kano da misalin qarfe uku na rana, a unguwar 'Yan kaba anan Lawwali ya sai masu gida mai kyau, da gate, matar Taheer mai suna Fateema nutuniyar kirki ce, ita da mahaifiyar shi,su na ce mata Goggo Larai, sai yaran shi biyu ,Nusaiba da Hamdiyya. Da addu'a dauke da bakin su ta neman tsari daga sharrin shaidanun aljanu da mutane suka shiga gidan,wata rantsattsiyar mota ce a harabar gidan, Taheer kallon Mubaraka ya yi, ya ce "Qauna ta wannan  gida da mota hwa duk na ki na" "Yah Taheer namu dai ba nawa ba, kai din a matsayin yaya ka ke a waje na,dan haka abinda na mallaka namu ne duka" "Allah shi bani ikon sauke nauyin nan Mubaraka" Mahaifiyar shi da matar shi suka taya su amsawa da Ameen. Ko da suka shiga ciki abun ya ba mubaraka mamaki, daga waje gidan bai da wani hatsabibin kyau, amma ta ciki ya qayatar da ita matuqa, bayan sun shiga kantamemen parlour mai dauke da dakuna uku, da kitchen da store akwai wata qaramar qofa, Taheer kiran Mubaraka yayi, ya ce ta bi shi . Dama ita bata wani zo da kaya ba, dan haka bin shi ta yi ziqau ziqau, su na shiga ta ga babban parlour again, da daki biyu, dakunan ya lalleqa ya na mata bayani, kowanne daki akwai bayi ciki, abinci kuwa Fateema ce za ta dinga dafawa ana kawo mata, Lawwali ya yi hani da babbar murya bai yadda ta yi aiki ba, ya bada umarni a kula da ita ne kawai. "Yah Taheer ban qi ta taku ba, Amma dan Allah a bani su Hamdiyya su dinga taya Ni kwana tsoro nika ji, kuma dan Allah kar a hana ni aiki, in bana aiki rashin lahiya ni kai, jiki na ciwo yakai," Yar dariya ya yi, sanan ya ce, "To mubaraka, ki zanka gyara bangaren ki, shi kenan?" "Girki hwa? Ni fa ina son girki Yah Taheer" Cikin shagwaba ta fadi hakan, murmushi kawai yayi, sannan daga baya ya ce, "Tau wannan kuma sai na yi wa Fateema magana,dan yanda Oga ya min warning har ita da Goggo sai da an ka yi mata warning, in ta aminceee tau sai ku na yi tare" "Dan Allah ka hwada mata ba komi, Yah Auwal baya gani, kuma ba zan hwada masa ba" "Tauu ya yi, bari na tai na samo mana abinci" "Na gode" Kallon ta ya yi, ya yi murmushi ya fita. Ya na fita ta zauna sai hawaye. Yanzu wannan gidan da ace da kudin halal aka same shi ai mutum ya gama more wa, amma da kudin haramun ne, kwata kwata abun bai burge ta ba, amma ba yanda zata yi, yanzu ta samu dama ne da zata duqufa wajen roqon Allah ya shirya mata yayan ta, ya ganar da shi gaskiya, ya bar mummunar dabi'ar shi, yanzu ba lokacin hutu bane, lokaci ne na ibada. ************************* Da misalin biyu na dare ya ji motsi ya yi yawa a gidan nashi, kamar ana dira ta katanga, da sauri ya kashe fitilar dakin nashi, tsabar kwarewa da fada da kuma zama cikin shirin ko ta kwana ya san inda komai yake a dakin nashi, cikin sanda ya gama d'aukan duk abinda yake buqata. Qofar dakin ya bud'e a hankali ya leqa parlour ta jikin glass din window ya ke ganin gilmawar mutane, wani waje ya nufa a cikin duhun ya danna wani makunni kamar makunnin wuta, kujera ya samu ya yi zaman shi. Daya daga cikin mutum ukun da suka haura gidan na Lawwali ne ya kama hannun qofar, da wani dan qaramin qarfe ya na so ya bude qofar da shi, amma sai ya ji wani irin shocking ya kama shi, ya ja hannun shi ya ja inaa ya maqale, ihu ya dinga zabgawa wanda ya sa abokan aikin nashi tsorata kar a kama su, su ka ruga da gudu suka haura katangar suka bar gidan, Lawwali na jin haka ya miqe ya gyara bindigar shi, ya kunna hasken parlour sannan ya kashe wajen da ya danna dazu. Matashin ya fadi yifff a qasa. Makulli ya sa ya bude qofar parlour ya shigar da matashin sannan ya rufe qofar ya sake danna abinda ke saka shocking in an taba qofar . Madara Lawwali ya je ya kawo mai sanyi ya ba matashin ya ce ya shanye. Kamar wanda yake a yunwace, haka ya dinga diddikar madarar  nan, ya na gamawa Lawwali ya ce, "Wa ya aiko ku? In ka yi min qarya a maganar farko sai na fasa kan ka,na san wa ya aiko ku, ina dai son ji na daga bakin ka" Cikin in ina matashin ya ce, "Matar gwauna Hajiya Ikeeleema ta wallah, dan Allah ka yi min rai, ban san gidan ka na wanga ba, ta dai bamu adireshi na kawai, tace mu kashe duk wanda shike cikin gidan ga, dan Allah...." "Ya isa haka nan, ba abinda zan maka, na san ba ka san waje na an ka aiko ka ba, tashi ka zauna, ni zan kwanta gobe da sahe kar na tashi na gan ka gida na, zan manta dana tab'a sanin ka," "To Oga, ni yanzu ma in ka min izini tafiya zan yi" Daga kafada Lawwali ya yi, ya ce, "Wad-da ka ga dama" Lawwali kashe shocking din ya yi, ya shige dakin shi ya fada gado ta ruf da ciki. "Mtsss Hajiyar ga qaramar yar tasha ta wallah, diyan ga zata turo min su kashe ni, ni ta hana min kwana, mtssss" Pillow ya ja ya rufe kan shi, ya na son ya samu bacci kafin safiya.......... *Allah dai ya biya ogaaaaa* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 37: Duk jikin Lamishi ya yi laushi, bata da burin da ya wuce na ta san a wanne hali Mubaraka take yanzu, shin Lawwali gidan shi ya maida ta ? Ko itama ya tsunduma ta harkar shi? Bata da amsar tambayar nan, gashi 'yan gulma har sun yad'a komawar Mubaraka, ana ta zuwa barka, da kuma son ganin ta, amma sai dai su yi qarya su ce ta fita da yayan ta wajen 'yan sanda, dan a ji su waye suka sace ta. Kwana hudu mutane basu daina zuwa jaje ba, har iyayen su Murjanatu sun je, dan a tambayi Mubaraka su waye suka sace su, tunda su sun qi fadi, ko da suka je suma aka ce musu har yau Yayan ta bai maida ta ba. Labari ya fara sauya salo, wasu na ganin ko yayan ta ya aurar da ita ne? Wasu na ganin qarya ne dama ba a gan ta ba, aka ce an gan ta,wasu na ganin tsoro ne ya sanya aka boye ta, kowa dai da abinda ya dasa a zuciyar shi, yake gani kuma shi ne daidai(haka halin dan Adam yake, sai ya sa maka maganar da ba ita ce a zuciyar ka ba a bakin shi) Mai Buruji ta shawarci Lamishi da komawa wajen aiki, tunda dai an ga Mubaraka, yanzu zama shirun zai sa mata kadaici. Haka kuwa aka yi, wata ranar Litinin da sassafe, suka shirya, suka dauki hanyar gidan gwamna Halliru, adaidaita na aje su, suka hango Lawwali tafe, zai je gidan shi ma. Lamishi bata taɓa tsayawa ta masa irin wannan  kallon ba, kallon uwa da d'a, kullum kallon wani abu mara daraja da amfani, take masa, da ace tun sanda ya na da halin kirki take masa kalar wannan kallon, wataqila da Allah ya tallafa mata sun zama kamar sauran yara na gari. Ciki suka shiga suka jira zuwan shi. Ko da ya zo yi ya yi kamar bai gan su ba, Mai Buruji ce ta ce, "Lawwali Barka da swahiya," Ko kallon inda take bai ba, ya je ya jingina da motar Sultana, Lamishi kuwa bata yi fushi ba, bin shi tayi, ta hade hannayen ta ta na wasa da su, ta ce, "Yayan Mub...." "Kar ki sake ki ambaci sunan ta abakin ki, zan manta ba a gida muke ba na karta Maki rashin mutunci,me ki ke so? Kuddi na ki ka bida?" Wasu hawaye ne masu dumin gaske suka zuba mata, da hanzarin ta sa hannu ta share su, "Uhmm dama cewa na yi, ku na tare da ita ne? Na ga baka maishe ta gida ba tun sanda ka kawo ta mun ka gane ta" "Ban yi niyyar maishe ta gidan ba, kuma ba amfanin ki san inda take, ko akwai? Ke dai san ni ba zan cutar da ita ba, ke kuma fa? Duk duniya ta shaida ke ki na iya kashe ta ma da hannun ki, tunda kin ka kashe ta da bakin ki" Ita kan ta ta na mamakin yanda maganganun Lawwali ke qona zuciyar ta, ta ya uwa za ta kashe dan ta? Duk da ta sani bata kyauta ba matuqa, amma ba za ta iya kashe Mubaraka ba, jinin ta ce. Murmushin mugunta Hajiya Ikee ta yi, a daidai lokacin da ta saki labulen d'akin ta, ta d'auki dan kwalin ta ta d'aure kan ta da kyau, ta fita daga d'akin ta, sauka take a matattakalar benen, cikin sauri, dan bata son Lamishi ta bar wajen, bata isa ba. Ta na fita kuwa Lamishi na isa bakin qofar shiga cikin gidan, dan gudanar da aikin ta, Mai Buruji ma ta wuce nata aikin. Da sauri Lamishi ta yi baya, tare da duqar da kan ta, ta hau gaishe da Hajiya Ikee, cikin tsawa da hargowa Hajiya Ikee ta bangaje Lamishi ta fadi qasa, sannan ta ce, "Keeee! Mahaukaciya, daqiqiya, mai warin talauci, halan baki gani ne? Ko kuwa hayaqin icce ya makantar maki da ijiya? (Idanu)" Mamaki ne mai girma a zuciyar Lamishi, ta san Hajiya Ikee bata da mutunci, amma haka bai taba shiga tsakanin su ba, duk kalar rashin mutuncin da take musu baya wuce akan aikin su, su na gyarawa ta bata, ko in Sultana na musu magana ta yi ta hantarar Sultanan ta na hana ta magana da masu aiki, amma wannan bangazar da zagin rashin mutuncin daga ina? "Ran ki shi dade ki yi min ahuwa, ban gan ki ba" Sai da Hajiya Ikee ta kalli inda Lawwali ke tsaye, sannan ta ce, "Ina hwa zaki ganni ana Allah Allah a shigo AC, a yi aiki a saci abinda aka sata a tai gida, tau bari ki jiya, daga yau, duk na qara diba abu ban gani ba, sai nasa an daure min keyya, da shegiyar kishiyar can taki, da duk wani dangi naki, barauniyar banza barauniyar yohi" Wani irin tashin hankali ne ya shiga Lamishi, a barta da rashin mutunci, da rashin ragawa kowa, gulma da munahurci,amma banda sata, sataa, ita Lamishi ake zargi da Sata? Wai me ke faruwa ne yau? Ko dan dai ta jima bata zo bane? "Ran ki shi dad'e ki yi min ahuwa, diya ta ce ta bace, ba mu gane ta ba, sai kwanan nan, shi yasa bana zuwa, na aiko Mai Buruji ta sanar da ku," Sultana da ta fito ta ga Lamishi a qasa, a wulaqance, sai ta ji ran ta ya ɓaci, ko da ba mahaifiyar Auwal bace, bai kamata a yi wa mace mai shekaru haka ba,da hanzari, ta d'aga Lamishi ta na kad'e mata jiki, kallon motar ta tayi, ta ga Lawwali na tsaye ya na jiran ta, ko kallon wajen ma baya yi, alamu sun nuna kamar ma baya wajen, ballantana ya san me ake aikatawa, daidai da kwayar zarra ba bu digon baqin ciki a fuskar shi. Ran Sultana ya baci da hakan kuwa matuqa, ya na tsaye ake wulaqanta mahaifiyar shi? Wane irin yaro ne shi? Kafin ta gama tunanin ta taji Muryar mahaifiyar ta na fadin, "Aka neme ta anka rasa ko ta bi duniya? Zamani ne na in talauci ya wa mutum yawa shi hwara biyar samari, dan su samu kuddi" Kusan a tare suka kalli Lawwali, kowannen su da abinda yake saqawa a cikin zuciyar shi, Hajiya Ikee ba karamin kaduwa hanjin cikin ta suka yi ba, da ganin yanayin fuskar shi, wani irin gurnani ya saki kamar wani zaki, da sauri ya zagaya ya bude mota, tare da yi wa sultana alama da su tafi. Kamar wadda ya yi wa magani, haka ta bi umarnin shi zungui zungui ta fada mota, da wani irin gudu ya bar gidan,tsoro ne da tashin hankali a bayyane a fuskar Sultana, wannan wanne irin gudu yake da ita. Bangaren Lamishi kuwa sai ta ji wani sanyi ya mamaye ta, ta tabbata Hajiya Ikee bata zagi banza ba, ko bai rama dan ita ba, sai ya dau mataki dan qanwar shi, qarasa miqewa ta yi ta na murmushi, ta tsaya sosai, ta na jiran Hajiya ta matsa, ta shiga ta hau aikin ta. Hajiya Ikee kuwa, ji ta yi qirjin ta na bugawa da sauri da sauri, idanun Lawwali kawai take hangowa, tafe take zuwa daki, ba tare da ta san sanda ta fara tafiyar ba. Tunani take mai zurfi, game da abinda ya faru, zama ta yi a bakin gado, ta na nazari, cikin murmushi ta miqe, ta ce, "Wato duk wanda ka son ya sami nasara akan ka Lawwali, shi tabi qaunar ka, da kyau" Hannayen ta biyu ta tafa, cikin jin dadi, tare da ganin ta samo babbar hanyar da za ta yi maganin Lawwali. Lamishi kuwa, ko da ta shiga dakin Sultana Dan gyarawa, sai ta ga babu datti, kuma Mai Buruji ta tabbatar mata da cewar ba mai zuwa gyaran dakin ta, tun bayan batan Mubaraka, da alama da kan ta take gyarawa,duk da cewa akwai masu aiki sosai a gidan, wanki ne dai gashi nan, ta tara mai mugun yawa, sake dan gyara abinda ba a gyara ba ta yi, ta debi wankin, ta tafi wajen yin wanki. Sai da ta gama aikin cikin gidan sannan ta tafi wajen su Mai Buruji, nan ta labartawa Mai Buruji duk abinda ya faru, dariya Mai Buruji ta dinga yi, daga qarshe ta ce, "Aiko yau ta kai qarshen iskanci, da wulaqanta tallaka, kee Yaya watarana ma haihuwar dan iska na da rana, dan ko walle na sani Lawwali ba shi barin wanda duk ya ɓaci (zagi) qauna tai, ko da ke ta kuwa, balle wata can," "Bari ke dai,shi ne na ka wa dariya nima, yo Allah na tuba zagi ko ga unguwa sha nai mukai kullum, abu d'aya ya yi min ciwo da ta ce muna mata sata,na san banda halin kwarai, amma hwa bana sata bana maita," Haka sukai ta hira a tsakanin su, su na aikin su. Bangaren Lawwali da Sultana kuwa, duk yanda ta so ta yi magana, ko da kalmar bada hakuri ne kuwa, ya gagara, saboda yanda Oga ya daure fuska abun ba a cewa komai, banda tafasa ba abinda zuciyar shi take yi, har shi za a zagarwa qauna? Yarinyar da yake jin ta kamar tsoka daya a miya? Duk wanda ya zage ta, ko ya taba ta, ji yake kamar ya soka mishi kibiya a idanun shi, ya na matuqar jin ciwo ya ga wani na zaluntar Mubaraka. Hajiya Ikee da ta san tanadin da yake mata da bata taba masa qanwa ba, abinda ya wa Lamishi ya bata ran shi, domin kuwa Uwa uwa ce, amma da ya tuna shegen kwadayi da son abin duniyar su ya ja musu walaqanci,dan ba shi da tabbas akan abinda Hajiya ikee ta fadi, na suna sata, duk wani mai son abun duniya in ya samu na wani, zai iya sata,dan haka  sai ya dauke kai ya dena kallon su, amma duk abinda take fada a kunnen shi, kuma tabbas ta dauki bashin da ba zata iya biya ba. Tsaye take a daya bangaren, ta kasa tafiya ta na so ta masa magana, duk ya bi ya hade gabas da yammar fuskar shi, ya qi sakin ta, zagayawa ta yi saitin inda yake zaune ta duqar da kan ta, wani irin qamshi ya ji ya shaqa mai kwantar da hankali, bai gama shaqar qashim ba Muryar ta mai sanyi da kwantar da hankali ta daki kunnen shi, sai da tsigar jikin shi ta miqe, "Auwalll.." Rintse idon shi ya yi, da suka yi jawur, dan bacin rai, ya wara su a kan ta, maganar da ta kwaso a bakin ta take so ta yi, tini ta maqale a maqoshin ta, cikin sauri ta bar wajen, ta shiga office din ta, ta jima a zaune kafin nutsuwa ta same ta. Lawwali kuwa wajen ya bari, bai tsaya ko ina ba sai wajen da ake horar da No 1, zaune ya gan shi, an bashi abinci da ruwa, Lawwali ya san mene ne yunwa, a lokacin baya can kafin tsohon Gwamna Lamido da suka kashe ya ja shi jiki, sai su kwana su yini basu ci ba, wannan dalilin ne ya sanya, ba ya qaunar barin duk wani wanda ke qarqashin shi da yunwa ko da kuwa kai mai laifi ne a wajen shi, qiyyyar No 1 da ke ran shi bata hana ana bashi abinci sau uku a rana ba, kuma abinci mai rai da lafiya. Ya na zuwa danqar wuyan No 1 ya yi, ya danna a cikin doya da kwan da yake ci, sannan ya dago kan shi ya dinga falla masa mari, "Duk a dalilin ka ne, a sanadin ka ne qauna ta ta samu mummunan tabo, da baka sace ta ba, da ba mai yi mata kallon 'yar iska, da baka sace ta ba, da har yanzu martabar ta da qimar ta na nan a idon mutane, yarinya ce mai daraja, yarinya ce kamila,ba ta da laifin kowa akan ta, in na muku laifi ku zo gare ni in kun cika maza, amma qauna ta? Qauna ta, mi tai muku halan, dole na sai kun tabe ta? Ka lalata wa qaunata rayuwa, ka mata tabon da ita kan ta ta na kyamatar kan ta, ta na zargin kan ta, me ya sa? Me ya sa kun ka taba qauna ta? Sai na yi ajalin duk wanda ke da hannu akan tabin qauna ta, wannan alqawarin Lawwali na," Wurgi ya yi da No1 gefe daya, ya fadi yaraf kamar tsumma, fuskar shi ta kumbura sintim, kamar wanda akai sukuwa akan ta, Da rarrafe ya kama qafar Lawwali, ya ce, "Oga...dan Allah,...dan Allah ...ka kashe ni ...in huta...na gaji....na gaji da shan kashin wahalar ga..dan Allah ka kashe ni..." Damqo wuyan shi Lawwali ya yi, sannan ya ce, "In kashe ka? In dinga huce haushi na a ina? Ai daga yau na dena kisan kowa in rayuwa ta ta ɓaci, wajen ka zan taho in huce haushi na" Wani irin kuka mara hawaye No 1 ya saki, kuka ne na azaba, da tashin hankali, wurgi Lawwali ya yi da shi, ya fita ya bar wajen, wani dan bayan gida ya shiga dake a cikin wajen, ya samu ruwa a jarka ya tsiyaya a buta ya wanke hannun shi da fuskar shi, sannan ya bawa yaran shi umarnin, su ci gaba da gana wa No 1 azaba, amma kar su sake su bari ya mutu. Amsawa suka yi da "To Oga" Sannan suka raka shi har bakin mota, ya tafi. Sai da ya biya ta wani super market ya sayi kayan kwalama, da abin sha mai sanyi, sannan ya wuce, kafin ya isa sai da ya daidaita nutsuwar shi, sannan ya isa NGO din, ya na zuwa ya tadda ta zaune a saman kujera ta na ta danna laptop din ta, ta yi matuqar bada hankali akan laptop din ya shiga ba ko sallama, har yau ya kasa sabawa da yin sallama in zai shiga waje. Daga kai ta yi, a dan tsorace ta kalle shi, murmushin da ta gani a saman fuskar shi, ya jawo nata murmushin waje, dan kuwa nan da nan ta bayyanar da haqoran ta a waje, kamar yaron da aka yi wa dariya ya rama. Hannun shi na maqale a bayan shi ya shiga, sai da ya samu waje ya zauna sanan ya ce, "Ran ki shi dade in shigo?" Wata hararar wasa ta mishi sannan ta ce, "Inna ce ah ah komawa za ka yi? Tunda har ka yi wa kan ka wajen zama" "Eh sai in koma mana, tunda haka ki ke so" Dan tura baki ta yi kadan sannan ta ce, "Dan Allah ka daina hushi, ka daina hushin da zai tsorata ni har na kasa yi maka magana" Dan bata rai ya yi, na wasu yan dakiku da ba za su wuce uku ba, ya sake fuskar shi, "Mu bar waccan maganar, yanzu za ki sha wanga?" Ledar ya dakko ya miqa mata, wani irin haske da annuri ke fita a fuskar ta, ba dan bata taɓa shan chocolates ba, ko sauran kayan kwalamar da ya kai mata ba, ah ah ,nashi na daban ne, kuma ko ba komai dama ta fara jin yunwa. Lemo mai sanyi ta dauka za ta bude, hannu ya sanya ya karba, hannayen su sauran kadan su gogi na junan su, Lawwali ya yi saurin janye na shi. Murmushi ya yi, sannan ya bude ya miqa mata, a baki, ta kawar da kan ta, "Ran ki shi dade, mi na na ki ka tsoro, ni hwa ba dodo ba ne," "Ni dai ban ce maka dodo ba, kuma ni ban ji tsoro ba," Miqewa ya yi, zai zagaya inda take, ya na wani kashe mata idanu, ta na ganin haka ta fara tari, saboda kwarewa da ta yi, shi kuwa dariya ya fara sosai, ya zira hannayen shi duka biyun a aljihu, ya yi hanyar fita, sai da ya bude qofar sannan ya kalle ta ya ce, "A haka ki ka son aure na ki na jin tsoro na? Ko kin zata na zuba wani abu ga lemon na? Ni ba dodo bane, Ni masoyin ki na Sultana, ina son ki, ina son ki da dukkan wata tsoka da jini na jiki na, ina son ki da ruhi na, duk randa aka ce maki Lawwali ya daina son ki, to ki tabbata ruhin shi ne babu" Rufe qofar ya yi,ya na zuba Murmushi ya tafi, shin wannan ma kalaman yaudara ne? Domin jin su yake su na fita daga qasan zuciyar shi, ba qarya a cikin su. Bayan fitar shi Sultana narkewa ta yi a kujerar, da kyar ta iya daidaita zaman ta ta ci gaba da aikin da ke gaban ta, duk cikin wata daqiqa dake wucewa cike take da farin ciki, da annashuwa a wajen ta, wanda bata yi zato ba, mussmman in ta tuna yanda suka zo wajen, rai a bace. Lokacin tashi na yi, Lawwali ya dauki Sultana ya wuce da ita wajen cin abincin da ya taba kai Mubaraka, a tare suka ci abincin ya na ta musu hotuna, sultana ba qaramin dadi ta ji ba ranar, ta tabbatar wa da zuciyar ta, ba ita kadai take haukan son Auwal ba, shi ma ya na son ta. Basu koma gida ba sai yamma liss, Sultana ko duba lokaci bata yi ba, sakamakon ranar ta na cikin yanayi na mata, ba sallah zata yi ba,ta kula da abu daya, wanda ya tsaya mata arai game da Lawwali, haka za a kira sallah a gama, bai je ba,gashi har an yi la'asar, ba ta son bata moment din su, dan haka ta bari kawai, sai watarana za ta masa magana. Hajiya Ikee na ta jimamin ina Sultana ta tsaya, dan dai ta san duk iskancin Lawwali ba zai taba diyar Gwamna ba, akan abinda ta yi dazu (hummm baki san oga ba lalinyaaa🤭) Motar su na shiga ta tashi a guje har ta na buge qafa da jikin kujera, ta leqa window, dauke ta ga Sultana da ledojin shopping, shi kuma ya rataya jakar ta ya na yanga, irin na mata, Sultana na ta kyalkyala dariya. "Kan uban can, wato yaron ga ta nan ya bullo ko? Zai ko ci uwar shi Lamishi, gobe Daddyn su zai dawo, sai na sa an yi gunduwa gunduwa da naman jikin ka, na kaiwa karnu (karnuka)sun canye" Kallon su ta ci gaba da yi, ta ga ya je daf da Sultana kamar zai hada jiki da ita, ita kuma ta sunkuyar da kan ta qasa, hannu ya sa ya daga kan ta, cikin kasala, ta wara idanun ta akan fuskar shi, tare da cije leben bakin ta na qasa kadan. "Sulty Babyn Daddy, da gaske za ki iya auren driver din ki, kuma mai tsaron lahiyar ki?" Cikin bude kyakkyawan bakin ta, tare da sassanyar magana ta ce, "Auwal alqawari fa na maka zan aure ka, ba zan taba saba wa ba, ni ba na daga mutane masu saba alqawari" "Kin tabbata kin yi alqawari za ki aure ni? A kowanne hali nake, kuma a kowanne yanayi nake?" "Auwal in ka sake min fuska natsuwa ta ta dawo jiki na zan baka amsa ta gaskiya" Murmushi ya yi mai sauti, sannan ya sake mata fuska, Itan ma murmushin take, sannan ta gyara tsayuwar ta ta ce, "Na maka alqawari zan aure ka, a kowane yanayi ka ke, ba ruwa na da yawa ko qarancin ilimin ka, ba ruwa na da nakasar ka in ma akwai, ba ruwa na da kyau ko rashin kyaun ka, ni dai kai nake so, zuciyar ka ce ta qulla soyayya da tawa, ruhin ka ne ya ga ruhi na soyayyar ta qullu, gangar jiki na ta yarda taka ta zama abokiyar  rayuwar ta, Auwal zan aure ka, this is my promise to you" Lawwali jin shi yake kamar ba ya duniyar,kalaman ta sun shige shi sosai . "Idan Daddy ya dawo ki na ganin za ki iya tuntubar shi, maganar aure na, dan naturo manya na?" "Ya ka ke magana kamar ka shiga zuciya ta ka yi leqen asiri?" Hajiya Ikee fa ta kasa jure wannan iskancin, qoqarin barin wajen take dan ta isa ta ci wa Lawwali mutunci ta ga abinda bata taɓa tsammani ba, Lawwali ne ya duqa ya sumbaci kuncin Sultana, ita kan ta sai da ta saki ledojin hannun ta suka zube qasa, shi kuwa ko a jikin shi,ido ya kalli sama ya kashewa Hajiya Ikee dake tsaye a jikin window ya ajewa Sultana jakar ta ya tafi. Sai da ya bar gidan gaba daya, ta dawo hayyacin ta, wajen da ya sumbata ta shafa, ta saki murmushi, can kuma ta ɗan bata rai ta ce, "Auwal ba kyau fa," Kamar ya na ganin ta, wani sassanyar murmushi ne ya kubuce mata a karo na ba adadi, ita ta na taba shi, shi ya na guduwa, shi ne yanzu zai nuna mata ya iya taba jikin mutum yi ne kawai ba ya yi,daukan tarkacen ta tayi, ta shige gida cike da nishadi, Allah Allah take su hadu da Sultan ta bashi labari, ta na sanya qafar ta, a cikin gidan, ta ji an ce, "Kee Sulatana, zo nan!" Cikin tsananin firgita da tsoro ta taka zuwa babban parlour'n  na su........... *A yi hakuri da wanga sai zuwa anjima ko gobe inshaa Allahu zan ci gaba, thank u mutanen Ogaaa😂* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 38: Mubaraka na matuqar jin dadin zama da su Taheer da iyalan shi,domin duk wani abu da take so, ko suka kula ta na da buqata da wuri za su yi mata shi. Da kyar Fateema ta yarda ta ke taya ta girki,shi ma dan Mubaraka ta dage ne, kuma cikin ikon Allah, sai ya zamana su na samun qaruwa da juna, abinda dayan su bai iya ba, sai daya ya koya ma daya. Yaran su kuwa kamar qannen ta haka ta dauke su, ita ke musu wanka, ta shirya su, su je islamiyya su dawo tare. Ranar Monday mai zuwa za ta fara zuwa Makarantar boko, a tunanin Lawwali makarantar Army Day ne kawai za ta samar wa Mubaraka tsaro, dan haka can ya saka ta, ya sa Taheer ya nemar mata driver da zai dinga kai ta, saboda shi bashi da lokacin kai ta, ya fara zuwa kasuwa, ya na saida shaddodi. Ranar farko da Mubaraka ta fara zuwa, ta samu masu son  qawance da ita kala kala, musamman dan ganin a irin motar da aka kawo ta, amma dake tin kafin Lawwali ya bata gargadin yin qawaye barkatai, ita ba me son tarkacen qawaye bace. Dan haka gaisuwa ke hada ta da kowa, ta raba ta da kowa lafiya. Tun ranar da aka kai ta makaranta wasu sojoji wanda suka addabi d'alibai mata, suke kula da zuwan ta, da tafiyar ta. Yanayin kamun kan ta, ya ja ra'ayin su, su na son sai sun lalata mata rayuwa, (wannan duniya yanda ta lalace Allah ne kawai zai gyara mana ita, in ka yi shigar banza, maza na kallon ka, su na dakon ka, in ka yi ta kirkin ma, wasu so suke su yaga maka rigar mutunci) Lokuta da dama ta kan gan su, in ta je shago siyan wani abun, shagon na dan nesa da asalin cikin makaranta. Watarana ta zo makaranta sai ta kula an sace pen din ta, gashi an basu assignment ta na son ta yi, in ta isa gida, dan haka tsayawa ta yi a shagon dan siyan pen. Ta na tsaye ta na jiran a sallami wasu,sannan a bata abinda take buqata, kurtun sojan nan ne dai da ya sa mata ido shi da abokan shi  ya zo shiga wajen, duk warin hayaqin sigari da wiwi ke tashi a jikin shi, ga hanya can da za ta ishe shi ya shiga shagon amma sai da ya rabi jikin Mubaraka har ya na gogar qirjin ta. Tura shi baya tayi ta ce, " Allah ya saka min azzalumi " Kurawa sunan dake jikin rigar shi ido ta yi, ta kasa gane sunan nashi Saboda sunan arna ne da shi, kuma da yare aka rubuta,duk qoqarin ta na ta karanta sunan ta kasa. Zuwa ya yi ya daddafe ko ina na jikin qofar, ya sanya ta a tsakiya kenan, da kyar take shaqar numfashi, hannun shi ya sa ya shaqe mata wuya, duk wajen ana tsoron shi, dan ya saba zuwa, in ya ga mata masu kyau, ya yi ta bibiyar su. "Hey, what are you doing, pls let me go, stop touching me, I will tell my brother if I go home" (Kai me ka ke yi ? Dan Allah barni na tafi, bari tab'a ni,se na fad'a wa yayana idan na ne gida ) Kuka ta fashe da shi, duk jikin ta na rawa ko ta ina, da kyar mutanen wajen suka bashi hakuri ya rabu da ita ta fita daga wajan a guje, motar ta ta nufa ta ga drivern da Taheer ya daukar mata baya ciki, ashe abokan sojan nan ne suka kira shi, suka tsare shi, sun tabbatar dole zata je inda motar take, daga nan za su kamata su tafi da ita, sai sun gama abinda suka so da ita su dawo da ita. Haka kawai jikin ta ya bata ta gudu, tunda bata hango driver a motar ba, dan acaba ta gani, irin masu fitar da mutum wajen gate dinnan, ta haye, ta ce ya Kaita gida ko nawa ne zata bashi. Ai kuwa ya na jin haka ya ce ta hau, ta haye ta rufe fuskar ta dan kar a gane ta, gudu suke zubawa, har suka kai gate, sun fita kenan, ta hango qaramar motar da sojojin uku suke ciki, dira qasa tayi daga machine din, ta buya a gefen wasu ciyayi da ke bakin kwata, duk abinda ta ke su na ganin ta, gani ta yi sun tunkaro ta, bayan sun rufe motar su, cikin Barack ta  shiga da mugun gudu, duk ta daddauje jikin ta, ya na mata zafi,sojojin da ke bakin gate ta dinga roqa kar su bari su tafi da ita, ta na ta rusar kuka, bata fatan sake riskar abinda ya faru da ita a baya. Su na ganin haka suka koma, domin ana ta complain akan su, kar akai rahoton su. Cikin sa'a kuwa ta tarar da wani babban soja na qoqarin shiga motar shi, gefen shi wani karamin soja ke bude masa mota, wajen shi Mubaraka ta kwasa a guje, ta masa bayanin komai, akai akai ta fadi sunan shi ta kasa, sai ta rubuta a qasa, Sojan na gani, ya gane wa take nufi, duk da bata rubuta daidai ba. A nan take ya bada umarni a je a nemo driver din ta, a cikin daji aka same shi an daure shi, ya sha duka ,har gida sojan ya raka ta shima a tashi motar. Godiya ta dinga mishi, ya ce aikin shi ne, ba sai ta yi godiya ba, bayan ya koma Barack ya sa aka nemo wadannan sojojin, aka musu hukunci daidai da abinda suka aikata, su kuwa cikin zuciyar su sun qudirta duk inda suka hadu da Mubaraka sai sun dau fansar abinda aka musu. Mubaraka kuwa Taheer na dawowa daga sabon wajen sana'ar da Oga Lawwali ya bude masa a kasuwa, wato shagon saida shaddodi na mata da maza, ta sanar da shi komai, ya kuma yi mata alqawarin daga ranar ta bar zuwa makarantar barikin sojoji, tunda ba diyar soja take ba. Da kan shi ya sauya mata makarantar private da ba ta da nisa da su, a kai ta a maida ta hankali kwance. Ya gargade ta da kar ta sake Lawwali ya ji wannan maganar, in ya ce me ya sa aka sauya mata makaranta su ce ba a karatu a can shi ya sa. Dariya ta yi, ta daga kai, ko dama da ta ce za ta gayawa yayan ta shi take nufi ba Lawwali ba. ************************ Tun saukar shi a jirgi ya ke gwada layin No 1 bai dauka ba, Gashi dai ta na ta ringing amma ba a daga ba, lambar No 4 kuwa ma sam ba ta tafiya, damuwa ce qarara a fuskar shi, tsoron shi kar dai yaran sun hade masa kai da Ogan su? Da sanyin safiyar masu tsaron lafiyar shi ne tsaye a bakin motocin da suka zo da su dan daukan shi, bude masa motar da zai shiga aka yi ya shige ya zauna, sake gwada No yake amma gashi ta na ringing ba a dauka. Cikin zuciyar shi ya ke tunani, 'Na manta yanzu safiya ne, wataqila ko tashi ba su yi ba' Maida wayar shi ya yi, ya ajiye, har suka isa gida bai dena jin yanayin da yake ji ba, na rashin dadi a zuciyar shi. Hajiya Ikee da ta san da dawowar mijin ta, ta sha gayu, har ta gaji, ta bawa masu aiki umarnin hada abin karin kumallo masu rai da motsi, na musamman. Kwararru kuma hadaddun masu girkin tuni suka fara bade gidan da qamshi, Sultana na zaune a saman sallaya, bayan idar da Sallah da azkar, ta fara karan ta qur'ani, ta na jin qamshi na tashi kala kala, ta tabbatar Daddyn su na tafe, murmushi ta yi, tare da qara qaimi wajen karatun ta, dan ta na so ta haɗa da addu'ar samun nasara daga wajen Allah. Da misalin shida da hamsin da bakwai 6:57am Gwamna Halliru ne a zaune bakin katafaren gadon su, ya zubawa Hajiya Ikee ido, ta na ta rattaba masa bayanai, akan abubuwan da ke ta faruwa a bayan shi,(rashin iya tarbar miji, daga dawowar shi, ba a bashi ko da abin da zai sha ba, balle a bari ya huce gajiya an fara bashi munanan labarai) Gwamna Halliru shiru ya yi ya na sauraron ta, ".....shi ya sa na fada maka, ka kori Yaron nan, ka qi, gani ka ke in ba shi Sultana ba zata iya takawa ko da gate bane ba tare da an halaka ta ba" "Kwarai da gaske, baki da masaniyar waye shi, har yanzu cikin jahilcin sanin waye shi kk, shi ya sa ki ke wannan surutan," Miqewa ya yi ya shiga wanka, ko da ya fito be ga Hajiya Ikee ba, bai wani damu ba, dama ita ba mace bace mai taya mijin ta shirya wa, sai da ya gama shiri tsaf, ya ga wayar shi na ringing, dauka ya yi, ya na tsaki, "Ko mi zata hwadi, da ba zata iya dawowa daki ba" Amsawa ya yi, ya kara ta a kunnen shi, "Ka sakko parlour 'n baqi yanzun nan" Shi ne kawai abinda ta fadi, cikin rawar murya, aka kashe wayar. Cikin sauri ya dauki wayoyin shi ya fita, sai da ya wuce parlour biyu kafin ya isa inda take neman shi, ya na bude qofar ya yi turus ya qame, "Barka da dawowa Excellency ,Bismillah shigo, kai da gidan ka?" Wani yawu Gwamna Halliru ya hadiya makwat, Allah yake ta roqo ya sa ba wannan bace ranar da tun farko No 1 ya guje musu. Lawwali ne zaune ya harde kafar shi daya bisan daya, hannun shi daya riqe da bindiga, ya aje wayoyin shi da na No 1 a gefen shi, sai jujjuya bindigar yake, Hajiya Ikee na gurfane kamar me neman gafara, "Hajiya wai mi na na hakan ga ki ka yi? Na ce miki ki hau kujera, yanzu in Sultana tag-gane ki duqe gaba na ai sai ta hwasa aure na, tunda kin ka shigo ni ke baki baki ki hau kujera, ko sai na taimaka Maki ne" Gyara bindigar shi ya yi, ya bata rai, da sauri ta miqe ta zauna a kujerar dake daf da wadda gwamna Halliru ya zauna, jikin ta sai rawa yake, a duniya Hajiya Ikee na tsoron mutuwa . "Lawwali mi na na ka ka yi haka? A gida na za ka fiddo bindiga, ga iyali na? Me ke damun ka?" "Ni ka ke tambaya me ke damu na? Ashe baka bawa matar ka labari na ba? Ashe baka hwadi mata ko ni wane ne ba? Take ta min wasan yara" Hajiya Ikee ce ta matsa kusa da Gwamna Halliru, ta na magana kamar me rad'a, kunnuwan Lawwali kuwa a bude suke tsaf dan sauraron ta, "Ka danna kiran Yaron nan na ka shi taho, shi kawo mana dauki, wajen wanga qaramin dan iskan" A hanzarce Gwamna ya kalle ta, ya maida kan shi wajen Lawwali, Lawwali ma cikin sauri ya dauke kan shi, kamar be ji me suke fada ba, cikin rad'a Gwamna ya ce ma Hajiya Ikee. "Lawwali shi na yaro na da ni ka hwada maki," Wata 'yar siririyar qara Hajiya Ikee ta saki, ta damqe bakin ta da dika hannayen ta biyu, ta na zaro idanu, domin duk wani labarin ta'addanci da rashin azziqin lawwali ba wanda ba ya riskar ta, wani irin tsoro ne ya sake damqar ta da qarfin gaske, "Hajiya ni kin ka aikawa 'yan iska su kashe ko? Ni kin ka hana kwana, kin ka b'aci uwa ta da qauna ta gaba garen, Hajiya ke ko san irin laihukkan da kin ka aikata min?" Da sauri Hajiya ta kada kai, alamar ah ah. Gwamna Halliru dai ya yi shiru, domin ko ya kirawo jami'an tsaro a kama Lawwali kamar ya yi ihu ne ya yi kirari ya dabawa kan shi wuqa a bainar nasi, in securities ne na gidan kusan rabin su Yaran Lawwali ne, shi ya horar da su, ga dai su nan yanzu sai yanda Oga yace. Lawwali Wayar shi ya dauka, ya shiga videos ya kunna video Na farko da ya fara yi wa No 1 azaba, ya kunna ya miqa wa Gwamna, "Ka bi ka ishan da waya tun hwarar sahiya, shi na nit-taho da kai na dan kawo maka wayar da mai wayar dan ka gan shi, gashi ku gani tare, dan Hajiya ta fi gane shin wane ne Lawwali, ya yake maida mutane in an ka ci amana tai" Sanda Hajiya ta ga yanda ya ke zubawa No 1 ruwan batir a baya, fatar na qonewa kuka Hajiya Ikee ta fashe da shi,kan ta ta hango ana mata wanan izaya, ya zata yi? Duk wata wahala No 1 ya sha ya gode Allah,kuma Gwamna da Hajiyar sun gani. "Ina yarinyar take?" Cikin matsancin fushi Lawwali ya miqe ya daki glass table din dake center din su, da bakin bindiga ya tarwatse a wajen, qara mai qarfi Hajiya Ikee ta sanya, ta qanqame Gwamna, "Gwamna Halliru ina mai tabbatar maka da cewa ka tafka babban kure da ka ɗauke min qauna, ka san a wane hali wancan qaramin dan iskan ya jefa ta? Ka san me ya mata!  Ko akwai sa hannun ka a lalata ma qauna ta rayuwa? Akwai sa hannun ka ne!" Cikin matsanancin tsawa yake maganar shi,wanda ta sanya Hajiya Ikee gama rushewa da matsanancin kuka, wannan shi ake kira da madaki kusa maceci nesan, da ta san wannan shi ne yaron da ake bata labari da bata so ma yi masa iskanci ba, labarin ta'adi da ta'asar shi ba wanda bata ji, ido da ido ne basu taba haduwa ba, da kuma sunan shi, ta san dai kowa Oga yake ce masa  amma bata san shi ne Lawwali ba. Sultana da ke shiryawa ce ta ji qarar fashewar abu da qarfi, dan guntun tsaki ta ja, sannan tace, "Masu girkin nan basu rabo da hwashe kwanna, (kwanuka) aiki suke kamar su na aikin hwashe dutsi" Mai ta hau shafawa ta na tunanin kayan da za ta sanya dan burge masoyin ta, sannan ta na tunanin shin ta masa magana akan abinda ya mata ne jiya? Ko ta bari? Dan gaskiya ita bata son irin soyayyar nan ta zamani a yi ta kiss da sauran irin romace din nan. A can parlour kuwa Lawwali ya titsiye Gwamna akan sai ya sanar da shi dalilin da ya sa ya sace masa qaunar shi, "Lawwali baka san me ya hwaru ba, ranar da kun ka kawo mani yaro nan...wani almajiri, har niyyi wani aiki, to qaunar ka ta na gidan nan, ta gane ni, shi na dalilin da ya sa nic-ce a ɗauke ta, kuma ban ce a mata komai mara kyau ba, hasali ma har gida da kuddin da za a zanka sai mata abubuwan more rayuwa sai da na aika wa yaran ka, ban dauke ta da nuhin a cutar da ita ba" "Me ya sa ba ka hwadi min abinda ke hwaruwa ba? Qauna ta ba mai Surutu bace,ta san aikin duk da nake maka, bana boye mata komi, bata hwasa yi min addu'a ita ko, akan Allah ya shirye ni, ko ta sani ba matsala bane, dan kuwa ba ta hwadi ma kowa, ta san komai, kahin ta gan ka,dan haka yanzu dai ka san ba a yi min ban rama ba ko?" "Kai wa Allah Lawwali maganar ga ta wuce," "Ta wuce? Ashe ma ni ba dan halak bane, shin da na hwadi ma an lalata rayuwar qauna ta ka tambaya ka ji ya take? Saboda bata dame ka ba, kamar yanda lalacewar rayuwa ta bata dame ka ba,to ka sani, abubuwa daya zuwa biyu za ka min dole, in ba ka min ba,.....in baka min ba....ka ga wanan? Sai ya shiga duniya" Hotuna ne da video da aka dauke su a tare, suna aikata mugayen ayyuka, wanda Gwamna ya yi matuqar mamakin yaushe aka dauka, a take anan, ya qara sallama wa lamarin Lawwali, abun nashi babba ne. "Yan zu mi ka ka so? Kuddi, kadarori? Ko muqami a gwamnati, dan Allah kar ka tona muna asiri," "Kar in tona maka asiri dai, dan kuwa tunda kagga an doka hotuna da video din ga da niyya ka san ina da plans, ba haka nan nike zaune ba, and ko da an kama ni ka sani bani da asarar komi," "Lawwali ka sanar da shi abinda ka ka bida, ko mi ne ne zai maka ka ruhwa muna asiri" "Ba kullum ikirarin in Gwauna yaddawo zai sa yaron shi ya kashe ka, sai na ga bayan ka...tau yanzu ta qare, ni ba na buqatar komi wajen ku a yanzu, amma ban muku alqawarin ba zan nemi wani abu ba a gaba, a yanzu buqatar diyar ku nake baku umarnin ku karba, in ba haka ba....." Miqe wa ya yi, ya na bin su da wani irin mummunan kallon da ya sanya Hajiya Ikee matse hannun Gwamna  tare da toshe bakin ta da hannu daya dan kare kukan da ke son ya fito. Bai ce komai ba bayan kallon daya baza musu ya bi ta hanyar da baqi ke shiga parlour'n ya bar wajen, kafin ya isa bakin motar Sultana ya maida bindigar shi bayan wando, ya mayar da wayoyin shi wandon shi, wayar No 1 kuma a gaban aljihun shi. Hajiya Ikee kuwa ya na fita ta hau yi wa Gwamna masifa, "Ashe annubar da ka dakko muna kenan? Yanzu ya zamu yi? Ya zame mana qadangaren bakin tulu, duk ta inda munka yi ba mafita, ka san me yake nufi da biyawa diyar mu buqatar ta? A aura wa Sultana shi fa, ni kuwa ba zan taba bari wannan al'amarin ya hwaru ba, ko zan rasa raina kuwa".......... *Oga ko zaka dawo ne? Dan bana jin Hajiya ta ji Warning dinnan* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGGE 39: Tinda ta duba ko ina bata ga iyayen nata ba, kawai se ta karya a gaggauce ta fita, da qudirin in ta dawo za su tattauna akan maganar Auwal din ta. Tsaye ta gan shi, ya na yarfe hannun shi, jini ta ga ya na zuba, cike da tashin hankali ta kira sunan shi, su na hada ido ya sakar mata murmushin da ke sake nannade zuciyar ta cikin son shi, kashe mata ido daya ya yi, sanan ya ce, "Ran ki shi dade kin gama mu tai?" "Me ya sami hannun ka? Ka na zubar da jini! Mu je ciki na sa maka magani," Bai mata musu ba, ta kama hannun shi zuwa main parlour din su, su na shiga ta tarar da Sultan na bude qofar dakin shi,ya na fito wa, da alama bai jima da tashi daga bacci ba, shi ma da jinin da ke zuba a hannun Auwal ya yi arba, da hanzari ya qarasa isa gaban su, "Subhanallah me ya faru haka?" Hajiya Ikee da Gwamna ne ke tafe, kowannen su zuciya ba dadi, ganin me ke faruwa ne ya sanya su zuwa wajen suma,Hajiya ta tuna ya akai ya samu wannan raunin, sanda ya fasa masu table din su mai kyau da tsada ne ya samu ciwon, kauda kai ta yi ta bata rai, dan ba ta so ma ta kalli jinin da ke diga a saman tsadadden carpet din ta. "Sultana tai ki dakko fist aid box,yi sauri" "To Yah Sultan" Duk ta kidime ta rude, a wajen Lawwali wannan is just a scratch ,amma su a wajen su babban ciwo ne, sai da Sultan ya gama gyara ma Lawwali ciwon sannan Sultana ta kalle shi, cikin kulawa ta ce, "Gaskiya yau, ba inda zaka, ka zubar da jini da yawa, ka zauna, a samu wasu guards din su kai ni" "Ba za a yi haka ba Ran ki shi dade, ba damuwa ai an saka min magani, zan iya kai ki" "Ni dai gaskiya ahhh ahhh, Daddy ka ce wani abu manaa" Gwamna Halliru ba abinda ya ke da ya wuce kallon ikon Allah ,yaushe Lawwali ya ci shi da yaqi haka?'yar shi har bata iya boye soyayyar shi a gaban su, murmushin gefen baki Lawwali ya yi, ya kafe Gwamna da idanun shi da ke dauke da kallo irin na tsokana. "Daddyyyy ka mishi magana pls, ya ji ciwo a hannun shi fa" "Amm...uhmmm..Lawwali ina ga ka d'ai zauna, zan samu masu kai ta kawai" "Ran ka shi dade Sultana ba uwar daki na bace kadai ta nada matsayi mai girman da ba zan iya barin wani abu ya same ta ba, kasan yanzu yanda duniya talalace, kana kauda ido sai ka nemi naka ka rasa," Cikin wani irin salo da kwarewa ya yi maganar, Hajiya Ikee da Gwamna sun gane karatun, karr kuma tarr a zuqatan su. "Sultana kar ki damu, kuje kawai, wa ya fada maki, dan wanga ciwo na damun mazaje? Ai zaman gida se mata" Har sun kama hanya za su fita Sultana ta koma ciki,cike da dan jin nauyi ta tsaya gaban Daddyn su, tare da kama hannun shi ta ce, "Daddy, tunda Allah ya dawo da kai lafiya, ga ka ga Hajiya, Yah Sultan da Auwal din kan shi, ka jima ka na min magana akan rashin kula maza da nake, ka na cewa a haka zan yi aure watarana? Tau Daddy yau ina so na sanar da ku cewa na zabi Auwal ya zama abokin rayuwa ta, dan Allah Daddy kar ka ce ah ah, shi nake so, shi nake fatan ya zama abokin rayuwa ta, ba zan iya rayuwa da kowa a matsayin miji ba bayan shi,dan Allah Daddy" Hajiya Ikee ce ta bude baki za ta yi magana, suka hada ido da Lawwali da ya sunkuyar da kan shi, amma idanun shi na d'age ya na kallon kowa,kallon da ya mata ya yi matuqar shiga kowace kafa ta jikin ta, nan take ta tuna maganar da Gwamna Halliru ya mata a can parlour'n baqi. 'Ke hwaa baki da hankali, sai ki dinga abu babu lisahi,halan baki ga mi ya nuna mana ba, ido da ido kin gan ni sanda na ke duba makaman da za a kai musu daji,tare da ni da su muna hira cikin nishadi, ido da ido kin ganni ina yanka jarirrai har guda ukku (jarirai) kin ga yanda ya ke kisan mutane kamar ya samu kiyashi,amma kin fi so wai har sai asirin mu ya tonu sannan ki nutsu, d'iyar da ki ke taqama taki ce, za ki aurawa shugaban qasa ta san me muke aikatawa sai ta tsane mu,Za ki iya jure tsanar da 'ya' yanmu za su yi mana? In ki na iyawa ni ban iyawa, Sultana ruhi na ce, ba zan taba bari wani abu ya same ta ba, dan su nake duk wanga abu da kika gani, dan na wadata su da dukiya da jin dadin duniya nake abubuwan ga, dan haka in ki ka kuskura ki ka kawo abinda Yaron nan zai bata min suna a duniya, sai na halaka ki da hannu na wallah' Ihun murnar Sultana ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, Sultana ce ta saki daddyn ta,ta tafi da gudu kamar wata qaramar yarinya, ta fada jikin Hajiya Ikee, ta ce, "Hajiya Daddy ya amince, zai aura min Auwal, Hajiya ba ki ce komai ba, kin amince da zabi na?" Wani abu ne mai daci da maqaqi ya tokare wuyan Hajiya Ikee, har wani d'aci-d'aci take ji a wuyan ta, idanun ta sun qanqance, saboda baqin cikin da ke cin zuciyar ta, amma ba halin bayyanawa, cikin Muryar da kamar shaqe mata wuya akai, ta ce, "Na amince, Allah ya sanya albarka" Rungume ta Sultana ta yi, ta na farin ciki sosai, ranta fari tass, kamar madarar shanu, Sultan ma sai wangale baki yake, ya na taya qanwar shi murna. Dan gyara tsayuwar shi ya yi, ya wani turo qirji gaba, shi a dole ga babban yaya, gyaran murya ya yi, sannan ya ce "Ban gane ana ta neman izini ba , ba wanda ya nemi nawa?" Lawwali ne ya duqa cikin wasa, da dariya, ya ce, "Ran Babban yaya shi dade, a mana ahuwa, ina neman izinin auren Sultana a hannun ka" Cikin dake wa, Sultan ya dafa kan Lawwali, ya ce, "Na baka izinin auren qauna ta, Allah ya muku albarka," Dariya sosai Sultana take, Lawwali na taya ta, Sultan ma cikin dariya ya dafa kafadar Lawwali ya ce, "Congratulations man,Allah ya sa ayi da mu" "Thanks bro, ameen, bari mu tai, lokaci na tahiya" "Yau ba za mu zauna mu yi murnar wannan rana ba?" Cikin shagwaba Sultana ta fadi hakan, ta na dan noqe kafada, ba qaramin kyau ta wa Lawwali ba, iyayen ta kuwa a zuciyar su sai suka gan ta, kamar yar qaramar yarinyar su, da suke matuqar lele, da qauna a zuqatan su. Sultan ne ya kama kumatun ta, cikin sigar wasa ya ce, "Ohhh Baby Sulty za ta zama babbaaa, ki tafi NGO din ki, ki gode Allah ma ki na da abun yi, unlike me, sai dai a dahwa a bani na ci, na kwanta, da jikin qiba gare ni, da na fi wata mata da aka kira da Hameedan Hamma (Lols)" Dariya sosai Sultana ta yi, amma abu daya na d'an damun zuciyar ta, kallon kallon da ke tsakanin iyayen ta da Lawwali, da kuma rashin fara'ar su, da walwalar su, a wajen ta wannan babban abun farin ciki ne, da sauri ta kawar da tunanin komai, da ta tuna dalilin da ya sa iyayen ta ba su cikin farin ciki sosai,Lawwali talaka ne, kuma driver, sun amince ne kawai saboda farin cikin ta, babu komai, hakan ma sun taimaki rayuwar ta ai, ta na godiya. Sallama suka ma iyayen na su suka tafi, ko da ya je bude mata mota da sauri ta bude, ta ce ta gode, ya kula da hannun shi, ba dan ya ce ba komai ba ma, yau ba inda za su. Zuciyar su fari tasss suka isa, Lawwali kan shi jin amincewar su Hajiya Ikee ya ke a matsayin wata babbar nasara da ya taba samu a rayuwar shi,duk da dai har yanzu auren Sultana ya na nan a matsayin auren daukar fansa a zuciyar shi, (zan so ganin anyaa Oga zai cika wannan alqawari da ya daukar wa kan shi? Sultana ce fa). ************************ Kwanan su Hansatu uku ba wuta, saboda NEPA sun yanke musu wuta, sakamakon rashin biyan kudin da ba su yi ba, wayar ta babu caji, sai dai ta kai gidan 'Yabbuga, daga kaiwa jiya, yau an kai 'Yabbuga ta fara masifar za a dame ta da saka cire din caji, ba aikin ta ba kenan, kar su dame ta. Dan haka Hansatu da kan ta, ta saka Hijabi ta kai wayar ta gidan Asshibi, dan sun dan saba yanzu, su na dan ziyarar junan su. Ta tarar da Mijin Asshibi zai fita, suka gaisa, ta tambaye shi ko Asshibi na nan ta kawo caji ne, ya tabbatar mata da cewar ta na ciki, ya fice abin shi. Ya na shiga Mota ya danna kiran Isah, bayan sun gaisa, ya tambaye shi ya Makkan, Isah ya kalli kayan abincin da ke gaban shi, ya shafa tumbin shi da ya fara ajiye wa ya ce, "Laminu Makka ta yi, ka ci ka sha ka kwanta ka yi bacci, ba me tashin ka,in kuwa ka na da suruka kamar tawa ko ba ka sana'a zaka warwasa Alhaji" "Shegen kaya, ka na can ka na tatsar surukar ka a nan" "Bari kawai Laminu, shekaran jiya ni ce mata an kwace sauran goro da ni tai da shi, ta tausaya min sosai, ta aikon da dubu dari biyu," "Dan iska, shi ne ba ka turo min ko yar hamsin ba ce nima na dan more kuddin surukar taka" Hansatu ce ta je zata wuce, ya yi shiru ya dena magana, sai da ta fita ya ce, "A gaskiya Isah in ka dawo ka ga Hansatun ka ba zaka gane ta ba, ka ga yanda ta yi qiba, ta yi mulmul da ita, wagga ba da ban taka ta ba ai sai na kai mata ziyara" Da sauri Isah ya zauna daidai, ya ce, "Kar ka kuskura, kar ka soma taba min mata, ko da ka ga ina abinda na ke so, dan na san na kama ta a hannu ne, har yanzu a hannu take, ina son mata ta, kar ka kuskura....akwai wata harqalla da ya kamata fa mu hada Alhaji, za ta kawo wuta sosai, ya kamata a hada ta yau yau din nan, kafin ta zo karbar wayar ta anjima" "Kwantas, ni ba abinda zan da matar aure, ga 'yan mata nan, masu taken zawarawan gida? Ka biya kudin shawarma yanzu ka samu yadda ka ka so, wace harqalla ka ke magana akai?" "Shegen sama Asshibi na gida ana cin amanar ta a waje, sai ka koma gida ka zam kamar bawan ta, ita ko gani takai kamar duk duniya ta hi kowa Sa'ar miji" "Iya taku kenan" "Wani abu sai ka zo Makka,takarun nan na nan Alhaji, bari kawai, sai ka zo kawai, yanzu mu yi magana akan wannan babbar harqallar da za mu hada," Nan Isah ya sanar wa da Laminu duk irin abinda yake son su yi, cikin dariyar kwararrun 'yan duniya Laminu ya ce, "Shegen sama, ka na son ka hini iya tsiya hwa" "Babu komai, kai ne dai uban gida na" Sallama suka yi Laminu ya duba wayar shi, ya ga Isah ya tura masa da No da zai kira, nan da nan kuwa ya danna kiran yaran shi biyu, ya basu umarnin da ya dace da abinda suke qullawa,barin gidan ya yi ya tsaya nesa da unguwar su sosai, sannan ya cire sim din shi da yake amfani da shi,ya sanya wani ya danna kiran No da aka tura masa, cikin maqale murya ya ke magana, ya na gamawa ya cire sim din ya karya shi ya yar, sannan ya tada motar shi ya bar wajen. ************************ "Yaya ba fa zaki hushi ba akan abinda ya faru ki ce baki koma zuwa aiki, ke ma ke san aikin da mukai ba wani aiki bane, alfarma ce dai aka mana ba komi ba, walaqanci kuwa ba kalar wanda bamu gani ba a baya" "Wani ya taba kiran mu da barayi? Cewa fa tay-yi in mun tai su na rasa abubuwa, ana musu sata, Allah na tuba duk a halaye na marasa kyau bana sata bana maita, yo akan cin mi, za a ce na yi sata?" Dan Talo ne ya ajiye butar hannun shi, ya zauna a bakin qofar dakin su Jameelu, ya wage baki ya na hamma. "Ke dai san in baki tai ba yawan abinci na raguwa ko? Tunda in an tashi kason ragowar abinci ba a kasawa da na ki, tunda baki tai ba, ko wanda aka dafa wa masu aiki ba a sawa da kason ki, ko dai baqin ciki ki ke mana" Wani mummunan kallo Lamishi ta watsawa Dan Talo, cikin bacin rai ta ce, "Ban zuwa din, lalataccen yohi kawai, baka da aiki sai son banza, baka b'arkata komi a gidan ka sai dai mata su maka, kaii Arrrr, tur da miji irin ka, ni na rasa ma mi na sa na aure ka, ba fusss, ba ka da lissahin da ya wuce wanne abinci muka kawo, da ya akai ya qare kamar