RUBUTU A KAN RUWA   بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* *Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya* *SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci. *AUTAR MANYA* *ALEESHATULKHAIR* kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏 FREE PAGE 1 Mafari...! Zubewa take kokarin yi cikin gigitacciyar kukan dake ratsa duk wani me sauraro, da sauri jama'ar wurin suka yunkura da nufin taro ta gudun mugun faɗuwa amma inaaa basu samu nasara hakan ba, a kan gwiwowinta ta zube tana rero kukan dake fita daga ƙasan zuciyarta, kukan da duk me sauraro ke tabbatar da lallai an yiwa wannan yarinya rashi me girma, babu abunda ya kai rashin mahaifi ɗaci sbd dashi ne ake ado, yau babu majinginarta babu bangon ta ya rushe ba tare da ta tsammatar mishi mutuwa kwana kusa ba, ya tafi ba tare da sun yi cikakkiyar sallama ba, gabaɗaya ta hautsine ta hautsina kowa sbd kowa ya kwana ya tashi ya san da irin fitinanniyar ƙaunar da mahaifinta ke mata haka ita ma girman ƙaunarta gareshi ma'auni baya iya aunawa yau ya tafi ya barta, a gabaɗaya gidan kowa ya dawo bata baki sede wannan kuka ba na bari kwana kusa bane.. Kaman yadda mutuwa take da wani ɗabi'a, ta kan ɗanɗana maka ɗacinta ne ka gigice a lokaci ɗaya amma duk inda aka samu kwanaki dole ka rungumi hakuri ka fawwala Allah lamuransa, ka cigaba da bin wadda ka rasa da addu'a Dukda ze kasance chan Kasar zuciyarka amma dole ka koma rayuwarka kaman koda yaushe, haka ta kasance a rayuwar matshiyar budurwa Ayusher, yau kimanin kwana huɗu kenan da ta rasa baffanta me ƙaunarta, kaman kullum tun bayan rasuwar tana zaune ne cikin kayan saƙi na Fulanin usul farare ƙasan ɗan ficiciyar rigar sakin wani jan riga ne da mahaifinta ya saya mata a chan birni har kala uku take anfani dasu, zaninta ta ɗaura shine daga kan shafaffen cikinta da kaman ba'a sanya masa hatsi, idanunta sanye da farin gilashi me kyau wadda ya ainihin fito da kyaun fuskarta, kyakyawar gaske fara tas da ita daga ka ganta da yanayin sumanta da tayi kitso biyu duka baya ta kuntosu ɗaiɗai ta gefen kafadunta har suka sauka kirjinta zaka san eh lallai wannan yarinya cikakkiyar bafulatana ce. Motsin Shigowar Nene be sa ta ɗauke idanunta daga inda ta kurawa ba tana ji dai ana ta hada hada da wasu baƙin masu gaisuwa sbd mahaifinta me jama'a ne har yau huɗu da rasuwarshi mutane basu daina tururuwar zuwa ba, amma hakan be sa ta motsa ba bare ta fito ayi gaisuwar da ita. "Indo!" Mahaifiyarta ta kirayi sunanta tana dafa kafaɗarta. "Na san rashin baffanki babban rashi ne da har Abada ba ze daena miki ɗaci ƙasan rai ba sede ki sani, da rai da rayuwa duk na Allah ne bawa iyakarsa yayi hakuri dasu ya kuma rungumesu a duk halin da ya same su, baffanki ba abunda ya so miki ba kenan kin san illar da hawaye kan yiwa idanunki taya zaki cika mishi burinshi na zama kwararriyar likita me taimakon al'umma idan kika rasa idanun gabaɗaya mamana? Ki daure ki tashi kinji aminin baffanki ne yazo daga chan birnin shugaban ƙasa. (Habdu ummu a vurta un hifnindira a nani?) yi kokari ki tashi ki fito ku gaisa kinji?" Kai ta gyaɗa kan cikin yanayin sanyin da ya aure ta a kwana huɗun wadda sam da ba haka take ba yarinya ce ta kwaramniya da magana, son mutane da yawan tambaya ga tausayi da iya mu'amala duk halinka Ayusher me iya zama da kai ne kuma ta san ta yadda zata bi baku batawa juna rai ba, bata taɓa shiga inda za'a wulakantata takalawa ne su futuk da suke rayuwa a jeji wadda gabaɗaya rugar nasu be haura gidaje ashirin da biyar ba, amma suna da matukar wadatar zuci, mahaifinta na matukar son mata karatun likitanci hakan yasa tun tashinta da kanshi yake kaita makarantar gomnati na kauyen dake gaba dasu in ta tashi ta dawo duk rugar daga ita se ƙaninta ne a makaranta wadda hakan ya janyo tsegumi masu yawa daga mutanen kauyen inda ake mata wani kallo na daban har a yanzu da take matakin aji na huɗu a sakandiri wato SS1. Kwatsam mutuwa ta ɗauke wannan gata nata taya burinsu ze cika? Taya zata taimaki al'umma idan aka gama watse wa aka barta da Nene wa ze hidimtawa karatunta? Wa ze iya kula da lafiyarta kaman Baffanta? Gashi jiya kanin mahaifinta da ze koma chan kudu ya ɗauke ƙaninta da take dan gani taji sanyi ya tafi dashi, mutuwa fa kenan! In ba mutuwa ba wa ya isa raba kan wannan gida me cike da tarin kaunar juna da sanin ciwon kai? Baffanta da ko yini a wani wuri se ya kama dolenshi suke yi amma daga rasuwarshi da kwana uku har an gangada ɗan shi kwalli ɗaya  namiji zuwa east. Idanunta da ta soma gani dishi dishi sbd zub da hawaye ya sakata dakatawa ta cire glasses ɗin idanunta wadda atake duhu ya mamaye ganinta dishi dishi take kallo, hawayen ta share tana kokarin maida glasses din a lokaci ɗaya ta yunkura don yin gaba se taji ta Buge mutum wayoyin hannunsa gabaɗaya suka yi ƙasa, a razane ta ja baya tana shakar sassanyar kamshin da tun dazu take mamaki daga ina ne ashe na baƙin gaisuwa ne. Da sauri ta duƙa ta ɗauko wayoyin tare da Miƙewa tsaye Allah ya sa babu abunda ya samesu, Z fold ɗin kawai ya karɓa bayan ya gama kare mata kallo ya zagaye ta ya wuce don bata gaisheshi ba bare ya tsaya amsawa kuma waya ce ya fito dashi me muhimmanci dole ya karbi Samsung din ya bar mata IPhone ɗin, daidaita kanta tayi tare da sallama ta shiga cikin falon na baffansu shimfide da jar babbar darduma irin na sarauta din nan, wata tsaleliyar macece zaune daga gefe sanye cikin rantsatsiyar lace da ya amsa sunansa ta yafe gyale, baƙa ce sede kyakyawa ce ba laifi se danna waya take tana ɗan murmusawa kaman ba gidan rasuwa ta zo ba. Ɗauke idanunta tayi ta sauke kan ɗaya matashin me sanye da shadda ruwan ƙasa kansa ba hula se ɗan gashi da ya tara, bata raba ɗayan biyu tsara yake da wadda ta Buge awaje ko ma tace ze iya girmanshi don wanchan murjewar ƙashi da tsawo ne ze nunawa wannan da yake me ɗan kiba, ɗauke kanta tayi ta sake mayarwa kan ɗaya matashin shi kam sanye da kananun kaya bakin wando da farin riga, shi kam tsiriri ne kuma baƙi saɓanin wannan da wanchan da suke farare. "Jam bandu mon na? On wari jam?" (Ina kwananmu? Fatan kun zo lafiya?) Duk ido suka zuba mata kaman sun ga nama ɗanya babu me jin yaren nata cikin su, Naina ta dubi Murad tace "kaine Fulani se ka amsata ai" Zaro idanu yayi yace "Matar yaya ai nima a suna ne se kalar fata amma babu abunda na iya gwara dae Yaya suna yi sossai da Ammah da Abba" Cikin hausar ta da be wani riƙe harshenta ba ta kara gaishesu suka amsa, amma Murad da aka ambata yafi bata kulawa da tausayawa ya ɗan mata nasiha, duban kakanta ta wurin uba tayi da wani kaninshi se amininshi ta gaishe su suka amsa cikin kulawa, yace cikin harshen fulatanci "Na san baki rasa jin suna Emran daga bakin mahaifinki ba ko?" "Eh malam ya kan ce min bashi da amini sama dashi babu sirrin juna da basu sani ba, sannan babu abunda ze iya nema daga wurinshi ya rasa a duniya, idan har na ganshi kaman na ga Baffa nane sbd shine amininsa guda ɗaya jal da ya zama jininshi, amma ban taɓa ganin shi ba in ze zo ya kan zo muna makaranta kuma be taɓa kwana ba kan a tashi mu dawo da yamma ya tafi" Anan ta dakata tana kallon matasan biyu har ma na wajen da ya dawo yanzu ya zauna ya ɗan kalli wayan shi da ta ajiye chan nesa da ita duk basu yi kama da waenda zata ce sun yi tsara da mahaifinta ba. "Aisha?" Ya kira sunan yana kallonta da oily eyes ɗin sa lumsassu. Da sauri ta amsa tana gaishe shi da harshen fulatanci, da turanci ya amsa yana mata gaisuwa sede sam bata ma fahimci me yake cewa ba sbd irin slang  ɗin shi ko wurin malamansu na sakandiri bata taɓa ji ba, shiru tayi abin ta. Sun ɗan jima sossai kan ya dubi Baba yace "Baba ina da wata alfarma da nake son roƙo, wannan yarinya mahaifinta na da buri me girma a kanta kuma idan har kaji Isma'il na maimaita min abu to tabbas so yake nayi wani hubassa a kai ne, duk nazari da tunani da nayi akan rayuwarta ba zan iya taimakonta a cikin wannan ruga ba, idan ba damuwa ina so a bani riƙonta in shaa Allah zaku sameni me riƙe amanarta har Allah yayi cikon burin mahaifinta" A razane take kallonshi da idanunta dake zub da ruwa zuciyarta na tsitsinkewa tunanin ta na kasuwa kashi biyu zuwa uku, taya zata fara barin mahaifanta ta bi mutumin da a yau ta soma kallonshi a rayuwarta? Taya zata iya rabuwa da mahaifiyarta a wannan gaɓar da take bukatar abokin kuka? Amma kuma burinta da na mahaifinta fa? Idan tana so ta kasance yadda mahaifinta ke so dole se ta bar rugar nan amma.... "Ai Emran baka buƙatar shawara da mu akan ɗiyar Isma'il duk abunda kaga ya dace se ayi" Da sauri ta kalli kakan nata ta ɓangaren uba dake magana, hawaye ne ya wanke mata fuska tana tunanin yadda zata tsallake ahalinta zuwa inda bata saba ba, mutuwa mai tonon asiri kuka ne ya kwace mata. Da kallo Naina ta bita tana tunanin abunda su Emran suka tattauna da wannan tsohon bororon har ya saka yarinyar kuka, ta san Emran ba wani faɗa mata zai yi ba hakan yasa ta taɓe baki, tsakani da Allah ma ta gaji da rugar se ƙarnin nono yake mata... Kaman Emran yaji kuwa yace su fara haramar tafiya. Shi ya fara Miƙewa ya isa gabanta ya ɗauki wayarshi kan cikin dattako irin tashi da sanin darajar na gaba duk talaucinsa ya duƙa gaban baba ya fiddo bundles na dubu daidai har guda uku ya ajiye ya miƙe ya fice baban na ta mishi adu'o'insu na tsoffi da godiya bayan duk tarin kayan abincin da ya zube. A jikin mota ya ɗan jingina yana amsa waya ɗayar hannunshi kuwa na daddana ɗayar cikin sauri da kwarewa, su Naina da suka gaji da tsayuwa ta kalleshi mijinta mai kyau ne, a kullum kara godiya take da ta sameshi ji take tayiwa mata dayawa zarra domin shi ɗin zaki ne a cikin maza, komai nashi cike da charisma da class yake aiwatarwa yanayin magananshi da tafiyar shi cike da ginshira shi ke kara burgeta dashi a ko yaushe, babu abunda ke bakanta mata rai irin miskilancinshi da har ita be bari ba, gyaran murya tayi tace "Dear me muke jira ne? Naga Murad da Nameer duk suna mota" "Aisha" Ya faɗa bayan tsawon minti ɗaya da maganar ta ba tare da ya kalleta ba. Yanke tsamannin jin wani kalma daga bakinshi tayi bayan ta tsura mishi idanu na sama da mintuna uku tana jiran jin cikakken bayani tace "ban gane ba Emran? Aisha muke jira? Me zamu yi mata?" Tsaki yaja yana Miƙewa daga jinginen da yake kaman ze ce wani abu kuma se ya fasa daidai lokacin da kunnuwansu suka soma jiyo musu kukan Ayusher kaman zata tsaga gidan, lumshe idanun shi yayi ya buɗe kn ya sake jn tsaki, baki sake Naina ke kallon Ayusher da mutanen da suka rakota da kullin kayanta cikin zani ta kalleshi "Emran ina zamu kai yarinyar?" "Shes staying with us from now on" "what????" Ta yi exclaiming ranta na dugunzuma wani bala'i na kunno mata, ya fa san yadda ta tsani ganin wata kusa dasu taya zata fara rayuwa da wannan bagidajiyar kauyen da ko hausa bata iya ba ita da bata ma jituwa da Ƴan aiki bare wannan kazamar? Daga mutuwan uba se a lika mishi wata yarinya? "Emran ni ce matar gidan kuma dole idan yarinyar nan ta bimu a gidana zata zauna don haka ni ban amince ba" Kallon gargadi yayi mata kan ya maida kanshi cikin harshen fulatanci yace ta shiga, se kuka take haka tana ji tana gani aka sanya ta a jibgegiyar motar ya zagaye ya shiga, Naina da bala'i ke cin ta ranta a ƙone cike da kyamar Aisha ta shiga tana wani manne wa da kofa, turaren ta ta fiddo daga handbag ta feffesa a motar ba wadda yace mata ci kanki wadda hakan da tayin kuwa yasa Aisha sake tsinkewa da sabon hawaye, wallahi mutuwa be yi ba... A hankali take sauke ajiyar zuciya idanunta na bisa bishiyoyi zuwa dabbobi da suke wucewa jefi jefi har suka bar rugar su zuwa karamar hukumar garin har suka dangana da cikin birnin yola zuwa jimeta duk ta san wuraren sbd jigilar asibiti da mahaifinta kasancewar an haife ta da matsalar ido wadda likitoci suka tsayar kan Fatar jikinta ne ke affecting idanun. A hankali motar su ta shiga Airport, bayan ɗan zirga-zirga se gata a gaban jirgi taka kafa tayi don shiga se ta koma baya da gudu tana zazzare idanu, ta gwada haka ya kai sau uku kan na huɗun ta saki kuka tana kokarin komawa da gudu hakan yasa mutanen da hankalinsu ke kanta kwashewa da dariya ciki har da Murad, Naina kam takaicin ace tare ma da ita suka zo yasa tayi ciki abin ta tunda mijinta ya jima a ciki Nameer ma bayan gama dariyar wannan kauyanci ciki yayi Murad ne ya tsaya yana kwaɓa mata hausa da ɗan abinda yake ji cikin fulatanci. Se da yayi da gasken gaske ganin kowa ya shiga ana shirin rufe kofa kan ya kamata kamar wata tsohuwa tana takawa da kyar tana hawa suna shiga tayi turus daga bakin kofa ganin yawan fasinjojin cikin jirgin kuma dayawa hanaklinsu na kanta ganin bororuwa da kayan saƙi cikin jirgi wadda hakan ya firgitata ta kwasa da gudu ta koma kasa me za'a yi in ba dariya ba wasu har suna kokarin yi mata video. Goshi Murad ya dafe ganin yayanshi ya ja tsaki ya miƙe ya fice daga jirgin cikin takunsa na ƙasaita da ginshira, yarinyar nan kar tayi yayansu ya wanke mata fuska da mari sbd saurin fushinshi da zuciya irin tashi don har shi yanzu da girman shi be gami yayan nasu tsinka mishi mari ba in har ya kai shi kololuwa bare ita wannan da ya karɓa amanarta a matsayin ɗiyarshi dole tayi hankali da Ya Emran saukinta ma ba sossai yake zaman Nijeriya ba.. "Ke!" Dakakkiyar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta wadda yayi sanadiyar kara mata tsoron ta a firgice ta miƙe tana ja baya a kuma tsananin tsorace ganin ya nufo ta gadan gadan... *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 6039380652 Keystone bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰                        🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA   بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* *Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya* *SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci. *AUTAR MANYA* *ALEESHATULKHAIR* kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏 FREE PAGE 2 "Wuce muje" Ya faɗa babu alamar wasa a lamarinshi se taji tsoro da shakkarshi fiye da yadda taji na jirgin, Dukda zazzare idanun da take haka ta yi gaba ya tasa keyarta har seat nata, air hotess yayiwa magana akan ta saka mata seatbelt dinta don ko sun nuna yadda ake yi sun kuma faɗa sun bada leaflet a duba wannan yarinya ba lallai ta iya ba, haka ko aka yi ita ta saka mata kan ya koma mazauninshi ya zauna, sam be kula irin maganganun da Naina ke yi ba ko nuna ya ji ma be yi ba bare ya kulata wadda hakan yake kara bakanta ranta ta kuwa ci alwashin yarinyar bazata zauna dasu ba sede ayi wacce za'a yi. Har jirgin ya sauƙa idanun Aisha a rufe suke ruf babu kalar adu'ar da bata yi ba, numfashinta ma sede ta riƙe na mintuna ta saki ta shaki kaɗan ta sake rikewa tsabar tsoro da firgici da aka sauka kasa takawa tayi sbd jiri, da taimakon wata air hotess ta sauko se kuma amai, kyawawan dogayen yatsunshi ya saka a Goshi ya ɗan murza sbd sarawar da kan nashi yayi, tsiririn tsaki ya ja wadda idan na kula yana daga cikin ɗabi'arshi amma fa shi kuwa duk duniya abunda ya tsana a mishi kenan... "Murad pls take care of her i've an emergency patient to attend now" Ya faɗa yana ɗan tafiya, kan ma ya ɓace First aid na airport din suka zagaye ta sanin da wadda take tafe, aka ɗan bata taimako kan Murad ya riƙe ta sbd jirin da take ji har suka isa mota, Naina ta cika pim kamar fulawar da aka sakawa yeast duk yadda ta so ya ɗauke ta a motar shi kamar yadda suka zo ya kiya yace asibiti ze yi ta jira Aisha Murad ya sauke su, ganin yadda suka fito ɗaiɗaikun mutane na kara nuna Aishar kamar ya zama musu wani sabon abu ne ganin bafulatana da kayan saƙi a cikin jirgi yasa tayi saurin kwala kiran ƙaninta "Nameer!" Tsayawa yayi ta ƙarasa har inda yake "i would rather follow a taxi than to rode a vehicle again with this gurl" "amma sis bakya kaunar taxi naga, sannan ai yarinyar nan bata isa ta hana ki shiga motar gidan inlaws ɗinki ba" Nameer ya faɗa Tana kwaɓa fuska tace "gwara min taxi din sau dubu baka ganin yadda duk tayi ta amai ewww, na rasa me ya hau kan dear da ya jajiɓo mana wannan kazantar in taimakonta ze yi yayi mana a chan kawai, mtseww" Nameer ya saka dariya yana tare musu taxi ya riga ya san sis ɗin tashi da mita sam abu baya wucewa a wurinta barin ma in bata so abun ba, taxi suka shiga tana cigaba da korafinta. Naina Adam shine sunanta ita ɗin cikakkiyar ƴar kasuwa ce da ta samu shedar kamallah digiri har biyu a harkar kasuwanci, hakan ya bata damar jan ragamar kanfanunnukan mahaifinta da ya kasance hamshakin attajiri a Arewacin Nijeriya, ƙaninta be zaɓi kasuwanci ba kuma su biyu ne kadai Allah ya bashi hakan yasa ta jajirce take kuma kai akan duk wani al'amari na companies ɗin su na *Adams industries* ita ɗin tana da son a san ita wata ce, kaman yadda Allah yayi ta me kyau tana son komai nata ya kasance me kyau kuma na daban ne hakan yasa a koyaushe in ta tuna Emran mai yaƙi take aure se taji kanta yayi sama, kaman duk duniya ba na biyunta. Naina bata da son mutane ko jansu a jiki a ganinta kowa yayi rayuwarshi yafi, ta tsani talaka bare wani suna wai talauci, ita kanta kawai ta sani se family ɗin ta, sam bata son ganin wani ya raɓe su har familyn mijinta kuwa. har Nameer ya ajiyeta kofan gida bata daena kananun mita ba ita babban haushin ta yadda yarinyar zata zauna dasu dindindin, ko da ta shiga gidan direct bangarenta tayi ta wuce bayi ta soma da cire kayan nan a cewar ta ya kwashi ƙarnin nono ta zube su cikin laundry bag dake bayin ta isa chan inda aka keɓe don wanka seda ta fara sakin shower ya jiƙe daga kanta har kafafunta a cewarta ɗauraye datti kan ta isa ga jaccuzi ta haɗa ruwa ta shiga tana relaxing, ta jima sossai kan tayi wanka a bayin tayi ta kwalkwale kwalkwalenta su skin care routine da dae sauransu kan ta fito ta sa karamar shirt da wando ta haye gado don baccin huce gajiya.. Tunda suka doshi cikin Layin take ta aikin kallon irin ɓarin kuɗaɗe da aka yi a gidajen da suke zagaye da Layin, babu gidan da zaka kirashi tsoho don kowanne fentinshi na kyalli da ɗaukar idanu, fari tas ɗin gidan da fence ɗin shi be cika tsai ba zagaye da electric wire sbd tsaro gabanshi ɗauke da wasu irin flower masu ɗauke hankali da kawatuwa, gate ɗin shi Black da yaji ado da gold taga Murad yayi horn kaman mintuna biyu taga gate din ya zuge da kanshi a hankali ya siɗaɗa motar ciki, baki sake galala take kallon gidan. Idan suka shiga birnin yola da Baffanta ta kan ce mishi waenda suke gidajen birni sun ji daaɗi kuma suna aljannar duniya bata san akwai inda ya take waenchan da take santi ba, gidan ba dublex bane flat ne da yake kaman an rakubeshi a dunkule a gefen fankacecen tsakar gidan da yaji ado da flowers daban daban, motoci basu wuci shidda bane a parking lot ɗin sede kowanne ka kalla ka san mota ce da ta amsa sunanta, dubanta Murad yayi ganin yadda take ta kallon cikin gidan da take ta hangen glass yafi ginin dake jiki ta waje yawa, irin glass me garai garai da kana iya hangar wadda ke waje ko yake ciki.. "Aisha zan tafi" "Ina zaki tafi?" Ta faɗa cikin gurɓatacciyar hausar ta, yana mata alama yadda zata gane da kyau.. "Babanmu ni da Ya Emran yana jirana akwai takaddu da zan kai mishi" "useni ta accam ha ɗo wala mo mi andi, yiwu saare mai bana ha (Ayya karka barni a nan babu wadda na sani, kalli fa gidan kaman a mafarki)" Ta faɗa idanunta na yin rau rau sam be gane ba shi kam, sede ya fahimci a tsorace take. "Matar Yaya na ciki, muje in raka ki parlor zaku zauna tare" Yana maganar ne yana alama da hannu sbd ta fahimta, kai ta gyaɗa Dukda ta kula matar ƴar wulakanci ce, ko da shi ke ba ita kadai ba har mijinta ma ɗan wulakanci ne wannan Murad din ne kawai me kirki, da in ya san baze iya kula da ita ba Meyasa be barta a rugar su ba, tana tunanin ne tana turo ɗan karamin bakin ta Red dashi sharrr. Seda Murad ya buɗe mata kofa ta shiga rungume da kullin kayanta kan ya juya ya koma da sauri sauri sbd Alhajinsu dake ta kiran shi. Tsayuwa tayi tana kallon farare sol ɗin sofas ɗin daga gani ba karamin taushi zasu yi ba, komai na parlorn daga fari se lighter Brown wadda ma kaɗan kaɗan ne mixture ɗin, dan kadan gefen gini da aka yi ado dashi se na carpert kaɗan, se na wasu vanity trays parlorn ba wani hayaniya, sallama tayi tayi shiru tun tana tsaye har ta gaji a hankali ta ɗosana ɗuwawunta kan kujerar ai da gudu ta miƙe jin suna shirin burmawa da ita tsabar laushinsu, gefe ta koma ta zauna daga ƙasan farin tiles ɗin tare da zabga tagumi. Wasa wasa tun tana saƙe-saƙenta har ta koma shiru a hankali ta juye zuwa abun tausayi sbd yunwar da ya fara sasakar cikinta tun safe banda madarar shanu tafasasshe da tasha bata ci komai ba gashi tayi amai, bata ji motsin kowa ba bare ta nemi agaji gashi har duhu ya fara rufuwa bata yi ko sallahr la'asar ba, hawaye ta fara akai akai tana sharewa sbd yadda suke zuba cike da tausayin kanta, me yafi mutuwa ciwo da firgici? Da yanzu suna chan da Baffanta da Nene da kuma zayyad(ƙaninta) suna hirarrakinsu da tsokanar juna cikin raha. A hankali ta kai kwance akan tiles ɗin da sanyin shi ke ratsa har cikin ƙashinta, jikinta na ɗaukar rawa, tafi awanni biyu cikin wannan hali kan a hankali ta soma jin sassanyar kamshi me ratsa zuciya da sanya natsuwa, kamshin da ta riga ta san me shi a yinin yau kawai sbd yadda yake da masifaffen daaɗi yana shiga hancin ta wadda yayi sanadiyar ƙara murɗawar cikinta da babu komai ciki, sam be kula da mutum a wurin ba sbd rashin hasken parlorn Ƴan kwayayen lantarkin masu kyau dake kunne wutar su ba farare bane wasu kaman Orange kaman Red haka dae wutar ya bada wani colour me duhu duhu haske haske. Tuntuɓe yaji yayi da kullin kaya chakk ya dakata a saninshi dae a nan kan hanyar babu abunda ze iya cin karo dashi, maida idanunshi yayi kan wurin se yaga kaman mutum a kwance a takure, da sauri ya miƙa hannunshi ya kunna fararen hasken wadda a take ya haske parlorn tarrr kaman rana oily eyes ɗin shi zube a kanta... "Aysher" ya furta sunan yana duƙawa ganganta "Ya Salaam" Ya kara faɗa da deep husky voice nashi "Me kike yi a nan? Don't tell me tunda kika shigo anan kike zaune?" Hawaye kawai ta sake farawa bata iya ta amsa shi ba, haka kuma bata iya kallonshi ba hannunshi taji a goshinta da sauri ya janye yana sake ambaton Allah, Ranshi gabaɗaya yayi baki kirin, amma Naina bata da hankali yanzu amanar da ya ɗauko kenan take wulakantawa tun daga yanzu a yau ɗin nan?. "Ni kam zan koma Nene ABBA" Ta faɗa cikin karyayyiyar muryarta wadda ya saka shi lumshe idanunshi ya buɗe, tana reffering din shi da Abba ne sbd haka Baffansu ke kiranshi a gabansu, ko da Nene ze yi hirarshi ya kan ce Abban yaran nan kaza ko kin san me Abban yara yace? Haka dae so Zayyad da su kan haɗu haka yake kiranshi shiyasa itama ta kira da hakan. Kallonta kawai yayi be bata amsa ba se ta kara sautin kukanta, dafe goshinshi yayi da tafin hannunshi ya ɗan murza kan ya miƙe tsaye yasa hannu ya dauki kullin kayanta, ɗayan hannunshi kuma ya sanya ya kama nata ya miƙar da ita sbd magana da baze iya yi ba, kaman rakumi da akala haka take binshi suka kutsa cikin gidan zuwa wani parlor se wasu kofofi da dining da aka rufe wurin da labulaye masu haske, komai royals ne anan kam golden da milk da suka haske parlorn, wani kofa daga farko ya buɗe suka shiga ciki, Brown set na Italian bed ne hade da wardrobe din shi da rabi madubi, dressing mirror da shoe rag, a tsakiyar ɗakin ya saki hannunta ya nufi wardrobe ya jefa kayanta ya dawo ya tsaya gabanta duk ya cika mata ido da faɗin kafaɗunshi, tsawon shi da idanun shi masu kaifi dake kanta, so yake yace taje tayi wanka kan ya nemo mata abinci da magani amma maganar na mishi matukar wahala. Tsaki yaja ya juya ya nufi toilet seda ya buɗe kofa kan ya kalleta ya yafito ta da hannu, a hankali ta fara takowa har ta iso ya wuce ciki ta bishi, da kallo ta bi bayin lallai kam wannan wai makewayi? Ta ayyana a ranta Dukda zafin zazzabin da take ji baki galala take karewa bayin kallo "Hey!". Ya faɗa bayan ya ɗauko bucket don ya san ba iya shiga jaccuzi zata yi ba, ba kuma iya anfani da shower zata yi ba, "This..." Ya nuna blue "ruwan sanyi ne, but if you turn to this.." Ya mayar Red "ruwan zafi ne, ki haɗa kiyi taking shower i will be right back" Daga haka ya fice, ta ƙarasa bakin tap ɗin ta mayar ruwan sanyi tare da sa hannunta se taji sanyi ƙalau, ta mayar jan se taga ruwan zafi na zuba har da turirin hayaƙi dariya ta saki ta ma mance tana jin zazzabi ta fara kalle kalle a fili ta furta "ko daga ina ake dafa ruwan a sako shi a tiyon nan kuma?" Bata da me bata amsa haka ta surka tayi wanka ta mayar da kayan da ta cire abunta ta fito a ƙasa ta zauna tana nazarin yadda zata yi sallah se gashi ya buɗe kofa ya shigo da sallama iyakarsa kan lips ɗin shi.. "Abba ina so nayi sallah ban san inda ake kallo ba" Ta faɗa cikin harshen fulatanci, ɗan kallon kayan sakin da ta