💘SHIN SO DAYA NE?💝 *MALLAKAR:HAFSAT AL-MUSTAPHA*                       *WATPADD:HAFNANCY* *Gaisuwar ban girma gareku my wadpaddians & Hafnan's novella group,thanks for showing me true love,I also love you all so very much... 💗💗💗💕*         *KASHI NA BIYU:RIKICIN KARSHE*          🌼BABI NA DAYA🌼        Page 1-3 Ban kai ga isa kofar fita ba,sae kawai naji kaina ya harba,atake naji kamar ana buga min ganga akan,dakatawa nayi tare da rik'e kan da hannaye bibbiyu.      "Muido lafiyarki kuwa? " haka naji Anty Hajaar ta fada.Ni kuwa ko tankata banyi ba sabida wani irin jiri da naji yana nemar kwasheni ya kifar akasa. Gani nayi tsayuwar na nemar gagarata don haka sena koma da baya na zauna da k'arfi agefen gado.     "Amaryar Nakowa lafiya kike kuwa?" Hakan naji k'awayena sun fad'a tare da tasowa suka zagayeni,wasu ta saman gado ayayin da wasu kuma ke tsaye agabana suna meh jiran nayi musu bayanin abinda ke damuna.     Ash ce ta shigo dakin tana fadin"Oya Fateenah,'yan mata duk ku taso aje ayi ho....... " Ganin da tayi an zagayeni,sae sannu ake min ya saka ta cillar da mayafinta tare da rugowa da gudu,ture wasu friends dinmu tayi wanda hakan ya bata damar samun kusanci dani.    "Fateenah wats wrong? Lafiya naga kin dafe kai da hannuwa bibbiyu?" Ash kuwa tsoro ne ya cika xuciyarta fal. Azuciyarta tace"Oh! Yah Allah kar dai ace Fadima ta samu labarin wanda aka daura mata aure dashi shiyasa ta shiga cikin wannan halin?"     Ita Ash tana waje sanda su angwaye suka shigo,sae taci karo da Mahmood wanda kuma aka nuna mata cewar ai shine angon Fadimar.Atake anan taji cikinta ya duri ruwa,ji tayi tana matuqar buqatar toilet awannan lokacin don yadda taji kamar tana shirin sakin gudawa ajikinta.Ai kuwa da azama tayi toilet din. Koda ta fito,sake komawa tayi,alokacin suka ci k'aro da Suhaima wacce itama kiranta akai da ta fito suyi hotuna da angwaye,itama tana ganinsa wai amatsayin angon yar'uwartata,murza idanuwanta tayi da kyau don ta kara tabbatarwa da lallai ko shi dinne.      Ai kuwa shi dinne dai ba wai kamanni ba,da azama ta koma ciki don labartawa yayartata shine suka ci karo da Ash din. Ash tace"Ke kuwa kanwa meya faru ne naga kina rafka wannan uban saurin har bakya kallon gabanki kike tafiya?"     Arud'e tace"Hmmm! Anty Ash kin san wa kuwa nagani amatsayin angon Yaya Fadima? Wallahi wannan wan saurayinta Mubarak dinnan na Kano ne.... Kin tunashi ai? Wannan Engr.Mahmood ne yake da suna ko....?" Ash tace"Wallahi nima na ganshi,ganinsa ya saka nayi toilet don wata gudawa naji ta taho min alokaci guda don fargaba..... "     "Amma taya hakan ta faru? Dama yana sonta ne? Kuma taya akai har ya samu ya shawo kan mahaifiyarsa ya aureta bayan tun ganin farko da tayi mana bata qaunarmu musamman ita yaya Fadimar?mafi daurewar kan wannan al'amari ina shi Mubarak din yake ne da duk hakan ta faru??" Suhaima ce take fadin wannna maganar ahankali cike da kuma tashin hankali.Ita kuwa Ash cewa tayi"Wannan tambayoyin duk abakin shi uban gayyar zamu samu amsoshinmu..... Kuma.... "    "Wae Suhaima kuskus din meh kukeyi ne tsaye anan baza kizo ayi hotunar ba kun shanye mutane can tsaye arana suna jira? " Anty Hajaar ce ta katse musu hirarsu alokacin da take kokarin xuwa ta kira Fadimar itama ta fito ayi da ita. Da sauri Ash ta janyo hannun Suhaima suka rab'a ta gefen Anty Hajaar suka fice waje.Suna fita suka hada idanuwa da Engr.Mahmood,sakar musu pretty smile yayi.     Su kuwa kallon junansu sukayi,Ash ta rad'awa Suhaima magana akunne.Murmushi tayi sannan tayi wajensu don daukar hotuna.ce mata tayi kada ta kuskura ta nuna masa surprise face ko kuma tayi gangancin tambayarsa taya akai ya samu auran Fadima? Ita kuwa Ash komawa tayi dakin Fadima,Allah-Allah kawai take tayi Fadimar tayi creating wani scene wa Anty Hajaar kamar yadda tayi kwanakin baya,don idan tayi hakan ai babu yadda za'ayi ta fito tayi hotunan.Tasan tabbas Fadima nayin ido hudu da Mahmood amatsayin mijinta,xata iya zauncewa kuma ita bazata so ace Fatin ta nunawa duniya cewar bata san mijin da aka aura mata ba.Shiyasa take ta addu'ar Allah yasa kafin ta isa dakin ta tarar kawai Fadimar ta riga tayi creating wani scene.Ai kuwa dadi ne ya kusan kasheta ganin yanayin da Fadimar ta shiga duk da cewar ba hakan taso ba.Ta fison koda Fadimar xatayi wani tashin hankalin toh ta bari sae bayan an kaita gidan Mahmood din amma ba wai tayi anan idan ta ganshi ba.     (Back to the scene). Dakyar na budi baki nace"Ash wani azababben ciwon kai ne naji ya saukar min yanzun nan..... "      "Subhanallah.... " ta fada tare da kai hannu tana taba wuyana. Zaro idanuwa muka ga tayi tana fadin"Fateenah wallahi jikinki har ya dau zafi,zazzabi ke shirin rufeki..... "     Anty Hajaar ce tayi saurin taran numfashinta wacce take tsaye tun dazu take kallon ikon Allah,cewa tayi"Iskancin banza da wofi.... don kawai nazo kiranki ayi hotuna dake shine xaki kirkiro wata k'aryar banza can....? " Ash ta kada baki tace"Haba Anty wannan wacce irin magana ce kike yi haka? Kema zo ki taba jikin nata kafin ki karyata zancen.... "     "Yi min shiru anan! mara kunyar banza da wofi ai daga ke har ita jirgi daya ce ta kwasoku ta rashin kirki da mutumci..... " Karkata akalar zancen nata tayi xuwa gareni"Ke kuwa Fadima ni abin naki ya dena bani mamaki sae tsoro donni de ban taba ganin amarya irinki ba,ranar da aka kawo gaisuwarki some mana kikai,yau kuma daga cewa ki fito ayi hotuna kin kirkiro xancen rashin lafiya,ko dae auran ne kawai bakyaso ayi miki ita gaba daya? "     "Anty Hajaar don Allah ni ki tafi kawai kada ki k'ara mata wani ciwon akan nada..... " acewar Ash wacce ta soma fusata da xancen Anty Hajaar. "Eh! tatacciyar mara kunya ai dama wucewa xanyi yanzun nan kuwa,kuma ke Fadima bari mah kiji na gaya miki,gwara mah ki bar wannan k'aryar rashin lafiyar don ko kina shure-shuren mutuwa ne anjima zamu kaiki dakin mijinki,kuma ai ke kikace kina sonsa don haka ya zamar miki dole ki zauna dashi don an riga an dauraku kuma anjima kadan xamuyi miki rakiya xuwa gidansa..... " (lol kai Anty Hajaar din nan 'yar gari ce).     Fuuu! ta juya ta fice kamar kububuwa.Sae ayanzu hawayen da suka makale acikin ramin idanuwana suka samu damar gangarowa.Sam Anty Hajaar bata dauko halin Umma ba,Umma sam bata da wani hayaniya kamar Anty Hajaar,komanta da sanyi take yinsa,maganarta mah cike da salo da karairaye murya,sab'anin Anty Hajaar maganarta da fada take yinsa,shiyasa sam bata cika shiri da mutane.    Kawayena sae sannu suke ta min.Haka aka gama hotuna banje anyi dani ba.wasa-wasa sae da zazzabin nan ya kwantar dani,har allurai biyu sae da madam Iyabo ta min (da yake ita din nurse ce). Jama'a kuwa sae cewa suke wai amarya na zazzabin bankwana da iyayenta ne.       Ash ta gargadi Suhaima da kada ta kuskura ta gayawa Fadima cewar Engr.Mahmood ai shine mijinta,ta bari idan aka kaita ta sani kuma tasan dole zata haqura ta xauna. Ni kuwa sae ji nake ana 'amaryar Mahmood Nakowa' azuciyata nace"Nakowa shine sunan mijin nawa? " (Dayake su Mahmood basa amfani da sunan Nakowa shiyasa bata sansu da sunan ba.... Kai Engr. akwai brain,shi ya bada wannan sunan awajen daurin aure don kada Fadima tayi saurin d'agowa don ta siyasa ya tambayi Mubarak ya gaya masa cewar be taba fada mata family name dinsu ba...)    Shi kuwa Mahmood picture daya ya dauka sannan suka fice da tawagarsa don be ga amfanin tsayawa daukar hotuna ba bayan babu sahibar tasa aciki.Shi kansa was juz like Ash,yayi murna ba kadan ba da addu'arsa ta karbu,Fadima bata fito ba balle ayi tashin hankali,dama can Anty Hajaar ce da iyayinta tace ya tsaya ta kira Fadimar suyi hotuna.     *** Wuraren karfe hudu da rabi aka bugo musu waya cewar ga 'yan daukar amarya nan tafe na ita Fadimar.    "Fadima lallab'a ki shirya tunda jikin naki da dan sauki,ki hanzarta don an bugo wai 'yan daukar amarya na kan hanya....... "     Da sauri na tari numfashin mama Jamila wacce k'anwace ga Abbanmu"Mama ina za'a kaini? " Mama tace"Can kano za'a kaiki don nan danginsa suke,idan yaso daga baya shi mijin naki da kansa zai maido dake nan Zaria gidan da zaki zauna...... "     Wani kuka ne ya kufce min jin cewar kano mah za'a kaini garinsu Mubeen dina,nace"Gaskia ni dai mama babu kanon da zaku kaini,ni dai kawai awuce dani gidana kawai..... " Bud'e baki tayi tace"Ikon Allah! yau ni Jamila gani ga mara kunyar amarya,Muido ina kika tab'a jin anyi haka?kul! kada mah ki bari wani yaji don dariya zasu miki suce kuma baki da kunya,an san kina mararin zuwa dakin mijinki amma ki bari asoma mik'aki ga danginsa kafin ki koma dakinki kamar yadda akeyi ah al'adance.... "    Wani haushi ne ya rufeni ganin ita sam Mama bata fahimci abinda nake nufi ba,ita azatonta kawai zumud'in tafiya gidan miji nake.     "Ki tabbata kafin na dawo kin shirya kanki,maza kawayenta ku tashi ku taimaka mata ta shirya kanta.... "    Had'iye wani muyau meh daci nayi,kana nace"Mama banda lafiya fa,haka kuke son ku kaini?" Afusace tace"Kya warke acan,idan kuma mutuwar ta tashi xuwa kya cika adakin mijinki kinga kuwa asirinki arufe tunda kina da aure akanki,sannan ga wata daraja,rahama da kuma haske da gawarki zata samu,kuma mutane zasu fi ganinki da mutumci da kima ah idanuwansu,uwa-uba mijinki meh masifar sonki nasan ze daga miki tafin kafarsa ki samu aljannarki...... "      "Mama pls ki bari banso,ya isa haka jeki xan shirya.... " na fada tare da rushewa da wata sabuwar kuka.Mama cikin jindadi ta wuce abinta don ganin maganganun nata sunyi tasiri ak'wanyar Fadimar.Kawayena kuwa sae dariya suke ta min.Ash ta taimaka ta shiryani cikin wani tsadaddan light brown swiss lace wanda akayi masa kwalliya da flowers navy blue.    