kai ka nemo, baka nemo ba amma ka iya bin diddigi, kai....." Mai buruji ta san in aka bar Lamishi sai tai awa uku tana zage Dan Talo, gashi lokaci na ta tafiya, dan haka ta katse ta ta ce, "Yaya ki wa Allah, ki rabu da wanga mai matacciyar zuciya, ga hijabin ki na doko miki, mu tai ki dena ganin shi ko ran ki ya yi hwari, ni kai na mamaki ni kai, wai hankalina na ina sanda ya je garkar mu neman aure na, har na amince na auri miji kamar shi" Dan Talo ne ya miqe tsaye ya na dariya ,ko haushin zagin da suke masa baya ji, ya kade rigar shi ya ce, "Haka dai kun ka ganni kun ka ce ku na so" ************************* Driver take ta jira ya dawo daga inda duk ya tafi ya kaita asibitin amma shiru, ta tambayi mai gadi ya ce be jima da fita ba, bai san inda ya tafi ba, gani ta yi lokaci na tafiya, bata san takamaimai me ya faru ba, har aka kira ta, cikin sauri ta dauki hijabin ta saka jakar ta dauka ta fita harabar gidan. Makullin mota ta fitar daga jakar ta, tare da bude daya daga cikin motocin gidan, zama ta yi ta kunna, tare da danna horn da qarfi, cikin tashin hankali da damuwa ta bar gidan. A hanyar ta ta barin unguwar tasu ta ga wani yaro a saman titi ya na ta tsala kuka, cikin sanya birki mai qarfi ta tsaya gaban yaron, fita tayi ta duqa zata tambaye shi daga ina yake dan da ganin shi ba a irin gidajen unguwar yake ba. Wani abu ta ji an fesa mata ta shaqa, kan ta ya mata nauyi, kafin jiri ya qarasa diban ta ta kai qasa an tare ta, da kyar suka ciccibe ta suka danna a motar su, suka sanya wata takarda a motar ta daidai mazaunin driver, suka ja tasu motar a guje su ka bar waje . ...... *Allah ka shiryi kilimapas* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 40: Inda suka saba ajiye mutane nan suka kai ta, suka yi wa Laminu waya, ya isa, ya na zuwa ya leqa ta bulin da ya saba leqen wanda ya sa akamo,  agogon hannun ta da sarqar wuyan ta ya sa su cire su kai masa. Ko da suka ciro ya jujjuya su a hannun shi, ya girgiza kai, a kiyasi in aka siyar za su kai million daya da dan motsi haka, murnushi ya yi, ya ce, "Aikin ku na kyau, yanzu ku taho mu tai, a saishe da wanga, sai na baku kuddin sallama a ciki, dan wannan kayan da kuka gani, mai hatsari ne, ba zan so ku zauna kusa ba, asiri ya tonu, a yi kame da ku" Godiya suka yi ta yi, dan ba wani wayo ne da su ba, ya samu irin majiya qarfin qauyawan nan ne kawai su na masa aikin da ya so, ya sallame su da kudi qalilan su tafi su na murna abin su. Ya kira Isah ya sanar da shi duk abinda ke faruwa, Isah ya sanar da shi duk wata hanya daya kamata ya bi,dan ba ya so ma abun ya dad'e, gudun tonuwar asirin su. ************************* Asshibi ce ta yi lullubi ta tafi gidan Hansatu, ta na zaune ta na tsintar gumi, (shinkafa yar gida kenan) ta ji sallamar Asshibi. "Ahh ah maraba, Bismillah shigo" "Ba zama zan yi ba, na dora sanwa, wayar ki ce ke ta kuka, na ce bari na kawo maki, wataqila kiran na da mahimmanci, ko mutanen Saudiya na sun ka kira, na taho shigowa na ga waccan wahalalliyar matar garka, ita da abokiyar  fadan ta, har sun shirya kenan?" "To ina na sanin musu, ni da ke cikin gida, Allah ya sa sun shirya din ne, ai hwada ba dadi" Dan guntun tsaki Asshibi ta yi, ta ce, "Ke ai ba ki son rikici, gashi nan an sake kira ki doka" Da sauri kuwa Hansatu ta amsa, zuciyar ta na tsananin fata da begen Allah ya sa mijin ta ne, wata iriyar murya ta ji, na mata magana, "Ke ta Hansatu ko?" "Eh ni ta, da wa naka magana?" "Ba ki da buqatar sanin wanda ka batu, ki sanar da yayan ki, mun dauke Hajiyar ku, mu na da buqatar kuddi kafin mu sake ta, in kun kawo yau, ba tare da kun sanar da jami'an tsaro ko wata hukuma ba, yau din ga muna sako maku ita, amma in kun tsaya bin diddigi da kwakkwafin mu, tau ku na ganin gawar ta kuwa,ko da an kama mu mun dai kashe ta" Hawaye sun jima da wanke fuskar Hansatu ba abinda take kira sai Innalillahi wa inna ilaihirraji'un. "Bawon Allah, ka yi wa Allah kar ku cutar min da ita, zan sanar da yayana ko nawa kuke so indai muna da shi za a baku, dan Allah kar ku cutar mana da ita," "Zan sake kiran ki" Kuka take sosai ta na neman hijabin ta, da dan kudin ta da zai kai ta gidan su. Asshibi na tambayar ta me ya faru, ta na kuka ta na sanar da ita komai, "Dan Allah ki min alfarma diyan ga su zauna wajen ki, har na tai na dawo" "Ba ya da komi, Allah shi bayyana ta cikin aminci, wadannan mutane masu aikata wadannan laihukka Allah shi tona musu asiri azzalumai, su ko satar ma ba basu iya ba, su rasa wadda za su dauka sai boyar Allah, irin Hajiya mace mai sauqin hali, da halin kirki, anya masu satar ga basu san ku ba kuwa?" "Hummm Asshibi kenan, su ina ruwan su da halin ta, in ba na kuddi ba? Tunda ko sun san ta na da halin kuddi ai shi ne dalilin dauke ta, bari na tai,ku yi ta taya mu da addu'a dan Allah" "To Ummaa sai kin dawo, Allah ya bayyana Hajiya lafiya" in ji Ameena, da ta fi sauran 'yan uwan ta wayo, dan haka ta fahimci me ke faruwa. "Ameeen" Kafin ta kai bakin titi yayan ta ya kira ya sanar da ita, an kira shi an fada masa an sace Hajiya, sun fadi cewar a basu milliyan ashirin, sun yi ciniki za a basu million goma, yanzu hada kudin yake ze kai, ta zauna a gida ba sai ta fito ba, kar a yi biyu. (Mutane na kuskuren qin sanar da jami'an tsaro irin wadannan abubuwan, ko dake jami'an tsaron suma tsoro suke ji, Allah dai ya bamu tsaro da kan shi a wannan qasa da duniya baki daya) Hankalin ta bai kwanta ba, amma bayanda za ta yi, dole ta koma kamar yanda ya Umar ta, ashe ma sun kira Yayan nata shi ne suka kira ta kamar ba su sanar da shi ba, Allah ya saka musu, ya bayyanar da Hajiya lafiya shi ne addu'ar da ta dinga yi, har ta koma gida, ta na zuwa kuwa ta tarar da su Asshibi na qoqarin rufe gidan, za su tafi, labarta mata komai ta yi, ta mata godiya, akan ba sai yaran sun bi ta bama tun da ta dawo. Ko da suka shiga gidan alwala ta yi ita da yaran ta, suka yi nafila, raka'a biyu, sannan suka yi ta addu'a, ba qaqqautawa, akan Allah ya kare Hajiya ya bayyana ta da gaggawa cikin aminci . Har goma da rabi na dare basu sake kira ba, ga kudi an hada su kawai ake jira, ranar haka gidaje biyun suka kwana cikin tashin hankali , Yayan Hansatu kuwa damuwa ta masa yawa, shi kadai ne a gidan ba mai lallashin shi, ran shi ya ɓaci, kuwa da rashin matar shi a kusa, cikin fushi ya dau waya ya dinga kiran ta, a so samun shi ya sake ta ya huta, tunda bai ga amfanin ta ba. Cikin rashin sa'a bata daga wayar ba, haka ya hakura, ya dinga sintiri, daga daki zuwa parlour, zuwa dakin Hajiya, qarshe a dakin Hajiya ya kwanta, bacci mai dadi ya  dauke shi. Da misalin qarfe biyu na dare, wayar shi ta hau qara, ya na dubawa ya ga No masu garkuwa da mutanen ne, hannu na rawa ya dauka. "Ina ta kiran ku ba ta shiga, na hada kuddin tun dazu gasu" "Tauu ka hito ka kawo su daidai inda kun ka samu motar Hajiyan zan karba, in ka yi gangancin zuwa da jami'an tsaro ina mai tabbatar maka, na bada umarnin in na qara minti uku ban koma ba su kashe ta" Jiki na rawa ya dauki jakar da kudin suke waya na kunnen shi ya fita daga gidan a qafa, "Ba zan zo da kowa ba, gani nan zuwa, da qafa, ita ko Hajiya yau she za ta dawowa?" "Kai dai ka kawo kuddi, ai ni na maka alqawarin zata dawo lahiya ko?" "Tau gani zuwa" Tafe yake ya na nishi, saboda ba laifi ya na da dan jiki, gashi bai saba da motsa jiki ba, duk inda za shi sai a mota,sai waige yake ko zai ga wanda yake waya da shi . Har ya isa wajen da aka ce ya aje kudin ya tafi bai ga kowa ba, ya na ajiye wa kuwa ya juya dan komawa gida. Bai sake waigawa ba sai da ya yi nisa sosai, duk da wajen da dan duhu, bai hana shi ganin wani mutum ya dauki jakar ba ya tafi, a can nesa da wajen mota ce kunne ta na jiran mutumin, ya na zuwa ya shiga suka bar wajen, wani irin kukan takaici ne ya zo wa Yayan Hansatu, ina aka kai musu Hajiyan su, a wanne hali take? Dama Hajiya ita ce ke tada shi sallar asuba, to yanzu bata nan, baccin shi yake ta sha, musamman dama bai samu kwantawa da wuri ba. Buga qofar shiga gidan ya ji ana yi da qarfi kamar za a balle qofar, a gigice ya tashi cikin magagin bacci, ya nufi qofar ya na fadin "Wane na?" "Alhaji Hajiya ta taddawo,bude qohwa" Ai ya na jin Muryar mai gadi kuma ya ji an ce Hajiya ce ta dawo, da sauri ya bude qofar, shi ya kamo ta suka shiga ciki, kwana ɗaya ta yi ba a gida ba, amma duk ta fada, bakin nan ya bushe, su ko dan ruwa ba su san su bawa mutum ba, (ashe gwanda su Oga Lawwali ma). Ruwa mai dumi Hajiya ta haɗa ta fara yin wanka, kafin masu aikin gidan su zo da safe ta samarwa kan ta abinda za ta ci, dan kuwa wata baqar yunwa take ji, da misalin bakwai na safe, ta kira Hansatu ta sanar da ita, Allah ya dawo da ita gida lafiya. Murna da godiya ga Allah Hansatu ta yi ta yi, ta ce za ta je duba Hajiyan,Hajiya ta ce ah ah ta bari ba yanzu ba, domin ta kula ko ma wa ke kidnapping din nan idon shi na kan su ne, saboda an ga su na da azziqi, hira suka sha sosai, Hajiya na bata labarin yanayin yanda aka dauke ta, da wajen da aka aje ta, Hansatu ta tausaya ma mahaifiyar ta, sannan ta mata fatan Allah ya kiyaye gaba, Allah kuma ya ninka musu arzikin su da suka rasa. Bayan sun kashe wayar take sanar da Asshibi, Asshibi ta taya ta murna sosai, sannan kuma ta mata fatan alkhairi, yara ma sai murna suke kakar su ta dawo lafiya. A ranar Isah da abokin sheqe ayar shi suka raba kudin su daidai, kowa na ta farin ciki da murna. Ya tafi yawon bude ido a cikin garin Makka Hajiya ta kira shi, kamar ba zai dauka ba, ya daga cikin bata rai, ya yi sallama, bayan ta amsa sun gaisa ne ta ke tambayar shi, ya taji Muryar shi qasa qasa? "Ban da lafiya ne, yanzu ma asibiti zani, zazzaɓi ya kama ni, ina so na ga likita" "Subhanallahi, Allah shi baka lahiya, ni ma jiya ina zaune an ka kire ni an ka ce Hansatu ba lahiya ta na asibiti, na hita ni d'ai dan na duba jikin ta,ina hita a mota an ka samu wasu marassa imanin sun ka sace ni, sai da an ka biya million goma da subahi sun ka maido ni gida" "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, ya Salam, subhanallahi, Hajiya ke da kan ki aka sace, ince dai ba abinda ya samu lafiyar ki? Dan ta kudi ai mai sauqi ne, Indai lafiya bata tabu ba," Yanda ya rude sai ya sanya Hajiya ganin rashin kyautawar ta, da ta sanar da shi, musamman labarin tunda ya ce ba shi da lafiya, ya na ma asibiti. "Kar ka daga hankalin ka dan Allah, ina nan lafiya qlou, ai Hansatu nacewa zata zo duba ni, nace dan Allah ta zauna, masu satar nan, da dukkan alamu sun san ko mu su waye" "Tabbas kuwa Hajiya, ya kamata kuma a tsananta bincike,abun ya yi yawa haka nan" "Inshaa Allahu, bincike kam za a yi shi, yanzu haka magana na ga hukuma" Wani yawu Isah ya hadiya mai qulle wuya, sai ga tari, ba qaqqautawa, sannu Hajiya tai ta masa tare da yin sallama da shi, ta kira Yayan Hansatu ta na ta masa fada akan ya dawo da matar shi . *************************** Soyayya tsakanin Sultana da Lawwali ta bunqasa, ta girmama, ta yanda Sultana ba ta iya kwana ɗaya bata gan shi ba, shi kuma ya na sane watarana zai fashi ya qi zuwa, da kan ta take sanya driver ya aje ta gidan Lawwali ta duba shi, kafin ta wuce. Lawwali yanzu ba shi da burin da ya wuce na ya ga ya mallaki Sultana a matsayin matar shi,duk da ya rasa dalilin jin hakan, amma abu daya ya sani, zai aure ta ne dan daukan fansa, Itan ma bata da burin da ya wuce na ta auri Auwal,babban burin ta kenan yanzu a duniya, ta ga ta zama mata a wajen Auwal din ta. Lawwali ne ke kulle gidan shi, ya shiga motar shi, sai gidan Gwamna Halliru, dan ya na sane da cewar bai je ko ina ba, ya na da masu leqen asiri a gidan Gwamnan ba tare da kowa ya sani ba, duk wani bayanai da ya ke da buqatar sani ana sanar da shi, kafin ma ya tambaya. Har cikin gidan ya shigar da motar shi, a dadai wannan lokacin Sultana na NGO, sun rabu da shi akan ba shi da lafiya, ba zai samu damar zuwa ba. Har parlour ya shiga ba tare da ya sanar da kowa zuwan shi ba, da Sultan suka fara haduwa ya shirya tsaf zai fita wajen abokin shi, bayan sun gaisa ne ya ke sanar da shi ya zo wajen su Hajiya ne, Sultan ne ya sanar da su zuwan Lawwali, sannan suka sake gaisa wa ya tafi, Lawwali na zaune harde da qafa daya kan daya kamar ya na a gidan shi, Hajiya Ikee da Gwamna Halliru suka fito a tare. Cikin daure fuska tamau Lawwali ya miqe tsaye, ya na wasa da glass din shi, sannan ya ce, "Ba na son jira ka hi kowa sanin haka Excellency ,me yasa ka ke bari na yin jira?" "Lawwali har yanzu ina da tantama akan baka d'iya...." A zafafe Lawwali ya juya ya kalli Gwamna ya ce, "Tantama? Tantama hwa kacce, ka na da wani zabi ne da ya wuce ka aura min ita, ko ku na so ko ba ku so,na ga alama kun zaci ba zan aikata abinda na hwadi ba ko? Ka san ni, ka san wane ne ni, ka san mi zan iya da wanda ba zan iya ba, kar ka bari raina shi fi haka ɓaci, abin ba zai mana kyawu ba" Cikin hura hanci Hajiya Ikee ta ce, "Yaro yaro ne bai san wuta ba sai ya taka, in ka na da abinda ka ke ganin za ka yi, ka je ka yi, diya ta bata auren dan iska irin ka, lalatacce d'ebabbe" Abu kamar sihiri, kafin ta rufe labban ta Lawwali ne a gaban ta, ya sa hannun shi guda daya ya shaqe mata wuya, ya sanya bakin bindigar shi cikin bakin ta, jijiyoyin kan shi, da hannayen shi sun fito rudu rudu, idanun nan kamar an watsa masa barkono, leban shi na qasa ya ciza sai da jini ya fito,Gwamna ne ya isa gaban shi ya fara qoqarin kwace Hajiya Ikee da ke fitar da numfashi a wahalce, idanun ta na ta tsiyayar da hawaye, sai miqawa gwamna hannu take, wata tsawa Lawwali ya daka mata, akan ta dena wannan motsi da kukan da take, diffff ta hadiye kukan nata, ido ya fito ya mata gulu gulu. "Me ki ka ce, yaro bai san wuta ba sai ya taka? Waye yaro? Na ce waye yaro? A duniya akwai lalatattu d'ebabbu Sama da ku ne? Har ni zaki kalla ki wa zagin d'iban albarka, ke ba dan ina da burika masu yawa ba kin isa na bar ki ki kai gobe, (subhaballah kamar ran a hannun shi yake)" Ba damar magana bindiga na baki, ga wuya ya sha shaqa, Da qarfi ya wurga ta qasa ta fad'i, a gigice take neman iskar shaqa, tsabar azabar da take ciki, dishi dishi take gani, Gwamna ne ya duqa gaban ta, ya na taimaka mata wajen daidaita numfashin ta. "Ku na ji na ko? Nan da sati guda nika so a yi auren mu da Sultana, in hakan bata faru ba, ku sani, har cikin dakin ta, zan shiga in dauke ta, domin babu abinda ba zan iya ba akan cikar buri na, kamar yanda kai ma ba abinda baka yi dan cikar burin ka" "Lawwali d'iya ta ka ke son a yi wa irin wanga aure? Sati guda kamar d'iyar tallaka?" Da sauri Hajiya Ikee ta ce, "Kar ka ja mana magana, ka bari kawai a yi nan da sati guda din, kaga Lawwali, ka turo magabatan ka kawai a sa rana a yi komi a gama lahiya" Murmushi mai kyau Lawwali ya saki, ya dauke qafar shi da ya dora a saman kujerar su, ya duqa gaban Hajiya, Ita kuwa ta yi baya da azama, dan ba ta so ma ya rab'e ta ko kusa, rabon da a dake ta ba zata iya tunawa ba, amma gata da girman ta, ta sha shaqa . "Yauwa suruka ta, da kyau,bari na tai gida na sanar da iyaye na, gobe za su zo, a gobe nake so a saka rana, duk wanda ya lalata min shiri, zan lalata masa rayuwa, wanan alqawari na ne" D'aga kai kawai Hajiya take, Gwamna kuwa kallon Lawwali kawai yake, ba komai, zai aurawa Lawwali Sultana, amma zai nuna wa Lawwali mulki gaba yake da dabanci................ *Hummmm kun amince Mulki gaba yake da dabanci?* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 41: Zaune ya ke a kujerar da ke kallon ta a cikin office din na ta, su na fuskantar juna, hannun ta ya kama guda daya ya riqe a na shi, ya na kallon yanda gyararran farcen ta yake sheqi, cikin sassanyar murya ya ce, "Ran ki shi dade, ki na ganin za ki iya zama da ni a duk inda na ajiye ki? Domin ba zan taba karbar gida ko wata alfarma da iyayen ki za su bani ba, ke sani Hajiyan ku da kyar ta yarda da auren mu, dan kawai ina diyan tallaka, ina so na yi komai da kuddi na, ina so ki goya min baya akan wannan, za ki iya?" Tunda ya fara magana take kallon shi, ta gano gaskiyar maganar shi, ta kuma fahimce shi, ta na alfahari da kasancewar shi mijin da za ta aura, ya san yanda zai ya tsaya a matsayin shi a koda yaushe, baya manta tushen shi, sai dai ta na tsoron rayuwar wahala, amma indai da Auwal din ta ne ba komai, ba abinda ba zata iya yi domin shi ba, sai dai in abun  sab'on Allah ne, dan haka ta na ji a jikin ta, za ta iya taya shi cika duk wani burin shi, indai su na tare komai zai zo da sauqi da yardar Allah. Cikin murmushin da ke nuna gaskiyar maganar da take son furtawa, ta d'aga kai, tare da janye hannun ta daga nashi ta ce, "Na amince, na amince Zan zauna da kai a duk inda ka ajiye ni, duk inda ka sa qafa nan zan aje tawa, ni kai nake so,ba kudin ka ba,zan amfani da tushen ka ne, ba na iyaye na ba, kai nawa ne, ni taka ce" Godiya ya mata, suka ci gaba da hirar su sama sama, ta na tsara takardun da za a ware tallafi zuwa ga mabuqata. Bayan ya maida ita gida, suka ga motoci masu numfashi an Parker su a harabar gidan, Sultana na gani ta gane su waye a ciki, juya ido sama ta yi, ta amshe jakar ta a hannun  Lawwali da ke mata sai da safe,  sallama suka yi ta shiga gida, ta samu Hajiya Ikee a parlour su na hira da qawayen ta sai zuba musu qarya take, akan shaharar Lawwali a kasuwancin qasashen waje, duk da haka bata tsira ba, sai da  suka dinga yada mata da baqar magana, akan 'yar ta bata samu auren shugaban qasa ba. Gaida su Sultana ta yi ta haye sama, ta na matuqar takaicin rayuwar qaryar da mahaifiyar ta ke gudanarwa. A can parlour kuwa su Hajiya da qawayen ta sun gama tsare tsaren  yanda bikin zai kasance, a cikin qawayen ta akwai wadan da sun taba aurar da yara mata, sun yi alqawarin kawo masu gyaran jiki na musamman har gida. Wani party da duk abinda Hajiya Ikee ta ke da buri ya faru a bikin nan, sun kammala tsara yanda zai kasance, a bangare guda kuma Lawwali ya gama hurewa sultana kunne kar ta yarda a yi wadannan abubuwan, kuma ta yarda da hakan, bata bayyana ma Hajiya abinda suka tsara ba ita da Lawwali sai bayan tafiyar qawayen Hajiya ne Sultana ta sanya  riga da skirt na bature, ta daure gashin ta a bayan ta, ta sanya takalmin ta ta sauka qasa, zama ta yi kusa da Hajiya,dauke da wayar ta a hannu, ta na dannawa ta na wa Hajiya bayanin da ya zama kamar dukan tsiya take wa Hajiyan. "To kin ji yanda mukai da Auwal, Hajiya in ba gyaran jikin ba ni dai dan Allah ki bar zancen wasu party har kala hudu, ayi guda daya ma ya isa, ni dayan ma da za a bi nawa da ba za a yi ba, amma saboda kema ki fita kunyar qawayen ki za mu yi, yanzu yaushe Juwairah din za ta zo, na ji ana zancen gyaran jikin ta, irin na sudanis ya na da kyau" (ta na a garin Bauchi ga mai neman kwararriyar mai gyaran jiki irin na sudanis ku min magana) "Na ji duk bayanan ki, kenan ki na nuhin shi Lawwalin ne yacce ba a yin komi?" "Eh Hajiya, ko na kira shi ku yi magana, dan..." "Ahhhhh ni ba na neman tashin hankali da ki ka ganni nan, magana ta qare, ai auren ku ne, in ma cewa kun kai a daura a kai ki haka nan ku kun ka sani, ni na hau sama, in Sultan ya zo ki kire min shi, ba mu da lokacin fita waje dan siyayyar kayan aure, in ma mun ce order za a yi, yanzu yaushe mun ka gama zabe zaben abubuwan da duk muke da burin saye? Ni dai wanga aure naku Allah dai shi hisshe ni kunyar abukkai na" "Ai Hajiya ki kwantar da hankali ki, domin kuwa ya na da inda zai aje ni, ya ce ko cibi (tsokali) ba shi so a siye, ni kad'ai ya ke so a bashi, kin san hwa gidan da yake a nan shiyyar yake, kuma gida ne mai kyawu daidai misali, dama ni kin san rayuwar qarya bata gaba na" "Hummmmm in ji me ciyon haqurra, ba ke ji komi daga baki na ba, ballantana ki hwadi mai, na hau sama, Allah dai shi gwadi mana ranar bikin" "Ameen Hajiya ta" Sama ta haye ta na ta maganganu qasa qasa, ita kadai ta san me take ji a zuciyar ta, na baqin cikin auren Lawwali amma ba halin bayyanawa, da ace wani na sauraron abinda mutum ke quqqullawa a zuciya, lallai da Hajiya Ikee ta shiga bala'i. Ko da Sultan ya dawo, ya ji dadi matuqa da ya ga qanwar shi cikin farin ciki, fatan alkhairi ya mata sosai sannan ya je kiran da Hajiya ke masa. ************************* Lawwali ne ke ta Video call da Mubaraka, sai tsokanar ta yake wai ta girma, ya ga ta na fari, ko bleaching take ne? "Haba Yah Auwal, mi zai sani bleaching, baqi na mai kyawu na wallah, tau ko ba shi da kyawu ma yanda Allah ya yi ni haka nan zan zauna, sab'a halittar Allah haramun na, ina dai gyara jiki na da abubuwan da muke da su na gida shi na yas-sa ka ga na yi haske, Aunty Fateema ke yi min gyaran jiki, in ta yi," "Ohhhh Mubaraka, wanga bayanin kare kai, anya ba bleaching din ki ke ba? Tau ba wannan ba, ke san kuwa maganar aure na ta tashi ni da mutuniyar ki?" Hamdala ta dinga yi, tare da babbaka dariyar farin ciki, "Yah Auwal yaushe ne bikin? Kuma yushe za mu taho" Dan jimmm ya yi, kafin ya gyara zaman shi ya ci serious dan ba ya so ta masa daru, "Ke gane ko, saboda abubuwan da suka hwaru a baya, shi ne nicce ko za ku zauna ba sai kun...." Cikin kukan shagwaba ta katse shi, "Ni dai gaskiya sai na zo, bikin ku ne fa" "Baraka na ki saurare ni da kyau, zan so a ce ki na nan, rashin ki zai zama kamar bani da dangi ne a wajen, amma ba zan iya sanya rayuwar ki cikin hatsari ba, hatsarin da nake ciki a yanzu ya hi Wanda kin ka sani,ki bani goyon baya, na miki alqawari hatta da hita ta daga gida, sai an miki video kin gani, kwanciyar hankalin ki da zaman ki lahiya ya hiye min komi ga rayuwa ta, dan Allah kar ki min taurin kai" Cikin hawaye da sanyin murya ta ce, "Yaushe ne bikin?" "Asabar din ga me zuwa, yau saura kwana biyu,ki yi hakuri, i am very sorry, in ji ku turawa" Cikin kama kunnuwan shi duka biyun ya ke bata hakuri, ran ta ya ɓaci , wai a ce sauran kwana biyu bikin shi, sai yau yake fada mata, amma ba komai, za ta girmama maganar shi, wataqila hakan da ya yi shi ne daidai, fatan alkhairi ta dinga musu, ta na murnar yaqe, qasan ran ta kuwa ta na jin ba dad'i , za ai auren Yah Auwal din ta guda ba ita. Shi kuwa wasa da dariya ya dinga mata dan dauke hankalin ta, ya samu nasara kuwa dan ba su bar video call din ba sai da ya tabbata ta saki ran ta. Kwantawa ya yi ya na kallon sama, tunanin iyayen shi yake yi, a rayuwa shi dai ba shi da sa'a, wai ace  ya na da iyaye a cikin garin Zamfara, amma kamar ba shi da kowa, ba wanda ya ke da kusanci da shi, da zuciyar shi, balle ya ji damuwar shi, ba wanda ya damu da rayuwar shi,tunawa ya yi da sanda ya kai musu maganar auren, kafin ya fita daga gidan ya na dakin shi, ya ji mata na ta shiga ana fita, ana yi wa Lamishi Barka, d'an ta zai auri diyar gwamna, wa ya je ya baza a unguwar sai Allah masani. Gaba daya basu damu da wai bari a bincika a ga mene ne dalilin yin auren ba, farin cikin su kawai dan su zai auri yar gwamna, ba komai, Allah dai ya kai mu biki lafiya. Tunani ya dinga yi, na me ya rage a bikin wanda yake haqqin shi ne bai ba? Domin hatta da lefe da ya yi wa Sultana maganar shi, cewa ta yi ba sai ya yi ba, Hajiya Ikee kuwa ta ce bata san zance ba, ba a ɗauke masa lefe ba, sai ya yi, duk abinda ake buqata, dan haka kudin kawai ya tura ta account din Hajiya Ikee, ya ce su sai duk abinda ya kamata, ganin mahaukatan kudin sun rudar da Hajiya Ikee, amma bata yi mamaki ba, duba da wa ya tsaya masa a garin, ba qananan kudi yake samu ba a wajen Gwamna, Hajiya ta dau alqawarin ita zata kula da lefe, to amma ya rasa dalilin da ya sa yake neman dalilin da zai kai shi gidan su Sultana, ya na so ya sanya ta a idanun shi, zuciyar shi na azalzalar shi ta na tunzira shi akan ya je ya gan ta, daya bangaren na zuciyar shi na kwabar shi, bai biye wa daya daga cikin su ba, ko da ya fita ya dauki hanya, bai tsaya a ko ina ba sai gidan su. Ko gaishe su bai ba, ya tsaya a tsaye ya ciro kudi masu uban yawa daga aljifan jikin shi, ya ajiye wa Lamishi, ya ce gashi nan su samu inda za a musu ɗinkin gaggawa in sun sai tufafin da suke so su sa a bikin, ba ya so su je masa wajen biki a hargitse. Godiya suka dinga yi kamar za su kwanta, makullin mota ya bawa Jameelu, ya ce ya dakko wasu manyan ledoji a bayan motar, a guje ya fita ya na tsalle, ledoji ne manya masu nauyi Jameelu ya shiga da su, Dan Talo na ta bata rai ba a bashi komai ba. Lawwali murmushin takaici ya yi, dan duk ya fahimci komai, tura leda daya gaban Dan Talo ya yi, ya ce, "Sai ka bar bata fuska, ka sanya ranar daurin aure, kuma ka yi wanka dan Allah, kaya duk kyawun su in ba wanka ba sa kyau, Jameelu ga naku nan,ga wannan ku tai ku sai takalma da hulla, bana so ku taho wajen nan kamar almajirrai," "Tau Yaya mun gode" "Kaiii wanga yaro Allah shi  qaro bud'i" in ji Dan Talo. "Addu'ar ku kenan,bud'i dai bud'i dai, to Allah shi bud'a din, ba bu ruwan ku da ta ina bud'in zai taho" Fatali ya yi da dan karamin kwanon man gyadan da Mai Buruji ta soya, ya bar gidan, cikin takaicin iyayen nashi. Ko da ya koma unguwar da yake zama, har zai wuce gidan shi, kawai ya tsaya, ya kira Sultana, ta na dauka ya ce, "Ki shirya ki hito, zamu daukan hoto, ina jiran ki, nan da awa guda" "Daukan hoto kuma? Na ko aza bai dame ka ba irin wannan abubuwan" "Za mu yi ne dan Hajiya, ke san wadda taka son ayi komai a bayyane, hoton zai faranta ran ta" Ta ji dadin yanda ya duba lamarin Hajiyar ta, da gaskiyar shi, hoton zai faranta ranta matuqa. A gaggauce ta shiga wanka,ta fara shirya wa, dan bata so ta bar shi ya zauna jiran ta. Shima gida ya wuce, ya samu ya watsa ruwa, ya yi shirin shi tsaf cikin farar shadda mai golden din aiki, ya na daga cikin dinkunan da suka siyo ready made shi da Sultana, a qalla sun siya kaya masu kyau da tsada kusan kala goma goma, a gogon shi na  gold ya daura, kuma kalar aikin kayan shi (maza ku sani haramun ne namiji ya sanya agogo gold ko zoben gold sai azurfa). Takalmin shi ma kalar aikin rigar shi, sai hula fara mai ratsin golden, Masha Allah, ko shi kan shi sai da ya jima gaban madubi ya na kallon kan shi, a fili ya bayyana cewa, "Lawwali kenan, dan gidan Lamishi da Dan Talo, Yayan Mubaraka, Angon Sultana" (Aunty Asma'u😆) Murmushi ya yi, ya dauki turarukan shi ya dinga fesawa a hankali, ta yanda qamshin su ba zai hau kai ba, ya na gamawa ya taje gemun shi da ke qarawa fuskar shi kyau da kwarjini, (Team Gemu🥰) Sai da ya rufe gidan sannan ya shige motar shi da ya bari a waje. Ya na zuwa qofar gidan su Sultana Kiran ta na shiga wayar shi, dauka ya yi, ya ce ta fito ya na waje. Ya na nan zaune a mota ya ga securies guda uku sun bude mata qofar, kamar hadin baki ta fito sanye da doguwar riga golden color, ta na ta walkiya a cikin duhun daren, Lawwali sakin baki ya yi ya na kallon Sultana, anyaa ita ce kuwa? Sultana ta ji dad'in yanda Lawwali ya shagala da kallon ta, sai yanzu ta ke godewa Hajiya da ta dage sai an kawo wadda zata shirya ta, dan kuwa in ita zata shirya ba zata fito a matsayin amarya ba, dunkunan da a ka kashe makudan kudi aka yi su, a banza za a sanya su ba su yi kyawun da ake so ba. Da sauri ya fita ya bude mata qofa, ta shiga, ta na murmushi qasa qasa. Bayan ya zauna kafin ya tada motar,suka kalli juna, a tare suka furta, "Ka/kin yi kyau" Dariya suka yi, sannan Lawwali ya tada mota, sai hadadden gidan Hoton da ke cikin garin na Gusau, tun da suka shiga wajen mutane ke kallon su, domin kusan duk amaren da angwayen da suka je wajen dan d'aukan hoto Lawwali da Sultana sun fi su yin shiga mai kyau, da tsari, da burgewa. Sai da aka gama wa mutum uku, sannan aka zo kan su, a lokacin qarfe goma na dare ta gota. Style kala kala aka dinga nuna musu su kuwa su na kyafewa ana daukan su hoto, style din da suka ga ya sabawa shari'a in ance su yi, sai Sultana ko Lawwali d'aya daga cikin su yaqi. A haka dai aka gama daukan su hotunan, wasu matasa ne suka gane Sultana, habaa manaa nan da nan waje ya cika da surutai kala kala, wasu na yabon ta, su na ta so a dauke su hoto da ita, wasu kuma na tsangwamar ta saboda mahaifin ta. Lawwali bai tsaya biye wa shiririta ba, ya ja ta suka tafi gida. Hajiya ta rude ta rikice da ta ga hotuna, ga su an tura musu ga waya, ga wasu sun taho da su a envelope,kallon Lawwali ta dinga yi daga sama har qasa, ko ba shi da arziki ya na da kyauwun huce takaici. A cikin daren ta dinga dora hotunan a social media, qawayen ta kawai take jira su ga wannan hotunan, ta ga reaction din su akan mijin Sultanan ta. Sultana ma ta dora hotunan a social media, musamman Instagram ,ganin yanda suka rude da kallon hotuna kamar basu da lokacin shi ne ya sanya Lawwali yin sallama da Sultan ya tafi gida. Kayan shi ya cire ya tafi daji, domin ya na da mahimmin abu da ya ke so ya gudanar a can................. *Biki bidiri buredeee* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 42: Tokare take jikin gini, kamar wadda aka jingine, ta na ta dariyar yaqe, hannun ta dauke da kwano, shinkafa ce a ciki, ta sha ganyen zogale da quli, tumatur da albasa, da soyayyan mai, abincin da Lamishi ke matuqar so kenan. "Ko ni mutan gidan ga ba su amsa sallama ne? Sai buga sallama nake tun garka shiru ka ke ji" Lamishi ce ta fito, sanye da kayan da ta ke gwada wa, in da kudin ka yanzu za ka samu abinda ka ke nema, har sun samu ɗinkin da suka kai, guda bibbiyu, manyan leshi guda biyu atampa manya biyu, kowa d'aid'ai, sun siyo takalma da jakunkuna, sarqoqi da abun hannu, sai sabbin mayafai . Lamishi ce ta yatsina baki ta ce, "To wa ya ji ki mu na can mu na harikar azziqi" "Ai fa, na ga harikar azziqi, mutumi na zai yi aure shi na ko a fad'i min, duk abin da ya faru a baya ai ke san sabanin harshe da haqori ne, to Allah shi sanya alkhairi, ni zan koma, ga gwaben shinkahwa na kawo miki, na san ki na so" Wangale baki Lamishi ta yi, ta amshe kwano, ta gauraya gaban ta ta afa a baki, dad'in abun ne ya soki kunnen ta sai da ta sosa. 'Yabbuga na ganin haka ta saki jiki ta na zuba, ta ce wannan ta ce wancan, nan dai Lamishi ta manta da komai, suka hau hira akai ta bawa 'Yabbuga labarin abun azziqin da ke ta gudana a gidan. "To ni dai ba wannan ba, ke dai ga bikin ga da  ya taho a qurarren lokaci, ko tuwahi sabo ban dunka ba, dama ya kai wata guda ne, da na sa Dan Jumma ya sai min Holan ko Suhwa, nima na daura ana bikin Babban d'a" Dariya suka sanya sukai shewa, tare da tafawa, "Kar ki damu, ina nan da wata da Hajiya Ikeelima tabban, ke san su irin wannan ba shi gaban su, sai su sa sutura su ɗebe su basuwa kyauta, anjima in sun gane ta ba su ganewa " 'Yabbuga guda ta kama hanci ta zabga, ji take kamar ta jawo goben a d'aura auren, "Ohhhh Allah na gode maka, ashe da rabon zan daura suhwa a duniyar ga,Allah ya kaimu wannan rana da rai da lahiya" "Ameeen, ki na da takalme da jikka?" "Ina da su, amma tun wanda na ci bikin Kareema ne wallah" "Kayya, ki ce baki da su kawai" "Sai goben ki taho akwai wanda zan baki, na Mubaraka ne, Sultana tabbata su," Wani tsallan bad'ake 'Yabbuga ta buga ta yi baya, ta ce, "Yo ance miki kwana na na yaqare da zan saka kayan Mubaraka? Banni na tai bukin ga lahiya mu dawo lahiya, ke san halin Lawwali akan abun Mubaraka, walle ba ze ji nauyin yagan rigar mutunci ba gaban kowa, banni na tai da tsohhin nawwa, ai guntun gatarin ka ya hi sari ka bani" Dariya Mai Buruji ta ke ta yi, bayan ta dasa kujera a gefen Lamishi ta zauna. "To bid'i wuri ki zauna in ke qare tsallen, matsoraciya, jiya kuwa yattaho, na san yau ma shi na nan tahe" Rarraba ido 'Yabbuga ta fara, tuna ranar da ya dawo cikin bacin rai ta yi, ta na baccin wahala, takalmin ta ta shura ta ce, "Too mutanen ga na yi gida, zan bawa bisashe(awaki/tumaki) ruwan yami, rabon su da ruwa tun jiya" "Ke dai hwadi gaskiya, dan an ce Lawwali na tahe, shi na ki ka son gudu" "Ko ni ba haka nan na ba, ai ko Allah sanya alheri ina tsayawa na yi mai, zan dai je ne na ba bisashe ruwa" "To ya yi, jira na doko miki kayan da za ki saka goben" Lamishi ce ta shiga ciki, ta dakko atamfar ta bawa 'Yabbuga, kaya ne kamar sababbi fess da su, Godiya ta yi ta yi, ta tafi. Su kuwa suka ci gaba da shirin kayan zuwa biki, har lalle suka tsara za su daura a daren. *************************** A gidan gwamna kuwa, ko ina ka wurga ido mutane ne, na birni da na kauye, Sultana ta yi mamakin ganin yawan mutane, ko dan ba a taba aurar da kowa a gidan bane, tunda sukai kudi, mahaifin su ya zama Gwamna dangi suka dena shiga jikin su, saboda tsabar wulaqanci da tozarcin da Hajiya Ikee ke musu, in ka ga ta kula wani a dangi, to fa ya na da maiqo,bata bar dangin ta ba, balle dangin miji, kowa ma tabawa take. Sai gashi mutane sun yi hakuri da halayyar da ta musu a baya, sun zazzo bikin, domin zumuncin Allah ba dan halin ta ba. Amarya ta sha gyaran jiki da gyaran gashi, duk inda Sultana ta wuce qamshi ke bin ta,a cikin yan uwan su, har da masu taba jikin ta, dan kawai su ji ya yake, tsabar kyaun da ta musu a ido. Sultan kuwa na can na hada ma Sultana babban surprise din da ya san in ta gani sai ta yi murna sosai da sosai. Washe gari kuwa da safe tun safiya ake qawata hall din da za a yi bikin na su, duk wanda ya ga yanda aka qawata wajen zai tabbatar da bikin na manya ne ba na qananan mutane ba. Amarya da ango kuwa kyawun da suka yi ba mai faduwa ba ne. Lawwali ba shi da abokan da suka wuce abokan shi na cikin daji, sabbin matasan da suka horar suka bari tsaro da gadin dajin nasu, su No 2, No 3 da no 5 su ne manyan abokan ango. Da yamma kuwa Mota biyu Lawwali ya aika unguwar su, dan ya san sai su Lamishi sun yi gayya, ai kuwa motocin nan sai da aka cika su taf da mutane. Su Aunty Asma'u, Khadeeja Katuru, Halima (Maman yayana),Khadeeja Jabo, Eeshaa, Maman Jasrah,Aunty Rumma,Ameena Saudia, Su uwar gida Sarautar mata Iyar Ilham, Ashwal, Mom Sawwama, Maman Husnah,Maman Muhseenah,Mum Basheer, kai da dukkan mutanen group din A GARIN MU, sai da suka samu mota guda ta kwashe su zuwa event center din nan. Amarya Sultana kuwa a zaton ta tunda bata da qawaye Lawwali ne kawai zai je su tafi, sai ta ga an kawo motoci da yawa, da damar su gilashin su baqi ne, har wadda akai wa decoration wato ta amarya da ango, a tunanin ta sauran motocin da ke take musu baya securites ne a cikin su, haka ta shiga motar cike da son ganin irin kwalliyar da angon ta ya yi. Lawwali ma Allah Allah yake ta qarasa shiga motar ya qarewa kwalliyar da ya hango ta baqin gilashin motar kallo. Ana budewa qamshin su ya qauraya da na juna, kasa lumshe idanun su suka yi, saboda yanda suke kallon juna. Kowannen su na godiya ga Allah, da ya haɗa shi da abokin rayuwa kyakkyawa kamar dan uwan shi. Hawayen farin ciki ne suka fara sauka daga idanun Sultana, tissue lawwali ya miqa hannu gaban mota ya zaro, ya fara goge mata hawayen ta, duk abinnan da suke, masu video da hotuna na ta dauka. Mai hoto guda daya aka samu ya zauna a gaban motar, da ya ga sun yi abinda ya burge shi sai kuji kyasss kyarasss ya dauki hoto. A hankali motocin ke tafiya, har suka isa wajen event din, wani irin kidan waqar Hamisu breaker aka saki da ya yi wa amare, Lawwali ne ya fara fita, ya zagaya, ya budewa Sultana mota, ta fita, hannun ta na cikin nashi, kan ta a qasa, ta fara takawa, duqawa ya yi kadan ya mata rad'a a kunne, daga kai ta yi, a lokaci daya ta fashe da wani irin kukan farin ciki, hannun ta ta sanya bakin ta ta na zubar da hawayen farin ciki, ba kowa ta gani ba illa qawayen ta da suka yi karatu da ga na nan gida Nigeria har turawa na can qasar waje, sai tsirarun abokan Sultana da Sultan din kan shi, sun yi ankon baby pink din wani tsadadden material, larabawa da hausawan mu na nan sun yi rolling kan su da mayafai masu adon duwatsu. Turawan cikin su kuwa an musu dinki daidai da yanayin su, an gyara gashin nan sai sheqi yake, an ci dogayen takalma masu tsini. Yau kwanan su biyu a Nigeria, Sultan ne ya gayyace su, tare da tsara komai da ya kamata, duk da cewa a qurarran lokaci ne ya samu nasarar tsara abubuwan yanda ya kamata, a hotel din City king hotel Gusau, ya musu masauki. Nan da nan kuwa suka dinga zuwa daya bayan daya suna gaisawa da Sultana, ana rungume rungume ,da sumbace sumbace irin na gaisuwar mutanen qasashen turawa. Sai da suka gama tsaf ta taka zuwa gaban Sultan,ta rungume shi da kyau, ta na kuka tare da yi masa godiya. Share mata hawaye ya dinga yi, ya na girgiza mata kai, shiru ta yi, ta na murmushi, basu shiga main wajen taron ba, sai da suka je wani daki a hotel din da ake taron, aka gyara mata kwalliyar ta, sannan qawaye suka fara shiga aka sanya amarya da ango a tsakiya, ana tafe  Hamisu breaker na waqe su. Ranar su 'Yabbuga an yi ciniki, dan duk kudin da iska tai gangancin kawo shi wajen zaman su, to fa b'atan dabo yake, ba a sake ganin shi . Biki ya yi biki, Hajiya Ikee da qawayen ta, sun samu abinda suke so, an ci, an sha, an raqashe, an watsa kudi,su Asshibi, sai kallon turawa ake ana musu hoto, Mai Buruji da Lamishi kuwa sai fad'i ake wa mutanen unguwa ana tinqahon bikin d'an su ake. Lawwali kuwa can qasan ran shi kewar Mubarakan shi yake, ana hidimar bikin shi amma bata nan, da gwamna bai mishi abinda ya masa ba da tuni, auren nan, da zuciya daya za a yi shi, ba wata boyayyar manufa, da tuni masoyiyar shi, kuma qanwar shi abar qaunar shi na wajen, in ma ya kyale gwamna bai rama abinda ya masa ba a rayuwa ai bai cika dan halak ba......... *Wai ni dan Allah ba za a hakura da wannan daukan fansa bane??* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 43: An tashi taro lafiya, babu wani wanda ya tafi da qorafin bai samu abun biki ba, ko bai ci ya qoshi ba. Bangaren su Lamishi kuwa ta so su gaisa da Hajiya Ikee da qawayen ta, ko dan ta qara kankaro wa kan ta aji da mutunci, wajen mutanen unguwar su, amma haka Hajiya Ikee ta dauke kai, ta na yatsina ta ce musu ta na zuwa, ko da ta tafi sallama tai ta yi da qawayen ta da suke komawa gidajen su, ta na gama sallamar su, ta tafi ta ta motar, aka ja ta sai gida. Haka su Lamishi suka gaji da jira suma aka kwashe su sai gida, Sultana ranar a hotel din da qawayen ta suke ta kwana, duk da Lawwali ya so ya maida ta gida,amma ta nuna masa rashin dacewar hakan, tunda dan ita suka zo. Ai kuwa kwana suka yi su na hira, suka ci suka sha, suka yi games kala kala, irin na al'adun wasu qasashen. Basu suka kwanta bacci ba sai bayan sun yi sallar asuba, su na idarwa kuwa suka hau baccin gajiya. Sha daya na rana suka tashi, suka hau wanka, da shirin tafiya gidan Gwamna, yau za a Daura auren Sultana da Lawwali, masu gyaran jiki da kwalliya sun hallara, nan da nan amarya da qawayen ta suka sha gayu, ankon purple din yadi suka sanya, amarya ta saka nata kalar golden da milk, qamshi sai tashi yake ko ta ina, in ka kalli wannan sai ka ga kamar tafi kowa kyau a wajen, da ka kalli 'yar uwar ta sai ka ga ta doke ta farkon kyau , kowacce na ji da kyau, aji, ilimi, da gayu. Manyan motocin da suka je daukan su abun kallo ne, cike da nutsuwa ake tuqa su har zuwa gidan Gwamna halliru, tin daga farkon layin unguwar har qarshen shi motoci ne, na alfarma, matan manya ne danqam a cikin gidan, wasu daga wasu garuruwan suka zo, wasu a cikin garin suke. Amarya na shiga gidan hankali ya koma kan ta da qawayen ta, Sultana ta gode ma Sultan a ran ta ya fi sau a qirga, ba dan shi ba da sai dai ta yi ta yawo ba qawaye, da kuwa abun bai yi armashi ba. Bayan an yi sallar azahar ne aka daura auren Auwal da Sultana a Central mosque, da ke cikin garin na Gusau, a kan sadaki Naira dubu dari biyar, lokacin da Dan Talo ya ga Uban kudin da Lawwali ya damqa masa a hannun shi ya ce na sadaki ne, ji ya yi kamar ya suma dan takaici, a cewar shi wannan qarawa mai qarfi qarfi ne ai. Haka dai ba dan ya so ba ya bada sadakin nan. Kowa ka gani cikin farin ciki yake, Lawwali kuwa ba a magana, bakin shi ya qi rufuwa, sai doka murmushi yake, daga qasan zuciyar shi, ya na jin wani irin dadi mara misaltusa, kwanciyar hankali da nutsuwa ta baibaye shi. Bangaren gwamna Halliru kuwa, zuciyar shi baqiqqirin haka yake jin ta, amma haka yake ta murmushi da dariyar dole, ga mutanen da suka halarci daurin auren. Lawwali ne ya ja abokan shi gefe ya ce musu, "To an daura auren hwa, daga yanzu zuwa kowane lokaci wasan zai fara" "To Oga, muna maka fatan alkhairi" "Godiya ni ke, da irin jajircewar ku, da tsaya min bisa gaskiya da amana, sai na taho" Sallama suka mishi, suka koma inda suka fi wayo, masu iyalin cikin su, sai da suka leqa iyalin su, da iyayen su, sannan suka tafi daji. ************************* Gidan Alhaji Dan Talo mutane ne danqam,Lawwali ya saki bakin aljihu, sai wadaqa ake da abinci da abun sha, Hajiya aunty 'Yabbuga su ne akan abinci, sai abinda tace a zuba, a gefe kuwa Kareema 'yar ta ta zo itama, sai ta debi kaji, da drinks ta boye a zani, ta wurga mata, ita kuma Kareema ta dauke ta kai gida, in ta juye ta koma, haka suka dinga yi, sai da 'Yabbuga ta tara naman kaza me yawa da snarks da drinks . Kusan duk wanda ya zo daga kan 'yan uwan Lamishi da Mai Buruji, da Dan Talo sai da suka yi ta tambayar Mubaraka, Lamishi ba ta da amsar bayarwa, dan haka sai ta shashantar da maganar, Mai Buruji ce ta qirqiri karya ta ce Yayan ta ya kai ta karatu qasar waje,shi ya sa ba a gan ta ba. Ba qaramin dad'in wannan qaryar Lamishi ta ji ba, sai ta ji ta qara son kishiyar ta ta, Dan kuwa Mai Buruji abokiyar zama ce ta gari. Lawwali ya sanar da su, ba sai sun je daukan amarya ba, shi da kan shi zai dau amaryar shi, su yi bikin su kawai anan. **************************** Kamar yanda al'adar amare take, yin kuka a duk sanda za a kai yarinya dakin mijin ta, Sultana ma, ba a barta a baya ba, daga ita har Gwamna Halliru kuka suke, Hajiya Ikee kuwa idon ta kyamas ba alamar hawaye, sai dariya take musu, Gwamna Halliru na matuqar ji da Sultana, gashi ya zama dole a gare shi ya hannun ta ta zuwa ga Lawwali, Lawwali da kanshi ya je daukan amarya, ko aboki daya bai raka shi ba, Hajiya Ikee ta tanadi wanda za su raka amarya dakin ta, ba su da wani yawa. Da kyar Sultan ya samu ya banbare Sultana daga jikin Gwamna Halliru, ya na kuka, itama ta na kuka, haka Sultan ya damqa ta a hannun Lawwali, wanda ya ke jin zuciyar shi ta karye matuqa. Anya zai iya bada auren Mubaraka kuwa? Wani iri yake ji a zuciyar shi na rauni, wanda ya sanya shi zubar hawaye, bashi da abinda yake so sama da mubaraka a rayuwar shi, nisan da ta mishi ba qaramin qona zuciyar shi yake ba, kallon gwamna Halliru yayi, cikin tsananin takaici da tsana ba dan shi ba, da tini da Mubaraka a wajen. Da sauri ya ja Sultana suka shige motar da ya zo da ita. Hajiya Ikee sai da ta ga Sultana a mota ta tabbata tafiya zata yi, sannan ta ji hawaye na gangare mata, daga musu hannu mutane suka dinga yi, mota biyar ne suka dafe musu baya, dan raka amarya dakin mijin ta. Gidan da Lawwali ke da zama suka nufa, gidan ya sha gyara, an qawata shi sosai da sosai . Lawwali qin bude motar ya yi, ya ce ma driver ya sanar da su, su shiga su ga gida, in sun gama su tafi, da kan shi zai shigar da amaryar shi. Dariya mutane suka dinga yi, su na ganin he is very romantic, qawayen ta dik sun mata sallama, kuma sun shiga sun ga waje, sun yaba, mota suka koma aka maida su hotel din da suka sauka, washegari kowa zata koma garin su da qasar su. Sai da wajen ya rage daga Sultana sai Lawwali, Sannan ya fita, ya bude mata qofa, ta na zira qafafun ta waje, ya sunkuya ya dauke ta, driver ya buɗe musu gate ya na dariya, wayar Lawwali na hannun shi ya na musu video. Har saman gado ya ajiye ta, sannan ya amshi wayar shi, ya je ya rufe gida,ya koma dakin amarya, wadda ke ta kukan rabuwa da gida. Lallashin ta ya dinga yi, ya na bata hakuri, da kyar ya samu ta yi shiru, gani ta yi ya cire kayan shi ya sanya na bacci, ya haye gado ya dau laptop din shi, da kallo ta bi shi, dama haka ake yi? Ina dan abinda ake kawo wa amarya? Ba zai je su yi Sallah ba dan godewa Allah? Ba zai mata addu'a ba da ake wa amare? Me ke damun shi? Muryar Mubaraka ce ta karade dakin, cikin zumudin son gani da jin Muryar ta yake magana, "Barakana an gama komai , an daura auren, an kuma kawo min amarya ta, ohh ni na manta, ni na dakko abata ta da kai na," Murna wajen Mubaraka ba a magana, se dariya take, ta na sanya albarka, "Yah Auwal ina Aunty Sultana? Yaushe za ka turon pictures videos na yau,na ga na jiya, sun yi matuqar kyau,ba kadan ba gaskiya" Da hannu ya yafici Sultana, wadda ita ma ta ji dadin ganin Mubaraka, gaisawa suka yi Mubaraka, ta musu fatan alkhairi, sultana ce ta ce. "Wai Ni ina ki ka tafi ne akai bukin ba ke?" Cikin shagwaba Mubaraka ta ce, "Ina nan a Kan....." Kit Lawwali ya kashe kiran, ran shi a dan bace, ya dauke laptop din ya sauka daga gadon. Mamaki ya gama kashe Sultana a zaune, me kenan? "Me ya faru? Bamu yi sallama ba ka kashe muna? Ban gama jin mi tace ba, ko dake da dukkan alamu Kano take son cewa" Wata iriyar firgitacciyar tsawa Lawwali ya bugawa Sultana, "Inji uban waye yace a Kano take? Ko kin ji sanda tace a Kano take? Kar na sake jin maganar inda Mubaraka take a wajen ki, ko da da nj ne, ballantana da wani" Wasu irin hawaye ne masu quna, suke zuba a idon Sultana, mamakin shi ya hana ta rufe bakin ta, bin shi kawai ta dinga yi da kallo. Bayan ya aje laptop din kwanciyar shi ya yi, ya juya bayan shi, ya na kallon gini . Jiki ba kwari haka Sultana ta miqe, ta rage kayan jikin ta, ta shiga bathroom, ta yi alwala, ta zo ta tada Sallah ,dan a yanda ta kula ran shi ya dagule ba ta jin zai yarda su yi nafilar ma a tare. Ta na idarwa ta miqe ta kashe fitila, ta kwanta cikin tsananin tsoro. Lawwalin duk ya sauya mata a dare daya, dama maza haka suke lokaci qanqani za su sauya, to amma me ta masa da zai bata ran shi haka? A hankali ta zira hannun ta jikin shi, cikin murya mai sanyi ta ce, "Ka yi hankuri, ba zan sake maka, maganar inda Mubaraka take ba, balle in wa wasu." Hannun ta ya riqe sosai a na shi, sannan ya ce, "Dan Allah kar ki sanar wa da kowa, inna ce kowa ina nuhin kowa," "Inshaa Allahu" Sultana dai na ta jira ta ji ango ya yi wani motsi ta ji shiru, har bacci mai dad'in gaske ya yi awon gaba da ita......... *Ikon Allah, wannan wanne irin ango be????* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 44: Abu kamar wasa, Lawwali ya qi sam wata alaqa ta auratayya ta had'a shi da Sultana, ba dan ta san dad'i ko wahalar abun ba, amma dai ta san kowanne miji da mata suna kasancewa a inuwa guda, bayan aure. Duk wata kulawa da soyayya Lawwali na bawa Sultana, amma banda ta auratayya. Yau sati Daya cif cif kenan da auren su, sultana na zaune gaban Laptop din ta, dan yanzu duk wani abu da ya danganci qungiyar ta, ta social network ta ke gudanar da shi, ta na transfer din kudi, da bada umarnin bude store a debi kaya duk ta internet ba tare da ta je ba. Lawwali ne ya shiga gidan, cike da gajiya, da dukkan alamu ya yi wani aikin ne fitar shi, dan kuwa har da ciwo ya ji a hannun shi, da sauri Sultana ta isa gaban shi, ta kama hannun, ruwan dumi ta samo a yar qaramar roba, ta sanya detol ta wanke masa hannun, duk Surutu da sannu da zuwan da take masa bai amsa ba, sannan bai nuna mata yanda yake jin zafin taba ciwon da take ba, kalmar da taji ta fito daga bakin shi, shi ne ya  bata mamaki, dan bata ga dalilin sake yi mata tambayar ba. "Kin ce kin amince za ki zauna da ni a ko ina ko?" Cikin mamaki ta amsa masa, tare da qarewa fuskar shi kallo. "Kin amince kin ji kin gani, ki na so na a kowanne hali nake a dukkan yanayin da nake ko?" D'aga masa kai ta yi, alamar Eh, dan ita da kan ta ta rubuta masa hakan a wani message da ta taɓa yi masa. "Kin yi alqawari ba zaki sauya alqawarin ki ba komai wuya komai rintsi? Kuma ko da ke san asalin gaskiyar wane ne Lawwali?" "Dan Allah ka na bani tsoro, ka sanar da ni me ke hwaruwa, na ji na amince a kowanne yanayi, a kowanne hali, kuma ko kai wane ne zan zauna da kai,zan ci gaba da son ka,na maka alqawari, Sultana ba ta alqawari ta karya ka san da haka" Hannun ta ya kama, ya zaunar da ita a saman cinyar shi, sannan ya ce, "Ki shirya, akwai inda nake so na kai ki, ni ma na maki alqawalin duk abinda zan hwada maki ba zan hwadi qarya ba,na miki alqawalin ba zan riqe ki ki zauna da ni akan dole ba, daga lokacin da kin ka ce baki yin aure na, a lokacin zan sauw....." Hawaye ne ke gudu a saman fuskar Sultana sosai, dan ta tabbata duk abinda za ta ji anan gaba ba mai dad'i bane, dan haka ba zata bari kalmar sauwakewa ko rabuwa ta hau saman labban shi ba, ta yarda da shi,ta san ba zai mata qarya ba. "Ki shirya kayan ki a akwati, duk abinda ki ka son anhwani da shi naku na mata, ko akwati nawa zaki hada ki hada,daga nan zuwa dare, ko qarhe nawa zaki kai, kar ki damu,zan kai ki wani waje, nan gidan ba nawa ba ne, sultana ina so ki bar qungiyar ki hannun ma'aikatan ki, saboda tahiya ce za mu yi mai nisa" Tsoro ya fara shigar ta ainun, amma abu daya ta sani,shi ne, ta yarda da shi, ta amince ba zai cutar da ita ba, cikin sanyin jiki ta tashi zata sauka daga jikin shi, ya kama hannun ta ta koma, fuskar ta ya qurawa ido, ya ga yanda take cikin damuwa da tsoro, a hankali ya ke share mata hawayen ta, ya na shafa bayan ta, irin yanda ake lallashin yaro in ana so ya bar kuka. Bai barta ba, sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa, sannan ya daga ta, ya raka ta har dakin,shi ma had'a kayan shi ya fara, ganin haka sai ita ma ta fara hada nata,su na yi su na hira sama sama. Laptop din ta da wasu abubuwan ta hade waje guda,Lawwali ya kalle ta ya ce, "Ki ajiye su a gefe, ga wasu can a can dakin na sawo maki, ki yi anhwani da su,ki maida komai naki cikin su, wadannan ki goge komai ki bar su nan" Kallon shi ta yi kamar zata masa tambaya sai ta fasa, ta yi duk yanda ya ce. Basu suka kammala duk abinda suke ba sai qarfe takwas da rabi na dare. Suna gamawa Lawwali ya yi waya, sai ga qofar parlour ta bude, wasu zaratan matasa Sultana ta gani na shiga, sai da ta gudu bayan Lawwali ta buya, saboda tsoron da suka bata, janta ya yi jikin shi ya rungume ya na buga bayan ta, da alamar lallashi. Sai da aka kwashe kayan nan tasss aka zuba a bus guda biyu, sannan Lawwali ya kama hannun Sultana da ke sanye da doguwar rigar ta, da mayafin kayan. Su na fita ta ga motoci Bus uku, qarama guda daya. Cikin qaramar suka shiga ita da Lawwali, da kan shi ya ke jan motar, sauran kuma yaran shi ne a ciki. Sun wuce qofar gidan Gwamna Halliru sai ta ji kamar a tsaya ta ga mutanen gidan su, amma ba hali, ta na ji ta na gani suka wuce gidan iyayen ta, suka dauki babban titi. Tun ta na gane unguwanni, da qauyukan da suke wuce wa, har ta dena gane wa,tsoro da tashin hankali sun fara shigar ta, ba dan itan ta na son abun duniya ba, ah ah tsoron irin qauye da rayuwar qauye da zata fara take, bayan bata taɓa yi ba. Gani ta yi sun shiga daji ba gida gaba, ba gida baya, waje ne daji sosai , ta bude baki za ta yi magana, Lawwali ya dora yatsan shi a labban shi, shiru ta yi, ta na tsiyayar da hawaye. Ina ne nan? Me suke yi anan? Wajen wa suka zo? Shin a irin wannan dajin za su ci gaba da rayuwa? Wadannan su ne tambayoyin da Sultana ke ta yi wa zuciyar ta,amsar ta bata samu ba sai da suka share awanni biyu da mintuna su na keta dajin, sannan ta hango wasu fitulu masu kama da na solar, dan kuwa a dajin nan zai wahala a samu wutar lantarki. Kade kade ta dinga ji ya na tashi, da ganguna, ana waqoqi irin na kai amarya a qauye dinnan, bata san sanda murmushi ya kubuce mata ba,  a ran ta ta ayyana cewar, 'Ashe ma qauyan su ya kawo ni, duk na bi na damu,' Sun tsaya a harabar wajen da ake ta kade kaden da raye raye, nan da nan murnar ta ta koma ciki, sakamakon ganin matasa mata da maza dauke da makamai, da bindigogi. Cikin ta ne ya bada wata iriyar qara, sai da ta damqe shi ta ɗan duqa. Lawwali ne ya d'aga hannayen shi sama ya na rawa,wajen kuwa aka dauki ihuuu, ana ci gaba da kid'a da waqa. Sai da ya yi rawa sosai ya gaji, sannan ya kama hannun Sultana da ke tsaye a tsorace ya yi alamar a yi shiru, ko tari ba wanda ya sake yi a wajen kuwa, hakan ba qaramin sake firgita Sultana ya yi ba, ta kalle shi, ta ga ba alamar wasa a fuskar shi, sai dai wani kwarjini, da izza da ta gani kwance a fuskar shi. "Ga amarya ta na kawo cikin mu, ina fatan za ku girmama ta, a mata duk wani abu da take so, kamar yanda za a yi min, sannan ina fatan za ku kiyaye dokoki na, dan mu zauna lahiya, ba cutaaaa???" "Ba cutarwa, ba cin amana, ba karya alqawali" "Da kyau, a ci gaba da shan shagali" Kafin ya gama rufe bakin shi an dauki kade kade da raye raye, masu shaye shaye na yi, masu zinace zinace na jan abokan su suna barin wajen, kamilallun mutanen da aka kamo aka ajiye wanda suke da burin komawa gidajen su watarana na gefe, su na kallon masu rawa, a ranar zuqatan su sun taya Oga farin cikin kawo matar shi, domin ko ba komai, sun san ba ruwan shi da neman matan wajen, su na girmama yanayin yanda yake gudanar da wajen, ba yunwa, ba qishirwa, in baka so a kusance ka, ba mai maka dole wadan da aka wa dole ma a baya, yanzu sun wattsake, sun maida wajen kamar gida. Babban abun takacin shi ne, ba ibada a wajen, duk da ba a hana mai so ya yi ba, amma fiye da rabin wajen basu damu da bautar Allah ba, basu damu da kiyaye duk wasu dokokin Allah ba, shaye shaye da zinace zinace sun yawaita. (Ta yaya za a rabo ka da ga gidan iyayen ka, ko cikin iyalan ka a kai ka wata rayuwa mara 'yanci sannan ka dinga ganin an kyauta maka? Yau ko a wahale ka ke a rayuwa sace mutum ba abu ne mai kyau ba, Allah na sane da yanda ya aje dikkan bayin shi, dan haka sace mutane ko ta wacce fuska ce me kyau ko mara kyau ba daidai bane, Ya Ubangiji Allah, masu satar mutanen nan bayin ka ne suma da ka ke so, ka halicce su ka sanya su daga cikin halittu mad'aukaka, Allah ka basu ikon gane d'aukakar da ka yi musu su sauya rayuwar da suke kai zuwa wadda ka ke so Ameen) ************ Kayan su Lawwali an gama jere su a dakin su, akwatuna ne sun kai takwas, dakin babba ne, an qayata shi da kayan more rayuwa, sak dakin amarya, Lawwali duk ya ɗebe giya da duk wani kayan maye dake dakin, an maye gurbin wajen da lemuka manya irin masu tsadar nan,Sultana ta gaji da yin shiru, gaban shi ta tsaya, ta na hawaye, ta ce, "Dan Allah ka warware min wannan qullin da ke cikin kai na da zuciya ta, kar ya matse ni na rasa raina " "Ba zaki rasa ran ki ba Ran ki shi dade...auuu Sultana, taho nan ki zauna,abinda zan nuna maki, ba zaki iya kallon shi a tsaye ba" Kwace hannun ta tayi, ta had'e su a qirjin ta, ta na jiran ya nuna mata duk ma me yake son nuna mata, ta gaji da yin shiru, Murmushi ya yi, ya kwalawa No 5 Kira, ya shiga a guje, ya miqawa Lawwali wata baqar Laptop qirar Lenovo . Ajiye ta ya yi, a saman wani dan table, ya kunna, ya shiga wani file, ya kunna wani video, nan da nan kuwa ya fara playing , abubuwan da Sultana ta fara gani, sun sanya mata jin jiri. Jikin ta na rawa ta samu waje ta zube a qasa, ragwab a gaban laptop din, hannun ta ta sanya a bakin ta, ta na kuka, ta na jin wani irin sanyi na shigar ta, Duk wasu kashe kashe da qone qonen garuruwan bayin Allah da akai, yau ta ga su waye ke yi, da kuma mutanen da ke sanya su yi din, duk wani tsafi, da fyaden yara qanana maza da mata, ta ga masu aikatawa, da masu kai musu yaran a aikata din, duk wani sabo da aka aikata da littafin Allah, ta ga wanda ya aikata dan kawai mulki, da son duniya. Sultana kam qarshe numfashin ta ne ya dauke,ta zube a wajen. Lawwali ya san za ayi haka, dan haka a shirye yake, yar locker da ke wajen, da yake ajiye ruwan gorar shi ya bude ya dauko, ya watsa mata, sannan ya dauke ta cakkk ya ajiye a saman gado,ya fita, dan ya bata waje, ta yi nazari akan abinda ta gani,ya san yanzu in ya yi magana ma ba zata fahimce shi ba, har sai ta dawo dadai . Lawwali na can na casun shi, da mutanen shi, kamar ba abinda ke damun shi, nan kuwa qarfin hali ne, ba ya so ya gina rayuwar auren su akan qarya, tsakanin shi da Sultana ya na so su fahimci juna, su gina zaman su akan gaskiya da gaskiya, in ya yi nasara ta karɓe shi, ta aminta da shi,zai fi kowa farin ciki, da hakan zai amfani, wajen musguna wa Gwamna Halliru. In ta qi karbar shi ya na da sauran shaidun da zai nuna mata, ya tabbatar da cewa za ta yarda da shi, za kuma ta zauna da shi. Bai koma dakin ba sai sha biyu da rabi na dare,dauke yake da abinci, wanda gasasshiyar kaza ce, da madara, sai ruwan sha. Ajiye wa ya yi, ya zauna a bakin gadon ,a zaton shi ta yi bacci ne, ya ja bargo ya rufe ta da shi, zai tashi, ya ji Muryar ta da ta sha kuka ta gaji, ta ce, "Me ya sa ka biye musu, ku ke aikata barna a bayan qasa? Mai ya sa ka zama daga bayin Allah wadan da yake fushi da su, ya tsine musu? Ko ka san hukuncin wanda ya kashe rai kuwa a wajen Allah? Me ka ke nema a duniya da ya kai ka aikata munanan zunubai haka? Kaico na ni Sultana na yi asara a duniya, ban yi dacen masoyi da iyaye ba, kaico na, kaico na" Yanayin yanda take kuka, sai da ya kawo wa Lawwali kwalla a idon shi, cikin qunar rai ya ce, "Ba da so na bane, ba laihi na ne ba, laihin shugaban nina ne, sun qi su bani taimako a lokacin da na je musu ina cikin mawuyacin hali, na je su tallafe ni su agaje ni a lokacin da nake tsananin buqatar hakan,amma suka maida ni dan ta'adda,mai sace yaran mutane ya kai musu, ba na mantawa ina da qarancin shekarun da ba za su wuce shekara sha biyar ba, lokacin mahaifi na ya na ganiyar zaman banzan shi, caca da shan sigari su kadai ya sanya a gaba, ga iyayena mata basu da aiki sai dambe da tashin hankali a shiyya ( unguwa). Duk inda zaman lafiya bai samu ba, talauci ya fi wahal da wadannan mutanen. Sai mu kwana mu wuni ba mu ci abinci ba, a lokacin mahaifiya ta na dauke da cikin Mubaraka, na matsu matuqa na samu qani ko qauna, wanda zan dinga gani na ji dadi ga rayuwa ta, wanda zan dinga hwadi wa abin da ka damuwa ta, tunda iyaye na basu damu da rayuwa ta ba tun asalin tashi na, sai na kwana na wuni ban ci ba, ban sha ba, ba mai tambaya ta ya na wuni, ko ya na kwana, sai nai ciwo na warke ba wanda ya sani,sai an ga na rame a ce 'Baka da lahiya ne halan?' Na sha wahalar rayuwa matuqa a baya, saboda wahala dole na bar makaranta, na fara bin abokan banza bayan na sauke qur'ani, na ajiye boko, ina Jss 2, na fara bin wani babban dan daba a nan shiyyar mu, muna bin qananan 'yan siyasa, su na saka mu nemo musu yara qanana, tun ban san mi ake da yaran ba, har na sani, sai da  ya zamana na hwara dokan yaran shiyyar mu ina kaiwa, sai dai a nemi yaro a rasa, kuma da ni za ai ta bid'a a shiga nan a shiga can, in yi shiru . Mahaifi na kuwa tun da yaga na dena kwana da yunwa, ina sauya kayan sawa ta, sai ya fara ja na a jiki, inna tafi na samo  dan wani abu, sai na samma sa, ana haka Lamishi ta haihu, ta samu diya, an ka sa mata Mubaraka, tun da na dawo daga yawo na, na dora ido na kan Mubaraka na ji qaunar ta ta shiga zuciya ta, na sha ji a wajen Lamishi in mai jego na samun abinci me kyawu diya na samun ruwan nono mai yawa mai kyau, daga nan na hwara siyo abinci ina kawo wa dan ta ci qauna ta ta samu ruwan Nono mai kyau, kar ta zauna da yunwa kamar yanda na yi rayuwa da yunwa. A hankali a hankali na hwara zama gagararre, kuma mutane suka hwara sanin mi nake ina samun kuddi, ni dinnan da kin ka gane ni, na yi gidan yari, sai da ya zamana in an kama ni, 'yan siyasa da kan su, suke hiddo ni, saboda ba qaramin nasara suke samu ba in suna tare da ni. Gwauna da ya gabata shi ne ya tsunduma ni a babbar harkar da nake ciki yanzu, shi ne ya dauki su Lamishi aikin wanke wanke a gidan, mahaifin ki kuma shi ne wanda ya hwara koya min kisan mutane, har sai da ya zamto in ban kashe mutum ba a rana ina jin kamar ban tabuka komi ba a ranar, sai da ya zama ni ke jagorantar kisan gari guda,na qone shi ni da yara na, duk bakowa ne ya maishe ni haka ba face mahaifin ki. Mahaifin ki ya aikata min laifin da ba zan iya yahe masa ba, ya sa an sace qauna ta, an yi lalata da ita da qananan shekarunta, duk wani buri nawa da nata an rusa mana shi. Shi yasa na yi alqawarin yanda ya cutar da  qauna ta, da nafi so a rayuwa ta, ni ma sai na cutar da abinda ya fi so a rayuwar shi, na so kwarai na cutar da ke, kamar yanda ya yi ma qauna ta, amma ki sani a baya na yi zina, daga baya da na girma sosai na fara jin kyankyamin ta,se na dena, dan haka ni yanzu a duk abinda ni ke bana zina, na biyu soyayyar da nake miki ta hana ni cutar da ke ta kowace hanya, dan haka da na yunqura zan yi lalata da ke sai na kasa, Sultana ke da Mubaraka ku na da matuqar mahimmanci ga rayuwa ta, ba zan bari a cutar da ku ba, balle ni na cutar da ku da kai na. Kamar yanda na yi miki alqawari, duk sanda ki ka ji ba ki so na, ki fadi min zan sauwaqe maki aure na, ki koma ga iyayen ki, amma fa ki sani, ba zan kyale mahaifin ki ba, sai na dau fansar abinda an ka yi wa qauna ta ta wani wajen,zaman ki anan zai banna mai rayuwa (bata masa rai) sama da yanda kike tunani, domin na zauna da shi, kamar yanda mubaraka take a waje na, haka ki ke a wajen shi" Sultana ta ma rasa me zata ji a wannan labarin da Lawwali ya gama bata, abu daya kawai ta sani shi ne ta na son shi, alqawarin da ta masa ya na nan ba za ta sab'a ba, ta sani mahaifin ta ya fi bada mahimmiyar gudun mawa wajen lalacewar Lawwali, duk da ba shi ne ya fara b'ata shi ba, In ba a taimaki matashin da ke da basira ba to kuwa zai illata qasa shima, kamar yanda Lawwali yake yi a yanzu. Miqewa ya yi tsaye, ya ce, "Wannan shi na dalilin da yasa ban kusance ki ba, ina jiran na samu yardar ki da amincewar ki, saboda ban aure ki dan sha'awa ba, na aure ki ne dan ina son ki, kuma ina so in dauki fansar abinda Gwauna ya yi wa Mubaraka na" Shirun da ya ji, ya tabbatar masa da cewar Sultana bata yarda da shi ba, dan haka takawa ya fara yi, zai bar dakin, har ya kama hannun qofar ya ji Muryar ta da ta gaji da kuka ta ce, "Ina zaka je ka bar amaryar ka ta na jin yunwa?" Ta na nan kwance cikin bargon da ya rufe ta, ta ke maganar, cikin farin ciki ya juya ya na qare mata kallo, komawa ya yi ya zauna a gefen ta, ya janye mayafin da ya rufe mata gefen fuskar ta, ya shafa kuncin ta sannu a hankali . 'Daga ta ya yi kamar ya na daukan k'wai, a saman cinyar shi ya zaunar da ita,ya bata abincin, ta ci ta qoshi. Sannan shi ma ya ci, qarfe daya da rabi na dare ya yi, a tare suka shiga dan bandakin da aka yi musu na musamman, duk da cewa na qasa ne, amma dai ba a hade yake da wanda kowa ke shiga ba. Gani ya yi ta na alwala bayan ta wanke bakin ta, fita zai yi abin shi ta ce, "Ba zaka yi alwala ba? Na ga baka yi sallah ba fa" Kamar ya fada mata shi ya manta rabon da ya dora goshin shi a qasa ma, kawai ya tsaya, ya na kallon ta, bata sake masa magana ba, ta idar ta fita, ya jima a tsaye kamar ba ze yi ba, ya dau butar ya yi alwala, ya bi bayan ta. Babu abin sallah a wajen, a saman carpet din wajen ta tsaya, ta ce "Bismillah ka ja mu, muyi sallar isha'i, dare na yi, kar lokacin ta ya fita" Shafa kan shi ya yi, ya zauna a bakin gado, ya ce, "In ma na yi sallah yanzu ba zata karbu ba sultana basshi kawai ke ki yi sallar ki, na tabbata Allah zai karb'i taki, saboda baki zamo daga mutane iri na ba" Gyara zama ya yi a saman gadon ya kwanta. Mamaki ne danqare a cikin zuciyar Sultana me yake nufi da hakan???....... *Hummmm hummmm* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 45: A daren ranar haka Sultana ta na ji ta na gani, mijin da ya ke nata ya kwanta bai sallah ba, ba ta samu bacci ba sai da ta yi sallolin ta, sanan ta roqi Allah da ya shiryar mata da shi, a da in ta ga bai sallah ba sai ta yi tunanin ko ya yi a waje kafin ya je wajen ta, ko kuma zai yi in ya koma gida, amma tabbatar mata da ya yi, ya jima baya sallah abun ya daki zuciyar ta, mummunan duka kuwa. A qasan carpet din ta kwanta, har bacci ya dauke ta. Cikin dare ya tashi zai zaga, ya gan ta a qasa,  bai tashe ta ba sai da ya zaga can wajen yaran shi, ya ga kowa na lafiya, masu gadi na aikin su, masu bacci na baccin su, sannan ya koma daki, a inda ya barta nan ya same ta, tashin ta ya yi, cikin magagin bacci  ya taimaka mata ta kwanta a gado, suka ci gaba da baccin su. Da asuba Sultana bata tashi ta ga Lawwali ba, sannan ta yi mamakin ganin ta a gado, dan dai ba zata iya tuna sanda ta hau da kan ta ba. Lawwali bai shiga dakin ba har takwas na safiya ya gota, sultana ta yi wanka, ta gyara gadon da suka kwanta, ta dauke ledar da suka ci nama ta leqa waje ta wurgar, ta na hango yanda mutanen wajen ke ta mu'amalar su, kamar ba abinda ya dame su, ba alamar tsoron wani abu, ko fargaba a tattare da su, daga nan inda take, ta ke hango yanda suke bin layi su Barirah su na zuba musu abinci, wasu kuma na zaune a dandaryar qasa, sun kama kai, da alama a wajen suka kwana, sun shawu sun yi tatil, sun kuma tashi da ciwon kai. Daga nesan ta hango Lawwali da wasu zaratan mazaje a wani fili, ya na koyar da su fad'a, kura ma jikin shi da babu riga ido ta yi, daga baya ta sauke ajiyar zuciya, ta juya za ta  koma ciki, d'an dakatawa tayi, a daidai lokacin da ta kula ba ita kadai bace ke kallon surar jikin Lawwalin, wasu 'yan mata ne zaune riqe da plates da cups na abinci da suka karba,sun Qura wa jikin mijin nata ido, kamar su jawo shi gare su . Sultana tunda take bata taɓa jin wani abu mai zafi da ciwo a qirjin ta mai kama da wannan ba, da sauri ta fada dakin ta, ta dauki mayafin rigar ta, ta zira takalmin ta, ta tafi inda Lawwalin yake,tafiya take  cikin sauri, ta na kartar qasa da takalmin ta, saboda yashin da ke wajen, bata saba da tafiya cikin yashi haka ba, har qoqarin faduwa take amma haka ta isa gaban Lawwali, duk idon mutanen da ke wajen ya koma kan su. Cikin tura baki ta ce mishi. "Ina ta neman ka tun dazu ban gan ka ba, ashe ka na nan ka na bude musu qirjin ka su nata kalla ko?" Dan had'e girar shi ya yi, cikin rashin fahimta, su wa ya budewa qirjin shi? Juyawa ya yi, ya ga yanda wasu matan ke kallon shi, to indai wanan ne ai ba yau aka fara ba, shi be ma dauki wannan wani abu ba, kallon yanda take ta tura baki, ta na babbata fuska yake, a hankali murmushi ya fara maye gurbin hade fuskar da ya yi. Hannayen shi biyu ya sanya ya daga ta sama, ita kuma wata iriyar kunya ce ta kama ta, sai da ta yi da ta sanin zuwa wajen shi, da ta sani ma aikawa ta yi aka kira mata shi, yanzu wannan abun kunyar da ya ke qoqarin ja mata fa? Dariya wajen ya dauka, dan ganin yanda take ta dukan qirjin shi, ta na wutsil wutsil da qafa, Ita dai ya sauke ta qasa ya saka rigar shi, shi ne burin ta, "Ran ki shi dade, nan wajen da ki ka gan  su, duka qanne na ne, ba wadda nika so, ko ta ke so na, su na d'ai so na a matsayi na na shugaban su, kuma yaya a wajen su, ki kwantar da hankalin ki, jikin ga naki na ke dai," A hankali suke magana, wanda ba lallai ne na gefen su ma ya ji me suke fad'a ba, iya burgewa kawai sun gama burge mutanen wajen. Kwantar da kan ta tayi a kafadar shi, ya sassauta riqon da ya mata, su na dariya, baki ta dan tura, ta daga kai ta kalle shi ta ce, "Ni dai ba na so ka na zama ba riga,ko vest ne ka na sawa pls" "Ok" Ajiye ta ya yi, ya dau rigar shi, ya rataya a wuya, ya ja ta, zasu koma ciki, matasan da ya ke horar wa sun zaci tafiya za su yi, suka ji ya ce, "A ci gaba sai 10am, a tashi" Ba bata lokaci kuwa suka ci gaba, shi kuma ya shige dakin su da matar shi, mai kishi. Matan wajen wasu sun ji haushin yanda ta dauke musu shi, wasu kuwa ta burge su, yanayin yanda take shagwaba da jan ra'ayin ogan nasu ya basu sha'awa, basu tab'a ganin shi a irin wannan yanayin ba. Su na shiga ya jingina da bakin qofar ya wurgar da rigar shi, ya tokare qofar wajen da hannun shi daya, dayan kuma ya sa shi a qugun shi ya na kallon ta. "To Sultyn Lawwali, ga Lawwali gaban  ki, ki kalla har sai ke ce ya isa haka nan" Rufe fuskar ta tayi, ta ce, "Ni fa ba haka na ke so ba" Takawa yayi gaban ta, ya zauna daf da ita, ya na kallon fuskar ta da ta rufe, ya zare hannun ta ya dora a qirjin shi, ya ce, "Haka ki ke so to?" Da sauri ta janye ta miqe tsaye, cikin shagwaba ta sa kukan da ba ko hawaye ta ce, "Ni fa yunwa nake jiii" Da sauri ya nutsu, sai a sannan ya tuna ba fa a kawo musu abinci ba, su Bareerah ya sa su dafa abincin da zata iya ci, kuma har yanzu shiru. Ran shi b'ace ya sanya rigar shi ya tafi wajen su, su na tsaka da gyara cups din da suka dora musu a farantin ya isa. "Mi da ba ku kawo abincin ba tun dazu?" Cikin ladabi da kuma ban hakuri, suka masa bayani, ba ta iya irin abincin da ya ce a yi ba, sai da suka nemo wadda zata koya mata, sakin fuskar shi ya yi, ya musu godiya, ya karba da kan shi, zai kai, a tsorace Bareerah ta riqe farantin, ta na bashi hakuri ko da ta yi  wani laifin bata sani ba, "Yaseerah da Barirah tsakani na da ku sai godiya, na dai hi so na kai mata da kai na ne, amma ba ku yi min lehin komi ba, na gode, ku tai ku ci abincin ku" Godiya suka yi, ya tafi, hira suke a tsakanin su, Barirah ta ce, "Walle na hankura, da gani nike kamar Oga na so na, tunda ba shi yi min hwada, kuma komi nicce ya na yi, ko ya bari, ban dai iya shiga tsakanin shi da matar shi, yanda ya ka son ta haka, kallo ma ba zan ishe shi ba" "Ai na fada maki tun hwarko, da ya na son ki da ko so guda ne, da ya maki maganar, kin dai ga yadda kowa ke da budurwa wajen ga, a manyan nan, sai wanda suke da mata ne kadai basu da budurwa, ai da ya na da ra'ayi da ya yi magana" "Kaiii mu je mu ci abinci yunwa ni ka ji wallah" A can dakin su Lawwali kuwa sun ci sun qoshi, sai suka tsaya hira abun su, ranar dai ba wanda ya sake ganin Oga sai azahar. Ya na ganin za ta yi sallah ya bar dakin, takaici duk ya dami Sultana, wato ba ma ya so ta masa maganar sallah ko? Ba komai za su hadu ne, shi ma abinda ta kula ya na kwadayi tsakanin safiya da azahar dinnan ba zai samu ba. *************************** Da yamma motar gidan su Hansatu ta tsaya a qofar gidan su Isah, driver ne ya yi ta doka sallama, kamar an mintsini 'Yabbuga ko an kira ta haka ta bar majalisar su data cika da su Lamishi, ana hirar bikin Lawwali, da takura wa Lamishi ta kai su gidan Lawwalin su ga gida, yau ma Mai Buruji ce ta yanka qarya tace sun tafi qasar waje, fadawa gidan Hansatu 'Yabbuga ta yi kamar an aike ta, ta na ta kwala wa Hansatu kira, "Ke hito, motar gidan ku ta taho, ana ta bidar ki,kin qule a qurya," Hansatu ce ta miqe daga kwancen da take, cikin duhu, share hawayen ta tayi sosai, yanda ba za a gane ba, ta daura dankwalin ta, ta gyara doguwar rigar ta, da Hajiyan ta ta dinka mata, ta fita. "Wane na ka bid'a ta?" (Wa ke nema na) "Nace maki motar gidan ku ce ta taho, ana ta miki sallama ba ki jiya ba" "mu je, gani nan zuwa" Hijabin ta ta sanya, ta bi bayan 'Yabbuga da ta qi tafiya, sai ta ga kwal uwar daka. Bayan sun gaisa da driver ne ya ce Hajiya na gaishe ta, ta kuma bada saqo a kawo mata, ga takarda, ga kuddi, ya zaro ya miqa mata. Fita ya yi ya dinga shiga da kayan da ya zo da su, sai daya gama tass, ya ce "Ta ce ki na ganin bayanin komi cikin takardar, abinda baki gane ba ki mata waya" "Tauu ya yi Malam Jafaru, ka gaishe ta, na gode" Sallama ya mata ya tafi, 'Yabbuga kuwa majalisar da bata koma ba kenan,  Hansatu kuwa kayan da bata bude ba kenan, dan bata san mene da mene ba, kar ta bude gaban ta ya zamana bai kamata ta gani ba. Har sai da suka ji Machine din Dan Jumma sannan ta fita a gidan ta na b'ata rai. Ta na fita kuwa ta sa su Ameena suka shigar da kayan parlour suka rufe qofa, cikin ladabi Ameena ta tattare kan qannen ta suka bar  wajen, ta ji dad'in hakan sosai, albarka ta sanya musu, sannan ta bubbude kayan, har da akwati qarami. Kaya ne na sanyawa kala biyar, sai rigunan bacci, da undies ,takalma biyu, da turaruka kala kala, har da musk. Sai dabino mai kyau mai yawan gaske, sai kayan qamshi, da bagaruwar mataa danya, ganyen magarya, da lalle . Kaiiii makaranta abubuwa ne masu tarin yawa Hajiya ta aiko mata, har da kayan abinci da nama soyayye. Hansatu ta na dubawa ta na godiya ga Allah, tare da sanya wa mahaifiyar ta albarka, da yi mata fatan samun cikawa da kalmar shahada. Takardar ta bude ta karanta kamar haka. ~Hafsat ina fatan ki na lahiya da jikoki na? Na san dai mijin ki ya sanar da ke shi na nan dawowa qarshen wanga sati, to ga kayayyaki nan,ki yi amfani da su yadda na nuna maki rannan da ki ka taho, sannan wannan bagaruwar da ganyen magaryar, ki na diban bagaruwar kadan da ganyen magaryar ki tafasa ki zauna ciki, amma a yanzu ki dauki bagaruwar danyar ki matse ruwan ta ki liqe a wannan haqorin da ya bule- Ta na gama karantawa ta dinga dariya,dan ta gane haqorin da Hajiyan ta ke nufi,Hajiya akwai hikima, ta tuna sanda take mata complain din ta na jin gaban ta kamar ya bude, shi ne Hajiyan ta yi wannan dabarar,dariya ta dinga yi, sanda ta tuna, wani lokaci kafin auren ta, an yi auren qanwar Hajiyan, sai suka je gidan, suka shiga har dakin amaryar suka ga gadon amaryar duk ya ɓaci, ta na ganin Hajiya na kallon wajen, sai ta cire dankwalin ta ta rufe wajen, ta na ta jin kunya. Bayan sun koma gida sai Hajiya ta haɗa dankwalaye ta bawa Hansatu, ta ce ta kai ma auntyn ta ta ce mata, in ji Hajiyan wai ta yi amfani da dankwalin nan ta rufe saman gadon nata saboda qura, amma da zata cire ta wanke qurar da ya fi. Sai bayan ta yi aure a washe garin daren ta na farko ta fahimci me Hajiya ke nufi da hakan. Ta na tsaka da dariya ta koma kukan baqin ciki, Wannan wace iriyar rayuwa take ciki? Wai ace mijin ka bai damu da kai ba, yau kusan watan shi daya da tafiya, ba kira ba saqo, sai dai ta ji maganar shi a bakin mahaifiyar ta, ba komai, za ta bashi mamaki. Tattare kayan ta yi, ta ware duk wanda ya kamata ta ware, sannan ta kira su Ameena ta deba musu soyayyan naman suka ci, cikin nishadi. ************************** "Ni fa Sultan ban san me ke faruwa ba, yau kwana biyu kenan, ina kai qawaye na gidan su Sultana Amma ina ganin gidan a ruhe ,shin lahiya? Ko ba kuyin waya ne kaima? Dan ni dai na kira layin ta ba shi shiga" "Ni ma dai layin nata bai shiga Hajiya, amma na san duk inda take ta na tare da mijin ta, kar ki damu" Ai sai a wannan lokacin ne hankalin ta ya shiga jikin ta, a zabure ta miqe, ta hau kiran layin Gwamna Halliru, ta kira ya fi sau hudu ana sanar da ita ya na meeting,daga qarshe masifa ta balbale mai amsa wayar ta ce ya kai ma gwamna wayar shi, ba ruwan ta da wani meeting ita. Yanayin yanda ta daga hankalin ta ya bawa Sultan Mamaki. Mene ne abun damuwa dan an ce mace na tare da mijin ta ba kwarto ba????...... *Gane min hanya Sultan, wai makaho ya so gulma* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 46: Fitowar gwamna Halliru daga meeting ba wuya, Hajiya Ikee ta sake kiran wayar, da  sauri aka miqa masa ya karba, bayan ya amsa ne ya kara a kunnen shi,jin Muryar Hajiya cikin tashin hankali ne ya sanya shi matsawa daga cikin mutane, ya fara tambayar ta dalilin tashin hankalin ta, Sultan ta kalla wanda ya dauki remote ya na sauya tashoshi hankali kwance, ta ɗan matsa daga inda yake, ta fara magana. "Sultana fa da wannan shegen yaron ba su gidan su,ni ina jin tsoro musamman tunda ka ga basu fada muna inda su ka tafi ba, Kuma gashi ba a samun ta ga waya" "Kwarai da gaske yau nake so na tambaye ki ko ku na waya, ban samu dama ba, tunda ban kwana gidan ba, amma abin ya na dauren kai ace ba ta kiran kowa, bari zan bincika in ji, ki kwantar da hankalin ki, kin dai san ba yarinya bace ke, tunani kadan zai sa miki ciwo" "Wai kai in ba ka fadan baqar magana ba baka jin dadi ko? To ai na san ba yarinya ni ke ba, ba se ka maimaitan ga kunne na ba" A hasale ta kashe wayar ta koma ta zauna, tunani ya mata yawa, ina su Sultana suka tafi? Miqewa ta yi ta haye sama, Sultan na bin ta da kallo, tunawa ya yi, me ya sa wai ba zai kira Lawwalin ba, ya ji su na ina? Gwada layin Lawwali ya dinga yi be samu ba, murmushi kawai ya yi, da dukkan alamu ba sa qasar nan, kallon shi ya ci gaba da yi hankali kwace. **************************** Hansatu ce ke ta duba kayayyakin da babu a gidan,ta na ta rubuta abinda za ta siyo in ta je kasuwa, gani tayi garin da Hajiya ta haɗa mata, take kunu da shi ya qare, gashi bata san kayan hadin ba, daki ta koma ta dauki wayar ta, ta kira Hajiyan, sai da suka gaisa, sannan ta ce, "Hajiya kayan hadin garin kunun nan ni ka so ki hwadi min, ya qare, ina so na hada wani" "Tau ki na ji ba, in kin je kasuwa, ki bidi wajen masu awo, ki siyi, alkama Sa'i guda (kwano daya/mudu daya), ridi rabin sa'i,(kantu) farar shinkafa rabin sa'i , aya irin qananan nan na kunun aya rabin sa'i, sai ki tai wajen masu Islamic chemist, sun fi saida hulba mai kyawu, ki sai hulba mai kyawu roba biyu, ki sai diyan ('ya'yan) habbatussauda, to da kin dawo gida gyara kowannen su za ki yi, ki wanke, ki busar, hulba kuma ki soya ta haka nan, sai ta yi qamshi, sai ki game su, a niqa miki kamar gari, sai ki zanka damawa ki na sha da madara, wannan hadin man shi na nan be qare ba ko?" "Eh Hajiya be qare ba, ko ba man tahwarnuwa (tafarnuwa) da man hulba, da man zaitun, da man hancin kade, (kaninfari) ba? Shi na nan ina yin matsi da shi, kuma na ji sauqin qaiqayin da na ke ji sosai, na ji har da matsi shi na yi Hajiya," "Kwarai da gaske shi na da kyawu kwarai wallah, tau yanzu ga wani ki siyo in ki na tahowa, ki siyo man zaitun, da man hulba, ki game su waje guda, ki Zanka shafawa ga maman/nonon ki, shi na da kyau kwarai kwarai," "To Hajiya na gode sosai, Allah shi saka maki da alkhairi" Sallama suka yi, ta kira Ameenah ta ce ta kula da gida,da qannen ta, ta ce ta kulle gidan, in an buga bata leqa ta gan ta ba, kar ta bude ko da ta ji Muryar ta,ta sanar da ita za ta duqar da kanta jikin wata yar bula da ke kofar in suka hada ido to sai ta bude mata. Ta na fita kuwa Ameenah ta yi kamar yanda Umman su ta ce, Ita kuwa hansatu bakin ta dauke da addu'ar bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala quwwata illa billah ta bar gidan, ta na tafe ta na yin dik wani tasbihi ga Allah da ya fado bakin ta. Hansatu saboda ta san ta bar yara su kadai bata wani jima ba ta koma. Sai da ta musu abinci, ta gyara gidan sannan ta samu carrot da cucumber ta goga su a abun goga kubewa, waje mai qanana qananan, sai suka fito kamar an markada su, ruwan ya fito sosai. Tace ruwan ta yi, ta zuba masa zuma, da lalle, da madara kadan, sai sugar da dan gishiri, sai baking soda da ta siyo, ta fasa kwai guda daya, ta matse lemon zaqi daya, da lemon tsami daya, sai madarar turare mai qamshi, sai kurkur, ta juya sosai sannan ta bi jikin ta duk ta shafa, Ahmad ne ya dinga nuna ya na jin tsoro, ai kuwa ta dinga bin shi, su na ta guje guje da wasa da yaran nata, su na kyalkyala dariya. Bayan ya yi awa daya ta je ta wanke jikin ta ta yi fesss. Man carrot din da ta hada sati biyu da suka wuce ta dauko ta ga ya yi yanda ake so, ta tace, ta diga masa madarar turare ta shafe jikin ta da shi, nan da nan ta dau qamshi da kyalli, duk wanda ya san Hansatu a baya, ya gan ta yanzu ba zai tabbatar ta samu sauyi mabayyani, ta hadu ta hadu ta gaji da haduwa, ta cika ta yi bul bul da ita. (Yanda ake hada man carrot, za ki wanke carrot din ki ki kankare dattin ki goga a abun goge kubewa, ki zuba a mazubi mai murfi, sai ki kwara masa man zaitun/kwakwa ki rufe, duk bayan kwana biyu ki dauko ki juya ki juya,ki mayar ya qara kwana biyu, a haka har sai ya kai sati biyu, zaki tace, ki na shafawa ya na matuqar gyara fata kwarai) Hansatu dai da yara kullum a cikin gyara gida suke da kan su, ta sanya sabuwar ledar daki, ta sauya zanin gado da labulaye, ta sauya masa food flask ,ta sauya masa jug da spoons,hatta da sleepers sai da ta sauya masa, ta sai masa towel din wanka. Yau ma kamar kullum sun gama gyara gida Hansatu na zaune ta na kallon qaramin madubi, ta na ganin yanda fatar ta ke sheqi, kalar ta mai ruwan cakulan mai duhu na komawa wani ruwan madara mai haɗe da coffee kadan, sai zabga murmushi take, dan ta san ta gama komawa mace mai aji, macen da ta fi qarfin walaqancin namiji, ta kowanne fanni, sauran abu daya take so ya faru, dan ta qara kankaro darajar ta. A baya rashin kudin gyara jikin ta, da rashin bata abincin da zata ci mai kyau ya gina mata jiki, ta amfana shi ma ya amfana da ita, ya sa duk ta lalace ta kowanne fanni, hatta da gashin ta a da ya lalace, ba wani tsaho ba kyawun gani, dan ko man kitso bata da shi. Komai nata a lalace a wulaqance, amma a yanzu wannan Hansatun ta daban ce, dan ko a da ba ta yi wannan haduwar ba, a yanzu in Isah ya gan ta ya kuma kusance ta bai sauya hali ba, to ba zai taba sauyawa ba. Tashi ta yi ta shiga daki, ta dauki turaren musk fari mai kyau din, ta dangwala a hannun ta ta shafa a gaban ta, ta fita wanke hannu, ta tsaya cak, cikin tsananin mamaki, da farin ciki. Tunawa da abubuwan da Isah ya mata ne ya sanya ta shanye farin cikin ta a cikin ta, ta wuce ta wanke hannun ta, ta koma inda yake a tsaye ya na bin ta da kallon mamaki, shin Hansatu ce ko wata yar uwar su? Ya na nan tsaye ta isa gaban  shi ta karbi jakar da ke hannun shi, ta bar masa akwatin, "Sannu da dawowa Baban Ameenah" Kasa magana ya yi, domin kuwa hatta da Muryar ta in ba ya b'ata ji ba, sai ya ji kamar ta sauya. Tafe take ta na kada mazaunan ta da suka fito yanzu, ta shige, dakin su ta ajiye kayan, ai ya na ganin ta b'acewa ganin shi ya ture Ahmad da ya qanqame shi ya bi bayan ta. Ameenah tattara yaran ta yi tace su je dakin su, Ahmad ya so ya mata musu, ta masa tsawa dole ya bita suka tafi dakin su. Ya na shiga ya ajiye kayan hannun sa, ya nufe ta, kamar yanda ya saba, ba wani wasanni, ba komai, haka zai yi ya tafi, ba ruwan shi da ta samu biyan buqata ko bata samu ba, shi dai zai yi ya tashi. Dakatar da shi ta yi da hannun ta ta ce, "Meye hakan? Ah ah malam dakata mana? Daga dawowa ba sannu, ba Allah shi sawaqa, baka san a halin da muke ciki ba, kawai zaka fara qoqarin debe wando! To ka na kuwa maida shi, dan banda ra'ayi" "Hansatu, Hansatu ni ne fa, ni ne Isah ko baki gane ni ba?" "In na gane ka kai ka gane ni ne? Haka ka tafi ka bar ni? Ka ga wai shin ma in tambaye ka, dama aure na na bisa kan ka ka tafi ka bar mu ba abincin da zai kai wannan kwanakin da ka dauka,ba kudi, ba kira ka ji lahiyar mu, ba kira ka ji mun ci ko bamu ci ba, wanne hali nake ciki da yara da dakon soyayyar ka, da auren ka me....." Kuka ne ya kwace mata, mai maqaqi a wuyan ta, bata so yin kuka ba, a yanda ta tsara yi masa, amma ta kasa jurewa. Barin dakin ta yi gaba daya, ta je ta haɗa masa ruwan wanka, ta dumama miyar da ta dafa musu shinkafa, ta zuba masa komai yanda ya dace, ta zuba soyayyan naman da Hajiya ta aika musu. Inda ya saba cin abinci nan ta aje masa, ta shige cikin yaran ta, ta kwanta ta juya musu baya, su ma shiru suka yi kamar ruwa ya ci su. Isah kuwa wanka ya je ya yi, dan yanzu zaman Saudiya ya sa ya fara tsafta, ya na komawa ya ga abinci ya dauka ya ci, har lumshe ido yake, ya yi kewar abincin ta mai dadi . Bayan ya gama ne dabara ta zo masa, murmushi ya yi, ya kwalawa Ameenah kira, da ta je ya ce ta kira masa Umman su Ya san ba zata qi ba, dan a halayyar ta ya jima da sanin ,ba ta son yaran su na gane rashin jituwar su. Ai kuwa Ameenah ta isar da saqon gyatumi, ina nan tsaye ina jira na ji shin Hansatu zata je ta wa Isah Barka da dawowa mai kyau ko kuwa?????? *Mutanen kwarai me kuke gani? Zata biye masa nee ko kuwa?* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 47: Hansatu na nan kwance ta na jin yanda ake dambe tsakanin soyayyar Isah da tsanar shi a cikin zuciya da ruhin ta. Ameenah ce ta shiga ,cikin ladabi ta ce, "Umma na fada maki fa Baba ya ce na kire ki tun dazu amma ba ki je ba, kar shi yi fada fa" Ita kan ta ta yi mamakin rashin zuwan shi ya fara sababi, amma bari ta je ko dan kar ta sawa yaran ta tunanin rashin kunya a zuciyar su, hakan zai yi matuqar tasiri wajen d'arsa musu tunani kala kala akan qin zuwan nata. Bismillah ta yi, ta sauka daga katifar su, ta gyara rigar ta, sannan ta tafi. Ta na shiga ta gan shi,kwance, alamar jiran ta yake, har yanzu zuciya da ruhin ta ba su tsaida hukunci akan abu d'aya ba, shin za su ci gaba da son Isah da daraja shi kamar da, ko za su tsane shi ne da nuna masa tsantsar qiyayya? Ta na nan tsaye ta ji Muryar shi, "Wai ke me ke damun ki ne? Ko kin zama kurma ne kuma makauniya? Ba ki ga kiran da nake miki bane ki ke a tsaye?" Wani baqin ciki ne ya tokare mata wuya, a yanda take jin ta, yanzu ta wuce wadda namiji zai nema a haka, ita mace ce da namiji zai bi, zai nunawa tsananin maitar shi da kwadayin shi,wadda za a nema da soyayya, da wasanni,ba wai a neme ta kamar ana neman akuya ba. Wani tunani ne ya shigi zuciyar ta nan take, fita ta yi, ta zuba abinci da nama, ta kai wa Ameenah ta ce, "Ameenatu zo ku kai wa Mama 'Yabbuga, ku zauna can kar ku je ko ina, zan zo da kai na na taho da ku," "To Ummaa" Cikin zumudi da son yawo Bilkisu ta sanya hijabin ta, dan sun jima rabon da su fita waje, ko za su fita sai da Ummaan su. Su na tafiya ta saka sakata, ta koma dakin da Isah ke kwance ya na ci gaba da jiran Hansatu, ya fara quluwa da sabon abinda take masa, ta na shiga ta tura qofa ta rufe window, duk qoqari na na dauko rahoto ya gagara. Ba su suka bude qofar nan ba sai bayan awanni biyu cur, tashin kuka nake ji, ina kasa kunne sai na ji ashe ba mutum daya ke kukan ba, cike da Mamaki na leqa, Isah na gani durqushe gaban Hansatu ya na kuka har da majina, ya na roqon ta bai qoshi ba kar ta masa haka. "Dan Allah Hansatu ki barni na qara ko sau guda ne," Hawayen ta ta share, ta d'auki sabon towel din ta, ta daura, ta kalle shi, sannan ta ce, "Ka san kuwa da yaya na taushi zuciya ta ka yi har so biyu? To Bari na fada maka wani abu da ban so fada maka ba, a baya ina maka son da tunda nake ban taba jin ko ganin macen da ke son mijin ta ba kwatankwacin yanda ni ka son ka, ban ta ba ji ko ganin macen da ke wa mijin ta biyayya ba kamar yanda ni ka ma, ba dan ban san darajar kaina ba, sai dan tsananin son da nake maka, ka san mi? Abun haushi abun takaici, wannan son har yanzu ya na nan, amma wani sabon al'amari ya shiga son, tsanar ka ta gauraya da soyayyar ka a zuciya ta, na rasa wanda zan dauka, na amsa kiran ka ne kawai, saboda ni bautar Allah nake a zaman mu, ba bautar ka ba ISAH, (cikin sauri ya kalle ta, domin bata taɓa kiran sunan shi ba, tun bayan auren su) da bautar ka nike da na sa qafa ta na shure ka, na yi fatali da kai, na tofa maka yawu ga huskar ka, dan qasqantar da kai, da bautar ka nike ba bautar Allah ba, da yanzu ina gidan mu, ba zan zauna da namijin da ba shi ganin daraja ta ba, da qima ta, da mutunci na ba, da bautar ka nike da kafin ka dawo na bar gidan nan, kar ka yi zaton wai dan na samu iyaye na sun amshe ni ne yanzu,na gwammace ni da d'iya na mu kwana a titi da mu ci gaba da zama da kai,.... amma....amma ba zaman kaina nake ba, har yanzu kai miji na ne, kuma qarqashin ka nake, sannan bautar Allah na ke, bai cin haka nan,....da zan biye wa zuciya ta, da zan biye wa zuciya ta Isa,......" Kasa qarasa kalaman ta tayi,saboda ba zasu fad'u ba, abubuwan da ta ke da qudirin yi mishi a zuciyar ta su na da yawa, tsoron fushin Allah akan ta ne kawai ya mata katanga da aikata su, komai bawa zai yi, kar ya tuna kan shi, ya tuna mahaliccin shi, kafin ya aikata komai, shin Allah ya yarda da abinda zai aikata ko bai yarda ba? Wankan ta ta je tayi, ta sake yin na sabulun da ta yi wa hade haden kayan gyaran jiki, da turaruka masu qamshi. Ta koma d'akin dan shirya wa, a nan durqushe inda ta fita ta bar Isah ya na nan, bai motsa ba, ran shi a matuqar bace ya ke, amma ko karen hauka ne ya cije shi, ba zai iya mata komai ba, ko da da harara ne, dan a yanzu bai san iya ina Hansatu ta tsaya ba, bai san me ne ne akan ta ba, kwarjinin da ta masa ba zai bar shi aikata mata komai ba, wannan shi ake kira aji, Hansatu ta kankaro ajin da Isah na matuqar shakkar ya kusance ta da rainin wayo, dandana masa kan ta da ta yi, ya sake birkita masa kai, ko da farkon auren su bai samu abinda ya samu ba a yanzu daga gare ta, wannan Hansatun kamar an sauya masa sabuwa ne. Bata kula shi ba, haka ta gama shirya wa, yamma ta yi sosai, dan an kusan kiran sallah ma, ta sanya sabon takalmin ta da sabon mayafin ta da ya yi kala da riga da skirt din da ta sanya na qananan kaya ta fita zuwa gidan 'Yabbuga, Hansatu fa jama'a ta koma Hafsatu, gaba daya ta sauya ta kowane bangare. Sallama ta yi, ta gaishe da 'Yabbuga da ke zaune a qule gaban yaran, sai zabga tsaki take. Mamakin ganin bacin rai kwance a fuskar 'Yabbuga ne ya kama Hansatu, cikin mamakin ta ke tambayar ta me ya faru. "Hummm Hansatu ke dai sai dai ni ce Allah shi yi miki sauqi, kin bi kin koyawa yara baqar tabi'a, tunda sun ka shigo sun ka kawo abinci na yi godiya sun ka amsa, nace kwana (bacci) ki ke ne da Ameenatu tace ke ce su zauna sai kin taho, Diyan ga sun ka debo ijiya(ido) sun ka zuba min(Aminatu ta ce kin ce su zauna sai kin taho,suka dauki ido suka saka min) qalallahu qala ta'ala ba wanda yace min cikin su, har da wanga d'an tatsitsin yaro, maganar duniya sun manna min hauka, ba wanda yace min komi, sun yi didd'didd'ifff" Dariya Hansatu ta sa, dan ta san wannan aikin Ameenatu ne, ita ce zata hana su magana kan su shiga, Bilkisu ta sha fad'a mata, in sun je waje Ameenatu na hana su magana, komai aka tambaye su, su ce su ma basu sani ba, ko su yi shiru su zubawa mutum ido kawai. "Ki yi hankuri, na gode da ki ka aje min su, bari mu tafi gida, mangariba ta yi" Tsaki 'Yabbuga ta yi, ta miqe daga gaban Ahmad, da tai Wa zaman neman gafara, ba kalar lallaba yaron da bata yi ba, dan ta ji labarai a wajen shi ya qi bude baki sam. Ita kuma kamar mayya, a nan gaban su ta cinye abincin da suka kai mata, ta na yi ta na tambayar su gidan su, su kuma su na ta kallon ta, sun qi amsa ta. Sai da Hansatu za su fita ta juya ta ce ma 'Yabbuga, "Yau fa Baban su Ameenah ya dawo," Wata gud'a da shewa 'Yabbuga ta buga, ta buga cinya, kafin ta yi magana Hansatu ta tisa qeyar yaran, ta ce su yi gida, ita kuma ta tsaya, dan 'Yabbuga na iya bin ta, har gida, ta fadi abinda zai sa wa yaran ta tunanin me ake nufi da kazan nan da aka fada. "Hahaiiiiii cassss! ko da na ji, yanzu na ji batu,dan ko na san ruwa da iska ba ki barin d'iyan nan zuwa ko ina, ku na nan manne da juna, ashe ashe uban su ne yaddawo ana can ana biyan bashi , shi yasa aka koro su, tauuuu, to ko za ki kawo su su kwana nan? Kar su yi mummunan gamo" Cikin takaici Hansatu ta kalle ta tace, "Bayan na haifi Ameenatu, Bilkisu ta biyo baya, duk su na nan sun fara wayo nayyi cikin Ahmad, kuma har yau idon su ko kunnen su bai gane musu komi ba in shaa Allahu, ke ga kuwa ba abinda za su gani a gaba ma, in shaa Allahu, na gode sai da safe" Hansatu na fadin haka ta tafi, 'Yabbuga kuwa ran ta ya ɓaci, nan da nan ta hau sakin maganganu marasa dad'i. "Keeeee wagga ban ce ki fada min baqa ba, yaushe na an ka jone da mijin har da za ki yi min kitihin yohi? Mijin da mun san komi, ba qaunar ki shi kai ba? Wanne irin kashin wahala ne baki sha hannun shi ba? Ba ci ba sha, ba sutura, nan nan gidan kin shigo shi kin yi maula ba a ko qirgawa, yo Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba, kai ku ji min yarinya da kitihi," Hansatu na cikin gidan ta tana jin komai, kasa jurewa ta yi, ta fita, ta koma gidan 'Yabbuga dake ta sababi, ta ke yi mata gori kala kala. 