sake mayarwa jikinta yayi ya ɗauke kai, ba tare da yayi magana ba ya je wardrobe ya buɗe ya fiddo sallaya ya shimfida daga ɗan gefen ɗakin yana fuskantar gabas ya dawo inda ya ajiye ledojin da ya shigo dashi, "karki sake zama a ƙasan tiles ɗin nan, wannan ɗakin ki ne as from today, sannan bana so na sake ji kin yi maganar komawa ruga, ni ba karamin mutum bane ba zan ɗauki alkawarin da na san ba zan cika ba, pray, eat and take this medicine ki hau gado ki kwanta..." Yana kai nan ya juya ze fita da sauri ta miƙe tana karewa ɗakin kallon da yanayin shirun da gidan ya ɗauka, ta fahimce shi sarai sbd da fulatanci yayi maganan hade da turanci kadan kadan so ta gane yana nufin nan ɗin ɗakinta ne kuma ita kadai zata zauna ciki irin wannan shirun da gidan da unguwan ke dashi? "ABBA" Chak ya tsaya ya juyo yana kallonta, se ta fara kokarin kuka cikin Muryar kuka tace "Tso..tsoro nake ji...ni ba zan iya zama ni...ni kaɗai ba..." Se hawaye sharr, hannunshi ya sa ya murza goshinshi tare da sakin tsiririn tsaki kawai ya juya ya fice. Sallah tayi tana kuka, ita kam bata kwana ita kadai ba kab rayuwarta ta saba ko yaya kana jin surutun mutane ko makota amma ji nan kaman makabarta? Kuma ta kwana ita kadai? Karar da wannan abu da aka makala a sama kaɗai ya isheta tsoro ga ɗakin kaman lokacin hunturu don sanyi, to ko dai yanayin Rugarsu da nan ɗin daban daban ne? Don ta dae san a kauyensu damina ne. Haka tayi Sallar a tsorace ta dawo ta zauna ta buɗe abincin, kura mishi idanu tayi ganin abubuwa daban daban gauraye da shinkafa gashi yayi kalar ɗorawa, se dankwaleliyar kaza a saman shi, kazar ta cire ta sa a murfi ta fara aikin tsince su carrot ɗin tana ayyana ko basu sani bane suka saka ko sun cuce Abban ba tare da ya buɗe ba suka saka mishi abubuwa har da ganye, ko karas bata gane ba sbd bata ci ba kuma bata saba ganin an yanka shi haka ba, bare su peas, green beans, baked beans, cucumber. Hanta kawai ta bari da shinkafar wadda hakan ya ɗauke ta sama da mintuna ashirin kan ta soma cin ɗan shinkafar da ta rage ta haɗa da kaza, Admiral A ya siya mata hakan yasa ta shanye tas sbd gardin nono da kuma kamshin shi da take ji, maganin da ya ajiye ta dauka ta sha se taji ta rasss se a lokacin ta tuna tsoronta ta soma zazzare idanu, gadon ta hau tunda yace kar ya kara ganinta a ƙasa ta dunkule tana mamakin wannan sanyi, neman zazzabin da ya rufeta dazu tayi ta rasa a take bacci yayi awon gaba da ita tana ta santin laushin gadon da pillown ga kamshi.. Bayan ya gama duk abunda ya san al'adarshi ce har ya kwanta se kuma ya miƙe ya yaye White duvet me taushi da ya shige ya sauka, a hankali cikin salon takunshi ya isa wani karamin drawer ya janyo ya fiddo wata karamar woofer me kaman Apple yana fidda blue light a ɗakin ya kunna akwai memory me full qur'an ciki ya kai baqara cikin kira'ar shuraim ya rage sauti ya fito, seda yayi knocking tukuna ya tura ya shiga tana chan dukunkune yaje ya ajiye bedside har ya juya kuma ya sake dawowa, ita kam kaman ƴa take a wurinshi ze kula da ita kaman yadda mahaifinta ze kula da ita har ranar da Allah ze fiddo mata miji tayi aure kaman yadda yayi alkawari don haka ze yi kokarin ganin ya rage miskilancinshi ya bata kulawa kamar yadda ze yiwa ƴaƴanshi idan ya haifa, duvet ya janyo ya rufe ta kan ya juya ya fita ya ja mata kofa. Idanunshi ya ɗan sakar mata na mintuna biyu daga inda take tsaye riƙe da kugu ya zagaye ta ya nufi ɗakinshi. "Emran me kake yi a ɗakin yarinyar nan? Meyasa ma ka ajiye ta anan din alhali akwai Boys quater?" Chak ya tsaya... *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 6039380652 Keystone bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰 🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA   بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* *Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya* *SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci. *AUTAR MANYA* *ALEESHATULKHAIR* kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏 FREE PAGE 3 "Naina!" Ya faɗa cikin Muryar gargaɗi ta san shi in akwai abunda yayi mugun tsana a ɗabi'arta shine mummunar fassara da kuma mitar ta, ita kishi kishi dae na banza da wofi, cigaba da tafiyar shi yayi kawai se yaji ta rushe da kuka, abunda yake saurin tsinka shi kenan baya so sam, Juyowa yayi ya dawo da baya ya sanya hannu kawai ya ɗauke ta suka nufi ɗakinshi a tare ba tare da ya ce da ita uffan ba. Kan gadon shi ya shimfiɗe ta kan ya bita ya matse a tsakanin hannunshi cikin kunnenta ya fara raɗa mata... "Kin dae san duk abunda ze sa ni hayaniya da ɗaga murya ba son shi nake ba, why a kullum burin ki kiga mun yi faɗa hun?" Narkewa ta sake yi a cikin jikinshi ita ta san kayanta da yadda ya iya ririta mace in yana yi dake, shiyasa take mugun kishin ganin wata mace ta raɓe shi kar ya sakar mata romon soyayyarshi garɗinta yasa ta raba su "Amma dear ai ni aka ɓatawa dole nayi magana aure fa muke da ni da kai, be kamata in zaka kawo wata ta zauna karkashin kulwarmu ka kasa shawartata ba, gashi yanzu da daren nan Kaje har ɗakinta alhali dae ka san ba muharramarka bace" "dake da gidan duk mallaki nane a tunanina ina da iko da ku duka, taimako nake shirin yi da aikin lada idan har ba zaki taimakeni akai ba please do not involve ur self, case closed." Kara shige wa jikinta yayi yana saka kanshi tsakankanin wuyanta yace cikin Muryar da ita kanta yaso hautsina ta chan ƙasan maƙoshi "I'm damn tired love a kula dani" Tana murmushi ta fara biye mishi nan da nan ta ƙarasa rikita shi don fa shi ta ɓangaren nan be san wasa ba kuma babu sauƙi, seda suka natsu suka yi wanka a tare ya rungume ta suka yi bacci. Washegari da misalin karfe takwas ya fito a shirye tsab cikin tsadaddiyar gezna me sheƙi navy blue an mata aiki da farin zare gefen hagu da kan aljihu se chan ƙasa gefe da gefen tsagun rigar, hannunshi ɗaure da rolex ɗin shi kafafunshi sanye da wasu half covers na FENDI baƙi sidik se sheki yake hakan ya kara bashi wani kyau da class na musamman, kanshi ba hula don shi ba gwanin saka hula bane, as usual kamshin shi na Khamar lattafa shi ya cike ɗakin da duk wani inda ze ratsa. Be bi ta kan Naina dake bacci bisa gadonshi ba ya fice tunda yaga yau bata tashi da wuri ba to bazata office bane, kai tsaye ɗakinta yayi yana kara duba agogon hannunshi, knocking yayi ya ɗan tsaya har tazo ta buɗe still kayan jiyan nan ne dae a jikinta cikin harshen fulatanci tace "Jam bandu na Abba?" Ya amsa da kalma ɗaya tak kan yace "je kiyi wanka ki sameni parlor." Kallon jikinta tayi ita ta san tunda tayi sallah tayi wanka tunda ba baccin safe ta iya ba take zaune shiru shiru har lokacin. "Nayi" Tayi saurin faɗa ganin ya juya don komawa parlorn, sake kallonta yayi kan yace "let's go" Ta san wannan kam Dukda yadda ya faɗa ɗin da kyar ta gane, da sauri tabi bayan shi tana ɗan kama jelar kitsonta ɗaya tana wasa nashi sbd yadda taji gabaɗaya wurin ya mata faɗi tsabar kwarjininshi tafiyar shi ta zubawa idanu cikin natsuwa da zaati kaman zaki, key ɗin da ya zara ba tare ma da ya duba wace mota bace ya danna ta nuna kanta ya nufeta ya buɗe ya shiga, itama da sauri taje ta buɗe gaban ta shiga ta takure se zazzare idanu take sbd firgici,  a natse yake jan motar suna ratsa tamfatsa tamfatsan gine gine na birnin tarayya har suka sadu da guzabe yayi ta kutsawa zuwa wani tamfatsetsen gida da tun daga waje ta jinjinawa kyau da tsaruwar gidan, ita dae tana maƙale jikin Window tana ta kalle kalle yayinda shi kuwa yake ta aikin amsa calls tana ta mamakin yadda baya gajiya se zuba turanci yake cikin kwarewa, inda Allah ya taimakeshi tented glass ne motar da an yi ta kallon Aysher Indo da kauyancinta. Gidan sama ne lafiyayyu guda uku a dunkule a wuri guda, gidan bashi da yawan shukoki kaman gidan Abba, amma ya tsaru. Parking yayi ya fito itama tayi saurin fitowa tabi bayanshi, lokaci lokaci sukan haɗu da ma'aikatan gidan suna kai mishi gaisuwa yana amsawa cikin kulawa sbd shi fa yana matukar mutunta ɗan Adam ko yaya yake, dayawa da suke mishi kallon me girman kai sam basu fahimce shi bane da irin tsarin rayuwarshi amma da ka fahimce shi zaka san mutum ne me saukin kai da taimako, ga tausayi ainun. Da sallama iyaka lips ya tura kofar parlorn ya shiga, wata kyakyawar matashiyar yarinya ce ta amsa tana me Miƙewa tsaye "sannu da zuwa big bro" "Asma'u ya kike?" "Lafiya ƙalau big bro" Murad da shima ya miƙe ya kara so ya miƙa mishi hannu yana cewa "an tashi lafiya Yaya?" "Alhamdulillah Ammi fa?" "tana sama ta haura yin walaha" Duba time yayi ya gyaɗa kai sbd almost 10 sun bata lokaci a holdup na garin Abuja sannan da nisa tsakaninsu da gidan iyayen nashi be ce komai ba ya nufi saman. Se a lokacin Murad ya kalli Aysher hannu ya ɗaga mata "ƴar bororo ashe tare kuke da yaya?" Murmushin sanayya ta sakar mai tana gaishe shi da fulatanci ya amsa da Hausa, ta gaida Asma'u da taji Abban ya faɗa itama cikin murmushi ta amsa da fulatancin da ta dage take koyo. "Ya Murad ina kuka samo ta? Ko da ita kuka dawo?" Asma'un ta faɗa tana sake kallon Aysher da irin kyaunta Dukda har yanzu ba wani girma ne tayi ba don bata da girman jiki, kyau ne dae da gashi masha Allah. "Ɗiyar Big bro ce ƴar wajen marigayi Ya Isma'il shine Big bro ya ɗauko ta riƙo" Wani tsalle Asma'un ta daka ta dire "yeeeyyy yanzu ne zan koyi fulatanci da tushe tunda daga Alhj har Ammi da Hajiya sun ƙi koyamin" Ita dae Aysher se kallon yadda Asma'un ke murna take, a shekaru zata iya cewa Asma'un nan tayi ishirin amma tana abunta kaman ƴar yarinya, kamu hannun Aysher tayi tace "ɗiyarmu zo zauna kina ta tsaye nan fa gidan kakanninki ne!" Da Hausa tayi maganan se Aysher ta ɗan yi murmushi ba tare da ta fahimta ba seda taga tana nuna mata kujera ta zauna "wani zama zata yi auta? Kin san Big bro sarai karki kaita ta gaida Ammi da Hajiya zauna kiyi ta zuba mata surutu" Uhmm ta faɗa tana Miƙewa ta rike hannun Aysher suka haura sama, banda kamshi babu abunda gidan ke fitarwa komai kal kal cike da kyau da tsari, ɗakin Ammi suka shiga da sallama. Tana zaune kan sallaya yana zaune daga gabanta ya tankwashe kafafu ba wani hira suke ba tunda suka gaisa suke zaune haka, Asma'u na shigowa tace "Ammi kallo ɗiyarmu so masha Allah, Namesake ɗinki ce ma" Kallon wa ya tambaye ki da Emran ya mata yasa tayi shiru, hannu Ammi ta miƙa mata cikin harshen fulatanci tace "zo nan ɗiyata, matso" Zuwa tayi ta kama hannun matar tana yaba kirkin su lallai Abba da matarshi kam nasu kaɗan ne har gwara Abban ma. Gaishe da Ammi tayi Ammi ta amsa cikin kulawa tana mata gaisuwar mahaifinta ta dinga yi mishi Adu'a Aysher na amsawa. "I will transfer some token to ur account, anjima ki ɗauke ta ki samar mata gurl stuffs, make sure u get anything in be yi ba just give me a call" Cikin murna Asma'u ta amsa don ta san zata samu kuɗi, Yayansu be iya aika da kuɗi kaɗan ba sam. Ammi tace "Ki kaita su gaisa da Hajiyarku.." A hankali Emran yace "Ammi ta fara karyawa pls" Ya faɗi hakan ne sanin a kauye zuwa yanzu sede abincin rana, shi karan kanshi aure ne ya sabar mishi karyawa a makare da yake gida ko seven baya kaiwa be karya ba. Kallonshi Ammi tayi ya fuske yana danna wayarshi bata ce komai ba har Asma'u ta fice da Aysher "yanzu a haka zaka iya riƙe marainiya?" Ta faɗa tana kallonshi, kanshi ƙasa ya amsa "Ammi in shaa Allah zan yi kokarin ganin ta koyi girki sbd ta dinga dafawa kanta" "kai kuma fa? Haka zaka ke zama da yunwa sbd wani tsari naku na banza?" Shiru yayi ya ma yi mamakin yadda ta iya maganar don ya santa in abunda ya shafe shi ne sede Hajiya ita bata saka kanta sam, yawanci in ze zo sede su gaisa su yi ta zama shiru in ya gaji ya miƙe ya fice. "Ammi bara na isa wurin Hajiya" Girgiza kai tayi tace "a gaishe ta" Miƙewa yayi ya fice ta bishi da kallo. A kan carpet ya samu Aysher tana cin jollof Rice da aka yi shi da nama zuku zuku, yayi washar se kamshi yake, Asma'u na zaune tana danna waya yayinda Murad ke kallon Tv "Murad" Ta Kira sunan yana dan tsayawa hannunshi ɗaya cikin aljihu "I will send some token to ur account u should find a very good school within Abuja on monday ka kai yarinyar nan, pls make sure the school is standard nd good" "Ok sir, in shaa Allah" Juyawa yayi da nufin tafiya part din Hajiya da sauri Aysher ta saki cokalin ta miƙe don binshi, Asma'u tayi hanzarin katse ta "zauna Aysher ki ci abincinki ba yanzu zaki tafi ba" Zama tayi, tsoro take kar ta mishi laifi ta lura magana na mishi wahala, shiyasa yake ta sha ma kowa kamshi yake magana ɗaiɗai kaman me kirge... Bayan ta gama Asma'u ta sake janta sama zuwa ɗakinta da ya sha kyale kyale komai pink su wallsticker ne su waye ne babu abunda babu, tura ta bayi tayi ta sake wanka ta bata towel bayan ta fito, ta ajiye mata manta ta shafa ta bata turare ta nunnuna mata inda zata fesa bayan ta gama ta ajiye mata wani dogon rigar atmfaarta da yayi mata kaɗan amma tana matukar son atamphar shiyasa take ta ajiyar shi, sakawa tayi masha Allah, da yake beda breast curve irin flay din nan ne se ya mata kyau be Mata wani yawa ba, dankwalin Asma'u ta ɗaura mata ta bata gyale bata iya yafawa ba sun saba yawo haka se gyalen ke ta faɗuwa tana rikowa amma masha Allah tayi kyau abunta. Gyalen Egyptian Abaya me walwalin dake jikinta Asma'u ta warware ta yafa a kanta ta zari car key ɗin ta, wayanta IPhone 15 pro max dake chargy ta zare tana dagawa fuskanshi ya kunnu zaro idanu tayi tana kallon yawan kudin da Big bro ya saka mata, kai ta gyaɗa tace. "Ah lallai Big bro an yi ɗiya" Fitowa suka yi zuwa ɗakin Ammi bata nan, kila ta sauka se suka sauka kawai zuwa kasa, anan suka sameta tana kallon sunnah Tv sallama suka mata tana maimaitawa Asma'u su shiga wurin Hajiya fa kan su bar gidan. Ɗaya building ɗin suka nufa Aysher bata da magana yayinda Asma'u ke da surutu sede bata iya fulatanci ba hakan ne yasa dole suke tafiyar shiru shiru, Da Sallama suka shiga parlorn wadda shima a tsare yake gwanin kyau da burgewa, wata kyakyawar farar mace ce zaune bisa carpet ta miƙe kafafunta tana ta aikin mita da alama da Abba take sbd ganinshi da Aysher tayi a kwance kan three seater dake facing matar tsawon shi yayima kujerar yawa don haka kafafunshi ya miƙe su a chan saman kujeran ya zubawa matar idanu se kallonta yake, sallamar su ce ya katse ta wadda hakan ya saka shi shima lumshe idanu. A ƙasa Aysher ta zube tana kwasar gaisuwa matar ma na da fara'a da son mutane a take ta sake da ita ta fara mata gaisuwar mahaifinta, daga nan Asma'u ta miƙe "Hajiya bari muje sayayya" "Toh Allah y tsare se kun dawo" Kan su amsa wayar Emran ta ɗauki tsuwwa, jin wayar wurin aiki ne ysa ya buɗe idanu ya ɗaga ya kara a kunne, mintuna biyu kan ya sauko da kafafunshi yana furta "subhallah! On my way pls do the needful, arrange everything in order..." Yana sauke wayan ya dubi Hajiya "Hajiya ina da emergency bari naje" Hajiya tace "hala lamarin babba ne bokan turai?" "Accident ne wai rodi ya shiga har cikin left abdominal artery na matar she needs urgent surgery i hope she lives..." Yana kai nan yayi saurin ficewa tana mishi Adu'a. Fitowa suka yi, a hankali Aysher ta tambayi Asma'u "Aunty Asma'u aikin me Abba ke yi?" Tunani Asma'u ta tafi kan tace "wai Alhajinmu?" Girgiza kai Aysher tayi "A'a Abbana!" Dariya Asma'u ta saka sossai.... *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰                          🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN          (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* *Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya* *SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci. *AUTAR MANYA* *ALEESHATULKHAIR* kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏 FREE PAGE 4 "Wai Big bro?" Kai Aysher ta dage daidai suna shiga hadaddiyar SUV lighter brown wadda ya kasance motar Asma'un ce, bayan sun zauna tana yiwa motar key tace "Ai Big bro babban surgeon ne da ba Nigeria kaɗai ba har ƙasar waje suna matukar ji dashi, duk wani harka da ya shafi tsaga mutum musamman a ciki to ya kware anan, na san Dukda ruga kike kila ba zaki rasa jin CITY CLINIC ba nan ne asibitin shi baya zuwa ko ina banda kasashen waje in kana bukatar aikinshi kayi booking appointment ka zo asibitin shi ya maka aiki, kai ko a Abuja babu asibitin da yake musu aiki, kuma kin san me?" Ta tambaya tana kallon Aysher da wasu bayanan ta fahimta wasu ko bata fahimta, girgiza kai tayi "Big bro na da zafi matuka a harkar aiki baya son sakaci da aiki baya yarda ka mishi wasa da aikin hakan ysa duk wadda yake aiki karkashin shi yake taka tsan-tsan da kuskure, sannan sam ba'a tsawwalawa a asibitin yana iya kokari wurin ganin da Talaka da mai kuɗi sun zo asibitin kuma sun ji daaɗi sbd da matukar wuya yayi aiki ba'a samu nasara ba, shiyasa kullum zaki ga yana asibiti ko ya tafi wata ƙasa Dukda tafiye tafiyenshi da sauƙi tunda se ayi booking daga Kasar waje a zo Nigeria yayi aiki a koma" Ajiyar zuciya Aysher ta sauke a ranta tana ji dama ita ce, wannan shine burinta da na mahaifinta sede tunda ta shigo Abuja ta fara tambayar kanta zata iya kuwa? Har suka isa shopping mall suka yi parking suka fito tunani take yayinda Asma'u ke ta mata surutu wani ta amsa wani tayi murmushi har labarin gidan seda ta bata... "Kinga Alhajinmu asalinshi haifaffen rugar ku ne, mahaifinshi me kuɗin gaske ne a cikin Fulani sbd ya mallaki dabbobi masu yawan gaske kama daga shanaye, tumaki, akuyoyi, zabi, kaji da dai sauransu, yana da mata har uku da mahaifiyar Alhajinmu itace uwargida amma Alhj shi kaɗai ne ya fita da namiji duk sauran ƴaƴansu mata ne, na biyun tana da yaya mata har biyar, na ukun ƴaƴa matan ta guda biyu se hajiyarsu Alhajinmu dake da guda Alhajinmu da kuma kanwarshi wacce ta rasu da jimawa bayan tayi aure ta haihu shima yana wurin Ammin mu ne da zama tun daga yayenshi har yau. Kakanmu Dukda be yi boko ba sede yayi sha'awar ɗan shi kwalli ɗaya tal yayi hakan yasa tun da Alhajinmu yayi wayau ya kai shi cikin birnin yola inda anan yayi karatu tun daga farko har ya kamallah jami'a ya karanci business, bayan bautar Kasar shi a wani company a Kano se suka riƙe shi a matsayin sun bashi aiki sede yaje ruga ya dawo, bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana aikin suka maida shi Abuja a wannan komawanshi da New appointment na promotion babanshi yayi mishi aure inda ya aura mishi Hajiyarmu ya dawo da ita Abuja. Sun ɗauki tsawon lokaci da Hajiya bata haihu ba wadda hakan ya kawo mata tsana a familyn mijin ta yadda bata isa taje ruga ta dawo cikin natsuwa ba, barin ma hajiyar Alhaji bata iya ɓoye ƙin ta Sam a ranta, daga karshe ta ba Alhaji umarnin kara aure, mahaifinshi be ja ba sbd a lokacin ma ba wani lafiya ta ishe shi ba, shi kam ya san iya biyayya Hajiya wacce ainihin sunanta Zaliha tana yi mishi, zaman su bata taɓa saɓa mishi ba wannan rashin haihuwa kuwa ya san daga Allah ne in lokaci yayi zata haihu saide hajiyar shi ta kasa fahimta, dole a wani zuwa da yayi suka tafi wurin dukiyar Alhaji dake chan wani ruga daban ya Ga Ammin mu ya yaba. Kama kama aka ɗaura auren su da Ammi, Hajiya tayi namijin kokari a zaman su sbd kowa ya sani muddin Kaga gida zaman lafiya ya mishi karanci mafarin uwargida ce kaman yadda idan Kaga yayi kyau to duk uwargida ce, ta riƙe girmanta ta kyautatawa Ammi fiye da tunaninki, ta janyo ta a jiki Dukda irin gargadin da dangin Alhajinmu suka dinga yiwa Ammi, itama dake ba me son fitina bace ta rungume kishiyar ta suke wanzar da zaman lafiya me girma a tsakaninsu. Ammi bata shekara ba ta haifi Big bro, a sunan Big bro babu irin cin kashin da ba'a yiwa Hajiya ba wadda har Ammi seda ta taya ta kokawa don haka se ta sakarwa hajiyar ragamar Big bro ta ɗauke idanunta kwata kwata a kanshi kullum in zasu je ruga to mitar hajiyarsu Alhaji shine yadda Aka bar Emran hannun kishiyar uwa, lokacin yayenshi tasa dole aka kai mata shi, mafarin amintarsu da mahaifinki kenan, sun taso tare a ruga don kama kama seda Emran ya shafe sama da shekaru huɗu a ruga yana rayuwa dasu sbd kawai a nesanta shi da Hajiya, a cikin wannan shekarun ne Allah yayiwa Alhajinsu Alhajinmu rasuwa, an raba gado an ba kowa nashi sbd yawan na Alhaji se ya fara wani tunani akai. Wasu ya sayar a lokacin shanu na da daraja sossai ya dawo Abuja ya samu fili ya fara gina campany na kanshi, wasa wasa se ga Alhaji ya tashi da ma'aikata babba ta yadda aka koma aka kwaso mishi dabobbinshi yayi paultry farm daga karshen companyn ya dibi ma'aikata da kwararrun turawa aka fara sarrafa madarar shanu, zuwa youghut, su madarar gari, su fresh milk da dai sauransu, hatta kyankyashar kaji da waye waye duk ana yi, bunkasar companyn yasa ya sake buɗe wata inda ake sarrafa fatun dabbobin zuwa abubuwa dayawa takalma, jakunkuna, da dai sauransu. A zaman Big bro a ruga kar kice da son iyayenshi kawai ba yadda suka iya ne don Ammi har ta sake haihuwar Ya Salma har ma an sakata play class Big bro be fara makaranta ba, da kyar da suɗin Goshi Alhaji ya lallaba mahaifiyarshi suka dawo Abuja ya sama musu gida na musamman ita da Asma'u kanwarshi da naci sunanta bayan rasuwar ta, sauran matan kam sun ƙi sbd yadda hajiyarsu Alhaji bata raga musu ko da wasa suka kama dukuyoyin ƴaƴansu suka cigaba da rayuwar su. Dawowar Hajiya nan yasa aka saka Big bro karatu yana gama primary Alhj ya fitar dashi waje inda a chan yayi secondary yayi degree na farko da na biyu, shi da Nigeria sede hutu kuma yawanci in ya zo ze je ruga sbd mahaifinki kawai ko yini guda ya kan yi ya dawo, a shekarar gama degreen shi na uku Allah ya karɓi Hajiyar su Alhaji ta aurar da Asma'u da shekaru masu yawa... Ammi kuwa bayan Ya Salma ta haifi Ya Nurain da Ya Murad, bayan haihuwar ya Murad da jimawa ne aka haifi Ya Naufal wadda mahaifiyarshi ta rasu wurin haihuwarshi se Alhaji ya karbo shi ya baiwa Ammi Dukda Hajiya ya so bawa se ta ƙi sbd Ammi ce kawai mahaifiyarshi ko da take raye ta kuma bada uzurin sashen Ammi ne da yara se ya fi sakewa, a lokacin Big bro na chan Kasar waje yana practical wadda daga nan ne za'a bashi matakin professor a harkar likitanci. Bayan zuwan Ya Naufal gidanmu da shekaru kusan biyar tukuna aka haifo ni, Alhaji ya mayar min da sunan Asma'u kanwarshi, kowa ji dani yake barin ma Ya Naufal tunda sunan mahaifiyarshi naci Maaama yake kirana yayinda sauran daga me Auta se Big bro da Asma'unshi kai tsaye... Ta faɗa tana ɓata fuska. Ehen Ya Salma tayi aure tana nan cikin Abuja itama da yaranta, Ya Nurain yana Cyprus tunda ya tafi karatu yaki dawowa sede zuwa ya auri wata baturiya yaransu biyu, kwararre ne a harkar ƙarafuna, Ya Murad na nan da Alhaji shi yake taimaka mishi a komai na companies ɗin su na nan don field ɗin shi kenan se Ya Naufal da yace shi irin aikin Big bro yake so, The young surgeon kaman yadda Big bro yake kiranshi, se Ni ta nuna kanta ina karatun harkar karbar haihuwa da kula da jariri wato unguwar zoma. Toh kinji tarihin gidan Zubair mai yaƙi da iyalanshi". Tana wannan surutun suna nan suna zagaye ne tana ɗaukan abubuwa yayinda Aysher ke tura chart ɗin, ya cika makil da abubuwa kama daga mayuka, turaruka, gowns, kananun kaya, atampha, laces, shoes da bags. Aysher na ta murmushi Dukda tana fahimta sbd zallar hausa take yi bata sa turanci se kaɗan kaɗan kuma ta fahimta sossai, Allah sarki hajiya ta ayyana a ranta, irin su Allah yayi musu tanadi me girma ranar gobe. Wurin biyan kudi suka tsaya Asma'u ta bada Atm card dinta aka cire ko rabin kuɗin da Big bro ya tura mata basu ci ba, komawa Asma'u tayi ta jidi choculates masu yawa aka saka musu a leda daban, daga nan Saloon ta kaita ana ta santin gashinta aka warware aka yi mata gyara na musamman, bata son kitso se aka bar mata kan a haka bayan an gama, daga nan suka yi wurin tailor ɗin Asma'u ta fidda mishi atampha da laces ta bashi kudinshi suka yi akan express ne rana irin ta yau zata dawo ta karɓa ta kai mata gidan Big bro. Daga nan gida suka dawo a gajiye likis ga yunwa don ma sun yi sallah a Saloon, la'asar da ake kira yanzu kawai suka yi suka nemi abinci Ammi kam tana chan wurin Hajiya don ta kan je a matsayinta na karama su yi hirasu kan ta dawo. Bayan sun ci abinci suka sake bajewa duk wani abu da suka saya wadda Aysher bata san anfanin shi ba seda Asma'u ta nuna mata, wani shakuwa suka yi na nan take hatta shaving stick seda ta nuna mata yadda ake anfani dashi da cream ɗin veet da ta saya mata na shaving, abu kaɗan se tace "ɗiyarmu ki dage ki zama yar gayu kika wanku ba karamin gwara kan samari zaki yi ba" Se Aysher tayi dariya ta ce "kai Auntyna" Wannan Auntyna da take faɗa ke fasa kan Asma'u take kara ƙaunarta, se tace "Ba wannan kaɗai ba ɗiyarmu Big bro baya harka se da Ƴan gayu baki ga Aunty Naina ba? Kaman zata chanza fata sbd kyale kyale da gayu?" Aysher murmushi kawai take tana ayyana yadda zata saje a cikin matasan gayun Abuja, taji daaɗi kwarai zuwanta gidan don da dare da