Fati mamza wacce dawowarta kenan daga gun wani biki anan Zariar,itace ta cigaba da shiryani,ta min daurin dankwali meh shegen kyau,sannan ta yafa min tsadadden mayafina navy blue meh kwalliya ajikinsa na kyalkyali da flowers.Mayafin daga saman kai ta yafa min ita.takalmana flat ce brown colour kalar kayan.     Ta feffesheni da turare,aka fito dani xuwa bangaren Abba inda anan ne za'a mana fada da nasiha.Gida ya rud'e da rangad'e rangad'en guda.Koda na shiga falon na tarar har Suhaima ta rigani isa,zaune take akasa kusa da kafafuwan Umma,ta kifa kai asaman cinyar Ummar tana rera kuka ahankali ayayin da Umma ke dan bubbuga bayanta alamun rarrashi.Can gefensu Abba ne zaune sae karkada kafafuwa yake yana meh fesar da iskan bakinsa.     Ganin shigowar Fadima da Kuma kukan da itama take rerawa ya saka Umma saurin mik'ewa don bazata juri tsayawa yin bankwana da 'ya'yan nata ba. Hanyar fita ta nufa alokacin da taga Fadimar ta sami gu ta zauna akasa akusa da Abba.      "Haba! Kareemah dawo ki sallami 'ya'yanki mana,ki dawo kiyi musu fatar alheri acikin sabuwar rayuwar da zasu shiga..... " Sabon kuka dukanmu muka rushe dashi har Umman,dakyar ta dawo ta nemi gu ta zauna.Abba ya shiga lallashinmu da Kuma ban baki,dakyar muka haqura mukayi shiru don sauraren nasiharsa agaremu.    Abba yayi gyaran murya sannan ya soma jawabinsa"Alhamdulillah! Alhamdulillah! godiya ta tabbata ga mahallicin sammai da kassai,mahaliccin dabbobi,aljan,mutum da duka komai meh rai ko mara rai.Na godewa Allah da ayau ya bani damar sauke nauyin daya rataya bisa wuyana amatsayina na mahaifinku na ganin na aurar daku ga nagartattun mazaje na gari,Fadima hakika nasan ko kadan ban kyauta miki ba dana hana miki auren zab'inki,amma ina son ki san cewar ko kadan banyi kuskure ba,don idan baki manta ba,ah addinance wajibi ne iyaye su zabarwa 'ya'yayensu abokanan rayuwa na gari,don haka karki ka laifina don na aurar dake ga wanda ba zabinki ba,Wallahi Fadima ina meh tabbatar miki da cewar watarana keda kanki zaki zo kice Abba nagode da zab'inka,ashe zab'inka alheri ne agareni.........."    Haka de Abba yayi ta mana fada da nasiha kan mu riki aurenmu da kyau Kuma mu baiwa auren muhimmanci sosae,mu bi mazajenmu sau da kafa sannan kuma mu k'yautatawa  danginsa.Haka mah Umma itama tayi mana fad'a sosae.Ashe wai wasu acikin danginmu wayenda suka sanni tare da Leedar sunyi ta mamakin yadda akai ya koma mijin Suhaima,Abba de ce musu yayi haka Allah ya tsara tun fil'azal cewar Suhaimar itace matarsa amma ko kadan be labarta masu komai na game da shashancinmu ba.     Su goggonnina,mamannina da wasu kawunnina duk se da suka shigo suka mana fada da nasiha meh ratsa xuciya.Ni da Suhaima babu abinda muke illa kuka.Daga k'arshe akayi waje damu don har 'yan daukar amarya hadda na Suhaima sun iso.Sae da akayi da gaske kafin arabamu da su Abba da kannena. Abba yace baya son tarkacen mutane da nufin kai amarya,sam an bar yayin nan.Mama Jamila,Anty Hajaar,Mama Sadiya cousin dinsu babanmu,sae kuma kawayena biyu,Ash da zuwairah kadai akace zasu bini.    Ita kuwa Suhaima mutane har Kusan goma ne wai zasu bita tunda nan cikin Zariar za'a kaita kuma ayau din zasu komo,kuma duka kawayenta suma zasu bita.Nayi kuka sosae,sae nake ganin kamar an nuna min rashin gata ne.    Ni da Kawayena muka shiga mota daya,ayayin da dayar motar kuma su mamanni ne aciki. Sae gud'a ake tayi har motocinmu suka bar kofar gidan.....             A/N Hey Fadima sa'ad Mainasara welcome to Nakowa's family!!!    Ina kuke tunanin za'a kai Fadima? Family house ko kuwa gidan Baba Mu'azzam za'a sauketa? Ku biyo.        Sorry guys! chapters na kashi biyu zasu dunga zuwar muku a little bit scanty don novel din ya Kusan zuwa karshe & I want the chapters too be a little bit much..... Yeeeepeeee shout out to Hafnan! Her first novel is about rounding up!!! 💗💗     ©QUEEN CE©         *💘SHIN SO DAYA NE? 