'Yabbuga bata ji shigowar Hansatu ba sai kalaman ta, "Na gode wa Allah, kuma na gode miki da Allah ya azurta mu a lokacin da muke cikin matsin rayuwa ta hanyar ki, na gode miki da kika taimaka mana a lokacin da muke da tsananin buqatar taimako, banda bakin yi miki godiya sai dai na roqi Allah da ya sauya maki halayen ki, daga munana zuwa kyawawa, shi saka maki da alkhairi, duk abinda kin ka fadi gaskiya ne, amma ki sani, in a baya Allah ya baki lada, to fa a yanzu zunubi ki ka dauka, domin kin zobe ladan da yabbaki ta hanyar yi min gori, kin san kuwa hanin da aka yi akan gori? kin tozarta ni akan abinda ki ka min a baya, kin yi min gori, ni kuma ba zan rama ba, amma kar ki manta abu guda, shi zama in ya hada ka da koma wane ne, abu guda dole sai ya faru, ko ku zauna lahiya kowa shi amfana da kowa, ko ku cutar da junan ku, ki dinga tuna baya kahin ki yi min gori, sai da safe" Jikin 'Yabbuga bai taba sanyi ba irin na yau, ashe Hansatu na da baki? A fakaice wadannan maganganun da ta wa 'Yabbuga dukkan su suna da fassarar su da ma'anar su kala kala, da 'Yabbuga na tuna baya da bata yi wa Hansatu gori ba, domin sai da ta fara morar Hansatu kafin Hansatu ta more ta, sai dai duk abinda Hansatu ta yi wa 'Yabbuga Hansatun bata taɓa sanar da kowa ba, itama 'Yabbuga bata taɓa fadawa kowa ta mori Hansatu ba sanda ta na amarya, amma ko gishiri hansatu ta karba wajen ta, sai ta qara tace har da Maggi da mai ta bata. Jiki ba kwari ta yi alwala ta shige daki. Hansatu kuwa ko da ta koma bata ga Isah ba, ba kuma ta ga akwati guda ba, a cikin kayan da ya zo da su,bata ce komai ba, ta jawo dan qaramin gas din su, ta ɗora ruwa, ta na so ta yi musu abincin dare. ************************** Gwamna Halliru ya kira wayar Lawwali, cikin nasara kuwa ta shiga, ya na dauka Gwamna ya fara magana cikin fada. "Lawwali ina ka kai min d'iya ta? Lawwali in wani abu ya samu d'iyaa ta..." "Uban mi zaka min in wani abu ya same ta? Na ce uban mi za ka min? Ka ga.." Sauke Sultana ya yi, da ke kwance a jikin shi, ta na wa kan shi susa, wai ta na so ya yi bacci, ya huta da horon da ya dage ya na bawa yaran shi, fita ya yi waje, dan baya so ta ji da wa yake magana, duk da ya kula hankalin ta ya tashi, da jin kalaman shi. "...na ce uban mi ka isa ka min? Kai ka san ko ni wane ne, inna ga dama a yau ba zaka kwana gidan gwamnati ba ko gidan ka, ka san ba ka kwana ko? Kaiii inna so yau da kai da iyalan ka kafff ba ku kwana duniyar ga baku kwanan ta ko? To mi zaka min?" Wasu irin jijiyoyi ne manya manya suka fito rudu rudu a goshin Lawwali, qirjin shi da babu riga, sai bugawa yake da qarfi, hannun shi d'aya ya dunqule kamar mai shirin kai naushi. Gwamna Halliru ne ya sassauta murya ya ce, "Lawwali kai wa Allah kar ka cutar da d'iyaa ta, she is innocent, ba ta da wani alaqa da abinda ke tsakanin mu, na amince, na yarda ban kyauta maka ba, duk yanda kake so ka yi ka yi da ni, amma kar ka cutar da diya ta" Wata mahaukaciyar dariya Lawwali ya saki, sai da yaran shi da ke waje suka kalle shi, sun san kalar dariyar, dariya ce ta ɓacin rai matuqa, kuma ko waye Lawwali ke wa irin dariyar nan, ya na gab da d'and'ana azabar Lawwali. Tafiya ya yi jikin wata bishiya ya tsaya, sannan ya ce, "Kar na cutar da d'iyar ka fa kace, she is innocent, me qaunata ta yi maka? Bari in maka da Yaren da zaka fi ganewa Excellency you are going to regret making me the way I am today, ba dai turanci ne ba? Na iya shi, ga shi nan na yi ma, innocent d'iyar ka ka san yanzu haka ta na can na..." Cikin b'acin rai Gwamna ya ce, "LAWWALIII !" Lawwalin ma a hasale ya ce, "HALLIRU ! Babu yadda za ka yi da ni, sai na shayar da kai gubar da ka dura min ta ta'addanci, sai na lalata rayuwar ka ta inda baka yi zato ba, sai na qarar maka da duk wani abinda ka mallaka, ko me ne ne shi, sai na maida kai abin kwatanci a Nigeria kai har da wasu qasashen, sai na nuna maka ba kowanne d'a ya kamata Ku manya ku lalata wa rayuwa ba ! Sai na shayar da kai abinda ka shayar da ni na baqin cikin rayuwa da duhun ta" Kashe wayar ya yi, ya wurgar, ya dinga sauke wani irin nishi, duka ya dinga kai wa bishiyar da ya ke tsaye a jikin ta, yaran shi duk sun tsaya cirko cirko, ba mai zamar da ya isa ya tunkare shi a wannan halin da yake ciki. Gashi duk ya ji wa kan shi ciwo, da dane zuwa zai yi ya debo mutane ya yi ta kisa ba gaira ba dalili, amma yanzu ya na qoqarin sauyawa, daga yawan kashe kashen da yake. A guje Barirah ta fad'a dakin su Sultanan ba tare da ta nemi izini ba, kwance ta ga sultana ta na ta tunanin da wa Lawwali ke waya, ta ga ran shi bace, har ya na kiran uban wa. "Ran ki shi dad'e ki gafarce ni, na shigo ba tare da izini ba, amma Oga na buqatar ki a waje, ya na can shi na ji wa kan shi ciwo" Ai kafin Barirah ta qarasa kalaman ta Sultana ta dire a qasa, jikin ta har rawa yake, wanne irin ciwo kuma? Dankwalin ta take ta ja, ya maqale a jikin gadon, sakin shi ta yi ta fita da gudu, Barirah na gaba, su na zuwa wajen Barirah ta nuna mata Lawwalin ta maqale a baya, Sultana na hango jini a hannun Lawwali ta sa kuka, ta tafi da gudu ta fada jikin shi da qarfi,hannu ya sa ya fizge ta daga jikin shi ya wurga ta gefe, ta fadi qasa, cikin bacin rai ya kalle ta, ya ce, "Me ye laifi na dan na je neman abinda zan ci? Ashe ba su da kuddin da za su iya ciyar da dika mutanen unguwar mu ma ba ni kad'ai ba? Ashe ba su da kuddin da za su iya daukan nauyin rayuwa ta ta kyautatu kamar yanda suka yi wa nasu 'ya' yan? Ashe ba za su iya ciyar da ni domin Allah ba tare da sun koyar da ni mugayen abubuwan da sun ka koya min ba a yanzu? Ashe ba su da halin taimakon mutanen qasar su sun ka fito siyasa? Ba su da zuciya da kishin qasar su sun ka ce za su mulke mu? Ashe su din azzalumai ne, shedanu ne, mayaudara ne, maqaryata ne? Ashe kan su kawai suke so da iyalan su da abokan su, babu ruwan su da tallaka, ko tallaka ya ci abinci, ko tallaka ya sha Magani, ko ya sha ruwa, ko ya ga hasken wutar lantarki, ko kar ya samu wadannan abubuwa duk ba damuwar su ba ne? Idan na rantse da Allah, Allah ba zai kama ni da lehi ba, mutum guda a manyan 'yan siyasar ga ya na da kuddin da zai ciyar da unguwa guda, ya basu kuddin yanke talauci, amma ba za su yi hakan ba, sun gwammace su maishe mu lalatattu, su yi anfani da mu dan cikar burin su, sun gwammace su juyar mana da basirar da Allah ya mana dan kar mu amfanar da kanun mu komai, mu amfanar da wasu, sun gwammace mu lalace mu haukace da shaye shaye da kashe junan mu, daga yau ina musu albishirin su fara qirga lalacewar tasu rayuwar,wannan alqawarin Lawwali ne" A guje ya bar wajen ya shiga dajin wajen, da qafa yake keta dajin cikin kuka, da hawayen shi, da Muryar shi,ya na jin yanda qayoyi ke huda kafar shi, amma bai tsaya ba, sai da ya koka duk wani baqin ciki, da bacin ran da yake ji, sai da ya fitar da duk wani qulli da ya dabaibaye masa zuciya, ya hana shi samun cikakken farin ciki. A qasa ya zube da guiwowin shi, ya kifa kan shi cikin yashin da yake fitar da hucin zafin ranar da ya sha, sama ya kalla ya ga yanda hasken farin wata ya wadatar da dajin, sakamakon duhun dare da ya yi,ajiyar zuciya kawai yake saukewa mai qarfi, cikin wata iriyar murya ya ce, "Na dau alqawari da Allah daga yau na ajiye duk wani abinda ni ke aikatawa mara kyawu, na kashe bayin Allah da qona gidaje da garuruwan su, na daina shaye shaye kuma zan yi hani da yin shi a sansani na, na dau alqawari da Allah da sani na ba za a qara aikata zina a sansani na ba, na dau alqawari da Allah sai na ga bayan duk wanda ke da hannu a lalacewar mu, na dau alqawari da Allah zan kawo qarshen ta'addanci a nahiyar nan tamu ta Zamfara da kewaye" Motsi yaji, cikin duhun dajin, juyawa ya yi bayan shi,dan ganin me ne ne ke tahowa, ba ya ganin komai daga nesa, cikin itatuwan akwai duhu, inda yake kuwa fili ne fallau yashi ne sosai a wajen. Da dukkan alamu koma me ke tahowa ya na ganin shi,amma shi baya ganin komai.......... *Hummmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmmm* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 48: Motsin na sake matsowa, Lawwali na sake yin shirin ko ta kwana, duk da ya na da tabbacin cewar wannan wajen dajin shi ne, hatta da namun daji masu cutar wa duk babu, sun kashe su. Mazaje ne guda biyar daga cikin matasan da ke sansanin shi, kewaye shi suka yi, kowanen su. dauke da makamai, mamaki ne fal zuciyar shi. Ta ya akai ya ke tare da mutanen da za su cutar da shi be sani ba? Har ma yake basu horo da kan shi. Bai gama tunani ba, daya daga cikin su ya kai mishi wani irin sara, cikin rashin sa'a kuwa ya same shi a dantsen hannun shi. Cikin kwarewa da jajircewa ya murde hannun shi wuqar ta fadi qasa ya dauke ta ya yanka wuyan shi. Fada ne sosai ya kaure tsakanin Lawwali da matasan nan, sai dai ko minti biyar ba a cika ba Lawwali ya gama da mutum hudu, ya raunata na qarshen, wuyan matashin na hannun Lawwali, ya ke tambayar shi, wanda ya aiko su, cikin kakari da azaba ya ce, "No 5 ne Oga, shi ya ce in mun ka yi nasarar kashe ka, zai maishe mu mu zam na kusa da shi, gwamna ya yi muna alqawarin manyan kudi" Ya na gama jin bayanin da yake so ya ji ya murde wuyan shi, makaman da suka zo da shi, ya diba, ya nufi sansanin nasu, hannun shi na zubar da jini. Sultana na nan tsaye a bakin dajin, ta kai ta dawo, ta kai ta dawo, su Barirah na tsaye a gefen ta, suma cikin damuwa, Ta na jin motsin tafiya ta nufi wajen da gudu, ganin Lawwali cikin jini ne ya sanya ta sanya kuka mai cin rai, ko kallon inda take be ba, No 5 na ganin Lawwali ya dawo ya diba da gudu zai bar wajen, wuqa daya Lawwali ya zaro ya saita bayan No 5 ya wurga masa, qara ya saki, tare da gantsare wa. Lawwali ne ya isa gaban shi ya zare wuqar da qarfi, sannan ya shaqe wuyan shi, filin da suke taruwa Lawwali ya ja shi a qasa ya kai shi wajen ya wurgar. Nan da nan ya bada umarnin kowa da kowa ya taru a wajen, cikin abinda bai kai minti hudu ba kowa ya hallara, mamaki da tsoro duk ya cika su, hasken fitilar su na solar na haske ko ina na wajen. Sultana na gefen su Barirah a tsorace, Ita dai wannan rayuwa ta zubda jini ta fara sanya ta jiri. "A cikin ku akwai wanda ke jin haushi na? Akwai wanda ya yi saura da ke so shi ga baya na? A cikin ku akwai wanda ya ke ganin zai hada kai da gwaunan da ya cutar da rayuwar mu dika, sannan ya yi sanadin zaman mu 'yan ta'adda, kuma ya cutar da rayuwar mu duka, akwai wanda zai taimaka masa wajen kawar dani saboda na gano gaskiya? ina so kowa a cikin mu ya samu 'yancin shi, kuma mu bar zama bayin su mu ci gashin kammu, ku na ganin akwai me so ya kauda ni saboda wannan manufar tawa? Wane ne ya yi saura? Kar na bincika daga baya na samu wanda ya yi saura," Shiru wajen ya dauka, damqo No 5 ya yi, ya shaqe shi da kyau, sai da ya ga idon shi ya fara alamun dauke baqi sannan ya sake shi, cikin wani irin wahalallen nunfashi yake tari, da kyar ya daidaita numfashin shi, "Fada wa mutane me ya faru, da ka ganni ka ke so ka gudu" Shiru ya yi kamar ba zai magana ba, Lawwali na daga hannu zai make shi ya fara bayani. "Oga ka yi hakuri, sharrin shaidan ne wallah, tun ranar auren ku mun ka haɗa da gwamna zan kashe ka, na gaje ka, ya yi min alqawarin manyan kudi, ya kuma yi min alqawarin in na kashe ka zai aura min diyar shi, ya......" Jinin Lawwali ne ya tafarfaso, da jin kalmar wani zai auri sultana ba shi ba, No 5 bai gama magana ba, Lawwali ya sa wuqar hannun shi ya yanke wuyan shi, jini ne ya yi tsartuwa, sultana kuwa ta zube a wajen a sume, bayan ta kwalla wata iriyar razananniyar qara. Lawwali ne ya wurgar da wuqar a wajen, ya bada umarni a binne shi, a je can inda sauran yaran suka mutu a binne su. Durqusawa ya yi a gaban Sultana ya dauke ta da hannu daya, ya nufi dakin su da ita. A saman gado ya ajiye ta, ya debi ruwa ya watsa mata, zubewa ya yi a qasa, idanun shi na lumshe wa, saboda jinin da ke zuba a jikin shi. Ko da ta farfado ta ga baya motsi, sai hankalin ta ya tashi, taimako ta nema a wajen, nan da nan masu kula da lafiyar mutanen wajen suka zo aka duba shi, aka yi ma wajen ɗinki ,sannan suka masa allurar da zata kashe masa zafi, sai magunguna na kashe zafi da aka bawa Sultana suka fita, suka barta ta na kallon ikon Allah. Nan kuma Allah ya kawo ta, ba komai da sanin shi, zata yi hakuri da qaddarar ta, fatan ta Allah ya bata ikon cin jarabawar nan. Ta na nan zaune ta tuna da bata yi isha'i ba, a hanzarce ta fita, ta yi alwala, ta koma dakin, ta hau sallah. Ta na idar da isha'i ta yi shafa'i da wutiri, sannan ta dora da nafilfilun da bata san adadin su ba, ta na sallah ta na kuka, tare da roqon sauqi akan lamurran da ke faruwa a kowacce sujjada. Fatan ta Allah ya shirya mata mijin ta, ya kawo qarshen wanan zubar da jinin da ya dauka kamar ba komai ba. Sai da ta ji idon ta ya mata nauyi ta kasa bude shi sannan ta hakura ta dena sallah, ta kwanta a gefen Lawwalin da ke qasa,kwantar da kan ta tayi a qirjin shi ta yi lufff kamar yaron da ke jin sanyi. Hawayen ta na diga cikin baccin da ya dauke ta mai nauyin gaske. Lawwali ne ya bude ido a hankali, jin kamar an danne shi ne ya sanya shi kallon saman qirjin shi, ganin ta ya yi ta haye jikin shi ta yi lufff,hawaye na sauka daga idon ta, duk da cewa bacci take. Cikin tsananin tausaya mata ya rintse idanun shi da suka kada suka yi jawur. Ba zai kyale Gwamna Halliru ya qara rayuwar farin ciki ba, in ma ya bar shi ya yi rayuwar farin ciki bai haifu ba cikin asararrun iyaye kamar Dan Talo da Lamishi ba, wanda ke haifawa duniya annoba, kuma su ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali . Zai hukunta duk wanda ya yi sanadin lalacewar shi, har iyayen nashi, ba zai barsu ba, ya san maganin su, ba dai kudin shi suke so ba? Kuma da shi suke taqama da fadi a gari ba? Zai ga wanda zai dinga basu kudin. Ya na nan ya na ta tunani, har bacci ya fara kama shi,sannu a hankali ya miqe, tare da Sultana a hannun shi mai lafiya. Dora ta ya yi saman gado, sannan ya hau, ya rufe su, suka yi baccin su. Da safe kuwa ya dauki wayar No 5 ya kira gwamna, ta na shiga gwamna ya kece da wata mahaukaciyar dariya, tare da fadin. "Yaro bai san wuta ba sai ya taka, aza shikai yadda muka sa shi ya zama wani a fagen ta'addanci, ba zamu iya creating wani ba, to gashi yanzu ka ga bayan shi, alqawari na ya...." "Dad'i na da kai qaramar kwalwa wallah(qaramar kwakwalwa), shin mi yasa ka ke abu kamar wanda be je makaranta ba! Baka tunanin ko na kashe shi wayar shi na hannu na? Tunani ka ke ya kashe ni ya kira ya fadi maka ko? To ka tafka babban kuskure" Lawwali na fadin haka ya kashe waya, bangaren gwamna Halliru kuwa hankalin shi in ya yi million ya tashi, wani irin tsoro da tashin hankali da damuwar makomar shi ne suka bi suka dabaibaye shi. Ba shiri ya fara kiraye kirayen waya, akan ya na neman qarin masu tsaron lafiyar shi, da ta iyalin shi. Hajiya Ikee da ke tsaye ta na so ta ji qarshen Lawwali kuka ta sanya, "Se na dana fada maka kar a yi haka, yaron nan ba mutunci ne da shi ba, ni kad'ai na san yanda na ji sanda ya shaqe ni, baka taba shiga hannun sa bane, shi ya sa, yanzu Allah kad'ai ya san mi ze wa Sultana da ke hannun shi, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, mun shiga uku mun lalace" Kukan ta ne ya jawo hankalin Sultan da ke karyawa ya shiga parlourn, kalaman da ya ji na Hajiya sun juyar masa da kai, waye zai cutar da Sultana? "Waye zai cutar da sultana? Ku fada min me ke faruwa ne, kwana biyu babu natsuwa a tattare da ku, kun damu da rashin su Sultana, mata da mijin ta a dinga bin diddigin su bai dace ba" "Dan uban ka Lawwali tsohon dan ta'adda ne ba mutunin kirki ba ne, ya dauke ta ta na can inda ya ke ya na gana mata azaba" "Ban gane ba? Kun sake sanya ni duhu" "Kai ba kalar daqiqai ba balle na ce ko takkwalanci(daqiqanci) ke damun ka, shin wane yare ne baka fahimta ba? Lawwali dai dan ta'adda na, ya ha'ince mu, ya auri qaunar ka, ya gudu da ita" Qaryar da ta yi ta sa gwamna Halliru yin ajiyar zuciya mai qarfi, dan kuwa ta ce ce shi, a yanda ran shi ke tafasa dinnan, abu biyu za ai, ko ya bada amsa daidai, ko ya hasala ya wa Sultan abinda zai zo ya na dana sani da kan shi. Sultan ne ya kalli Daddyn su cikin damuwa ya ce, "Daddy u have to call the police and let them know about this, a gaggauta daukan mataki" Cikin wata kakkausar murya gwamna ya ce, "Kar wanda ya kuskura ya yi involving hukuma a maganar ga har sai na bada izini" "But daddy what if suka cutar da Sultana? I can't let anything happen to her,ba zan yahe wa kai na ba in wani abu mummuna ya same ta" Yanda Sultan yake ji a zuciyar shi, da zai samu ko kukan ne ya yi, kamar yanda Hajiyan su ke yi, da ya ji dadi. Duk yanda yake tunanin shawo kan Gwamna a hada abun da hukuma ya gagara,qarya kan qarya suka dinga shimfida wa Sultan, daga qarshe suka bashi shawara ya je ya yi ta addu'a har Allah ya dawo da qanwar shi gida lafiya. Sultan na fita Gwamna ya yi waya, Hajiya Ikee na jin me yake fad'a a wayar ta rikice, ta rude da kuka. "Me ya kai ka nemo Mubaraka? Ga iyayen shi a gari? Ka rufa muna asiri akan wanda Allah ya lulluba muna, kar ka tone shi,ka sa a kama iyayen shi, ka bar batun yarinyar nan yar ido, yanda yaka son yarinyar nan, ko kan shi ba ya so haka" "Wanne iyayen nashi za a kama? Yo Allah na tuba ko halbe su zan yi zai damu ne a ka fada Maki? Ke bari ki ji, ba na duba, kuma ba na ganin zuciyar kowa, amma wallah ba wanda yaron nan ya tsana a yanzu duk duniyar ga wanda ya wuce iyaye shi da ni, dan haka bar batun su ma, in na gano qaunar shi na kame ta, zai sako Sultana lahiya".......... *Hummmm wai haka???* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 49: Gidan talabijin na NTA da ke garin Zamfara ke haska wata gagarumar gobara da wasu ke zargin Bomb aka sanya a wani babban wajen ajiya  na kayyaki kala kala,mallakin gwamnati,kayan sun had'a da, kekunan d'inki, kekunan guragu, shinkafa, man gyada, wake, katifu, da dai abubuwa masu tarin yawa, gwamnati ta danqare su ta ajiye su, saboda zagayowar zabe, sai a yi ta raba wa mabuqata ana neman quri'un su, mutane kuma da yake a matse suke da lalure  laluren duniya, in aka basu sai su karba su na murna, su na ganin an musu wani babban alkhairi ne, ba tare da sun yi tunanin cutar da su ake yi ba a hakan. Wuta sai ci take an kasa kashe ta, mutane kuwa a hakan suka dinga qoqarin diban kayayyakin abinci, su na guduwa, labari ya kai har gidan Gwamnati, Gwamna Halliru kuwa ba qaramin tashin hankali ya shiga ba, domin wannan ce babbar ma'ajiyar shi,gashi an qona ta, kuma mutane sun samu damar kwasar abinci, da duk wani abu da ya adana domin zabe mai zuwa, gashi mutane sun gano manufar shi ta qanqame kayan more rayuwa a lokacin da ya dace a ce gwamnati na taimakon su, ta saka musu da wahalar da suka sha na zaben ta, ana jiran sai sanda suka matsu da neman abinci a basu. Har haushin yanda ake ta masa waya ana sanar da shi abun  jimamin yake, a fusace ya fita daga office din nashi ya na kiran wayar wanda ya bawa aikin bincika masa inda su Mubaraka suke. An sanar da gwamna Halliru Murtala Gusau, garin da Mubaraka take,amma me ya sa har yanzu ba a gano inda take ba? Duk da cewar Ya sani Kano tinjimin bajimin gari ne, nemo  Mubaraka zai wahala, amma ba zai gaji ba, ba zai huta ba, har sai an same ta. Bai samu layin wanda yake nema ba, dan haka cikin fushi ya bar gidan gwamnatin gaba daya,ya fada motar shi, ya na ta waya tare da bada umarnin kula da ma'aikatu da duk inda ya kamata a bawa tsaro,masu tsaron lafiyar shi, tuni suka tada motoci, sai gida. Lawwali bai fito ba sai da ya shirya, kafin sati ya sake zagayowa ya yi wa manyan ma'aikatun gwamnati, da ma'ajiya kala kala,da kadarorin gwamna Halliru barna, kusan wasu abubuwan da gwamnan ya mallaka,ba wanda ya san da su, Lawwali ne kawai ya san ya mallaki wasu kadarorin, tunda shi yake aika,ya sama masa su, ta qarfi da yaji,Lawwali ba qaramin birkitawa gwamnati da hukumar tsaro ta jiha da ta Nigeria gaba daya lissafi ya yi ba, gwamna Halliru ya koma kamar mahaukaci, a yanzu yanda yake ji, bai qi ba kowa ya san me ke faruwa a tsakanin shi da Lawwali da yaran shi ba, amma tsoron shi daya, kar ya aika da jami'an tsaro a buɗe musu wuta kuma Sultana na cikin su, ya zai yi ne. Sati Uku currr ana abu daya ba d'aga qafa, Sultana ta yi iya bakin kokarin ta dan ganin ta taushi zuciyar Lawwali amma abun ya faskara, daga shi har yaran shi a tunzire suke, ta barauniyar hanya ake shigo musu da makamai daga wasu qasashen,gwamna Halliru ya yi danasanin  damqa masu manyan makamai, domin kuwa ya tabbatar da su ake tarwatsa masu gari, sun bata masa suna a duniyar siyasa, dan ya tabbatar da cewa yanzu mutane na ganin baqin mulkin shi,da su na da yanda za su yi da sun tsige shi. Ba gwamna Halliru Murtala kadai ba, hatta da Hajiya Ikeeleema bata da ikon shiga manyan taron matan gwamnoni lafiya, ba tare da an yi maganar tabarbarewar mulkin garin nasu na Zamfara ba. Mummunan labarin neman da gwamna Halliru ke yi wa Mubaraka ya iske kunnen Oga Lawwali, cikin tsananin damuwa da tashin hankali Lawwali ya kira No 4, tare da bashi umarni, duk yanda zai yi, ya yi, ya kawo masa qanwar shi wajen shi cikin qoshin lafiya. No 4 ya shiga damuwa matuqa, dan kuwa labarin tashin hankali da rashin zaman lafiya da ake ta samu a yankin Zamfara ba boyayye bane, ga shi ba ya so ko da kwarzane ne ya samu Mubraka, dan kuwa a yanzu ya gama tabbatar wa da zuciyar shi ya na tsananin qaunar Mubarakan, tsoron cin amanar Oga ne ya hana shi bayyana mata, da tinanin halin da Fateema za ta shiga in ta ji ya na so ya auri Mubaraka, Taheer No 4 na cikin matsala, ya rasa yanda zai ya cika umarnin oga ba tare da Mubaraka ta samu matsala ba, dan kuwa ya san duk wata hanya da gwamna zai bi dan ganin ya gano su zai bi ta. ************************* Zaune ya ke ya na jefa soyayyan naman rago a bakin shi, ya na korawa da lemo kwali, in ya cinye ya gutsiri meat pie, Hajiyan Hansatu kuwa na ta zuba godiya da yaba wa surukin nata. "Dan Allah Hajiya ki dena min godiya haka, ai ke uwa ta ce, musamman ma da ban da kowa ke nake gani na ji dad'i a raina" "Ai dole na maka godiya Isah, irin wanga kayayyaki kamar dan ni ka tahi Makka, lallai na tafka babban kuskure a baya, da na qi ka, Allah ya bawa d'iya ta mijin maraniya, Allah ya jiqan Alhaji, da ya ga zab'i nai yau," Murmushi kawai Isah ke zubawa, cikin sunkuyar da kai ya ce, "Hajiya ai ni ke da godiya, ba abinda zan ce da Hansatu sai Allah ya mata albarka, Allah kuma ya haɗa ta da dukkan alkhairi duniya da lahira" Farin cikin da Hajiya ta shiga ba mai faduwa bane,kowacce uwa zata so jin wadannan kalaman a bakin surukin ta, to gashi ita Allah ya jiyar da ita, tun da sauran rayuwar ta. "Ban ga Yaya ba, ko dai ba shi nan na?" "Eh shi na office, ai sai yamma zai dawo, wan mata tai yak-kirai tun sahe akwai abinda suke yi" "Allah Sarki, Allah ya bada sa'a, Allah ya jiqan Alhaji, har na tuna sanda muke tafiya, tun sahe sai dare, ba ya bari na da yunwa, komi yaci shi zai ban, haka zai wuni aiki, rayuwa kenan" Hira ce sosai ta shaquwa da sabo ke gudana tsakanin Isah da surukar shi, tun sanda ya bar gida nan ya nufa, ya ke ta Suratu, hankalin shi gaba daya ya tattara ya koma gida wajen Hansatu, amma ya fi so sai ta huce ya koma, dan ya san ba ta iya fushi da shi, kamar daga sama ya ji  maganar Hajiya ta ce, "Ai shawarar da kabban ita na bi, ana nan ana binciken mutanen da sun ka yi kidnapping di na, kuma da alama ana nan ana samun nasara, dan har jami'an tsaro sun Kama yaro guda da an ka had'a baki da shi an ka swace ni" Wani irin tari Isah yake sakamakon kwarewa da ya yi da lemon da ya daga glass cup ya na korawa, sannu Hajiya ta dinga zuba masa, miqewa ya yi, cikin yaqe, ya ce, "Allah dai shi tona ma koma waye asiri, bari na tai na ga ta na ta yi min flashing, wataqila suna bidar wani abu" Murmushi Hajiya ta yi, ta ce ya jira ta kawo masa saqo ya kai mata, ji ya yi kamar ya gudu kan ta dawo, kuka ne kawai Isah be ba, saboda jimawar da Hajiya ta yi. Kwalin madarar ruwa ta kai masa da galan din zuma, ta ce ya kai ma Hanstu, godiya ya dinga yi, ya na sauri ya bar gidan, mai gadi na gaida shi ko kula shi be ba, da da ne kuwa sai ya tsaya ya masa kurin shi surukin gidan ne. Ya na fita titi sosai ya lalubi No Laminu, bai dauka ba, ji ya yi kamar ya fashe da kuka dan takaici, in asirin shi ya tonu ai ya kade. Bari ma, saudiyar nan zai koma zaman Nija be kama shi ba........ *Yayah Isah namu na mudunci😂* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 50: A cikin daren Isah ya je gidan Laminu, Asshibi na ta mitar an hana su sakewa da mijin ta, ya fita tun safe, sai daren ya dawo, hakuri Laminu ya bata ya sanya rigar shi ya bude gate ya fita, Isah ya gani tsaye cikin tsananin damuwa, da tashin hankali, murmushi ya yi, ya ce wa Isah, "Na san me ya kawo ka, kwantar da hankalin ka, magana ta qare dazu da rana, na aika wani yaro da maganin kusa (bera) an sa mishi ga abincin da an ka kai, ya ci ya mutu, sai in ga me bada shaida" Wata iriyar ajiyar zuciya Isah ya sauke, tare da sakin kwalin madarar a qasa, ya rungume Laminu, ya na murna, "Kai sake ni menene haka, sai an gan mu a ce 'yan iska muke, kai jaye" Tura Isah baya Laminu ya yi, ya na waige waige, cikin jin dad'i Isah ke bawa Laminu labarin yanda ya san an kama yaron nasu, Laminu ya ce, "To rudewar da kayi na yasa bata idasa baka labari ba, da ta baka, da ka gane cewar an kashe shi , ko kuma ba a sanar da ita ya mace ba" "Kaiii Laminu amma kai shege ne" "Ahafff hauka nike da zan bari asiri na shi tonu? Kai fa ba dan garin nan bane ba, ka na iya guduwa ko baka da iyaye a Kano ,ni kuwa uwaye na da uwayen matata nan suke" Hira suka dan taba Laminu ya ce shi zai shiga matar shi na can na jiran shi, Isah ma murmushin da bai taba kalar shi ba a rayuwar shi ya yi, tare da cewa, "Ni ma tun dazu take min waya, bari na je gida" Sallama suka yi, kowa ya kama hanyar shi. Ko da Isah ya isa gidan, ya tarar da shi kamar kullum, a share, a tsaftace, abincin shi na wajen da aka saba aje masa, har da sabuwar tabarma. Komai da yake buqata ya same shi har da qari ma, amma fa Hansatu ce kawai bai gani ba kamar yanda ta saba, ko qarfe nawa ze kai a waje, ta na nan ta na jiran shi. Ko daya leqa dakin da kyau kwance ya gan ta, sanye da wata iriyar rigar bacci mai daukan hankali, sake leqa wa ya yi shin Hansatu ce ko wace ce? Kafff rayuwar su bata taɓa sanya rigar bacci ba, tunda ya aure ta ba ko lefe, balle ya ce ya saka a ciki. Baccin ta take cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, Isah kuwa hankalin shi in ya fi cikin unguwar ya tashi. Cike da damuwa ya zauna bakin gadon, ya kai hannu zai tashe ta, da sauri ya janye, dan bai san da me zata farka ba, rashin sanin meye a zuciyar ta na sa Isah damuwa, da dakatar da shi akan abinda ya so aikatawa. Ya kai qarfe goma da minti sha daya ya na ta kai komo, tsakanin daki da parlour, motsin shi ya yi yawa, har ya hana ta bacci, da wata iriyar miqa ta tashi, wadda ta sanya Isah kai mata runguma, turashi baya ta yi, sannan ta ce, "Meye haka? Bacci fa ni kai, duk ka ishen da motsi, mi ka ke bid'a wanda ban aje maka ba? Ko kuwa kwanan da nikai ka ke baqin ciki na yi duk da wuni da na yi aiki?" Zama Isah ya yi a bakin gadon, ya na kama wandon shi, jijiyoyin kan shi har sun bayyana rud'u rud'u, "Dan Allah Hansatu ki taimaka min, ni ba ni buqatar komi sai ke, na qoshi da abincin ma ni, ki taimaka min" Tashi ta yi, ta na wata iriyar tafiya da ni kaina sai da na yi mamakin shin anya Hansatun Isah ce? Ko kuwa Hafsatun Hajiya ce? Hijabin ta ta zira ta fita waje, fitsari ta yi, ta wanke bakin ta, dan ta yi bacci ta ji ya sauya mata, sai da ta wanke fuskar ta sannan ta koma d'akin, Isah ta gani cikin mawuyacin halin da ba zata iya kauda kai ba, ko ba dan shi ba, dan tsoron fushin da Allah da Mala'iku za su yi da ita, ta sani duk matar da mijin ta ya neme ta a shimfida komai fushin da take da shi, haramun ne matar nan ta qaurace wa mijin, in ta qaurace masa direct, ta ce ba zata ba, ko ta dinga yin wasu abubuwa indirectly har ya gaji da jiran ta ya yi bacci, to fa ta na cikin tsinuwar Allah da mala'ikun shi, har gari ya waye. "Ni da kai akwai banbanci, domin kuwa na san Allah, na san dokokin da ya gindaya akan aure, kuma ina qoqarin kare kai na da take su, sai dai in da rashin sani, amma ka san wani abu, daga yanzu ba zan sake kwanciya da kai ba ba tare daka yi wanka ba, ba tare da ka wanke bakin ka da kyau ba, ba zan kwanta da kai ba ni ina cutuwa kai ka na mora ta ba wallah, an wuce wannan lokacin, in ka na buqata ta, ka tai zuwa wanka,in ka dawo ka wanke bakin ka, ban cuce ka ba na daina bari ka na cuta min wallah" Komawa ta yi, ta yi wata iriyar kwanciya mai daukan hankali,a sukwane Isah ya bar dakin, ya shiga wanka, ya jima ya na dirzawa da cud'a jikin shi, sai da ya tabbata ya fita fess sannan ya dauraye jikin shi ya fita, abun ya bashi mamaki, da ya ga brush da toothpaste a ajiye a saman buta a qofar bayin, bai tsaya dogon bincike ba ya dauka ya wanke bakin shi tass, sannan ya koma dakin. "Shin wai da ka taho ba alwala, ka yi sallar Isha'i halan?" "Hansatu ba na jin sallah ta tana amsuwa innayi ta haka nan, dan Allah ki taimaka min" "Watakam za ka iya yin wanka da brush dan biyan buqatar ka, amma ba zaka iya yin Sallah ba, dan cika umarnin Allah, lallai baka tashi kwana ba wallah" Juyi ta sake, cike da kwarewa, sai da na dauki Style din juyin (lols) ta koma ta kwantar da kan ta a pillow, hankalin ta kwance. Isah kuwa kuka ne kawai bai yi ba dan takaici, Gashi yanzu yanda ya ke hango rashin jin tsoron shi a idanun Hansatu, ba ya jin ko fada ya tsaya yi da ita zai samu riba. Sallah ya je ya yi, a gurguje, ya koma dakin, gani ya yi ta kashe wutar dakin, a cikin duhun ya qarasa gadon...... Hansatu ta bawa Isah mamaki matuqa, ta shayar da shi zumar da ya dinga tunanin anya duk duniya akwai wadda ta fi Hanstun shi kuwa? Maqale ta ya yi gam da jikin shi, kamar ya na tsoron wani zai janye ta. Ita kuwa kwace jikin ta tayi, ta tafi ta yi wanka, ta yi nafila raka'a biyu, tare da addu'ar Allah ya qara kawo mata zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan ta, sannan ta haye gado ta kwanta, kusa da Isah da ke ta sheqa munshari. Da safe kuwa haka Isah ya debo kayan da ya samo a Makka wanda Larabawa suke bayarwa, sadaka, ya dinga bawa Hansatu ya na zuba mata qarya, ya na kurin shi ya siyo mata da kudin shi. Ita kuwa fuskar ta ba walwala, ba fara'a take furta "Na gode, Allah shi biya" Isah dai ya qi shiru, sai zuba yake, qarshe da ta ga ba zai daina cika mata kunne ba, daki ta koma, ita da Ameenatu, suka bar shi da su Bilkisu a wajen. Sai da ya ga Ahmad na qoqarin balle stone din wata riga, ya tattare duk haushin Hansatu da yake ji na qin kula shi da ta yi, ya gaurawa yaron mari, ai kuwa ya gigice, ya dinga zindima ihu, murmushin mugunta Isah ya yi, dan ya san zata je bada hakuri, ya qara bankawa yaro mari, Ameenatu na ta yi wa Hansatu magana akan ta je ta bawa Baban nasu hakuri, ta yi Murmushi ta ci gaba da gyara dakin ta abun ta. Isan da yaga ba wanda ya kula shi sai ya hau masifa da zage zage, nan ma ba wanda ya ce masa ci kan ka. Haka ya qaraci masifar shi ya bar gidan, tare da tabbatar mata da a sati na sama zai koma Makka,tunda abin nata iskanci ne. Shirun da ta masa ne ya qara tunzura shi ya bar gidan gaba daya. ************************** Ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda labarin da ya samu, Gwamna Halliru ya raba hotunan Mubaraka, ma jami'an tsaro dake tare motoci a hanya su bincika, ko da za a ga Mubaraka akai masa ita direct wajen shi, babban abun takaicin shi ne Dan Talo da kan shi ya bada hoton diyar tashi, ba tare da ya san me ke faruwa ba. Sultana ce ta kwantar da kan ta a bayan shi, ta rasa da me zata kwantar masa da hankali, gaba daya naman jikin shi rawa yake, hankalin shi a tashe yake, damuwar shi what if aka kama su Mubarakan shi fa? Ina zai saka ran shi, ya zai ya cika mata alqawarin da ya daukar Mata na bata kariya? Daga shi har ita ba su da kowa mai qaunar su domin Allah sai junan su, in wani abu ya same ta ba zai taba yafewa kan shi ba. Zama ya yi a qasa dabar, ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi, Sultana ma kukan take, duk ta bi ta rame, saboda rashin kwanciyar hankali. Kallon ta ya yi, ya rungume ta sannan ya ce, "Ki yahe min Sultana, ban zama miji nagari a gare ki ba, ban san ya zan da raina ba in wani abu ya same ta, kin dai san ta na shiga hannun mahaifin ki kashe ta zai ko? " Ta na qoqarin kwatanta yanda yake ji a ran shi, amma bata san ya zata bayyana masa hakan ba, ba tare da ta yi tunanin komai ba, ta kai bakin ta nashi,wannan shi ne karo na farko da suka jima su na sumbatar junan su, kuma shi ne karo na farko da sumbatar ta zarce, har sultana ta cire duk wani tsoro, da tsaro, da kuma dokar da ta shimfida a tsakanin su, na sai ya fara sallah zata yarda ya Kusance ta, tunawa ta yi a ran ta cewar, ita addu'ar saduwa tsakanin ma'aurata, ba dole sai namiji ne kawai zai yi ta ba, mace da namiji duk ana so su yi, in daya be yi ba, saboda wani dalili, misali mantuwa, ko rashin iyawa, wanda ya iya zai iya yi shi. A yammar Lawwali ya yi nasarar karbar haqqin auren shi a wajen matar shi ta sunnah kuma diyar fitaccen maqiyan shi,Lawwali bai taba hango cewar rayuwar aure dama haka take da wani sinadari, da dandano ba, sai a yau, wanda da ya san haka abun yake, da bai kai wannan tsahon lokacin ba, ba tare daya karbi haqqin shi a wajen Sulty Baby ba. Lawwali ne ya taimaka mata ya maida ta saman gadon su, duk qasan carpet din ya ɓaci, cikin tausaya wa ya ce, "Sannu Sultana, yanzu ya za mu yi? Na ga kin ji ciwo,ni ban san ya zan yi ba" Duk da ciwon da take ji a jikin ta, bai hana ta, murmusa wa ba, tare da godewa Allah, da bai yi ta mazinaciya ba, hannun shi ta kama ta sumbata, shi kuma cikin damuwa ya kalle ta ya ce, "Ki sanar da ni, mi zan yi yanzu? Ban san me zan ba, na ga har yanzu jini na zuba a jikin ki" Cikin dasasshiyar murya ta ce, "Ina so ka yarda da Allah,ka yarda Allah ne kawai zai iya bawa Mubaraka kariya ba kai ba, ka yarda cewar mubaraka ta na cikin kariyar ubangiji, ba wanda ya isa cuta mata sai idan Allah ya so,ina so daga yau ka min kyakkyawar kyautar da zata faranta raina,kyautar da har na koma ga mahalicci na ba zan daina jin dad'in ta ba" Kafin ta sauke numfashi Lawwali ya ce, "Na miki alqawarin baki duk abinda na mallaka, na kuma amince Allah shi ne kaɗai wanda zai kare min Barakana a duk inda take" Murmushi ta yi, gefen idanun ta kuwa hawaye ne ke zuba da gudu, "Ina so ka koma bautawa Allah, kamar kowanne musulmi cikakke, kuma nagartacce, wannan ita ce kyautar da nake so, a matsayi na na matar da ta kawo mutuncin ta gidan miji" Lawwali bai san sanda ya rungume ta ba ya na kuka, tare da fadin "Allah na tuba, Allah ka yahe min, ban san wanne aikin alkhairi na aikata ba ga rayuwa ta, da ka bani mace kamar wagga, Allah ka yahe min, Allah ka tausaya min ka yahe min ba dan hali na ba, Allah na san ka na so na da rahama ne ya sa ka azurta ni da mace kamar Sultana, Allah ka bani ikon sauya halaye na ka yi min afuwa" Daga shi har ita kuka suke, da kyar suka lallashi kan su, suka yi shiru, "Ka ce wa Barirah ta kawo ruwan zahi, kai kuma ka je ka yi wankan tsarki, ka shirya ka je gidan mu, ka taho da Sultan,ba tare da kowa ya sani ba, ka ce zaka kawo shi waje na mu gaisa, in ka yi haka, Daddy ya ji labari daga baya, ba zai sake ya cutawa Mubaraka ba har ta iso nan lahiya, ko ka na da wata shawara da ta hi wagga sauqi?" Lawwali sake fashewa ya yi da kuka, ya rungume Sultana, yau zuciyar shi ta koma danya shataff a gaban matar tashi,su na haka, ta koya masa yanda ake wankan, ya tafi ya yi, ya kuma bada umarnin a kula da ita, ya bar dajin. Kamar yanda suka tsara kuwa haka aka yi, tun Sultan na ganin nisan waje,har ya fara tambayar shin ina za su ne? Lawwali kuwa budar bakin shi sai cewa ya "Za mu tai ne ka ga inda Daddyn ku ya bamu dan mu zauna ni da mata ta" Mamaki ne fal ran Sultan,yanzu duk gidajen da suke da shi a cikin gari a rasa inda Sulty Baby na ta zauna sai kauye?????...... *Hummmm Sultan kenan, U never see anything* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAEH PAGE 51: Mutanen da ya gani sanye da qananan kaya da bindigogi, sun tsoratar da shi matuqa,nan take ya tuno da kalaman iyayen shi akan Lawwalin, amma ya rasa dalilin da ya sa ya kasa gasgata maganar su a qasan ran shi, har yanzu ya na ganin Lawwali a matsayin mutumin kirkin da ya ke gani a baya. Su na isa sansanin Lawwali ya bude mota ya fita, ya na jiran Sultan, Sultan cikin daurewar kai ya fito,kwakwalwar shi da kowacce gab'a ta jikin shi na so a masa qarin bayanin abinda idanun shi ke gani. "Kar ka samu damuwa ran ka shi dade Sultan, mu je za ka san duk wani abu da ka ka buqata, Sultana na ciki na jiran mu" "Wai dan Allah da gaske anan Sultana ke rayuwa? Ko dai wasa ka ke min, me ya had'a ku da irin wadannan mutanen?" Gaisuwar da Sultan ya ga ana miqawa Lawwali ne ya sake sanya shi cikin rudani, sun kusan isa dakin su sultana, sultanan ta fito cikin wata iriyar kwalliya, mai ban sha'awa, ta yafa mayafin ta kalar shaddar da ke jikin ta, ta saka flat shoe, sai qamshi take zubawa, Lawwali na dora ido akan ta, ya ji duk wata soyayyar ta da yake ta qoqarin dannewa, da wadda bai ma san ya fara yi mata ba, ta taso ta lullube shi, wani qayatacce, kuma sassanyan murmushi yake zuba mata, Itan ma haka, sai dai kunyar shi ta fi yawa a tattare da ita a yanzu, bata iya hada kwayar idon ta da na shi, Sultan tsaye yake ya na kallon ikon Allah, cikin gyaran murya, da gyara tsayuwar shi ya ce, "Baby Sulty ta dena so na yanzu," Da sauri ta kauda kan ta daga kallon qasan ido da take wa Lawwali, ta fara takawa, cikin tsananin kulawa dan kar su gane sauyawar tafiyar ta, ta isa gare shi, rungume ta ya yi, ita ma ta sa hannayen ta biyu ta rungume shi, sai da suka gama farin cikin ganin junan su, sannan Lawwali ya saqale hannun shi daya a qugun ta,  sannan suka shiga ciki. Lawwali ya yi mamakin yanda aka gyara wajen, sai kamshi ke tashi, ga abinci nan an kawo, da abun sha. Aikin Barirah ne wannan. Zama suka yi gaba dayan su, tare da yiwa Sultan Bismillah, kame hannayen shi ya yi, a qirjin shi, sannan ya ce, "Ni fa ba zan iya sanya ko da ruwa ba ne a ciki na, ba tare da na san mi ya kawo ku dajin ga ba, shin sace ku an ka yi ko mi na na?" "Mun yi maka kama da wanda anka sace?Kai dai aka sato, domin kuwa a yanzu haka in ba mun samu abinda muke so ba a wajen mahaifin ku, ba zaka koma cikin gari ba" Wata dariyar rainin hankali Sultan ya yi, ya kalli Lawwali ya ce, "Habaa habaa suruki na, ai ni nafi qarfin a sace ni, in ka ga an sace ni to qaddara ta ce ta zo da haka, ni da ka gane ni ban wasa da azkar, ban wasa da addu'ar hita da shiga gida, ka ko ga me sace ni sai ya shirya" Sultana ce ta yi dariya ta ce wa Lawwali, "Kira Daddy" "Ban gane shi kira Daddy ba, me ke faruwa ne? Ku na ta sa wa kai na na daure wa," "Yah Sultan in har ka bamu goyon baya akan abinda muke shirin yi, na maka alqawarin sanar da kai komai game da iyayen mu, wanda nake boyewa ba na so ka sani, dan kar ka shiga damuwa" Kallon su kawai yake, ya ma kasa magana, kenan ta tabbata sato shi aka je har qofar gidan su aka yi, kuma ya zo ba tare daya san sato shin akai ba. "Excellency sir, ka na lahiya?.....yi hankuriii ba fada ne yasa na Kire ka ba, wasu kadarorin ka ne a waje na, wanda duk duniyar ga baka da kamar su, ina mai tabbatar maka da cewar in baka dakatar da neman qauna ta ba, ta iso gare ni lahiya, zan manta da wai an tai central mosque an daura min aure da diyar ka, zan sa bakin bindiga na halbe ta, d'anka da na tai na dakko dazu...." Cikin wata iriyar tsawa Gwamna Halliru ya miqe tsaye daga saman dining table din da ya ke cin abincin dare shi kadai, ya ce, "Lawwali kar ka kuskura, kar ka sake ka taba min yara na,....... kai wa Allah Lawwali ka dawo min da yara na lahiya, zan janye binciken da ake akan qaunar ka" "Nooo ka ci gaba da yi min fadan mana, me ya sa  ka dena? Ga Sultana na so ta yi magana da kai" Wayar Lawwali ya miqa wa Sultana, tare da daga mata yatsan shi babba, cikin maqale murya da kukan qarya ta fara magana, "Daddy ka zo ka cece mu, mutumin nan mugu na..." Lawwali ne ya amshe wayar, ya kunna a handsfree ,Gwamna sai magiya yake, kamar zai kuka, "Sultana are you ok? Ina d'an uwan ki shi ke? Lawwali kai wa Allah ka sake min yara na, zan janye duk wani neman qaunar ka da nake, kai zan manta ma da kai da rayuwar ka, zan kyale ka ka yi duk abinda ka ga dama, amma na roqe ka kar ka yi wa yara na komi" "Amma dai ka san qa'idar aikin mu ko? Kai ne fa ka ce in mun amshi kuddi, in diyan 'yan siyasa ne,ko 'yan siyasan da kan su, mu kashe, kar mu bari da rai, yanzu kuma ka ke son sauya muna doka?" "Lawwali na janye wannan dokar, ga sabuwar doka nan, Lawwali kai wa Allah ka sake min diya na lahiya, ina Sultan? Sultan..." Sultan na zaune ya na saurara kuma ya na ganin abun kamar wasan yara, ah ah mafarki ne, bai ma san me ya dauki abun ba, gashi nan dai ne kawai. "...Sultan ka yi min magana,Lawwali kaji tsoron Allah kar ka cutar min da  yara na,ba su da haqqin kowa, kar ka cutar min da yara na, ka sanar da ni ko nawa ka ke so, zan baka, ka sake su" "Ashe ka san Allah?Ka dai san na san kuddin ka kuddin sata ne ko? kuddin tsafi ne, to ni a yanzu mi zan da kuddin ka? Baicin na gama samun iya abinda nake buqata a wannan harkar, kawai yaran ka nika son kashewa, dan na rama lalata min rayuwa da ka yi, ai na fada maka, sai na dau fansar abinda ka yi wa qauna ta,da iya ni ka taba,da na kyale ka, tunda ni ma ina da laifi nawa na kai na,ni na kawo kaina gare ku dan neman taimako, ku ciyar da baki da tumbin da ke tsananin jin yunwa da qishirwa,amma me kuka yi? Sai ku ka jefa rayuwa ta cikin halaka da lalacewa, amma duk da na san mugayen halayen ku,na ci gaba da zama da ku, tunda in na yi abinda ku ke so ku na bani abinda zan ci har da iyaye na ma, da ace ni kad'ai ka tab'a a yanzu, wataqila da na hakura, amma qauna ta? Ka yi na farko, yanzu ka na so ka yi na biyu? Inaaa, ba zan iya hakuri ba sam sam" Gwamna Halliru bai san ya na kuka ba tun farkon fara wayar, sai da kukan ya ci qarfin shi ya kufce masa da qarfi, tura kujerar da yake kai ya yi, ya durqusa da guiwar shi a qasa, ya na roqon Lawwali, da ya kyale masa yaran shi, kar ya cutar da su. Lawwali ne ya bawa Sultan wayar, shi kuwa ya rasa me zai ce, kalma ɗaya ce ta fito daga bakin shi, wato, "Daddy" Haba mana Gwamna na jin Muryar Sultan da gaske sai ya sake rikicewa, domin sai ya ji Muryar Sultan kamar a wahale, bai san tsantsar mamaki ke damun Sultan din ba, ya nufi sama, a gigice, Hajiya Ikee na ta kyale kyale,duk da halin jimamin da ake ciki bai hana ta kwalliya ba. Yanayin da ta ga mijin nata ne ya sa ta sakin kwalbar turare a qasa, ta nufe shi zata kai masa cacuma ya bangaje ta, ya dauki  sauran wayoyin shi zai fita, maganar da ta ji ya na yi ne ya sanya ta fahimtar inda aka dosa, cikin tsananin damuwa kuwa ta bi shi ta na kira, ko juyawa bai ba, sai da ya kai waje, cikin fada ya juya ya ce, "Ke dayalla can ki koma gida ki zauna gani nan zuwa yanzun ga" Wayar shi ya kalla dan yin magana ya ga an kashe kiran, bin kiran Lawwali ya dinga yi amma ba a dauka ba, tashin hankalin da ya shiga ba abun kwatanta wa bane, balle misali, da kyar ya ke ganin inda yake sanya qafar shi, kiran waya ya dinga yi, ya na dakatar da neman Mubaraka ta kowanne bangare. Video'n yanda Lawwali ke ganawa wanda suka kama azaba ne ke gilmawa a idon gwamna, Muryar Sultan da Sultana sun cika masa kunne ,hango su yake a yanayi na azabtuwa da uqubar Lawwali. Kafin ya kai jikin motar shi,jiri ya kwashe shi, ya fadi a qasa,drivern shi da securities ne suka daga shi aka sanya shi a mota, asibiti aka nufa da shi direct dan kuwa ba ya motsi. Hajiya Ikee kuwa kuka take ta na qarawa, tare da tsinewa Lawwali albarka. ********* A can daji kuwa Lawwali da Sultana sun bawa Sultan labarin duk abinda yake a boye a gare shi, na shekara da shekaru, har da wanda basu sani ba ma, sai da Lawwali ya basu. Duk dauriya da qarfin zuciya irin na Sultan sai da ya yi kuka, da wahala ya yi kuka akan abu, sai dai a ga jijiyoyin kan shi na tashi, a ga idanun shi sun yi ja jawur, amma banda kuka. Zuciyar shi ta gama karyewa, yanzu ace duk mahaifin shi ke aikata wadannan mugayen laifukan saboda son duniya da abinda ke cikin ta? Saboda siyasa da son mulki? To me ya tanadar wa kan shi a lahira? Me ya ke aikatawa na gari wanda Allah zai yafe masa wadannan mugayen laifukan? Shin mahaifin su musulmi ne kuwa? Ya na tantamar imanin shi da Allah, wanda ya ce Allah shi ne Ubangijin shi, Annabi Muhammad shi ne annabin shi, qur'ani da Hadith ne littafan da ya yadda su zama madubin shi, ba zai aikata shirka ga Allah ba, ba zai aikata abubuwan da gwamna Halliru Murtala Gusau ya aikata ba. Miqewa ya yi ya fice daga wajen, bai san ina yake tafiya ba, kawai sai ganin shi ya yi, a wajen mutanen da aka kamo,a cikin hasken solar da aka sa a wajen yake hango wasu har da jariran yara a hannun su, wasu da ciki, wasu kuma gasu nan a wahale saboda hana shan kwaya da giya da Lawwali ya yi. Hawaye ne kawai ke zuba a idanun Sultan da sultana dake take masa baya, Lawwali kuwa na tsaye ya na hango su, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, to meye amfanin wannan rayuwar mara mamora? Shi nashi iyayen su na can hankalin su kwance, basu damu da shi ba, basu damu da halin da yake ciki ba shi da qanwar shi, anya kuwa da ake cewa ba wanda zai haifi d'a a cikin shi ya qi shi gaskiya ne? Domin shi gashi ya gani da idanun shi, shi shaida ne,iyayen su basu damu da su ba, jiya ya amsa kiran 'Dan Talo ya na washe baki, wai gwamna ya ce ya bada hoton mubaraka sati Uku da suka gabata, wai gwamna ya mata miji, kuma sun ji shiru, ko zai bincika a ji me ke faruwa, a qarshe ya fara masa qorafin basu da abinci su da bisashen shi (awakin shi) gashi su Lamishi sun dena zuwa aiki,tunda yanzu su gwamna surukan su ne, be kamata su na zuwa aiki gidan ba. Sai da Lawwali ya gama jin surutan Dan Talo ya fada masa jimla daya wato "Ku saida bisashen ku ci abinci" sannan ya  kashe wayar shi. Jikin wani kututturen itace Sultana da Sultan suka zauna, hannun su na cikin na junan su, sultana ce ta kwantar da kan ta a kafadar Sultan, ta share hawayen ta da ke zuba, ta ce, "Yah Sultan ka ga rayuwar da iyayen mu suke aikatawa, a tunanin su dan jin dad'in mu suke yi, su na quntata rayuwar wasu bayin Allahn, su na haskaka ta mu," Sultan ya kasa magana har a wannan lokacin, wani abu yake ji ya tokare masa maqoshi ya qi wucewa. Hannu ta sanya ta na ta shafa bayan shi, a hankali ya ke sauke ajiyar zuciya, cikin wata iriyar Murya mai rauni ya ce, "Iyayen mu sun halaka, sun biye wa son zuciya, da son duniya sun halaka, ya Allah mai shiryar wa ka shiryar da su, ka yahe musu zunuban su,...sultana yanzu ina Daddy zai kai haqqin rayukan da ya salwantar?" Wani irin kuka ne mai maqaqi da zafi a wuya ya turniqe Sultan, tausayin shi ya gama kashe zuciyar Sultana, wannan halin da zai shiga take tsoro tun farko, saboda ta san he is very sensitive kamar ta, har ma ya fi ta. Su na nan zaune, Lawwali ya je wajen nasu cikin murna, ya sanar da Sultana mahaifin su ya janye neman Mubaraka da ake yi, amma fa ya na kwance a asibiti ba lafiya. Hankulan su ya tashi, da jin mahaifin su ba lafiya, shi kuwa ya na sanar da su, ya tafi ya na neman layin No 4, yanayin network din wajen akwai matsala, dan haka da kyar ya same shi, ya na dauka ya ce, "Gobe da subahi ku taho, hanya lahiya lau ne yanzu" "To Oga Allah shi kai mu" "Ameen, lahiya kuwa Taheer? Akwai damuwa ne?" Da sauri No 4 ya daidaita Muryar shi ya ce, "Lahiya qalou Oga, kwana na hwara shi ya sa ka ji murya ta haka nan" "Tau yayi, ka sanar da Barakana gobe mu na tare, ba na so na kira ta yanzu na san ta yi kwana" "To Oga zan isar da saqon ka, kahin mu taso ma ai na san za ka kire ta ko?" "Kwarrai da gaske, sai goben" "Tauu Allah shi kai mu" "Ameen" Cikin murna ya fada dakin nasu,  Sultana da Sultan ya gani har sun riga shi isa dakin, su na jayayya akan zuwa ganin mahaifin su, Sultana na bawa Sultan hakuri, akan ya bari ba yanzu ba, shi kuwa ya dage sai ya tafi. Lawwali ne cikin nuna halin ko in kula, dan ba wai ya ji wani abu bane dan gwamnan na asibiti, budar bakin shi ya ce da Sultan "Ka ga Suruki na Sultan, na san kai mai addu'a ne da ibada, amma wagga qaddara kai ma ta kamma, ba ka tahiya ko ina, har sai mahaifin ka ya warke ya biya mana bukatun mu, domin ba rayuwar shi ce kad'ai adda mahimmanci ba, mu ma mutane ne" Lawwali na gama fadin haka ya fita,Sallah ce a zuciyar shi, amma bai san ta yanda zai fara zuwa ya yi alwala ya gabatar da Sallah ba, gani yake kamar in ya yi ba zata karbu ba, kuma ma dai maganar gaskiya, ya na ganin kamar ya manta wasu abubuwan, shekarun da ya dena sallah da yawa, Gashi yanzu Sultan ya zo, ya na neman kawo masa wata maganar komawa gida, ba zai taba barin shi komawa ba, sai ya cika alqawarin dawo da mubaraka wajen shi lafiya. Dakin marigayi No 5 ya sa aka gyarawa Sultan, ya je ya lallaba shi, akan lallabawar da ya tarar Sultana na masa, ya raka shi har dakin, suka yi sai da safe ya koma nasu dakin. Alwala ya je ya yi, ya zauna, ya kasa tashi ya tada sallar,Sultana kuwa ta fada duniyar tunanin halin da mahaifin su ke ciki, dan haka bata kula da halin da mijin ta ke ciki ba. "Uhummm na ce, kin yi sallah ne?" Da sauri ta zare hannun ta daga tagumin da ta yi,ta kalle shi, dan ta na so ta tabbatar da shin Lawwali ne ya ke tambayar ta tayi sallah ko ah ah, ganin ya kafe ta da ido ya na neman qarin bayani ne ya sa  ta ce, "Eh na yi magariba kahin Ku zo, amma ban yi Isha'i ba" "Ok to ki tai ki yi mana, mu kwanta, kwana nika ji" Tashi ta yi, ta tafi ta yi alwala, duk tunani da damuwa sun addabe ta. Tada sallah tayi, Lawwali kuwa ya maida hankali ya na kallon me take, da yanda take bin qa'idojin yin Sallah, duk ya na haddace wa a kan shi. Sai da ta idar ta yi sallama sannan ta kula da kallon da yake mata. Murmushi ta yi, dan kuwa an ci gaba, in zata shekara Sallah dan ya kalla ma abun ya bashi sha'awa ya yi, ba zai kalla ba, qarshe ma bar mata dakin yake, yau kuwa Gashi sai binta yake da kallo. "Ka na buqatar wani abu daga waje na ne" Sunkuyar da kan shi ya yi, cikin jin nauyin ta, ya ce, "Ki koyar da ni yanda  aka yin sallah" Gyara zaman ta tayi sannan ta ce, "Ba a jin kunyar tambaya a addini, duk girman mutum duk qanqantar shi, duk sanin shi duk rashin sanin shi, a kullum shi mai neman sani ne, dan haka kar ka ji kunya, ni ma har yanzu akwai abubuwan da ban iya ba, ina neman sani akan su" Nan dai Sultana ta koya masa abubuwan da ya mance. Ya kuwa yi sallah,ranar Sultana sai da ta yi kukan farin ciki, saboda yanda Lawwali ya jima a sujjada ya na kuka ya na qasqantar da kan shi gaban ubangiji, sai neman gafarar Allah yake ya na kumawa. Tausayin shi ya gama ratsa duk wata kafa ta jikin ta, ya jima ya na sallar da bai san adadin ta ba, sai da ya ji qafafun shi sun kasa tsayuwa sannan ya sallame, da gudu Sultana ta fada jikin shi, suka rungume juna su na kuka. Cikin kukan ya ce, "Ki na ganin Allah zai gafarta min kuwa? Abubuwan da na yi a rayuwa su na da yawa Sultana, rayukan mutane da na dauka da hannun ga nawa su na da yawa, ba zan iya qayyade miki su ba, Sultana wasu lokuta in mun ka kashe gari guda hukuma na qiyasta mutane ne fa kawai su ce an kashe mutum kaza, amma adadin ya hi haka nan, ki na ganin Allah zai yafe wa mai laifi da yawa, kuma manya kama ta?" Shafa fuskar shi ta yi, ta na share masa hawayen shi, ta kai labban ta da suka bushe saboda kuka, ta manna a nashi, ba tare da ya mayar mata da martani ba, ba tare da Itan ma ta na jiran martanin shi ba, ta daga ta kalle shi tace, "Allah subhanahu wata'ala ya ce, kar mu yanke tsammani  daga rahamar shi, shi mai rahama ne, Allah subhanahu Wata'ala ya ce, da bawa zai je masa da zunubin da ya kai kumfar teku, ya tuba, tuba mai kyau, to zai gafarta masa dukkan zunubin shi, bawan da Allah baya gafarta wa yake sawa a wuta shi ne, bawa mai shirka, har ya mutu ya na shirka, kuma bai dena ba, to wannan bawan zai dawwama a wutar Allah ne, ba ranar fita, dan haka ina kyautata wa Allah zato, zai karbi tuban ka, da izinin Allah" Tunda suka zo Hajiya Ikee bata taɓa kiran Lawwali ba sai yau, ringing din wayar ne ya cika dakin, Lawwali ya kalli Sultana, Sultana ta kalle shi....... *A daga ko kar a dagaaaa????