driver ze maida ta harda kwallarta Asma'u tace zasu dinga ziyartar juna kar ta damu, dama bata zuwa gidan ne sbd Aunty Naina se tayi ta dagawa mutane hanci kaman tafi karuna arziki, amma zata ke zuwa sbd Aysher... Ko da suka iso drivern shi ya taya ta shigar da kayayyakinta har parlor, me gidan na zaune matar kwance kanta akan kafafunshi yana anfani da waya tana ɗan mishi hira jefi jefi, ya sauya kaya zuwa kananu wadda suke matukar amsar shi su ɓoye shekarunshi, da idanu Naina tayi ta bin tulin ledojin har drivern ya gama shigowa dasu kan ta kalli Aysher ta juyo ta kalli Emran "wannan fa?" Se a lokacin ya ɗaga kai ya kalli kayan kan ya kalli Aysher da ke gaishesu ya amsa ya maida kanshi kan wayar, ganin babu wadda ya amsata yasa ta miƙe ta nufi kayan tayi ta bubbudewa tana mamaki harda super sheraton zanin da yayi 200k yanzu? Ga egyptian Abayas na 40-40k har kusan bakwai, man shafawa ma kaɗai na CreaVe aka saya mata. "Emran waennan kaya duk na wannan village girl ɗin?" In dutse ya tanka to ko Emran ya tamka ko kallon ta be sake yi ba, kokarin tattare kayakin take cikin muryar gargadi yace "Ki ajiye mata kayanta Naina, wai whats wrong with you ne?" "Ko de whats wrong with you ba! Taya zaka kashewa wannan yar kauyen wacce ko anfanin kayan bata sani ba irin wannan kuɗi? And ina magana ka ba banza ajiyata a gaban yarinyar salon ta yi ma kanta kallon kan mu ɗaya?" "Naina! Naina!!" Ya kira sunan yana kallonta, hawaye ta fara tare da zubar da kayan tayi ball dasu ta wuce kaman iska zuwa ɗakinta, idanunshi ya lumshe. Duƙawa tayi ta tattare kayan ta mayar leda sam bata ji wani haushin matar gidan ba, taji dae rashin daaɗin ganin yadda fuskan Abban nata ta nunawa damuwa, a nan ƙasa ta tsuguna bayan ta gama mayar da kayan leda, sam be san tana wurin ba se chan ya buɗe idanunshi don Miƙewa har ta fara tunanin bacci yayi a hakan ne ko yaya se suka haɗa idanu, saita Muryar shi yayi yace "Da wani abu ne?" "A'a, dama zan ce ne na gode Allah ya saka da alkhairi ya kara buɗi" Da Ameen ya amsa tana nan tsugune kaman ta tambayi wannan matar patient din na dazu se bata yi wannan katsalandan ba taji yace "se da safe ko?" Tayi saurin Miƙewa tana cewa "se da safe" A hankali tayi ta tattare kayakin har ta shigar, a tsakiyar ɗakin ta zube su kan ta yaye gyalen ta ta isa gaban wardrobe se kallon kanta take tana mamakin wai itace wannan, nace tukuna ma. A natse tayi ta shirya kayan tana tuna yadda tsarin na Aunty Asma'u yake tana shirya nata tsab se ga ɗakin ya fito kaman na Ƴan mata, tsalle tayi ta faɗa kan gado tana jin daaɗi, ta jima tana juyi kan ta yi toilet ta ajiye kayan wankanta da su shaving stick din, tayi alwala tazo tayi isha'i, zuwa wardrobe tayi ta buɗe tana tuna abunda Asma'u tace "kin ga anan birni, waennan night wear ake kiransu akwai na matan aure akwai na en mata shiyasa na ɗauka miki riga da wando riga da wando dogaye, da daddare duk kayan dake jikinki zaki cire ki saka su se kin fi jin daaɗi, sannan babu maimaita kaya kina cire na jikinki ki saka shi cikin basket na wanki, in ta kama ma duk dare kan ki kwanta kiyi wanka ki sa turare zaki ji yadda zaki ji daaɗin bacci a wannan rana" Murmushi tayi ta dauki sabon towel shima seda ta jadadda mata dashi ake wanka in an fito a goge jiki se a shafa mai kan a shanya shi a sa kaya, kayan jikinta ta cire ta haɗa da na saƙinta da ta sanyo a leda ta zuba cikin basket da ta gani irin shi a ɗakin Asma'u na kayan wanki, bayi ta shiga ta farke sabon sosonta ta buɗe shower gel kaman yadda Asma'un ta nuna mata, Allah ma ya sa tana da kwakwalwa bata manta duk zantukan Asma'un ba, wanka tayi da ruwan dumi ta fito ta shafa mai sama sama ta fesa turare kaman yadda ta nuna mata yadda ake sawa tun kan su tafi mall, ta sanya Cotton riga da wandon ta se taji wani daaɗi na ratsa ta, se shakar kamshin jikinta take haka ta kwanta a gadon tare da lumshe idanu bacci me daaɗi ya ɗauke ta... Be bi ta kan Naina ba ya wuce ɗakinshi yayi shirin kwanciya ya kwanta abun shi. Hawaye take tsakanin ta da Allah "Mommy wai kinga abubuwan da yake yiwa yarinyar nan? Ni abubuwan ma basu dameni ba, ya kaita duk inda ze kaita sannan ya mata na tsani yarinyar ba tare da na san dalili ba" "wai yaushe kika zama haka ne? Ina ke kika gaya min yadda ya dinga lallaba ki akan in ba zaki taimake shi akan yarinyar ba ki fita harkar ta? Wannan abunda kike yin shi ze sa ta raina ki, ki kama kanki a matsayinki na me ilimi kuma matar gida, tun yaushe baki maida ita ƴar aikin da ya ƙi samar miki ba!" Shiru tayi tana nazarin maganan maman tata, hakane kuma fa, kuma ta san fushinshi bashi da kyau shiyasa be cika yi ba don in ya birkice kaman wadda ya sha shaferin Fulani, zata fita harkar yarinyar ta kama abunda ke gabanta tunda ta riga ta zame mata ƙashin wuya. Sun ɗan kara tattaunawa da mommy kan ta miƙe tayi wanka ta shirya cikin wasu sexy nighties ta nufi ɗakinshi don bashi hakuri irin ta masoya, ta san kayanta cikin lokaci kankani ta samu ta saukar da fushin suka sha baccinsu ita kanta ta san mijinta na son ta to me na wani damun kanta akan yar kauye?.... *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰 🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN          (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* *Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya* *SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci. *AUTAR MANYA* *ALEESHATULKHAIR* kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏 Jira jira jira lanta Ina Zaki Naga kina sauri aa larai kyale ni yanxu zamanin idan kin ga mace ta zauna ita taso gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata Aa wanan shaharren campany da suke taimakawa Mata masu son Fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida Akan farashi me Kama da kyauta Zaki jiran ki kawai lantis inda da wata yar marainiya 10k din zanje Naga ko zan samo abun da zan Fara Mai da taro sisi So kike ki Fara sana'a ko Kuma har yanxu baki gaji da tambayar megida kudin biki da na suna Yana Sha Miki kamshi ba to idan kin shirya Nima na shirya tsab domin baki kayana sari akan farashi sauki kema kiji ki nime naki Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944 Sai kunzo *FREE PAGE 5 Washegari da wuri ta tashi sede bata yi wanka ba, ta gaji da zaman ta dubo choculates da Asma'u ta jida mata ta fara sha, jin daaɗin su ya sa tayi ta shan abunta har taji ya isheta, ƙishi take ji don haka ta miƙe ba tare da ta damu da neman dankwali ba gashinta se rito yake daga tsakiya da aka mata parking ta fito, blue Cotton nighties din nata se ya mata kyau kaman ƴar baby, fuskanta banda farin glass dinta babu komai, a hankali ta nufi inda tafi tunanin kitchen ne jin gidan yayi shiru sossai. Tana sa kanta ta tsaya chak tana karewa bayanshi kallo, bata shiga mamaki ba seda ta fahimci me yake yi, girki fa yake yi kaman, baki ta saki tana kara zura idanu don tantancewa ina namiji ina girki? Ta ayyana tana kama haɓa, shi kam be ma san da mutum ba, yana sanye da farin karamar shirt da ya kama shi ya fidda kakkarfar surarshi da three quater Black me aljihuna dayawa, ya gama soya irish yana soya kwai gefe kuma ruwan zafi na tafasa a kettle. Tunani take ta shiga ne ko ta koma kuma kishin ruwa take ji, ita dae wannan abun kunya ne namiji a kitchen abunda bata taɓa gani bane a gidansu, bata tunanin ko ruwan zafi baffanta ya iya dafawa, to ina matar gidan? Ta tambayi kanta, tana shirin juyawa ya juyo se suka haɗa idanu... A jikinshi yaji kaman mutum na tsaye wurin hakan ya saka shi Juyowa se ya kalleta, ya ɗan yi mamakin sauyin da ta samu a kwana biyu kacal da Shigowar tata birni, a ladabce ta gaishe shi ya amsa yana cewa "yunwa ko? Breakfast is ready" Ji tayi wani sabon kunya ya rufeta, ina ma da ta iya anfani da waennan abubuwan nasu kuma ta iya girkin en gayu? Ina zata bar Abbanta a kitchen yana musu girki suna mata? "A'a diyam mi ho'ata (ruwa zan ɗauka ne)" Frigde ya nuna mata ta ƙarasa ta ɗauka se taji ya ce. "Wait" Dakatawa tayi, ya haɗa mata tea ya daura a gefen tray da ya ɗauko ɗan ƙarami gefe ne dauke da irish da kwai da ya soya se ya zuba mata ketch up daga gefe incase bata iya taci ba zata barshi a wurin, ya riƙo trayn yazo ya mika mata. Karɓa tayi bayan ta ajiye ruwan da ta dauka a kai "Na gode" Ta faɗa tana me ficewa sum sum sum Allah ya gani bata ji daaɗi ba. Daki ta shiga ta ajiye trayn ta fara ci kuma yayi daaɗi sede shayin ya mata kauri kuma ita kam be ji sugar ba se gardin madara, haka dae ta shanye ta kuma cinye abincin tass yayi daaɗi, trayn ta dauka ta kai kitchen babu kowa yanzu hakan yasa taje ta wanke ta mammayar inda taga en uwansu kan ta koma ɗakin ta tayi wanka, riga er kanti ta saka baƙi me dogon hannu ta koma gado ta kwanta.. Haka ta yini shiru shiru se chan around 3 yayi mata knocking ta tashi taje ta buɗe leda ya miƙa mata ta karɓa tayi godiya, abinci ne a ciki kala biyu kila har na dare, taliyar taci ta bar tuwo da Miyar egusi da yaji naman se chan anjima ta sake kwanciya, sallah kaɗai ke dagata shirun ya mata yawa, haka dae ta kai dare taci tuwon ta fiddo abubuwan ta zuba cikin dustbin na kitchen ba kowa ta ɗauki ruwa ta koma ɗaki. Washegari monday tana sane da yau ne Murad ze kaita makaranta da wuri ta tashi ta shirya ta sa Abayarta guda ɗaya colour purple da ado sossai White ya mata kyau sossai, ta yafa gyalen kan gashinta da ta taje ta sake kamawa yadda taga sun mata a Saloon, ta samu wuri ta zauna tana jiran tsammani. Bata jima da zama ba kuwa taji an mata knocking Da sauri ta isa kofar ta buɗe se ta saki murmushi ganin Murad ta gaishe shi shima ya amsa yana me tsokanarta ina kayan saƙinta ko yanzu kan mage ya waye? Ta bashi Amsa da ko yanzu zata iya sakata ta shiga ko'ina ai ba'a gudun asali, murmushi yayi suka fito a tare bata haɗu da duka ahalin gidan ba suka fice. Ko da ganin irin tsaruwar ginin makarantar ma ta san ba makarantan wasa bane ba kuma na yaran talaka bane don da alama ze yi kuɗi motoci kawai take gani manya manya ana tsayarwa yara suna fita maza da mata suna shiga, yanayin uniform din ya ɗan sa ta rage marmarin nata, Maza kam nasu yayi don dogon wando ne ruwan toka se farin shirt da jacket me ɗan kauri kaman suit amma akwai ratsin ruwan tokar daga wuya da kuma hannu, nectie ɗaure daga ƙasan jacket din se tambarin makarantar daga kan jacket din, amma matan kam skirt ne shima ruwan toka me tattara iyakarshi gwiwa se farin riga da jacket ɗin, wasu socks ɗin su ya haura har saman gwiwa yayinda wasu socks ɗin su iyakarshi idon sawu kuma kawunansu babu dankwali dukkansu. A baya take binshi har office na principal suka shiga cikin harshen turanci suka gaisa ya mishi bayanin kawo sabuwar daliba, duk wani abu daya kamata a take ya biya mata, aka kira wani malami yazo ya mata interview "ba laifi yarinyar tana da kokari sede akwai matsalan magana da turanci da kuma dae waenda ba za'a a rasa ba, za'a barta SS1 ɗin amma a shawarce a kara mata da lesson teacher da ze na taimakonta a karatun" Malamin ya faɗa bayan tambayoyi da yayi ta mata wasu ta amsa wasu kuma bata sani ba. Godiya Murad yayi mishi aka kawo mata uniform da littatafanta suka fito, a mota ta dubeshi tace "Yaya ka kaini wurin Aunty Asma'u" Ta faɗi hakan tana kallonshi da alamar roƙo "ke rabani da ya Emran, baki san baya son wuce gona da iri a abunda ya shafe shi ba ko? Balle ma ko na kaiki family house Auta bata nan tana school itama" Bata ji daaɗi ba kuma shirun gidan ne bata so, wani shopping mall suka tsaya a tare suka shiga ya duba mata school bag da sandals da wasu socks duk tayi mamakin kudinsu Dukda kyaunsu kaɗai ya isa ya sa ka san zasu yi tsada ba irin na kauyensu ba, ba'a maganar Rugarsu don ba kasuwa bane dasu a chan, kayan tea ya saya se suka zaga wurin kwanoni waenda yawancin su na fashewa ne a cikin glass glass ya saya mugs guda uku ko wanne da ɗan plate ɗin daurawarshi a kwali aka basu ba wadda ya nuna ɗin ba, se kuma taga ya saya mata bottles har biyu masu kyau pink da blue. Yana parking gaban wani hadadden gidan abinci ya ce "Yaya yace baki karya ba in sama miki wani abu yana sauri ne yana da theater da safen, Meyasa ba zaki shiga kitchen ki samarwa kanki abunda zaki ci ba?" Ya faɗi hakan ne sanin cewa babu wadda be san Naina bata iya komai a harkar kitchen ba, Yayansu kuma ya tsani me aiki kuma haka suke rayuwarsu a cewar shi tunda yana son matarshi ya wadatar ba ruwan kowa da sha'anin gidan shi. "Abubuwan ne ban iya anfani dasu ba" Ta faɗa cikin gurɓatacciyar hausar ta. "Zan faɗawa Auta ta samu lokaci tazo ta kokkoya miki kin ji ƴar Fulani?" Ya faɗa yana kwashe kayayayyakin tana taya shi da wasu suka yi cikin gida fuskarta dauke da dariyar tsokanarshi. Har ɗakinta ya ajiye mata kan ya mata sallama ya fice, arranging komai tayi ta kara gyara ɗakin kan ta buɗe abincin da suka saya din shinkafa ce da miya me kaza se plantain, ta ci ta koshi kan ta kwanta ta sha baccin ta, ba ita ta farka ba se azahar tayi sallah ta zauna a wurin babu wani abunda zata yi ga shirun yayi yawa se ta faɗa tunanin Rugarsu da Baffanta Allah sarki duk daaɗin wuri babu kaman gida, kuka tayi tayi kaman wacce aka dake ta seda taji ya isheta kan tayi shiru. Anan ta kwanta kan sallayar ta sake bacci se la'asar ta farka tayi sallah, tana nan zaune taji knocking. Miƙewa tayi taje ta buɗe hannunta na ƙasan glasses dinta tana kaikaya idanunta dake radadi sbd kukan da tayi dazu, ganin shine yasa ta gaishe shi ya amsa yana ɗan kallonta har kaman ze yi maganar anan se kuma yace "zo" Ya juya tabi bayanshi har cikin parlor, a kujera ya zauna ta samu wuri daga ƙasa ta zauna yace "ya kuka yi a makarantar?" Dukda yaji komai daga wurin Murad sede tausayinta ne ya ɗan tsarga mai ganin tayi kuka ya kuma san zama shirun nan ne da bata iya ba yake damunta, zaman gidansu se su, matarshi in ba office ba to bacci shima kuma ba zama yake ba yo to ko zaman ma yake ina ya iya dogon surutu? Nan ta fara bashi labarin yadda suka yi daga fitar su har dawowarsu harta kara da ko ta ɗauko mai uniform din ya gani? Yace ta bari, suka dan yi shiru kan yace "me yasa kika yi kuka? An miki wani abu ne?" Da sauri ta girgiza kai tana mamakin yadda ya sani "u know ur condition right? Ko kina so ki makance gabaɗaya ki kasa cika burinki da na mahaifinki?" Nan ma ta girgiza kai da sauri "words pls" Tace "A'a" cikin sanyin murya "Good kar in kara gani kin yi kuka, karɓi" Ya faɗa yana miƙo mata bunch daya na 1k Miƙewa tayi taje ta karɓa tana mamakin abunda zata yi dashi. Shiru yayi na mintuna har kusan biyar kan a hankali kaman me kirgen words yace "Na sa an saya miki kayan tea ne saboda ki dinga karyawa dashi da safe, kudin nan u should use it kina break dashi a makaranta in ya kare se ki faɗamin" Jujjuya kuɗin tayi, a Rugarsu in tayi tsanani ne Baffa ya basu Ashirin na break amma ina zata kai wannan ita? Kuma harda in ya kare tayi magana? Godiya tayi mishi sossai da Adu'a ya amsa da "Ameen" Kan ya miƙe ya nufi ciki har ya kusa barin parlorn ya tsaya tare da Juyowa "Ki dinga fitowa parlor atleast zaki kalli ko Tv ne" Har ta gyaɗa kai se kuma ta yi saurin cewa "Toh" Ya juya ya shige. Bata tashi ba se ta fara kallon tvn, tana nan zaune har aka magarib ta miƙe kenan don shiga ɗaki shima ya fito ba tare da yayi magana ba ya fice da alama masallaci za shi, ita ɗaki ta wuce taje tayi alwala tazo ta yi sallah anan ta zauna har aka yi isha ta gabatar kan tayi shirin kwanciya, choculates taci ta sha ruwa tayi baccin ta abunta. Da sassafe ta gama shirin ta saide ta kasa fita a haka barin ma gashinta dake reto a bayanta wani iri take ji Dukda nata socks ɗin yana da kauri sossai kuma har gwiwarta, wardrobe din ta ta buɗe ta duba hula fari ta cusa gashinta a ciki se ya zamana gaban goshinta ya ɗan fito gashin ya kwanta a wurin yayi lub, fitowa tayi bayan ta sha tea, a parlor ta same shi yana tsaye Naina na tsaye daga gefenshi sanye cikin wasu peach suits na mata da yayi matukar amsar ta kanta karamin gyale ne ta ɗan yafa, takalmin kafanta kuwa ya kai 5inches a tsawo White kaman yadda gyalen kanta ma White ne haka fashion ear rings din ta ma White ne, wow matar ba laifi ta iya ɗaukar wanka ta ayyana a ranta kan ta gaishe su cikin girmamawa, shine kaɗai ya amsa Naina kam ko ta tanka. Ɗan kallonta yayi from head to toe, Naina ma ta kare mata kallo tana ayyana yadda uniform ɗin ya karɓi yarinyar yayi mata kyau ainun, ɗauke kanshi yayi yace "kin karya?" "Eh na sha tea" "akwai driver a waje he will drop u" Da sauri ta fice bayan tace mishi ta gode sbd mugun kallon da Naina ke aika mata, tsaki taja tace "Don Allah dae akan maganan mu pls pls" "kin san dae ba zan bar aiki in tafi wata kasa na tsawon kwanaki ba ko?" "Sbd buƙatuwar mu zaka iya mana, its something that would help us all" Ɗan pecking goshinta yayi yana sa hannu a kumatunta ya ɗan shafa tare da jan iska yana sanya lip din shi na ƙasa a baki na seconds kan ya saki yace "Babe lets talk in mun dawo Ok?" Idanunta da ta ɗan lumshe ta buɗe tare da gyaɗa kai ya riko hannunta suka fito, har lokacin su Aysher basu tafi ba, tsayawa yayi yana tambayar drivern ya? Yace yana sa ruwa ne a motan kaman ze yi maganan Meyasa be yi da wuri ba kuma se ya fasa ya juya ga Naina da ta kalli motar da ya bayar don kai yarinyar makaranta na seconds wata Camry ce 2020 edition, ɗauke kai tayi ta buɗe tsadaddiyar motar ta ta shiga tana daga mishi hannu seda yaga fitan ta kan shima ya shiga nashi Black BMW a kusan tare motocinsu ya fice. Ko da suka isa makarantar godiya ta yiwa drivern tayi office na principal kaman yadda ya faɗa mata a jiya in ta zo nan zata je, ta gaishe shi ya amsa, kan ya kira wata malama a waya cikin mintuna ta zo yace "Miss Veronica this is ur New student Aysher Isma'il pls introduce her to the class" "Ok sir" ta faɗa kan ta dubi Aysher tace su tafi, a baya ta bita har ajin nasu single single seat ne a ajin amma suna da ɗan yawa don zasu iya yin ashirin da biyar, a gaban class ɗin ta tsaya suka miƙe suka gaishe ta bayan ta amsa ta basu izinin zama suka zauna kan ta faɗa musu ta kawo musu sabuwar class memeber ne hope zasu karbeta hannu bibbiyu, suka amsa kan tace Aisha ta gaya musu sunanta da kanta, tana ɗan ɗari-ɗari ta faɗa, seat ta nuna mata daga gefen Windows amma be mannu da Windows ba sbd wucewan malami tace ga seat ɗinta ta zauna, zuwa tayi ta ajiye Jakarta ta zauna nervously. Cikin awa ɗaya da rabi da tayi a ajin malamai uku sun shiga sun fita, maths, biology da kuma physics bata wani fahimci abunda suka yi din ba don fa ba'a fara term din da ita ba so an ɗan wuce ta amma dae ta maida hankali, tana nan zaune bayan shuɗewar awa da rabin tana ta kallon dalibai dake shiga da fice ana ta hidiman break, wasu yan mata uku suka zo suka tsaya a kanta, ɗaya na gefe tace "Ina faɗa miki yanzu duk ajin nan zasu daena ganin kyaunki se na wannan, Allah ya sa ma bata da ilimi don Abun se ya miki yawa, har muka kare jenior ba'a samu wacce ta fiki kyau ba se anan?" Ɗaya dake ɗayan gefen kaman tana cikin alhini tace "hmmm akwai aiki Maryam" "ya isheni haka!" Ta daka tsawa cikin masifa tana sake karewa Aysher kallo cikin tsananin jin haushi. Ita dae kallonsu kawai take har suka tafi fuu, me abun fushi don wani ya fi ka kyau kuma Allah na? Ta tambayi kanta sede babu me bata amsa, Miƙewa tayi ta fice daga class ɗin a hanya ta tsayar da wata tana mata tambay la da Hausa, yarinyar tace cikin harshen turanci "in an kama ki kina hausa u r dead" Hannunta ta ja ta kaita cafteria ta saki ta juya ta tafi. Meatpie ɗaya ta saya da Nutri milk bata kashe dari bakwai me kyau ba ta ajiye chanjin ta ci ta sha kan tayi class ganin an buga yara na ta gudu don shiga azuzuwansu, Miss Veronica ce ta shigo. Har ta fara english se wadda aka kira Maryam dazu ta ɗaga hannu, Miss vero ta bata damar magana "Miss vero ina ba'a amince da saka komai a kai ba a wannan makaranta?" "Yes dear" Miss vero ta amsa "then Miss is that girl different? Me ma sunanta Aysher Abi Fatima?" Tayi maganan cikin izgili. Miss vero ta dubi Aysher tace ta cire abun kantan, zaro ido tayi se tayi ta yawo kai banza a makarantar?? "I Said remove the cap in ur head Aysher.." Duk aka zuba mata idanu ganin ta fara hawaye se Maryam da kawayenta ko in ce yan gidan ta suka kwashe da dariya har da tafawa... *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰                          🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN          (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* *Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya* *SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci. *AUTAR MANYA* *ALEESHATULKHAIR* kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏 *Aleesha collection* ''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?" "a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata'' ''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi'' Hajiya ta zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar mai gida ko saurayi kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai sauki ke ma ki je ki nemi na ki. Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944 Sai kun zo FREE PAGE 6 A hankali ta kai hannunta ta fara zame hular sbd kama kanta da yayi garin zarewa ta haɗa har da ƴar karamar ribbon da ta kama gashin dashi tuni gashinta ya baje yana yauƙi shi kaɗai kaman haɗin baki Ƴan ajin suka yi ihun "wooooow" Da sauri Aysher ta zare ribbon din ta sake fara kokarin kama gashin idanunta cike da hawaye, Maryam dake kallonta ranta ya sake baƙi kirin ina ma ace yarinyar bata da gashi da sun sha dariya, ta tsani competition se gashi ta samu wacce daga zuwanta ta tsole mata idanu, makarantar suna da wani ɗabi'u na turawa kaman contesting na model of the school, face of the school, festivals, field trip da dai sauransu. Su kan zabi face of school ko model ne daga js 1 har Ss3 za'a fidda mutum ɗaɗɗaya, in an samu six a cikin wannan six ɗinne za'a fidda ɗaya ayi mata picture da uniform kala kala a mammana a duk hallway na makarantar, ita ce wannan kambu ke hannunta be taɓa fita ba amma ga dukkan alama wannan yarinyar zata kawo mata cikas cikin al'amura yadda take ganinta wata goddess of beauty. Ita dai Aysher tana nan zaune tana kallon malamai don kallo zata ce sbd yadda gabaɗaya take tsarge ba wani mai da hankali take ba har aka tashi karfe ɗaya da minti ashirin, cafteria ta koma ta sake sayan snacks ta nufi inda aka tanada don ajiye motoci a nan ta samu driver ɗin da ya kawota ta buɗe ta shiga tana gaishe shi, shima gaishe ta yayi suka nufi gida. Se dare ya kawo mata abinci tayi godiya, haka rayuwarta ya cigaba da tafiya abunda ya chanza shine zuwan malamin dake mata islamic da yamma hakan ya rage mata kaɗaici, kuma ba laifi tana kokarin ganin tayi picking karatun, kan sati ya ƙare ta ɗan yi rama sbd matsalar Maryam ta zame mata bully, har aikenta suke cikin izgili da raini, har wani tsoron Maryam din ne ya shige ta na masifa ko muryarta taji se jikinta ya hau rawa, hakan ya samu tasiri ne sanin cewa duk wadda ta gani a makarantar ta san ɗan wani ne saɓanin ita da alfarma taci har Allah ya kawota nan ɗin, sannan tana da zurfin ciki shiyasa bazata iya faɗawa kowa ba to yo ko ta so faɗa din ma wa zata sanarwa? Babu. Yau Jumma'a tunda suka tashi daga school ta dawo gidan tana kwance idanunta a lumshe ko uniform bata cire ba, banda hawaye babu abunda take sbd irin fusgan gashinta da su Maryam suka dinga yi a chan baya wurin garbage na makarantar, ta aike ta shawarma taje ta kawo shine wai Meyasa ta sayi me Sausage bata san bata ci ba, suka dinga gayamata maganganu marasa daaɗi har da fisge mata gashi, wani irin sarawa kanta ke yi.. Buɗe kofar ɗakin taji an yi da sauri ta share hawayenta tare da Miƙewa zaune, a take ta saki murmushi ta sauƙa da wuri taje ta rungume Asma'u "Aunty Asmy sannu da zuwa" "yauwa ɗiyarmu, me ya faru na ganki so silent haka? Yanzu ko uniform baki cire ba tunda kika dawo?" Asma'u ta faɗa tana zama bakin gadon ta ɗakin kal kal, itama zama tayi tana cewa a hankali cikin hausarta "Kaina ne ke ciwo shine na ɗan kwanta ko ze lafa" "sannu ɗiyarmu, baki sha magani ba?" Kai ta gyaɗa ina zata ga wani magani yau kwananta uku daga matar har mijin bata sanya kowa a ido ba, driver ɗin dake kaita school dae kan kawo mata abincin dare bata san wa yake sanya shi ba. "Akwai firt aid a kitchen ai muje ki sha maza... Tsaya ma ke ga fa dinkunan ki nan ya gama kinga yadda suka yi kyau?" Ta faɗa tana fiddo kayayyakin daga cikin leda, da sauri Aysher ta fara dagawa tana yaba kyaun su gaskiya yayi kokari, wani batik Red nd peach ta ɗaga ya zuba mata adon Red lace a jiki sannan an yi mata tail kaman me zuwa dinner haka, fitted ne ya mugun yi mata kyau tace "kai Auntyna bari nayi wanka na sa wannan gaskiya ya min kyau" Dariya Asma'u tayi tace "ciwon kai har ya ware kenan ana ta