💝*    *MALLAKAR:HAFSAT AL-MUSTAPHA*        *WATPADD:HAFNANCY💞*    *KASHI NA BIYU:RIKICIN KARSHE*           🌼BABI NA BIYU🌼      *💧💧💧KAI  AMARE💧💧💧*           💧💧                               💧💧               💧                                     💧     *page 3-6*        Har muka isa kanon ban mah san mun iso ba sabida tun shigata motar,cigaba nayi da sana'ar kukana,Ash kuwa sae aikin rarrashina take don ni da ita kawai muke xaune agidan baya,ita kuwa Zuwairah gidan gaba ta xauna wacce jefi-jefi suke d'an taba hira da meh tuki wanda na lura kamar yana cikin abokan ango.Shi din mah yayi rarrashin duniyar nan amma naki nayi shiru,can yace arabu dani kila so nake shi angon nawa yazo ya rarrashi abarsa da kansa,abin ya baiwa su Ash dariya,ni kuwa haushi maganar tasa taban kamar na tashi na kifa masa lafiyayyun mari.    Mubarak ne ya fad'o min arai,yanzu shikenan mun rabu kenan? Yanzu baza'a taba k'irana da matar mubeen ba kamar yadda nake ta burin hakan sae matar Mahmood Nakowa?abin mamaki mah wai dangin mijin nawa ah kanon suke,kada watarana fa mu had'e dashi.... Wani b'angaren xuciyata kuma yace"xancen banza keda mah ah Zaria zaki zauna? Sannan meye naki na wani damuwa akan mutumin da baya qaunarki,mutumin da kuma sam be damu da rayuwarki ba?       "Toh! amaryar Nakowa mun iso,sae ki had'iye kukan naki ya isa hakanan kinga gidan surukai xamu shiga kada suga kina koke-koke su aza ko surukar tasu ba jaruma bace...... " Ash ce ta katse min gajeriyar tunanina alokacin data bud'e min kofa da k'yau wai na fito,sae asannan na ankara da cewar har mun iso ban sani ba.     Sannu ahankali na sako kafafuwana waje tare da dire su akasa,wani daddad'ar ni'imtaccen iskar yammacin nan ne ya soma min barka da xuwa.fitowar tawa tayi daidai da wayar da wannan meh tukin keyi wanda ayanzu nasan sunansa don naji Zuwairah ta ambaci sunan wai *'KHALEED'*.      Cewa yayi"Kai dan iskan ango kana ina? gashi fah mun iso amma anki bamu amaryar..... " Saurarawa naji yayi,can yace"Na taba maka irin wannan wasar ne? Ka yadda dani anki bamu ita wai sae kaje da kanka.... " Ya sake saurarawa,can ya d'an d'ara yace"Kai wasa nake maka mallam karka min hauka,ga amaryarka nan mun kawo maka ita,tasha kuka kuma har yanxu tana kan yi ne sae kazo ka lallashi abarka........ "     "Ayyyirihiiiiiiii,lale marhaba da zuwan amarya.... " rangad'e rangad'en gudar dangin mijina ne ya hana min jin k'arshen maganar Khaleed da mijina.Ni kuwa jin sun nufoni ya saka na k'ara jan mayafina gaba don kada suga fuskata.         Wata 'yar matashiyar budurwace naga ta rungumeni tana fadin"Oyoyo!amaryarmu sannu da xuwa...... " Mama Jamila ce ta rad'a min magana akunne,cewa tayi"Ki shiga da kafar damarki tare da bismillah,haka kuma xakiyi idan aka maidaki can gidanki.... "     Daga mata kai nayi alamar naji jawabin nata,daga haka naji wasu mata su wurin uku suma sun rungumeni kamar zasu kada ni akasa suna min sannu da xuwa har muka shige gidan. Wani daki aka saukemu aciki wanda muka ji wani daddad'ar kamshin turaren wuta ya mana maraba da xuwa,gaskia ba laifi suma kanawa akwai son kamshi.Maganar gaskia ba k'aramin karramamu akai ba,nima sae naji na d'an saki jikina amma har xuwa wannan lokacin ban yaye mayafin kaina ba,ina nan lullub'e aciki kamar wata munafuka,lokaci xuwa lokaci nake dago kai na d'an saci kallon mutane.     Cikin k'ank'anin lokaci muka ga an cika mana gaba da kayan ciye-ciye da shaye-shaye.Mama Sadiya ne suka dan taba amma babu yadda basuyi dani ba amma naki ci.Ce musu nayi ak'oshe nake.Ak'arshe dai ruwa kawai na d'an sha.    Mama Jamila ce tace"Yarinya idan zaki mah saki jiki toh tun wuri ki saki don anan zamu barki,gobe idan Allah ya kaimu komawa gida abinmu xamuyi..." Juyawa tayi ga Mama Sadiya tace"Sadiya hanzarta ki gama cin abincin ki min rakiya xuwa gidan wata k'awata dake nan jambulo,bazamu jima ba..... "    "Toh Addah... "acewar Mama Sadiya don Mama Jamila na gaba da ita. Ni kuwa wani sabbin hawaye naji sun ziraro min saman k'unci,tayaya xan soma rayuwa agidan wasu bayan na sab'a da namu?taya mah xan soma had'a shimfid'a daya da wani k'aton gardi amatsayin mijina?     Yaye min mayafi naji anyi ana fad'in"Ai kya bari muga fuskartaki muga ko kin fini kyau koh? " Ji nayi an fashe da dariya,ni kuwa gabana ne naji ya yanke ya fad'i,dakyar na iya d'ago kai ina duban wacce ta yaye min mayafina,ido hudu nayi da wata tsohuwa wacce kana ganinta kasan ta dad'e ana cin sallar idi da ita.Sae dai ba'a wani gane tsufanta don jikinta meh k'yau ne.     Tace"Masha Allah!.. Ashe dai megidan nawa balarabiya ya zab'o mana shiyasa yake ta rawar kafa da dokin auranta..... " Aka sake fashewa da dariya akaro na biyu,ni kuwa d'an murmushin leb'en baki ne kawai ya sub'uce min,atake anan na gane cewar wannan tsohuwar kakarsu ce.     Tace"Amarya share hawayenki,don ni dake xamuyi zaman lafiya idan da hakan kika zo,idan kuwa da akasinta kika zo,toh nima nan uwargida ashirye nake...... " wasu 'yan mata ne naji sunce"sae kakus! Kakaaa rigima.... " aka fashe da dariya.    