😂* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 52: Sultana ce ta miqa hannu za ta dauka, Lawwali ya yi saurin janye wa,ya kafe ta da wani mugun kallo, idanun ta ne suka ciko da kwalla, saboda ta na so ta ji a wanne hali mahaifin su yake,ganin idanun ta na qoqarin zubar da ruwa ne ya sanya Lawwali sassauta kallon da yake mata, bin kiran ya yi ba dan ya so ba, sai dan ba ya son duk abinda zai sanya ta zubar hawaye, a handsfree ya sanya wayar, kamar jira Hajiya Ikee take a kira, ta yi sauri ta dauka. "Hello,...Hello,...Lawwali ka na ji na kuwa? Ka wa Allah, ka wa iyayen ka ka maido min da yaran mu," Fashewa ta yi da wani irin kuka, mai ban tausayi,sultana ma kukan take, ba abinda ke tsakanin su da iyayen su illa matsananciyar soyayya da kulawa, duk wani abu da zai sanya su farin ciki su na musu shi, duk wannan halin da suke ciki, dan ganin sun faranta musu ne,sai dai kashhh ba su bi hanya madaidaiciya ba, wannan shi ne babban kuskuren su a rayuwa. "Ka na ji na kuwa? Don Allah ba dan halin mu ba ka sake mana yaran mu,His Excellency na cikin mawuyacin hali, tunda an ka kawo shi bai san wanda ke kan shi ba, bai san wanda ke gehen shi ba, ko motsi ba shi yi, ka taimaka ka maiso mana da su, ko Allah zai sa shi bude ido" "Hajiya ki na bata bakin ki,domin ke baki san kala da kalan dokoki da yasa ba,kuma ni ban tab'a tsallake umarnin shi ba, shin su iyayen da munka d'auke Wa yara mun san halin da suke a yanzu? Ko kin san cewa akwai wad'anda sun shekara uku zuwa hudu nan wajen? Akwai wad'anda suke anan wajen tun farkon fara aikin da shi mijin ki yasa mu yi, su to ya iyayen su suke ji? Ke San ciwon ka nemi naka ka rasa? Baka san inda shike ba? Ba za ki sani ba, ni zan baki labari, lokacin da mijin ki yaci amana ta, ya dauken qauna ta, lokacin nan ba irin tashin hankali da u'qubar da ban shiga ba, ashe ta na nan kusa da ni, ban sani ba, ku gode Allah kun san inda suke, kar ki qara kira na," Sultana ce ta matsa jikin shi za ta amshi wayar, ya wurga mata wani kallo mai dauke da warning, sannan ya wurga wayar saman gado ita kuma ya dauke ta cak ya dora a saman cinyoyin shi, ya manna bakin shi a nata, ranar Lawwali ya bawa kan shi mamaki, ashe ya iya irin wannan soyayyar bai sani ba. Sultana kuwa tun ta na kukan hana ta magana da mahaifiyar ta da ya yi, har sai da ta manta kowa da komai, jin ta kawai take a duniyar da Lawwali ya kai ta, mai cike da ni'ima da nishad'i, mai cike da gamsar wa, duk wata nutsuwar da ke tattare da ita ta kwace, ba abinda take gani a idanun ta, sai Auwal din ta, ta na tsaka da amsar saqon salon soyayyar shi mai wuyar fassara ta ji ya na qoqarin cimma burin shi, da sauri ta bude ido, dan kuwa bata gama warkewa ba, kyabe baki ta yi, irin na shagwabar nan, Lawwali ya kalle ta da rinannun idanun shi, da alamar tambaya, sauke idanun ta tayi, ta kalli qasa, ta na wasa da qirjin shi ta ce, "Da zafi fa, ban warke ba" Da sauri ya d'aga ta, ya na nuna nadamar abinda yake son aikatawa, ganin hakan da ya yi, sai ya bawa Sultana dariya, hancin shi ta ɗan ja kad'an tare da kai wa lips din shi kiss sau daya ta ce, "You are so cute," Murmushi ya yi sannan ya ce, "Sannu Sultana, ki yafe min, ban San zaki ji ciwo ba, ko za mu tai gari ki ga likita?" Kwantar da kan ta tayi a qirjin shi, a ran ta ta na ayyana, da ta san inda aka kwantar da mahaifin ta da sun je asibitin ko daga nesa ne ta hango shi, hawaye ne taji su na zuba a idanun ta, da sauri ta sa hannu za ta goge, lawwali ya riga ta, cikin murya mai sanyi ya ke magana, "Sultyna ki dena kukan ga, ya na karyar min da zuciya, na ji kamar na faasa abinda na ke da niyya, ke dai san quduri na da yasa na ke abinda nake a yanzu, ki bani goyon baya komi zai wuce,in shaa Allahu" "Allah ya yarda, ina son ka miji na" Wani irin dad'i ne ya lullube Lawwali, kalmar da ba wanda ya taba furta masa bayan qanwar shi sai Kuma ita, amma a bakin Mubaraka kad'ai ya fara jin wannan kalma, se ga shi ya samu  matar dake yawan furta masa, yi ya yi kamar bai ji ba ya ɗan had'e gira ya ce, "Na'am mi ki ka ce??" Murmushi tayi dan ta gane me yake nufi, so yake ta maimaita masa, tashi tayi ta haye jikin shi, ta kwantar da shi a saman gadon sosai, ta yanda suke fuskantar junan su, sai da ta sumbace shi sosai sannan ta kalli kwayar idon shi ta ce, "Cewa nayi....ina son hancin ka, da idon ka, da nan wajen..(ta nuna lips din shi) ina son kowacce gaba da ke jikin ka...ina son ka, ko da ace ni makauniya ce, kuma kurma ce, sannan bebiya ce, zan qirqiri kowacce hanya ce dan sanar da kai ni Sultana ina son ka Auwal, ba zan taba dena son ka a raina ba, har sai sanda na dena numfashi a duniya, ina maka son da ban taba yi wa wani ba, kai ne na farko a cikin zuciya ta, kuma kai ne na qarshe" Wani irin numfashi mai sauti Lawwali ke saukewa ya rasa kalar dad'in da Sultana ke sanya shi ji a wanan lokaci, rungume ta ya yi sosai a jikin shi, har sai da ta saki wata siririyar qara, sannan ya sake ta ya na murmushi. "Yi hankuri Sultyna, ji nikai kamar na bude fata da tsokar jiki na, na balle qashin da ya yi wa zuciya ta rumfa na ajiye ki a can ciki ki zauna daram, saboda yanda nake jin...." Shiru ya yi bai furta ba, a hankali ta daga kan ta, cikin wani kallo mai kashe jiki, ta na lasar leben ta na qasa ta ce, "Me ka ke ji?" "Ina jin son ki Sultana, ina jin qaunar ki sultana, ba na son rabuwa da ke har bayan mutuwa ta, amma na san zai wahala mu had'u, saboda kowa makomar shi d...." Ba tare data shirya ba ta ji saukar wasu hawaye Masu zafi, a kuncin ta, dan kuwa ta fuskanci me yake so ya fada, "Subhanallahi, haba haba Auwal, ka dena kalar wannan tunanin, rahamar Allah mai yalwa ce, Allah ba so ya ke ya sanya bayin shi a wuta ba, Allah so yake bayin shi masu zunubi su tuba domin ya yafe musu, ya lullube su da rahamar shi komai laifin su, wanda ma ya yi shirka ga Allah in ya tuba kan ya mutu Allah na yafe masa ballantana kai, da baka taba duqawa gaban boka ko malam ba, sannan baka sani ba, ni din da ka ke wa kallon zan shiga aljannah wataqila Allah ya sanya ka a aljannah din mu zauna tare saboda ni din, sannan Allah zai iya jarabta ta da wani abun, ni kuma na yi wasa da shi na aikata zunubin da zai kai ni wuta, hadisi ne fa guda, akwai mutanen da za su yi ta aikata ayyuka irin na 'yan aljannah, saura kad' an su shiga aljannar, amma se su aikata aiki irin na 'yan wuta, se Allah ya sanya su a wutar, sannan akwai mutanen da za su yi ta aiki irin na' yan wuta, sauran kad'an su shiga wutar se kawai su yi aiki irin na 'yan aljannah, sai Allah ya kare su ya sanya su a aljannah, ka gani? Allah ba ta inda baya wanzar da rahama da ikon shi" "Sultana ban taba shirka ba, amma ina taimaka wa masu yi, duk abinda mahaifin ki ya buqata da sauran 'Yan siyasa a baya ko mene shi ina samar musu shi, duk da na san tsafi za a yi da abun" Hawayen ta ne suka qaru, jin cewar har da mahaifin ta a aikata shirka, "Ka yi istigfar Allah zai amsa, ka yi da kyayyawar niya, Allah zai yafe maka" "Allah na tuba ka yahe min, Allah ka yahe min manya da qananan zunubbai na, Allah ka yi min rahama, ka cika min buri na," "Ameen," Kafin bacci ya ɗebe su, sun tattauna akan abubuwa da dama, sun kuma tsara duk wani abu da ya kamata su aikata a gaba, a haka bacci ya dauke su suna manne da junan su. *************************** Kamar yanda Isah ya yi alqawari, ya siyi goro mai yawan gaske, dan tafiya Makka, wanan karon dubu hamsin casss ya cake wa Hansatu, amma bata ci su a banza ba, sai da ya mori jikin ta da kyau da kyau, dan duk girman ta, da jarumtar ta, sai da ta dinga shiga ruwan zafi, Ita dai ta sawa ran ta, ba zai sake ganin wani rawar kan son shi awajen ta ba, tunda ta yi a baya bai mata amfani ba, sannan ba zai sake ganin murmushin ta ba, tunda a baya sai da ta ce wa audiga bata iya murmushi ba,ta fita iyawa, duk bata samu ribar murmushin ba,hakan kuwa na matuqar damun Isah, kula da cewar ko sau nawa zai neme ta ba zata qi ba,shi ya sa ya ke fanshe haushin rashin sakewar a jikin ta. Hajiyar Hansatu da Yaya Musa sun yi qoqari sosai wajen ba Isah wasu kudin da zai qara akan jarin shi, sai da ya musu sallama sannan aka bada mota kamar wancan karon aka kai shi airport, wannan karon ko kwalla Hansatu bata yi ba, balle ta koka, Isah kuwa ya ji haushi matuqa, sannan ta ce ba zata yi rakiya ba, a fusace ya fad'a mota, aka tafi kai shi,ko da takoma sai ta ce wa Hajiya ita bata so ta ga ya tafi ya barta, kuka za tai, kuma bata so ta daga masa hankali,dan haka Hajiya bata ce komai ba, sai suka ci gaba da hirar su. Isah sun isa airport, ya sauke kayan shi da komai, cikin dabarar da suke yi kar a gane goro ne, ya na tsaye wani mutum fari ya tsaya gefen shi, sallama ya masa shi ma ya amsa, sai ya ji maganar kamar ta Inyamuri ko bayerabe, Mutumin ya fara yi wa Isah magana da turanci, Isah ba turanci, fuska ta muzanta da kunya, sai bawan Allahn ya gane Isah fa wala ingilishi, cikin gurbatacciyar Hausar shi ya ke tambayar Isah, Makka zai je ko Madina in sun isa Saudiya? "Makka zani" "Masha Allah, ni ma can nake da zama, ina da gida da iyali a can, kai fa ina ka ke zama?" "Ni a hotel kawai nake sauka, banda gidan zama," "Allah Sarki, ka fad'a min inda ka ke sauka in na samu natsuwa zan neme ka, se ka dawo gida na da zama, tunda duk qasar mu d'aya, in a foreign land in ka ga d'an qasar ku ji ka ke kamar d'an uwanka ne" Sunan hotel din da yake sauka ya sanar da bawan Allahn nan ya na ta murna, a qalla ba shi ba biyan kudin hotel, zama suka yi tare, suna ta hira, kamar abokan juna, duk inda CCTV camera yake a wajen bawan Allahn nan ya sani, kuma daidai gwargwado juya bayan shi yake, ba ya bari fuskar shi ta hasku, ya yi shiga irin ta larabawa ya saka face mask, se surutu yake wa Isah da gurbatacciyar hausar shi, Isah kuwa banda washe baki ba abinda yake. Sai da aka shiga jirgi ne suka rabu, saboda wajen zaman su ba daya bane. Tafiya ta miqa zuwa Saudiya, Isah ba abinda ya ke banda tunanin Hansatu, wannan karon ji yake kamar ya bar wani bangare na jikin shi, qudirtawa ya yi in Allah ya sauke shi lafiya, ita zai fara kira su gaisa. ********************** A hanyar su ta zuwa garin na Zamfara duk wani motsi na Mubaraka na kan idon Taheer, zuciyar shi kuwa na ta kakkaryewa zuwa qananan pieces ,ya yi zurfi akan son ta ba tare da ya sani ba, wataqila dalilin gano ya na son nata, rabuwar da ta zo musu ba tare da shiri bane, da ya kula ya na son ta tun da, da ya yad'a manufar shi a wajen ta, gashi yanzu lokaci ya qure masa. Mubaraka ce ta yi qarfin halin yi masa magana, ta ce, "Yah Taheer akwai damuwa ne?" Da sauri ya sanya murmushin yaqe ya ci gaba da tuqi, bai ce komai ba, tafiya suke kamar ba zai magana ba, can kamar wanda aka shaqe ya ce, "Yanzu in kin tafi shikenan? Mantawa zakiyi da mu ko? Ga yaran ki can kin bar su suna ta kuka, ke kad'ai ka lallashin su in su na rikici, sun hi sabawa da ke,gashi zaki tafi ki bar su" "Yah Taheer ku din wani bangare ne mai girma a rayuwa ta, ba zan taba manta wa da ku ba, ka sani na jima ban ga yayana ba, ina kewar shi sosai, amma in na je na gan su, ai zan koma wajen ku, in Allah ya yarda" Wani irin murmushi Taheer ya sake, har da sosa kai, murmushin shi ya bawa Mubaraka mamaki, sai ita ma ta fara murmushin, cikin daurewar kai, dan ta kasa fahimtar inda Yah Taheer din ya dosa da wannan bayyanannen farin cikin................ *Allah kai ku lahiya ke dai, mu ai mun gane murmishin meye😂😂* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 53: Jefi jefi suke hirar su, cikin nishadi, da kuma sabo, Taheer na matuqar jin dad'i da girmama wannan lokaci da hirar tasu baki daya, domin bai sani ba, ko na qarshe kenan da za su hadu har su yi hira haka, ko kuma akwai rabon haduwar su a gaba. Sun isa garin zamfara da misalin qarfe 12 na rana, saboda gudu sosai da yake zubawa, hamdala Mubaraka ta yi, sannan ta kalli Taheer, ta na qoqarin motsa baki tai magana ta ga wasu sojoji na nuna ta, amma ba su tsaida motar su ba, sunkuyar da kan ta tayi qasa, dan ta san dalilin da ya sa suke nuna ta, da an basu dokar kama ta, yanzu an janye. Sai da suka shiga gari sosai, Taheer na qoqarin daukan hanyar dajin nasu Mubaraka ta cire nauyin baki ta ce, "Yah Taheer Dan Allah tsaya," Bai tsaya jin dalilin tsayawar ba, ya samu gefe ya tsaida motar, Sannan ya tattara duk wata nutsuwar shi ya miqa mata a hannun ta, d'an cizon leben ta tayi na qasa, cikin tsoron me zai je ya zo ta ce, "Dan Allah ka fara kai ni gida wajen su Umma, dan ban sani ba ko Yah Auwal zai  bari na je na gan su, dan Allah kar ka qi, in ka qi kai ni na ga Ummana zan yi maka kuka, kuma Yah Auwal zai ga na yi kuka, kuma..." "Tau ya yi haka nan, ban ce ki bani tsoro ba daga shigowa ta, tau yanzu in munka tai ya ji labari fa? Kin dai san in kin tsira ni ina ruwa ko?" Cikin zumudi da murna ta ce, "Ba abinda zai yi maka, Indai na ce ni ta ni nace ka kai ni, Please Yah Taheer ka kai ni naga su Umma" ta qarasa magana cike da shagwaba. Taheer dai bai so ba, amma an sa shi na dole, tiryan tiryan take nuna hanya, har suka isa, ya na tsaida motar ta fita a guje, ta fad'a gidan,shiru ta ji ba kowa, daga iyayen nasu, har yaran. Cikin sanyin jiki, ta dinga leqa d'akuna,ta fita, gidan da ke manne da nasu ta shiga, suka gaisa,mutane ne na kirki, masu dattako, tambayar su ta yi inda iyayen ta suke, nan suka sanar da ita Kareeman 'Yabbuga ce ta haihu, yau suna, dan haka su na can gidan Kareema. Sallama ta musu da godiya ta koma wajen Taheer jiki ba kuzari, idanun ta sun cika da kwalla. Hakuri ya bata bayan ta masa bayanin komai, ya ce in sun je, ta roqi Auwal, ya san zai kai ta da kan shi. Hanya suka miqa sai daji. A can dajin kuwa Sultana da Lawwali sai zumud'in zuwan mubaraka suke, sun yi kwalliya, sun sha ado gwanin ban sha'awa, kamar masu tarbar wani hamshaqin, su Barira da yaran Lawwali kuwa ,sun matsu su ga wace ce wannan yarinyar da ta shiga ran Ogan su? Ya take? Shin ta kai wadda za a gigice da so ko bata kai ba? Abinci da abun sha, mahallin kwana, da duk abinda za su buqata komai an tanadar musu, su kawai ake jira. Da misalin qarfe hudu da arba'in su Mubaraka ne a cikin jejin Oga Lawwali, tun daga hanya Mubaraka ta tsure, ganin mutane dauke da makamai, kamar masu zuwa yaqi,Taheer ne ya yi ta kwantar mata da hankali. Lawwali ya kasa zama, sultana sai dariya take masa,Sultan da ke tsaye ya na kallon su, shi ma murmushi yake ta zabgawa, Lawwali na hango motar su No 4 ya zabura zai yi wajen, Sultana ta d'an kwalla qara kadan, juyawa ya yi ya kalle ta, ya ga ta dafe cikin ta, da sauri ya duqa gaban ta, ya na mata sannu, a lokaci daya kuma ya na juyawa dan ganin rabin ran nashi. Sultana bata d'aga daga duqawar da ta yi ba sai da ta ga Mubaraka ta fita a motar, cikin washe baki, da murna, Sultana ta kwace hannun ta daga na Lawwali ta kwasa da gudu, ta nufi Mubaraka, suka rungume juna, mamaki da haushi ne suka kama Lawwali, kawai sai ya tsaya ya kama qugu, mutanen wajen kuwa me za su yi banda dariya. Sultan kuwa har ya na duqawa dan dariya, ga dai Lawwali qatoto, maji da qarfi, amma Sultana yar firit ta masa wayo,Mubaraka gani ta yi ba shi da niyyar zuwa wajen ta, sai ta shanye dariyar ta ta daga murya ta ce, "Yah Taheer mu juya kawai, ka kaini wajen su Umma na, tunda Yah Auwal din baya son gani na" Wata harara Lawwali ya zuba mata, sannan ya taka da sauri, Itan ma da sauri ta ke zuwa wajen shi, rungume ta ya yi kamar ba zai rabu da ita ba, Ita kuwa kukan farin ciki ta saka, wani abu ya ji ya tokare masa maqoshin shi, wanda ya ke bayyana tsananin kewar ta da ya yi, ji ya ke dama zai iya kwaranyar da hawaye wataqila da ya ji sauqin abinda yake ji a ran shi,sake qanqame ta ya yi, ya na godewa Allah, da ya dawo masa da ita lafiya. Sun jima a haka, sannan ya dago da kan ta ya juya ga mutanen da ke wajen, fuskar su dauke da kallo na sha'awar soyayyar da ke tsakanin yaya da qanwar shi. "Kunga yanda  qaunata ta dawo gare ni lahiya? Na muku alqawarin zan maida ku ga iyalin ku lahiya, da yardar Allah, ba zan gaji da neman yahiyar ku a gare ni ba, ku yahe min, ko ba yanzu ba, ko bama tare ne, ku yahe min dan Allah" Hayaniya ce ta karade wajen, Sultan na gefe ya na murmushin jin dad'in ganin shaquwa da aminci da ke tsakanin Oga da mutanen shi. Ta gaban shi su Sultana suka wuce, shi ma ya bi bayan su. Kafin su qarasa ciki Mubaraka ta gaida shi, amsawa ya yi, cikin sakin fuska, sannan ya tambaye ta ya hanya, ta bashi amsa da, "Alhamdu lilLAAHi" "To masha Allahu, sannun ku da zuwa" "Yauwa Muna godiya" No 4 da Lawwali sun tsaya daga waje, su na tattaunawa, kafin daga baya suyi sallama, ya tafi tsohon dakin shi, da ya samu baqi a ciki, amma still gadon shi na nan, a ciki, ga abinci nan da abun sha an aje masa. Sai da Mubaraka ta fara wanka, sannan suka hadu dikan su a saman carpet suka ci abinci, su na yi su na hira. Sultana kan ta ta sallama, ta sani ba zata tab'a samun kalar soyayyar da Lawwali ke wa qanwar shi ba, Mubaraka ta yi gaba, ta na bayan ta, ta yarda da hakan, kuma bai dame ta ba, domin dama kowa da matsayin shi . Ranar Lawwali ya sha labarin Kano, har tsokanar ta ya soma yi da cewar, "Ohhh su Barakana daga zuwa Kano a yi watanni, har an koma yin kananci, Sultyna, qaunar nan taki bata ko yadda ba wallah, gani takai yanzu ta zama bakanuwa" Dariya sukai tayi, ita kuma ta na qoqarin kare kan ta, haka suka yi ta shan hira, tare damurnar dawowar ta lafiya. ************************* Jirgi ya d'aga sai Saudiya, Isah kuwa wayar shi ya zaro a aljihun gaban rigar shi, ya na ta kallon hotunan Hansatu, wanda ya mata, ta na bacci, da wanda ya mata ta na aiki, duk bata sani ba, sai murmushi ya ke zubawa, ashe akwai ranar da zai kalle ta da soyayya a ciki? Ni kuwa nace ba soyayya ba ce sha'awa ce, ai da can da take son ka san da baka da komai, kai baka so ta ba, sai yanzu da ka ga ita Allah ya mata komai ka ke son ta. Jirgi ya tsaya a king Fahad international airport, mutane na ta qoqarin sauka, Isah na tafe shima cikin ayari, wayar shi ya mayar a aljihu, ya riqe 'yar qaramar jakar kayan shi,ya sauka. Wannan bawan Allahn ya gani daga nesa da shi, ya na masa murmushi, tare da yi masa sallama. Mayar masa da sallamar shi ya yi, ya nufe shi, dan su je su d'auki kayan su, sai bawan Allahn nan ya nuna wa Isah qaramar jakar shi, ya sanar da shi ita kenan yake da, dan haka anan suka yi sallama, ya tafi, Isah kuwa dole sai da ya je daukan manyan jakunkunan da ya isa da su. Ina can ina kalle kalle Hameeda ta shiga Saudiya (Allah ka amsa ka bama duk wanda be je ba ikon zuwa) sai na ji ihun mutane, larabci na tashi ko ta ina, kafin na koma wajen dan ganin me ke faruwa sai na hango askar sun kewaye Alhaji Isah, Isah ya durqusa qasa ya na rantsuwa tare da baza musu Hausa, ya na bayani ba na shi bane. Ko da na leqa da kyau, sai na ga wani abu fari tasss a leda guda hudu, da na kasa kunne da kyau, sai na ji ana fad'in koken ne abun, hankali na ya tashi nai baya, ina leqe daga nesa, bawan Allah'n nan na hango cikin tsananin damuwa da b'acin rai ya na kiran "Shit, shit, this man na mumu, de don catch am" (Wannan mutumin Wawa ne sun mama shi) Da sauri ya rataya  jakar shi ya bar wajen, a cikin gudu-gudu, sauri-sauri. Tuni an sanqame Isah, ya na ihu ya na kuka, sai fadi yake ya na kumawa. "Goro ne kaɗai nawa na rantse, koken din ban san na waye ba, dan Allah ku maida ni Nigeria ba zan sake safarar goron ba,ni Ko zuwa ma ba zan sake yi ba" Gaba daya fuskar Isah ta sauya, cikin qanqanin lokaci ya zama kamar ba shi ba, saboda shiga tashin hankali. Ba su tsaya da shi ko ina ba sai wajen ajiye masu manyan laifuka. Isah na nan na kuka, da roqon gafara, tare da qoqarin bayyana musu gaskiyar shi, amma ba mai sauraron shi, balarabe d'aya aka kawo wanda ya ke dan jin Hausa, duk wani bayani da Isah yake yi, abu dai na komawa kan shi ne, tunda ya kawo goro ta boyayyiyar hanya to tabbas koken tashi ce, "Innalillahi, yau na shiga uku, na lalace, wai da wane yare kuke so na muku bayani ne, ba tawa bace," Wani baqar fata Isah ya gani, da uniform din 'yan sandar qasar, cikin yaqe Isah ya yafice shi, ya na washe baki, "Yauwaa ga na gida nan, bawan Allah, dan Allah zo kai mana tafinta, ka fada musu goro kawai na kawo, yasin ban san koken din waye ba, ni ma yanda suka gan ta haka na gan ta, dan Allah fassara musu, ni na yarda su karbi goron su zubar, ai dama haka ake yi ko, amma kar su hukunta ni da laifin da ban aikata ba" Sai da Isah ya gama jawabi, ya kalli baqar fatar nan, ya kalli larabawan nan, ya na jiran ya ji baqar fatar na zuba Hausa, sai ya ga baqar fatan na kallon shi ya ce masa, "Ana la afham ma taqool" (ban fahimci me ka ke fada ba) "Bawan Allah me ka ce? Dan girman Allah in ka iya hausa ka yi min mu fahimci juna,yasin ba kaya na bane," Tafiyar shi baqar fatar ya yi, Isah na ta kiran shi ya na fadin, "Malam musulmi fa dan uwan musulmi ne, ka zo ka fassara musu, ba kaya na bane, goro ne kawai nawa" Qarshe dai dole suka sa Isah yin shiru. Isah ba baki sai hawaye, dan kuwa ya riga ya san hukuncin masu shigar da ƙwaya musamman manyan miyagun kwaya irin wannan shi ne kisa. ************************** Hansatu kuwa bayan sun koma gida,hankalin ta kwance ta yi wanka, ta yi wa Ahmad da Bilkisu, Ameenatu ta yi, suka yi alwala, suka shige ciki, sai da suka yi magariba, sannan suka ci abincin da suka je da shi daga gidan Hajiya. Suka yi hirar su har isha'i, ta riga ta san ba zai kira ta ba kamar wancan karon,amma bata san me ya sa ba, ta nace ta saka rai, ta ke jiran kiran shi,kallon wayar ta tayi, ta sauke ajiyar zuciya, daga qarshe dai ta tashi ta kai Ahmad dakin su, sannan ta koma ta tashi su Bilkisu. Rufe ko ina ta yi, ta koma cikin yaran ta ta kwanta, ta yi nisa a bacin ta, ta yi mummunan mafarkin da ya sanya ta tashi a firgice kuma a tsorace............ *Kun dai san mafarkin wasu bayin Allahn na zama gaskiya ko😂🤭🙏🏼* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 54: Addu'a Hansatu ta yi ta ce, "A'uzubi kalimatillahi taamat, min galbihi, wa iqabihi, wa sharri ibadihi, wamin hamazatisshayadin,wa'an yahdhurun" Sai ta juya daga ɓangaren dama da take, ta koma hagu, ta sake cewa, "A'uzu billahi minas-shaidhanir-rajeem," Ta tofa dama da hagu, ta rintse idon ta, bacci fa sam ya gagari idanun Hansatu, dan haka tashi ta yi, ta yi alwala, ta hau yin nafila ba qaqqautawa, ta na neman tsarin Allah akan abinda ta gani cikin mafarkin ta. Sai da ta ji bacci ya mata yawa a ido, sannan ta yi sallama, ta sanya alarm ta qure volume din wayar, dan kar ta makara sallar asuba. ************************** Cikin nasara da taimakon Allah, Lawwali ya fara rage mutanen da suka yi garkuwa da su, su na maida su wajen ahalin su, da kudin fansar da suka karba, ba qaramin tanadi Lawwali yayi ba, dan gabatar da hakan. Mubaraka ta zama mai ban hakuri a duk inda suka je, kusan saboda ita ake kyale su Lawwali, dan kuwa Mubaraka Allah ya hore mata baiwar iya kalamai, masu sanya nutsuwa, Allah ya mata suffar mutanen kirki, ta yanda duk wanda ya kalle ta zai ji ta shiga ran shi, sai dai in mutum ya kai qololuwa a hassada. A cikin sati biyu, kudi sun fara gazawa, sai da Sultan ya bada gudun mawar shi, Lawwali da ya qi karba, a cewar shi, dole a koma wajen Gwamna Halliru ya biya, ai shi suke bawa kudin ya sammu su. Sultana kuwa ta ce, "Daddyn da bai san wa ke kan shi ba, ai ba yanda za ai shi ba da kuddi, a dai yi anhwani da nawa da na Sultan" Barirah da masu yin girki a wajen, sun kafe su dai za su zauna anan, tunda dama can su an qi sakin su ne saboda ba wanda ya biya kudi a dangin su, ba kuma wanda ya damu da neman su. Lawwali ya ce sam ba za a yi haka ba, su zauna a daji, a na cikin haka wasu daga cikin matasan wajen maza suka amince za su aure su, Lawwali ya yi farin ciki da hakan sosai. Dan haka sun yanke shawara za su shiga gari, su nemi wani babban malamin ya daura musu aure. Sultan kuwa ya musu alqawarin wajen zama a cikin gari. Ranar an yi wata yar kwarya kwaryan walima a wajen, saboda murnar yanda komai ke tafiya musu cikin sauqi. Yamma ta yi liss, ana zazzaune a harabar wajen da suka saba zama, Lawwali na tunanin yanda za su yi da makaman nan nasu, shin ma jami'an tsaro za su miqa, wanda tun asali su Gwamna Halliru ke aikowa su kawo musu, ko kuma siyarwa za su yi, ko kuma lahanta su za su yi kar kowa ya amfana da su? Shawara dai suke ta yi, ba su samu matsaya ba, Mubaraka kuwa tunanin da ke cikin zuciyar ta daban, ta na zauna gefen su, shiruuu ta na tunani, Lawwali ne ya bar cikin yaran nashi ya zauna a gefen ta. Murmushin yaqe ta masa, shi kuma ya kalle ta da kulawa, "Barakana me ne ne, ban ganin fara'a ga huskar ki? Ba haka ki ke so ba, na ajiye komai na zama mutunen kirki? Shin ba burin ki ba kenan?" "Alhamdu lilLAAH, babban buri na ya cika, amma ina da wani burin bayan wanga, kai kuma b'acin rai ne a gare ka, ni kuma ba na so na aikata duk wani abu da zai b'ata ran ka," "Barakana me ne ne burin ki? hwada min ko menene, zan cika maki shi, indai bai hi qarhi na ba" Kauda kan ta tayi, ta share kwallar idon ta, nan da nan kuwa hankalin Lawwali ya tashi. "Barakana me ne ne, me kike so?" "Ummana" Sai ta fashe da kuka, sakin qaramar bindigar da ke hannun shi ya yi a qasa, ya kama ta a gefen hannun shi, ya na lallashin ta, kwata kwata bai da plans din komawa gida wajen lalatatun iyayen su, ya san dama ita kadai zata kawo masa cikas, ta sanya su a rai over,shi kuwa ba sa gaban shi, kamar yanda ya tabbata ba su gaban iyayen nasu. "Ki dena kuka, zan maishe ki duk inda ki ke so, amma ba yanzu ba" "Yah Auwal to dan Allah ka kai ni na gan su,tunda na zo na ke tunanin su, yau ji nake kamar ba zan iya ci gaba da numfashi ba in ban gan su ba" Cikin bacin rai ya kalle ta ya ce, "Shin ban hana maki maganar mutuwa ba? Mi sunka tsinana maki a rayuwa banda lalacewa da tagayyara? Sun san inda ki ke? Sun damu da ke ne? Ko kuwa ni me ne ne bana maki da ba zaki tattare soyayyar da ki ke musu ki min ita ba?" Ya na gama fadin haka ya bar wajen rai a bace, mubaraka kuwa kuka ta sanya ta na kiran shi, bai koma ba. Sultana da Taheer da Sultan ne suka hau rarrashin ta, cikin kuka ta ce, "Aunty Sultana ki roqar min shi dan Allah,I want to see my parents ,I love them so much, duk da na san ba sa son mu, lokuta da dama ina mamakin me ya sa to suka haife mu in ba sa son mu? Amma ba zan iya dena son su ba, iyaye na ne, komai lalacewar iyaye dole su na da mahimmanci a wajen d'an su, dan Allah ki fahimtar da Yah Auwal, ba wai ba na son shi bane, ina son shi sama da yanda nake son komai da kowa a rayuwa ta, ban da abu mafi mahimmanci sama da shi, amma ina so na ga iyayen mu, na jima kwarai rabo na da su" Kuka take ta yi, gwanin ban tausayi, su na ta lallashin ta, Lawwali ne ya kutsa tsakiyar su ya rungume ta, ya ce, "Ni ma ina son ki sama da komai da kowa a rayuwa ta Barakana,ki shirya gobe zan kai ki ki gan su,kalar tarbar da za su miki ita zata sa na barki wajen su, ko na dauke ki gaba d'ai" Murna ta fara yi sosai, Sultana na taya ta dariya. Lawwali ne ya kalli Sultana da Sultan ya ce, "Ku ko jibi in mun dawo, ku na iya zuwa ku ga su Hajiya, amma sai kun min alqawarin ku na dawowa" Wani tsalle Sultana ta daka ta d'afe su daga shi har mubarakan, sai da suka fad'i cikin yashin wajen, "Mun maka alqawari mu na dawowa," Dariya mutanen wajen sukai ta yi, lokacin sallah ne ya yi, suka tashi dan gabatar da Sallah . Kowa ka gani fuskar shi dauke da nishadi, banda No 4 dan ya kula da irin kallon da Sultan ke bin Mubaraka da shi,shi kuwa ba ya so. Bayan sallar Isha'i ne kowa na d'akin shi,  sultana na kwance ta fara bacci a jikin Lawwali, ya kwantar da ita a hankali, ya sauka cikin sand'a ya bude wata locker, laptops guda biyu ya dakko, sai wasu qananan qundin ajiya, da disk din CD guda uku, sai Camera da waya d'aya, sanya su ya yi a gaba, ya na kallo, ya na hawaye. Sultana da ta farka tun sanda ya sauka, ta Qura masa idanu, cikin ranta ta na ayyana ba zata bari ya aikata abinda yake da niyya ba, ba zata bari ba sam. Washe gari da safe, Mubaraka tun da ta yi asuba ta kasa komawa bacci, sai murna take, wajen Taheer ta je, ta na ta masa hira, a can ta tarar da Sultan, su na shan dumi, a wutar da suka kunna. Cikin hasken wutar Sultan ke kallon yanda kwayar idon ta ke fitar da wani irin haske, a zuciyar shi ya ke ayyana dama kar gari ya qarasa waje wa, ya tsaya a haka, dan ya dawwama ya na kallon cikin idon ta. Taheer na kula da haka kuwa ya hade fuska ya ce ma Mubaraka. "Ke da kin ka taho nan, ki na surutun banza, da ba zuwa kin kai ki ka shirya kayan ki ba, ki ka sani ko shi bar ki can?" "Kuma fa haka ne Yah Taheer, ina zuwa" Miqewa ta yi cikin azama, da murna kamar qaramar yarinya, Taheer kuwa da sauri ya ce, "Ki zauna can ba sai kin dawo nan ba" Sultan da ya fuskanci inda Taheer ya dosa ne ya saki wata siririyar dariya, ya dauki wani dan qaramin kara ya saka a wuta, ya kafe kallon shi a cikin wutar. Sai da Mubaraka ta bacewa ganin su sannan, Sultan ya ce, "Ka dena bata ran ka aboki na, ita mace irin wannan allura ce cikin ruwa, sai ka ga mai rabo ya dauka, mu yi addu'a mu barwa Allah komi" Taheer ya dan ji kunya da nauyin fadan da ya yi, sai kawai ya miqe ya bar wajen. Tun da sultana ta leqa ta ga ana ta shara, ta ji gaban ta ya fadi, domin abinda take shirin aikatawa zai iya jawo mata mummunan hukunci wajen Lawwali, amma ta riga ta yi niyya, ba zata fasa ba. Sauri ta yi ta koma d'akin, ta taya shi shirya wa, kaya masu kyau ta daukar masa, sannan ta d'aukar wa Mubaraka ma wasu kaya masu kyau daga nata dan ta saka, sun yi kyau sosai, Lawwali gaba d'aya ya sauya, nutsuwa kamala, da hankali sun samu wajen zama a jikin shi. Su na kammalawa suka yi wa sultana sallama ya kama hannun Mubaraka, suka fita, mota suka shiga su na d'agawa juna hannu, Sultana kuwa yaqe take ta yi, tafin hannu da qafar ta sai zufar tashin hankali suke fitar wa. Motar su na barin harabar wajen, sultana ta fad'a dakin su, ta tattaro, laptops wayoyi, da duk wani qundin ajiya, ta yi waje,direct d'aya daga drums din da ake kunna wuta a qona shara ta nufa, ta fara zuba su, d'aya bayan d'aya, ta na zuba disc na qarshe a wuta ta ji qarar motar Lawwali, wani irin tsoro da tashin hankali ne ya shigi sultana, sai da cikin ta ya murda, ta dafe marar ta, ta durqusa a wajen. Ta na nan duqe Lawwali ya nufo ta, cike da tsananin bacin rai, idanun shi sun kad'a sun yi jawur, hannun shi dunqule ya nufe ta, bakin ta ne ya fara rawa, hawaye na zuba, hannun ta dafe da marar ta, ta ke ja da baya, tana kad'a masa kai, leqawa ya yi, ya ga yanda abubuwan da ta sa ke ci da wuta, ga baqin hayaqi ya turnuqe wajen. Cikin tsawa da hargowa ya nufe ta ya daga hannun shi zai kife ta da mari, ya ji an riqe hannun, ido suka had'a da Mubaraka, na zubar da hawaye, cikin tsoro, abinda bata taɓa ji ba game da yayan nata, dan ta san ba zai taba cutar da ita ba, amma yanayin shi a yau ya firgita ta. Hannun shi ya sauke ya fara kaiwa da komawa, ya na shafa kan shi da hannun damar shi, cikin bacin rai ya kalli inda Sultana ke durqushe ta na kuka, Mubaraka na lallashin ta, ta na so ta d'aga ta tsaye. "K..k...kayi hankuri....bb.ba zan iya bari ka aikata...abinda ka ke da niyya ba...ba domin kar mahaifi na ya shiga hannun hukuma ba,...ko kar a hukunta shi...ya cancanci dukkan hukunci...ba zan iya rayuwa ba kai ba...zan mutu a duk sanda na budi ido na ga babu kai....dan Allah kar ka yi abinda ka ke shirin aikatawa....na qona shaidun ne saboda a kowannen su ka na ciki,..." "Yi min shiru ! Kar ki kara magana ! Kin ci amana ta Sultana, ba zan yahe miki ba,ke qona ne saboda ba ki son wancan azzalumin mahaifin na ku ya karbi hukunci a hannun hukuma ko? To ki sani, a yanzu in na je na bada shaida, na kawo jami'an tsaro nan, suka ga komi, hakan ya wadatar, mahaifin ki ba shi da wani qarfi a gwamnati a yanzu, har an dora wani a madadin shi, ba zai iya mulkar jama'a ba, da shayayyar qahwa, sultana me ya sa ki ka ci amana ta, bayan na yarda da ke, wadannan bayin Allah da muka zalunta shekara da shekaru ki na zaton sun yahe muna ne? Kin san yanda muka lalata rayuwar su ne? Har yanzu ina jin zahin lalata qaunata da aka yi, kamar mashi a qahon zuci, su fa? Ki na tunanin sun mance ne? Ko kuma ba su jin zahin abun? Sultana me yasa ki ka aikata haka? Me ya sa?" Naushi ya kaiwa drum din da ke ci da wuta, ya fadi qasa, wutar ta yi taratsatsi, mutanen da suka taru a wajen yanzu duk sun fuskanci me Lawwali yake magana akai, zuciyar su ta karye matuqa da jin kalaman shi, ashe shi ya sa ya maida wasu ga iyayen su, kuma ya ke qoqarin ba wa wasu wanda suka rage a wajen ingantacciyar rayuwa, ashe ya na so ya miqa kan shi da duk mai hannu a kamen su ga hukuma? Lallai zuwan sultana cikin su alkhairi ne,domin ta sa Lawwali ya sauya daga Oga Makashin mutane zuwa Auwal mai tausayi da sanin ya kamata. Mubaraka ce ta jingina Sultana jikin wata bishiya, sannan ta tsaya a gaban Lawwali, cikin zuciyar ta cike da tsoro, amma ta na qoqarin nemo jarumta irin tashi ta sanya a fuskar ta. "Yah Auwal ba laifin Aunty Sultana ba ne, ni ta na bata shawara a qona, saboda na gan su, kuma na yi tunani in wani abu ya same ka wa nake da shi a duniya? Ka riga ka tuba ga Allah, ka kuma dau duk matakin da ya dace dan ganin ka gyara abinda ka bata, kana tunanin su hukumar da za ka kai kan ka wajen su, mutanen kirki ne? Ko ka na tunanin in aka binciko lehin da wasun su ke aikatawa za a bar su a raye ne suma? A yanzu yanda hukuma ta lalace mutane na gari ma da ke cikin ta ba su da qarfi,neman durqusar da su ake kullum, Yah Auwal kai wa Allah ka fahimci Aunty Sultana, ba ta da lehi, ba ta so ta fadi gaskiya ne ka ji haushi na, shi ya sa tai shiru" Hawaye ne kawai ke zuba a idon Sultana,tare da jin qauna da soyayyar mubaraka na ratsa ta, tabbas wannan dalilin na cikin dalilan da ya sa Lawwali ke son ta, ta na da hankali da hangen nesa. Lawwali bai ce komai ba ya bar su a tsaye a wajen,ya tafi dakin shi ya dauki wayar shi da ya manta, ya shiga cikin daji sosai, dan so yake ya yi nesa da su, ya na so ya kad'ita. *Ohhhh Oga akwai son kai, dake Mubaraka ce ya yi shiru, amma da zai kai wa yar mutane duka😏* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 55: Mubaraka da Sultana kuwa d'aki suka koma, bayan Mubaraka ta taimakawa Sultana ta zauna a bakin gado, Sultanan ta kalli Mubaraka ta ce, "Mubaraka me yasa kin ka yi wa yayan ki qarya, bayan a kullum shi na yabon ki akan rashin yin qarya? Me ki ke tunani in ya gano baki da hannu a abinda ni na aikata ba ke ba? Gashi yanzu kin rusa muku tafiyar da ki ka jima da burin ki na son  ya amince ku yi," "Babu komi aunty na,nasan ba zai iya kwana shi na hushi da ni ba, zai sakko ne, ni kuma ba zan iya jure ganin ki cikin halin baqin ciki ba, zai fahimce ki, bashi lokaci ya yi tunani, haka yake, ya na da saurin hushi, amma da ya fahimci gaskiya ya na saurin sauka" "Allah ya sa ya sauka da wuri, ba zan iya jure fushin shi ba, amma me ya sa kuka dawo?" "Waya tai yam-mance, shi na mun ka dawo dauka, ya shiga dakin yaga waccan locker a bude, shi ne na ga hankali nai ya tashi,ya na neman ki" Murmushi Sultana ta yi, ta kalli Mubaraka ta ce, "Na gode" Su na nan zaune kamar marayu ya dawo,  a rayuwar Lawwali ya tsani rashin cika alqawari da cin amana. Ya san ya yi wa Mubaraka alqawarin kai ta gida,ga kuma Sultana ta ci amanar shi, dan haka dole ya dau mataki, "Ki taho mu tai,...ke kuma na janye zuwan ku gida a gobe, har sai na gano gaskiya game da abinda kin ka yi min" Murmushi mai quna ta yi, akwai zafi, wanda ka ke so, ka yarda da shi ya zama shi bai yarda da kai ba. "Babu komi, Allah ya sa ka gane irin son da nake maka, ba zan yi komai dan na cuta maka ba" Kallon cikin idanun ta ya yi, nan da nan na shi suka fara sanyi, da hanzarin shi ya bar dakin,tare da fadin "ki taho mu tai" motar shi ya shige, ya na zaune ya na jiran Mubaraka,  qasan zuciyar shi na ayyano masa fuskar Sultana,mai cike da ban tausayi, da tsantsar soyayyar shi, ba ya so ya yarda da cewar amanar shi ta ke son ci, amma ya kasa dauke hankalin shi daga abinda ta yi din, anya ba da gaske saboda Daddyn su ta qona ba? Mubaraka ma bata b'ata  lokaci ba ta bishi , ta na shiga ya bar wajen da gudu, ta waya ya bada umarnin a shiga wajen Sultana a duba ta, a ga me ya sa ta ciwon ciki. Sun isa gidan Dan Talo da misalin sha daya na rana, har a wannan lokacin mazaje masu zaman banza na zaune, a jikin katangar gidan,a jingine da gini, su na shan hantsi, ana ta zuba qarya,domin abun na su ya wuce hankali . Hango mota mai kyau suka yi ta na tunkarar su, nan da nan kuwa a cikin su aka samu wani maqaryacin ya ce ai ya taba ganin me motar har sun ma gaisa rannan, wasu sun yarda wasu sun qaryata, tunda sun san junan su. Dan Talo dai sai gwale ido ya ke, ya ga mamallakin motar, domin dukkan alamu sun nuna gidan shi motar ke tunkara, nan da nan kuwa ya miqe ya kade rigar shi da ta fara nannadewa saboda yawan zama da ake akai. Mota na qarasa tsayawa a gidan shi ya karkata kai ya na kallon motar har sai da su Mubaraka suka fito, ba qaramin jin dad'in hakan ya yi ba, nan da nan kuwa ya yi gyaran murya, da qaramar dariya ya ce, "Dama k'yale ku ai niyyi, ku qarqare qaryar ku, tun subahin munkayi waya da su suna tahe, Mubaraka ta dawo daga qasar waje, sanda na fadi maku ta tai qasar waje karatu mi kun ka kira ni? Zubairu ko? Tauuu yanzu wa ka qarya ni da ku? Nan nan gaba gare ku, gwauna ya aiko a basuwa hoton yarinyar ga za shi yi mata miji, kun ka qaryata ni, tauu ga dai shi ta dawo ko?" Wani fad'i ya dinga yi, ya na qobarewa, shi a dole mai gaskiya, kuma yaran shi sun dangwalo azziqi. Ya na daga cikin sharadin Lawwali kar Mubaraka ta kula kowa a waje, in ya ce kowa ya na nufin kowa, sai sun shiga gida. Dan Talo na ta washe baki, ya na musu barka da zuwa, Mubaraka ta yi wuf ta fad'a gidan, Lawwali kuwa yanda ya daure fuska kawai ya isar wa da Dan Talo babban saqo, su na shiga ciki suka ji hayaniya kamar za a d'aga gidan, qarasa tsayawa suka yi a qofar shiga gidan, Lawwali ya nade hannun rigar shi, ya zuba hannayen shi a qirjin shi ya na kallon su, 'Yabbuga ta fi kowa zaqalqalewa, Lamishi kuwa ta yi kalar tausayi,yau ko masifar ma ta kasa. "....An fadi d'in barayin banza barayin wofi, talauci ku kad'ai ke fama da shi? Daga zuwa bukin suna sai a nemi atamfa a rasa? To waye ya dauke  ta in ba ku ba? Tunda ku na amince ku zauna qofar mai jego kar dangin mijin ta su shiga suyi sata, to walle biyan ta za ku yi, dan ba bar maku za mu yi ba" " 'Yabbuga ni ta ce fa Lamishi, aminiyar ki, ni ki ka wa d'iban albarkar ga? Akan atamfar da ko dubu biyat bata kai ba? Ke mance har kyautar Suhwa (super) sai da na miki? Ranar bikin yaron nan ba abinda baki sata kin kai gidan ki kin boye ba, ko aza ki kai bamu sani ba? A gidan nan kin sha zuwa ki ci abinci ki qoshi ki tai, wa ya taba cewa ki biya?" "Ki na barin yi min gori ki biya ni atamfa ko sai na maki d'iban albarka yanzun ga?" Haushi ya gama cika Dan Talo, dan kuwa su na b'ata masa lokaci, ya matsu a gama gaggaisawa, in Lawwali zai tafi a bashi dan wani abu, kutsawa zai cikin gidan Lawwali ya dakatar da shi. Jikin katangar gidan nasu da ba ta wani cika tsayi ba Lawwali ya jingina,ya ci gaba da kallon haukan da suke. Mubaraka ta rasa me zata yi ta jawo ra'ayin su, ta na tsaka da tunani, ta tuna me ya kamata ta yi, magana ta fara qoqarin yi wa Lawwali, kawai sai ta hau tari, ta dinga tari ba qaqqautawa, nan da nan kuwa hankalin Lawwali ya tashi, ga hayaniya ta masa yawa, ya na ma tambayar Mubarakan me ya same ta ba ta ji, da ya juya ya daka musu wata gigitacciyar tsawa, gaba dayan su suka juya a matuqar firgice, su ka kalle su, shi kuwa da ya ji an yi shiru, kama Mubaraka ya yi ya na tambayar ta lafiya take tari? "Yah Auwal zan....sha...ruwa, tari na ya sarqe ni," Da sauri ya fita mota, dan dakko mata ruwa,hankalin 'Yabbuga in ya fi cikin garin Zamfara to ya tashi, rasa inda zata saka kan ta tayi, Lamishi kuwa me zatai banda dariya tace, "Shi kenan ma, tsaya ki karbi kuddin atamfar ki da ki ka mana sharrin sata," "Habaa Lamishi, ke ba ki san wasa ba halan, wasa ta ni kai miki, bari ma ki ga na tai gida, Dan Jummaa bai ko hita aiki ba" Ta sa kai zata bar gidan kenan taga Lawwali na dawowa, da ihu da kururuwa ta koma ciki, ta ja turmi, ta haye katangar gidan, ta dira a maqota, duk kurjewar da ta yi bai dame ta ba, maqota kuwa na ganin mace ta dira cikin gidan su,suka d'iba da mugun gudu, kowa na takan shi,basu san me ya diro da ita ba, ko ta kan su bata bi ba, ta arce sai gidan ta. Lamishi da Mai Buruji na ta sheqa dariya. Mubaraka ta shiga suka hau dariyar a tare, ko da Lawwali ya shiga ya gan su tare sai ya juya ya yi d'akin shi. Duk dakin ya yi matuqar yin datti da qura, duddubawa ya yi duk an dauke masa abubuwa masu mahimmanci, har kayan sawa da takalmi. Ya na nan tsaye ya na tunanin rayuwa, ya dinga jiyo dariyar su Mubaraka, da mahaifan nashi,can kuma ya ji Mubaraka na bada hakuri, da sauri ya bar dakin ya fita. "Menene ke faruwa?" Cikin qoqarin maida kwallar ta ta ce, "Babu komi" A tsawace ya ce, "Menene na ce? Waya tab'a ta?" Lamishi ce ta ce, "Yo gani nayi ta dawo daga tahiya ba ko tsaraba, hannu na dukan cinya, kuma dai nasan bata kasa sanin irin halin talaucin da muke ciki, abinci ma gagarar mu shi kai, dan rashin tausayi irin naku, kun bi duniya kun....." Kallon da Lawwali ke mata ne ya sa maganar ta maqalewa a wuyan ta, Dan Talo kuwa ji yake kamar ya buga mata mari sai kumatun ta sun fi na Hameeda tashi (lols) duk za ta bata masa shirin qorafin da yake tafe da shi a lissafe, yanzu in ran shi ya ɓaci ya fita a hasale wazai bashi sisi? "Wai ku yaushe ne za ku yi hankali?....shin dan Allah na tambaye ku, ku ne iyayen mu kuwa? Kun san ma'anar haihuwa kuwa? Kun san wane ne d'a ko d'iya kuwa? Ina su Jameelu? Ko kun san ina da labarin irin barnar da su Jameelu suke yi yanzu na sace-sacen kayan mutanen unguwa? Iyaye kala kala ne a duniya tabbas, akwai iyaye nagari, masu kula da d'iyan su, ta bangaren ,ciyarwa,tarbiyya,tuwahi,ilimi, da duk abinda ya kamata, Sannan akwai iyayen banza, irin ku, baku kula da tarbiyyan d'iyan ku, ballantana abinda za su ci, ba ku san ku basu ilimi ba, balle sutura, da ku da iyayen da ke kai d'iyan su almajiranci,ba su san cin yaran su ba, balle shan su, ba su san a wanne hali suke kwana ba,da ruwa da sanyi da zahi, ciwo da halin qunci, duk basu san ya d'iya suke ba, baku da bambanci,duk d'aya kuke, a zato na tunda kun ka ga baku gammu  ba na tsahon wannan lokacin, za ku neme mu, za ku damu, ku na nan ba ma cikin ran ku ma, burin ku, mu je mu kewayo, mu kawo maku kuddi ko? Kuddi kuka so ko? Yunwa kuka ji ko? Ina zuwa" A haukace ya nufi garken awakin Dan Talo, ya bude su, sun kai guda tara, ai kuwa suka fita a guje, Dan Talo na ihu, Lamishi na Ihu,dan akwai uku nata a ciki. Har qofar gida ya raka awakin ya kalli abokan  Dan Talo ya ce, "Duk wanda ya kama shi tafi da su gidan shi, na bashi," Ai kuwa kamar qananan yara haka dattijan nan suka kwasa a guje su na bin tumakin nan, Dan Talo kuwa sai fadi ya ke ya na kumawa "Walle ban bayar ba, ku bar min bisashe na" Komawa Lawwali ya yi ya ce, " kun gane ta nan, ta san darajar ku, ta na son ku, ta na qaunar ku, shi ne dalilin da yasa ta dage sai mun taho ta gan ku, kun san me nake aikatawa, amma ko a jikin ku, ita kad'ai ce ta damu da yi min nasiha, da addu'a dan na bar abinda ni ke, ku fa?....kun san me, ba zan taba yahe muku ba har abada, sai Allah ya tsai da  mu a gaban shi, ya ji dalilin da yasa ku ka  haife mu, ku ke walaqanta mu, ku ka barmu a lalace haka, sai Allah ya saka muna, ba iyaye na taqama da tsinuwa ba, komi ta yi maki, mai kyau, ko kure ki tsine mata, ki hada ta da mummunan kalami, ke san me ya same ta a dalilin kalaman ki?...." Da sauri Mubaraka ta zube a gaban shi, ta na kuka,ta na bashi hakuri akan kar ya tona mata asiri, dan kuwa tonon asiri ne wannan, tun da ta san iyayen ba wani son ta suke ba. "Bari na sanar da ita fatan da take maki kullum na kiyi gantali, baki yi gantali ba,gantalin ne yasame ki, inda ki ke, ko ke san cewa an yi mata fyade? Ki na da labari ko baki da shi?" Mubaraka ce ta rushe da wani irin kuka mai matuqar ban tausayi, shi kan shi bai san hawaye na zubar masa a idanun shi ba, zuwa jikin rigar shi, tsabar qarfin fitar su. Bai san ya zai fahimtar da su, ya yake jin baqin ciki a cikin zuciyar shi ba, duk wani irin bayani da zai yi ba zai bayyana yanda ya tsane su ba, Dan Talo da ya shigo ya ji kalaman Lawwali sai da ya zauna dabar a qasa, Lamishi da Mai Buruji Kuka, Mubaraka kuka,  dariya Lawwali ya yi ya share hawayen shi ya ce, "Lallai ku na da abun mamaki, menene kuma na  kuka? Fyaden da an ka yi ma diyar ku? Ko kasancewar d'an da kun ka haihwa na kisan mutane da hannayen shi? Ko kuwa salwantar da rayuka da dukiya, da mahallin mutane da gudan jinin ku ke yi, shi ke sa ku kuka? Barakana tashi mu tai, mun ji, mun amince, ku ba iyayen mu bane, mun yarda ba ku son mu, ba ku damu da mu ba, za mu rayu ko ba ku, mun kuma godewa Allah da ya nuna mana gaskiya, dan haka ku zauna ku ci gaba da rayuwar da kuke kamar ta dabbobi, yau ko dabba ta haihi d'a ta na so nai, ta na kare shi daga miyagun da za su cutar da shi, ta na bashi abinci, amma ku...ku ban san mi zan kira ku da shi ba" "Yah Auwal ya isa haka, kar ka je ka jawo Allah ya yi hushi da kai, Iyaye na da girma da daraja, dole ne mu kyautatawa musu, ko muna so ko bama so, ko da basu zamo nagartattu ba, ko da kuwa kahirrai ne, ka yi hankuri mu tafi, kar ka hwadi kalmar da zata sanya Allah shi yi hushi da kai, duk yanda suke iyayen mu ne, dole mu yi musu biyayya" Kallon Dan Talo ya yi, ya ga yanda ya ke ta kuka, shi abun ma dariya yake bashi, to kukan me suke? Kudi ya kwaso a aljihun shi ya wurga masa, Mubaraka ta yi saurin kama hannun shi, ta na hana shi wulaqanta iyayen shi,domin ta ji wa'azi sosai akan girman iyaye,durqusawa ta yi ta na kwashewa ta na zubawa Baban nasu a jikin shi, a ladabce, wajen su Lamishi ya je ya wurga masu kudi suma, sanan ya kalli Mai Buruji ya ga yanda take kuka sosai. "Ki dena kuka yanzu, kuka na tahe zuwa nan gaba, ba dai kin biye mata ba, dan kar ta dake ki, yanda kuke yi a baya, ki sha kashin banza, shi ne ki ke qin yi wa diyan ki tarbiyya ko? Ta saki nata sun bi duniya, kema kin saki naki ko? Da kyau, kuka na nan tahe, ki bar taya ta kuka, naki na tahe," Kama hannun Mubaraka ya yi, suka bar gidan, cikin tsananin fushi, basu zame ko ina ba sai gidan da ake ajiyar No 1........................ *Jama'ar kwarai gobe ranar Arfa..dan Allah kar ku manta a ajiye duk wasu ABUBUWAN da ba su da mahimmanci kamar yanda alhazai suke can Makka suke kwasar lada mu ma mu kwashi namu a gida, a yawaita karanta LA'ILAHA'ILLAHU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHULMULKU WALAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADEER.* *Happy sallah in advance love you mutanen kwarai* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH *Assalamualaikum barkan ku da sallah 'yan uwa musulmi...Allah ya maimaita mana mai yawa mai albarka...Allah ya karbi ibadun mu...ina nan ina jiran barka da sallah na😃❤️* PAGE 56: Mubaraka dai na zaune a mota, har wannan lokacin ba ta daina sharar hawaye ba, hawayen da ke zubo mata daga can qasan zuciyar ta ya ke tahowa, rayuwar da suke ciki bata da suna, balle fassara, ina ma ina ma su na da iyaye na gari? Lallai da ba wanda zai fi su jin dad'in rayuwa ,amma inaaa, rayuwa na ta gara su, duk inda ta kad'a can take kai su, su kuwa bin ta suke a koda yaushe. Hanyar da ya ke shiga sabon waje ne a wajen Mubaraka , Ita dai nata ido, bata ce komai ba, har suka tsaya a wani madaidaicin gida. Fita ya yi, ya zagaya ya bude mata qofar, sannan ya kama hannayen ta biyu, ya tsaida ita a gaban shi, fuskar ta ya d'aga ya na kallon cikin kwayar idanun ta, hawaye ya gani kwance su na rige rigen fitowa, wani abu me zafi da rad'ad'i ya ji a zuciyar shi ya na dukan shi , cikin kad'a kan shi ya ce, "Ya isa haka nan, daga yau in shaa Allahu ba ki koma yin kuka Barakana, indai su ba za su so mu kamar kowanne iyaye ba, na maki alqawalin zan so ki kamar yanda iyaye nagari ke son d'iyan su, zan so ki kamar yanda yaya nagari yake son qaunar shi, Barakana duk abinda ki ke so na zamo miki ni Lawwali na maki alqawalin zama shi, abu guda ni ka so wajen ki, shi na ki dena kuka, ban san ya zan fahimtar da ke kukan ki ke yi min ga zucciya ba," Kwantar da kan ta ta yi a qirjin shi, ta qanqame shi, ta na jin dikkan soyayyar da ya lissafa na shigar ta, tabbas Lawwali babbar katanga ce a rayuwar ta, bata fatan abinda zai raba ta da shi duk duniya, za ta yi ko mene ne da bai sabawa Allah ba dan ganin ta tabbata tare da shi cikin farin ciki. Kama hannun ta ya yi, suka shiga ciki, yaran oga na ganin shi suka hau fara'a, domin tun kan ya zo ya sanar da kowa shirin shi, ya kuma yi wa kowannen su alkhairi, No 1 aka kira ya fito, gaba daya Mubaraka bata gane shi ba, dan kuwa ya zama gurgu, ya daku matuqa, ya azabtu, duk jikin shi ya nuna alamar wahala da gajiya da azabtuwa. Godiya ya yi wa Lawwali da ya kauda kai daga ganin shi, ba dan alqawarin da ya yi na dena kisa ba, tabbas da No 1 ba zai bar wajen nan da rai ba, amma ko gurgantakar da ya samu a qafar shi ta hagu ta ishe shi tuna abinda ya aikata har qarshen rayuwar shi. Kallon da ya kure Mubaraka da shi ne ya sa ta gane ko wane ne, ai kuwa da sauri ta labe a bayan Lawwali, Lawwali kuwa a harzuqe ya kai masa shaqa, "Shin kallon mi ka kai mata? Ba ka tahiya sai na sauya ra'ayi na na sa harsashin bindiga na hwashe ma kai?" Da sauri Mubaraka ta riqe hannun shi, amma har a wannan lokacin bata fito sosai inda No 1 zai gan ta ba, ta na labe a bayan Lawwali, hakan ke baqanta ran Lawwalin, No 1 kuwa zubewa ya yi a guiwowin shi duka biyun, ya duqar da kan shi,sai da mubaraka ta saki qara ta yi baya ta sake qanqame Lawwali. Hakuri No 1 ya fara bata, cikin wata iriyar murya mai son yin kuka, Lawwali ne ya janyo Mubaraka gaban No 1 ya ce, "Sanya ijiyar (idon) ki cikin na shi, ki gan shi a qasqance a qasa a gaban ki,ba shi iya miki komai wallah, in har baki dena jin tsoro nai ba zan kashe shi yanzun nan, dan ba zan bar abinda ki ke tsoro ya ci gaba da yawo a doron qasa ba" A hankali ta fara jin tsoron No 1 na barin jikin ta, ko dan kar a kashe shi, dole ta ware, sai da Lawwali ya ga Mubaraka ta daina kyarmar da take sannan ya sa aka tusa qeyar No 1 ko na mota ba wanda ya bashi, ya na ji ya na gani aka rufe gidan,aka bawa Lawwali key, suka shige motocin su suka bar shi a wajen. Su Lawwali basu tsaya a ko ina ba sai asibiti. "Yah Auwal waye ba lafiya?" "Mu tai ki na ganin ko waye" Asibiti ne na hamsaqai, riqaqqun masu abun hannu, Mubaraka sai kalle kalle take, sai da Lawwali ya samo dakin da za su, ya ja hannun ta suka tafi, 'yan sanda ne guda biyu a bakin qofar dakin, su na tsaron wajen, Lawwali bayani ya musu da cewa shi surukin mara lafiyar ne, sannan suka barshi ya shiga. Hajiya Ikee na ganin shi ta tafi da sauri cikin kuka ta tsugunna a gaban shi, "Dan Allah Lawwali ka yi hankuri, ka yahe muna, ka tausaya wa halin da Daddyn Sultan ke ciki, ba shi iya magana, qafar shi ta shanye, hannun shi guda ba shi motsi, gashi har yanzu damuwa bata bar shi ba, rashin ganin yaran shi na damun rayuwar shi,duk daren duniya da ihu, da kururuwa muke kwana, kamar ya na ganin wani abu, gashi ba shi magana balle mu gane me ya ke gani, " Dariya Lawwali ya yi sannan ya ce, "Me zai gani ko banda aljannun da ya ke wa tsafi? Bai basu jinin bil'adama ba kwana biyu, ba dole su biyo sahu ba? In ba ku je aka rushe dakin da ya gina ya na tsahi cikin shi ba,kuma baku yi wa aljannu sadaka ba walle yana cikin tashin hankali, kad'an ya fara gani" "Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, yanzu ya za mu yi?" "Ina nissani? Na so gobe yaran ku su zo ganin ku, Sultan ya dawo gare ku, amma 'yar ku ta lalata shirin, ta ci amana ta, ta qone duk wata shaida da zan hannintawa hukuma, dan mu karbi hukuncin mu daidai da abinda muka aikata, amma ta qone su, dan haka ba za su dawo yanzu ba," Kuka Hajiya Ikee ta fashe da shi ta ce, "Yau na shiga uku ni Ikileema, ina zan sa rayuwa ta? Yanzu Lawwali ba wata alfarma da zaka yi muna mu gan su?ka duba halin da Daddyn Sultan ke ciki" Dariya Lawwali ya yi, sanda ya kalli yanda Excellency ke dalalar da yawu, ya kasa magana sai hawaye. "Ke walle wanga aljannu ka damun shi ba kewar d'iya nai ba, in ku na neman maganin aljannu ku nema, sai an jima"(ke wannan aljanu ke damun shi ba kewar yaran shi ba, in zaku nemi maganin aljanu ku nema se an jima) Mubaraka ce ta ce, "Hajiya ki gafarce ni, ni qarama ce, amma ina mai baku shawara, da ku nemo mallammai na kwarai,wanda sunka san Allah, su yi addu'a aljannun su tafi, amma in kuka yi musu yanka, za su dawo su ce wani abu suke so, ko rayuwar wani a cikin ku, Allah shi kiyaye" Ai Hajiya ikee na jin rayuwar wani a cikin su, ta tsure, kallon Gwamna Halliru ta yi, ta ce, "Mu na zaman zaman mu da rufin asirin mu ka doko muna siyasa, gashi nan, mu na ganin ibtila'in rayuwa, ba mulkin, ba dukiyar, ba d'iyan mu, ga wani tashin hankalin yanda za mu rabu da aljanun da ka jajibo muna" Lawwali kam dariya kawai yake kamar wani wawa, cikin surutai da sambatu suka bar Hajiya Ikee, Gwamna Halliru kuwa na kwaranyar da hawaye ta gefen ido. Sai da suka tsaya Lawwali ya yi siyayya ta kayan kwalama, da duk wani abu da ya san Mubaraka na so, har zai fita daga wajen shopping din bai sai wa Sultana komai ba, sai ya ji ya kasa tafiya, komawa ciki ya yi, ya daukar mata best chocolate din ta, da candy din da ta fi so, sannan ya ga wani turare mai kyau na mata, daukar mata ya yi, ya na murmushi. Sai da ya biya kudin komai, sanan ya koma mota, Mubaraka na nan zaune, ta na ta tunanin yanda za ta sanya Lawwali ya bar Su sultana Su je su ga iyayen su, Hajiya Ikee ta matuqar bata tausayi. Ajiye mata ledojin ya yi a cinyar ta, ya koma mazaunin driver ya zauna. "Barakana ga naki nan, wancan na Sultyna ne, ki bata amma kar ki ce ni ne na bayar a bata," "Yah Auwal kenan, ana soooo ana kaiwa kassuwaaa" Dariya suka yi, sannan ya tada motar dan komawa gida. Mubaraka ta matsu su koma, dan basu yi sallar azahar ba, ga la'asar ta Kunno Kai. ************************ Hajiyan Hansatu ce ta kira Hansatu, ta ke tambayar ta, tunda Isah ya tafi sun yi waya kuwa? Saboda yau sati d'aya da kwana uku ba labarin Isah ko ta ina, layin shi tun ya na shiga ba a dagawa, yanzu ya ma dena shiga. Hansatu ta rasa amsar da za ta ba Hajiya, kawai sai ta ce, "Shi na lahiya qalou Hajiya, kar ki damu, in mun kai waya zan sanar masa ki na so ku gaisa" "Ahhh ahh basshi d'ai, dama son nikai na ji lahiya shike ko ah ah" "Shi na lahiya lumui Hajiya, ina Yayah Musa? Shin aunty bata dawo ba har yanzu?" "Shekaran jiya dai Yayan ki ya aika musu da takardar saki, ya ce ya gaji da iskancin ta,na so na hana shi, na kira na mata magana, ta inda take shiga ba ta nan taka hita ba, wai na bi na qanqame d'a na, na hana su sakewa, ban barin shi ya je wajen ta, ke ki ji hwa?" "Kayyaa ban ji dad'in rabuwar su ba, Allah shi sa hakan shi ne ya hi alkhairi" "Ameen, ina wannan me gidan da bai iya cehwane ba?" "Shi na lahiya, ya ce zai siyo maki haqorin roba ki laqa, tunda na ki ya hwara tsuhwa" Dariya Hajiya ta yi, suka ci gaba da hira cikin nishadi, ita da yar ta ************************ A kurkuku kuwa, Isah............. *Sai anjima Inshaa Allahu* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 57: Isah na can an miqa shi wajen kuliya manta sabo, ba irin bayani da Isah bai yi ba,amma abu ya ci tura, duk iya bincike da shaidu sun nuna koken ta Isah ce,dan haka nan take aka yanke masa hukuncin shekara goma a gidan maza da horo mai tsanani,dan kuwa Saudiya ba kamar Nigeria  bace, ba su b'ata lokaci wajen yanke wa duk wani mai laifi hukunci, Isah ya yi kuka, ya yi kuka, ya godewa Allah, ba irin yunquri da bai ba na a bashi dama ya kira gida ba wanda ya bi ta kan shi, haka aka ingiza qeyar shi zuwa kurkuku. Duk da cewa kurkukun su ba irin namu bane, mai cike da datti,qazanta da rashin abubuwan da mutum zai buqata, amma kurkuku kurkuku ne, Isah ya yi dana sanin zuwan shi Makka, ya yi dana sanin sanin sana'ar saida goro a rayuwar shi. Tun ya na kuka da qarfi, ya koma yin na zuci, sai dai hawaye da ke kwaranya kamar an bude magudanar ruwa, rayuwar shi tun daga yarinta ya ke tunawa, shi dai gaba d'aya bai da sa'a a rayuwa, bai rabu da iyaye lafiya ba, ga iyalin shi ya baro su na fushi da shi, bai kyautata alaqa da su ba balle su neme shi, yanzu da ace a baya ya na kiran Hansatu da ya zo,ya san da ta ji shi shiru dole za ta neme shi, "Kaico na, kaicon rayuwa ta ni Isah, yanzu ina zan saka rayuwa ta na ji dad'i, shekara goma ba kwana goma bane ba fa," (A haka Isah ya samu rangwame ne, domin kuwa wasu hukuncin kisa ake yanke musu a Saudiya, indai aka kama mutum da miyagun kwayoyi, wasu shekara biyu da bulalai, wasu goma da bulalai) A ranar ko abinci Isah bai iya kaiwa bakin shi ba, duk ya fad'a ya yi zuru-zuru kamar ya yi shekaru a wajen. A can gida Nigeria kuwa Hansatu ta d'auki shawarar Hajiyan ta, sun saka yaran a makarantar kud'i, driver guda Yaya Musa ya sama musu da mota, ya je ya kai su, in an tashi ya maida su gida. Da yamma kuma Hansatu da kan ta za ta raka su Islamiyya, ta kuma gargad'e su kar su kuskura su koma gida ba tare da ta je daukan su ba, su zauna wajen Baba me gadin makarantar har ta je. A cikin gida kuma ta kama sana'ar had'a sabulan gyaran jiki, dan kuwa ta kware sosai a haɗawa, jikin ta ya yi luwai luwai kamar matar wani hamshaqin. Ta na yin sabulun tumeric Sabulun water melon Sabulun hinna Sabulun carrot da Sabulun cucumber. Sai man kitso mai kyau da gyaran gashi, ta dage sosai wajen bunqasa sana'ar ta, da inganta ta, ta yanda kowa ya gani zai sha'awa, in mutum ya siya ya yi amfani da su, sai ya koma, kafin wani qanqanin lokaci Hansatu ta fara shiga gari itama,ta maida wa yaran ta da sana'ar ta hankali,lokuta da dama, in ba wani abu ne ya faru ba, mantawa take da Isah, ita kan ta ta na mamakin yanda a lokaci daya ya fita a ran ta. (Duk Mai son man kitso Mai Sanya gashi tsaho da santsi da maganin amosalin Kai da karyewar gashi, ko Kuma Mai son sabulu Mai kyau da zai gyara wa mace fata ta yi kyau da sheqi, ko body scrub ko body oil ta nemi wannan No 09031416423...HAMIBRAH PRODUCTS sune na d'aya wajen maida TSOHUWA YARINYA ) (Haka lamarin yake, duk sanda aka samu namiji azababbe, da ya addabi iyalin shi da mugun hali da d'abi'a, to za a wayi gari duk wata soyayya, biyayya, da tsoron shi da iyalin ke ji ta kau, qiyayya mai qarfi da rashin jin qai za su maye gurbin soyayyar da aka masa a baya, haka in mace ce da bata iya magana ba, kuma bata da kyakkyawan hali da d'abi'a, a hankali take fita a ran miji, duk kauda kan da yake akan ta, kuma da ya fito mata da halayyar shi ta musguna wa shima, sai ka ji mace na fad'in mugu ne, ba shi da dad'in zama) In sun samu lokaci da weekend sukan kai wa Hajiya ziyara, watarana kuma Hajiya da kan ta take zuwa,su gaisa. Bayan Hansatu ta tura yaran ta makarantar boko ne, ta yi wanka, ta shirya cikin wani yadi mai kyau, da tsada, Hajiya ce ta musu anko har su Ameenatu, kulle gidan ta yi, ta fad'a na maqotan ta, wato 'Yabbuga, bakin ta dauke da sallama ta shiga. Shiru ta ji ba wanda ya amsa, "Shin mutanen gidan ga su na nan kuwa?" Cikin wata iriyar murya, kamar an shaqe mutum, ko kuma mutum na cin abinci, haka ta ji an amsa mata da, "Ko ni shigo ciki,na amsa" Qarasawa ta yi, dan ta san masifar 'Yabbuga, ko ba abinda akai, ta na iya b'ata rai, ta na amsa wa mutum magana d'aya d'aya. Hansatu ce ta ja ta tsaya, tare da rafka salati, "Waggaa, mi ya faru hakan  na gankin  huska ta qabe (kumbura) me ya kwashe maki huska? Shin gobara ta kun ka yi ban sani ba? Ko hatsarin mota?" Wata harara 'Yabbuga ta samu da kyar ta wurgawa Hansatu, sannan ta lashe dan saman bakin ta da ya haye, ya yi sintim, zama Hansatu ta yi a gefen 'Yabbuga, ta nata watsawa'Yabbugan tambaya, dan ta na son sanin me ya faru da ita, ta ga guiwar ta d'aya a dauje, ga gefen fuskar ta ya dauje shima, baki ya haye, 'Yabbuga dai bata kula ta ba, sai ma wani tuquqin baqin ciki da ke taso mata a rai da take ji, wai me ma ya kawo Hansatu gidan a irin wannan yanayin? Sallamar Dan Jumma ce ta karad'e tsakar gidan, Dan Jumma da Hansatu sun gaisa ta masa ya me jiki ya amsa, tare da fad'in, "Jiki dai ga shi nan, mai shi na jin shi,tunda kin gane ta nan, ta dai girme ki, amma kin hita hankali, da sanin ciwon kai, ta je jidali(fad'a) , can gidan Dan Talo, sun ka liqa mata mugun kashi" A hasale 'Yabbuga ta kalle shi da kumburarran baki, ta ce, "Wai shin uban wa yacce kashi an ka ban? Wacce ma kashi an ka ban eyee?" "Tau sanda kin ka yi aniyar tahiya yin hwada(fad'a) akan atanhwar (atampa) da ko dubu uku ba a siye ta ba ban hana miki zuwa ba? Nan nan na dinga baki hankuri, zaman tare ba a haka nan, kema su na kyautata maki, kin ka ce ba ki iya hankuri sai sun biya, ki ka tai, kuma ki ka dawo a haka, bani cewa liqa miki kashin wahala an ka yi?" "Banga wahala ba, sai dai ka gan ta nan bisa kan ka, ba wadda ta isa liqa min kashin wahala duk shiyyar nan balle gidan Dan Talo, bai auri matar da zata liqan kashi  ba, nace bai auri matar da zata ban kashi ba," "To in ba kashi sun ka baki ba mi na na ya hwaru?" Cikin bata rai ta labarta musu duk abinda ya faru, Hansatu da Dan Jummaa kasa riqe dariyar su suka yi, sai da suka dara sosai, sannan Dan Jummaa ya ce, "Ko da na ji, ashe ke da giinaa (gini) kin kai hwada tak-kashe ki qas, (ashe ke da gini ki kai fada ta kayar da ke qasa) kuma ke da d'an ki menene na gudu har da haure gini? Inda kin samu karaya hwa?" "Walle gwanda na samu karaya a gini, da ace yaron nan mai baqar zucciya ya kammin, na zama abar kwatance ga shiyya,iyayen shi ma ba barin su ya yi ba balle ni" Dariya kam ranar Hansatu ta yi ta har da hawaye, daga qarshe ta zari dubu daya ta bawa 'Yabbuga ta ce ta sai madara, dan kuwa bata ga ta inda abinci ze shiga bakin nan ba, ba tare da an ci azaba ba, Godiya ta dinga yi kuwa, ta na so ta yi murmushi ba hali. Hansatu bakin titi ta je, ta sai musu kayan miya da naman miya, ta koma gida, dan d'ora girki, kafin yara su koma gida. ************************ Sultana na zaune a bakin qofar dakin su, ita da Sultan su na hira, ta sanar da shi abinda Lawwali ya ce, na hana su zuwa ganin Daddyn su, bai b'ata rai ba, bai kuma nuna damuwa ba, ya ce kar ta damu, duk sanda ya bar su za su je ne, hira suke sosai akan abubuwan da suka faru a baya, suka ga motar Lawwali ta nufi wajen da suke aje motoci, gaba dayan su hankalin su ya tattara ya koma kan masu fitowa daga motar, Sultan na ta kallon mubaraka, sultana kuwa idon ta na kan gwarzon mijin nata. Lawwali na ta wani had'e fuska, shi a dole kar Sultana ta ce ya sakko daga fushin da yake da ita, gaisawa suka yi sama sama da Sultan ya shige daki, Mubaraka na qunshe dariya, cike da murmishi ta miqa wa Sultana ledar ta na kallon idanun ta, dan ganin kalar murnar da za ta yi, in ta ga me ke ciki, Sultan kuwa ita ya ke kallo, ya na murmusawa, yana yin ta ba qaramin tafiya da shi ya yi ba. Taheer ne tafe zuwa wajen su Mubarakan, dan tunda ya ji dawowar su ya tsaya ya ɗan gaggyara shi ma a gan shi fess, tun daga nesa ya hango irin kallon da Sultan ke yi ma Mubaraka, kwafa ya yi, a ran shi ya ce, 'kaii wanga ba dan yanzu mun aje harka ba, ai da tuni na sheqe shege, ji wani kallo awa baqin maye' Sake kwafa ya yi, sannan ya d'aga qafa dan zuwa wajen nasu. "Mubaraka wannan fa?" Dan duqawa Mubarakan ta yi saitin kunnen Sultana, ta mata rad'a, ita kuwa wani irin annuri ke fita daga fuskar ta, ta na fitar da siririyar dariya,mai dad'in sauti, "Mi na na kuke fadi ba a so na ji? Mubaraka ba kyau fa abinda kin ka yi yanzu, mu na tare ki ware ta ku yi magana a gabana ban ji ba" Dariya ta yi, sannan tai qasa da murya ta ce, "Ba na so yaya ya ji mi na ce, matso ka jiya" Matsawa ya yi, sannan ta  kai bakin ta  kunnen shi za ta masa rad'a Taheer ya katse su da fadin, "Mi na na haka? Ke Mubaraka me ke nan?" Ba tare da ta kula da yanda ya b'ata rai ba, ta ce, "Wata magana zan fada masa, bana so yaya ya ji" "To muje ta can ki fada masa, amma me ye na masa rad'a ga kunne?" Sultan kuwa ba abinda yake banda dariya, shi gaba daya Taheer dariya yake bashi, ko ta ina Sultan ya masa zarra, amma ba laifi wajen gwadawa, wataqila ta zabi Taheer din shi ta bar shi. "Basshi kawai Sulty Baby za ta hwada min, ba dai ke sanar da ita abinda za ki fadan ba?" Daga kai Mubaraka ta yi, ta na dariya, "Tau ya yi, sai an jiman ku" Sallama ya miqa wa Taheer hannu su yi, kamar kar ya miqa hannun, amma ya miqa, ya kuwa matse hannun Sultan din da qarfi,Sultan ya ji matsar da aka masa, amma sai ya yi kamar bai ji ba, sai da Taheer ya gaji dan kan shi, sannan ya sake masa hannu, Sultan ya wuce ya bar Taheer da Mubaraka a wajen, anan ne Mubarakan ke bashi labarin zuwan su wajen No 1. Sultana kuwa ta shiga d'aki ta tarar da Lawwali na ta kaiwa da kawowa, daga shi sai dogon wandon kayan da ya sanya, jikin shi babu ko vest, ajiye ledar ta yi, ta zagaya ta bayan shi, ta zira hannayen ta ta rungume shi, idanun shi ya kulle, dan jin yanda take taba shi a hankali, kan ta ta kwantar a bayan nashi, cikin murya mai sanyi da sace zuciyar mai sauraro Sultana ta ce, "Auwal ka yi hankuri, ka yahe min duk abinda ka ke tunanin na yi maka shi, ba haka bane a raina,ka sani a duk duniyar nan ban taba son kowa ba, bayan kai, kai ne namiji me matuqar mahimmanci ga rayuwa ta, kai ne dalilin da ya sa na aikata komai,ban yi dan Daddy ba, dan Allah ka min murmushin ka mai kyawun nan ko zan ji sanyi ga rayuwa ta,bana so na wayi gari ban ga hwarin ciki ga huskar ka ba, ina so ka ci gaba da kasancewa cikin walwala da annashuwa, da annuri,ina yi wa Allah godiya da ya bani kai a matsayin miji na,kai ne rayuwa ta, kai ne komai nawa,kai ke bawa rayuwa ta farin ciki, jin dad'i da nishad'i, ina murmushi ne kawai in ka na murmushi, zan shiga damuwa da tashin hankali in ka dena fara'a,soyayyar ka da kulawar ka, su ne kawai abinda suke riqe da ni a yanzu, inna rasa su, zan rasa rayuwa ta ne gaba daya" Hawaye ke zuba a idanun ta, kalaman ta sun yi gini mai qarko a zuciyar Lawwali, cikin sanyi ya juya, ya daga fuskar ta, ya sanya hannun shi duka biyun ya na share mata hawaye, bude idon ta tayi, ta kalle shi, gani ta yi ya na murmushi, nan da nan kuwa ta saki na ta, daukan ta ya yi cak, ya nufi gadon su da ita ya ajiye ta a bakin gadon ya durqusa a gaban ta, ya na wasa da hannun ta. "Sultyna na fahimce ki, amma abinda na ke so ki gane shi ne, na yi wa qasa barna,ni babban mai lehi ne,ki na sane da cewa gwamnatin tarayya na nan ta baza jami'an tsaro a nemo mu duk inda muke, da ba dan mahaifin ki na da hannu a lamarin ga ba, kuma ba wanda ya sanni sai amintattun jami'an tsaro, tabbas da tuni an kama mu, to su ma su na so asirin su ya ruhu, shi ya sa ba su hwadi ba, amma tunda ni Allah ya sa na fahimci gaskiya yanzu ba ki ganin ya dace ace na kai kai na ga hukuma?" "Auwal ka hini sanin halayen shugabannin nan namu, su kan su ba gaskiya ne da su ba, da ace qasa ce da ake tsaida Shari'a irin ta addinin Musulunci, tabbas da ni da kai na zan raka ka dan ka wanke kan ka, duniya da lahira, amma a irin wannan qasa , wannan yanayi, indai ka san ka yi lehi, to ka nemi yahiya wajen Allah, ka tuba iyakar tuba shi kenan, in Allah ya yahe maka shi kenan" Dora kan shi ya yi a cinyar ta, ya zauna sosai a wajen, ya yi shuru ya na nazarin maganganun ta. Fata take ta yi Allah ya sa ya fahimci abinda take so ya fahimta...... *Ni ma fata na kenan amarya Sulty* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 58: "Ki shirya gobe ku je ku ga Daddyn ku, ki zauna a can nan da sati guda zan je na dauke ki, mu koma gidan mu" Da wata iriyar murna ta fad'a jikin shi, ta qanqame shi ta na ihu, cikin hanzari ya daga ta ya na dariya, ya sanya hannun shi ya toshe mata baki, sannan ya sanya yatsan shi guda a kan labban shi da ke murmusawa, "Shiiiiiiii, so ki ke a ce wani mugunta na ke miki?" Janye hannun nashi ta yi, ta maida lips din ta, ta sunbace shi sau daya, sannan ta ce, "Ko ma me zaka min, ko ma me ka min, ni taka ce, kai nawa ne, ina qaunar ka miji na, ina son ka miji na, kai ne abokin rayuwa ta har abada" Shiru ya yi, ya ja ta ta zauna a jikin shi da kyau, sannan ya kama hannayen ta ya na wasa da su, kan ta ta ɗora a qirjin shi ta na sauraran bugun zuciyar shi, a hankali cikin sanyin jiki da murya ya ce, "Sultyna sai yanzu na gano wani abu, wato duniyar ga aikin banza ce wallah, amma muke ta aikata sabon Allah, da ace na mutu ina kisan mutane fa? Da ace na mutu ina jagorantar ta'addanci da fasikanci fa? Da shi kenan wuta zani ko? da shi kenan ni rayuwa ta na zo a wahale zan koma a wahale, Sultana ba na jin na samu cikakke kuma ingantaccen jin dad'i, nutsuwa da kwanciyar hankali tunda an ka haihe ni na shekara hudu a duniya nake faman shan wahala, daga wannan na fad'a wancan, kullum cikin damuwa nake, shi kan shi farin cikin da ni ke ganin ina samu, ta hanyar shaye shaye, zunubi ne, kuma wahala ce wallah, indai har kin tabbata Allah zai yahe min duk kalar abinda na aikata, ko yanzu mutuwa ta risken ba ni da baqin ciki" Da sauri ta kalle shi, tare da kada masa kan ta, murya na rawa ta ce, "Auwal na tabbatar , kuma na yi imani da Allah, Allah ya yafe maka, domin shi ya yi alqawalin yafewa duk wanda ya nemi gafarar shi, ka kuma nemi gafarar shi, ina kyautata wa Allah zato, amma ba daidai bane ka dinga tunanin mutuwa ta dauke ka, in mutuwa ta dauke ka na zauna da wa?" Hawaye ne suka fara zuba daga idanun ta, ita kan ta ba za ta iya tantance kalar soyayyar da take wa Lawwali ba, amma ta na da tabbacin duk sanda aka ce yau ba shi ba zata iya ci gaba da rayuwa mai kyau ba. "Dan Allah ka dena irin maganar nan, ba na so" "To ban koma wa, shi kenan?" "Eh shi kenan," "To wace hira za mu yi?" "Ina zuwa," Tashi ta yi ta tura ni waje, ta rufe musu qofar su, cikin jin haushin Sultana, na bar wajen ban tsaya a ko ina ba sai d'akin Mubaraka, ta na zaune, ta na shan ice cream, Taheer ya yi sallama, d'aga kai ta yi, ta kalle shi, dan ya riga ya shiga tun kafin ta amsa masa sallamar shi, balle ya jira ta bashi izinin shiga, "Yah Taheer lafiya dai ko?" "Lahiya qalou Mubaraka, sai dai abinda na ke tahe da shi, shi na iya jaddada zaman lahiya ko samar da rashin ta" Cike da mamakin kalaman shi ta miqe ta daura zani a saman qaramin wandon dake jikin ta, Taheer kuwa ko irin d'an kauda kan nan, ta na gama daurawa ta zauna a bakin katifar dakin, ta bashi dukkan nutswar ta, dan sauraran abinda ya ke tafe da shi, "Mubaraka, kin sani, na dauke ki kamar qauna ta ko?" Daga kan ta tayi, cikin gasgata maganar shi, "Mubaraka son da ni kai miki a matsayin qauna, ya rikid'e ya koma soyayyar da na ke hwatan ta kai mu ga yin aure, amma har sai kin amince, zan sanar da Oga da Fateema, amma in ki ka tabbatar min da baki so na, gobe zan koma Kano, na hakura da ke har abada" Wani irin nauyi ta ji Taheer ya dora Mata akai, wanda ta rasa ma na mene ne, shin kunyar shi take ji, ko ganin rashin dacewa ya ce ya na son ta ne ya sa ta jin nauyin shi? Bakin ta na so ya fadi abinda ke zuciyar ta amma ya kasa furta komai, gyara zaman ta tayi,cikin sanya jarumta a Muryar ta ta ce, "Yah Taheer, ba zan boye maka komai ba, dan in na boye maka ban kyauta ba, saboda matsayin da na baka na yaya na, Yah Taheer ina matuqar Son ka amma a matsayin yaya na, da ace ba Aunty Fateema ko ba na maka so irin na soyayya, zan aure ka, saboda ban ga wani abun kushewa a tare da kai ba, amma ba zan taba iya auren mijin auty Fateema ba, ana barin halal dan kunya in ji bahaushe, jin ta ni kai kamar uwa daya Uba daya muke da ita, dan Allah Yah Taheer ka yi hankuri, wannan maganar ba mai yiwa bace" Kalaman ta sun masa zafi a zuciya, amma ya fuskanci abinda take nufi, ta kuma fad'a masa iyakar gaskiyar ta, ba boye boye, ya ji dad'in yanda suka fahimci juna shi da ita, ko ba komai magana bata je wajen Oga ba, ballanta zumuncin da aka fara ya rushe, ko kuma ya qara kulluwa. "Na fahimce ki, kuma na gode da hwada min gaskiya da kin ka yi, baki boye ba,amma dai ke san ya zama dole ki hidda miji ko? Dan kuwa girma d'ai ki kai, bai kamata ace har yanzu ba ki da wanda ki ke so ba" Rufe fuskar ta tayi, shi kuma ya na kallon ta, da wani irin yanayin da bai san ya zai fassara shi ba, ya sani ba hurumin shi bane, amma tunda shi be samu ba, bari ya taya Sultan campaign, "Ya kin ka ruhe huska? Ki dauke ni kamar Aunty Fateema, ki sanar da ni ,ko dai can Kano mun yi suruki na?" Da sauri ta bude ido ta na kada kai alamar ah ah. "To a ina ne?" "Yah Taheer ni kunya nake ji" Sake rufe fuskar ta tayi, sannan ta juya bayan ta, "To ko na kira maki fateema ne sai ki sanar da ita, ko kuma na kira Oga shi kenan ma bari na kira Oga" Miqewa ya yi kamar zai fita, da sauri ta juya ta ce, "Yah Sultan na ke so" Taheer ji ya yi kamar ta soka masa wuqa a qahon zuciya, ya jima a tsaye bai juya ba,ita ma ta na can tsaye ta rufe fuska cikin jin kunya, Taheer kuwa cikin ran shi ya ce, 'shegen yaro ya yi nasarar sace Mata zuciya ba tare da ya sha wahala ba,' A zahiri kuwa cewa ya yi, "Lallai na taya ki murnar samun saurayi nagari, amma kina ganin shi ya na son ki?" Ya fadi haka ne dan ya ji me za ta ce,zama ta yi ta tankwashe qafar ta, ta tura baki, cikin shagwaba ta ce, "Yah Taheer ba zai taba so na ba, ni na sani, kar ka manta hwa ni diyan tallaka nike, shi kuwa mahaifan shi manya na,sannan yarinya nike qarama, kuma ka san dai yanda ya waye, ya yi karatu a qasar waje ba zai auri baqar mace kamar ni ba, shi ya sa ma tun sanda na fara ganin shi, na ji ina son shi nake addu'a Allah ya zaba min abinda shike alkhairi" "Ba zan so sanar dake wani sirri ba, amma ina maki hwatan alkhairi, sannan ina miki albishir da samun kyakkyawar kyauta kahin ta riske ki" Cikin rudanin da ya jefa ta da kalaman shi ta kalle shi, ta ce, "Yah Taheer mi ka ke nuhi?" "Babu komi, lokaci zai sanar dake komai, bari na tai na hwara shiri, gobe zan koma" Sabo turken wawa, tabbas Mubaraka ta ji dad'in zama da su Taheer,dan haka sai ta ji wata kewar shi mai girma ta mamaye zuciyar ta, nan da nan idanun ta suka fara zubar da hawaye, "Yah Taheer ba na so ka koma ka barmu, dama ka dawo da su Aunty Fateema nan garin," "Ki dena kuka dan Allah, yanzu Oga yaggane ki ki na kuka ai bone ya ci ni,kar ki damu kuma, za mu zanka zuwa akai akai,ga waya, duk dai, ai ba a rabu ba, bari in tai na sanar da oga batun tahiya ta gobe" "To Yah Taheer, Allah ya kaimu goben, bari na hada maka saqo ka kaiwa yarana" "To shi kenan, sai da swahe," "Allah shi kai mu" Daga nan dakin Oga ya je ya kwankwasa ya jima tsaye kafin a bude, a nan ya sanar da Oga duk tattaunawar da sukai da Mubaraka, amma bai fada masa maganar ta na son Sultan ba,sannan ya sanar da shi tafiyar shi a gobe,Lawwali ma ya so a ce ta amince da Taheer, dan ya na son Taheer a duk yaran shi,amma tunda mubaraka ta ce bata yi, ba zai tursasa ta ba, duk abinda take so shi ma shi yake so. Daga nan dakin Sultan ya nufa, zaune ya gan shi saman sallaya, da alama sallah ya idar, ko kuma karatun Alkur'ani, sallama suka yi wa junan su, sannan Taheer ya samu waje ya zauna. "Sultan ni hwa gobe zan koma Kano, saboda na gabatar da kai na wajen Mubaraka, ta ce bata yi,ban ga ta zama ba, zan koma ga iyali na,na zo ne na maka sallama, kuma na baka shawara, ka gaggauta sanar da Mubaraka soyayyar ka, dan kuwa yarinya ce, daga sanda kun ka bar dajin ga ta shiga gari, ta samu wani, sai dai na zo maka Jaje," Siririyar dariya Sultan ya yi, sannan ya ce, "Kar ka damu, in shaa Allahu ka na daga cikin manyan abokan ango, na gode da shawarar ka, Allah kuma ya sa haka shi ne yafi alkhairi, Allah shi maida ka gida lahiya" "Ameen, na gode, sai da swahe" "Allah ya tashe mu lahiya" Bayan fitar Taheer daki ya koma, ya gyara kayan shi,Sultan kuwa kasa kwanciya ya yi, ya rasa ta ya zai ya tunkari Mubaraka da maganar soyayya, shi dai be taba budurwa ba, bai san ya ze yi ba, ko Sultana zai sa ta sanar da ita? Kaiii inaa, ko Lawwali zai gaya wa direct?? Mubaraka ita ma da tunanin Sultan ta kwana cikin ran ta, tun daga ranar da suka fara zuwa ta ɗora idon ta akan shi, ta ga ya qara haske, da kwarjini, akan sanin da ta masa a baya, sai ta ji qaunar shi ta kama ta, amma haka ta daure bata nuna ba, kasancewar ta sa wa ran ta cewa ya fi qarfin ta. Amma daga baya ta ga wasu alamu da ke mata nuni da cewa wataqila shi ma ya na son ta, duk da dai ba ta tabbatar ba. ******** Washegari kuwa Sultana da Murna ta tashi, da asuba ta yi wanka, ta shirya, Lawwali na ganin zumudin da take ya kira ta, ta je gaban shi, ta na dariya, zama yayi ya na nannade hannun rigar shi, wanda hakan ya zamar masa kamar wata al'ada, "Shin ba ki bari a d'aura auren su Barira sannan ku tai?" Dafe goshin ta ta yi, sannan ta ce, "Kashhh, ka ko ga na mance wallah, qarhe goma kacce limaman da kun ka samo za a kawo su ko? To wa zai tsaya a matsayin waliyyin su Bariran?" "Wai yaran ga sun ce ni suka so, ni Ko ban san wad-da ake ba, kunya suke son bani cikin mutane" Dariya sosai Sultana ke yi, saboda yanda ta ga damuwa sosai a fuskar shi, to shi daurin auren wata ibada ce me wahala? An bayar na karba ne fa, tsokanar shi ta dinga yi, ya na daure fuska, dan shi da gaske yake bai san ya ake yi ba. Da misalin bakwai daidai, matasan suka shiga gari, dan shigo da Limamai guda biyar da suka roqa arziki, za su daura musu aure, cikin rashin sanin ina za a je limaman suka amince, sai da aka dakko hanya suka ga ana nausawa daji hankulan su ya tashi. Wasu masu raunin zuciyar har da kuka. Ko da aka iso, suka ga waje masha Allah, an gyare shi, ya yi tass, kowa cikin kwalliya mazan da matan, ga abinci da abun sha, sai hankula su ya fara kwanciya, amma sun dasa wa zuqatan su ayar tambayar me ya kawo mutane cikin wannan surquqin daji? Kamar yanda Lawwali ya ce, da misalin qarfe goma na safiya, aka daura auren mutum goma sha huɗu,a kan sadaki dubu talatin talatin. Lawwali ana gama daura auren ya bar wajen, wani waje ya nufa da ba mutane ya zauna shi kadai, ya na hawaye, tunanin rayuwar shi tun daga farkon ta zuwa yanzu yake yi,daga gobe zai bar wannan dajin ya koma zama a cikin gari kamar kowanne mutum mai 'yan ci, sai yanzu ya gane su aka sa a kurkuku, ba su suka sa a kurkuku ba, tunani ya ke, shin tuban da ya yi ya karbu kuwa? Ko dai har yanzu Allah na hushi da shi? Abubuwan da ya aikata manya ne, masu girma ne,tunanin kalaman Mubarakan shi ya yi, a duk sanda take masa nasiha, ta na sanar da shi cewar, 'Yah Auwal ka tuba ka dena wanga harkar, ka samu aiki na halal ka yi, in ka tuba Allah mai yawan gafara ne, mai son bayin shi masu yawan tuba ne, kar ka yanke tsammani daga rahamar Allah' Nan da nan ya ji wani qarfin imani da Allah na ratsa shi, ya na jin tabbas Indai tuba da yarda da Allah na sa Allah Ya yafewa bawan shi, to tabbas ya na saka rai Allah ya yafe masa. Ya na nan zaune ya ji kan reshen da yake kai ya yi qasa,alamar an zauna, kafin ya duba gefen shi qamshin ta ya sanar da shi wace ce, kwantar da kan ta tayi a kafadar shi tare da zira hannun ta a nashi. Za ta yi magana ya ce, "Shiiii, kawai mu yi shiru,mu saurari iska, da karar busassun ganyayyaki, mu saurari kukan tsuntsaye da bugun zuciyar mu, ina so na zauna da ke a haka na wasu mintuna kahin ku tahi" Kissing din hannun shi ta yi, ta sake qanqame hannun, ta kwanta a jikin shi sukai shiru. Suna nan zaune Mubaraka ta same su, murmushi ta yi, da ta ji sun yi shiru, ba abinda suke fadi, manne da junan su, a hankali ta taka, duk da qarar ganye da ke qoqarin tona asirin zuwan ta, ta na isa daf da su ta sanya hannayen ta ta rungume su a tare ta baya, Lawwali lumshe ido ya yi, sannan ya kama hannun ta ta gefe ya sumbaci yatsun ta, "Barakana ya akai kin ka san muna nan?" "Duba ku muke kawai sai na samu nasarar ganin ku anan" Murmushi suka yi, a tare dukan su, "Yah Sultan na jiran ki ku tai" Kamo su duka biyun Lawwali ya yi, ya rungume su a jikin shi da kyau, suka fara takawa a hankali,sannan ya yi kissing goshin kowaccen su, ya ce, "Ina son ku, ina qaunar ku, ku ne rayuwa ta, ina hwata mu dawwama a tare cikin hwarin ciki, duk da na san hakan ba lallai shi kasance ba, dan kuwa a rayuwa ta kaff na koyi wani abu sabo, ka na naka shirin duniyar ne, Allah shi na maka shirin komawa gare shi,kai d'an Adam, ba zaka taba gama naka shiri ba, shi ko Allah ya gama nashi Shirin akan ka Dan Adam,lokaci ne kawai da ya yi zai kire ka gare shi, kuma dole ka amsa kira nai, ina muku nasiha ku had'a kan ku, ku so junan ku, kuma ku riqe gaskiya da amana, kar ku ha'inci kowa a rayuwa, kuma ku nemi sanin Allah kahin ku bauta masa, da ace nasan Allah yanda ya kamata, da duk abinda ya hwaru bai hwaru ba, amma sai na aje neman ilimin sanin Allah, na nemi duniya, ina roqon Allah ya bar mu tare har a aljanna" "Ameeen Yah Auwal /Auwal" Suka hada baki suka fada, Lawwali ne ya sake Sultana ya dan tura baki, "Ni dai gaskiya Sultyna ban yarda ba, wai shin ke ko dan sweetheart dinnan ko dan honey din nan baki iya ce min?" Haba me za su yi banda dariya, shi kuwa tafiyar shi ya fara, ya na ta fadan rashin jin dad'in shi akan kiran shi da Auwal da Sultana ke yi, ba dan sunan soyayyar nan. Bin shi ta yi da gudu, dan ya kusan isa filin wajen nasu, ta kama hannun shi ta ce, "Zan fada maka wani suna mai daaadii, amma ba yanzu ba, sai mun koma gidan mu" "Ni dai yanzu nake so" "Ah ahh ba yanzu ba" "To ke Aunty Sultana ki sanar da shi mana, ba a fa jinkirta bayyana soyayya, sai wata ta kwace miki shi" Kukan shagwaba Sultana ta saka, ta na nuna Mubaraka, "Ka gan ta ko? Har ta hwara yi min fatan kishiya ko shekara ban yi ba" Dariya kowa ya ke yi a wajen,Sultan kuwa hankalin shi ya tashi, dan maganar da Mubaraka ta yi sai ya ji kamar da shi take, duk da bai ga alama ba,abinda bai sani ba kuwa shi ne, Mubaraka da shi take, amma ta yi kamar bata san ma ya na wajen ba, ta na so ta san shin hasashen ta gaskiya ne? Ya na son ta ko dan ta na son shi ne ya sa take ganin kamar ya na son ta? Sallama Lawwali da Taheer suka yi, Taheer na qoqarin barin motar Mubaraka a nan, Lawwali ya ce ya je da ita, ya dinga kai yara makaranta, godiya ya dinga yi sosai, sannan ya cire yar qaramar jakar shi daga motar da za akai shi tasha ya mayar a wadda suka zo da ita. Sallama ya dinga yi da mutanen wajen d'aya bayan d'aya,sai da ya zo kan Sultan ya rage murya ya ce, "Kar ka tsaya kallon ruwa kwado ya maka qahwa wallah" Kada kai Sultan ya yi, cikin yaqe, dan gaba d'aya hankalin shi ya tashi, ga dai Mubaraka ba wata babba ba, amma kwarjinin ta ya cika masa ido matuqa........ *Washhh na gaji,amma ya kuke gani mutanen kirki, shin ya kamata Sultan ya bayyana soyayyar shi a dajin Oga, ko kuma ya bari sai sun shaqi iskar gari???* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 59: Taheer ya tafi  da rabin awa, Sultana ma su ka yi haramar tafiya, zaune suke a cikin mota ita da Sultan, sai wanda zai kai su, dan ba za su gane hanyar fita ba. Ido Sultana ta zubawa Lawwali kamar ta ce masa su je tare, ba ta so su rabu ko na awa guda ne, amma ta san ba ta da wannan damar, in ba shi ya sakko da kan shi daga fushi da Gwamna ba, ba wanda ya isa ya ce ya sauka din, to wataqila sai Mubaraka . Mubaraka ta gama yadda da cewar hasashen ta na Sultan na son ta qarya ne, hasashen farko na ita din bata kai wadda zai so ba shi ne gaskiya, sallama ta musu, zuciyar ta na matuqar quna, ta bar wajen, za ta koma dakin ta, dan a yanzu ba ta so ta bude baki ta yi magana, za ta iya fashewa da kukan da ya tokare mata wuya. Muryar shi ta ji a bayan ta, cikin sanyi ya kira sunan ta, "Mubaraka" Bata gasgata kunnen ta ba, dan haka bata juya ba, a zaton ta gizo Muryar shi ke mata, saboda ta na tsananin so ya kira ta din dan ya furta mata kalmar so. Tafe take shi kuwa binta yake, tun da ta juya ta fara tafiya ya kasa samun sukuni, kasa jurewa ya yi, ya ce a jira shi, Sultana da Lawwali na tsaye su na kallon shi ya bi ta da gudu. Maimaita kiran sunan nata ya yi, Ita kuwa a yanzu ta tabbata ba gizo Muryar shi ke mata ba, dan haka tsayawa ta yi cak, bakin ta dauke da murmushi, da hope din son jin kalmar so daga bakin shi,idanun ta taf hawaye, "Mubaraka, na kasa tafiya ba tare da na bayyana maki saqon da zuciya da gangar jiki na ke ta bani ba, Mubaraka ina son ki, I love u so much, tun randa na fara dora ido na akan ki a gidan mu, na ji wani baqon lamari ya darsu a zuciya ta game da ke, ban fahimci ko me ne shi ba, saboda ni baqo ne a fagen so, tun daga lokacin nan ba ranar da za ta zo ta wuce ban tuna ki ba, amma na bar wa zuciya ta, dawowar ki daga Kano, na ga kin qara girma, kin qara nutsuwa sai na ji abinda nake ji game da ke ya na nunkuwa a rai na, a yanzu na tabbatar da cewa, ke kadai nake so, ke ce macen da na ke jira, shi ya sa na kasa kula kowacce mace da sunan soyayya" Wata ajiyar Zuciya suka sauke kusan a tare, Mubaraka ta ji dadi kwarai, wanda ba shi da misali,Sultan kuwa ji ya yi kamar an sauke masa wani babban nauyi da ya jima ya na dauke da shi akan shi. Juyawa ta yi a hankali suka hada ido, cikin jin kunya ta sauke nata idon,sannan ta saki murmushi, shi ma ita yake kallo, cike da so da qauna,amma ya tabbata da ta na kallon shi ne tun dazun da ba zai iya furta kalaman da suka dinga fita daga bakin shi ba kamar ruwa. A hankali ya ce, "Baki amsa min ba, kin karbi soyayya ta, ko dai ban miki ba ne?" Da sauri ta kalle shi, daga sama har qasa, sannan ta ce, "Wacce mace zaka ce wa ka na so ta ce bata son ka Yah Sultan?" "Macen da ba ta son na miji mai kama ta, ko mai irin halaye na mana Mubaraka" "To ni dai kamannin ka, da halayen ka duk sun yi min, ba ka da makusa a iya sanin da na maka" "Hakan na nufin ki na so na kenan?" Daga kai ta yi, ta juya cikin sauri ta nufi hanyar dakin ta, kallo ya bi ta da shi, Lawwali ne ya dafa shi, ya ce, "Tau baban soyayya, tunda ka qare aman zucciyar ka, yi hankuri ka dena kallon qauna ta haka nan, kar ta faɗi" Dariya Sultan yayi,ya ce, "To babban Yaya za a bani?" "Shi kadai ne buri na tun farko ,kuma gashi kun had'a kan ku, ya na daga cikin sharadin da nake da burin mahaifin ku ya cika min, sai ga shi kun hada kan ku da kan ku, Allah shi sanya albarka cikin wanga lamari" "Ameeen, ina godiya, waccan matar taka ta matsu na san taji me ke hwaruwa, bari mu tai, sai ka iso," "Tau ya yi, Allah shi kiyaye hanya" "Ameen" Mota Sultan ya shiga cike da farin ciki,ya bayyana wa Sultana me ya faru,ta yi murna kwarai da jin hakan. Mubaraka kuwa leqawa ta dinga yi ta window ta na kallon Sultan, bayan tafiyar su Lawwali ya kira kowa da kowa, ya fidda makullan gidajen da yake da su a hannun shi, wanda ba shi da su kuma a wajen shi Sultan ya ce zai bashi in sun hadu a cikin gari. Miqawa wasun su makullan yayi sannan ya sanar da su, ba zai yu kowa ya samu gida shi daya da matar shi ba, wani gidan sai dai mutum biyu, wani gidan ma sai dai mutum uku, daga baya duk wanda Allah ya horewa ya tashi. Godiya suka dinga yi, tare da addu'a da fatan alkhairi,wasu daga cikin matan har ma da mazan kuka suka dinga yi, sabo kenan, turken wawa. Suna nan su na jajanta rabuwar su da juna mazajen da suka maida Limaman da suka daura musu aure suka dawo, nan aka sanar da su me ya faru, sun yi godiya sosai, sannan suma sun jimanta rabuwa da junan su. Lawwali dakin su ya je, ya aika a kira masa Mubaraka. Ita ta taya shi hade kayan su shi da Sultana, ya bada umarnin kayan gadon a kai masa gidan su, can dakin Mubaraka za a saka. Su na gyara dakin ne ya bijiro mata da maganar Sultan, kunya ce ta kama ta, shi kuma dariya ya yi, ya ce, "Ohhh rayuwar duniya kenan, wai Mubaraka 'yar qararramar nan ce yanzu ta girma har ta kai ga saurayi, Allah to shi sanya alkhairi, " "Kaiii Yah Auwal ni fa ba yanzu za ka yi min  auren ba, ni dai ba na so na rabu da ku" "Tabbb ai kuwa ya zama dole, ko ba aure ai akwai mutuwa ko? Ballantana mace dama ita ba mazauniyar gidan iyayen ta bace, komai daren dad'ewa za ta yi aure, sai wadda Allah ya nufa ba zata taba aure ba a rayuwar ta" "Haka ne, Allah ya sa mu dace,...Yah Auwal yau za mu bar nan?" "Ahh ahh, sai gobe ko jibi ma, sai an kai kayan ga gida, an gyara miki d'akin ki, sannan zan maishe ki da hannu na, na damqa musu amanar ki,na gaji da faɗa da kowa ni yanzu, ba na son tashin hankali da kowa, in kin koma ki sanya wa zuciyar ki hankurin zama da su, tunda kin dai san yanda halin su shike," "Haka ne Yah Auwal, in shaa Allahu, za ka same ni mai hakuri" "Allah ya miki albarka Barakana, dama can ke mai hakuri ce,Allah shi qara maki hankuri akan duk abinda zai same ki" Ameeen, Yah Auwal dina" Haka sukai ta hirar su, su na tattara kayayyakin Sultana. ************************* Wata mata ce a tsaye a jikin mota, a gaban wani babban super market ta na waya, kaya aka debo niqi niqi za a saka a bayan mota, ta danna key din hannun ta, ma'aikatan super market din suka zuba kayan, Laminu na can gefe ya na kallon ta, ya jima ya na bin matar tun safe da ya fito daga gida, har yamman nan. Su na gamawa ta sallame su,ta shige motar ta, ta tada ta, ta hau titi, Laminu ma bin ta ya yi a baya, wata hanya ta dauka, wadda take shiru ba mutane sosai, shi ma binta ya yi, ya sha gaban ta, wani burki ta ci, tare da daga kai, a tsorace, ta kalle shi. A tare suka fito daga motocin su, Laminu ne ya nufe ta da fuskar tausaya wa, da ban hakuri, ya shammace ta ya shaqa mata wani tsumma a hanci, dauke numfashin ta tayi, ta kama hannun shi ta juyar da shi ta murde shi, ya fadi qasa da guiwowin shi, su na haka wasu motocin jami'an tsaro suka qaraso, su ma tafe suke su na bin su a boye dama. Sake numfashin ta tayi, ta shaqi iska, duk da haka sai da d'an wanda ta shaqa ya sa ta jiri. Kamata wani daga jami'an tsaron ya yi, suka sa ta a mota, Laminu kuwa tuni an danna shi a motar 'yan sandan, nan suka dunguma baki dayan su, sai police station, ana zuwa dakin tuhuma aka miqa Laminu. Binciken da jami'an tsaron suka yi akan mutuwar yaron da suka kama dan  ya bada shaida akan wanda ya sa su sace Hajiyan Hansatu ya nuna musu cewa akwai sa hannun Laminu, dan haka suka had'a masa wannan tarkon da jami'ar tsaro mace, suka samu nasarar kama shi. Laminu ya qi bayyana abokan ta'addancin shi da fari sai da ya ci na jaki, ya ga za su masa lahani a banza, shi ne kuwa ya bayyana sunan Isah, nan da nan kuwa aka kira Yaya Musa aka sanar da shi su na buqatar su a station din, dan jin yanda ta kaya. Hajiya na ta murna ta shirya ta ce ma Yaya Musa su je,a hanya ta kira Hansatu ta sanar da ita an kira su a police station, an ce a samu wani mahimmin bayani, da ya kamata su sani. Fatan alkhairi ta musu sannan ta ce in su Ameenatu sun taso daga makaranta za su zo. Su na isa station din aka sanar da su mummunan labarin da ya sanya Hajiya kuka wiwi, da idanun ta, sai lallashin ta ake ta kasa denawa, ta dauki soyayya mai tsafta ta sanya a zuciyar ta wa Isah ashe mutumin banza ne. Har wajen Laminu aka je da su, ta kalle shi ta ce, "Allah wadai da samuwar irin ku cikin al'ummar Annabi Muhammad, Allah ya shirya masu hali irin naku, yanzu ka dube ka, yaro kyakkyawa, wa ze ce za ka aikata wannan mugun abu? Yanzu shi abokin naka kuna waya ne? Dan tun da ya tahi bai kire ni ba, wancan karon kuwa ya na kira na" Cikin jin kunyar dattijuwar Laminu ya ce, "Hajiya Isah bai dawo wa yanzu gaskiya, dan kuwa abokin harka ta ta saida koken wani inyamuri ya ce ya sanya koken cikin kayan Isah kamar yanda mun ka tsara, kuma an kama Isah, an kulle shekara goma zai yi a kurkuku," "Innalillahi wa inna ilaihirraji'una, kaiii wanga yaro kwai baqin mugu, wato abokin naka ka ci wa amana haka? Shi na can daure ga hukumar da bata san sassauci ba, ka mayar min da d'iya ita da zaura (bazawara) ba su da banbanci, Allah ka isar min, Allah ka isar mana abinda yaran nan su ka yi muna" Kuka sosai Hajiya take faman yi, a haka suka koma gida, Laminu na nan ana shirye shiryen miqa shi ga kotu, asirin shi ya gama tonuwa. Tun a hanya Hajiya ta kira Hansatu ta ce ta samu abun hawa ta taho,ta wa driver waya ya kawo su Ameenatu gidan ta, cike da damuwa Hansatu ta ce to, bata so ta tsaya tambayar Hajiyan meke faruwa ta waya. Rurrufe ko ina ta yi, sannan ta leqa gidan 'Yabbuga ta gaishe ta, ta sanar da ita zata gidan su,a hanyar ta ta zuwa bakin titi, ta wuce ta qofar gidan su Lamishi ta ga ana ta shiga da kayan gado. Ga wata rumfa nan Dan Talo na ta bugawa a qofar gidan da kan shi. A bakin gate din gidan su aka ajiye ta, ta shiga, bayan ta gaida mai gadi ta wuce cikin gidan. A parlour ta tadda Yaya Musa da Yaya Abdullahi (Yayan matar Musa) su na zaune cikin jimami, su na ganin ta kowannen su fuskar shi ta sake danyancewa da tausayin ta. Hajiya kuwa kuka ta sanya, ta dinga yafitar Hansatu da hannu, wajen ta ta nufa ta zauna daf da ita, ta na so ta yi kuka, dan ta san duk abinda ya sanya Hajiya kuka ba qarami bane. "Hajiya mi ya faru? Mutuwa an kai? Me ya samu Aunty Azizah?" Ta na fada ta na kallon Abdullahi, da sauri ya kada mata kai, alamar Ah ah, "Lafiyar ta qlou, ta na Spain ma yanzu haka," "To me ya faru?" Yaya Musa ne ya daure ya labarta mata komai, Hansatu kuka ta sanya, tare da fadin "Ba zan taba yafe maka ba Isah, soyayyar ka ba ta amfanar da ni komi ba,ka cutar dani, ba iyaka, na hakura, amma sai da ka haɗa da mahaifiya ta, Isah me ta yi maka? In ni ce baka so sai ka sawwaqe min, me mahaifiya ta ta maka?......Hajiya, Hajiya, kin tuna sanda an ka sace su Ameenatu? Tabbas Isah na da hannu a wannan satar" "Ahh ahh Hansatu, babu kyau zargi, dan kuwa wannan zargi ne, ba ki tabbatar ba" "Hajiya ina da yaqinin da sa hannun Isah a wannan lamarin saboda tun sannan suke abota shi da Laminu, Hajiya akwai abubuwan da ban sanar da ke ba saboda bana so hankalin ki ya tashi, na dauki alqawarin tunda ni na bijire muku na zabe shi, komi ze yi min zan shanye ba zan fada wa kowa ba, Hajiya Isah na min......" Nan dai Hansatu ta dage ta sanar ma da mahaifiyar ta komai da Isah yake mata, Hajiya da kowa da ke wajen ya tausaya mata,sannan sun mata faɗa sosai, musamman akan qin sanar da Hajiya tunda ya tafi wancan karon bai neme ta ba, ai da ta sanar tun a sannan da an dau mataki. "Tau shi kenan yawuce ,Musa ai ka ga da rabon Allah shi hannunta shi can ga hukumar da sun ka fi mu iya hukunci, yanzu yanda za a yi, kai da Abdullahi,ku shirya ku je can wajen shi, ya sakar min d'iya ta, walle ta gama auren shi, ya qarasa shekarar shi goma ya bid'i wata ya aura, ina dalili. In ya tsaya muku taurin kai, ku faɗa masa za ku yi qarar shi akan abinda ya yi wa hansatu a can, ku tsoratar da d'an nema, ya sake ta dolen shi, yarinya ta da kyawun ta ba zata rasa mashinshini ba" Abdullahi ne ya kalli Hansatu da sauri, a zuciyar shi ya na ayyana abubuwa da dama, babban abinda ya sani shi ne, wannan karon ba me auren ta sai shi, ba zai bari ta sake kufce masa ba. An tsaida magana a cikin sati na sama za su tafi zuwa saudiya, Hansatu kuwa ta ce ba za ta koma unguwar su ba, unguwar gulma, dan ta san yanzu magana ta karade unguwar, za a yi ta nuna ta da baki da ido ne. Hajiya ma cewa ta yi ta yi zaman ta, ai kuwa ita da yara nan suka samu wajen zama abun su, tun daga ranar Hansatu ta samu abokiyar hira, haka zata zauna ta yi ta bawa Hajiya labarin abubuwan da Isah ke mata, Hajiya kuwa ta ce, "Ke ko gama zama da baqin mugu,dan neman sallamamme kawai" **************************** Da isar su asibiti, Hajiya Ikee ta ɗora idon ta akan yaran nata, sai ta fashe da kukan murna, fess ta gan su, wanda ba haka suka zata ba gaba dayan su, wani haske da sheqi ma taga su nayi, musamman Sultana. Bayan sun gaisa ne, ta ja su har gaban gadon da gwamna yake kai, duk ya fada ya rame,sai gulu gulun idanuwa, bakin shi ya karkace hannu da qafar shi kamar wanda Inna ta taba,asibiti sun tabbatar da cewa ba shi da wani ciwo da ya danganci asibiti a yanzu,sai qarancin jini da yake fama da shi,kullum ana qara masa jini leda biyu zuwa uku, hawan jinin da ya kama shi ma ya sauka, tun da jimawa, sun yi gwaje gwaje sun rasa dalilin da ya sa yake a shanye haka, kuma jinin shi ke yawan qarewa. Hajiya Ikee na gama basu labarin rashin lafiyar mahaifin nasu Sultan ya ce, "Hajiya ai da wahala Daddy ya warke,ko da zai warke din ma, domin kuwa mutane irin shi na fama da cututtukan da ake rasa gane kan su ne sakamakon Allah ya isa da mutane ke yi musu, da za a ce za a tara duk mutanen da ya zalunta, su yahe masa, na miki alqawalin sai ya miqe, amma in basu yahe masa ba, zai wahala ya tashi " "Innalillahi, na shiga uku ni Ikilima, ina zan saka rayuwa ta? Yanzu fissbillahi haka ka ke ganin ba zai tashi ba sai mutane sun yahe masa? To mu yanzu ina mun ka san adadin wanda ya zalunta?" "Ba lallai bane kuma, ta yu Allah shi bashi lafiya, amma fa zai karbi hukuncin da ya aikata a ranar gobe, in dai be tuba ba" "Yau na shiga uku na lalace ni ikilima" Kuka sosai Hajiya Ikee ke yi, shawara Sultana ta kawo, akan su maida Gwamna gida a na maganin Islamic, saboda yanzu kusan watan shi biyu a kwance, komai sai an masa, Hajiya duk ta rame, "Ai dole gida zamu kai shi, in kunka ji kuddin da asibitin ga ke karba duk kwana guda sai tsoron Allah ya kama mutum, gwamnan da an ka mayar yanzu so guda ya taho da tawagar shi sun ka duba Daddyn ku, da 'yan jarida, akai ta hotuna da video, ko sisi basu bamu ba, amma sun ce sun basuwa kuddin jinya har ya  ji sauqi, kuma ga shi asibiti kullum ni ka biyan kuddi" "Hummm Mum kenan, a bar tone tone, mu samu yanzu a kama muna shi mu tai gida" Bayan komawar su gida ne suka sha kallon ikon Allah, gwamna banda ihu da shure shure ba abinda yake, abun ya yi matuqar basu mamaki,Sultan ne ya ce su fitar da shi waje, ai kuwa ana fita waje ya dena ihun, sai zare ido kawai yake, da jin tsoron kar a maida shi ciki. "Sultan mu tai gidan mu na can titin zanna, wataqilan nan ne bashi so" "Bamu da wani gida da ya yi saura sai wanga, dan kuwa duk na bayar, anjima ma za a taho amsar makullai,nan din dai zamu koma, dole ya yi hankuri," "Yau na shiga uku na lalace ni Ikillma, kai wa Allah ku bamu makullin guda, wanda ka bawa wancan su amshi wanga" "Muka san menene acikin gidan da za mu ba wa wasu shi? Mu din dai mu za mu shiga,koma menene ku ne kun ka jawo muna, dole a haka zamu shiga mu zauna da koma me ne ne a ciki" Sultana ta kula da cewa ran Sultan ya fara ɓaci, abinda bai taba yi da iyayen su ba kenan, bayyanar da bacin ran shi irin haka, su kafe ya kafe, dan haka shiga maganar ta yi, "Hajiya mu shiga sai a nemo mallammai masu ruqiyya su taho su taimaka muna, ko ya ka ce Yah Sultan" Dauke kan shi ya yi, sannan ya ce, "Ku shiga ciki, bari na shiga gari na samo malamin da zai zo a hwara tun yanzu, makullan gidan su na cikin safe din Daddy, ki bude ki basuwa in an zo amsa" "Toh sai ka dawo" *Ku taimakawa  gwamna Halliru da malami me ruqyaaa* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 60: Sultan ya yi yawo, iya yawo amma bai samu dacewa da malami ko guda d'aya da zai taimake su ya je ya yi wa Gwamna Halliru ruqiyya ba, wanda suka amince za su je kuma bai gamsu da kalar tasu ruqiyyar ba, dan kuwa cewa suke aljanun yanka suke so a musu su sha jini, za su rabu da shi, (da damar masu cewa su na cire aljanu da yanka, ko kuma aljani ya fadi buqatar shi a masa sanan ya fita, ba rugiyya suke ba, domin ba haka ake ruqiyya ba a sunnar Annabi Muhammad ,bai bamu umarnin yi wa aljani hidima ba, kar fa mu manta Allah ya daukaka mu sama da su, kuma cutar da mu suke saboda ba ma ganin su, amma kuma a dinga musu hidima? Ko a je wajen su neman taimako? Duk wanda yake haka ya sabawa Allah, in bai tuba ba Allah zai kama shi, ko ya azabtar da shi kamar yanda gwamna halliru ke shan wahala a hannun su, ya nemi taimakon su ba na Allah ba, su kuma a yanzu suna azabtar da shi, saboda abinda ya kasance ya na aikatawa). Da kyar ya samu wani malami guda ɗaya da ya amince zai je ya ga Gwamnan, amma sai da yamma, bayan ya sallami d'aliban shi da ke d'aukan karatu a wajen shi. Sultan ya koma gida a gajiye, tun daga gate ya ke jiyo kururuwa da ihun gwamnan, gidan shiru, ba wata hayaniya, dan kuwa duk ma'aikatan sun gudu, mai gadi ne guda d'aya kawai ya rage, shi ma dan bashi da wajen zuwa ne, ya sa ya ke zaune a nan din. Da shigar Sultan gidan, Sultana ta tunkare shi, idanun ta sun yi luhu luhu, saboda kukan da ta sha ta qoshi, ganin mahaifin nasu a cikin mawuyacin halin nan ba qaramin tashin hankali bane a gare ta, ko ba komai, ya gwada masu soyayyar da bata da misali. "Yah Sultan ya na gan ka kai d'ai? Suman Daddy uku bayan tahiyar ka, na rasa me zan masa ya samu sauqin abinda yake ji" Kuka ta fashe da shi, saboda tsananin tausayin mahaifin nasu, sultan ne ya kama hannun ta, idanun shi sun yi jajawur, ya ce, "Mu je ciki, ki dena kukan haka nan, kukan ki ba shi zai bashi lahiya ba,daddy addu'a shi ke buqata, mu tai a samu a kunna karatun Alkur'ani kahin mallam ya taho, dan ba yanzu ne zai taho ba, sai yamma" Cikin ikon Allah kuwa ana kunna masa karatun Alkur'ani bacci mai dadi ya dauke shi, zama suka yi jingum jingum su na kallon shi, kowannen su da abinda yake saqawa a zuciyar shi. Hayaniya suka jiyo sosai, daga wajen gate din gidan, a tare suka tashi suka nufi waje, Hajiya babu ko mayafi, daga ita sai leshin jikin ta da d'ankwali, Sultana kuwa tun da suka je bata cire mayafin ta ba, haka suka fita. 