santin kaya" Murmushi kawai tayi ta shige toilet wanka tayi tana feeling sulɓin skin ɗin ta sbd yadda take samun kulawa na Mayuka da abubuwan wanka, ramarta kuwa bayanna kyaun surarta ya kara, hancin ta ya kara tsawo idanunta suka kara girma, a gaban madubi ta zauna tana shafa ƙasan gashinta da scalp din yayi Red sbd fusgan da ya sha. Wani abu me zafi ta haɗiye kan ta shafa mai tana kallon Asma'u dake zaune tana ta dannan waya, bayan ta gama ta fesa turare ta ɗauki rigar ta saka wow wow wow, ita kanta ta yaba da yadda yayi mata mugun kyau, barin ma da ta kama gashinta sako sako ta ɗaura dankwalin daga gaban gashin baya da gaban goshinta dake kwance lublub ya bayyana. "Auntyna!" Ta Kira Asma'u da hankalinta ke kan waya, ɗagowa tayi se ta zaro idanu "wooooow i got a fine daughter, ke kinga yadda ya miki kyau? Yanzu muje ki sha magani" Miƙewa tayi suka fito suka shiga kitchen, First aid ta ɗauko ta duba pcm ta bata ta kuma ce mata ko gaba zata ji wani ciwo akwai magani anan tayi anfani dashi. "Aunty Asma'u Don Allah ki koyamin yadda ake anfani da wannan" Ta Nuna gas ɗin ta faɗa ne sbd ta gaji da cimar da take samu tana missing abubuwan su na ruga kuma shi take so amma bata iya anfani da abun ba tana kuma tsoro shiyasa bata yi kiriniya ba.. "Kinga har na manta kuma wlh Ya Murad ce min yayi in zo in koya miki sbd ki samu abunda zaki ke ci na san matar gidan ba girki ta iya ba, ina ma izzarta ze barta shiga kitchen" Ita dae Aysher bata ce komai ba. A hankali Asma'u ke koya mata, kunna gas ita dae taga wani abu kaman bindiga kuma wai ashana se jujjuya shi take, bayan nan ta nuna mata ɗayar da ba se da ashana ake kunna shi ba kana murdawa ze kawo wuta, se suka ɗaura ruwan zafi, locker locker take buɗewa tana nuna mata abubuwa se mamaki take chan tace "Auntyna yanzu da ba'a dafawa basa ɓaci?" "Ruɓewa kai sede a zubar, shiyasa lokaci lokaci ze sa a turo ma'aikatan gidanmu su kwashe ya saka sabbi ke farkon auren su fa har shinkafar garar Aunty Naina ya zama gari basu buɗe buhun ba, kina taɓawa ze wargaje sbd ajiya" Murmushi kawai Aysher tayi amma zuciyarta fal mamaki, shinkafar tuwo suka fitar ba wani tsinta suka wanke suka zuba cikin ruwan da suka ɗaura suka ɗan sa muciya suka juya kan suka rufe, komawa gaban frigde na kitchen ɗin suka yi, Buɗewar ma da yake ba normal bane seda Asma'u ta nuna mata frozen chicken, fish, beef gasu nan birjik se kayan miya babu abunda babu a gyare suke tsab cikin ziplock daban daban sun kankare har dusa dusa suke. Kaza Asma'u ta fiddo ta sa a cikin bowl da ta sanya Aysher ɗaukowa ta ajiye kan ta zari ziplock ɗaɗɗaya ta dibi kayan miyan da zata buƙata, suka koma gaban blinder wadda na buchimix ne a hankali ta nuna mata yadda ake anfani dashi, ita kuwa tana dauka a kanta tace "kai na gode Auntyna kinga yanzu zan yi duk abunda na san zan iya ci" Murmushi Asma'u tayi tace "kin ma yi kokari ai sati guda kina nan kina ta kame kame duk kin rame". Dariya Aysher tayi tace "ba fa kame kame Abba yana kawo min abinci" "da ke da Abban duk kuna cikin wani hali" Tayi maganan cikin alhini wadda ya sa Aysher sakin dariya. Ɗaya frigde din da suka buɗe kayan madara madaran kamfanin Alhaji ne jibge se Aysher taji sha'awar shan nono me ɗauke da dakkere. "Auntyna akwai turmi kuwa?" neman turmi suka fara da kyar suka samu, Ayusher ta koma inda taga hatsi a robobi masu kyau ta dibi gero, ta baya suka fita bayan Asma'u ta sa kazar da ta fiddo ta sa mishi spices ta ɗaura kan dayan gas ɗin, ruwa take zubawa kadan kadan cikin geron tana surfa shi har ya surfu, a bakin pampon bayan suka wanke shi tas suka rairaye duk wani ƙasa dake tare dashi, ta ɗan baza shi suka koma kitchen tuwon Asma'u ta bar mata ta tuke ita kuma ta komawa kazar, ta zazzare ƙashin tas kan ta zuba mishi ruwa da manja ta sake wani haɗi da daddawa tayi adjusting seasoning din kan ta rufe ta dawo wurin Aysher tana nuna mata yadda ake kulla tuwo a leda don ta tambaye ta tace duk abincin da ake kawo mata in tuwo ne se ta ganshi a ƙulle a leda ya ake yi? Shine take koya mata. Bayan sun gama tace "bari na duba gero na in ya sha in daka" "kaii wani irin daka kuma ga fa buchimix blender dutse ne kaɗai ba zaki markade a ciki ba, komai yana yi" Cikin rashin amincewa tace "dakan hannu ai yafi daaɗi" Ita dae Asma'u bata ga wani bambanci ba haka ta bita suka koma ba wani yawa kuma abunka da wadda ya riga ya saba a take ta dake shi ya zama gari suka tankade suka koma kitchen. Lokacin Miyar ta gama nuna yadda ya kamata sbd sirrin kuka na cikin nunar shi, kaɗawa da whisk Asma'u tayi be yi kauri ba yayi daidai se kamshi yake, namar kazar yayi daga daga a cikinshi, ta kwashe a ɗan namiyar kular da suka zuba tuwo. A bincikensu suka samu gammo irin na kaba ɗin nan da Fulani kan yi, kila ma daga cikin kayayyakin kyautar en uwa su na kauye ne suka kawowa matar yayan da alama ko sanin anfanin shi bata yi ba, harda kwarya me ɗan girma da fai-fai da ludayi na asali, wankewa Aysher tayi don duk yayi kura tunda ba anfani ake dashi ba taje ta buɗe frigde se ta tsaya tunani. Asma'u tace "matsa je ki murje dakkeren don ni ban iya ba bari na fiddo madarar da naga Ammi na hadawa idan zata yiwa Alhaji kawai dae nashi ba masu sugar bane" Komawa tayi ga garin geron in ta baɗa ruwa se ta murza ta murza ta ɗaga kwaryar ta kaɗa shi tsakiyar hannunta take yake shure wa a hankali hankali tana fiddawa har ya ƙare, Asma'u se kallon ta take, lallai yarinyar ta samu horo me kyau don tana da tsabta, dama Ammi kan ce mata in ta ganta tayi wani abu Fulani ba'a san su da kazanta ba, bata tabbatar ba se yanzu ji wannan daga Ruga take amma tsabtar ta wanda ma yayi karatu ba lallai yana dashi ba anan, a steamer Asma'u ta saka musu shima tana nuna mata yadda ake har ya dahu, madarar ta zuba kala har uku a cikin kwaryar kan suka zuba dakkeren, Asma'u ta ɗauko kankara ta zuba da sugar kaɗan ta kara flavour ɗan kaɗan take ya bada wani kamshi na musamman. Se zumudin son sha Aysher ke yi Asma'u ta hanata suka kwashe komai suka kai dining, suka dawo suka gyara kitchen din fes kaman yadda suka same shi, kan suka koma dining din kofi da cokali Aysher ta ɗauka taje ta dibi damammiyar nonon. "Yanzu ba zaki bari ki fara cin abinci ba?" Shagwaɓe fuska tayi tace "Ni dae se na sha damimmayar Nono tukuna in iya cin wani abu, a andi no mi wairi kuje ɗo(kin san yadda nayi kewar abin nan kuwa? Hmmm) Tana soma zubawa aka dannan door Bell, Asma'u dake cin tuwonta tace "ɗiyarmu duba kofar nan" "To Aunty Asmy bari na gama zubawa" Se dariya Asma'u ke mata kaman ze gudu? Seda kuwa ta gama zubawa ta sa cokali tayi tasting tana lumshe idanu kan ta nufi kofar rike da kofi da spoon din ta. A hankali ya fara sauke idanunshi bisa kofin da take ta kaɗa cokali a cikinshi kan ya ɗago zuwa dogon wuyanta dake bayyane, ɗauke idanun yayi ya mayar fuskanta da yayi fayau, murmushi ta sakar mishi a bazata, ɗauke kanshi yayi tare da lasar lip ɗin shi yana jin zazzakar muryarta na cewa "Abba sannu da dawo..." Bata ƙarasa ba sbd Naina da ta fito ta bayanshi ta hankade ta a bazata tuni tayi baya zuwa ƙasa kofinta ya hantsila ya zube mata a jiki daga wuyanta zuwa kan kirjinta, sanyin ya ratsa ta wadda a take ta lumshe idanu ta fara hawaye sbd ta matukar firgita..... *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰 🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA   بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* *Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya* *SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci. *AUTAR MANYA* *ALEESHATULKHAIR* kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏 *Aleesha collection* ''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?" "a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata'' ''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis  marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi'' Hajiya ta  zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar  mai gida ko saurayi  kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai  sauki ke ma ki je ki nemi  na ki. Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944 Sai kun zo FREE PAGE 7 "Naina? Ya subhallah! Are u out of ur sense me wannan?" Ya faɗa yana shiga cikin parlorn, Asma'u da ta kara so wurin tayi saurin duƙawa tana taɓo Ayshern jin tayi shiru kaman wacce ta suma ko wani abu taji Nainan na cewa "Yes, am out my sense tunda idanunka sun rufe, yarinya ba gidan ta ba na ubanta ba muzo mu tsaya muna danna door Bell sama da mintuna biyar har ka koma ka ɗauko keys naka daga car da ka bari kan ta wani zo ta buɗe kuma ta tsaya akan hanya, akan dalilin me? Tana da gadon gidan ne ko da kuɗin babanta aka haɗa aka gina?" Juyawa tayi kan Aysher da Asma'u ta ɗago ta, tana aika mata wani banzan kallo tace "Mayya kawai" Daga haka ta ja tsaki tayi wucewarta Dafe goshinshi yayi ya ɗan murza kan ya ja tsaki, idanunshi akan Aysher da ta share hawayen fuskanta ya ɗan kalli wuyanta da duk Damammiyar nonon ya ɓata ya ɗauke kai yace "Je ki wanke jikinki" Asma'u haushi ne ya zo mata har wuya, shikenan abunda ze ce? Ji fa maganganun da matarshi ta gama faɗa, dama sun san ba iya tsawatar mata yake ba amma kuma ai wannan wulakanci ne, cikin Muryar kuka Aysher tace "Kayi haƙuri" Kan ta juya ta nufi ɗakin ta, tausayinta ne ya kama Asma'u, ita ya kamata a ba hakuri amma shi take bai wa. Ɗauke idanunshi yayi daga kallonta bayan ta rufe kofar ya sauke kan nonon dake zube yace "Ammi ne ta aiko ki dashi?" Ta san yadda yake matukar so, kuma duk sadda ze shiga gida se ya sha na Alhaji idan Ammi tayi, kusan abunda kaɗai yake sha a kofar Ammi kenan don na Hajiya baya mishi daaɗin na Ammi. "Aysher ce tayi" Sake kallon Nonon yayi se ya nufi dining inda yaga kwanoni. Asma'u kuma ta soma gyara wurin, bubbude kulolin yayi, baze iya cewa ga sadda yaga kuloli haka akan dining ɗin gidanshi ba, kai be ma taɓa gani ba sbd abubuwan da yake dafawa daga kwai, doya, dankali se ɗan spaghetti su kuma daga tukunya se plate ne, amarcinsu ma ba a Nigeria suka ci ba shiyasa ba'a aiko musu da abinci ba, sannan Asma'u ma baze ce ta taɓa zuwa gidan nashi tayi ko mintuna goma bane ze iya kirga sau nawa tazo amma yanzu yadda ya gantan nan ya san ta jima kuma me yiwuwa ita tayi girkin. Dama yunwa yake ji banda coffee daya sha a office tun safe be ci komai ba gashi yanzu almost to 3, don yana sauƙa Juma'a Naina ta kirashi akan motar ta ya tsaya shine ya biya ya ɗauko ta suka barwa machanic motar. Zama yayi yana jiran Asma'u, bayan ta gama gyara wurin tazo ta soma zuba mishi abincin, a ranta tana raya eh ai mune kake yiwa muzurai, idan kaganmu a wuri ko Hajiya sede tayi serving naka amma idan bama nan kana iya shiga kitchen ka girka ka kaiwa wata katuwa har kan gado, kaman ta ja tsaki amma ta san halin shi baya so kwata kwata a ja mishi tsaki nace Toh wanzami baya son jarfa akwai wadda yskai shi jan tsaki kuwa? Ai ko tsaka ya sara mishi. Nonon ta zuba mai a wani bowl me garai garai ta tura mishi ta zauna ta cigaba da cin abincinta, a nan ne ta gaishe shi ya amsa yana cin abincin da cokali. "Tun yaushe kike nan?" "Tun 12:30 nazo, na kawowa Aysher ɗinkunanta shine ta roƙi na koya mata anfani da abubuwan kitchen nan" Kai ya gyaɗa, tuwon ya ture Dukda yayi daaɗi sossai ya janyo bowl din ya fara shan furar, wow ko na Ammi se haka ko da shike baze yi mamaki ba Fulanin ruga ce. "Aysher kam lafiya? Duk zumudin shan Nonon kuma ya tafi ne?" Ta faɗa tana Miƙewa bayan ta gama cin abincin jin shiru shiru Ayshern bata fito ba. Ya shanye wadda ta saka mishi har ya kara be ce mata komai ba har ta wuce ɗakin Ayshern, a kwance ta sameta sanye da plain riga Onion Colour har ƙasa, daidai cikinta ya kama se ya sake daga kasa. "Aysher kwanciya kika yi? Abincin fa?" "He'i am Aunty Asmy(ya isheni)" "wani irin ya isheki me kika ci da ze ishe ki? Tashi oya mu wuce ki ci abinci" Duk yadda ta so ƙi haka Asma'u ta sakata a gaba se tace tana tsoron ta sake laifi bazata fita ba se duk sun shige. Taɓe baki Asma'u tayi ta fice taje ta zuba mata abincin ta sake zuba mata furar yana kallonta be ce komai ba ta wuce zuwa ɗakin Ayshern. Basu suka fito ba se dab magarib da Asma'u zata wuce, kaman kar ta tafi haka Aysher taji don sun sha hira har class na fulatanci suka yi, ita kuma Asma'u ta koya mata assignments dinta na biology da physics, har mota ta raka ta, dubawa tayi ta ɗauko choculates ta mika mata tace "ɗiyarmu a sha wannan kuma kar ayi kuka" Dariya Aysher ta saki itama Asma'u tayi dariya tana cewa "ko kefa da kin yi wani kicin kicin da fuska, yauwa ga Big bro din nan ma" Ta faɗa tana kallon shi yana tahowa da alama yayi alwala don gyara hannun tsadaddiyar shadda dake jikinshi yake. "Dama tafiya zaki yi ba sallama?" Ya faɗa yana kallon Asma'un. "Big bro na kira line naka be shiga ba, ɗiyarmu kuma na tsoron matar Abbanta ta ƙi zuwa ta maka magana" Kallon Aysher yayi da kyawawan idanunshi masu girma da suke a lumshe, ta bata fuska sbd abunda Asma'u ke cewa kaman zata yi kuka, ya maida kallonshi kan Asma'u yace "ke kuma da yake gidan baƙon ki ne ko?" Ya ƙarasa yana mika mata bunch din 1k yace "Ki gaida su Ammi" Tunda ya faɗi hakan ta san yau kila be samu ya shiga gidan bane, godiya ta mishi ya wuce abunshi. Aysher na riƙe da choculates ɗin ta har Asma'u ta fice kan ta dawo ta shige ɗakinta. Washegari da wuri ta tashi sbd dokin yin girki, dama haka take inde zata yi girki tayi ta ɗoki kenan, kitchen ta wuce bayan tayi brush tana nazarin abunda zata girka, tas ta bubbude lockers din ta ja baya har da sa hannu a haba tana gyara glass dinta da ya karawa fuskarta kyau. Cikin sassanyar muryarta tace "Ina son kunu amma ba kamu, ko nayi Basise ne?" Basise wani nauyin kunu ne da mutanen yola ko Taraba ke yi da danyen shinkafa na tuwo, kai ta gyaɗa cike da gamsuwa ta dibi gyaɗa markadadde daga gani ta san markaden yola ne sbd sune suke yinshi yayi tililis mai ya kwanta me yawa a samanshi kaman kayi ta lasa kuma duk jimawar da ze yi baya lalacewa sbd wannan mai kuma an soya gyaɗar sama sama. Tacewa tayi ta zuba a tukunya, a wurin kunna gas din kuwa seda aka yi da gaske sbd tsoro irin nata, bayan ta kunna ta ɗaura tukunyar taje ta dibi shinkafa rabin cup ta wanke ta ajiye, tsamiya ta jiƙa a cup kan ta fara tunanin mahaɗar kunun nata, nan ta yanke yin ƙosai, wake ta diba ta surfe ta wanke ta haɗa da atturugu da albasa ta sa a buchimix blender din da Antynta ta tabbatar mata komai yana nikawa, a take ta markade yayi tilis ta juye a roba, da gudu ta koma wurin gyadarta ganin ya kusa zuba ta juye shinkafar ta tsaya tayi ta motsawa na mintuna kan ta ajiye ludayin ta koma ta buga kosan sossai. Tana yi tana dawowa ta duba kunun seda shinkafar ya nuna tilis ta kashe gas ɗin kan ta zuba ruwan tsamiyarta ta ta kara juyawa ta zuba sugar ta sauke, a wani madaidaicin jug me garai garai ta juye sbd shi baya son flask ze dafu sossai yayi kauri shiyasa ta barshi a jug, komawa tayi ta fara suyan ƙosan cikin annashuwa take komai. Iskar bakin shi yake hurawa wadda ke fitowa da zufa sbd gudun da yake yi na motsa jiki, wuyanshi maƙale da karamin towel, daga kanshi head Phone ne me kyau, riga marar hannu ne jikinsa wadda ya fidda murdaddun damatsansa alamar be ɗauki motsa jiki da wasa ba, dogon wandon Puma ne jikinshi se rufaffun takalma duka baƙake, sun yi nasarar fito da kyakyawar skin ɗin sa fari kal, kwantaccen sajenshi se digar zufa suke har cikin tattausan gashin kansa  duk da haka wani masifaffen kamshi yake fitarwa.. Tsagaita jogging ɗin yayi ya buɗe parlorn ya shiga, ko kan ya kai tsakiya ya tsaya chak yana nazarin kamshin da ya cike parlorn wadda babu tantama daga kitchen yake fitowa, ko ba'a faɗa ba ya san Aysher ce a kitchen nan don in Kaga Naina a kitchen ɗaukar cup ne ko plate se kuma in babu ruwa se a frigde na kitchen. Har kaman ze wuce zuwa ɗakinshi ya watsa ruwa se kuma ya karkata ya nufi kitchen ɗin, daga bakin kofa ya ja birki ya tsura mata mayun idanunshi yana mamaki ganin yadda take aiki hankali kwance fuskanta cike da annashuwa wadda ze iya cewa banda jiya zuwan Asma'u se kuma yau be taɓa ganin hakan a fuskanta ba. Riga da wando baby pink na Cotton ne a jikinta, kanta babu dankwali se gashinta da ta kama, fuskarta fayau se murmushi take tana kwashe abunda yafi kyautata zaton ƙosai ne. Ita kuwa tana cikin aikinta ta soma jin sassanyar kamshi wadda a wurin mutum ɗaya tak ta sanshi na ratsa kofofin hancinta, yatsina fuska tayi to ko don bata san yan birni sossai bane take tunanin shine kaɗai me irin wannan turare? Oho ta taɓe baki tana cigaba da aikinta a hankali taji inuwar mutum gefen ta a razane ta daka tsalle hakan yasa mai fallatsuwa a hannunta, ihu ta tsala tana yarfe hannun idanunta dake nuna firgici zube a kanshi. Da hanzari ya riƙo hannun yana cewa "Subhallah! Me hakan? Baki da hankali ne?" Hawaye ta fara wani na koran wani bata iya ta sake buɗe baki da niyyar magana ba, duba hannun yayi har ya soma tashi sbd jar fatar ta, gishiri ya ɗauka ya zuba mata a wurin yana sake kallon hannun, ya kalleta se Shagwaɓe fuska take.. "Next time idan kin tsorata Naji ko da wasa kin yi ihu i will deal with you, baki san Allah ake ambato ba in an tsorata?" Yadda ya sauke maganan da natsuwa cikin husky masculine voice nashi yasa ta kau da kai daga kallonshi tace "in sha Allah zan kiyaye, ina kwana Abba?" Ya ɗan yi shiru cikin natsuwar shi da kamalar da be ɓoye kanshi ba daga dabi'arshi yace "Lafiya, me kike yi?" Se lokacin ta kula da gas dake kunne har man ya fara konewa Allah ma ya sa ta gama se ta kai hannu ta kashe tace "girki nake" "wa ya koya miki?" Ya tsinci kanshi da tambayarta Dukda ya tashi a gidansu yaga kannenshi na girki sede zaman kasashen Turai da ɗabi'ar matarshi yasa yake ganin kowace yarinya ba lalle ta iya girki ba barin ma wannan da bata wuce 16 ba. Murmushi me sauti tayi wadda baze ce ya taɓa ganin tayi ba tace "Nene na mana, ai ni tun ina da shekara bakwai take bani girki, ni dae na en gayun nan ne ban iya ba" Murmushi shima yyi wadda iyaka lebenshi don shi ba ma'abocin dariya bane, murmushin ma ba ko yaushe zaka iya katarin gani a fuskarsa ba, ya kai hannu ya ɗauki kosan ɗaya ya kai baki, lumshe idanunshi yayi ya buɗe yana taunawa a hankali ita kuwa duk ta saki baki da hanci da ido tana kallonshi tana jira yayi compliment, ɗan kallonta yayi se ya yamutsa fuska kaman be yi daaɗi ba, yayi gaba yana taɓe baki ya buɗe jug din ya kalli kunun kan ya juya ya fara tafiya har ya kai kofa ya dakata yace "lemme fresh up" Ya fice yana murmushi. Da gudu taje ta ɗauki kosan ɗaya ta sa a baki tana jujjuya idanu.. "Wallahi yayi daaɗi Abbaaa" Ta faɗa kaman zata yi kuka. Hannunta ta duba seda ya tashi dama jikinta bashi da kyau sam akan irin abubuwan nan, a kula ta sa ta kai dining, ta kai jug ɗin ta lura kaman a birni ya zama dole ka kai abinci dining in ka gama ne oho! Dawowa kitchen ɗin tayi ta tattare komai ta ɗauraye abubuwan da tayi anfani dasu, ta kintsa komai a mazauninshi ta fito kenan da niyyan zuwa ɗakinta don yi wanka se gashi ya fito, kamshin shi ya cika parlorn gabaɗaya kananun kaya ne sanye a jikinshi wadda suka matukar amsarshi, yana tafiya cikin natsuwar shi da tsantsar kamala, dining ya nufa ya zauna. Har tayi kaman zata wuce se ta dawo, zuwa tayi kan dining ɗin ta fara zuzzuba mishi, bayan ta gama ta tura mai, cokali ya ɗauka ya dibi kunun da tunda ya gani yake son sha sbd abunda yake kauna ne yana shirin kaiwa baki yaji an yi sama da cokalin..... *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰                          🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN          (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* *Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya* *SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci. *AUTAR MANYA* *ALEESHATULKHAIR* kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏 *Aleesha collection* ''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?" "a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata'' ''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi'' Hajiya ta zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar mai gida ko saurayi kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai sauki ke ma ki je ki nemi na ki. Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944 Sai kun zo FREE PAGE 8 "What sort of Nonsense is this?" Ya dakawa Naina tsawa yana kaucewa kunun ya zube a ƙasa instead of jikinshi. Aysher kam kallon Naina kawai take dake sanye da karamar sky blue nighty da ko cinyarta be gama rufewa ba, yana da tsiririn hannu gashin da babu tantama na doki ne Dukda yadda aka gyara shi aka kalkaleshi don ya zama kaman na mutum hakan be hana shi bayyana ba rabi a zube a kirjinta rabi a bayanta.. "Emran please! Ni kake faɗawa haka? Why are you eating this? Yaushe ma ka fara cin irin waennan regular foods ɗin kai dake da kyankyami ba ko wani hannu ne ze dafa ya baka ka ci ba?" Danne fushinshi yake kokarin yi kaman yadda ya saba, tafin hannunshi da ya jike da zufa Dukda Acn parlorn da komai ya kai ya murza goshinshi ya ja tsaki, a lokaci ɗaya ya ɗan ciza harshenshi he looks so cute and charming da fushin.. Shi karan kanshi ya san ba abincin kowa yake iya ci ba but this girl from day one da ya soma ganinta ya tabbatar ko me ta bashi he will not hesitate kuma ya san saboda yana iya cin komai da ya fito daga gidan Isma'il babu tantama ne, so why all the fuss? "Naina leave my sight, just go" Ya bata umarni yana me zama ya ɗauki sabon cokali ya bar na ƙasan ya fara shan kununshi, kaman ta makuro shi don haushi juyawa tayi ga Aysher dake tsaye cikin tsoro ta buga mata banzan Harara kan ta wuce kaman iska, kallonshi Aysher tayi cikin mamakin yadda baya tsawaita fushi idan ta fahimce shi, sannan da yayi ta magana gwara yayi shiru, kitchen ta koma ta ɗauko mop ta zo ta gyara wurin kan ta wuce daki be ce mata komai ba. Bayan tayi wanka ta fito ta zo ta ci nata a nan parlorn tana kallo, har ta gama babu wadda ya fito, Miƙewa tayi ta fito tsakar gidan ta fara ɗan zagaye anan ta ga wani karamin hanya me ɗauke da furanni daban daban masu kyau, hanyar tabi tana mamakin nan ɗin kuma ina ne? A hankali ta bayyana cikin wani lambu me masifaffen kyau bata san sadda ta buɗe baki tana karewa kyaun wurin kallo ba. Shukoki ne masu kyau da tsari gabaɗaya wurin, kasanshi shimfide da carpet grass, yadda flowers dake wurin suka kawata wurin da kalolinsu kama daga ja, kore, dorawa se taji kaman ta fita daga Kasar ne gabaɗaya, takawa tayi kaɗan idanunta ya gane mata kwantaccen ruwa a cikin wani farin kwami me kalar sararin samaniya, daga gabanshi wani gado ne har guda biyu, gefe chan kuma kujeru ne masu taushi da tebur a tsakiyarshi. Wurin yayi matukar burgeta ainun, shawagi tayi tayi a wurin tana kallon itacuwa da aka shuka suke fitar da ƴaƴayensu masu burgewa, guiva da yayi yellow kato ta tsinka ta wanke ta soma ci tana ta aikin murmushi, ta jima a wurin sossai don seda taji ana kiran azahar kan ta koma ciki don yin sallah. Shi kuwa yana tashi daga dining ɗakin Naina yayi, tana lumtse cikin wata lumtsatsiyar cushion nata na ɗakin dake maroon hannunta rike da waya tana dannawa, Bakinta chewing gum ne tana taunawa a hankali, fusge wayar yayi ya wullar kan gadonta yana aika mata wani irin kallo yace "Naina whats wrong with you? Menene ya hau kanki?" Kallonshi take tana jin hawaye na cika idanunta ta miƙe tsaye ta nuna shi "this... You, kaine ke damuna! Emran taya bazan tsani yarinyar nan ba ma for goodness sake? Akan yarinyar nan kuma a gabanta kake ta danganta ni da sunaye kala kala, harda mahaukaciya ka kirani, akan wannan kazama ƴar rugan.." Idanunshi ya lumshe da karfi se ya buɗe a kanta yana shafa kwantaccen sajenshi kaman wadda ya rasa abun yi se ya taune lip din shi ya saki.. "Taya ba zan dangantaki da irin waenchan sunaye ba? Come back to ur right sense mana! I told u time without number in ba zaki iya taimakona a kanta ba ki fita harkarta, yarinyar nan bata miki komai ba kina aibatata son ranki ina guje miki randa zata iya ramawa bcs zuciya bata da kashi, that time zaki san cewa na gargade ki akan zub da girman ki, yarinya kuma bazata bar gidan nan ba se aure... Shine kaɗai abunda ze fidda ta so pls take a chill pill" Hawaye ta soma zubarwa wani na bin wani, cikin Muryar kuka tace "Emran ka daena so na, did you hate me this much?" Rikitattun idanunshi ya zuba mata, she knows baya son kuka, kukan ma daga macen da yake so sannan kuma shine silar zubar hawayen, amma Meyasa ta kasa fahimtar shi? Ganin tana shirin kaiwa ƙasan tiles da kukan da ya kwace mata yasa yayi hanzarin janyota jikinsa, kuka take tayi kaman an mata wani abun a zo a gani. "Please stop it Naina, ki daena bana so" "abunda kake so kenan Emran, kana dae sane da cewa bani da wani farin ciki a