Haka dai tayi ta mana barkwanci da wasannin wanda atake anan naji kawai tsohuwar ta shiga raina.Su Mama Jamila kuwa suna gama ciye-ciyensu suka sa kai suka fice xuwa unguwar da suka ce xasu,muka rage daga ni,Ash,Zuwairah sae kuma Anty Hajaar wacce ga dukkan alamu jininta ya hadu dana Kaka rigima,don sae hira suke ta xubawa.      Ba'a wani jima ba muka ji an soma k'iraye-kirayen sallar magrib,daya bayan daya muke shiga bandaki muna dauro alwala.     *** Itama Suhaima anata b'angaren an musu tarban mutunci,sosae aka karramasu.Reedah itace wacce ta soma rungumota,ta rad'a mata magana akunne"Oyoyo sahibata,barka da xuwa,yau Allah ya cika muku burinku ta mallakar junanku,Suhaima dear welcome home as matar yayanah...... "     Ita kuwa Suhaimar murmushi kawai tayi abinta tana meh jin wani irin farin ciki mara misaltuwa na ratsa xuciyarta.     Leedar da Engr. bazan iya kamanta muku irin tsananin farin cikin da suka tsinci kansu aciki ba na ganin ayau sun mallaki 'the women of their dreams'.Bama kamar Mahmood wanda jinsa yake kamar Zaynab d'insa ce ta dawo.     *** "Anty Fadima inji Yaya Mahmood wai na kawo miki wa'ennan kayan ki saka wai xuwa qarfe takwas za'a taho ah daukeku xuwa reception...... "     Hafeezah 'yar baba Mu'azzam ne ke yiwa Fadima wannan maganar wacce take kusan sa'ar su Suhaima. Kokarin magana nake sae naji Ash ta rigani,cewa tayi"K'anwata zubasu saman gado yanzu xata shirya kinji? "     "Toh.. " kawai tace sannan ta zubasu saman gadon dakin ta fice. Ina gama ganin ficewarta na dubi inda Ash ke xaune nace"Sannu sarkin felek'e da iyayi,ina fatar da kika amshi wannan kayan ke zaki sakasu kuma ki bisu donni yadda kika ganni nan babu inda zani.... "    Zuwairah ce tayi saurin taran numfashina"Haba babe ya kike neman kwafsa mana ne?" "Ke dai Zuzu banni da ita da meyi take yi,yanzun nan kuwa xamu hau sama mu fad'o don bazan tab'a bata goyon baya wajen wulaqanta sirikai ba..... "          "Toya isheki hakanan tunda de ba surukan naki bane,don haka babu ruwanki idan mah zaginsu nayi.... " acewata. Ita kuwa Ash cewa tayi"Wallahi hadaki xanyi da Anty Hajaar ai kin san halinta sarai.... " tasa kai ta fice daga d'akin da nufin xuwa gun Anty Hajaar din wacce take dakin Kaka rigima suna shan fira.     Dama ashe taku ce tai wa Fadimar,babu kai kararta da xatayi gun Anty Hajaar,taku ce kawai tayi,nemo Hafeezah tayi tace mata"Don Allah k'anwata lambar yayan naki xaki ban,wayar amarya ta mutu balle akirashi da ita,ni kuma xancen gaskia bani da lambarsa.... "     Ta fad'a tare da mik'a mata wayar,murmushi kawai Hafeezah tayi tare da k'arban wayar ta latsa mata harufofin layinsa don tasanshi aka,lambarsa babu wuyar rik'ewa.       "Nagode my chuchu... " ta fad'a ah sa'ilin da Hafeezah ta mik'o mata wayar. Babu b'ata lokaci ta sanya k'iransa,sae daya d'an jaah aji kafin ya d'aga.     "Hello!! pls who's on the line? " ya fad'a cike da k'asaitarsa. Saukar da ajiyar xuciya Ash tayi,kana tace"It's the bride's best lady Aysha...... "     Tabbas ya ganeta! Sahibar matarsa ce,adakile yace"How may I help you? " Tace"Gaskia fa kun mana laifi babba,meyasa ba'a fad'a mana cewar akwai reception agidan ango ba sae akurarren lokaci? "     Shi kansa yasan tabbas ko kadan basu k'yauta ba,kuma shi yama so afasa batun wata reception,amma kuma abokansa ne suka nace wai sae anyi don baza suyi asarar kudadensu ah iska ba sabida tun asali sune suka shirya masa wannan reception din.Sam be shirya fuskantar tashin hankali daga Fadima ba,amma kuma yaya ya iya? yasan kila Ash ta tsegunta mata zancensa don haka y xama dole yaje suyi ta ta k'are kowa ya huta,kuma yasan komin haukarta babu abinda xata iya yi don an riga an daurasu kuma igiyoyin auren ahannunsa take.Da wannan tunanin ya sami salama acikin xuciyarsa. Ahankali yace"Pls we are very sorry tabbas munyi laifi babba amma agafarcemu..... "     Da sauri ta tari numfashinsa"Ni abar wannan xancen mah,yanxu gashi nayi nayi da ita ta tashi ta shirya amma fir tace bazata ko'ina ba,don haka sae kazo ka lallashi abarka ko kuma afasa..... "          Da sauri yace"Am on my way.... " Ya fadi hakan da rawar murya tare da yanke call din.Dama acikin mota suke,suna kan hanyar xuwa daukarsu ne,abayansu wasu extra five cars ne ke biye dasu wanda za'a kwashi mutanen da keda ra'ayin xuwa agidan. "Khaleed drive the car fast..... " acewarsa,ai kuwa kamar jira Khaleed yake abashi umarni,nan da nan kuwa sae gashi sun iso. Sai dirin motoci kakeji ah layin.         Ita kuwa Ash tana jin dirin motocin,da sauri tayi ciki,inda tabar Fadima hakanan kuma ta dawo ta sameta,wato lazimi take saman sallaya.   "Oya maza ki gyara ga ango nan shigowa,ke kuma Zuzu fito mu basu wuri.... " Ta fadi hakan tare da janyo hannun Zuwairah suka bar dakin,Zuzu sae dariya take tana cewa"Kai Ash gaskia baki da dama,wato yanxu sae da kika kirashi shi yazo ya saka mata kayan kenan ko? "   Ash tace"Ai rabu da ita,dani take zancen,idan tasan wata ai bata san wata ba,dole gyad'a tayi mai,idan taki kuwa tasha matsa......... " Ni kuwa binsu nayi da ido da baki bud'e kamar wata shashasha har suka fice,kafin na tsaya wani dogon tunani naji an doko sallama wanda nake tunanin babu tantama ango nawa ne.     Tuni gabana ya hau dukan uku-uku,rud'ewa nayi nama rasa abinda xanyi da kuma inda xan saka kaina. Mik'ewa tsaye nayi tare da gyara saman hijab dina wacce ta Anty Hajaar ce na ara. Sae dana baiwa kofa baya sannan na k'arba masa sallamarsa,kai tsaye naji ya shigo yana furta"Amincin Allah da albarkarsa su tabbata agareki amaryar Mahmood..... "     Kunnuwana ne suka dauki kuwwar maganarsa,ji nake kamar na tab'a jin wannan muryar awani wuri,dakyar na danne wannan tunanin nawa tare da furta"Gareka kaima wanda ya yakice farin cikina har yaci nasara aka aura masa ni..... " Ina gama fad'ar hakan naji wasu hawaye masu dumi sun ziraro min saman kunci har ina ji suna diga ak'asa.Shi kuwa sautin murmushinsa kawai naji,kana yace"Subhanallah! ah ina kika tab'a jin wani masoyi meh matuk'ar qaunar masoyiyarsa ya rabata da farin cikinta? A'ah sae de mah dada tsundumata cikinsa da zeyi..... " K'ok'arin magana nake,sae kawai naji yayi saurin taran numfashina"Gimbiya pls safe the discussion for later,yanxu zuwa nayi na rokeki da pls ki rufamin asiri nasan sam bamu k'yauta muku da bamu sanar daku xancen reception da wuri ba sae akurarren lokaci,don Allah amaryata amana afuwa,ki taimaka ki rufa wa angon naki asiri ki halarci reception din nan,pls kada kisa naji k'unya agun abokaina don su suka shirya abin......... "    Afusace nace"Nasan tabbas an fad'a maka cewar bana jindadi,kuma yanxu ka nuna min cewar baka damu da rashin lafiyar matarka ba,ta k'unyar abokanka kake right? toh bari kaji,agaskia babu inda zani naje na kwaso sanyi abanza na janyowa kaina farawa daga square one ta rashin lafiyar ba......... "     "Fadima Zahra banfa sanki da Kafiya da taurin kai ba,haka kuma ban sanki da tsiwa da rashin kunya ba,infact ko bah kece da laifi ba,kina da saurin bada haquri,then why all diz all of a sudden changes? " Gabana ne ya tsananta faduwar gaba,ah iya tsawon rayuwata nasan mutum d'aya ne ke gaya min wannan kalaman da bawan Allahn nan ya fad'a kuma shine *ENGR.MAHMOOD*. Yana yawan cewa"Kai sister inlaw ni dai halayyarki sun mugun min,sam baki da hayaniya,baki da girman kai,komanki da sanyi kike yinsa,abinda yafi birgeni dake shine saurin bada haquri koda kuwa ba kece keda laifi ba.... "      For the very first time na samu kaina da son yin ido hudu da *Mijin Kaddarata* (another name for the novel). Sannu ahankali na juyo da kaina xuwa gareshi.Fes! na sauke rinannun idanuwana akan fuskarsa.Hasken lanta din dakin ne ya bani damar k'arewa handsome face dinsa kallo.      Shock!startled!astonished!Amazed!.... and any other type of surprise mood u could think of,duk na shigesu alokaci daya ah sa'ilin da idanuwana da nashi suka gauraye cikin na juna..... Kun san wah nake gani agabana??.......... 📝   A/N Hahaha! amaryar Nakowa maida wuk'ar,duk mun riga da mun sani kece kurum aka bari cikin duhu,yanxu tambayar itace "Taya zamar auranku ze kasance? " mun fa k'osa mu gani.        *Hey! Hafnan's freaking fans! wai atunaninku family house za'a sauketa?? Haba its too early to start separating fight mana,atleast biko let dem enjoy their first night tukun Koya kukace? Lol       Pls ur comments & votes are getting down,I need like 100votes before I move on,lol juz kidding amma nasan inda zan kamaku ai.....!!     *IT'S YOUR LADY HAFNAN*💞 *💘SHIN SO DAYA NE?💝*        *INTELLIGENT WRITER'S           ASSOCIATION*        *{Onward together}*      *{ we give the reader's of ours the        best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔           *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*        *WATPADD:HAFNANCY💞*           *IG:Hafsy___mustee*                     ✨✨✨     _*Jinjina gareku my slay queens,my surporters,I started diz novel kamar wasa,na fara first babi sae kuma na dakata naki cigabawa,wa'ennan qawayen nawa sune suka bani gwarin gwiwan cigabawa wanda har muka Kai inda muke ayau,gashi ayau na kammala littafin *SHIN SO DAYA NE?