'Yan jarida ne sun kai su takwas a qofar gidan, sai roqon mai gadin suke ya bar su su shiga daukan rahoto. Su na ganin iyalin gwamnan kuwa suka hau daukan su hoto, tare da qoqarin yi musu tambayoyi, tambayoyin kuwa sun matuqar sanya Sultan da Sultana jin nauyi da kunyar amsa su, tambayoyi ne wanda  da suke tattare da  gaskiya, amma kuma ba za su iya amsa su ba kai tsaye. Dan haka Sultan ya musu izinin shiga,kamar jira suke, cikin turereniya da rige rige suka shige gidan. Zama Sultan ya yi a saman kujera da ke a farfajiyar gidan, sannan ya ce, "Tambayoyin duk da kun ka yi muna, sun nuna cewa wasu daga cikin 'yan jarida musulmai ba su san amfanin aikin jarida ba ga rayuwar su, ta duniya da lahira, domin kuwa da damar su su yad'a labarin da zai jawo su yi suna, ko su samu wata daukaka ta duniya, ko arziqi shi d'ai suke bid'a, ba labaran da za su gyara, kuma su taimaki al'umma ba,misali, yanzu kun taho ku na so ku ji mi na na ya sami tsohon Gwamna, kun taho da list din zargin da mutane ka yi akan shi, me ya sa sanda shi na kan mulki, ba ku zuwa dan taimaka masa wajen yi mishi tambayoyin da za su sa ya yi aiki dole? Ko ku na nufin ba ku da wadannan tambayoyin tun gabanin ciwon shi? To Bari na baku amsa, amsar da na ke so ku yad'a ta a duniya kowa ya ji, da farko dai dole ne mu san cewa duk abinda ya ke faruwa gare mu a wannan qasa, da wannan yanki,na harikar kidnapping, da kashe kashen rayuka, da sace dukiyoyin al'umma, ba komai ya jawo mana ba, sai sab'awa Allah, daga mu har shugabannin mu, domin kuwa Allah ya ce, "Wancan ne, haka abin yake, lallai Allah bai kasance yana canza wata ni’ima da ya ni’imta akan wasu mutane ba face har sai sun canza abin da yake cikin rayukansu, kuma lallai Allah mai ji ne, kuma masani.” (Suratul Anfal: 53) Kenan mu na da laifi wajen barin tafarkin gaskiya, da annabin mu ya dora mu akai, mun qirqiri sab'on Allah kala kala, a jihar nan ne matasa da basu da ilimi, ba su da aikin yi ke sata, suke shaye shaye, su ke kisan kan mutane, su ke garkuwa da 'yan uwan su mutane, su ke tsafi, suke zina, suke luwadi, suke mad'igo, ba kalar zunubin da ba a aikatawa, to ku na tsammanin Allah ya kauda kai akan abinda ake yi? Ba daban Allah me rahama bane ba ma ku na tunanin yanzu da akwai wata halitta da ta yi saura a duniya? Allah ya na cewa a cikin qur'ani mai girma "Ka ce, Shi mai iko ne akan ya aiko da wata azaba a kanku, daga samanku, ko kuma daga karkashin kafafunku, ko kuma ya rarraba ku qungiya-qungiya, kuma ya dandana wa sashen ku masifar sashe (ma’ana: wasun ku su addabi wasu). Ka duba yadda muke sarrafa ayoyi, tsammaninsu suna fahimta.” (Suratul An’am: 65) Sannan Allah ya ce, "Barna (musibu da fitintinu) sun bayyana a cikin qasa da teku (a ko’ina), saboda abin da hannayen mutane suka aikata. Domin Allah (yana nufin) ya d'and'ana masu sashin abin da suka aikata, tsammaninsu za su dawo kan hanya (su daina laifin da suke yi, su tuba).” (Suratur Rum: 41) Da Allah ya so da ya halakar da mu gaba daya kamar yanda ya yi wa wanda suka gabace mu, amma ya jinkirta mana ya na nufin Mu tuba, shin baku da labarin al'ummar da ta gabace mu ne? Wadan da Allah ya halaka saboda sun saba masa?Allah ya ce a cikin alqur'ani mai girma. "Kuma da Allah yana kama mutane saboda dukkan abin da suka aikata (na zunubi, kuma ya zamanto baya yafe wani), da bai bar wata dabba ba a bayan kasa. Amma yana jinkirta masu zuwa wani ajalin da aka ambata. Sannan idan ajalinsu yazo, to, lallai Allah ya kasance mai gani ga bayinsa.” (Suratu Fadir: 45) Amma sai Allah ya ke hankuri da mu, ya ke yahe muna da mun roqe shi gafara, sannan Allah ya ke jinkirtawa wanda suka qi roqon gafara, dan in sun je gare shi ya musu azaba kwatankwacin abinda suka kasance su na aikatawa, ba dan ba zai iya kama mu ya azabtar da mu a duniya din ba ne. Da mu da shuwagabannin mu sai mun koma ga Allah za mu ga dadai, an riga an kashe matasan mu, ba ilimi, ba sana'a, ba kasuwanci, zaman banza ya yi yawa, mutum naso ya saka sutura ko ya ci abinci, ko ya samu abun hawa ba shi da ikon yin hakan, in ba shi da cikakken imani sai ya je zuwa neman kuddi ta kowacce hanya, me kyau da mara kyau. Ina mana nasiha mu ji tsoron Allah a duk abinda muke aikatawa, akan duk wani muqami komai qanqantar shi da Allah ya bamu, saboda wasun mu daidai da muqamin kwasar tutu mutum ya samu, buri nai shi cutawa na qasa da shi,ba tausayi, a tsakanin mu, ba soyayya a tsakanin mu, balle jin qai. Ina fatan na amsa dukkan tambayoyin ku a wannan jawabi nawa, mu ahalin Gwamna Halliru Murtala Gusau, mu na roqar mishi yafiya daga wajen mutanen da ya yi wa mulki ba daidai ba, mu na roqon ku da ku yafe masa, domin Allah, kar ku diba abinda ya shiga tsakanin ku da shi na rashin adalci ko kyautatawa, ku dubi Allah ku yafe masa" Duk dauriya irin ta Sultan a daidai wannan gabar sai da ya fashe da kuka, saboda ya sani, ba lallai ne mutane su yafe wa mahaifin nasu ba, sannan in masu redio da talabijin sun saurara ko kuma sun kalla, to wanda suke a qarqashin mulkin shi da ba su da kafar sadarwar fa? Wanda suka mutu fa? Wanda shi ya kashe su da hannun shi fa? Ta yaya za su yafe masa bayan ba su da rayuwa. Kukan shi ne ya tsananta, har ya sanya 'yan jaridan da kan su suka janye abun maganar daga gare shi, sun zo da niyyar tozarta gwamnan, sai gashi sun samu nagartaccen d'an shi ya musu bayani, da nasiha mai ratsa zuciya. Haka suka tafi jiki ba kwari. Masu karbar makullan gidajen da Sultan din ya bayar sun sallama sun karba sun yi godiya sosai, sannan su ka tafi. Har qarfe biyar ba malam ba bayanin malam, Sultan da sultana su ne suka yi alwala, suka ce wa Hajiya ma ta yi alwala, suka dauki qur'anan su suka yi ta karantawa, Gwamna ne ya farka da wani irin ihu, mai cike da razananniyar qara, wanda ya sanya Hajiya Ikee da Sultana miqewa suka buya a bayan Sultan a guje, sai makyarkyata suke, shi kan shi ba dan qarfin imani ba da ba zai iya zama a wajen ba, guduwa zai yi. Jijjiga jikin Gwamna ya dinga yi, Sultan kuwa na ci gaba da karanto ayoyin da ya san ana ruqya da su, bai daina jijjigar ba har sai da ya fado qasa, duk jikin shi ya nannade, musamman qafafun shi, idanun shi sun qara fitowa kamar wanda ake turo su ake musu hayaqin barkono tsabar ja da suka yi. Sultana da Hajiya Ikee ba abinda suke Banda kuka, dan ko addu'ar ma sun kasa. Yau ace mutum mai cike da isa da izza kamar gwamna Halliru ne a nannade kamar wata igiya, su na cikin haka, Gwamna ya fara motsa baki ya na so ya yi magana, Sultan bai tsaya ba, karatu kawai yake ya na kumawa, Hajiya Ikee ko qiftawa ba ta yi saboda kallon shi, a ina ya iya wanan karatun? Da yaushe ya iya wannan karatu mai dad'in sauraro haka? "Za mu sha jiniiii ! A bamu jinii ! Mu na so mu sha jinin d'an tayi !" Abinda Gwamna Halliru ke ta nanatawa kenan, kamar karatu, duk wani yunkuri na Sultan akan ya ga lamarin ya lafa, ya zo da sauqi inaaa ba wani sauqi, sai ma qara tunzura su da yake, suna jin zafi da qonewar da suke amma ba za su fita ba saboda taurin kai. A hankali tsoron da Sultana take ji ya fara tafiya, matsawa ta yi dan ta zauna, ta taimaka wa Sultan su ci gaba da karatun tare, ta ga Daddyn su na bin ta da wani irin kallo, ya na murmushi, sai dad'i ya kama ta, a zaton ta lafiya ce ta samu, a nannad'en da yake ya fara matsawa kusa da ita, hannu ta kai zata kama nashi hannun, kamar daga sama ta ji an ce, "Kar ki taba shi, tashi daga wajen, Hajiya ku shiga daga ciki, ku bar mu, da izinin Allah, Allah zai bashi lafiya" Sultana ta so yin gardama, amma ta tashi ba dan ta so ba, wani ihu gwamna ya saki, ya na fadin, "Za mu sha jiniii, za mu sha jiniii jinin d'an tayii ! Za mu sha jiniiin d'an tayin can !" Kallon su gaba daya ya koma kan Sultana da ke kallon hannun gwamna Halliru, wanda ya daga yatsan shi manuni, ya na nuna cikin ta, da sauri ta kama cikin ta ta na shafawa, cike da tsoro Hajiya Ikee ta ja ta jikin ta ta rungume, nan da nan kuwa suka bar wajen, Malamin da ya yi alqawarin zuwa ne, ya kunce jakar da ya zo da ita, ya daukko wani ruwan da ya yi wa addu'a, ya dauko wasu mayuka na korar shaidanun aljanu, shafawa Gwamna su ya yi, sannan ya fara karatu shima ya na watsa masa wannan ruwan. Azaba ta yi azaba, gumurzu ya yi gumurzu, Gwamna ya gaji da tumurmusa shi da suke yi, amma ba shi da ikon hanawa, a can cikin ran shi ya yi dana sanin fara siyasa, ya yi dana sanin sanyawa zuciyar shi son abun duniya, amma ba shi da damar hana duk abinda ke faruwa, a can qasan ran nashi ya ke addu'a, Allah ya dau ran shi ya huta, hawaye ne ke gangare masa, ya na bin Sultan da kallo, malamin ne ya ke magana, dan yanda ya ga jikin shi ya saki, da alama sun jigata kwarai,sun qoqqone, shi ya sa jikin su ya saki. "Ran ka shi dade, Ranka shi dade Halliru," "Ba za mu tab'a rabuwa da shi ba, sai dai ku kashe mu tare da shi," "Haka kun ka ce? To kuwa za mu yi addu'a Allah ya dauki rayuwar ku, ku ku mace ku bar shi" "Allah ma ba zai bar mutum kamar Halliru ya ci gaba da rayuwa a doron qasa ba, ka kuwa san wane ne Halliru? Ka san me ya aikata a doron qasa? Ka na da la...." "Ba na son sanin wane ne shi, ina roqon ku ta girma da azziqi, ku rabu da shi, kahin Allah ya ci gaba da qona ku,ta sanadin ayoyin shi da muke karantawa, don kuwa duk mun ka fara ba mu bari sai kun mace, maqiya Allah" "Sai dai ka kashe mu, amma ba inda za mu, kuma sai mun sha jini, dan lokacin da yake bamu jini ya gota" Sultan ne ya miqe cikin tashin hankali ya ce, "Malam jinin shi suke zuqa, in suka sha jinin shi yanzu ba wanda za a qara masa zai iya rasa ran shi" Kallon shi sosai Malam Ya yi, ya kalli gwamna da ya fara shure shure, qafafun shi na miqewa daga nannadewar da ya yi. Sultan ne ya ta fi da gudu ya na qoqarin rungume gwamna Halliru, Malam kuwa na ci gaba da karatun Alqur'ani, tare da yarfa masa ruwan da aka yi wa ayoyin ruqya, jikin gwamna Halliru sai makyarkyata yake, ya na jijjiga da qarfi, jini ne ya fara fita ta hancin shi, idanun shi sun kada sun yi jawur. Hankalin Sultan ya gama kaiwa qololuwa wajen tashi, "Daddyyy, Daddy, kalle ni, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, ya Allah ka kawo mana agaji, Daddyyy ! Daddyy Please open ur eyes, Dad.." A hankali jikin gwamna ya sake, kan shi ya fad'a qirjin Sultan, wani irin kuka mai cin rai Sultan ya sake,ya jima ya na kukan kamar zai shide Malam kuwa samun waje ya yi ya zauna ya na ta tasbihi ga Allah, duk abinda Allah ya yi shi ne daidai. Kukan Sultan ya yi yawa, ta yanda har sama su Hajiya Ikee na jiyowa, a tare suka sauka qasa ita da Sultana, ganin abinda ke faruwa ne ya sanya Hajiya yanke jiki za ta fadi, Sultana ta taro ta, tare da cewa, "Hajiya mu godewa Allah, tunda ya samu kwana, (bacci) mu isa, sannun ku Malam, Allah shi bada lada, mun gode,Yah Sultan ba kuka za ka yi ba, mu godewa Allah, tunda ya samu bacci , yanzu Mom ke fad'an ba su kwana, mu tai mu yi sallah mangariba ta yi" Da qarfi Sultan ya ce, "Wai ke ba ki da idanu ne? Daddy is gone, he is dead, ya mutu, ya rasu," Idanun ta ne suka cika da hawaye, ta fara kada kai, ta na so ta yi dariya, ta na kuma so ta yi kuka, "Wasa ka ke yi ko? Daddy ba zai mutu ba, daddy bai mutu ba" Da gudu ta sake Hajiya Ikee ta qarasa faduwa hannun kujera ta yi kan mahaifin nasu, da ya sake jiki, a jikin Sultan, jijjiga shi ta fara ta na kiran sunan shi, cike da kidimewa, gaba daya yau ilimin su, da tunanin su ya gushe (Allah kar ka gusar mana da hankalin mu, a lokacin da muke da tsananin buqatar shi, Allah kar ka sa mu aikata abu da jahilci a lokacin da muke tsananin buqatar aiki da ilimi) wani irin kuka Sultana take mai tsananin ban tausayi, tare da surutan da basu kamata ba ace musulmi na gari ya na furta su, a lokacin da ya yi rashin wani nashi . Mutuwar ta gigita kowa, Malam dai tun da ya zauna ya ke kallon kowannen su, tausayin su ya cika masa zuciya, ya san a wannan yanayin da suke ciki, wa'azi ko nasihar ma ba za su ji ba, a hankali ya fara furta "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un," Tun ya na yi a hankali har ya fara da qarfi, sai a wannan lokacin ne hankalin su ya fara dawowa jikin su, suka fara furtawa su ma, su na kuka su na maimaita wa. Cikin qanqanin lokaci Sultan ya fara waya, ya na sanar da dangin mahaifin nashi na nesa da na kusa, har da dangin Hajiya Ikee, hankalin shi bai kawo ba ya kira Lawwali ya sanar da shi. Har sai da aka wanke Gwamna Halliru, aka kai shi makwancin shi na gaskiya a wannan lokacin, sai bayan sun dawo ne ya tuna ya kira Lawwali, wanda ya ke ta gyaran gidan su dake nan unguwar. Lawwali ya shiga rudani, da tashin hankali jin mutuwar uban gidan nashi, tunawa ya yi da cewar, kafin magariba ya wuce ta qofar gidan  kafin ya isa nasu, bai ga kowa a gate ba, har ya ke tunanin yanda rayuwa ta koma, ace gidan Gwamna Halliru ne shiru a bushe ba mutane. Bayan ya katse wayar cikin sauri ya sanya kayan shi, ya yi alwala ya yi sallahr Isha'i, ya na idarwa ya fita dan zuwa gidan, mota ya dauka dan ya na so ya yi saurin isa. Tafe yake ya na ta tunanin rayuwa, ya na kukan baqin cikin irin rayuwar da ya kasance ya na aikatawa a baya........ *Yau ba appetite ɗin rubutu,amma a haka na cije na daure na ci gaba, sai gobe inshaa Allah kuma* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 61: Ya na daf da isa gidan, ya ga wata mata zaune a jikin ginin da aka saka street light, da dan qunshin buhu a gaban ta, sai sandar ta da ta jingine a jikin jakar ta, ta rufu da mayafi, da alama anan take da shirin kwana,duk yanda akai ba ta san a wace unguwa take ba, domin a iya sanin shi, wannan unguwar tuni wani zai ciki da ita, a yi wani sihirin da ita, dan neman abun duniya. Yi ya yi kamar zai tsaya, ya taimaka mata, kawai ya yi gaba, dan ya san yanayin yanda rayuwar ta koma, su kan su, sun sha haɗawa mutane trap da mabarata. Bai tsaya a ko ina ba sai a bakin gate din gidan su Sultan,mutane ne danqam a wajen gidan, kamar da rana, da kyar ya samu shiga ciki, har da 'yan jarida, da sabon gwamna mai ci,da muqrraban shi. Lawwali gaisuwa ya dinga miqawa mutanen da ya tarar, tare da ta'aziyya, wasu na yi mishi ta'aziyyar shi ma, kasancewar shi surukin gidan. Sai da wajen ya d'an lafa ne, Sultan ya raka Lawwali ciki, nan ya samu Sultana a yanayin da ya kasa jurewa sai da kwalla ta taru masa a idanun shi, matan wajen na ganin haka suka firfita, aka basu waje, a hankali ya isa gefen ta ya zauna,cikin murya mai sanyi ya ce, "Sultyna, ki yi hakuri, mu yi hakuri gaba daya, mu yi ta yi wa Daddy addu'a, dan ko ita ce kad'ai ya ke  bid'a wajen mu, kuka ba zai dawo da shi ba, ki yi hankuri kin ji, jarumar mata ta" A hankali ta ja jikin ta, ta kwantar a nashi, cikin kuka ta ce, "Ba ina kukan rabuwa da shi bane, dan na san komai daren dad'ewa sai mun rabu,ina kuka ne akan tunanin Daddy bai samu ya furta kowacce kalma da ake saka ran Allah zai yahe masa ba,na tabbata sai ya sha azaba a lahira, saboda abinda ya kasance ya na aikatawa" Da sauri ya sanya dogon yatsan shi a labban ta, ya ce, "Kar ki ce haka, kin mance da me kike fadi min kullum, ba a shiga tsakanin bawa da ubangijin shi, in mutum ya yi shisshigi tsakanin bawa da ubangijin shi, shi sai Allah ya hana mishi rahamar sa, ya yi wa wanda ya ke wa zaton Allah ba zai duba da idon rahama ba rahamar " A hankali ta fara jin wani sanyi a ran ta, "Haka ne, yanzu ba abinda ya mana saura da ya wuce mu yi ta masa addu'a" "Allah ya jiqan shi, ya gafarta mishi, na yahe mishi duk abinda ya yi min a rayuwa ta, ni ma ina fata ALLAH shi yahe min" Wani irin dad'i ne ya kama Sultana, ta qara kwantawa a jikin shi ta na murmushi, "Na gode miji na, na gode, Allah ya amsa addu'ar ka,....ina Mubaraka?" "Dazu da mun ka hito gaba daya, mun yi wa daji bankwana, bankwana na har abada da yardar Allah, sai nace zan kawo ta nan wajen mu ta zauna ta ce ah ah, na kai ta gida, to ban san an yi rasuwa ba sai d'azu" "Allah Sarki, ai da ta zo mun zauna, gidan ai da girma ba laihi, " "Ke San ta da son su Lamishi,ba ta tahowa wajen mu yanzu, ban qi ba in ta gaji da zama wajen su,amma ke san mi ya faru?" "Sai ka hwadi," "Da na je gida, na ga sauyi sosai wajen Baban mu,na tarar ya na yin rumfa, ban san mi ya ka son yi ba, mun gaisa cikin wani irin yanayi da ban san ya zan kira shi ba,ba wannan rawar kan kamar zai min kwacen kuddi, ita kan ta Lamishi haka, duk sun yi wani iri, har da yi wa Barakana oyoyo" "Alhamdu lilLAAH, Allah ya qara kawo mana zaman lafiya, da shiriya," "Ameen Allah ya jiqan Daddy," Ta ji dad'in yanda Lawwalin ke ta masa addu'a ko ba komai, hakan ya nuna ba wani riqo a tsakanin su. "Kin ci abinci kuwa?" "Ahh ahh, gashi can, an kawo mana ni da Hajiya, mun kasa ci,amma yanzu da ka yi magana, na ji ina jin yunwa, ba zan iya ci bane kawai, baki na ba dad'i" "Ayyaa dear, haka zaki daure ki ci, kin jiya?" Tashi ya yi, da kan shi ya haɗa mata tea, ya bata, ta shanye tass,ya bata abinci kadan, ta ci, ta masa godiya, sannan ya mata sallama,ya leqa dakin da Hajiya Ikee da qawayen ta ke zaune, ya musu ta'aziyya. Abun da ya gani ya bashi takaici, ba dan ace ya shiryu ba, da in ya buga wa wata mata da ta kafe shi da ido tsawa, sai ta rasa ina zata ta buya dan tsoro. Tsaki ya yi a daidai saitin matar da zai fita, ta na zaune kamar wadda ta zo biki, ko ina gwala-gwalai ne,ga wata arniyar shadda ta zuba sai maiqo take. Ta kunna snap chat kamar wata yarinya, ta na zaro harshe, ta na mayarwa, ya na shiga ta kafe shi da Mayun idanun ta, inda yake a tsugunne ta miqar da qafar ta sai da ta taɓa tashi,kallon da ya mata ne ya sanya ta janye wa da sauri ta na yaqe,ita a dole ba da niyya ta yi ba. An zo gidan rasuwa amma wasu rasuwar bata dame su ba ma, wasu kuwa sun sanya hijabi,an riqe carbi, amma ba abinda suke sai hira. A haka ya fita ya na takaicin yanda gidan rasuwa ya ke komawa kamar na biki, a wannan zamani. Bai sake komawa wajen Sultana ba, gaisawa suka sake yi da su Sultan, ya tafi gida. Sai sha d'aya na dare wasu mutanen suka dinga tafiya. Sai da Hajiya Ikee ta zo bacci hankalin ta ya sake tashi, ita kuka Sultana kuka, ba mai lallashin wani,tabbas ba su taba zaton sun shaqu da shi har haka ba sai yanzu, ko ba komai shi din uba ne mai kulawa, ko sun ci, ko basu ci ba, ko suna da wata damuwa, ko basu da ita, shin farin cikin fuskar su ya ishe shi? Ko ya na so su fi haka farin ciki? Har safiya Sultana bata rintsa ba, ta na kan sallaya, ga yunwa ta na ji, ta kasa cin komai. Hajiya kuwa ba zata iya tuna sanda ta saka ko da ruwa bane a bakin ta. Tausayin Hajiyar ne ya sa ta miqe da kyar, marar ta na murdawa, ta nufi hanyar parlour, za ta hado mata tea, wani irin jiri ne ya ɗebe ta, ta kusan faduwa, daddafe jikin bango ta yi, Hajiya Ikee da sauri ta isa wajen ta,cikin kuka ta ce, "Dan Allah samu waje ki zauna, ko me ki ke so za a miki,dan Allah kar ki sa wa kan ki damuwa ke ma na rasa ki, ba zan iya daukan rashin ku ba," Kuka Hajiya Ikee ke yi sosai, Sultana kasa bata hakuri ta yi, sai da wasu 'yan uwan Hajiyan suka sa baki, sannan ta rage kukan. Zama suka koma suka yi,tace a hadowa Hajiya Tea, da kyar aka tursasa ta ta sha, jin shi ta yi kamar mad'aci, amma haka ta daure ta sha. A haka, a haka dai har sai da akai sadakar bakwai,sannan mutane suka tattafi gidajen su, dan yanda suka saba in sun zo a ci a sha a raqashe da kaji babu, duk da ana kawo na sadaka, amma ba kamar da gwamna na da rai ba. ******************* A kwana na goma sha biyu, Lawwali ya je gidan Gwamna,dan gaishe da Hajiya, yanzu ya na bata girma sosai, saboda tausayi take bashi. Ya na nan duqe gaban ta, ta na ta bashi labaran yanda tsohon gwamnan yake kyautatawa iyalan shi, da yanda ya ke matuqar son su, su Lamishi suka yi sallama, amsawa Hajiya Ikee ta yi, cikin d'an sakin fuska . Zama su Lamishi za su yi a qasa, da sauri Hajiya Ikee ta ce, "Dan Allah ku tashi daga qasa, rayuwar ga duk labari ce watarana, dan Allah mu yahe wa juna, abubuwan da sun ka hwaru a baya," "Allah Sarki Hajiya komi ya wuce, ya hankuri?" "Alhamdu lilLAAHi," "Allah shi jiqan gwauna, shi mai rahama, Allah shi gafarta mai" "Ameen Allah shi bada lada" Mai Buruji, Mubaraka, duk sai da suma su ka bada gaisuwar su wajen Hajiya,da Sultana. Sultana ce da ta fito daga ciki, ta je yin alwala, ta ga su Lamishi, da sauri ta je ta durqusa gaban su, suka gaisa, suka mata ta'aziyya, Mubaraka ce ta zauna kusa da ita, ta na sake mata ta'aziyya, "Ameeen na gode, amma dai nan za a bar ki ko? Sai an yi arba'in" Kallon Lamishi ta yi, ta na neman izini, da ido,daga baya ta maida duban ta wajen oga Lawwali, ta dire shi akan Sultan,da ya kafe ta da ido ya na jiran jin amsar ta, kowa ya yi Mamakin yanda Lamishi ta yi sanyi, ta koma kamar ba ita ba, "Ki zauna, ba ya da komi, ai duk ɗaya ne" A tare Mubaraka da Sultana suka ce "Na/na gode Ummaa" Wani qayataccen murmushi ne ya bayyana a fuskar Lawwali, miqewa ya yi, ya ce in sun gama su masa magana, zai maida su gida Duk wani motsin Mubaraka na kan idon Sultan, duk ya sa ta ta kasa sakewa, qarshe sai da suka hau sama yin Sallah, sannan ta samu ta ji kamar an zare mata wani abu da ya takura walwalar ta. Sun kai kimanin awa guda,kafin Baraka ta raka su waje. A bakin motar shi ya tsaya, ya na jiran su, da kan shi ya budewa Lamishi mota, ta shiga, ta na mai jin dadi, da da suke tsananin maitar mota ma ko kusa da ita ya hana su zuwa, amma yanzu gashi shi ke bude musu su zauna. Sallama suka yi da Mubaraka, ya ce zai debo mata kayan ta, in ya kai su Lamishi, nan ta fara shagwaba, ita Umman ta ne za ta debar mata kayan, ta yi ajiya ba ta so ya gani, yafitar ta yayi, ta kai kunnen ta saitin bakin shi, "Na hwa san mi ki ke boye min, yo ni ma mata ta ta na da su, ko d'azu a gida sai da na wanke mata su, mi na na acciki to dan na gani, ni ne fa Yah Auwal d'in ki" Dariya take son ta yi amma dole ta daure, dan ko ba komai gidan rasuwa suke Shi kuwa fita ya yi da mota ya na dariya,. Lamishi kuwa cikin ran ta, ta na jin wani irin dad'i na ratsa ta, a baya haushi take ji, ta ga Lawwali na fifita Mubaraka akan su, amma yanzu sai ta gane hakan ba wata matsala bace da zata sa ta dinga jin haushi, hakan na nuna su din su na son junan su, da bawa juna kulawa. Bayan sun Isah gidan, ya sha mamakin ganin Icce da gawayi buhu uku, a aje a rumfar da Dan Talo ke ta yi da kan shi, juyawa Lawwali ya yi bayan motar ya ce ma su Lamishi, "Wa ka sai da ic-ce a unguwar  nan?" "Baban ku ne, ya ce yanzu in shaa Allahu ba zai sake zaman banza ba,da kuddin da ka bamu, ya samu ya siyo komai da shika bid'a, abokan shi  na masa dariya, shi ko ko a jikin shi, sai da ya qare ya siyo motar icce guda an ka juye mai, ya sa gawaiyi, har da barahuni (kananzir)yaka sayarwa" "Ikon Allah" Daga haka bai qara magana ba, fuskar shi dauke da murmushi ya qarasa rumfar. Sallama suka wa juna, Dan Talo ya dinga neman afuwa da gafarar Lawwali, ya ce ya nemi gafarar sauran yaran shi, ya kuma yi alqawarin zai zama uba na gari "Allah shi bada iko baba, ni ma ka yahe ni, in shaa Allahu, sana'ar ga sai tayi albarka, yanzu mi ka ke buqata a qaro?" "Babu komi, in ma akwai ina da kud-din siye, yafe min da ka yi ma ya ishe ni, ban san cin iyali na ba, ban san shan su ba, ban san suturar su ba, balle wajen kwanan su, ba su da lahiya, ko su na cikin b'acin rai, da quncin rayuwa duk ban sani ba, a da ji na nikai kamar wanda an ka d'ebewa tunani,amma yanzu hankali na ya dawo jiki na, na san fari na san baqi yanzu, da yardar Allah sai iyali na sun yi farin ciki da ni kamar yadda kowanne iyali ke jin dad'in mai gidan su" Lawwali ya kasa cewa komai, sai murmushin jin dad'i kawai ya ke zubawa, nan ya zauna su ka yi ta hira da mahaifin shi, daga qarshe shi ma ya yanke shawarar Kano zai dinga zuwa ya na kasuwanci, duk qarshen wata ya na dawowa. ************************ Zaman mubaraka da su sultana ya sa sun rage kewa kadan, dan kuwa, tare suke haduwa, da Sultanan su yi ta karanta qur'ani, Hajiya Ikee ba a iya karatu ba, ita daga qulhuwallahu sai Fateeha su ma a sallah take yin su, da mutum zai saurara zai rantse da Allah Yaren mutan China take ba larabci ba, rayuwar ta kafff ta qare ta ne wajen neman duniya, amma harafin alif da baa na mata wuyar haɗawa, balle ta kai ga karanta qur'anin sukutum. Mubaraka ta kula da hakan, dan haka ta qudirta a ranta, za ta taimaka wa Hajiya, dan ganin ta samu tagomashin alkhairi da ladan da ake samu, wajen karanta littafin Allah. A hankali kuwa Hajiyan ta fuskanci me Mubarakan ke so ta yi,da sauri ta ajiye girman kan ta, ta na koya, Mubaraka ta yi amfani da koyar da Hajiya ta na rage mata kewa, da yawan tunani. Da ta gilma ta gan ta tana kuka, ko tunani, za ta ce, "Hajiya, in an had'a, ba'un da fataha, da mimun da fataha, me zai baki?" Sai ta yi shiruuuu ta na nazari, can sai ta washe baki ta ce, "Bama" "Yeeehhh Hajiya za ta ci Bama" "Yannema ni dai a dinga  yi min kad'an kad'an, kar karatun ga shi yi min yawa, in taho banni gane komi" "Ganewa ki kai inshaa Allahu, kahin Ramadan mai zuwa ke zaki zanka ja wa Aunty Sultana baqi, ita kau ta na fassarawa,tafsirin cikin gida za mu yi" Dariya sosai suke yi, in Mubaraka na musu irin wannan barkwancin. Sultan kuwa da ya gan ta zaune da su Hajiya, shi ba ta masa hira kamar ta su Hajiya, sai ya yi ta bata rai,ya na wani abu kamar qaramin yaro, ya na sane sai ya zubar da ruwa, ko tea, ko ya b'ata waje,ya kwala mata kira, Ita kuwa ta gane me yake nufi, ba ta kula shi, sai dai ta je ta gyara wajen, fuskar ta dauke da Murmushi, kallon ta zai ta yi, kamar ya samu TV, da ya ga za ta tafi, zai qara yin wata barnar,dan kawai ta tsaya. Watarana suna can sama su na hira, Hajiya na basu labarin yanda ta hadu da Daddy, har suka yi aure. Sultan ya zubar da tea, ya kwalawa Mubaraka kira, tare da sanar da ita ta je da abun gogewa. Har za ta miqe Hajiya ta ce, "Zauna, baki zuwa, ni bari na je, na goge masa, in ba ze zo ya ce  Hajiya aramin ita ni ma muyi hira ba,ba ki zuwa yi mai aiki, danneman rainin wayo kai, ya zaci ban gane komi ba, tunda takkwala na ke, na hi kowa qaramar kwanya gidan ga" (Tunda daqiqiya ce ni na fi kowa karamar ƙwaƙwalwa a gidan nan) Da kan ta ta shiga dakin na shi, Sultan an sha wanka da wata shadda da akai wa d'inkin half jumpa, kan shi ba hula, sai qamshi yake zubawa, ya na tsaye jikin TV, ya na rage volume Hajiya ta shiga, ba tare da ya juya baya ba, ya fara magana, "Mubaraka, ki yi hankuri da aikin da ni ke saka ki, ta haka ne kawai zan gan ki, dan na kula yanzu ke hi son su Hajiya akai na, jiya Daddy ya cika kwana arba'in da rasuwa, ina fatan nan da wasu kwanaki mu bayyana wa h......" Maganar shi ce ta maqale da ya juya suka yi ido hudu da Hajiya, fuskar ta ba wani emotion a jiki, ji ya yi gaban shi ya yanke ya fad'i, dube dube ya fara yi, ya na neman Mubaraka, bai gan ta ba, "Ha...haaajiya Mum, inaa Mubaraka?" "Dama kenan ta san ka na son ta?" Yanayin yanda ta yi maganar ya so ya bashi tsoro, cikin zuciyar shi ya fara tsoron kar dai Hajiya har yanzu ba ta dena qin jinin talaka ba? Bai san ya zai da rayuwar shi ba in ta ce ba zai auri mubaraka ba. Juya baya ta yi, Sultan na nan tsaye ya kasa magana, saboda rashin sanin me ne ne a zuciyar Hajiya Ikee game da zabin shi.......... 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 62: "Dan Allah Hajiya kar ki qi wannan auren, Mubaraka alkhairi ce a gare mu baki d'aya in shaa Allahu, ban ga wata mace da zan iya aura na ji dad'in rayuwa ta ba sama da ita,Kuma na ga yanzu ki na son ta, ko?" A hankali Hajiya Ikee ta samu waje ta zauna, idanun ta sun sauya kala, daga farare tass zuwa jajaye, saboda hawayen da ke barazanar sauka mata, hancin ta ta ja, sannan ta dora idanun ga a saman fuskar Sultan, da ke a tsugunne a gaban ta, kamar me neman gafara, ya na jiran ya jin kalar hukuncin da za ta yanke. "Wato Sultan na koyi darrussan rayuwa a qarshen shekarar ga, ba kadan ba, na koyi abubuwa kala kala, ciki ko har da sanin darajar Dan Adam, a baya ba kalar wulaqancin da ban yi wa iyayen yarinyar ga ba, da ita kan ta, amma ka diba ka gani, a yanzu ita ka qoqarin kwantar muna da hankali, saboda halin damuwar da muke ciki,ita ke qoqarin ganin na san wane ne mahalicci na, na shekara d'ai d'ai har shamshin da shidda amma ban iya karanta qur'ani ba na bata rayuwa ta a banza ban san wanene ubangiji na ba, ban taɓa karanta kalma ɗaya ta alqur'ani ba tsabar rashin rabo, boko kuwa ko da baturiyar qasar Amurka sai mun buga, ka diba ka gani, a wata d'aya yarinyar ga ta hwara sawa ina iya karanta wasu kalmomi na larabci, na qara yarda da cewa, kyawun huska, ko wani kyau na halitta, ba shi kad'ai ne  kyau ba, kyau shi na cikin kyakkyawan hali da d'abi'a, wanda ya rasa su, komai kyawun huska shi mummuna ne, ina goyon bayan auren ku, dubu bisa dubu ma Sultan, Mubaraka ita ce ta hi dacewa da rayuwar mu baki daya,Allah shi yi muku albarka" Hannun Hajiya Ikee Sultan ya riqe a nashi gam gam, sannan ya sumbace su, cike da murna, ya dinga godiya,a haka su Sultana suka tadda su, Mubaraka kuwa tun da ta ji Hajiya na yabon ta taso guduwa, amma Sultana ta riqe ta, sai da suka gama, magana sannan Sultanan tai gyaran murya, ta ce, "Mu shigo an bamu izini? Kar ku ce mun yi maku labe, mun ji shiru ne shi na mun ka taho mu ji ko lahiya?" "Ku shigo, 'yan sa ido, kun dai taho ku ji mi muka fadi, to kun dai jiya, Hajiya ta amince na auri B love di na" "Tauuuu mi na na kuma B love?" "Sultana ba kyau sa ido, ba ruwan ki, ni kadai na san me na ke nufi da hakan,kalla yadda Mubaraka kanta ta baza kunne ta na so ta ji ma'anar B love, ban fad'i to, yarinya rufe kunnuwan," Cikin jin kunya ta sa hannayen ta ta rufe fuskar ta, tabbas kuwa ta tsaya ne ta ji me ye ma'anar B love din, kuma ya gano ta. Juyawa ta yi da sauri za ta fita ta ji ya kira sunan ta, da wata iriyar Muryar da ta sanya ta tsayawa cak ba tare da ta shirya ba, daga Hajiya har Sultana ba wanda ya qara magana, dan su ma za su so jin me Sultan zai fadi da mahimmanci haka, har da sauya murya. Takawa ya yi zuwa gaban ta, ya tsaya, kallon idon ta yake so ya yi amma ta maida kan ta qasa, kunyar Hajiya take ji, amma ta kula su ba ruwan su, "Kalle ni Mubaraka," Da kyar ta d'aga kai ta kalle shi, idanun su na haduwa da na juna, ta ji kamar an kafe nata, kasa kauda kan ta tayi daga barin kallon shi, "Mubaraka za ki aure ni? Za ki taimake ni ki tausaya wa Maraya Sultan ki aure shi? Ki sani ba ni da dukiya, ba ni da aikin yi, amma ina tare da dimbin soyayyar ki, wadda na ke jin ta ishe ni qarfin guiwar zama komai da na ke so na zama a rayuwa, da izinin Allah, so Mubaraka za ki aure ni?" Wasu irin hawayen farin ciki ke mata gudu a kunci sai qaiqayi suke mata, gashi ta kasa daga hannu ta sosa kuncin nata, jikin ta ya mace murus, yau wai ita namiji had'add'e kamar Sultan ke neman aure ta wannan sigar? A gaban mahaifiyar shi, da qanwar shi, ita d'in wace ce? D'iyar tallaka, qanwar tallaka,sannan ita kan ta bata mallaki komai ba, ita ba wani kyau na a zo a taru a sha kallo ba, Sultan ya fita komai, kyawun shi ma abin kallo ne, kyawun shi ma kyakkyawa ne, ga kyawun hali, da d'abi'a, anya bai fi qarfin ta ba, ta sani ba wani namiji da take wa so irin na soyayya bayan shi, amma a yau sai ta ji gaba daya bata cancanci zama matar shi ba. Cikin murya mai cike da rawa, ta ce, "Yah Sultan ka dai san kai ba sa'an aure na bane ko? Ka hi ni komi da komi a rayuwa, ba...." Sultana ce ta katse ta, ta hanyar sanya hannu ta share mata hawayen ta, sannan ta ɗan ja kumatun ta, ta ce, "Kar na ji kalmar rejection ta fito a bakin ki, zan qi komawa gidan Yayan ki, Hajiya mu basu waje, wataqila kunyar ki taka ji, ke ko kin zauna dirshan ki na kallon su awa ke samu TV" Dariya sosai Sultan da Mubaraka suke, Mubaraka na dariya hawaye na qara saukar mata, yau rana ce mai cike da farin ciki a wajen ta, ina ma ace Yah Auwal na nan, yaji yanda Namiji kamar Sultan ke bayyana mata ra'ayin shi akan ta. Bayan fitar su Hajiya Sultan ya sake roqon Mubaraka, akan ta amince da auren shi, dan tura baki ta yi, cikin shagwaba ta ce, "Ni dai ka dena roqo na haka, dan kuwa ba ni da wani abun baka,mutum guda na zai iya baka amsa, shin zan iya auren ka ko ban iya wa," "Ni dai dan Allah kar ki had'a ni da Auwal" Cike da dariya Mubaraka ta ce, "Ashe ma ba ka so ka aure ni, wajen shi za ka je wallah, in yace shi na baka niii, to zan aure ka, in yace ba zai..." "Ya isa haka nan, zan je wajen shi,kuma na tabbata, in da zan je da sadaki na a lokacin zai aura maki ni, " "Me zai hana ka tai da sadakin gaba ɗaya, domin na mallake ka a matsayin miji na cikin gaggawa" Yanayin yanda ta yi maganar ya kawar masa da komai, na tunanin ko dai bata yi da shi,zuciya bata da qashi, dan har ya fara tunanin ko Taheer take so, sai ya ji kalamai masu ɗauke da gaskiyar abinda ke zuciyar ta. Cikin jin kunya ta bar dakin nashi, shi kuma ya bi ta har bakin qofa ya na murmushi, har ta sauka qasa gaba daya bai bar wajen ba, ya na nan tsaye ya na murmishi. Sultan kuwa bai bata lokaci ba, da daddare ya sha wankan shi, da manyan kaya, ya nufi gidan Lawwali, ya tarar da shi ya na waya da Sultana, sallama ya mata, ya ce zai sake kira ya yi baqo. Sai da suka gaisa, Lawwali ya sake yi masa ta'aziyya, sannan Sultan ya kalli gidan, ya ga yanda Lawwali ya qayata shi, ya gyara shi, kamar gidan sabuwar amarya. "Lallai ka na ji da matar ga taka, irin wanga gyara kamar za a kawo maka sabuwar amarya? " "Ka gyara kalaman ka, dan kuwa Sultana sunan ta kin fi amarya" Sultan kuwa langwabe kai ya yi, ya yi kalar tausayi, sanan ya ce, "Allah Sarki,mu gamu mu na son a bamu tamu amaryar amma ba wanda ya damu da halin da muke ciki, har yanzu an kasa gane mun isa aure, a aurar da mu, sai mun aje kunya a gehe mun roqa a muna aure" Lawwali me zai yi in ba dariya ba, shi ma Sultan d'in dariya ya dinga yi, cikin dariya Lawwali ya ce, "Yanzu dai ka ce aure ku ke so, kuma maganar neman aure ta kawo ka ko?" Gyara zama Sultan ya yi ya ce, "Gaskiyar kenan, ni na rasa iyakar son da Mubaraka ke yi ma, wai na yi na yi ta amsa min buqatar auren ta da na je mata da shi,ta ce sam sai ka amince" Murmushin jin dadi Lawwali ya yi, sannan ya ce, "Indai ni ne na amince, na baka goyon baya ka ci gaba da saye zuciyar qauna ta, har sai ta amince ba wani namiji sama da kai a rayuwar ta," "Tabdijam, ka dai ce ba wani namiji da zata so da aure sama da ni, amma har duniya ta tashi kaine namijin farko kuma na qarshe da take so, na gode sosai da amincewar ka" Nan dai suka yi ta hira, Lawwali na bashi labarai akan Mubaraka, abinda take so da wanda bata so, har qaddarar da ta fad'a mata tsakanin ta da No 1,Sultan ya tabbatar masa da cewa, ba namijin da ya dace ya auri Mubaraka sama da shi, ta sanadin Daddyn su haka ta faru, dan haka shi ke da alhakin auren ta, ko da ace ma ba ta sanadin Daddyn su bane, shi dai ya ji ya kuma gani ya na son ta a duk yanda take, ita yake so ba jikin ta ba,shi ma Sultan haka ya dinga fadawa Lawwali abubuwa akan sultana, daga qarshe Lawwali ya kira Mubaraka, ya fada mata amincewar shi, cikin jin kunya ta yi masa godiya. Lawwali ya bawa Sultan shawara, akan ya tura magabatan shi wajen Baban su, a da ya so shi zai aurar da ita da kan shi,amma ganin mahaifin su na nan da rai, kuma shiriya ta zo masa, ya yi nazari shi ya fi cancanta da ya aurar da diyar shi, sai dai in ya wakilta shi,zai so hakan. Sallama Sultan ya yi wa Lawwali ya tafi gida. Ko da ya isa duk sun yi bacci, abinci ya ci, ya je ya kwanta shima, cike da tunanin yanda zai mallaki  masoyiyar shi Mubaraka. ************************* Su Yayah Musah sun sha wahala kwarai kafin Isah ya hakura ya rubuta wa Hansatu saki,dan sai da suka had'a da barazanar za su had'a shi da hukumar qasar, a sanar da duk abinda ya aikata wa matar shi, ya tsorata kwarai dan ya san bai aikata daidai ba,gashi Saudiya ba sa wasa da jinkiri wajen yanke hukunci, Isah na kuka har da majina, ya rubuta wa Hansatu saki d'aya. A satin suka juyo gida Nigeria Yayah Abdullah murna a qasan ran shi kamar me, amma a fuska ya dinga jimamin lamarin, ya na jaddada rashin adalcin da Isah ya aikata wa Hansatu. Ko da suka iso gida, Hajiya ta yi farin ciki da samun nasarar raba Hansatun ta da azzalumi Isah, Hansatu kuwa yaqe ta dinga yi, ko ba komai akwai sabo, kuma shi ne uban yaran ta. Da dare sai da ta ci kuka ta godewa Allah, ta na tsaka da kukan ne ta ga wayar ta ta yi haske, ko da ta duba sai ta ga baquwar lamba, sallama ne kawai sai gaisuwa, da jajanta mata abinda ya faru da ita, mamaki ne ya kama ta, bayan ita da mutan gidan su wa ya san meke faruwa da ita? Lallai lamarin duniyar nan abun tsoro ne labari har ya baza gari. Ba tare da ta amsa gaisuwar ba ta ajiye wayar, koma waye, ta ji da safe, yanzu dare ya yi. Tunda Isah ya sawwake wa Hansatu auren wahalar da ta ke fuskanta, duk ta rame, ta zama wata kamar mara lafiya, a so samun ta, ya gyara halayen shi, su ci gaba da zama hakan, sai dai kashhh sanin abubuwan da ya aikata sun ja mishi rabuwa da ita, ba dan an ce sabo turken wawa ba ma, da ko tunanin shi ba zata yi ba, amma ta saba da shi, da halayyar shi, da kuma son shi, su ke wahalar da ita, kafin ta saba da rashin shi zata dau lokaci, wanda bata fatan hakan. ************************ Yau Mubaraka ke so ta koma gidan su, Sultana da Sultan sai lallaba ta suke akan ta yi zaman ta,ta qi sam,ta ce ya kamata taje  ta ga halin da iyayen ta ke ciki, mussamman tunda ta jima ba ta gidan . Hajiya Ikee ta yi ta mata godiya, da za ta tafi ta rasa me zata bawa Mubaraka, Mubaraka ta fahimci hakan, dan haka ta cewa Hajiya,ta sa mata albarka kawai, ya ishe ta, shi ne babban kyautar da ta ke so ta mata, albarka kuwa Hajiya ta saka mata, suka raka ta har bakin gate, Lawwali na mota ya na jiran ta. Su na had'a ido da Sultana ya marairaice fuska, shi adole ya na so ta tausaya masa ta koma haka, ba ya so ya furta, tunda ta yi babban rashi, ba zai so a ga rashin hakurin shi ba, bayan Mubaraka ta shiga Mota ne, Hajiya Ikee ta ce, "Allah shi kiyaye, muna godiya,kwarai kwarai, Allah shi yi muku albarka, Auwal in ka kai ta gida, ka biyo ka dauki matar ka ku wuce haka nan, Allah shi bada lada, Allah ya jiqan Daddyn su, rashi dai an riga an yi shi, ba a zauna ba ba tare da an koma zaman aure ba, zaman ya isa haka nan, gani ga Sultan babu komi, da ka Kaita ka dawo ku tahi" "Ni fa ba yanzu zan koma ba" Da sauri Lawwali da ke ta murna ya kalle ta, cike da mamakin yanda ta ke qin komawa qarfi da yaji, ga mamakin shi kuwa sai ya ga su na ta mishi dariya, dama wasa ta ke, "Auuuu zolaya ta ki ke ko? Ke dau bashi wallah" Jan motar shi ya yi, ya bar su nan tsaye su na mi shi dariya, Mubaraka ma dariya take. Kamar yanda Hajiya ta alqawarta kuwa, haka ya je da dare ya dauki Sultana, wadda ta sha gayu kamar amaryar da za a kai dakin miji, sai qamshi take zubawa, ta yi haske,ta ciko sosai, har Lawwali na mamakin qibar da ta yi, ita da take cikin jimamin rashin mahaifin ta. Sultana kuwa ta matsu su je gida ta masa babban albishir. Ko da suka isa gidan,ta yi matuqar farin cikin ganin yanda ya gyara gidan sosai,kamar baquwa haka ya dinga shiga da ita sashe sashe na gidan,ta na gani. A dakin su suka tsaya, ta na tsaye ta na kalle kalle ya dauke ta, qara ta saki saboda matse mata ciki da ya yi, da sauri ya ajiye ta, cike da shagwaba ta kai masa dukan wasa a qirji, ya tare hannun ta, ya na bata hakuri, "Ko dake ni za ki bawa hankuri, kin ji baya na, awa zai qalle, ke yi nauyi yanzu mi ki ke ci ne haka?" "Ba dole na yi nauyi ba, tunda ka min babbar ajiya," Cikin rashin fahimta ya ce, "Shin ajiyar mi na yi maki kamar wani maye? " Ta na wani irin kyakkyawan murmushi ta kama hannun shi ta ɗora a saman cikin ta, ta na shafawa, tare da cizon leben bakin ta na qasa, "Ga ajiyar nan, ita ta ke sani cin abinci sosai, har na yi qiba," Lawwali wata iriyar zabura ya yi, ya yi baya, ya na toshe bakin shi da hannayen shi dika biyun, murna ce sosai da bata iya boyuwa a saman fuskar shi, Ita kuwa bin shi ta yi ta fada jikin shi,ya kuwa rungume ta ya na sumbatar ta ko ta ina, su nata dariya, a hankali ya kai bakin shi kunnen ta ya ce, "Na gode Sultyna, Allah shi yi miki albarka, da ke da abinda ke cikin ki, Allah ya sauke ki lahiya, ya bani ikon kula da ku, Allah ya raya mana Muhammad, in mace ce kuwa Ayshaa nika so a sanya mata" "Ameen ya Allah miji na, kuma uban yara na,Sunan mahaifan ka ne?" Kama ta yayi, suka zauna a bakin gadon su, ya ci gaba da shafa cikin nata, da in ba an fadi ta na dauke da ciki ba ma, ba mai ganewa, "Ahh Ahh, ina son sunan Muhammad ne saboda ina fatan Allah ya sa ya yi koyi da Annabi Muhammad, in mace ta kuwa, ina so ta yi koyi da Nana A'ishah, domin kuwa yanzu ba ni da abin kalla in na zauna ni kadai ga YouTube sai wa'azi , da duk wani abu da nissan zai amfane ni, anan na ke jin tarihin su," Sultana ta ji dadi matuqa,cikin murmushin da ta kula ya qi barin fuskar shi tun da ya fara maganar Annabin rahama, ta fara kissing din shi, sannan ta ce, "Ya kamata na baka tukuicin amfani da lokacin ka akan abinda ya dace" Juya ta ya yi, ya kwanta a saman ta, ya na kallon cikin idon ta, fuskar su dauke da fara'a ya ce, "Ya kamata na baki tukuicin kular min da ajiyar da na baki, sannan ki karbi hukuncin qin sanar da ni da wuri da baki yi ba" Cizo ya kai mata a wuya, na wasa,daga nan na ga ya fara......sai na gudu, saboda an hana ni sa ayis a gidan mutane..... 