cikin zuri'arka se naka, yanzu kaima ka fara tsanata ko don ban haihu bane? Ko sbd ban haihu bane yasa bani da power a gidana?" Ajiyar zuciya me karfi ya sauke, hakane ya rasa me yasa family dinshi basa son ta ba kuma sa janta a jiki, amma shi kam yana son kayarshi kuma ai ya san haihuwa na Allah ne tunda dukkansu lafiyansu ƙalau. "Ban tsaneki ba Naina, ba zan iya tsanarki ba ke fa sirrina ce taya zan fara tsanar sirrina huhnn?" Haka ya lalace a rarrashinta sede duk yadda ta fito mishi inde kan maganar Aysher ne ze kauce sbd babu dalilin da ze sa ya biye mata ya butulcewa abokinshi tun na yaranta, bata huce ba seda ya amince zasu tafi New York a mata IVF, zasu gwada sa'arsu akan hakan kuma su gani. Fitowa yayi daga ɗakinta bayan ya tura ta bayi tayi wanka, alwala yayi sbd azahar da ake ta kira ya fice, bayan ya dawo ɗakinshi ya wuce sbd baya jin fita a lokacin har ya kwanta ya lumshe ido se ya tuna ƙunan da tayi dazu, Miƙewa yayi ya duba ointment ya fito ya mata knocking, jin shiru yasa ya tura bata ciki, ya duba kitchen bata nan, fitowa yayi ya fara dube dube a tsakar gidan nan ma bata nan, kuma ya san ba iya fita zata yi ba, garden ya nufa tun daga nesa ya hango ta a kujerar dake bakin ruwan riƙe da alqur'ani tana karantawa cikin sanyin murya da natsuwa. Ajiyar zuciya ya sauke kan ya nufeta ko sau ɗaya be ɗauke idanu daga kallonta ba, tana sanye da doguwar riga sky blue and White se ɗan baby hijab shima sky blue ya mata kyau sossai barin ma da garin yayi lublub alamar hadari hadari. Karatunta take a natse idan tayi tayi se ta rufe qur'ani tayi da kai, ta sake komawa farko ta haɗa, tana cikin bitarta se haddar ya gudu mata, shiru tayi tana son tunawa se ta ɗauko se ta chanza ayar zuwa wani chan daban, a hankali taji sautin shi yana ɗaga mata, waiwayowa tayi se suka haɗa idanu, karamin murmushi tayi kan tace "Na gode" Be ce komai ba ya zauna a ɗaya kujerar dake facing nata, se ta gyara zamanta tana maida dukkan kafafunta dake maƙale a saman kujeran ƙasa. Ganin tayi shiru yasa yace "ƙarasa haddarki" Cigaba da karatun tayi shi kuwa yana dannar waya, idan tayi ɓata kuma ze gyara mata har ta kamallah. "Muga hannun?" Yayi magana kaman me tambayarta. Qur'anin ta ajiye akan cinyarta ta wara hannunta cikin rashin fahimtar shi, shi kuwa ointment ɗin ya buɗe ya ɗan matse a hannunshi na dama ya ajiye se ya miƙa mata tafin hannunshi na hagu. Zara zaran yatsunshi dake ɗauke da zoben azurfa me kyalli ta kalla, kan cikin ɗan faɗuwar gaba da ya risketa ta ɗaura tafin hannunta na dama bisa tattausan tafin hannun nasa, a tare suka lumshe idanu suka buɗe, yatsunta ya zubawa idanu yayinda ita kuwa idanunta ke bisa kwantaccen sajenshi da ya matukar ƙawata fuskarshi ya mugun amsarshi. A hankali ya shafa mata ointment ɗin bisa ɗan ƙunar kan ya saki hannun ya ja da baya, daidai lokacin aka kira la'asar, dukkansu Miƙewa suka yi sede ita taja ta tsaya shi kuma ya fice daga wurin.. Bayan tayi sallah ta chanza hijab zuwa dogo kan ta fito zuwa ɗan hut ɗin da suke karatu ciki, a shimfide yake da tattausar darduma da tuntu irin na gidan sarauta, daidai malamin ya shigo ta zauna ta bashi hadda ya kara mata, suka yi hadith da take kan ya mata sallama ya tafi, ɗaki ta koma tana tunanin abunda zata girka musu da dare don matar gidan kam taga fitan ta tun suna karatu cikin wani rantsatsen paper lace da aka mata dinkin doguwar riga, karamin gyale a kafaɗarta se gashinta da ta zubo shi har baya wadda na ƙari ne. Tunawa da taga bishiyar zogale a garden din yasa ta maida karamin hijab ɗin ta tayi waje, cirowa tayi Allah ma ya sa bashi da tsawo da se ta nemi abin cirewar, kitchen ta dawo ta dibi shinkafa ta ɓarza ta wanke ta ciro dankwalelen kaza daga frigde, a tsanake ta haɗa dambunta me rai Allah ma ya sa ta iya anfani da steamer sbd dakkere da suka yi a ciki ranar da Asma'u, a hankali kamshin ke ratsa kitchen ɗin, bayan ta gama ta zuba a foodflask se ta fara yiwa kazar nan haɗin gashi irin na tukunya wadda ba'a raba asalin Fulani dashi idan har a ruga yake, sam bata wani san anfani da oven ba don haka a tukunyar ƙasa tayi gashinta dake ta zuba kamshi ta saka a kula daban, tattare kitchen ɗin tayi ta wanke abubuwan da ta ɓata kan ta kai abincin dining area. Komawa ɗaki tayi ta gabatar da Magrib da aka kira, karatunta ta ɗan yi bita har aka kira Isha tayi sallah da azkar kan ta fito don ɗiban abinci, har tayi serving kanta ta zauna a dining ɗin se gashi nan ya shigo parlorn bakinshi ɗauke da sallama iyaka lips ɗin shi, bayanshi Naina ce riƙe da leda me tambarin gidan abinci. Dukkansu Dining ɗin suka kalla sbd motsi da tayi na kokarin tashi ta koma ɗaki don gujewa haddasa rikici a tsakaninsu, plate ɗin hannunta ya ɗan kalla kan ya kalli dining ɗin, Naina tayi saurin cewa "Kaga na biya Fav restuarant ɗinka na samar maka favorite food naka gwara ka ci tun da zafin shi" A hankali yace "I think am not eating that.." "Toh me zaka ci? Da safe ma fa wani jagwalgwalo kaci" Murmushi yayi yace "ke kika ɗauke shi haka Babe, but trust me yana riƙe ciki sossai ba abunda ya kai abincin gargajiya gamsarwa". Daga haka ya isa dining ɗin ya buɗe flaskes ɗin don tuni ta tsufa a ɗakinta bayan tace musu sannu da dawowa. Har mamakin yadda yarinyar nan ta iya girki yake, ze iya cewa kusan sabon abu ne a wurinshi kuma ba sabo ba tunda ba yau ya fara zuwa ruga ba yana kallo ana aurar da yara a 12/13yrs kuma su yi girki na ban mamaki kai ko mahaifiyarta ze iya tuna a sadda Isma'il ya aure ta bata wuce 14 ba ake ta cewa ma ta tsufa a gidansu idan tayi girki duk yaje ya dinga yabon girkin kenan. Naina da ta biyo shi ta zauna ta fidda abincinta daga leda ta fara ci, shi kam zuba dambun yayi da kazan dayawa ya zauna ya ci sossai, shi ze iya cewa zuwan Aysher ai albarka ne a gareshi, idan yaci irin wannan dama se a gidansu to gidansun ba kullum yake samun zuwa ba sbd aiki da kan mishi yawa. Har suka gama Naina kam bata daena aikawa abincin shi Harara ba, shi kam yayi nak yayi hamdala kan suka wuce dakunansu, wanka yayi ya shirya kwanciya ya kwanta, be damu da duba Naina ba don ya san idan tana da wani bukata zata zo ko kuma shi idan yana bukatarta ya je amma ba kwana suke ɗaki guda ba. Washegari da safe bayan tayi sallah ta fito kitchen, bata ganinshi bare ta tambayeshi tana tsoron yin abunda basa ci, ita ce ta tattare dining da suka ci abinci jiya taga ya ci sossai kila yana son abubuwan gargajiyan, masa/waina ta fara kokarin haɗawa da Miyar kayan ciki wato offals me daddawa irin na ainihin kauye dahuwar tayi. Ta soya Masar Dukda ta sha wahala da tandar amma ba laifi yayi kyau sossai Masar, ta shirya a dining taje tayi wanka, doguwar riga ta sanya na Egypt maroon da yaji ado da fararen zare se ta zauna bakin dressing mirror din bayan ta kama gashinta ta fara gyara wurin, ta gyara ɗakin ta share. Ita dae bata san wa me musu shara ba kuma a koyaushe ta kan ga gidan fess cike da kamshin freshners daban daban sbd da su Naina ke anfani wai bata son warin hayaƙin turaren wuta yana sa ta tari. Daidai ta fito shima ya fito sanye da kaftan Ash da aka yiwa wani kalar ɗinki irin na zamani, hannun iyakarshi damtsenshi ya bayyana murdewarsu da irin kaurinsu, iyakar rigan cinyar shi, kafafunshi sanye da farin takalma palms masu kyau, hannunshi ɗaure da Black agogo, sajenshi zuwa gashin kanshi se sheki suke suna walwali, cikin seconds ta kare mai kallo kan ta duƙa kaɗan "Abba ina kwana?" Yace "Lafiya..." Har seda ya isa dining ya zauna yana kallonta har ta ƙaraso kan yace "ya hannun?" Ita mancewa take da ƙunan ma sbd ba wani me yawa bane tace "Yayi sauƙi" A hankali tayi serving dinshi se kallon kyaun masan yake, ita kuwa mamaki take yadda duk abubuwan da ta girka ze ci amma be taɓa cewa yayi daaɗi ko be yi ba, be taɓa ce mata sannu ba bare ya gode, tura mishi tayi se taga ya janyo spoon a ranta ta raya lallai ba zaka ji daaɗin wainar nan ba tab, ai ita da wuya taci abinci da cokali gani take rage mata daaɗin ze yi. Zuba nata tayi ta dauka zata juya yace "Aysher" Da sauri ta juyo tana amsawa "Sit, karki sake tashi don muna wuri we are like ur parents" Kallon abincin tayi ta san matsayin mahaifinta yake amma bazata iya sakewa taci da hannu kaman yadda zata ci a ɗaki ba ko gaban baffanta, zama tayi bayan taje ta wanke hannunta a hankali ta sa ta fara ci, babu wanda ya tanka har suka gama. "Hanzarta ki sameni mota" Ya faɗa kan ya miƙe yayi cikin parlor. Da ɗan sauri sauri ta gama, bata tsaya tattare wurin ba sbd Aunty Asmeey ta fada mata ya tsani jira, gyalen ta ta yafa kawai ta ɗauki takalmi ta fito, gidan gaba ta zauna ya ja motar suka fice. Sam bata gane inda suka nufa ba har seda ta gansu a gaban gidan su Ammi, farin ciki ne ya lullube ta har tana sakin murmushi me sauti a hankali ya juya ya kalleta, tana ta murmushi kaman wacce duniya ta yiwa daaɗi, bayan yayi parking suka nufi ciki, itace a gaba don ta barshi a mota knocking ta ɗan yi kan ta tura kofar sashin Ammin, sam bata kula ma da mutum ba se ji tayi an ce "Wowww what a damsel...!" *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰 🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA   بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* *Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya* *SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci. *AUTAR MANYA* *ALEESHATULKHAIR* kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏 *Aleesha collection* ''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?" "a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata'' ''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis  marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi'' Hajiya ta  zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar  mai gida ko saurayi  kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai  sauki ke ma ki je ki nemi  na ki. Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944 Sai kun zo FREE PAGE 9 Shi kam Naufal da kallo ɗaya yarinyar tayi mugun tafiya dashi, ji yayi kab duniya babu macen da ta dace ya mallakawa zuciyar shi kamar wannan yarinya, OMG! Ya ayyana a Ranshi a sadda ta kalleshi da idanunta masu kyau. "Assalamu Alaikum" Ta faɗa cikin sanyin muryarta. Ganin se kallonta yake ya kasa cewa komai yasa cikin hausarta tace "Ina kwana?"   Daga haka bata kara ba tayi sama, a hankali ta tura ɗakin Aunty Asmeey, tana zaune gaban dressing mirror suka haɗa idanu cikin tsananin farin cikin ganinta ta tashi ta rungume ta "ɗiyarmu kece da safen nan? Tare da wa kuka zo?" Tana murmushi tace "Ni da Abba, ina kwana Aunty Asmy?" "Lafiya ƙalau zo dama neman me tayani zaban kaya nake se gaki Allah ya turo ki, dubamin don Allah wanne ze fi karɓa ta?" Tana dubawa tace "zaki fita ne?" "A'ah ke Ya Naufal ne ya mana surprise visit ze ɗan yi sattuttuka haka tsakani da Allah bana so ya kalleni ba cikin gayu ba, shima irin taste ɗin Abbanki gareshi, yana son gayu" Murmushi kawai Aysher tayi tana nuna mata wani peach lace me emerald stones yana hade da mayafi emerald tace "Ina tunanin wannan ze fi karɓarki.." Ƙarba tayi ta manna da jikinta aiko ya mata kyau ta juyo cikin farin cikin da ya gaza ɓoyuwa a fuskanta tace "thank you ɗiyarmu bari na shirya" Shi kuwa Emran har ya nufi bin bayanta se kuma kiran Ahjinsu ya shigo mishi da alama yana son ganinshi ne, don haka se yayi chan ɗin, a ƙayataccen parlorn ya samu Murad da Alhaji suna wani lissafi baje akan hadadiyar rug carpet dake malale a parlorn, Ammi na daga dining a tsaye da alama Abincin Alhajin take haɗawa. Da sallama ya ƙarasa duk suka amsa ya zauna shima daga ƙasa yace "Barka da safiya Alhaji" "yauwa bokan Turai, idanunka kenan?" Murmushi ya saki yana ɗan shafa keya yace "Alhaji ina shigowa ai kaine bana samunka" Alhj yace "hakkun ai kwanan nan daga ni har Murad bamu zauna ba, wani kamfani ne na saya na sarrafa kaya irin na mata to audugar da muka saya ne ashe ba me kyau aka kawo ba muke ta asara, ina ga zan noma Auduga bana" "Alhaji ya kamata a huta hakanan jiki da jini" Murmushi kawai Alhajin yayi dama rikicin su da Emran kenan a kullum, shi dae yana kaunar business ɗin shi baya ji kuma ze iya bari sbd tana da daaɗi neman na kai babu abunda ya kaishi daaɗi da kwanciyar hankali. Murad ne ya gaida yayan ya amsa cikin kulawa, daidai Ammi ta kawo shiryayyen tray da abun karyawar Alhajin irin na masu ciwon siga, a ladabce ya gaida mahaifiyar tashi ta amsa ba tare da ta bashi attension ba, har ta juya se kuma tace "in kana buƙatar kari se ka ƙarasa dining ɗin" Girgiza kai yayi kaman tana kallonshi yace "Alhamdulillah! Na karya a gida" Maganar seda ya sa ta ɗan juyo ta kalleshi, ya fahimci ma'anar kallon Se kawai ya mata murmushi. "Shiga ciki Likita ka ɗauko aid box ɗina ka zo ka gwada sugar da hawan jinin nan ban san wanne ne ya min yawa ba kwanan nan se in ta jin jiri da ciwon kai" Marairaicewa Alhjn yayi yace "Alhaji ba ka gani ba? Yanzu jikinka na bukatar hutu, Don Allah kayi kokari ka barwa Murad wannan aiki yanzu" Cikin fara'a da alama dabi'arshi ce yce "Imrana kenan ai idan lokacin barin yayi za'a bari ne!" Miƙewa yayi ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi ɗakin Alhajin nasu anan ya ɗauko First aid ya zo ya mishi gwaje gwaje sugar din ne yayi rising don haka ya mishi allura, da kanshi ya haɗawa Alhajin tea wadda komai nashi na masu diabetes ne, anan ya zauna Murad ze cigaba da lissafe lissafen ya watsa mishi Harara wadda ya saka shi shirun dole, Ammi kuwa na zaune gefe tana kallonsu. Naufal ne yayi sallama ya shigo parlorn. "Babban yaya" Ya kira Emran yana sakin murmushin jin daaɗin ganinshi. "The young surgeon yaushe a ƙasar?" Ya faɗa cikin murmushi sbd Naufal mutumin shi ne sossai da sossai. "Ka ganshi nan wlh muma se ganinshi muka yi jiya ya diro mana ba notice" Alhaji ya faɗa, dariya Naufal yayi ga dukkan alama shi mutum ne me raha da faram faram. "Ammin mu yanzu naga wata yarinya ta shiga side dinki, yaushe kika samo wata ƴar ban sani ba?" Ammi tana kallonshi tace "Anya Naufal? Asma'u ce kaɗai a sashen nan ko dae nayi bakuwa ne bayan fita ta" Yace "kai A'ah Ammi wannan bata yi yanayi da bakuwa ba, se nine ma tayiwa kallon baƙo tana gaisheni ta haura upstairs se surutun su na tsinta da Mami" Haka yake kiran Asma'u don baya iya kiran sunan mahaifiyar tashi kai tsaye. Ganin suna ta wahalar da shari'a ne yasa Emran dake ɗan danna waya yace "Aysher ce" "Au ashe tare kuka zo da ƴar fullo tamu" Murad ya faɗa, Ammi kam bata ce komai ba se Naufal ne yace "wacece ita Murad?" "Me damuwanka da sanin wacece" Xe yi magana Ammi tace "ɗiyar yayanku ce" Ze sake magana Emran yace "kai kuje chan parlorn sashen ku ko na Ammi kuyi wannan dogon surutun baku san Alhaji ba daaɗi yake ji bane?" Shiru duk suka yi kan suka miƙe suka fice, Alhaji yace "ka korar min yara ai se ka min hirar..." Ammi ta saki murmushi me sauti tana kallonsu "yi dariyarki Ammin su, ai yau se ya buɗe wannan baki da ba ya doguwar magana ya min hira tunda ya kori masu tayani hirar" Murmushi me sauti kawai Emran ke saki yana ɗan shafa kai a tsanake cikin natsuwa yace "Ai Alhaji ba surutu kake buƙata yanzu ba hutu ne, ka samu ka ci abinci ka ɗan kwanta" "Mahaifiyarka ke ce min ka ɗauko ɗiyar sama'ila, to Allah ubangiji ya tayaka riƙonta, ya dafa maka wajen tarbiyartar da ita, Allah yaji kan mahaifinta" Da "Ameen" ya amsa a natse, hirar komawa yayi tsakanin Alhaji Da Ammi na irin karamcin Isma'il da iya mu'amalarshi, shi kam sede ya kallesu ya ɗan yi murmushi. Basu fi awa a sashen ba sbd kwanciya da Alhaji ya shiga yayi suka fito, tafe suke a tare da Ammi duk yadda ta so shiru ta kasa se cewa tayi "Yanzu kam kana samun karyawa kan ka fita aikin kenan?" Ɗan kallonta yayi cikin natsuwa yace "Eh yarinyar nan Aisha na kokari, kusan duk abubuwan da nake so na gargajiya ta iya su" Murmushi Ammi tayi cikin disappointment ba wai bata yi murna da taimakawa ɗan ta da Aysher ta fara daga zuwanta ba, kawai tana jin takaicin yadda Naina bata san girma da darajar miji bane, bata san sirrin dake cikin yiwa miji hidima bane daga nan duniya har lahira. Har suka isa sashen ta basu sake magana ba, a kan Dining suka samu Murad yayinda Naufal ke zaune kan kujera yana kallo hannunshi rike da Orange juice yana sha. Haurawa Ammi tayi yayinda shi kam ya zauna yana yiwa Naufal da ya bashi hankalinshi Ƴan tambayoyi wadda yawanci akan aikinsu ne don in har Kaga yana dogon magana akan aiki ne. A hankali Ammi ta tura kofan Asmeey da har yanzu bata gama shiri ba se wani rawar kai take tace "Toh sarkin zakwaɗi se ina?" Tura baki tayi tace "Ammi mutum ba ze yi wanka ba se ze fita?" Girgiza kai Ammi tayi ba tare da tace mata komai ba ta maida kanta kan Aysher da tayi saurin zamowa daga bakin gadon tana gaisheta, cikin kulawa ta amsa tana sake kallonta to idan wannan ƴar yarinyar zata iya shiga kitchen tayi girki me ze haka Naina dake da kusan ashirin da takwas shiga kitchen fisabilillahi? Kau da tunanin tayi ta nufi ɗakinta don gabatar da salatul duha ɗin ta. "Zo mu je" Asmeey ta faɗa bayan ta gama duk wani shirinta. "A'a Aunty Asmeey ni ina nan" "ba zaki shiga ki gaida Hajiya bane?" Miƙewa tayi jin hakan ta gyara yafin gyalen dake ta zamewa sbd ba saka shi suke a ruga ba, dama baffanta ke sakata sa hula dole in ba haka ba gyalen a kwankwaso za'a ɗaura shi. A hankali suke saukowa wadda karar saukowan ya fusge hankalin jama'ar parlorn banda Emran dake amsa call, Naufal kam babu inda idanunshi suka sauka se a kanta, Allah ya sani shi kam ya gani kuma yana so, Asma'u ta ƙarasa ta zauna ganganshi ta fara mishi surutu yayinda hankalinshi da natsuwarshi ke kan Aysher da ta samu wuri daga ƙasa ta zauna tana ɗan murmushi. "Mi hofni ma boɗɗi"(Na gaishe ki pretty) A tare Emran, Aysher da Asma'u suka kalleshi ita dae Asma'u ta san me boɗɗi ke nufi tunda tana tsinta, yayinda Emran hakan ya ɗan bashi mamaki, ita kuwa Aysher murmushi ta saki jin yana jin yaren ta sossai, kara gaishe shi tayi se ya fara mata tambayoyi akan Rugarsu. Hirar da ta kwana biyu bata yi ba ta sake suke tayi da fulatanci, Asma'u da take kallon wannan ta kuma kallo wanchan ne tace "Wallahi wannan abunda kuke yin ba kyau, taya zaku zauna cikinmu kuyi ta yaren da bama ji?" Gwalo ya juya ya mata yana dariya yace "In kin yi zuciya ki koya. Ko Boɗɗi?" Ya juyo yana tambayar Aysher, tana dariya ta gyaɗa kai daidai zata sake magana suka haɗa idanu sbd ɗagowa da yayi hakan yasa tayi shiru. Tsam ya miƙe ya fice daga parlorn ba tare da yace uffan ba, nan Naufal ya dawo hirar shi da Aysher tana amsawa, a hankali Asma'u da ta kura mishi idanu ta fara jin wani abu kaman haushi ko rashin jin daaɗi cikin zuciyarta, irin kallon da yake yiwa Aysher ya sha bambam da irin kallon da yake mata, tana da wayewa sannan tana da sani akan menene soyayya idan bata yi kuskure ba kaman Naufal na shirin kwarewa wannan yarinya ne, wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi a take yanayinta ya fara sauyawa.. Tsam Aysher ta miƙe tana ce mishi su yi hirar su da Aunty Asmeey tana zuwa, kitchen ta wuce me aikinsu ta samu ta fara ɗaura abun rana nan ta tsare ta da tambaya da kuma kula akan irin girkin na birni a tare suka yi suka gama, daga nan ɗayar zata kai na sashen Hajiya kaman yadda suke yi se ta bita ta baya suka bi zuwa sashen na Hajiya. A tsakar parlor suka sameta zaune yayinda Emran ke kwance bisa dogon kujera sambal idanunshi a lumshe kaman me bacci, cikin sakin fuska Hajiya tace "Ah me sunan Hajiya kece tafe da abincin?" Tana ɗan murmushi ta tsuguna kasa tace "tare da harira muke to zamu shigo nan se aka yi kiranta ta koma, ina kwana Hajiya?" Cikin harshen fulatanci suke maganar "jam ko ɗume noi school a ɗo habda kam?"(Lafiya ƙalau ya makaranta Fatan ana dagewa kam) Cikin murmushi da bata daena ba tace "Alhamdulillah" Miƙewa tayi ta isa dining ta ajiye abincin hannunta, har ta juyo se Hajiya tace "war wannu Abba ma ɗo yamdu ɗo tun nane o yiɗi nyamugo bo mi anda ko haɗi mo"(zo ki sakawa Abban kin nan abincin nan tun dazu yake son ci amma na rasa me ya hanashi). Karasawa tayi ganganshi ta tsuguna cikin sanyin murya tace "Sannu da hutawa Abba" Be tanka ba, ta buɗe abincin cikin natsuwa ta saka ta janyo table ƙarami ta ɗaura mishi akai, ta juya zata fice ya kira sunanta. "Zauna ki zuba ki ci" Ya faɗa ba tare da ya buɗe idanunshi ba. Kaman ta ce mai zata koma taci a wurin Ammi se kuma ta zauna, ta zuba ta fara ci jefi jefi suna hira da Hajiya, Miƙewa yayi zaune ya sanya spoon ya fara cin nashi sam be sa musu baki a hirar tasu ba. Naufal ne ya shigo idanunshi akanta "ke kuma daga bari kije ki zo se ki yi ɓatan dabo?" "Ya Naufal ai na tsaya taya su harira girki ne" Zama yayi gefen Emran yana cewa "eyeee yau muna da cin daaɗi kenan tunda kin sa hannayenki masu albarka" "Naufal pls in surutu ya kawo ka bama buƙata" Cikin harshen turanci yace "Afuwan Babban yaya ni kaina bana sanin ina sakin zance Allah yarinyar nan ta ruɗa ni za'a bani ita???" Kallonta Emran yayi sede ya fahimci bata gane abunda Naufal ke fada ba sbd accent ɗin shi, kuma ba da hankali yayi maganar ba bare tayi comprihending, shima cikin turancin yace "shiga hankalinka ba zan bada aurenta yanzu ba se ta zama cikakkiyar medical doctor sannan" "Ai se in jira ta, amma dae zaka bani ko babban yaya?" "In har dae zaka iya jira, but for now ka sahirta mata tayi karatu pls, and wannan zaƙewan bana son shi kaman janyo raini ne da zub da kai pls maintain" "in Shaa Allah Abban mu" Murmushi me sauti yayi a hankali yace "yaushe na zama Abbanka gardi da kai" Dariya Naufal yayi yace "Ai babban wa ubane don na kira ka Abba yanzu ba laifi bane" Girgiza kai kawai yayi yaci gaba da cin abincinshi. Basu suka bar gidan ba se yamma amma ta ɗan fahimci chanji daga Asma'u da ta tambaye ta se tace mata kanta ne ke ciwo, duk inda ta zauna Naufal na wurin tun bata sakewa har ta fara sakewa suke hira tunda ya iya yaren ta sossai gashi da son wasa da tsokana. Ko da suka dawo basu wani jira komai ba tunda duk a koshe suke suka wuce ɗaki tayi shirin kwanciya ta kwanta. Washegari Litinin da safe da ya tashi ya shirya a tsanake, yana fesa turare Naina ta shigo ta mirror ya kalleta ya ɗan sakar mata murmushi tana sanye da suit designer, wando blue me ɗan fadi se farin shirt da ta saka ta ɗaura bakin kyalle haka a wuyanta, bata sa rigar suit din ba se ta yafa shi a duka kafaɗunta, kafafunta baƙin hill ne me tsini sossai haka baƙin jaka ne a hannunta, gyalen kanta da ya bayyana jelar karin gashinta daga gaba har baya zagaye da wuyanta. A yangance ta ɗan yi hugging nashi tana gaishe shi, cikin kulawa ya amsa yana ƙarasa ɗaura tsadaddiyar agogon shi, a tare suka fito a natse ya kai idanunshi bisa dining ɗin be wani damu ba ganin ba komai ya san she's still a kid ga karatu baya ma so tayi ta stressing kanta, duk a tunanin shi ta wuce don haka ficewa kawai suka yi, a tsakar gida suka haɗu da driver ɗin ta, cikin mamaki Emran ya duba watch ɗin shi Its already 8am, me ya makarar da ita haka? Juyawa yayi ze koma Naina tace "Kayi mantuwa ne?" Girgiza kai yayi ba tare da ya tsaya ba hakan yasa ta bishi, daga parlor ta tsaya tana kallonshi har ya tura kofar Aysher ya shiga bayan knocking da yayi har sau uku... "Ya ilahil Alameen" ya faɗa kasa ƙasa yana nufan gadon da hanzari ganin tiny body ɗin ta dunkule a wuri guda, sanye take da dogon wandon bacci peach da rigar shi, baka iya ganin fuskanta sbd gashinta da ya hautsine ya baje gabaɗaya a kan fuskan gashi kuma a kife take kwance, daga kallon yadda ta kwanta ɗin da kuma yadda gabaɗaya gadon ya cukwuikuye da alama ba lafiya ba. "Aysher! Aysher!! Ke Aisha!!!" Ya jera kiran yana buga pillown da take kai sede bata iya ta amsa ba amma ta ɗan yi motsi alamar tana jinshi, komawa yayi da sauri parlor yana kallon Naina da idanunshin nan yace "I think yarinyar bata da lafiya please help me ki tayata kimtsawa mu tafi hospital" Kallonshi take kawai galala kan tace "am already late ina da meeting da board, bye" Tana kai nan ta juya ta fice. Lumshe idanunshi yayi ya buɗe kan ya juya ya koma ɗakin hannunshi ya haɗe yana kallonta yana sauke numfashi a hankali hankali, ledojin choculates na diary milk da snacks kusan biyar a zube a gaban gadon, iska ya fesar daga bakinshi kan ya sa hannu ya lalabo wayan shi, kai Tsaye Asma'u ya ƙira ringing biyu ta ɗaga ta gaishe shi cikin girmamawa "Ki zo mana in baki da class, i need u to help Aysher bata da lafiya" Tsurawa gaban dressing mirror da take zaune kai idanu tayi kan ta waiga ta kalli ɗakin nata ajiyar zuciya ta sauke kan tace "Yaya ina school yanzu zan shiga practical kuma a matsayin C.A yake" Katse kiran kawai yayi ba tare da ya ce komai ba ya sake tsura mata idanu.... *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰                          🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN          (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* FREE PAGE 10 A hankali ya isa gaban gadon ya tsuguna, hannunshi na dama yayi dropping bisa wuyanta, ɗayan hannun kuma kafaɗarta ya birkitota, hannun dake kafaɗan ya cire ya soma maida gashin kanta baya.. "Ya Salaam" ya faɗa cikin damuwa da alama cikin ciwon nan ta kwana ganin yadda gabaɗaya idanunta suka kumbure tsabar kuka kuma har yanzu hawaye take yi, dama Aysher bata iya ciwo ba se ta gigice ta gigita iyayenta da kuka da raki. "Aysher!" Ya kira sunan chan ƙasan makoshi, kokarin buɗe idanun take sede har lokacin hawaye ke zuba, bata ma iya kallonshi sbd idanun babu madubi. "Me ya faru? Menene matsalar?" Yayi maganan cikin tsantsar tausayi. Lip ɗin ta da yayi ja sharrr ta taune tana sake lankwashewa, hannunta ɗaya dake marar ta ya bi da ido. "Cikin ki ke ciwo?" Kai ta gyaɗa tana sake fashewa da kuka tana kuma yarfa ɗayan hannunta. "Me kika ci? Daena kukan nan and talk, me ya janyo ciwon?" Cikin Muryar kuka tace "ban sani baa Abbaa" Sake kallon marar yayi da lokacin ta janye rigar ta ɗaura tafin hannunta bisa marar tana murzawa cikin kuka, kallon fuskanta yayi a matsayin shi na likita kai tsaye ya hasaso abunda ke damunta "period pain? Dama yana miki ne?" Sam bata gane me yake nufi ba ta saukar da wuyanta daga tafin hannunshi ta sake kifewa, girgiza kai tayi ita kaɗai ta san me take ji. Sake juyo ta yayi "Ki natsu mana ban son rashin hankali, keep quite and tell me dama kina ciwon mara ne yayin al'ada?" Cikin kuka da ɗan tsoro sbd da ɗan tsawa haɗe da damuwa yayi mata maganan tace "Ni ban sani ba, ban taɓa yi ba" Wara idanu yayi "baki taɓa period ba? Shekarun ki nawa?" Numfashi taja tana yarfa hannu cikin sakin sabon kuka tace "wayyoo baffana wayyooo Nene zan mutu, wlh mutuwa zan yi..." Ganin gabaɗaya ta gama ficewa hayyacinta yasa ya sanya hannu ya sure ta kawai suka fito, drivernta ne ya buɗe mishi mota ya sanya ta, ya bashi umarnin tafiya kawai se gobe in taji sauƙi, da hanzari ya shiga driver seat ya ja motar suka fice. Har gaban tamfatsetsen building na asibitin nashi da aka rubuta CITY CLINIC a chan tsolon ginin dake nan kaman skyscrapper yayi parking, da gudu security dake tsaye daga bakin enterance ɗin ya je ya buɗe mishi kofa, fitowa yayi ya buɗe bayan ya sake daukar ta ya nufi ciki se bashi hanya ake ana miƙa gaisuwa sede be kula kowa ba. Katon floor ne dake malale da farin tile daga ka shigo enterance ɗin, chan daga gefe reception ne amma yayi nisa sossai, matattakalai har biyu ne daga nan ƙasa kana iya hangar saman sbd glass ne da shima kaman floor ne, in ka miƙa daga ƙasan akwai elevator wadda kaman har guda biyu ne daban daban, majinyata dake sanye da kayan asibitin ke ɗan kai kawo da en uwansu. "Sir in kawo wheelchair?" Nurse ɗin da ta iso da gudu ta faɗa, girgiza kai kawai yayi ta bishi da sauri ganin yayi elevator alhali emergency ɗin su na daga ɓangaren hagu a First floor ɗin, ita ta danna mishi ya shiga tana shakka shakka sanin halin shi ta tambaye shi wani floor? "8" Abunda ya faɗa kenan yana ɗan kallon fuskan Aysher dake kife a kirjin shi jikinta gabaɗaya a sake, likitoci uku ne suka shigo suma da sauri kan ya rufu, kowa so yake ya samu privilagde ɗin ogan nasu sbd mutum ne shi me kirki da sanin ya kamata, ma'aikatan shi suna matukar mutuntashi sbd shima yadda yake mutuntasu, abunda ze sa Kaga ya ɗauki tsatsauran mataki akan ma'aikaci to ba ƙarami bane, kawai dae baya son wasa da aiki in kana so ku shirya ka kasance ka san makamar aikin ka, mata kan mishi kallon marar mutunci da wulakanci sbd yadda baya basu fuskan kawo mishi wargi inda Allah ya tsare shi ma kwarjininshi baya bari mace ta fuskanceshi da wani banzan zance, ko kinyi kokarin yi yana tsura miki mayun idanunshin nan zaki rikice ki rasa abin faɗa a dole suka shafa mishi lafiya. "Someone should call Dr Hafsa ta sameni a office na now please" Ya faɗa yana kallon likitocin, a tare suka fiddo waya sede ɗaya ne ya samu ya kira ta. "Oga needs you in his office now! Its an emergency" Yana kai nan ya sauke daidai elevatorn ya buɗe kai tsaye ya miƙa doguwar floor ɗin. "Zaku iya komawa aikinku" Da sauri ya wuce ya shiga katuwar office nashi me ɗauke da wasu irin office furniture na garari, misalta tsaruwa da fasalin office ɗin ɓata lokaci ne, gabaɗaya asibitin kaman a Turai ba Nijeriya ba, a kan gado dake cikin office ɗin ya shimfideta se murkususu take yi tana kuka a hankali. Dr Hafsa da kwararriyar gynae ce ta danna door Bell yaje ya buɗe, ta shigo tana miƙa gaisuwa ya nuna mata gadon "My daughter.. I think she's having cramps matsalar inaga this is her First period gashi ta ja shekaru" Dr Hafsa da bata yi mamaki ba sbd ana samun irin cases ɗin wata se ta kusa twenty years ma bata fara ba, wasu kuma daga shekara goma kai har me shekara tara ma ita ta taɓa karo da ita a harkarta na gynae, isa gadon tayi ta yaye rigar na Aysher da sauri ya ɗauke kanshi ya koma kujeran shi ya zauna don ya barta tayi aikinta. Bayan gama observing tace mishi tana zuwa, pharmacy ta wuce ta karbo allurai ta dawo, shi kam yana zaune yana ɗan aiki Dukda ya tsinci kanshi da yawan kallonta kaɗan kaɗan se ya ɗaga idanu ya kalleta, Dr Hafsa na zuwa ta haɗa injections ɗin tayi mata har lokacin jinin be sauƙa ba kawai masifar ciwon marar ne ya hautsina ta.. Seda kuwa ya taso ya taya Dr Hafsa kan aka yi allurar se hawaye take yi. "Sir da alama this ur daughter sangartacciya ce, ji yadda take ta raki akan M.p da yanzu ta fara shi? Hmm akwai aiki kenan every month!" Yana kallon fuskan Ayshern ya ɗan yi murmushi kaɗan "she's in pain ne ba raki bane, now komai ze daidaita kenan?" Tana ɗaura mata drip tace "Yeah, in shaa Allah daga ruwan nan ya kare ina ga komai ze yi daidai dole ne ta samu irin wannan cramps sbd rashin farawa da wuri, ze iya yiwuwa ta samu wani watan ze iya kuma yiwuwa cramps ɗin na farko ne kawai, amma please ta rage shan zaƙi sbd gudun irin wannan wahala" Kai ya gyaɗa a ƙasa ƙasa yace "thanks" Juyawa tayi ta fice tana mamakin ganin yadda duk ya damu, se kuma tana mamakin ta yadda Wannan ɗin ta zama ƴar shi, gyaɗa kai tayi "ze iya yiwuwa don prof ba karamin yaro bane kawai jikinshi ne Allah ya halliceshi me kyau, sannan ma family ɗin shi da abunda ya shafe shi to him are confidential don baya taɓa magana akan family, ko matarshi bana tunanin akwai wadda ya santa" Ta ida maganar tana zama a kujeranta. "Amma fa yarinyar tashi kyakyawa ce shi ta biyo ga dukkan alama" Ni dae nace aiki ya sameki Dr Hafsa. A chan office nashi kuwa ya jima yana aikinshi don har drip ya kare bata farka ba yaje ya cire mata baccin da bata samu daren jiya ba take yi peacefully, yana da aiki a lokacin so change room ya shiga ya sauya kayanshi zuwa blue riga me karamin hannu da wando wadda yayi matukar amsarshi, hular ya riƙe a hannu tare da face mask ya tako ya fice zuwa theater, ya shafe awa uku cur kan ya fito daga nan bakin kofan ya cire rigan da ya ɗaura a saman blue kayan me kaman leda tare da handsglove da facemask duk ya zuba a cikin kwandon shara kan ya wuce kai tsaye zuwa office ɗin shi... Ita kuwa cikin bacci tayi ta jin wani abu na sauƙa mata me lema lema wadda yayi making ɗinta uncomfortable, juyi tayi a hankali ta soma buɗe idanunta da suka yi nauyi sossai, bata iya kallon komai se farin haske me surkin duhu, a hankali ta fara laluɓe se ta fahimci kaman ba a gadonta bane... "Akwai mutum a nan don Allah?" Ta faɗa a ɗan tsorace, shiru ta sake maimaitawa shiru.. Zaune ta miƙe a tsorace jikinta na rawa ta sake maimaitawa "wayyoo baffana...!" Buɗe kofan da aka yi ya sakata firgita ta koma baya tana sake laluɓe cikin rawan lips take cewa "wa...waye? Pls help me bana ganin komai.." A wurin ya tsaya yana kallonta fuskanshi with blank expression changing room ɗin shi ya nufa ba tare da ya ce komai ba, a cikin aljihun trauser suit ɗin shi ya fiddo glases din ta da har ya nufi barin ɗakinta da ita a hannu ya tuna ya koma ya ɗauka a bed side, fitowa yayi kai tsaye ya nufe ta.. Ƙamshin turaren shi ne ya sa ta natsu daga birkicewar da tayi ta zata ita kaɗai ce, hawayen fuskanta ta share cikin rawan voice tace "A...bb...a" Be yi magana ba seda ya sanya mata glases ɗin da kanshi idanunshi a fuskanta yace "ya cikin? Ya daena ciwo?" Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke se yanzu taji daidai ganin tana kallon komai rass, se kuma lokacin ta tuna da cewa tana ciwon ciki, da sauri ta matsa tana kallon inda ta zauna jin da gaske lema ne a ƙasanta a tare suka sauke idanunsu kan ɗan jinin da ya ɓata wurin kaman kiftawar ido ta koma da sauri ta sake zama a wurin tana sunne kai ƙasa cikin tsantsar kunya ji take ina ma ƙasa ya tsage ta shige da wannan abun kunya.. "Wait here ina zuwa" Yana kai nan ya koma change room ya chanza zuwa navy blue suites da ya zo dasu ya zo ya fice daga office ɗin har lokacin kanta a sunkuye. Sake matsawa tayi tana kallon jinin a ranta tace oh na shiga uku shi kuma wannan abu da tonon asiri ya zo, wayyooo Allahna ya zanyi da wannan kayan kunyar...? Tun tana da shekara goma sha biyu take jin wasu daga cikin Ƙawayenta kan yi labarin al'ada al'ada kan aka zo ma aka yi musu a fiqhu a islamiyya, kan ta isa sha huɗu kusan duka Ƙawayenta kowa na yi se ita, tun bata damu ba har ta fara damuwa har ma Nene seda tayi magana akan hakan duk alkunyar ɗiyar fari da take mata, amma da tayiwa baffa magana yace kar ta damu ze zo ne in lokacin yayi se yanzu da take sha shidda, tuna irin azabar ciwon da ta sha daga jiya zuwa safiya yau tayi a fili cikin Murya kaman me fashewa da kuka tace "na shiga uku yanzu ko wani wata haka zan yi wannan ciwo??" Ƙarewa office ɗin kallo ta soma yi, gaskiya bata taɓa ganin office me tsaruwar wannan da kyau ba, komai a kimtse a killace, a hankali ta sauƙa tana sake kallon gadon bedsheets din da yake fari sol ta cire ta nufi wani kofa da adu'ar Allah yasa toilet ne, tana buɗewa kuwa taga bayi ne, shimfide da fari sol ɗin tile se kamshin freshner yake fitarwa, da sauri ta shiga tayi ta dube dube kan ta samu liquid soap dashi tayi anfani ta wanke bedsheet din ta shanya, daga tsaye da take taji jini na gangara a jikinta alamun fa jinin ta na flooding sossai, hannu ta ɗaura a kai "Ya zanyi yanzu???" Tayi maganan kaman zata yi kuka, knocking ɗin kofan toilet din taji a anyi da hanzari ta ɗaga kai tana kallon kofan gabanta na faɗuwa ta kalli kafafunta jinin har ya kai nan. Muryar mace taji tana cewa "Aysher ki buɗe zan baki abunda zaki kimtsa jikinki ne" Ajiyar zuciya ta sauke kan ta nufi kofan ta buɗe. Dr Hafsa ce wacce tana haurowa ne don duba Aysher din se ta gamu da Emran, leda ɗaya daga cikin ledojin hannun shi ya miƙa mata yana ce mata "pls help her doctor" Karɓa tayi cikin murmushi tace "patient ɗita ce sir ba se ka rokeni ba" A tare suka shigo ganin bata gadon ne yasa Dr Hafsa isa bayin. Shiga ciki tayi tana kallon yadda jinin ya ɗan ɗidɗisa a ƙasa "sannu ya jikin?" Kanta ta sunkuyar tace "da sauƙi ina kwana?" "Yini dae yanzu ai sha biyu ya wuce" Tayi maganan tana fidda pad ɗaya daga cikin roll ɗin shidda da ya saya da wasu panties da suke cikin leda set guda tace "kin iya anfani da wannan?" Kai ta girgiza, a natse likitar ta nuna mata "amma kiyi wanka tukuna ga wannan kaya ne" Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke Dukda kunyar dake dawainiya da ita tace "Na gode" Fita Drn tayi yayinda ita kuma cikin kunyar kanta ta cire kayanta ta watsa ruwa, share bayin tayi tayi mopping ya bushe yadda ta same shi bayan ta saka pant dake ɗauke da pad ɗin, seda ta gama ta warware doguwar riga fari da milk stones da ya saya mata, rigan yayi bala'in yi mata kyau, daga ɗan karamin waist ɗinta a kame kasa kuma ya buɗu amma ba chan ba, dogon hannu yake dashi. Gashinta take son kamawa amma babu abun kamawan hakan yasa ta ɗauki tsiririn ɗan kwalin da be wani rufe kanta sossai ba ta saka, kallon kanta tayi a madubin bayin tayi kyau sede kam se taga kaman Naina sbd irin shiganta ne hakan, kila taste ɗin matarshi kawai ya sani ta ayyana, amma ita kam ina kunya ze barta ta ratsa mutane haka? Ɗaukar ledar pad da panties din tayi ta nufi kofa gabanta na faɗuwa, yanzu in yana nan ya zata yi? Da wani ido zata kalleshi? A hankali ta murda handle ɗin ta fito. Yana zaune gaban desk ɗin shi yana duba system, da ƙadan da kadan tayi ta matsowa kaman me tsoron taka ƙasa duk bata san ma tun fitowarta yake kallonta ba sede ta ƙasan idanu, dariya ma ta bashi amma da yake shi ba gwanin dariya bane se ya ɗan murmusa ƙasa ta duƙa "Abba ina yini?" "Lafiya, ya jiki?" Ya amsa bayan ya ja lokaci "Alhamdulillah" Ta faɗa tana tsugunen Da hannunshi ya nuna ledar dake zaune a gefen table ɗin nashi yace "zo ɗauki wannan ki ci" Miƙewa tayi ta zo ta ɗauka. "Seat there" Ya faɗa yana nuna army green ɗin cushions dake daga gaban desk ɗin nashi Dukda akwai tazara kaɗan, wurin taje ta zauna ta fiddo abincin lafiyayyiyar biryani ne da kaza a samanshi, a natse ta soma ci sbd yunwa da dama yake cin cikinta. Seda ta gama ta maida takeaway ɗin leda taje ta sa a bin da ta gani daga chan kusa da kofa, dawowa tayi ta zauna tana wasa da yatsun hannunta yau tayi missing school ta ayyana a ranta. Ta jima nan zaune kan taji motsin tashin shi gaban table dake daga tsakiyar kujerun da take kai ya isa ya ɗauki remote ya kunna Tv, kan ya juya zuwa change room ya sake sauya kaya zuwa na theater fitowa yayi yace "Ki jirani anan, ina da aiki" "Allah ya bada sa'a" Ta faɗa tana kallonshi har ya fice, Miƙewa tayi ta fara yawo a office ɗin tana kallo gsky ya mata kyau ainun, jikin Windows taje ta ɗan yaye se ta wara idanunta chabbb ashe a sama sossai take ganin wasu buildings din sun kai na asibitin wasu kuma basu kai ba, ga tituna a shimfide motoci se kai kawo suke, ta jima anan tana jin wayoyin shi dake zube kan desk ɗin shi na ringing sede bata yi gigin zuwa wurin ba ma. Tana jin kiraye kirayen sallah azahar ta dawo kujeran ta zauna tana kallon Tv, har ta gaji ta kwanta bata yi aune ba bacci ya kwashe ta anan. *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰 🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA   بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* FREE PAGE 11 Se after 3 ya shigo, a hanzarce ya nufi toilet turus ya ɗan tsaya yana kallon yadda ta shanya kayan baccinta da ta wanke a bayin, ɗan tsiririn tsaki ya ja ya nufi washing handbase ya saba in yayi aiki ya fi ɗaya a rana kan ya iya maida kayan shi se ya watsa ruwa sbd ze yi ta jin ƙarnin jini ne Dukda ko kusa ko alama jinin be taɓa fatar shi ba amma haka kawai ze yi ta jin rashin natsuwa, yau kam dae ba ze iya ba. Alwala yayi ya fito ya nufi change room ya sauya kaya kan ya matsa inda yake sallah idan be samu jam'i ba ya tayar, bayan ya idar yayi adu'o'inshi kan ya miƙe ya nufi gaban desk ɗin shi missed calls ya samu, na Naina, Asma'u da Naufal se wasu... Kaman ze kira Nainan se ya tuna yadda tayi biris dashi da safe akan Aysher, ya rasa me ke damunta wannan dae kam kai tsaye za'a ce rashin tausayi da imani, me Aysher tayi mata da zafi da hatta ciwo ma ba za'a ɗaga mai kafa ba? Asma'u ya ƙira ringing biyu ta ɗaga muryarta da alama tayi kuka ta gaishe shi "Me ya faru?" Ya tambaya. "Babu, Yaya ya jikin Aysher din? Is It serious?" Muryanta yayi sanyi dayawa kaman ba Asma'u ba, ba don ya yarda da babu komai ba kai ko kiranshi da yaya da tayi ya nuna akwai damuwa yace "taji sauƙi...." Ɗayan hannunshi cikin aljihu ya nufi gaban kujeran da take ya tsaya yana kallonta ya ƙara da cewa "bacci ma take" Ajiyar zuciyar da har seda yaji ta sauke kan tace "Allah ya bata lafiya" Daga haka suka yanke wayan. Kan ya sauke hannunshi kiran Naufal ya shigo dagawa yayi kan yayi magana Naufal ya fara jero mishi tambayoyi "babban yaya ya jikin Preetty? Maami ke ce min bata ji daaɗi ba naje gidan ma ban samu kowa ba, is it serious? An bata gado ne? In zo asibitin ne? Idanunshi da ya lumshe ya ware yana ɗan murmushi yace "taji sauƙi, we are heading home now" "Toh zan jiraku Yaya" Daga haka ya sauke wayan, wayan ya ɗan bi da kallo na seconds kaman wayan ya zama baƙon shi kan ya kalleta. "Aysher" Ya kira sunan yana ɗan bubbuga jikin kujerar, da alama tana da nauyin bacci. Seda ya kira sau uku kan ta farka, da sauri ta zauna tana gyara rigan jikinta, uncomfortable take jinta barin ma da ta zauna kasancewar ta jima a kwance tana jin yadda jini ke fita mata se taji gabaɗaya ta takure. "muje gida" Yana kai nan ya koma ya tattari abunda ze tattara kan ya nufi kofa tana tsaye rike da ledar ta ya buɗe ta bi bayanshi suka fice,  bata ga ya sawa kofan kwado ko key ba hakan yasa tayi ta juyawa tana kallon kofan kar dae mancewa yayi, gyara gyalen ta tayi tana kallo ya danna wani abu kaman kofa suka tsaya gaban abun tana daga bayanshi na mintuna kan abun ya dare biyu, shi ya shiga tabi bayanshi cikin tsoron da ya kama ta ta fara kalle kallen cikin elevator ɗin. Danna wani arrow da ya nuna ƙasa taga yayi, se taga abu ya rufu ya fara motsi da sauri ta rufe idanunta jin jiri na kwasarta baya tayi ta sake dawowa gaba se goshinta ya bugi bayanshi, karamin ƙara ta saki shi kuma yayi hanzarin Juyowa yana riƙe hannunta ganin tayi baya a tsorace zata faɗi. "Yi haƙuri jiri nake gani" Ta faɗa cikin diriricewa sbd idanu da ya ɗan tsura mata. Hannunta da be saki ba ya ɗaura akan wani handle dake gefe da gefe alama na rikewa ne se ta damke ta sake runtse ido jin da gaske jiri take ji. Har ya tsaya be daena observing ɗinta da ido ba, kofan na buɗuwa yace "muje" Se ta buɗe ido ta shiga gaba ganin ya bata hanya, kaman zata kife take tafiya, ga jiri ga kunya sbd gani take kaman kowa ita yake kallo. Seda yaga zata bi wani hanya kan ya shiga gabanta a tare suka fito ma'aikatan na ta mishi se da safe, motan shi da ya ɗaga a sadda ta fita yaje mall ya sama mata kaya da abinci ya nufa parking lot da nashi ne na musamman ya buɗe ya shiga, tana ɗan kallon kayatuwar harabar asibitin itama ta buɗe gaba ta shiga, a hankali ya ja suka fice daga asibitin se a lokacin ta tuna kayan baccinta dake shanye a office nashi kuma harda inner wear dinta da ta cire, runtse idanunta tayi gashi ba halin ta ce su koma kuma bata da zarrar da zata iya ce mishi gobe ya kawo mata, ina ma ta isa? Amma kuma ya ze yi gobe idan ya je ya gani.. Da wannan sake sake suka isa gida, ita ta soma shiga parlorn se taga Naufal da Naina suna zaune suna kallon Tv lokaci lokaci suna ɗan hira, dama shi mutumin ta ne ta kan sake mishi su yi hira. "boɗɗi..! Noi a ɓeɗɗi matugo?" (Ya kika kara ji da jiki?) Ya faɗa yana Miƙewa tsaye ba tare da ya amsa sallamar da tayi ba. "Alhamdulillah wodi dama(da sauƙi) Ina yini?" Ta haɗa gabaɗaya sbd ta samu ta wuce ganin Naina da irin kallon da take mata na sama da ƙasa. "Zauna mana!" Ya faɗa, a ɗan darare ta zauna a ƙasa tana kau da idanunta daga deadly look da Naina ke mata.. Wani irin abu ne ya tsayawa Naina a wuya yanzu wannan yarinya har she's worth of wearing thomb Brown? Sabon desinge ma da ko ita ta saya ne bata saka ba amma wannan ƴar kauyen ta riga ta sakawa, yanzu ma wai tare suke da mijinta tun safe? Tsaki me karfi taja ganin yadda duk Naufal ya ruɗe a kanta, ga Emran ma da ya shigo se ya samu wuri ya zauna, Miƙewa tayi ta bar parlorn ba tare da ta ko kula gaisuwar da Ayshern ke mata ba. Naufal ne ya gaida yayan nasu ya amsa mishi yana tambayar su Ammi sbd be shiga ba yau, amsa mishi yayi da suna lafiya suna yiwa Aysher ma sannu da jiki. Miƙewa yayi yace bari yayi wanka ya shige. Kaɗan kaɗan take amsa mishi sbd zama da tayi da dare tayi nazari akan chanzawar Asma'u a jiya, ta fara tsoron abunda Naufal ze iya cewa sbd kowa ya zauna da Asma'u ko bata fita fili ta faɗa ba zaka san akwai soyayyar Naufal a ranta gashi shi kuma inda ya dosa daban, sam bazata so ya lalata kyakyawar alaƙarsu ba sbd da ita ne kawai take zama taji daaɗi duk garin na Abuja da ta tsinci kanta ciki babu zato bare tsammani. Ganin yadda take amsa mishi ne yasa yace "ko har yanzu jikin ne?" Kai ta gyaɗa tace "Ina so ne in ɗan kwanta" "Toh Allah ya qara sauƙi, zan shigo gobe in duba ki" Girgiza kai tayi "Ai gobe zan je school ne" "har zaki iya zuwa school? Ki huta mana samu ki ƙara samun karfin jikin?" Nan ma girgiza kai tayi "Ai da sauƙi in shaa Allah zan iya zuwa" "to shikenan ko zuwa dare zan shigo, me zan kawo miki? Baki bukatar komai?" Girgiza kai tayi ba tare da tayi magana ba "sai gobe ɗin" Tana kai nan ta nufi ɗakinta, da kallo ya bita har ta shige, yarinyar is just a damsel ya ayyana yana murmushi a bayyane. Har aka kira la'asar kan Emran ya fito sanye da kananun kaya da alamun yayi wanka ya chanza a tare suka fice masallaci da Naufal, bayan sun dawo be shiga ba ya tafi shi kuma ya dauki mota yaje nema musu abunda zasu ci, har se bayan Magrib ya shigo don ya ratsa wurin friend ɗin shi Sufyan sbd kwana biyu sede suyi waya sam basu samu time na juna ba. Kai tsaye knock ya mata don ya bata nata ya kuma duba jikinta, buɗewa tayi har lokacin rigan ne jikinta ta gaishe shi ya tambaye ta jiki ta amsa a kunyace, diary milk dake hannunta ya bi da kallo a sadda take karɓan abincin, kaman baze yi magana ba chan ƙasa ƙasa sbd gajiya da yake ji yayi ga kasala dake rufe dashi tun safiyar yace "Hey in ba so kike duk wata duniya su san kina period ba to ki rage shan wannan zaƙin" Ya karashe yana nuna choculate ɗin ta idanu... Ina ƙasa ya buɗe ta shiga..kasa ta sunne kanta be jira amsarta ba ya juya ya tafi gab ze shiga ɗakin Naina ya ɗan saki murmushi da shi kaɗai ya san dalilin abunshi kan ya buɗe kofan ya shiga. Tana kwance a kan gadonta hannunta na ɗaure a kan goshinta jin motsin shi be sa ta ɗaga kai ta kalleshi ba "Babe" Ya faɗa chan ƙasa A hankali ta ɗaga idanunta ta kalleshi, yana zama gefen ta ya riƙe hannunta yana ɗan shafa bayan a hankali yace "whats ur problem?" "Ka daena ɓata bakinka wurin tambayata kaima ka san matsalolina biyu ne daga na wannan shegiyar yarinyar se na haihuwa" Idanunshi ya lumshe ya sake buɗewa "Meyasa? Meyasa burin ki ko yaushe ki ɓata min rai Naina? Sau nawa zan gayamiki muhimmancin Isma'il a wurina ne? Why zaki sheganta mishi ƴar da ya haifa ta hanyar aure da sunna?" Ganin Ranshi ya ɓaci ne yasa ta miƙe zaune se ta takwashe kafa ta kife kanta a kirjin shi "Am sorry... Ka sanni ban iya ɓoye so ko ƙi ba Emran ban san Meyasa a ko yaushe na kalleta se in ji kaman zan mutu ba" Sbd sanin yana da bukatarta ne kawai ya sa ya soma shafa bayanta "hakan babu kyau, bata miki komai ba fa hasali ma tsoron ki take ji ki daure ko ba zaki so ta ba karki ƙi ta, and ban ji daaɗin abunda kika yi ba yau ciwo ai ya wuce gaban wasa kuma kema baki fi karfi Allah ya jarabceki da ciwo ba kina tunanin ita zata iya ganinki ta kyale ki ne? She's just a little girl with a pure heart pls Naina drop all ur dramas i beg u" Shiru tayi bata iya ta ce mishi komai ba, abincin da ya kawo musu ya sakata ɗauko plates da sauransu suka ci a ɗakin nata, tana ɗan mishi hirar success din ta a company ɗin su da kuma business trip da take son zuwa chan Thailand, se a sannan ya faɗa mata tafiyar su ma ya gama komai its next week monday, sossai tayi farin ciki kila bazata dawo ba se da ciki. Bayan sun gama yace ta shirya kwanciya ta same shi a ɗaki, Dukda she's not in the mood amma ta san buƙatuwar mijin nata, haka dae ta shirya ta isa ma ta same shi Fitowar shi wanka kenan ɗaure da towel a kugu kayan baccin da be sa ba kenan, ta gurzu har seda yaga ta jiggata ya kyaleta ya kwanta daga gefenta yana runtse idanunshi da sauri ya kuma buɗewa ya ja tsaki tare da dirka ya shige toilet ya sakarwa kanshi ruwan sanyi... Washegari Aysher bata zauna ba tunda tayi sallah ta fita kitchen doya ta soya se ta mishi miya ya ji albasa sossai, a dining ta shirya tea take son sha, se ta tuna wadda Nene ke yiwa baffa itama kila ya taimakawa cikinta da lokaci lokaci yake ciwo, ruwa ta zuba a tukunya ta ɗibo kayan kamshi ta zuzzuba har da busashen lemon grass da ta samu a kitchen ɗin, ta zuba sugar se ta ɗauko madara cikin na kamfanin Alhaji, evaporated one ne ta zuba a ciki, seda ya dafu kan ta tace ta zuba a flask ta kai dining ɗin ta dibi nata ta koma ɗaki, sauri sauri ta ci ta shiga wanka ta fito ta zo ta shirya cikin uniform ɗinta. Hannunta rike da socks da take son sawa a mota sbd makarar da tayi ta fito, a dining ta same shi yana zaune yana karyawa hannunshi riƙe da kofin tea din da ta yin yana sha shi anya akwai randa ze daena mamakin hannun yarinyar a girki? Sossai tea ɗin ya mishi daaɗi, har gabanshi ta zo ta duƙa. "Ina kwana Abba?" "Lafiya ya jiki?" "Lafiya ƙalau Naji sauƙi" "ya daena kwata kwata?" Ya tambaya kai ta gyaɗa ba tare da ta ɗago ba, yace "to Alhamdulillah, Allah ya tsare" Ta miƙe ta fice bata ga motar Naina ba alamun ta riga su wucewa ne ta shiga wadda ke kaita driver ya ja ya wuce. A ranar da ya fita ya je gida ya sa me aikin Hajiya zuwa kasuwa