*tare da taimakon abokan arziki masu son cigabana,don haka gabaki daya wannan littafin na sadaukar dashi agareku my lovely squad*_    _**Ayusher Shafi'i💄*_ _**Zatifah,marubuciyar 'Neelam'*_   _**Nafisatouh unique👑*_   _**Sorphiyyerh Sorphie👜*_   _**Maryam 'yar fillo💋*_   _**Fatymerh Zahra🎉*_ _**Queen deeyana📱*_       _*Thank you all for your support,I love you all so very much irin sosan nan,am assuring you all dat ana mugun tare har abada juz lyk magnet da qarfe✌👌*_                       💥💥 *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*            *🌼BABIN K'ARSHE🌼*       *🔚🔚🔚🔚🔚👏*     Bayan Mahmood ya kammala waya da Momi,cike da tashin hankali ya dubi Fadima wacce tayi matashi da kanta asaman cinyarsa,itama hankalinta tashe ganin yanayin mijinta ya sauya ah sa'ilin da yake waya. "Dear nah what happened? Wani ne ya mutu?" na fada cike da fargabar amsar da ze biyo baya. Murmushin leb'en baki kawai yayi yace"Momi ce ta k'irani take fada min cewar Mubarak ya dawo don haka mu hanzarta xuwa kano yanxun nan kuwa,so Zahmood tashi muje ayita ta kare da zazzafin nama........" Ya fadi hakan tare da mikar da kanta,ya tashi tsaye.Ni kuwa duk wani na'ura meh aiki ajikina ya tsaya cak!,alokaci daya naji duk wani kuzari dake jikina ya kau,idan ka kasa kunnuwa kuma kana iya jiyo yadda xuciyata ke bugawa da sauri da sauri non-stop.      Har ya kusa shiga dakinsa sae jikinsa ya bashi cewar bata biye dashi,da sauri ya waigo,tana nan de inda ya barta,sae binsa take da kallo,kwayar idanuwan nan nata dauke suke da tsantsar tashin hankali.Jikinsa ne yayi sanyi qalau,Sam baya son ganinsu cikin tashin hankali haka,amma kuma toya ya iya?dolene dama su fuskanceta koba jima koba dade,kuma insha Allahu daga yau za'ayi ta ta k'are don ba tsoron Mubarak din yake ba.     Sannu ahankali ya taka xuwa gareta,ya tsugunna tare da dafe gwiwowinta don zaune take saman kujera.        "Zahmood dear nah...... " ya fadi hakan cikin wani irin siga ta salon soyayya. Ni kuwa kamar dama jira nake ya fadi hakan,sae kawai na rusa masa kuka meh daga hankali.beyi yunkurin hanata ba,seda tayi meh isarta don kanta tayi shiru ta koma 'yar shesshek'a.Can ya janyota ta fado jikinsa,ya lalubo lips dinta ya shiga tsotsarsa don kawai ya dan rage mata damuwar data shiga ciki.    Nima din biye masa nayi cuz I can't hold it back,bazan iya jurewa ba.saida yayi meh isarsa sannan ya cikani,ya riko hannuna tare da mik'ewa yana fadin"Oya let's go..... " Kokarin magana nake sae naga yayi saurin sanya 'yar yatsarsa saman lips dina,yace"Shhhhhh! Zahmood don't say anything again,Idan har kina sona then ki taho mu tafi muje ayita ta kare yau...... "    Runtse idanuwa nayi ba tare da furta komai ba,banyi aune ba kawai naji ya kinkimeni yayi daki dani,shida kansa ya saka min kaya,don ada daga ni sae wata yar shimi da bone shot ce,shi kuwa threequarter da kuma singlet.ya dan shirya mana wasu kayan acikin wata 'yar karamar akwati wai zamuyi weekend gaba daya ne acan,dayake yau jumma'a ce.Nide jinsa kawai nake da kuma binsa da kallo don gabaki daya hankalina baya jikina.Cikin kankanin lokaci muka kama hanya bayan na k'ira Umma nace mata mun tafi weekend kano,fatar alheri kawai ta mana.      *** _*✨KANO✨*_     Mubeen da Usee,sae kuma Hanan ne kadai xaune afalo,sunyi shiru kamar wasu kurame,Hanan ce kurum ke 'yar shesshekarta.Daya da daya matan ke shigowa ahargitse cikin kuma tashin hankali,kowacce Idan ta shigo sama-sama take gayar dashi sannan ta nufi dakin Momi.Ganin kowacce na shigowa fuska sam babu annuri akai yasa hankalin Mubeen tashiwa.'Yar wasar da suke da yayarsa Meema akodayaushe yau babu ita,hasalima sama-sama ta gaishesa kana ta wuce dakin uwarta da sauri-sauri.    Akalla yanxu an shafe kusan mintuna talatin kenan da zamarsa anan wurin yana jiran momi,amma shiru-shiru taki fitowa suyi maganar datace zasuyi,sae ganin yan'uwansa mata dake ta shigowa yake wanda hakan ya bashi tabbacin lallai an buga an sanar musu da dawowarsa ne shine suka taso suka zo,kuma yanayinsu ya tabbatar masa da cewar lallai babu lafiya,dakwai abinda ke kasa wanda suke tsoron gaya masa Kai tsaye.ya yanke shawarar k'ara mata wasu mintuna talatin din,wanda ze kama 1hr kenan,Idan har kuwa 1hr din ya cika kuma bata fito ba,toh kuwa shi zeje ya sameta ta gaya masa abinda ke faruwa.     shesshek'ar da Hanan keyi sosae ya soma isarsa,afusace ya dubi inda take yace"Wai zaki yiwa mutane shiru ne ko kuwa? Kin de san arayuwata na tsani kananan koke-koken banza ba tare da dalili bako?tukunna mah de meh aka miki kike kuka? Huh gaya man? " At once ta tsaida shesshek'ar,ta shiga jifarsa da kallon mamakin wannan sauyawarsa daga dawowa wai kuma duk akan Fadima wacce bema san cewar wansa ya aureta ba,yanxu muddin ya sani kuwa toh abin ze ninka wannan ninkin ba ninkin kuwa,wani dan marayan kuka ne taji yana nemar kubce mata don ita arayuwarta ta tsani ganin Mijinta cikin tashin hankali.    