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 63 A rumfar Dan Talo ya tsaida motar shi, Lawwali har qasa ya durqusa ya gaida mahaifin shi,cikin jin nauyin haka Dan Talo ya amsa, dan bai saba ba, shi kan shi Lawwalin be saba ba, ganin Mubaraka na yi ne ko da yaushe, ya sanya shi yi a yau. Abokan Dan Talo da ke zaune a rumfar sai mamaki suke, daya bayan daya suka dinga zamewa su na barin wajen,hira suka dan tab'a, Lawwali na tambayar shi yanayin kasuwancin, "Kassuwa dai gata mun godewa Allah, tafi zaman banza, ka ga ana samun na cefane,ga kuma hirar dai ana yi, abukkai na na zuwa kullum muna hirar mu, " "Da kyau, Allah shi taimaka, ai dama shi rai dangin goro ne,ya na bidar damshi," "Haka nan na, ka ga ban samu na koma gidan rasuwar nan ba gashi har an yi arba'in,Allah shi jiqan gwamna" "Ameen, ai ba komi,ga Barakana nan, ta je, ta zauna musu, ai ta wakilce mu dika,barakana shiga gida,gani nan zuwa" Amsawa ta yi da "to" sannan ta shige ta bar su, anan Lawwali ke sanar da Dan Talo abinda ke faruwa tsakanin Mubaraka da Sultan, ya yi farin ciki sosai, sannan ya amince Lawwali ya zama waliyyin ta, Lawwali ya yi ta godiya dan kuwa dama yana son hakan. "Amma fa nan za su zo, tambaya, dan zan so koma me za a yi ya zama an yi shi a nan gidan, nan ne tushen mu, da nan muke taqama," Dan Talo wani irin abu ya ji mai sanyi na kwaranya a zuciyar shi,ba ilimin addini, balle ya godewa Allah akan ni'imar da ya mishi, haka dai ya ke ta jin daɗin shi, a zuciyar shi, har suka gama magana Lawwali ya shiga ciki. Ya tarar da Matar Yahai na ta bada labarin abinda ya faru da mijin Asshibi da Hansatu, sai zaqewa take da qarin gishiri, su na hada ido da Lawwali wai ita wayayyiya, a dole ba ta tsoron shi, ta ce, "Ango ka sha qamshi" Daga mata hannu ya yi, sannan ya ce, "Sannu, sannu uwar gulai uwar munahurci, watakam waccan qandarabushe munahikar lungun ta dena zuwa, ke kin karbe ta ko? To ki kiyaye zuwa gidan ga ki na kawo gulmar mutanen unguwa, nan nan na wuce ta qofar gidan Malam Zakari, mata na ta zuwa makarantar Allah (islamiyya), su na daukan karatun da zai amfane su duniya da lahira, ke ki na nan ki na baza gulma,to daga yau na fada Maki, in ba alheri na zai kawo ki gidan ga ba, kar ki koma zuwa" A yau ta hango abinda Yabbuga ke tsoro a idanun Lawwali, wani irin tsoro da nauyin shi ta ji ya baibaye ta, yaqen ma kasa shi ta yi,sai nishi take fiddawa,wanda ya sanya Mai Buruji dariya, ta rasa me ya sa in Lawwali ya ritsa matan unguwar su ke shiga tashin hankali haka, cikin zuciyar ta tace, 'Na raba ki da mutane irin su Lawwali Mai Buruji, bar ganin ya shiryu, yanzu zai juye ya tuna da,ku din ma ai tsoron shi kuke' Kama bakin ta tayi dan kar dariyar ta ta fita fili, saboda hada ido da suka yi da Ta Yahai, idanun ta sun yi qanana qanana, sai zufar kan hanci ke tsattsafo mata, munafurci be ba a rayuwa . Lawwali bayan ya gama wanke Ta Yahai, ya gaishe da iyayen shi, ya wa Mubaraka Sallama ya tafi gidan shi. Bayan fitar shi ne Lamishi ta juya dan yi wa Ta Yahai magana ta ga wayam, Mai Buruji da dariya ta suqe ta har ta na zama a kujera,ta ce, "Ai ya juya ku na gaisawa ta sa kai ta hice, ke ga idanun Ta Yahai? Ita da ka wa Yabbuga dariya akan tsoron Lawwali ita ma yau ta shiga layi," "Ke dai Allah shi yi miki sauqi, mi ne ne abun dariya to anan?" "Yaya ke ma hwa dariyar ki ke,ke wallah zaman gida ya hi dadi akan shegen zaman gulmar nan da mu ke, haba, mi za ai da gulma da tsintse?" "Walle kau, ke gani dai hankali kwance ba ruwan mu da damben unguwa, walle in ba qarya zan yi ba, har wani dan fari na ga muna yi,...ke wagga ke dawo ba mu ko gaisa ba, ya su Hajiya ?" Mubaraka da ke ta gaishe su suna hira ce ta sake gyara zaman ta a tabarma ta ce, "Su na lahiya, yau ma Hajiya tace Aunty sultana ta shirya, in Yah Auwal yamaishe ni gidaa ya bi ya dauki mata tai, ai dai an qare zaman makoki" "Ai ko ta kyauta wallah, Allah dai shi jiqan gwamna," "Ameen, shin Umma da gaske ne abinda ya faru da Aunty Hansatun Isah?" "Humm haka dai labari ke ta yawo, yanzu haka shi Laminu an yanke mai hakuncin zaman gidan maza shi na can, Asshibi kuwa ta murje ido, ta toshe kunne da tsintsen mutanen shiyya, tunda bata san mi ya ka aikatawa ba, shi da kan shi ya wanke ta,ita ko Hansatu an ce uwatta ce ta tafi har can qasa mai tsalki ta amso mata takardar saki (kun ji yanda mutane kan juya zance komai qanqantar shi ko? Su Yaya Musa ne suka amso takardar saki, amma an ce Hajiya ce, duk yanda labari yake mutanen duniya sai sun juya shi, shi ya sa dole ne mu godewa Sahabbai da duk wadan da suka yi sanadin hade mana Alqur'ani da hadisai har suka riske mu lafiya ba dad'i ba ragi, Allah ya yarda da su, ya shirya masu qirqirar hadisan qarya, da labaran qarya)" "Ohhhh Allah shi kyauta, amma Ni Ko Umma ba dan kar a ce na ce ba, da sai in ce na wa Aunty Hansatu murnar rabuwa da Isah, mutumin nan azzalumi na wallah, Allah shi bata mafi alkhairi" "Ameen ke dai diyar ga" "Umma akwai tuwo? Na yi kewar cin abincin ki" "Akwai, bari na debo miki, Allah ya yi da rabon ki, kahin su Jameelu su tai wajen koyon dunki da Yayan ku yassa su, sai da sun ka kusan canyewa suka bar kingi" "Masha Allah, ashe sun sara zuwa, ya fadi min kuwa zai saka su, amma ban san sun fara zuwa ba, bana dinkin mu ba zai kwantai ba ashe, Allah ya taimaka" "Ameeen ya Allah" Mubaraka na zaune Lamishi ta kawo mata tuwon ta kuwa zauna ta gyare shi, dan kuwa Lamishi ba dai iya girki ba. *************************** Wata biyar kenan da kai kayan lefe, da duk wani abu da ake kai wa na bidi'ar aure,na Mubaraka, duk da cewa Lawwali ya ce a taqaita bidi'a amma still kaya sun qayatar da kowa, ranar aure kuma na ta qaratowa, dan kuwa bai fi saura sati Uku ba. Amarya Mubaraka ta ga gata wajen Iyayen ta biyu, wato Mai Buruji, da Lamishi, sai kuma qawar amana wato Mama 'Yabbuga kamar yanda Mubaraka ke kiran ta, duk wani sabani ya kau, an shirya, an dinke, Ta Yahai ma ba a barta a baya ba, wajen hidimar biki. Yanzu matan unguwar sun hade kan su, duk da in gulmar su 'Yabbuga ta motsa sai sun tab'a amma an samu sassauci, mutane sun fahimci abun ya zame musu kamar wani ciwo ne, (Allah ka raba mu da ciwon gulma da munafurci). Ango kuwa na can na hidimar biki, a bangare daya kuma ya na ta zuwa neman aiki, duk da gwamnati mai ci ta ce za ta taimaka masa, a matsayin shi na dan tsohon gwamna,amma shiru ka ke ji, ba wanda ya kira shi. Ya aika takardun shi ko ta ina dan neman aiki, kuma ya na saka ran albarkacin addu'ar da yake, da kuma tawassuli da kyawawan ayyukan da ya ke a rayuwar shi, Allah ba zai bari su wulaqanta ba, shi da mahaifiyar shi, da qanwar shi. Cikin ikon Allah kuwa ana sauran sati biyu auren shi, ya samu aiki, aikin da bai taba zaton samu ba kuwa, nan da nan kuwa ya bugawa Hajiya Ikee waya ya sanar da ita, murna ta dinga yi da sanya albarka, suna gama waya da Hajiya ya kira Mubaraka, ya na murna ya sanar da ita, sujjada ta yi ta godewa Allah, kafin daga baya ta dau wayar ta yi ta zuba masa addu'a ta kariya daga dukkan abun qi, da nema masa alkhairi da albarkar da aikin ke tattare da shi . ************************* Cikin Sultana na da watanni bakwai cif cif yanzu, Hajiya Ikee kan ce bata taɓa ganin wadda ciki ya yi wa kyau ba sama da Sultanan ta, Ita kuwa sultana kan ce son kai ne kawai, amma akwai wanda suka fi ta kyau. Lawwali ya gama aika sauran 'yan kudaden shi Kano, ya na so kafin ya isa Taheer ya buda masa shago ko qarami ne,Taheer kuwa ya dage sai dai Lawwali ya amshi babban shagon shi, shi ya nemi qarami ya ci gaba da kasuwancin,tun Lawwali na ahh ahh ahh, sai da Taheer ya ja ran Oga ya kai ga ɓaci har ya bada umarni, sannan ya dena jayayya da Lawwalin. Sun gama tsara bayan bikin Mubaraka, za su dunguma gaba daya shi da Taheer su tafi Kano din. ************************ Lawwali na matuqar bawa Sultana kulawa, kulawar da duk wani miji na gari, kuma uba na gari ya kamata ya bawa matar shi, musamman ma mai juna biyu, har Sultana na mamakin inda ya san yanda ake kula da mace mai juna. Ta na bincike a wayar shi ta gano, internet yake shiga ya yi ta research akan yanda zai kula da ita. Yau ma kamar kullum, ta na zaune ta ce da shi, Ita dai so take ta ci qosai, irin wanda ake saidawa a bakin hanya din nan, akwai wata mata akan hanyar shiga unguwar Tudun faila, ta na qosan to ita ta tuna, shi ne take ta rikici ita qosai take so, gashi bai jima da dawowa daga unguwar ba, ba ya so ya koma, amma haka ya hakura ya shirya, ya fita. A bakin titin fita daga Unguwar su ne ya ga wannan tsohuwar da yanzu kusan kullum sai ya gan ta, dunqule a waje daya, da kwanon barar ta a gaban ta, matsawa ya yi da motar shi, ya aje mata 1k a kwanon ya yi gaba, ya tabbata duk yanda akai, matsafan unguwar ba irin ta suke so ba, shi ya sa har yanzu take a raye, basu sanqame ta ba. Ko da ya je wajen mai qosai ya tarar ta kusan saidawa, qullin saura kad'an, cikin Hamdala ga Allah ya miqa kudin shi aka bashi, ya dau hanyar komawa gida. Ko da ya bi ta inda tsohuwar take sai bai gan ta ba, shi ma qara gudun motar shi ya yi, ya isa gida. Ko da ya je gimbiyar ta yi bacci,ya na ta tunani shin ya tashe ta neee, ko ya bar ta? Kar ya tashe ta ya yi laifi,Kuma ya karanta a internet ba a so ana tashin mai ciki, in ta yi bacci, ana barin ta har ta tashi da kanta, in ya bari kuma har qosan ya yi sanyi, ya san za ta masa rikici, dan haka yawo ya dinga yi, ya na buga abubuwa, har sai da qara ta ishe ta ta farka, nan fa ta ja qosai ta hau ci, ta na ta surutu, wanda ya riga ya san santi ne, shi kuwa ya na ta matsa mata qafar ta da ta kumbura. (Maza hausawa a dinga tausayin masu ciki,matan hausawa a dinga gyarawa, dan ba me kama qafa duk baso da qauje da datti ya matsa, sai mai tsananin qaunar ki da tausayin ki) ************************ Makaranta kun dai san an ce rana bata qarya, sai dai uwar d'iya ta ji kunya, to na tabbata wannan uwar d'iyar ba zata ji kunya ba,domin kuwa a shirye take tsafff dan gudanar da biki bidirin autar ta wato Mubaraka...... *Kun shiryaaa??* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 64: Biki fa ya yi biki, daga gidan ango har amarya kowa ka gani bakin shi a bude ya ke da fara'a, ga abinci daidai gwargwado ba yunwa, Hajiya Ikee ta yi matuqar mamaki yanda ta ga qawayen ta sun qi halartar bikin, wadan da ta ke rainawa a baya, take zaben wasu akan su, su ne suka je, su ne suka had'a mata gudun mawar da bata tab'a zata ba. Wannan karon Sultan bai gayyaci kowa a abokan karatun shi ba na can qasar waje, duk da cewa Sultana ta so hakan ya faru matuqa,amma ba su da kudin da za su yi hidimar da suka gudanar a bikin Sultanan, sai dai wasu daga cikin abokan nashi da suka ga sanarwar auren nashi a shafin shi na facebook, sun zo da kan su, ba tare da ya san za su zo ba, ya yi matuqar farin ciki da hakan kuwa, a qalla ya tabbatar da cewa in wani na son ka dan kai wani ne, to wani na son ka ne domin Allah. An daura auren Mubaraka da Sultan akan sadaki nera dubu hamsin,wanda yayan Hajiya Ikee ne ya bayar a matsayin tashi gudunmawar. Lamishi ji take kamar za ta rabu da jaririyar yar ta ne, domin kuwa a wadannan watannin da suka yi a tare,ta nuna wa Mubaraka gata kamar na qaramar yarinya, duk wata kulawar da bata samu ba a baya Lamishi ta yi matuqar qoqari wajen bata a yanzu, Ita kuwa sai ta ninninka akan biyayyar da take wa iyayen nata. 'Dan Talo dai ba shi da kudin kayan dakin amarya, dan haka ya dinga fafutukar yanda zai ko bashi ne ya had'a a yi mata, sanda Sultan ya samu labari daga bakin Sultana, da kan shi ya yi takakkiya, ya sanar da Dan Talo kar ya samu damuwa, domin kuwa Mubaraka kawai suke buqata, ba kayan daki ba. Dan Talo ya yi kukan dana sani, har ya godewa Allah, da ace shi mutumin kirki ne a baya, wanda ya kafu da qafafun shi akan neman kudin da zai rufawa iyalin shi asiri,da yanzu bai zo ya na shiga halin qunci akan ba shi da sisin sa wa yar shi komai a dakin ta ba, Lawwali kuwa a gefe guda ya na batun siyan kayan d'akin Mubarakan shi Sultan ke masa bayanin inda za ta zauna bata da buqatar kayan daki, komai akwai, dan haka kar ya damu da kashe kudi, se dai in ya na ganin Barakan shi ta fi qarfin kwana a tsoffin kayan d'akin shi, dariya Lawwali ya yi, ya ce "Wanne kayan ne tsoho? Dakin da kullum mamaki nake wai d'akin namiji ne kamar na budurwa tsabar yanda aka qawata maka shi?" Murmushi kawai Sultan ya yi, dan tunawa da Daddyn su da ya yi, shi ne ya tsaya tsayin daka dan ganin komai ya wadatu a dakin shi. Da yamma kuwa Mubaraka na ta kukan rabuwa da iyayen ta, Lawwali ya shiga cikin gidan,ya bada Umarnin in an gama shirya amarya a sanya ta a motar shi, shi zai kai ta har dakin ta kamar yanda ya ke da buri a rayuwar shi. 'Yabbuga ce ta leqa kan ta waje cikin ladabi ta ce masa "An qare shirya ta, tun dazu ba ta son hitowa na, su na nan su na kuka ita da Lamishi" Lawwali ne ya sake dubawa da kyau,dan ya ga shin da gaske yau 'Yabbuga ce ke masa magana? Wani murmushi ya sauke, mai sanyi, a cikin ran shi kuwa ya ce, 'Alhamdu lilLAAH, na tabbata yanzu rayuwa ta ta yi kyawu yanda ya kamata, ba dan ta dena jin tsoron na ba, sai dai alamar nutsuwa da ta bayyana ga huskata har ta jawo mutane yanzu suka daina shakkata, sai ma soyayya ta da ni ke gani ga ijiyar su (idanun su)' "Me ka ce?" "Cewa na yi bari in shigo in hito da amarya" Cike da murna 'Yabbuga ta koma ta sanar da su Ta Yahai shigowar Lawwalin, fita mata suka dinga yi a dakin, Mubaraka na zaune a qasa, ta ɗora kan ta a cinyar Lamishi da ke ta tsiyayar da hawaye. "Dan Allah ku bar wanga kukan, rayuwa fa dama haka take,kowace mace sai ta bar gidan iyayen ta in lokaci ya yi, kai watarana ma duniyar za mu bari gaba daya, sai mu manta da hankulan mu? Ko za mu manta da hakuri ne akan rashin masoyan mu? Ballantana hwa duk wadda ke son ganin wata cikin ku nerar ga dari biyu ta ishe ku, ku tai ku dawo, to mi?" Mubaraka ce ta daga kai ta kalle shi, hawayen ta da ke zuba kamar pampo na taba zuciyar shi, hannu ya miqa mata, da gudu gudu kuwa ta isa gare shi ta fada jikin shi,Lawwali kasa jurewa ya yi, sai da ya zubar da hawaye shi ma. Mutanen unguwa 'yan gulma sai leqen su ake, wasu har dauka suke a waya, a haka Dan Talo ma ya shiga, ya sanya wa Mubaraka albarka, Mai Buruji ma ta na kuka ta sanya albarka, Lawwali ya share mata hawayen ta, ya share nashi,suka fita daga gidan,motocin da suka je daukan amarya har sun yi gaba, dan an sanar da su Yayan Amarya ne zai kai ta da kan shi,Sultan kuwa da ya ji labari, ya ce, dama ya san za ai haka. Ya rage motar Lawwali kawai a wajen wadda  zai kai qanwar shi dakin miji da ita. Bayan ya sanya ta a mota ne, ya tada motar, sai GRA, gidan tsohon Gwamna Halliru Murtala Gusau. Tafe suke Lawwali na yi wa Mubaraka wata iriyar nasiha da ke ratsa dukkan kafofin jiki da ruhin ta, kuka kawai take saboda yanda take jin kalaman shi kamar mai mata bankwana, sun shiga kwanar da za ta sada su da GRA ne Lawwali ya ga wannan tsohuwar da ya saba gani kullum ta na zaune a bakin titi, ta miqe, ta yi wurgi da mayafin kan ta, abun bai gama bashi mamaki ba sai da ya ga ta zaro bindiga, ta nufe su ta na dingisa qafa, a sannan ne ya kula da kyau, ba tsohuwa bace, No 1 ne, nan take kuwa Lawwali ya take motar da gudu zai bi ta kan shi, kafin ya qarasa No 1 ya sake harsashin bindigar shi a qirjin Lawwali, nan take motar kuwa ta bi ta kan No 1 ko shurawa bai ba. Mubaraka kuwa ganin yanda jini ke zuba a qirjin Lawwali kuma a haka ya na qoqarin tsaida motar sai ta rikice, motar na gama tsayawa, ta bude ta zagaya ta wajen Lawwali ta na ta kuka, tare da kwalla ihu, ta na neman taimako, wajen shiru ba kowa. Kama shi ta yi, ta na ja, da kyar ta samu ta fitar da shi daga motar,  ta na kuka "Yah Auwal ka tsaya, yanzu za a kawo mana taimako, ya Allah ka tausaya min kar ka jarabce ni da rasa yaya na, ya Allah ka zama gatan mu,kar ka raba mu a daidai lokacin da muke buqatar shi, wayyoo Yah Auwal Dan Allah ka bude idon ka, ka dena ruhe shi, a taimaka manaaaa" Muryar ta ta dashe saboda kukan da take, su na nan zaune, masu gadin unguwar suka iso, da 'yan sanda, domin sun ji qarar harbi a wajen, ganin halin da Mubaraka ke ciki riqe da Lawwali a hannun ta ne ya sa nan da nan suka nufe su, wasu kuma su ka hau duba gawar No 1, a motar 'yan sanda aka saka Lawwali, sai bayan an saka shi a motar ne Mubaraka ta tuna da waya, a guje ta nufi motar su, ta na kuka, mai ban tausayi, ta dauki wayar ta ta kira Sultan,kukan ta ya hana shi fahimtar komai, sai wani mai gadi ne ya karba ya masa bayani, salati kawai Sultan ya dinga jerawa. A guje ya bar gidan, Sultana da Hajiya Ikee da wasu cousins din shi da suka zo bikin, sai tambayar shi me ya faru suke, bai amsa kowa ba ya bar gidan. Sultana kuwa ji ta yi abun da ke cikin ta na mata motsi sosai, har sai da ta samu waje ta zauna, ta na mamakin irin motsin da yake ta yi. Ko da Sultan ya je wajen bai tarar da motar 'yan sanda ba, sai Mubaraka da ke zaune dabar a qasa, ta na kallon waje d'aya, ba ta uhummm, ba ta Ah ah, ta gaji matuqa, ta kai qololuwa wajen gajiya da kukan, ya na ganin ta ya nufe ta da gudu ya rungume ta, kwantar da kan ta ta yi a kafadar shi kawai, ta yi shiru. "Mubaraka mu je asibitin mu ga ya ya ake ciki" Ba tare da ta amsa masa ba, ta miqe, ya taimaka mata, ya sanya ta a motar shi,kayan ta farare tass na amare da suka gaji da kyau sun yi face face da jinin Lawwali, d'aya daga masu gadin ne ya sanar da su asibitin da suka sanar za a kai Lawwalin. A haka suka isa asibitin, ko da suka je, sun tarar 'Yan sanda na tsaye a dakin da aka shigar da Lawwalin. Likita da nurses na fitowa daga dakin suka sanar da mummunan labarin da ya daki zuciyar Mubaraka ta tsaya cakk, ta dena aiki na wasu seconds, sannan ta ci gaba da bada jini ta kowanne lungu da saqo na zuciya da sassan jikin ta, nan take ta yanke jiki ta fadi a wajen. Sultan ya na ganin tashin hankali a wannan ranar,ranar da ya kamata ta zama ranar farin ciki, ranar murna, ranar kafa tarihi mai cike da nishadi, yanzu ta koma rana mafi baqin ciki, da muni a wajen su baki daya. Sultan rasa inda zai saka ran shi ya yi, ta ya zai fara sanar da wannan mummunan labarin? Wanne hali qanwar shi za ta shiga? Mahaifan Lawwali fa? Ya na nan zaune aka shige da Mubaraka dakin kula da marasa lafiya na gaggawa. Qoqarin ceto ran ta likitoci ke ta yi,abun na neman fin qarfin su, Sultan kuwa addu'a kawai yake yi, Allah ya jiqan Lawwali ya sanya wa duk wasu masoyan shi hakuri da juriya, tare da danganar rasa shi. Ya na nan tsaye likita ke sanar da shi, sun samu numfashin ta ya daidaita, cikin farin ciki, ya shiga, ta na kwance ta na bacci, dan kuwa allurar bacci akai mata, saboda zuciyar ta ta samu hutu. Wayar Sultan ke ta ringing, ko da ya duba, sunan Sultana ne a jiki, bai san sanda ya fashe da wani irin kuka ba. "Allah mun gode maka, duk abinda ka yi shi ne daidai, ba ka barin wani a duniya dan wani ya ji dadi, da ka na barin wani a duniya dan wani ya ji dadi,da ka barwa Annabi Muhammad Nana Khadeejah, da ka barwa Nana A'isha Annabi Muhammad, da baka raba Nana Fadeema da Annabi Muhammad ba a duniya, da ka bar mana shi mu al'ummar shi mun ji dadi, duk abinda ka tsara shi ne daidai, Allah ina roqon ka da ka kawo mana komai da sauqi, ka sanyaya zuqatan mu, ka bamu hakuri da juriya da danganar rashin makusantan mu" Ringing din wayar ne ya sake maida shi cikin hankalin shi, dauka ya yi cikin sanyin murya, sallamar Hajiya ya ji, ta na tambayar shi me ya faru, ya fita a firgice. "Hajiya ki na ina ne?" "Gani tare da su Sultana, a bangaren Daddyn ku" "Ok Hajiya ki sauka qasa za mu yi magana , dan Allah kar ki daga murya har sultana ta ji, ke dai san ta na da juna biyu ko?" Gaban Hajiya Ikee ne ya dinga bugawa, a sukwane ta sauka qasa, dan jin me yake faruwa, ta na zuwa qasa parlourn manyan baqi ta wuce, ba kowa a wajen, ya ma kwana biyu ba a shiga ba. Ta na shiga ta sanar da shi ta sauka qasan, cikin raunin murya Sultan ya sanar da ita abinda ke faruwa, salati ta dinga yi,jikin ta na matuqar rawa, nan take ta dinga hango Lawwali, kallon wajen da ya taba shaqe ta tayi, da kalaman shi, tunawa da irin girmama ta da kulawa da ita da sultana da yake yi a yanzu ta yi, nan da nan hawaye suka dinga rige rigen sauka daga idanun ta. Sultan na ta magana bata jin shi, dan haka ya kashe, sai da Hajiya Ikee ta ci kukan ta a wajen, sanan ta miqe, ta bar parlourn, dakin Sultana na da ta shiga ta wanke fuskar ta, sannan ta koma wajen su Sultanan, ganin sultana ta yi a zaune ta dafe kan ta, cikin tausaya wa Hajiya Ikee ta je wajen ta, ta dafa ta, daga kai sultana ta yi a hankali ta kalli Hajiyan, ta ce, "Hajiya kai na ciyo ya kai min, ga abinda ke ciki na na ta naushi na, motsin da yake min yau ban taba jin irin shi ba, dama in ciki ya kai wata bakwai haka ya ke yi?" "kar ki damu juyi shi kai, kunga yanzu dai ya kamata mu je mu kwanta shad'ai ta yi, bai kamata mu zauna zaman jiran su ba, tunda dai ba mu za a kawo wa amarya ba" Dariya cousins din shi suka yi, suka miqe,tare da yi wa su Sultana sai da safe. Hajiya Ikee cikin dabara ta kashe wayar Sultana, ta boye. Sun yi shirin bacci gaba dayan su,sun kwanta, Hajiya ta kasa bacci, Sultana ma idanun ta biyu, ta rasa dalilin da ya sa Lawwali be kira ta ba, gashi har sha biyu na dare ta gota. Jin motsin Hajiya ya yi yawa ne ya sa ta tabbatar da cewa Hajiya ba bacci take ba, "Hajiya ina waya ta?" Shiru Hajiya ta yi, kamar mai bacci, sultana ma shiru ta yi, daga baya ta sauka ta hau duba wayar ta. Bata gan ta ba, sai kawai ta dauki ta Hajiya,ta nemo No Lawwalin, ta Kira. Ko da ta kira ta jima ta na ringing ba a daga ba, sai daga baya,dan sandan da ke riqe da wayar Lawwali ne ya ga an rubuta, 'Hajiya' A jikin wayar, dauka ya yi, tare da yin sallama, "Hajiya har yanzu su na asibiti ba a bada gawar shi ba, akwai wasu 'yan bincike da muke so mu gudanar" Daga can gefe ta ji ana ma mutumin da take magana da shi fad'a,kuma an kashe wayar. "Gawar wa za a bada?" Kit ta ji an kashe wayar, kafin a kashe ta ji ana Wa wanda ya amsa wayar fada,akan me ya sa bai kashe wayar ba duka har sai an gama bincike. Cikin jikin ta ne ya harba da qarfi, sai da ta duqa a wajen, ta jima ta na cije leben ta, Hajiya Ikee kuwa na kwance hawayen tausayin yar ta na zuba mata, yau 'yar ta za ta fara dandana azabar rabuwa da miji, azabar rabuwa da miji daban ce a rayuwa. Murya can qasa ta ce, "Hajiya, Hajiya, ciki na,....Hajiya na kira wayar Auwal an ce ba a bada gawa ba, gawar wa za a basuwa?" Shiru Hajiya Ikee ta yi, Sultana na nan a duqe ta juya ta kalli Hajiya ta ga alamar idon ta biyu, amma ba ta amsa ba. Tashi ta yi ta na duqawa da kyar ta zauna a bakin gadon, ta fara buga cinyar Hajiya ta na tashin ta, kuka take so ta yi, amma ta kasa, saboda fargabar da ta cika zuciyar ta, fatan ta Allah ya sa ba gawar mijin ta ake magana akai ba. Hajiya dai shiru ya qare, dole ta tashi ta zauna, kukan da Sultana ta ga Hajiya na yi ne ya sanya ta gyara zama da kyau, "Hajiya dan girman Allah ki min magana, wam-mutu?"(wa ye ya mutu) Kuka mai qarfi Hajiya ta fashe da shi, sannan ta ce, "Sultana dukkan mai rai mamaci ne, mu yi fatan mu ma qarshen mu ya yi kyau, amma wanda Allah ya kira zuwa ga kushewa ba shi jinkiri, Sultana ki sawa kan ki salama,da dangana, ko...." "Dan Allah Hajiya ki dena wanga dogon jawabi, ki sanar dani gawar wa za a basuwa? ina Auwal yake? me yah Sultan ya ce miki da ki ka kire shi dazu?" "Sultana Ki yi hankuri, Allah ya bawa zucciyar ki hankuri, shi sanya maki juriya" Idanun Sultana sun cika da hawaye, har bata gani, cikin daga murya ta ce, "Wai waye ya mutu ne?" Hajiya Ikee ka sa fada ta yi, ta na ta kuka, "Auwal di na ne ya mutu Hajiya? Ki na so ki sanar da ni Auwal d'i na ne ya mutu? Inaaa ba gaskiya na ba wallah, ban yarda ba, ba gaskiya na ba, bari ki ga na kwanta sai da sahe, gobe zan koma gida na, tunda fatan mutuwa ki ke wa miji na" Juyawa ta yi hawaye na zuba a idanun ta, ta kwanta, kasa kwanciyar ta yi, ta miqe tsaye, Hajiya Ikee ma miqewa ta yi, ta taro ta, saboda qoqarin faduwa da take, "Ina zaki?" "Gida za ni in ga ko ya na can ya na kwana," Riqe ta Hajiya ta yi, ta na kuka ta ce. "Sultana kar ki zama mara tawakkali ga Allah mana, tunda ke san gaskiya Auwal ya rasu ki nutsu ki hwara yi mai addu'a,yanzu ita ya hi buqata, rasuwar mahaifin ku, mun yi aiki da jahilci mun biyewa kidimewar mutuwa mun dimauce, wannan karon bai kamata mu manta da Allah ba, bai kamata mu yi aiki irin na jahillai ba" Shiru Hajiya Ikee ta ji Sultana ta yi, jikin ta ya sake, komawa gado ta yi da ita, ta kwantar da ita, ta na maimaita "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" Duk da ba daidai ta ke fada ba, amma dai ta koma ga Allah, (a yanzu fa abun ya zama ruwan dare, ka ji babbar mata ko qarama ba su iya fadin wasu kalmomi na tasbihi ga Allah ba, amma magana mai amfani da mara amfani fal harshen su, kalmomi na tasbihi kuwa na shan baqar wahala a harsunan su) Ruwa ta yayyafa wa Sultana, ta farfado, ta tafi ta debo mata mai kyau, dan ta bata ta sha. Ko da ta dawo, zaune ta ga sultanan ta yi shiru, ta na kallon waje guda, ta yi tayi ta bata ruwan ta qi qarba, kuma ta qi magana, sun jima a haka, har qarfe biyu da rabi na dare, Sultana mai yawan ibada ce, kallon lokaci ta yi, ta ga be kai lokacin tashin ta ba, cikin dauriya ta miqe, ta fada bayi, har ta yi tsarki ta daura  alwala ta gama bata zubar da hawaye ba ko d'igo, sai da ta yi kabbara sallah ne, ta gan ta tsaye a gaban mahaliccin ta, kawai sai ta fashe da kuka. Daga farkon sallar nan zuwa qarshen ta, ta yi ta ne cike da qasqantar da kan ta ga mahaliccin ta, ta na nemawa mijin ta, da mahaifin ta gafara, da rahamar Allah. Ganin haka ne ya sa Hajiya Ikee ma yin alwala ta hau nafila, duk da cewa ba ta saba ba. Washegari da safe kuwa............. *Allah ya kai mu washegarin, dan Allh ku yi min hakuri akan mutuwar Lawwali, na san ba za ku so hakan ba, amma dukkan mai rai lokacin shi na zuwa, lokacin Lawwali ne ya yi, shima, namu muke jira Allah ya kyautata qarshen mu* 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻 BY HAERMEEBRAERH PAGE 65: Washegari kuwa tun asuba Sultana ta ce wa Hajiya ta bata wayar ta, dan ta gano ita ga boye dan kar ta ji wannan mummunan labarin, Hajiya Ikee ba musu ta duqa qasan gado ta zaro waya, dake da qafa ta tura ta, santsin wajen ya sa ta shige can ciki, sai da ta wahala ta samu fiddo da wayar. Ana bata ta kunna, ta kira Sultan, da fari bacci ya samu, a zaune a gefen gadon da Mubaraka ke kwance, ta na kira qarar wayar ta tashe shi, ya duba sai ya ga sultana ce, da sauri ya shafe idanun shi, ya qara dubawa, ya so ya qi dagawa, sai ya ga message din ta ya shiga wayar shi, 'Yah Sultan na san komai, ka sanar da ni inda kuke, gamu nan zuwa' Sake kira ta yi, Sultan ya dauka, jin Muryar ta a dashe ne ya sanya shi qara jin matsanancin tausayin ta, ya san tabbas ta sha kuka, har ta bawa zuciyar ta hakuri. Sanar da ita inda suke ya yi, sannan ta ce masa ga su nan zuwa ita da Hajiya, ai kuwa ta na kashewa ta tada Hajiya da ta fara bacci, rasuwar Daddyn su ta kwana ba bacci amma ba ta yi Sallah ba, ita a wajen ta, sallar ce ta kashe mata jiki, har ta sanya ta jin bacci. Sultana ta so ta tuqa motar da kan ta, kan su isa Hajiya ta ɗan rintsa, Hajiya ta qi sam, ba yanda Sultana ta iya, dole ta zauna wajen mai zaman banza, dan bata son magana balle ta yi ja in ja da Hajiya . Ko da suka isa asibitin shida da rabi na safiya ya yi, har inda aka aje gawar Lawwali aka kai Sultana,d'an da ke cikin ta kamar ya san me ke faruwa, haka ya dinga motsawa, ta jima akan gawar ta na masa addu'a ,tare da koka rashin shi, kafin a ce za a dauke shi a maida shi gidan iyayen shi,Sultana na cikin motar da aka sanya gawar Lawwali dan kai shi gida, duk yanda aka so kar ta shiga qi ta yi, ta dinga kuka ta na fadin, "Dan Allah ku barni da shi, na wannan lokacin na yi masa addu'a ,daga yanzu ba zan sake gani nai ba sai in na mutu,kar ku hana ni wannan damar ta kasancewa da shi dan Allah" Haka aka barta kuwa, har suka isa gidan su Lawwalin bata dena masa addu'a ba, ta na yi ta na hawaye, tunanin farkon haduwar su ta fara yi, har ranar da suka rabu da shi, dan zuwa dauko amarya. Su na isa kuwa Hajiya ta fara shiga gidan, su Lamishi ana zaune bakin murhu ana kunna wuta, za a dora abincin karyawa, ga wasu baqin nan ba su gama tafiya ba. Ganin Hajiya Ikee ba karamin fadar mata da gaba ya yi ba, cikin wani irin yanayin da ta kasa fassara shi ta hau yi wa Hajiya maraba,kafin ta juya ta shiga gaba sultana ta shigo, salati Lamishi ta sanya, cikin sauri ta fara tambayar Hajiya Ikee, "Hajiya lahiya? Tunda na gan ki da sassahe haka nissan ba lahiya  ba, me ke faruwa? Sultana menene na ganki kamar wadda ta shekara kuka?" Dakin Lamishi Sultana ta wuce, ta samu qasan dakin ta ta kwanta, ta kalli gini, shiga akai da gawar Lawwali, Hajiya Ikee kuka ta sanya a daidai lokacin da ta ga yanayin da Lamishi ta shiga, "Innalillahi wa inna ilaihirraji'una, yau na shiga uku na lalace, (haramun ne fadin wannan kalma ta na shiga uku na lalace,kaico na da sauran kalamai marasa kan gado a yayin da akai rasuwa), wa nake gani awa Lawwali? Laaaha'ila ha illallahu, na banu na lalace, wayyyoooo Allah na na shiga uku, d'ana ya mutu, na shiga uku na lalace" Sai ihu take zundumawa, da kyar aka samu aka rirriqe ta, ta na ta ihu ta na yarda tufafin ta,tare da cizgar gashin kan ta,ba kadan ba mutuwar ta shige ta, amma hakan da take ba dacewa bane, ko Hajiya Ikee da take ajin su daya wajen jahilci ta dauki hakan a rashin dacewa. Mai Buruji kuka Lamishi kuka, Jameelu da Kamalu da Dan Talo da ke ta shaqar bacci har a wannan lokacin ba su yi sallar asuba ba, ihu da kururuwar Lamishi ne ya tada su, har rige rige suke su isa cikin gidan, arba suma suka yi da gawar Lawwali, wanda aka budewa fuska , gaba dayan su kuka suka saka, su na ta hargowar kuka, da kiran sun lalace, sun shiga uku. Mubaraka kuwa na can asibiti, kwance, Sultan ya je ya yi sallah, ya siyo ruwa, da dan juice yunwa yake ji sosai, dan rabon shi da abinci tun bakwai na yammar washe garin ranar. Ko da ya sha sai ya ji ma ruwan ya daure masa ciki, zama ya yi kusa da Mubaraka ya na kallon fuskar ta, kamar wadda ta jima ta na ciwo, duk ta zabge ta rame. Wani irin tausayin ta ne ke ratsa dukkan wani sashe na jikin shi. Da misalin takwas da minti ashirin ta farka,da sunan Allah ta budi bakin ta, sannan ta fara neman Yah Auwal din ta, Sultan ne ya fara bata hakuri, ya na sake mata bayanin me ya faru, komawa ta yi ta kwanta, ta rintse idon ta, hawaye na zuba ta gefen fuskar ta, masu zafin gaske,ba ta so ta yi kuka irin na jahilai,ba ta so ta furta kalmar da zata sanya ta aikata zunubi,Dan haka shirun shi ne ya fi. Su na nan zaune wayar Sultan ta hau qara, ko da ya duba Sultana ce, dauka ya yi, ya mata sallama,amsawa ta yi sannan ta ce, "Da yanda za a yi Mubaraka ta zo ta ga Auwal kafin a kai shi gidan shi na gaskiya kuwa?" Da jin haka ya kalli Mubarakan, ya gan ta kwance, amma ya sani za ta so matuqa ta ga yayan ta kafin a kai shi makwancin shi, dan haka ya ce, "Eh gamu nan" Sallama suka yi, ya wa Mubaraka bayani, cikin iya saurin da take ganin za ta iya ta miqe, "Ina zuwa na je na kira likita na fada masa, sai a sallame mu, ko kuma mu je mu dawo" Daga masa kai kawai ta yi, cikin sauri ya fita, bai jima ba ya dawo da likita, duba ta ya sake yi, sannan ya ce za su iya tafiya, taimaka mata ya yi, ta sauka daga saman gadon, ta natsaye ta duba jikin ta, rigar jiya ce dai a jikin ta, me dauke da jinin yayan ta, wasu hawaye ne masu zafi suka dinga sauka daga idanun ta. A haka suka tafi motar Sultan, ya zaunar da ita a gefen driver, ya shiga sai unguwar Tudun Faila. A can kuwa Sultana ta kasa ta tsare ta hana a fitar da gawar Lawwali har sai Mubaraka ta iso, a tunanin malam liman da suka sallaci gawar ta Lawwali, ko ba ta so a kai shi ne, shi ya sa ta fake da hakan, nasiha ya dinga yi mata, ya na lallashin ta, motar su Mubaraka na zuwa ta miqe daga jikin gawar, ta koma gefe, idanun mutanen da ke wajen a tsaitsaye a bakin soron gidan ne ya koma kan su Mubarakan, waje aka ba wa su Mubaraka suka shige, ta na shiga Jameelu ya tura qofar soron, masu leqe da son ganin ya Mubaraka za ta yi suka dinga jin haushi (wai rasuwar ma sai an mata gulma, kamar ba za a mutu ba). Durqusawa ta yi a gaban gawar, hawaye na ta kwaranya a idanun ta, Lamishi kukan ta ne ya qaru, dan kuwa ta fi kowa sanin irin shaquwar da ke tsakanin Mubaraka da yayan ta, akan Mubaraka rayuwar  Lawwali ta zama duk yanda ta zama, domin kawai ta ji dadin rayuwa,kar ta wahala kamar yanda ya wahala. Cikin zuciyar ta take addu'ar,dan ko labban ta ba ta so ta motsa, 'Ya Allah ga bawan ka nan Auwal, ya dawo gare ka, ya Allah ina roqa masa gafarar ka, ina roqa masa rahamar ka, ya Allah ka tausaya mishi kai mai tausayin bayin kane, Allah duk abinda ya aikata na zunubi Allah ka yafe masa, domin kai mai yawan gafara ne,Allah ka ni'imta qabarin shi, ka yalwata masa shi, ka haskaka masa shi,ya Allah ka masa hisabi mai sauqi a ranar tsayuwa, ya Allah ka bashi ikon amsa tambayoyin kabari cikin sauqi, Allah ka mishi rahama, ka gafarta masa' Duqawa ta yi, bakin ta na rawa saboda kukan da ke taso mata, ta sumbaci goshin shi, sannan ta shafi fuskar shi, murmushin shi mai kyau ta ke so ta gani, amma ta san har abada hakan ba zai sake samuwa ba, kalmomin shi masu cike da so da qaunar ta take so ta ji, amma ta san hakan ba zai samu ba, kifa kan ta tayi, a qirjin shi ta rungume shi, ji take kamar kar a dauke shi, kamar ya farka ya ce Barakana wasa ta ni kai miki, Sultana ce ta duqa cikin qarfin halin da ke bawa Kowa mamaki, ta daga Mubarakan, ta rungume ta, sannan ta ja ta suka shiga ciki, su Jameelu suka bude qofar aka sake rufe Lawwali yanda ya dace, aka dauke shi sai makwancin shi na gaskiya. Tunda suka shiga dakin na Lamishi, ba mai magana, sai kuka, Lamishi ta tabbata ta yi babban rashi, rashin da ko sanda iyayen ta suka rasu bata ji zafin shi kamar haka ba, tunawa da kalaman shi take, a kullum ba shi da burin da ya wuce iyayen shi su so shi shi da qanwar shi, a basu kulawa kamar sauran yara,amma daga ita har uban shi, sun gaza. Rafka salati ta yi, ta fashe da kuka, na kusa da ita na ta bata hakuri, kukan 'Yabbuga da salatin ta ne ya ja hankalin mutane gare ta, "Mun yi babban rashi, mun yi babban rashi, sannun mu da hankuri Lamishi Sannun mu da hankuri,kaiiii duniyar ga ba matabbata ba ce wallah,jiya jiya mun ka rabu ina ta bawa Dan Jumma labari har magana mun yi da Lawwali asheee asheee Lawwali kau gawa ce tsaye, mai rai ba bakin komi shi ke ba wallah,sannun mu da hankuri jama'a sannun mu da hankuri" Surutai kawai 'Yabbuga ke zubawa, wanda ke nuni da cewa tabbas mutuwar Lawwali ta daki zuciyar ta, wani dogon numfashi ta ja sannan ta ce, "Ina can hangame da baki, ina kwanan wahala, Dan Jummaa yaddawo yatas-san,ya ce daga gidan ga shike Lawwali ya mutu,la'ilaha illallahu" Wata mata ce ta ce, "Boyar Allah hankuri zaki, hankuri kowa shi ke yi wajen ga da kiggane mu, mata tai da qauna tai na ciki, su ma hankurin suke" "Keeee wagga banni, banni yanda kin ka ganni, ba ki san ya nika ji ga zucciya ta ba,....Ohh rayuwa kenan, ina Mubarakar take, boyar Allah" Miqewa ta yi ta bazama zuwa dakin, zaune ta gan su, da su Hajiya Ikee da Sultana, sai Mubaraka da ke kwance kusa da Sultanan, ta na ta sauke numfashi da kyar,ji take iskar shaqa ta mata kadan, amma haka take daurewa, ko dan kar Sultana ta sake samun wata damuwar. "Sassanun mu da hankuri bayin Allah, Allah shi jiqan Lawwali, Allah shi gahwarta masa, sannun mu da hankuri, Hajiya Sannun mu da hankuri" Amsa mata suka yi, tare da yi mata godiya. Su na nan zaune mutanen unguwa aka fara kawo abincin sadaka, ai kuwa kafin kace me, masu zaman makoki an miqe an fara warwason abinci, kowa na son ya samu abinda zai kai bakin salati. Sai a sannan ne Hajiya Ikee ta tuna Sultana ma bata karya ba, ga ciki, waya ta yi wa Sultan, ta ce ya samu ya ɗan siyo ko da kayan shayi ne me yawa da bread a kawo, saboda su karya, ai ba a zauna ba abinci ba. Nan da nan kuwa ya aika su Jameelu, aka kawo kayan shayin da bread,bayan sun debi wanda za su yi amfani da shi, ta sa aka fidda sauran. Duk yanda ta so ta matsa wa su Sultana su ci abinci qi sukai, dole ta hakura, ta ci ta bar su. Haka akai ta zaman makoki, har kwana bakwai, sannan Hajiya Ikee ta tafi ta bar Sultana a gidan, ita da Mubaraka sun zama kamar hanta da jini, a koda yaushe su na tare da junan su, kowacce su na kallon 'yar uwar ta a matsayin Lawwali, domin su din masoyan shi ne, ya na ji da su. Sultana bata bar gidan ba sai da aka yi arba'in a lokacin cikin ta ya shiga wata na tara, Mubaraka ke raka ta ganin likita, Sultan ya yi hakuri iya hakuri, domin ba zai iya bijiro da maganar kai masa amarya a wannan lokacin ba, amma tabbas ya na da buqatar matar shi. Cikin Sultana har ya haura wata tara, ta wuce EDD din ta, haihuwa shiru, kuma ciki kullum aka je ganin likita zai ce lafiya qlou take. Yau ma sun shirya tsaf dan zuwa asibiti ganin likita, Sultana ce ta ke ta yi wa Mubaraka magana akan ta hanzarta Sultan na jiran su a qofar gida. Cikin sauri ta qarasa sanya hijabin ta ta sake yi wa Lamishi sallama suka fita, zaune yake a motar ya sha gayun shi da wata brown din shadda da baqar hula, hasken shi ya qara fita sosai, ya yi wani irin kyau,tunda suka shiga motar Suka gaishe shi, Mubaraka ta ja baki ta tsuke, lokaci zuwa lokaci ta na satar kallon shi ta madubi. "B love ki kalle ni kan ki tsaye, ni din naki ne, ke kadai, ba sai kin yi ta satar kallo na ba kamar wani baqon saurayi a unguwa" Kunya ce ta kama ta sosai, ta sa hannun ta ta kare fuskar ta, ta na kallon waje. Sultana kuwa murmushi ta yi, tunawa da nata masoyin sai ya sanya kwalla taruwa a idon ta, har suka isa bata san wainar da su Sultan ke toyawa ba a motar. Su na zaune a asibitin Mubaraka ta hango Hansatu riqe da Ahmad sai wani mutum a gefen ta, Hansatu ta yi shar da ita kamar ba Hansatun Isah da ta sani ba, ganin Ahmad ne ya sake tabbatar mata da cewa Hansatun ce dai. Ta gaban su za ta wuce, har sun gota su ta koma baya, "Ahhh Ahhh Mubaraka d'iyar albarka, kwana da yawa" "Aunty Hansatu ina kwana, ya gida, ya su Ameenatu," "Lahiya qalou, ya bayan rabuwaaa? Ina mutanen shiyyar mu, ya su Lamishi, ya yayan ki, ina hwata kowa lahiya" Cike da murmushi Mubaraka ta ce, "Kowa lahiya lau Aunty Hansatu, Yayana ne dai Allah ya yi mai rasuwa har an yi arba'in ma, waccan matar shi ta, mun ka kawo ganin likita," Salati Hansatu ta yi, sanan ta ja Mubaraka su ka ɗan koma gefe, "Allahu akbar, Allah ya jiqan shi, dan Allah ki gaishe min da su Lamishi, ina nan tahe, ban sani ba, ban da labari, dan tunda na tai ban koma ba da nayi aure ne ma Asshibi ta tai, dan mu na gaisawa ta waya da ita, jehi jehi, bata sanar da ni wannan babban rashi da an kai ba, Allah shi gahwarta mai" Mubaraka na son Hansatu, saboda mace ce mai kirki, ta ji dadin yanda ta nuna kulawar ta, kallon mutumin dake mata ta'aziyya ta yi, sannan ta ce, "Aunty Hansatu wanga na Yayan nawa?" "Shi na Mubaraka, shi na wanda iyaye na sun ka so na aura tun kahin Isah, Allah be nufa ba sai yanzu" "Allah Sarki, matar mutum kabarin shi,Allah shi sanya alkhairi aunty," "Ameeen na gode, Ahmad mun ka kawo ganin likitan yara ba shi da lahiya, bari mu tai, sai na shigo shiyyar" "Allah shi bi da lahiya sai kin zo din, na gode" Shafa kan Ahmad Mubaraka ta yi, ta ce ya gaida su Ameenatu, dan ya san ta sosai, Islamiyya daya suke zuwa, ita a babban aji take, murmushi ya yi, har da daga mata hannu ya tafi, Sultana ta shiga ganin likita, Sultan ya zo ya tsaya a gefen mubaraka, da ke kallon inda su Hansatu suka bi dauke da murmushi, dan dukan kafadar ta ya yi kadan, da tashi, sannan ya ce, "Da ace za a kawon ke yau, kema nan da wata tara ko goma za ki haifa mana baby, nan da shekara bakwai ya zama kamar wancan yaron," Kunya ce ta bi ta lullube Mubaraka, ta rasa ina za ta sanya kan ta, su na nan tsaye suka ga an gunguro da gado, Sultana na kai, da sauri Mubaraka da Sultan suka yi kan ta, gani suka yi ta na ta yatsina fuska, kamar za ta yi kuka. "Me ya hwaru?" "Daga duba ta naquda ta taso, zamu kai ta dakin haihuwa, ku je ku kawo kayan haihuwa" Cikin sauri kuwa Mubaraka ta duqa gaban Sultana ta ce, "Sannu Aunty Sultana, Allah shi sauke ki lahiya, Allah shi kawo miki haihuwar da sauqi, bari mu tai mu doko kayan," Shafa kan Sultana, Sultan ya yi, Sannan suka tafi. A dakin haihuwa kuwa banda kiran sunan Allah ba abinda sultana ke yi, irin azabar da take ji ba ta da misali. Cikin ikon Allah kafin Mubaraka su je su dawo, ta samu haihuwar yaron ta namiji, sambalele, dan lukuti kamar OO. Duk ya cika dakin da kuka, Midwife din da ta karbi haihuwar sai tsokanar shi take da kiran shi ragon maza, a ido gashi kamar namiji, amma sai kuka, Sultana kuwa kuka kawai take, zuciyar ta ta shiga wani irin yanayi wanda ba shi da misali,tun Nurses na ganin kamar kukan Murna ne, har abun ya basu mamaki, "Boyar Allah kukan ga ya yi yawa, ke da zaki godewa Allah, sai ki zanka kuka haka?" Mubaraka ce ta leqa kan ta dakin,riqe da kayan baby, kamar yanda aka buqata, Sultana na ganin ta, ta sake bare baki da kuka, Mubaraka ta fahimci kukan me take, kawai sai ta ji hawaye ya na gudu a nata kuncin, qarasawa ta yi, ta duqa ta rungume Sultanan, ita ma rungume ta tayi da duk wani qarfin da ya rage mata, kuka sukai ta yi, kamar ranar ne Lawwali ya tafi ya bar su. Da kyar Nurses din wajen suka raba su, cikin kuka Mubaraka ta ce, "Ku yi hankuri dole mu yi kuka, mahaifin yaron ya rasu,tunawa da shi ne ya sa mu kokawa, da ace shi na nan da na tabbatar sai ya maku kyautar da za ku san kun karbi haihuwar matar so, na tabbatar da ya na nan da kun tabbata kun jima baku ga  uban da ke son matar shi da d'an shi ba kamar shi,da za ku yi mamakin shin waya hi so a tsakanin mu ukun nan, matar shi? Dan shi? Ko qauna tai? Zuciyar shi cike take da soyayya, wadda in ya na wa mutum,sai mutum shi zaci shi kadai ya ke so,wannan dalili ne ya sa muke kuka, mun rasa wani bangare na jikin mu, kuma a yau mun samu wani bangare na jikin mu" Wata midwife a wajen ce ta share hawayen ta ta ce, "Allah Sarki, ku yi hankuri, Allah ba shi barin wani dan wani shi ji dad'i, Allah shi raya," "Ameeen" An gyara jariri, da mahaifiyar shi, Sultan ya yi wa yaro huduba da suna Muhammad Auwal,Sultana kuwa qin bari ta yi a aje yaro nesa da ita, in ba Mubaraka ce ta dauke shi ba, kowa ya dauke shi za ta yi ta magana a miqa shi, ba kunya ba tsoron surutun mutane. Kwanan su biyu a asibitin aka sallame ta, ta koma gidan Hajiya Ikee, nan fa Sultana ta ga gata, Mubaraka ba tare da wani tunani ba ta tattaro kayan su, ta taho gidan Hajiya Ikee,  Sultan ya ji dadin hakan matuqa. Ranar suna mutanen Tudun faila sun samu halartar sunan, an yi suna ba laifi, ba yabo ba fallasa. Bayan Suna Lamishi ta tattara sauran kayan Mubaraka ta aiko mata da su, tare da yi mata aiken Fatan alkhairi daga wajen Jameelu, yana ta mata dariya yake bata saqon, ya ce, "Mama 'Yabbuga ta ce dama haka ki ka so, ki koma gidan mijin ki, tunda ba su kai ki ba to gashi ke samu dama" "Kaiiiii ya Salam, matar ga ta iya sheri wallah," Sultan ne da ya shiga dakin da Mubarakan ke da zama a gidan ya ce, "Ai Jameelu na ke hwada maka harda roqo na ta yi wai na ce su Mama 'Yabbuga su maishe ta dakin ta" "Innalillahi Yah Sultan yaushe mun kai haka da kai" "Rannannn, ki tuna mana, rannan" Dariya Jameelu ya dinga yi, ya na jin dadin ganin farin ciki a fuskar yayar tashi ,sallama ya musu ya koma gida, Sultan kuwa cewa ya yi, "Tooo amarya ta, tunda yanzu kowa ya nutsu, mu ma ya kamata mu nutse cikin dausayin soyayyar mu ko? Yaushe za ki koma dakin ki? Nan dai dakin baqi na" "Ba rana, ba dai ka yi min sheri ba?" Dan tura baki ta yi ita a dole ranta ya ɓaci, ba tare da ta ji takun shi ba, ta ji an sumbaci lips din ta da ta tura gaba, da sauri ta kalle shi, dariya ya mata, sannan ya mata gwalo zai gudu, take masa baya ta yi, suka fita su na gudu su na dariya, dakin shi ya fada, ya na sane ya bar qofar a bude, ta na shiga ya mayar ya rufe, ya maida ta jikin qofar ya mata rumfa, kallon ta ya ke daga saman  idanun shi har zuciyar shi, ya na haddace duk wani tudu da kwari na fuskar ta,Itan ma da kallo ta bi shi, cike da wani irin yanayi da bata taba shiga kalar shi ba a rayuwar ta, murya can qasa Sultan yace, "Gudun mi ki ke yi haka?" "Ramawa zan yi" "Me za ki rama?" Shiru ta yi ta maida kan ta qasa, ta na wasa da rigar ta da ta kama ta gefen dama "Gani tau rama" "Na yahe maka" "Ni kuma ban yahe ba sai kin rama" "Ni dai nace na yahe" "Ni kuma na ce ban yahe ba" "Allah na yahe maka, ka ga ka bari na tai aunty Sultana na can qasa ita da Hajiya su na jira na na tai na goyi Yaya" "Ni kuma ga ni mijin ki ina so ki rama abinda na miki, ko ki bari na rama miki, sai ki koma" Shiru ta yi ta na kallon shi, cike da so da qaunar shi, "In rama miki ko?" Daga kai ta yi, a hankali,tare da runtse idanun ta, babu bata lokaci kuwa Sultan ya dora lips din shi saman nata, tun Mubaraka bata mayar masa, har sai data maida hankalin ta, da nutsuwar ta wajen rama abinda yake mata. A yammacin ranar Sultan ya samu angwancewa da amaryar shi Mubaraka. Hajiya da Sultana tunda suka ji shiru ba su bi sahun su ba, sai bayan da magariba ta yi, ba su ga Mubaraka ba, kawai sai suka yi sallar su, suka ci abincin su, suka bar musu nasu,ita da Sultan. Sultan ya so ya kira Sultana ta taimaka wa Mubaraka, amma ta qi sam, ta ce za ta iya kula da kan ta kar ya manta ba na farko bane ba, wanda shi ji ya yi kamar ba a taba mata wata hanya ba shi ya fara sanin ta 'ya mace (aikin d'inkin bature da cin kaji da kayan marmari kenan) , dan haka da taimakon shi ta gyara kan ta, ta gasa jikin ta da kyau da ruwan dumi, dan akwai komai da take buqata a dakin Sultan din, kayan ta ne kawai ke can dakin da baqin. Sai da ya bari qafa ta dauke, kowa ya haye sama, ya shiga dakin baqin ya tattaro komai na Mubaraka ya mayar dakin shi. Kafin ta gama shiryawa ya tafi debo musu abinci, ya na dumama abincin a microwave ya na murmushi,  ya na nan tsaye Sultana ta fito diban ruwan zafi a flask da take sha. Ganin shi ta yi ya nata zabga murmushi dariya ta yi, ta ce, "Ango ka sha qamshi, ni da na ji qamshin jikin ka ma na zaci Mubaraka ce, ashe kai ne" "Sultana baki da kunya ko?" Dariya suka kwashe da ita sannan suka tafa, "Bari kawai, Allah ya ma yarinyar can albarka, amma ni ina mamaki, an ce an taba mata fyade, amma ban ji wata alama da ta nuna hakan ba, ko dai dan ban san kan abun bane?" "Wataqila dan baka san kan abun bane, and akwai matan da suke da baiwa, kamar wadda ka ke fada yanzu ba zata taba komawa da budurcin ta ba, amma fa ba za a ji ta a bude ba sosai, sannan ka san matan garin ga dai da gyara ko? Na tabbata an gyara ta sosai, musamman da sun ka san me ya hwaru da ita a baya" Jinjina kai kawai Sultan ya yi, dan ya san me ya tarar, tabbas to iyayen ta sun masa qoqari matuqa. Abincin ya haɗa musu, ya mata sai da safe, ya ce ta shafa masa kan Auwal. Murmushi ta yi,ta na jin wani irin dad'i da farin cikin ganin annuri a fuskar yayan nata. Bayan sun ci abincin su,sukai kwanciyar su, Sultan ya rungume amaryar shi kamar an ce masa ga masu kilinafin matan mutane nan. ************************** Sai bayan wata biyu da haihuwar Sultana Hansatu ta samu zuwa can Tudun faila, dan yi musu gaisuwa, ta samu labarin an yi wa Mubaraka aure, nan ta nemi adireshin gidan aka bata, daga nan mijin ta abin son ta, ya kai ta gidan tsohon gwamna Halliru, ba ya jin nauyi ko ganin bata lokaci,in zai kai ta unguwa, ko ina ne kuwa. Mubaraka ta ji dadin ganin ta sosai, sun sha hira matuqa kafin Hansatu ta tafi. Tunda Hansatu ta je gida take bawa Hajiya Labarin Sultana, har sai da Hajiya ta ce, "Gaskiya da za su bamu ita Musa shi aure, da mun gode musu, maganar yaro kuwa ai shi d'a na kowa ne,na tabbata Musa zai riqe shi kamar shi ya haihe shi," Cike da murna Hansatu ta ce, "Kwarai kuwa, ki duba ki gani, yanda Yah Abdullah ke son su Ameenatu, yanzu hwa ba ya so na kira shi da kowanne suna sai da Baban Ahmad,diyan nan gaba daya sun mance da uban su, tunda daidai da rana guda ba na iya tuna sanda ya dauki dayan su, balle har ya musu wasa, amma shi har da su goyo, su doki, duk haka yake musu wasa indai shi na gida baya gajiya " "Allah Sarki, Allah shi yi muku albarka" ****************** An sha fama sosai kafin Sultana ta yarda ta auri Yaya Musa, abinda ya sa ta yarda ganin irin yanda yake son Muhammad kamar shi ya haife shi, shi ya ja ra'ayin ta, ta tabbata ba soyayyar nan bace da ake cewa, in zaka so bazawara ka so dan ta, ta tabbata wannan soyayyar gaskiya ce, dan wasu za su nuna suna son dan bazawara, sai bayan aure su yi ta rashin mutunci. Ba a wani ja dogon lokaci ba aka sha biki, amarya Sultana ta tare a gidan Hajiyan Hansatu, zama suke na mutunta juna, da karrama juna, tare da so da qaunar juna. Sultana bata taba ganin wani a gidan ya nuna wa Muhammad banbanci ba, daga manyan har yaran, hasali ma wata soyayya yake samu ta daban,saboda yaro ne mai kyau, da kazar kazar kuma ba shi da qiwa. Yaya Musa ya samu kulawa da soyayyar da yake fatan samu a rayuwar shi,ji yake kamar auren saurayi da budurwa suka yi da Sultana tsabar kulawar da take bashi. Sultana kuwa a koda yaushe qoqari take ta danne soyayyar Lawwali da ke binne a qasan ran ta dan faranta wa mijin ta mai tsananin son ta. ********************** Bikin suna ake ta yi, a gidan Hajiya Ikee, Sultana da Hansatu sune akan komai, Dan haka komai ya kayatar ya wadatu, ba wanda ya taba zaton Mubaraka za ta yi qiba, sai ga shi haihuwa daya ta zama masha Allah, wata yar kubul kubul da ita, gwanin sha'awa ,ta samu yarinya mace, an sa mata suna Ayshaa, sunan da Lawwali ke buri ya sanya wa diyar shi, in mace  ce, Sultana tai ta shagwaba ta na fadin an riga ta, dariya suka dinga mata, Mubaraka kuwa ta bata hakuri ta ce, "Next time ke kuma sai ki haifi Humairah" Dariya aka sake sanyawa cikin farin ciki, haka sukai ta nishadi, angon qarni na can tare da abokan shi,su na cin abunci. Tsohon gidan su Sultana da Lawwali kuwa, an maida shi islamiyyar matan aure, an saka mata Suna Muhammad Auwal Qur'anic recitation school, Mubaraka ce ke kula da makarantar da wasu malamai da suka d'auka. Su Mai Buruji da Lamishi da 'Yabbuga kullum da yamma Jameelu ke kai su ya maida su in an tashi. Tammat bi hamdu lillah. Nan na kawo qarshen labarin Oga Lawwali, ina fatan kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min,ya shafe shi cikin rubutu na da zuqatan wanda suka karanta, alkhairin da ke ciki Allah ya bani ladan shi, ya sa al'ummar musulmi su amfani da shi,Allah ya zaunar da ƙasar mu lafiya ya biya wa kowa buqatun sa na alkhairi daga kan 'yan qasar Nigeria zuwa shugabannin mu da su kan su 'yan ta'addan dan a daina kashe kashen da ake yi Ameen. *Haermeebraerh ce* (Hamibrah) *Haermeen Hammah❤️🙈* *Hameedah Sanusi Ahmad* *Ummu Fateemah wa Muhammad Muzakkir* ❤️