da driver aka sake siyayya me yawa aka kai gidan nashi, ko da Aysher ta dawo ta gani ta ji daaɗi don akwai ganyayyaki har da kubewa, wanda zata sa a frigde ta sa kubewa kuwa ta sa a kwando ta ajiye waje sbd in an sa a frigde yana baki, tun daga ranar har satin ya kare tayi abinci kala kala wadda sossai Yake jin daaɗinsu, ita ba wai tana yi don burge shi bane kawai tana yi sbd tana ganin hakan ne ya kamata bazata zauna yana dafawa ko kullum yana zuwa saya ba tunda komai a kwai ba babu ba... A ɓangaren makaranta babu abunda ya sauya daga yadda su Maryam ke treating dinta bata iya ta faɗawa kowa ba kuma, amma tana kokari wurin karatu sossai, ta ɓangaren Naufal kullum se ya zo da dare wani lokaci ma a gidan yake cin abinci, ran juma'a aka neme su a school dole ta sa ya juya Asabar duk yadda ya so ya saya mata waya ko gaisawa su ke yi Emran yace be amince ba waya ba yanzu ba, ita kuwa Naina babu abunda ya chanza daga kiyayyar da take yi mata sbd, ko zasu haɗu sau nawa baya hana Aysher gaisheta amma bazata amsa ba, ko kallon abincin da take dafawa bata yi idan Emran baze iya zuwa saya mata ba se tayi order ko ta fita taje ta sayo, ƙaninta Nameer shima tun da yazo ya ga yadda tashi ɗaya yar fullon da suka zo da ita ake ta musu dariya a jirgi ta sauya ya fara nuna yana ciki Dukda Addar tashi kai tsaye ta nuna bata amince ba kuma a shirye take ta haɗa shi da iyayen su hakan be hana shi zuwa sa'i sa'i ba... Yau Lahadi bayan ta gama girkinta na dare da tayi tuwon shinkafa da Miyar danyen kifi ta shirya dining, ta zo zata wuce da nata ya dakatar da ita hakan yasa ta samu wuri ta tsuguna a gefenshi, idanunshi ya cire daga system da yake operating tun bayan la'asar a wurin yace "gobe in shaa Allah zamu yi tafiya da Naina" Da sauri ta kalleshi se ta duƙar da kai tana wasa da hannunta ganin shima ita ɗin yake kallo "ba barinki zamu yi anan ba, ki haɗa kayan ki gobe da safe ki sa a mota idan driver ya koma daukar ƙi gida chan ze kaiki har se mun dawo in shaa Allah" Ajiyar zuciya ta sauke dama har ta fara tunanin ta yadda zata zauna a wannan gida ita kaɗai, a hankali tace "Toh in shaa Allah zan yi hakan Abba, Allah ya tsare muku hanya ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya" Murmushi me kyau yayi mata wadda seda gabanta ya faɗi ba tare da ya amsa a bayyane ba, ta miƙe ta shige ɗakinta. Washegari da safe bayan ta gama abin kari ta shirya ta janyo akwatin da ta haɗa duk abunda ta san zata buƙata ta janyo ta fito, yana zaune dining ta duƙa ta gaishe shi, cikin kulawa ya amsa ya kara da "Babu abunda kike buƙata?" Kai ta girgiza yace "karɓi" Kuɗi ne, ta miƙe ta karɓa tare da mishi godiya "se mun dawo ko?" Ya faɗa yana kallon fuskanta ta sake musu Adu'ar sauƙa lafiya kan ta janye akwatin ta fice... Kaman yadda ya faɗa driver gidan Alhj ke kaita bayan an tashi kenan sun tafi ɗin already, da akwatinta ta shiga parlorn, zaune Asma'u take tana kallon wani series, ɗan ɗagowa tayi ta kalleta ta maida kanta kan Tv ɗin ta bayan ta amsa sallamar, wani irin sanyi jikin Aysher yayi ta ƙaraso ta zauna tare da cewa "Aunty Asmy ina yini?" Ba tare da ta kalleta ba tace "Lafiya" Anan Aysher ta ci gaba da zama har tsakiyar ranta bata ji daaɗin hakan ba amma ya zata yi? Bata san wani hanya zata bi wurin fahimtar da ita cewa bazata ma iya auren Naufal ba ko da tana son shi kuwa sbd Auntyn nata ta wuce hakan a wurin ta. *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰                           🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN          (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* FREE PAGE 12 "Asma'u ya zaki barta da kaya anan parlor ko uniform bata cire ba bare ayi zancen cin abinci?" Ammi dake shigowa ta faɗa. Miƙewa Asma'u tayi tace "muje Aysher" Itama ta miƙe dauke da kayanta suka haura, ɗakin dake gefen nata ta buɗe mata, a tare suka shiga Aysher ta ajiye akwatin tayi saurin Juyowa jin Asma'u na shirin fita tace "Aunty Asmy!" Dakatawa tayi ba tare da ta juyo ba, daga bayanta Aysha ta tsaya idanunta na cika da kwalla tace "Kiyi haƙuri don Allah, ke kaɗai ce nake samun sanyi a wurinki a kab garin nan, kece kika fara amsata da hannu bibbiyu ba tare da kyama ko kyara ba idan kika yi fushi dani kika kyaleni ba zan taɓa jin daaɗi ba, wlh ba abunda kike zato bane tsakanina da Ya Naufal, ko karen hauka ne ya cije ni ba zan iya amsawa wanda kike so da ƙauna soyayya ba ko da kuwa zan mutu ne bare ma wlh babu ko ɗigon son shi a raina, kaman yadda na ɗauki Abbana uba haka dukkanku kuke iyaye a gare ni, don Allah kiyi haƙuri" Ta karashe da kuka da ta kasa controlling.. Asma'u ma da nata hawayen ya gangara ta runtse idanu tana tuna rashin hankalin da tayi, bata san Meyasa tayi pouring out fushin da ya kamata tayi da Naufal akan Aysher ba tunda shine ya nuna interest a kan Ayshan ba ita ce ta nuna tana yin shi ba, sannan ko da hakan ne ma ita ai me iya sadaukarwa Aysher Naufal ne sbd har ƙasan ranta Allah ya dasa mata kaunar yarinyar.. "Ni ce ya kamata in baki haƙuri Aysher ba ke ba, baki min laifin komai ba, zuciya ne kawai da sheɗan se kuma borin kunyar son maso wani da na jima ina yi ba tare da na san shi ba hakan bace a wurinshi..." Idanunta dake zubar da kwalla sossai ta ɗaga sama "ba zan hana ki son shi ba in har dae yana daga cikin irin mazan da kike so da burin aure, don Allah a duk sadda ya kawo miki kokon bararshi ki yi min alfarma kar ki ƙi, dukkanku ina son ku da alkhairi" Da sauri Aysher ta girgiza kai "ba zan iya ba, ya ma fi ƙarfina Aunty Asmy, ba fa zan iya ba kiyi hakuri mu bar maganan nan ni karatu zan yi" Ajiyar zuciya Asma'u ta sauke kan ta juyo tana ɗan murmushin yaƙe "je kiyi wanka ki sauko ki ci abincin kar Abbanki ya yanka min sammacin barin ɗiyar shi da yunwa" Murmushi Aysher ta saki cikin jin daaɗi ta fara cire uniform din jikinta. Bayan tayi wanka ta sauya kaya ta sauƙa ƙasan a nan ta ɗibi abinci ta zauna suna kallon wani hausa film da Asma'un lokaci lokaci su kan yi magana, har bayan la'asar suna nan kaman yadda Aysher bata sallah haka ta lura Asma'un ma, seda Ammi ta zo don shiga kitchen suka miƙe suka bi bayanta, a tare da ita suka yi girkin gida da na Alhaji wadda tuwon dawa ce da Miyar kuka da yaji man shanu, basu bar kitchen ɗin ba se Magrib, duk kowa ɗakinshi yayi, ita kam Aysher tana shiga azkar ta hau yi bayan ta gama ta kwanta cikin tunanin ko su Abba sun isa lafiya? Gashi bata da waya bare ta kirashi taji... Miƙewa tayi ta fito tana shirin yiwa Asma'u knocking se gata ta fito "ɗiyarmu ya aka yi ne?" Cikin jin daaɗin yadda Asma'un ta koma mata kaman da ta ce "Aunty Asmy ko kin kira Abba kin ji sun isa lafiya?" Murmushi Asma'u ta saki tace "sun isa lafiya ya kira Ammi, anjima se in kirashi ku gaisa tunda har kin fara kewar su" Dariya kawai tayi ba tare da tace komai ba. "Yauwa ya jikinki? Me yake damun ki daman?" Asma'u ta faɗa suna sauka downstairs "ciwon ciki, wlh na ɗauka mutuwa zan yi ai duk son da kika koya min na choculates na hakura dashi na rage sbd Abba ya ce shine ya janyo" Dariya Asma'u tayi sossai tana cewa "Allah sarki sannu ko, ba zaki mutu ba in shaa Allah se buruka sun cika, amma dama yana miki ne shan choculates ɗin ya ƙara shi?" "Ban taɓa yi ba ma se wannan" Ta faɗa tana jin kunya, da mamaki Asma'u da har ta fara zuba musu abinci ta kalleta lallai tayi delay, parlor suka dawo suka ci abincin a tare suna hira bayan isha suka yi wurin Hajiya ta fi Ammi sakewa da hira anan suka yi ta hirar ruga da abubuwan cikinta wanda duk suka yi kewa. Misalin karfe tara na dare wayan Hajiya yayi ringing ta ɗaga da sallama se kuma fuskanta ya washe da fara'a tana ambaton sunan Emran "Alhamdulillah kun sauƙa lafiya dae kam?" Ta ɗan yi shiru kan tace "masha Allah, ina Nainan ina mata sannu da hanya" Shiru ta ɗan yi se ta sake cewa "gasu nan ma muna ta hira dasu" "Asma'u karɓi" Ta faɗa tana miƙawa Asma'un waya. A ladabce ta gaishe shi, bayan nan ta ɗan yi shiru se kuma lokaci lokaci take cewa to ko in shaa Allahu. Se kuma ta kalli Aysher don kaman tambayarta yayi. "Gata nan, dama dazu ta gama tambayata ko mun yi waya kun sauƙa lafiya!" Ta faɗa tana miƙa mata wayar. Karɓa tayi cikin yanayin sanyin ta ta saka wayan a kunne tare da sallama, shima ya amsa ba tare da ta bari yayi magana ba ta fara gaisheshi "Alhamdulillah" Shine amsar da ya bata se kuma ya ɗaura da "Ga Asma'u nan duk abunda kike buƙata ki faɗa mata zata kirani ta sanarmin, na manta da safe ban baki pocket money ba na sanya mata a account ɗin ta zata cire ta baki, ayi karatu a kuma kula" Kanta na ƙasa kaman tana gabanshi tace "in shaa Allahu, Na gode Allah ya saka da alkhairi Abba ya bada sa'ar abunda aka je nema" Chan ƙasa ya amsa da Ameen tare da yanke wayar, saukewa tayi ta bi da kallo se ta saki ɗan murmushi kan ta miƙawa Hajiya da suka cigaba da hirarsu da Asma'u. Ganin tana ta hamma ne ga gobe akwai school yasa suka yiwa hajiyar sallama suka nufi part ɗin Ammi, a hankali Asma'u tace "Ni kam ɗiyarmu ko kin san idan wannan jinin ya ɗauke akwai wankan da ake yi nashi na daban?" Kanta ta ɗan sunkuyar kan tace "Eh Aunty Asma'u an koyar damu a cikin fiqhu" "Kinga faɗamin yadda ake in ma kin mance wani wuri se in tuna miki don fa Abbanki yace in tabbatar kin iya yadda addini ya koyar" "innalillahi....Abban ne yace hakan?" Tayi maganan kaman zata saki kuka wadda ya saka Asma'u kwashewa da dariya, tana ta kwaɓe fuska wai ita kunya ta faɗawa Asma'u yadda ake yin daki daki ta kuwa iya ɗin babu wani kuskure. "Masha Allah kin yi kokari, yanzu je ki kwanta sbd school kar ki makara Abbanki yace baya son hirar banza da wofi" Murmushi kawai tayi tace "Toh se da safe" "Allah ya bamu alkhairi" Haka ta cigaba da rayuwa a gidan, zata iya cewa gidan ya fi mata chan gidan sau dubu saboda tana samun yin hira da mutane kuma a sake take babu me mata kallon kyara ko tsangwama se ma janyota jiki, Ammi kullum se ta bata kudin break Dukda ta faɗa mata Abba ya bata kuma suna nan bata kashewa sossai se tace ta kara, idan weekend ne ba zuwa makaranta ta kan raka Asma'u unguwa in zata fita irin wurin Ƙawayenta ko Saloon ko kuma kasuwa, ta fannin girki sossai take sake koyan irin na zamani a gidan sbd in har tana nan bata taɓa zama a yi girki ba ita, tana nan ciki ta kan tambaye su abunda bata sani ba ko bata gane ba. Ta fannin assignments ma bata wani shan wahala Aunty Asmyn ke koya mata in aka basu, ga Ya Murad da kullum dare tare suke hiransu ya kan kuma sayo musu kayan makulashe su rage dare dashi, bata daddara ba ko in ce ta mance ne oho choculates kam suna sha kaman ba gobe da Asma'u don ita ma gwanar zaƙi ce. A kwana a tashi seda ta shafe sati uku curr a gidan, har kuma lokacin Su Abban basu dawo ba kuma bata sake waya dashi ba tun wayan da suka yi randa suka isa, yau ya kama Litinin cikin sauri sauri ta sauko sbd letti da ta ɗan yi wurin shiri ta isa gaban dining ta duƙa ta gaida Ammi, fuskanta a sake ta amsa ta tana cewa "jiya ba kin biye wa Asma'u kuka raba dare kuna hira ba gata chan tana bacci suna hutu ke kin makara zaki je a zane ki a banza" Kanta ta duƙar tana ɗan murmushi ba tare da tace komai ba "tashi maza ki ci abinci ki samu ki wuce" Sharp Sharp ta ci farin doya da kuli da aka yi wadda yaji man hannu da albasa tana ci tana haɗawa da tea bayan ta gama ta miƙe tana rataya school bag tace "Ammi na tafi" "Allah ya tsare se kin dawo" Da gudu gudu ta fice ta shiga mota tana gaida driver ɗin su ya amsa kaman kullum kan suka fice zuwa makarantar. Yau ake fidda sakamakon kuri'a da aka yi na face of the school, so bayan an yi period uku na farko ba'a sake komawa aji har a tashi, za'a tafi students hall a sanar a kuma ɗauki gwarzuwan hotuna da uniform ɗinta yadda za'a wanke su manya manya a manna a halls da gaban gate din makarantar. Bata wani ci abun kirki ba a break sbd har lokacin tana jin cikinta a cike yake daman doya ba dae riƙe ciki ba, kai tsaye daga cafteria hannunta rike da Fanta na gwangwani da ta saya bata ma bude ba aka buga seniors suka fara koran yara zuwa students hall, zama suka yiyyi, malamai biyu ne a stage din mace da namiji, bayan sun zauna suka sake Miƙewa suka miƙa musu gaisuwa, suka amsa Muryar namijin radau sbd shine yake riƙe da mic ɗin, bayan ya basu umarnin zama suka zauna. Cikin harshen turanci ya fara magana "kaman yadda kuka sani kuma muka saba, duk farkon session muna yin wannan gasa ta face of school, wannan shekarar ma bata sauya zani ba ranar Juma'a an yi zaɓe mun tara kuri'u na duka Junior and senior section kaman yadda kuka sani babu wanda makaranta ta cire a wannana gaasa ko ɗan js1 ne yaci lallai lallai shi ko ita za'a ba wa, Toh dae Alhamdulillah mun samu mun kirga kuri'u a weekend yau a yanzu kuma zaku ji sakamako" Kowa sai ya juya ya kalli Maryam dake ta kanainaya Allah kaɗai ya san kuɗin da tayi ta kwasa daga ɗakin daddynta tana zuwa tana kashewa ɗalibai don ta saye su su zaɓe ta, ta saka buri da hope ɗin ta akan wannan karon ma ita ce zata ci babu tantama har ta gama ba za'a tsige hoton ta a fuskan makarantar ba, se murmushi take. Kashe wutan hall ɗin aka yi aka bar dim Light se na stage kawai, gyaran murya malamar da ta karɓa tayi ta sake gaishe da ɗalibai kan tace "So the one with the hightest vote among the selected students of year is....!" Se ta ɗan yi shiru kan da karfi tace "Aysher Isma'il!!!!" Sowaa me karfi hall ɗin ya ɗauka a sadda spot Light ya dallare Aysher dake zaune rike da Fanta a hannunta, ita har ga Allah tsorata ma tayi hakan yasa manyan idanunta kara girma da haske se sheki suke yi, Maryam Usman da taji abun kaman sauƙar aradu tayi saurin Miƙewa tsaye tana dafe kirji nasara abu ne me matukar muhimmanci a gareta kaman yadda mahaifinta kan kwaɗaitar mata a koyaushe a komai a kuma ko ina ta kasance me kwato nasara ko ta halin yaya, bata san ta rikice ba seda kawarta mufida Umar ta janyota ta zaunar da ita "natsu mana baki ga kowa kallonki yake ba?" Murya na rawa tace "yarinyar nan tayi nasarar karya min record Mufida I'm screwed daddy ya samu labari kam na gama kaɗewa!" "Aysher Isma'il come over" da Aunty Doris ke ta maimaitawa ne yasa ta Miƙewa tana sake damke fantar hannunta, hantar cikinta se kaɗawa yake in ta tuna Maryam daga gefe, har ga Allah abunda yasa take bari suke mata abunda suka yi niyya banbancin matsayi ne, su ƴaƴan masu dashi ne ita kuma ba ƴar kowa ba. Kunna wutan hall ɗin aka yi dallllll a sadda ta hau stage ɗin, Allah ya sa ma ita ɗin me tsabta ce uniform ɗinta kal kal gashi sabo don kwata kwata wata na biyu kenan suke ciki a makarantar don suna shirin 2nd C.A test ne kuma ba ya wuce sati tsakaninshi da revision se exams da compilation, kayanta ya sha karin guga, gashinta dake gyare sbd Saloon da suka je da weekend da Aunty Asmeey se sheki yake gyaran da aka mata wannan karon raba gashin gida biyu aka yi se aka kwantar akan goshinta ya koma baya, yayi lublub tun tana kunyar zuwa makarantar haka har ta saba. Murmushin da malaman suke mata da kuma sowar ɗaliban ya bata kwarin gwiwar sakin murmushi me kyau wadda ya bayyana dimples ɗinta duk biyu da fararen hakwaran ta farare suka bayyana, nan me hoton ya matso ya fara ɗaukarta kala kala se murmushi take saki. Haka taron ya tashi kusan lokacin tashin su so wasu sun fara tafiya wasu ko na ɗan tattaunawa tsakanin juna, a hankali ta ratsa ta bayan classes bayan ta koma ta ɗauki text book ɗinta na physics da ta bari a locker ɗinta, kanta ƙasa take tafiya se ji tayi an bangajeta da karfi ta tafi duk yadda tayi kokarin balancing bata iya tsayawa ba seda ta kai ƙasa hannunta ya saki ƙara sbd faɗi da tayi a kai, glases ɗin ta ya faɗi chan wani waje, idanunta ta runtse da matukar karfi tana jin yadda zafin yake ratsa ilahirin jikinta. "Dama tun da na ɗaura idanuna a kanki Naji na tsane ki No wonder ashe da dalili ni aka turo ki ki dakushewa rayuwa! Miƙe tsaye in ga abunda kika fini dashi" Maryam Usman Ta faɗa tana Buge kafafunta dake miƙe da kafanta. Laluɓe ta fara da hannunta ɗaya a hankali ta soma cewa "taimakeni da glases ɗina bana iya gani se dashi don Allah" Dariya suka kwashe dashi su ukun Mufida Umar tace "Ashe ma makauniya aka baiwa face of school ɗin? Chabbdi yo to ai da sake" Amina bamanga tace "dole kuwa asiri ya tonu duk kyaunta in ba ido ai babu kyaun, ke kin tashi ko se mun miki laga laga?" Hawaye ne ya gangaro daga kurmin idanunta zuwa kan fuskanta "Me nayi muku don Allah? Me na tsare muku da zafi haka?" Su kam banda teasing ɗinta da suka fara babu abunda suke, ji da tayi Maryam Usman na cewa "wannan kike nema makauniya? Gashinan ƙasan kafata zan take shi in ga yadda zaki yi ki tafi gida yau" "don Allah karki karya min glasses, shine abu na karshe da na mallaka a wannan gari wadda baffana ya saya min da guminshi, ina son abuna karki karyami..." Kararass haka karan karya glass ɗin ya karade kunnenta idanunta ta runtse tana kokarin isa inda taji karan ta Buge goshinta a jikin wani karfe take shima ya fashe ya fara jini. A hankali taji an saka hannu biyu a kafaɗunta an ɗago ta, se kawai ta riƙe rigan mutumin da bata tantance waye bane sede yanayin jikin ya tabbatar mata da namiji ne tace cikin rawan lips "Please help me!" *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰 🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA   بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* FREE PAGE 13 *am very busy ayi min uzuri🙏* Zaune yake a kan three seater kafafunshi a miƙe a ƙasa, Naina na kwance tayi matashin kai da cinyarshi tana bacci cikin natsuwa, operating Phone ɗin shi yake yana wani ɗan research ne ma da wayar, se ya tsaya chak da dannar wayan, a hankali ya fita daga inda yake ya koma calender watan na 25, fita yayi kawai ya shiga App din da yake booking flights a take ya musu booking na me tashi 27 tunda sun riga sun gama duk abunda ya kawo su an yi IVF ɗin kuma komai normal. IVF shine conception da ake yi a waje a sanyawa mace a mahaifa amma ba da kwayoyin wasu ba da nata da na mijinta hakan kuma ba haramun bane, shafa fuskanta yayi tayi a hankali har ta buɗe idanunta dake cike da bacci ta kalleshi "Its time for prayer, ki soma shiri zamu wuce jibi da safe" A hankali ta miƙe zaune sossai take jin daaɗin hutun sbd kulawar da yake bata na musamman ne babu inda yake zuwa haka itama in sun fita to tare ne, to Meyasa zasu koma haka da wuri? "Ɗo you have any plans a Nigeria ne? Mu kara hutawa mana honey?" Girgiza kai yayi yace "I've already booked the flights karki manta ni ba ɗan kasuwa bane ni likita ne, me ceton al'umma bani da wani hutun hankali idan har na tuna na bar marasa lafiya da zasu iya bukatata a asibiti bana nan, maybe su zauna cikin ciwo suna jiran zuwana kinga ban kyauta ba in na cigaba da zaman, mu koma mu cigaba da renon cikin a gida" Bata da ta cewa don ta san shi akan magana ɗaya ko me zata ce yanzu ba sauya ra'ayin shi ze yi ba haka ta miƙe tayi ciki... On 27 din kuwa karfe tara suka fito a shirye, taxi ne ya ɗauke su ze kaisu airport a maimakon airport din se ta gansu a asibitin da aka mata aikin saka kwayayen hallitarsu. "Me kuma zamu yi anan Emran?" "Just wait here ina zuwa" Yana faɗa be jira cewar ta ba ya fice daga motar ya shiga ciki, bayan mintuna kaman goma se gashi ya fito ya shiga motar suka yi Airport kaman yadda be ce mata komai ba itama bata tambaya ba, karfe 9:50 suka tashi, karfe ɗaya na rana ya musu a Nijeriya, numfashi me nauyi ya sauke a sadda ya shaki iskar ƙasar tashi. Murad ne ya zo ɗaukan su, cikin farin cikin ganinsu ya shiga gaishe da yayan nashi ya amsa yana tambayar shi su Ammi, itama Naina amsawa tayi ba tare da ta damu da tambayar surukan nata ba, dama bata kiransu zuwa kuwa se idan wani abu ake shima bata wuce awa biyu wai bata son hayaniya zata tarkata ta bar gidan. Ko da suka isa gidansu ciki tayi ta barshi da Murad suna magana, basu wani jima ba ya mishi sallama ya tafi har ya nufi shiga ciki ya tsaya ya duba agogon hannunshi 1:30 fasa shiga gidan yayi Dukda gajiyar da yake ji a jikinshi, mota kawai ya ɗauka ya fice yana driving cikin natsuwa lokaci lokaci se ya duba agogo har ya isa harabar makarantar. Ɗaliban dake dan zirga zirga ya zurawa idanu kan ya sauke numfashi ya buɗe motan ya fito, en mata dayawa da kallo suka bishi yana tafiyanshi cikin ginshira da mazantaka dogon bafulani ne sossai har ya ɗan rankwafa, da sauri drivernta ya isa gareshi ya fara kwasar gaisuwa a mutunci ya amsa kan kaman ba ze ce komai ba se kuma yace "bata fito ba ko?" "Eh nima nayi mamaki don muna daga cikin na biyu zuwa uku masu fita a makarantar nan da zaran an tashi zaka ganta yanzu kuma har an kusa watsewa gabaɗaya" "ka je kawai" Ya faɗa yana nufan ciki ba tare da ya jira amsar drivern ba, wasu en Junior class ne da suke tsaye daga gefe ɗaya tace "chab yau akwai kura Aisha Isma'il ta doke Maryam Usman hmm" Ɗayar tace "Ni tausayinta nake ji yadda Maryam nan suka saka ta a gaba karfi da yaji take rayuwa ita kaɗai a makarantar nan tun da ta shigo bata taɓa sakewa ba" Wata tace "ke ai in Maryam Usman ta zama senior kowa a makarantar nan ya shiga uku, ni har tsoron zuwa SS1 nake lokacin na san suna 2" Duk cikin harshen turanci suke magana, wacce kaman dama ita suke jira da isowarta gangansu kenan tace "aiko ga ta chan ma sun tare ta bayan halls" Idanunshi ya bi inda ta nuna da hannu, tun kiran sunan Aisha Isma'il da suka yi be kara gaba ba be kara baya ba, sede ya fiddo wayanshi ya zuba mata idanu yana sauraransu, hanyar da yaga ta nuna ya bi baze ce ga yadda yake ji a lokacin ba se da ya hangi sun ture ta ta faɗi da karfi, runtse idanunshi yayi ya buɗe duk sun sauya gabaɗaya, be yi hanzari wurin nufarsu ba se ya tsaya ya shiga camera ya soma recording ɗin su. Ranshi be gama tafasa ba seda yaga ta karya glasses din nan da take ta roƙonsu akan kar su karya mata, maida wayan yayi aljihu ya nufe su daidai tana laluɓen glass ɗin ta Buge goshinta duk yadda yaso ya tare ta kan hakan ya faru be yiwu ba, jikinshi har rawa yake sbd yadda Ranshi yayi masifar ɓaci baze taɓa cewa a rayuwar shi gabaɗaya an taɓa ɓata mishi rai kaman na yau ba... "Please help me!" Ta sake maimaitawa tana Laluɓa hannunta me lafiyan ta inda take zaton inuwar mutum ne, hannun da ta faɗi a kai ya kama a hankali ya kurawa idanu daga wrist ɗinta Dukda shi ba likitan ƙashi bane amma ya fahimci babu tantama ta samu gocewar ƙashi a wurin, haƙori ya sa ya taune ƙasan lips ɗin shi ya ɗaga idanu ya kalli fuskanta se jujjuya idanun take jini na bin fuskan nata ta inda goshinta ya fashe. "Ina ruwanka da sh....." Wani irin gigitacciyar marin da ya hautsina hangin cikinsu har ita Aysher da bata gani ya sakarwa Maryam, seda ta zube a ƙasa tayi zaman yan bori numfashinta ya bar jikinta na tsawon mintuna kan ta fisgo da karfi har lokacin wasu irin taurari take gani a sama, controlling kanshi yake amma suna so se sun ga ainihin side na Fulaninshi, Ranshi yayi masifar ɓaci da har ji yake in numfashi ya fita daga kirjinshi baya dawowa ya ma kasa magana... Hannunta me lafiyan yake shirin kamawa tayi saurin ja baya jikinta na rawan tsoronshi don tunda marin ya sauka babu wadda ya iya motsi a cikin su su huɗun... "Zan tsinka miki mari kika sake matsawa..!" Ya furta cikin Muryar da ya bayyana tsantsar bacin Ranshi, se a lokacin ta fara analyzing Muryar, Dukda kamshin jini take ji amma hancinta seda ya zuƙo mata kamshin turarensa, gabanta ne ya faɗi, yaushe Abba ya dawo? Cikin rawan murya tace "A...Abbaa" Be amsa ba se hannunta da ya riƙe zasu bar wurin ba fa wai don an gama bane rikicin yanzu ya soma, jinin dake zuba mata a Goshi yake son wanke mata. "Meke faruwa anan ne?" Principal da suka taho da manyan malaman makarantar ya faɗa, dama a ka'idar makarantar malamai basa tafiya se sun tabbatar da babu dalibin da ya rage a makarantar, kuma se sun yi zagaye sun gama tabbatar da komai intact kan principal ke sallamansu. Da idanunshi da gabaɗaya suka birkice ya kallesu gabaɗayansu, se kuma ya juya da hannunshi wadda ke free ya nuna su Maryam da har yanzu zaune take a ƙasa mufida da Amina na sangame a tsaye "you should make sure among them babu wacce ta bar makarantar nan, and you all also" Yayi maganan kaman yana cikin asibitinshi ne da ya san kowa na karkashin ikonshi, ba neman izini ya basu ba umarni da gargadi ne ke tafe cikin Muryar shi, be sake cewa komai ba ya juya yana riƙe da hannunta gudun kar ta faɗi suka nufi inda ya ajiye motan shi, mazauninshi ya buɗe wato driver seat ya zaunar da ita, ya miƙa hannunshi ya ɗauko savage ya soma goge mata jinin fuskanta da har ya diddiga a uniform ɗinta, ruwa ya sa a tafin hannunshi ya wanke mata fuskan ya fiddo fari kal din hankey ya sa mata a hannunta me lafiya "share fuskan" A hankali ta share, duk gashin gaban goshinta ya sake mammanewa, hannu ya sa a aljihu ya ciro wani Brown cover na glass me azababben kyau ya buɗe, se ga rantsatsen glass kwance a ciki frame ɗin Light peach ne da fari fari yayi matukar kyau ya fiddo ya sanya mata a ido, lokaci ɗaya fuskanshi ya bayyana mata tar seda ta tsorata ganin yadda fuskar nan tashi ke a ɗaure, Dukda yadda yake ji ya ga kyaun da glass ɗin yayi mata dama kuma ya raya hakan sbd a wani shopping da suka fita da Naina ya ga frame ɗin ɗauke da lence ɗin shi sede ba medicated ba, be bari Naina ta ga sadda ya saya ba sbd ya san fitinarta, asibitin ya kai da yake ranar da ya kaita asibiti tana mp ya ga number ɗin lens din nata so kawai faɗa musu yayi ga abunda yake so a yanka a sa a frame ɗin. A yau da zasu taho ya tsaya asibitin ya karɓa ya sa a aljihu shine be cire ba se yanzu. "Why??" Ya tambaya yana kallonta da idanunshin nan da be ɓoye zafin da zuciyarshi ke ciki ba. Muryarta na rawa idanunta na sake cika da hawaye tace "Kayi haƙuri Abba, tsoro na ji... Ina tsoron kar daga zuwana in fara baka matsala da ciwon kai, sannan su ɗin sun fi ƙarfina in ka duba tazarar matsayi dake tsakanin....." "Enough pls!" Ya faɗa da ɗan tsawa, da sauri ta matsa baya hawayen da suka cika idanunta suka soma gangara, hannunshi ya sa ya murza goshinshi tare da sakin dogon tsaki me sauti. Ji yake kaman ya mammaketa itama ko ze huce kaɗan. "Me kike nufi? Da nace zan zama tamkar mahaifi a gare ki na karɓi amanar ki kina tunanin akwai wani wadda ze iya sake ɗaga miki yatsa in kyale? Karki kuskura ki sake haɗa matsayin ki da na yaran nan saboda ko ta ina basu kai ki ba bare su kamo ki har su zarta ki" Cije lip dinshi na kasa yayi. "Next time irin haka ta faru baki faɗamin ba har na gane ke zan soma sassaɓawa.. Mu je" Ya juya, da sauri ta fito ta rufe motar jikinta har rawan tsoro yake yadda yake faɗan kaman ze maretan itama. "Show me the principal's office" Yace yana kallonta, da yatsa tayi saurin nuna mishi arean yayi gaba ta bishi a baya idanunta cike da tsoron abunda ze faru. Kaman yadda ya faɗa ɗin kuwa suna nan zazzaune suna jiranshi don tambayar duniya sun yiwa su Maryam babu wacce ta iya cewa komai, tsoro ne da razani cike da idanunsu, rashin gaskiya baro baro ya bayyana a fuskokinsu. "Ta ina zamu fara? Ku zan yi ƙara ko iyayensu?" Yayi maganan daga tsaye ba tare da ya zauna ba cikin harshen turanci. "Yallaɓai da dae ka zauna mun ji Duka sides of the story sbd har yanzu mu bamu san Meke faruwa ba, su kuma basu ce komai ba" V.p ya faɗa cike da girmamawa da suke dashi ga guardians din students nasu. Zama yayi HM ya ɗauko mai ruwan sanyi a frigde ɗin Principal ɗin ya bashi, karɓa yayi ya sha sossai kan ya ajiye, a natse ya faɗa musu duk abunda ya faru ya kuma fiddo video din a matsayin shaida, gabaɗayansu sun girgiza sam basu san abu haka na faruwa a cikin makarantar ba, hakuri suka soma bashi a take yace be san shi ba, ya birkice musu da kyar ya hakura gobe a dawo in yaso za'a kira iyayensu se a haɗu gabaɗaya. Daga makarantar asibiti ya nufa da ita, Dr Safwan ya kira wanda shine yake kula da duk abunda ya shafi harkar ƙashi a asibitin ya tabbatar mai yana office kai tsaye nan suka yada zango, da sauri ya miƙe tsaye ganin shugabansu ne da kanshi a cikin office ɗin nashi yau Dukda ya kan yi ziyarar bazata sbd masu wasa da aiki amma Dukda haka ya ɗan tsorata kaɗan don ya san prof Emran bashi da sauƙi. "Sir ai da ka kira ni se in sameka ka zo nan da kan ka?" "Dr daughter na ce ta samu ɗan problem a hannu nake so ka duba mata" Yayi maganan yana zama. Daga tsayen da take ta gaishe da Dr Safwan ɗin tana kallon kwarangwal dake jejjere daban daban a kan desk ɗin nashi. Amsawa yayi yana zagayawa ya isa gareta "mu ga hannun?" Miƙa mishi tayi ya duba, Dukda yayi tunanin gaucewar ƙashin ne amma sbd gudun laifi yasa ya kaita wurin xray yayi mata cikin minti biyar ya fito ya duba, aiko dae gocewar ne ze yi gyara. "Zaki ɗan daure don ze miki zafi" Kanta ta gyaɗa duk tsoro ya cika ranta, runtse idanu tayi da karfi jin ya fara kokarin gyarawa seda kuwa tayi kuka, likitan na murmushi yace "babba dake ɗan wannan kike yiwa kuka?" "Allah ba ɗa bane Dr." Bata san ta faɗi hakan ba ma, tana kallon hannun  a lokaci ɗaya tana share hawayen fuskanta, har ya zagaye da farin bandage bayan ya shafa wani abu kaman mai, kallon Abban nata tayi idanunshi na kan wayanshi, be ɗago ba seda Dr Safwan yace "ranka ya dade an gama, ba wani abu in shaa Allah" Tsam ya miƙe yana mika mishi hannu "thank you Dr" Yana faɗan haka ya juya ya fice tabi bayanshi, office nashi ya shiga ta bishi anan ya fidda First aid yayi mata dressing na goshinta, in ya kawo Cotton me ɗauke da spirit ya ɗan manna tace "shhhh" se ya dankara mata Harara haka zata tsaya sbd tsoro har suka gama. Lokacin har an yi la'asar seda yaje yayi sallah a masallacin asibitin kan ya dawo suka tafi, yunwa take ji kaman taci babu, tana Allah allah ya tsaya ya saya musu don ta san kila yanzu kam gidanshi suka nufa ba gidan Alhj ba, kaman kuwa ya ji ya tsaya restuarant ya saya musu abinci, har sun bar wurin ma Naina ta kirashi, da Bluetooth na motan ya amsa cikin Muryar shin nan yace "ya aka yi ne?" "Ƙalau hun, ina kayi haka tunda muka dawo baka shiga ko cikin gida ba" "nace ya aka yi?" Ya sake maimaita maganan shi na fari ba tare da ya bata amsar tambayar tata ba. "Eyyaaa in zaka dawo yanzu pls baby na craving KFC kitchen ka biya ka samo min" Sun kusa isa ma a sadda tayi kiran amma be ce komai ba bayan Ok, ya juya akalar motan ɗan kallonshi Aysher tayi yunwa take ji wlh, gashi yanzu yamma ya soman nan holdup na garin in ya rikesu taya zasu koma har ta ci abinci ta cire wannan uniform da take ji ya takurata, baki ta ɗan turo tana sake kallonshi se suka haɗa idanu... *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 0545475847 Gt bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰                           🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN          (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* FREE PAGE 14 *Albishirinku💃 Toh gobe Free Page ze ƙare in shaa Allahu wacce bata saya ba kuma tana son jin yadda zata kaya a gidan Abba se ta garzayo ta saya* "Raki kam kin ƙware a kai amma baki iya kwatan kanki a faɗa ba, ɗauki abincin ki ci" Ya faɗa a fuske kaman ba shi yayi maganan ba. Murmushi ta saki tana mamakin hallayyar Abban nata, kaman me gani har hanji, juyawa tayi ta ɗauko, tint ne motar kuma ba zata iya hakuri har su koma ba ga holdups ya fara, abincinta take ci hankalin ta kwance sbd ko ta inda take ma Abban baya kallo se waya da ya kan amsa, kan su je KFC ta gama ledar na ajiye kan kafafunta, seda ya buɗe motan ya fita kan ya miƙa hannu ya ɗauki ledan ya rufe motar tana kallonshi ya cillar a bin kan yayi ciki, wani murmushin ta kuma saki. Babu wanda ya sake magana har suka iso gida, shi ya kwashi ledojin don tayi niyyar ɗauka ya hanata, da sallama ta shiga parlorn Naina tayi saurin tasowa sede ganin Aysher ne yasa ta dakata tana kallonta sama da kasa, ita har ga Allah ta ma mance da wanzuwar yarinyar "Ina yini Aunty Naina? Kun dawo lafiya?" Ta faɗa cikin girmamawa. Tsaki ta ɗan ja kan tace "lfy" shima sbd zura mata idanu da Emran yayi ne, ledojin ta karɓa don tana ji kaman ana yasa a cikinta, be zauna ba yabi bayan Aysher don shiga ɗakinshi ya watsa ruwa kan Magrib, daidai zata shiga ɗaki yace "Yau 27 in case kin ji wani ciwo makamancin na wanchan watan don't seat alone by yourself in pain, hope am clear?". Da sauri ta amsa kanta ƙasa ta kuma shige daki lokaci ɗaya, a jikin kofa ta tsaya ita har ta ma mance wlh cikin dabara ta zare uniform din ta ta shiga wanka sauri sauri sbd sallahn da bata yi ba, Sharp Sharp ta fito tayi rama Sallar da ake binta anan ta kwanta sbd ta gaji sossai, bata wani jima ba aka yi Magrib ta miƙe ta gabatar ta ɗan yi karatun alqur'ani yau ko malaminta kila ya zo ya gaji da zama ya tafi be ganta ba, bayan tayi isha ta miƙe ta ɗan saka turare kan ta zura kayan bacci, farin doguwar riga wacce tsawon ta daidai sharabarta be ida isa idon sawu ba ta kwanta... Washegari da safe seda ta shiga bayin ta ga uniform ɗin ta a bucket bazata iya wankewa ba sbd hannunta kuma bata da wani a gidan yana gidan Ammi, alwala tayi ta zo tayi Sallar asuba sbd yunwar da take ji ta haɗa tea ta sha da biscuit, bayan ta gama taje tayi wanka ta zo ta shirya cikin riga A shape na atampha da ya mugun amsar ta, bazata iya dauri ba ko gashin bata sake taje shi ba sbd hannunta ta ɗauko gyale da ya shiga da kayan ta yafa daga kanta, zama tayi tana tunanin abunda ka iya faruwa a makaranta yau sbd ta lura Abba bashi da sauƙi sam idan ranshi ya ɓaci... Jiya sossai ya tuna mata da baffanta, duk sanyinshi a kan yaranshi shi wuta ne, Dukda be san komai ba ya kare ta ya bata goyon baya, hannunta ta sa ta shafa glasses din da yayi mata kyau a ido sossai tana ɗan murmushi lallai Abba na da taste me kyau kaman ya san zata buƙata a lokacin ya taho dashi shi da be taɓa ma zuwa makarantar ba ma... Kanta ta sunkuyar tuna abunda ya faɗa na karshe kan ta shiga ɗaki, ko date ɗin watanta be mance ba, kunyar hakan ya lullube ta... Knocking da aka yi ne ya sakata saurin Miƙewa taje ta buɗe kofan, yana tsaye hannunshi ɗaya a aljihun three quater fari sol dake jikinshi ya hadata da baƙar shirt marar nauyi. "Ina kwana Abba" Tayi saurin faɗa tana ɗan duƙawa, hannunta ya kalla yace "Lafiya ya jiki?" "Da sauƙi Babu komai" Yana kallon goshinta yace "kije kitchen ki ɗauki abinci, where is ur uniform kika sa personal?" "Na jiya ya ɓaci kuma ba zan iya wankewa ba, sauran kuma suna gidan Ammi" Ta faɗa cikin sanyin muryarta. Kai ya gyaɗa ya juya ya wuce, fita tayi zuwa kitchen ɗin, doya ce fari ya dafa da faɗi fadi yayi egg sauce. "Abban nan na nan kaman hawainiya, babu kalar da baya iya zama" Tayi maganan a fili tana zuba abincin, a nan kitchen ɗin ta zauna ta ci ta koshi kan ta fito parlor tana rike da ruwan faro, se gashi shima ya fito a shirye cikin grey suit da farin ƴar ciki, ba karamin kyau yyi ba, hannunshi riƙe da briefcase ɗayan na ɗan gyara bakin nectie ɗin shi yace "mu je" Bayanshi ta bi, yanzu wannan wai har wasan kasa fa yayi da baffanta, to ya aka yi baffanta ya fishi tsufa? Dukda ba wai baffan tsoho bane sede bazaka haɗa shi da Abba ba, komai nashi daban, kai hatta murjewan skin ko Murad dake matashi me jini baze nuna mishi komai ba, da wannan tunani suka mota, ya mata wuta suka fice, be tsaya ko ina ba se harabar makarantar tasu kai tsaye suka dangana da office na principal. Shi da mahaifin Amina suka samu se wasu authorities na makarantar, a hankali ta kai idanunta kan fuskanshi ya murtuke fuskan alamar ba wasa, hannu ya miƙa musu daya bayan ɗaya kan ya zauna itama ta zauna nan ƙasan rug din kaman yadda Amina ke zaune, mahaifin Mufida da ita ne suka shigo tana sanye da uniform, kaman yadda Amina ke sanye da uniform saɓanin Aysher, daga karshe mahaifin Maryam ne suka shigo a tare, babban ɗan siyasa ne da kowa ya sani me mukami don dasu ake damawa a ƙasar, renon da yayiwa yaranshi shine be san faɗuwa ba a komai yana so su kasance masu nasara hakan ysa yaran basu damu da wa zasu taka ba wurin kaiwa ga nasarar tasu wanda dae dae yake da faɗuwa warwas. Da Adu'a aka fara kan aka baiwa Aysher damar faɗan duk abunda ya faru, turancinta be nuna ba kaman na su se ta kasa magana, kallon Abban tayi ya gyaɗa mata kai, kokarin soma magana tayi amma da ɗari-ɗari kuma ɗaɗɗaya take fidda kalaman gudun kwafsi, ta kuma yi kokari sossai wadda wasu a ciki ke ganin rigima da iyayi ne yasa take maganan a haka, Maryam V.p ya kalla yace "Maryam Usman an yi haka?" Kallon mahaifinta tayi a tsorace ta gyaɗa kai. "Mufida, Amina Meyasa kuka musgunawa Aisha? Ta muku wani abu ne?" Principal ya tmbya Suka girgiza kai Tsawa v.p academic ya daka musu "baku da baki ne ana magana kuna kallon mutane?" "Bata mana komai ba" Mahaifin Mufida ne yace "Ashe ke shashace? Yar uwar ki mace mufida ita kika ciwa zarafi? Shine da na tambaye ki kika ce baki san dalilin nema na da makaranta suke ba? Zaki yi bayani" Mahaifin Amina ma faɗa ya rufe ta dashi sossai kaman ze daketa, shi dae Abba be ce komai ba banda kallonsu da yake. Mahaifin Maryam yace "toh tunda dae abu ya riga ya faru faɗa ko maida zance bashi da amfani ai yara ne, duk shiriritarsu be kamata ana kaiwa zuci ba bare har a kai ga saka hannu jikin ƴar da ba'a san zafinta ba" Kallon shi Emran yayi se ya ɗan murmusa yace "daaɗin abun ƴa ai bata fi ƴa ba, tunda kuma babu wanda ze ci kashi a cikinsu ai zancen yara be taso ba, yanzu dae ba wannan ba ina jiran jin an kwatarwa tawa ɗiyar hakkin ta" Ya faɗa yana directing maganan to principal. "Bisa laifin da aka same su dashi a gaskiya idan ita bata hakura ba, to hukuncin Maryam shine kora daga makaranta su kuma mufida da Amina za'a basu suspension na sati uku uku" "saboda kawai faɗan yara? Akan hakan zaku kore ta? Kun ma san wanene ni kuwa da kuke zancen korin ƴa ta daga makaranta?" "Ko waye kai baka fi karfin doka tayi aiki a kanka ba, penalties din ma yayi sauƙi idan da ta nine we are going to court and they could definately pay a fine or even end up in jail depending yadda shari'a tazo" Kallon Dr Emran kawai Alhj usman ke yi, yadda yake gayamishi magana kai tsaye yayi matukar bashi mamaki, be gama mamaki ba seda ya ga principal yayi printing expulsion letter yayi signing aka bawa Maryam da ta soma kuka, mufida da Amina kuwa aka basu suspension, ita dae Aisha in ba don mugun kallon da Abban ya mata ba ta so tace ta yafe musu a barsu a makarantarsu tunda ita ta zo ta same su. Mahaifin Maryam se faɗa yake harda in ya ga dama bazata yi karatu a Nigeria ba ma, makarantar banza makarantar wofi. Emran dae murmushi ya mishi wanda kai tsaye yake nufin wannan matsalar ka ce... Murɗawar da mararta yayi ne yasa tayi saurin duƙar da kai tana runtse ido, to fa wannan abu haka ze ta mata? A take gumi ya soma tsatsafo mata a Goshi, ko hakurin da malaman da kuma iyayen mufida da Amina suka yi ta basu ita ba ji take ba, ta de san mahaifin Maryam ya jima da ficewa kuma itama ta bi bayanshi. Idanunshi ya sakar mata na mintuna kan Tsam ya miƙe "Allah ya kiyaye gaba, Aysher?" Ɗagowa tayi idanunta har sun chanza kala "mu je" ya faɗa chan ƙasan makoshi. Sallama yayiwa malaman suna ta kara bashi hakuri shi kam hankalin shi na kanta, a dudduke ta isa motan ta haɗa kai da gwiwa. "Sorry" Ya faɗa cikin kulawa yana tada motar be tsaya ko ina ba se asibiti, Dr Hafsa ya kira tun kan su isa, a office ɗin shi tayi mata allura, kaman wanchan karon shi ya fita ya nema mata pad, da ya dawo tayi bacci zama suka yi da Dr Hafsa yana tambayarta yadda za'a yi ta samu sauƙi sbd be kamata kowani wata ta sha wannan wahalar ba. Bayani ta mishi mata kala kala ne, kila in tayi aure ta daena kila kuma in ta haihu, amma saukinta a daena wannan allura tayi ta amfani da lipton me zafi da kayan kamshi da kuma lemon sannan ta koyi amfani da ruwan zafi a mararta daga ta soma jin alama, ya tabbatar mata in ta farka ze tura ta se tayi mata duk bayanin da ya kamata tare da mata godiya, Miƙewa tayi ta fice tana mamakin shi ita bata san haka boss ɗin nasu yake ba sam, ji shi so simple and caring. Da ta farka yau ma a bayi ta gyara Kanta Allah ma ya sa bata ɓaci ba tukuna, abinci ta gani kan table ta ɗauka ta ci, ta sake kwanciya idanunta na zagaye office ɗin, zuwa yanzu har ta san komai na kan office ɗin sbd yawan zuwa, knocking da aka yi ya sakata Miƙewa taje ta buɗe, Dr Hafsa ce. Cikin girmamawa ta gaisheta don ko ba'a faɗa ba Dr Hafsa zata iya haifar ta, dubata tayi ta bata shawarwari masu yawa kan ta fice Aisha na mata godiya, se after asr ya dawo da alama duk ya gaji, sannu ta mishi se kuma ta miƙe Tsam ganin ya zauna a cikin kujerun taje wurin frigde ta ɗauko mai ruwa da cup daga kan frigde din. A hankali ta zuba ruwan kan ta mika mai cup din, ta san dae haka Nene ke yiwa baffa idan ya dawo a gajiye da ruwan sanyi take soma tarbarshi wanda basa rabo dashi a randar ƙasar su, karɓa yayi ya shanye ta kara mishi ya sake shanyewa yana lumshe idanu jin sanyin ruwan na ratsa shi. "Thanks" ya ce bayan ya miƙa mata kofin, ta mayar. Miƙewa yayi ya shiga ya sauya kaya ya fito suka fice a tare, gidan Alhj suka yi yana parking Asma'u na parking. Da gudu ta zo ta rungume shi "oyoyo Big bro" "ya school?" Ya faɗa yana rabata da jikinshi. "Fin.... Aisha me ya sameki? A ina kika ji ciwo kuma yaushe?" Ganin Aisha ya katse mata maganan da take shirin faɗa, da sauri taje ta kamata suka yi ciki tana kwala Kiran Ammi, girgiza kai yayi kan ya nufi sashen Hajiya.. *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰 🖤Gureenjoh🖤 RUBUTU A KAN RUWA   بسم لله الرحمن الرحيم FATIMA MUHAMMAD GURIN (Gureenjo) ADABI WRITERS ASSOCIATION Marubuciyar: *Zuhraa* *Hamrah* *Igiyar Rayuwa* *Noor Iman* *Ruwan Sama..* *Lelewal* *GAMON JINI paid* *Kowa Ya ga zabuwa..* *Diddigar ƙaya... Paid* And now.. *RUBUTU A KAN RUWA* LAST FREE PAGE Ba karamin zagi su Maryam suka sha wurin Asma'u ba se dariya Aisha ke yi, Ammi kam banda Allah ya tsare gaba bata sake cewa komai ba, Wata kyakyawar mace da tayi kama da Abbanta sossai ta gani tana saukowa daga stairs hannunta riƙe da wata karamar fine girl, fuskanta ɗauke da murmushi take cewa "Auta ke da waye kuma tun daga sama nake jiyo Muryar ki?". Dama ya ya nan ta fara faɗa mata abunda ya faru kaman tana wurin, seda ta gama Aysher ta gaisheta ta amsa cikin kulawa tace "Amma Aysher be kamata kina fuskantar irin wannan abu ki ƙi magana ba, duk haka ta faru ki faɗa a ɗau mataki da wuri kin ji?" Kai ta gyaɗa, Asma'u ta dora mata da cewa wannan din itace Aunty Salma ƴaƴan ta biyar, Aunty salma na da kirki sossai sede Aisha ta lura bata da surutu kaman Aunty Asmeey tana nan so quite kaman Abba ne, a tare suka cigaba da hirarrakinsu bayan Aysher ta karɓi yarinyar me suna Hibba da hannu ɗaya yarinyar kuwa ta sake suna ta ɗan wasa, har Magrib suka tashi suka yi sallah suka dawo parlorn tana mamakin rashin shigowan Abba, se after isha suna cin abinci tsakar parlorn ya shigo da sallama. Duk suka amsa, a ƙasa ya zauna chan gefe kusa da kafafun Ammi yana gaisheta, seda ta ɗan muskuta kan ta amsa da kalma ɗaya, Aunty salma ce ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta yara, Asma'u ta gaishe shi ta ɗaura da "A zuba maka abinci Big bro?" Girgiza kai kawai yayi, ya jima zaune parlorn sede yayi operating waya ko ya amsa call be cewa ba'a ce mishi se lokaci lokaci salma ke ɗan mishi magana wanda yake amsawa ɗai-ɗai, Ammi kuwa ganin ya ƙi tashi yasa ta miƙe abinta tana cewa Aisha "kin tabbatar kin haɗa komai a akwatin ki ko? Kar ki mance wani abin" "Eh Ammi na haɗa" "to ki tabbatar kan ku tafi kin shigo akwai sakon da zan baki" Tana kai nan ta dubi salma "ke kuma kwana zaki yi ne kam?" Shagwaɓe fuska ta ɗan yi uwa me daaɗi "Da se na fi kowa farin ciki wlh Ammi, Ammi kora ta ma kike? Zan tafi to amma babansu ne ze zo ya ɗauke ni" Harara Ammi ta zabga mata tana cewa "Ai kin san mu bama son namu iyayen muka barsu muka dawo gidan babanku da zama" Asma'u da Aisha se dariya suke yayinda ita salma ta kara narke fuska, ita Kam Ammi tayi sama abinta. A hankali ya maida kanshi kan wayanshi ya ɗan Tsurawa wayan idanu ba tare da yana yin komai ba, in da sabo ya ci ace ya saba sede ya rasa me yasa yake jin shi out cast idan Ammi na mishi haka, babu abunda ya fi tsana a al'ada irin wannan a rayuwar shi kuma ba ze lamunci ayiwa ɗan shi ba capital No. Miƙewa yayi kawai fuskanshi sam ba walwala se ma sake tamketa da yayi. "Se da safe Yaya" Salma ta faɗa don ta san ba dawowa ze yi ba, da sauri Aysher ta miƙe ta haura seda ta shiga tayiwa Ammi sallama ta bata snacks da ta sa aka mata sbd zaman gidan Emran se da shiri da wasu designers Abaya guda biyu, sossai tayi mata godiya kan ta fito ta shiga ɗakinta ta janyo trolley dinta, Asma'u ta miƙe ta taya ta suka saukar zuwa mota, da gudu taje tayiwa Hajiya sallama sbd kar ta ajiye shi ta dawo, yana zaune ciki Asma'u ce ta sa a akwatin a boot, juyawa tayi wurin Hibba tana ce mata "byebye baby" Ba se yarinya ta soma miƙa mata hannu tana kuka ba, duk dariya suka yi Aunty salma na cewa "wannan kam se ki sami lokaci Asma'u ta kawo min ke ki mana yini tunda jinin ku ya gama haɗuwa da Hibba uwar Ƴan kyuiyan duk duniya" Tana buɗe motan ta cewa Asma'u "Eyyaaa Aunty Asmy ko ban je ba watarana ki karɓota ki kawomin ita?" Harara Asma'u ta zabga mata tana cewa a nawa? Duk dariya suka yi ta shiga motar tana ɗaga musu hannu, daidaita zamanta tayi ganin sun hau titi sossai, gabaɗaya se motar be yi mata daaɗi ba Dukda ta san Abban ba ma'abocin sakin fuska bane sede da kallo ɗaya a yanzu zaka san akwai abunda ya taɓa Ranshi har suka isa gida babu wanda ya tanka se sautin karatu dake tashi kasa ƙasa.. A tsakiyar parlor suka samu Naina tana kai kawo ganinsu tare yasa ta ja ta tsaya, tana sanye da doguwar riga baƙa shara shara da alama tana hutu ne sbd abun cikinta. "Emran ina kuka fito?" Tayi tambayar tana tsatsaresu da idanu, ita fa ba wawuya bace kuma auren soyayya suka yi da mijinta ba haɗi ba, kuma ta san kishi taya za'ayi wannan ƴar kauyen take zama gaban motar da ta saba zama cikin har tana haɗa kafada da mijinta? "What sort of question is this? Ashe kece mijin..." "Dole zaka ce haka, wlh dole zaka ce hakan saboda kun san baku kulla gaskiya ba, sau nawa kuna fita ku yini tare? Dabba ka maida ni ko ban san me nake yi ba? Ko jiya tare kuka yini wallahi yau se kun faɗa min me kuke kullawa.." "Abunda jakar kwakwalwanki ya faɗa miki shi muke yi, Wallahi Naina ki kiyaye ni nayi iya lallaɓakin da zan yi and i will not take it lightly kika ce zaki tsallake iyakarki" A tsorace Aisha ke kallon su ganin tana kokarin haddasa fitina a tsakanin ma'auratan hawaye ne ke bin fuskanta sam bata gane abunda Nainar take nufi dasu ba, wace kuma irin macece zata tsaya sa'insa da mijinta murya a sama? "Ni kake kira jaka imran? Ni Naina kake cewa jaka akan wannan banza kazamar ballazar? Wallahi zan yi ajalin yarinyar nan yau se in ga karshen karuwanci da mij..." Marin da ya ɗauke ta dashi a bazata ne ya ɗauke maganar dib sbd gigita da tayi bata san ta kai ƙasa ba, bata ji a kab rayuwarta an taɓa kai hannu jikinta se a yau... Gabaɗaya bata gani daidai haka bata ji daidai Ɗagowa tayi cikin matsanancin rawar murya ta ce "N...ni ka mara? A kan w..wannan" Ta karashe tana nuna Aisha da gabaɗaya hannayenta ke kan Bakinta idanunta gabaɗaya sun firfito cike da tsoro da firgita, daga Abban har Naina babu wanda fuskanshi ke da daaɗin kallo a cikinsu "zan iya miki fiye da haka tun da kin ce baki san abunda zaki ke furtawa a kaina ba Naina, sanin kanki ne ni ba mazinaci ba ne ko a da ban yi zina ba bare yanzu, idan kwakwalwarki ta sake kimtsa miki abu a gaba ki tauna kan ki furta min don wlh ba zan ɗauki wannan raini da rashin kunyar ba" Tsam ta miƙe tana jin mararta na Murɗawa da karfi kan Aisha tayi "Wallahi wallahi na rantse da Allah se nayi ajalin ƴar iskar yarinyar nan..jaka sakarya wacce uwarta ta wofintar da rayuwarta saboda dukiya, dabbar da ko a me sharar takalmi na ba zan ɗauke ta ba" Haukacewa tayi ta soma fashe fashe a parlorn duk abunda ta samu se ta wurga wa Aisha, da sauri ya janyo hannunta ya tura ta ɗakinta a rikice ta zube a wurin ta fashe da matsanancin kuka, Me ke shirin faruwa? Saboda maraici ne duk hakan? Ashe ta kai abun wulakantawa haka a idanun Naina? Ita kam seda tayi son ranta da tsine tsine babu abunda bata faɗa ba yana tsaye ya harde hannu yana kallonta, duk haukar ta tsoron shi take hakan yasa bata yi kanshi ba, ta fashe da tsananin kuka daga karshe tare da zarrar keyn motarta ta fice be ce mata ci kanki ba, se jajayen idanunsa da ya runtse da karfi... Tana tuƙi tana kuka har ta isa gidansu a parlor ta samu iyayenta kawai ta zube jikin Dad dinta tana kuka me gunji an yi mata abunda ba'a taɓa mata ba a rayuwa, ita Emran ya mara akan wanchan karuwar yarinyar. A rikice suka rufu suna tambayarta me ya sameta? Me aka mata har Nameer da Shigowar shi kenan yaga parking nata da yadda tayi cikin gida da gudu, mararta dake ciwo ta dafe ta ɗago tana kallon mahaifinta, a razane ya ɗaura tafin hannunshi samar fuskanta "wa ya mare ki Naina?" Tambayar se ya sake hasala ta ta sake fashewa da kuka irin wanda bata taba yi ba. "Wayyo cikina Daddy, mommy cikina zan mutu" A take suka sake rikicewa basu ankara ba se jini da suka ga yana malala daga jikinta, kan kace me jikin ya rikice se ta koma yaraf ta sume, da gudu Nameer yayi mota da ita iyayensu suka rufa musu baya se asibiti... Danƙari! Aisha kina ruwa tsundum... *To fa anan free Page ya kare, mallaki naki ki ji ya zata kaya a gidan Abba* *Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi* Zaki iya biya ta wannan akawun lamba 3118518476 First bank Fatima Muhammad Gurin Se ki tura shedar biya ta wannan layi 09039206763 In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰                           🖤Gureenjoh🖤