Murmushin leb'en baki kurum ya sakar mata ganin tana shirin sakin wani kukan,shi kansa yasan he's harsh on her wanda har ya lura mamakin hakan take,he juz have to act so don Momi ta tsorata da yanayinsa har ta bari ya auri Zahransa.     "Jiddanah pls stop crying lyk little Jasmin owkay?" Ya fadi hakan cikin muryar lallashi. Gyad'a masa kai tayi da sauri-sauri tamk'ar wata 'yar yarinya,alokaci daya ta hadiye kukan.      Kallonsa ya dauke daga gareta ya maida xuwa ga Usee wanda ya rafka uban tagumi da dukkan hannayensa,yayi nisa sosae cikin tunani don ko abinda Mubeen ya gayawa Hanan beji ba. "Lil fada min,anyi mutuwa ne shine kuka kasa fada min sae inda-inda kuke tayi?huh?"    Wannan tambayar ta Mubeen shine ya dawo da Usee cikin hayyacinsa,gabansa ne yaji ya bada rasss!,axuciyarsa yace"Ina ganin dama mutuwar ce akayi da zefi sauki akan wannan tashin hankalin da ake shirin fuskanta..... " Kafin yakai ga bashi amsa sae ganinsu Baba Mu'azzam sukayi da matarsa da kuma goggo Ladidi wacce ya biya ya daukota sun fado dakin hankali tashe,hijab din goggo ladidi mah bata sakashi dede ba.Abin kamar hadin baki sae gasu Momi dasu Meema suma sun fito don sunga shigowarsu cikin gidan ta window.    Yanayinsu ya saka hankalin Mubeen kara tashiwa akan nada,sama-sama ya gaishesu suka amsa masa,kana kowa ya samu wuri ya zauna.     "Toh kode wani ya mutun ne? Ina brother Mahmood yake?tunda abin yaga na taron dangi ne,toh Ina shi yake?" Tambayar da xuciyarsa tayi masa kenan,kafin ya sake yin wani tunani yaji kawai Baba ya katse masa hanxari.     "Mubarak ina son ka bani aron hankalinka da kuma tunaninka anan,ina son ka natsu ka saurari jawabina...... " Ji yayi gabansa ya yanke ya fadi,amma se ya daure yace"Na ara maka su duka Abba.... "     Yace"Madallah nagode,wato Mubarak tabbas kowanni dan'adam akwai irin jarabawar da Allah ubangiji madaukakin sarki yake yi masa domin gwada cikar imaninsa,ba kuma dan Allahn shi be sani bane yayi masa wannan jarabawar,a'ah Allah yasan komai,se de shi Allah yana yin jarabawar ne domin mu da bamu san abinda ze faru nan gaba ba.Haka kuma Allah madaukakin sarki yana yin jarabawar ne domin k'arama bawa da kuma kaishi wani matsayin da ayyukansa na ibada baze kaishi ba har abada,amma ta wannan jarabawar,idan bawa ya cinyesa,sae akaishi matsayin da ayyukansa be isa ya kaishi ba,wannan jarabawar fa dolece,don Allah madaukakin sarki yana cewa acikin alqur'aninsa meh girma acikin suratul Ankabut,yace_*"tsammaninsu su mutane suce sunyi imani abarsu haka kawai ba tare da an jarabcesu ba? (Allah yace:Lallai na jarabci wa'enda suke gabanninsu domin asan masu imani na gaskia,acikin imaninsu sukayi imani da gaskia,tsakaninsu da mahaliccinsu duk tsanani basu juya baya).Kuma lallai Allah yasan wa'enda sukayi k'arya,abaki cewa sukayi sunyi imani da Allah,amma axukatansu k'aryace suke yi,idan sunga musifa sae su juya baya suna masu kuka,Alhalin manzon Allah(SAW) yace mana yana daga cikin imani yarda da kaddara meh k'yau ko mara k'yau don duk daga Allah suke)......"*_    Dakatawa yayi yana duban Mubarak wanda ya nutsu sosae yana sauraren jawabinsa,kuma ya lura duk jikinsa asanyaye yake,kila zece wai meh tsohon nan yake shirin gaya min ne da har yake min wannan tunatarwar? Goggo Ladidi itace ta soma nata jawabin"wato sae ka yarda da kaddara meh k'yau ko mara k'yau,ka yarda da cewar duk abinda ya sameka daga Allah ne,asannan ne zaka zamo mumini meh imani,toh ni Kam nace,idan har komai ya zama daga Allah ne,meh k'yau ko mara k'yau,meh dadi da mara dadi,kuka da dariya,samu da kuma rashi,nasara da kuma akasinta,toh kuwa komai abin godewa ne,abin karba ne sannan kuma abin alfahari ne,sae mu amsheshi muyi farin ciki,muyi godiya ga Allah,sae mu amsa k'iran Allah(SWT) da manzonsa(SAW),muyi haquri mu kuma sallama mu mika duka lamuranmu ga Allah madaukakin sarki,Yah Allah ka bamu ikon cinye duk wani jarabawar da zaka mana,da wanda kake mana da kuma wanda kayi mana,ka temakemu karmu fadi jarabawar don alfarman gwaninka annabi Muhammad........ "    Gabaki daya kowa ya amsa da"Sallallahu alaihi wa sallam.... "     ahankali Mubeen ya budi baki ya soma magana"Abba wai duk meya kawo wannan tunatarwar ne?ku fada min ko wani nawa ne ya rasu shine kuke tunanin idan har kuka gaya min toh ina iya tada hankalina shine kukayi tunanin kwara ku soma da min tunatarwa?Yah Mahmood ne ko kuwa Zahrata? "    Babu wanda beji gabansa ya fadi ba jin cewar direct ya ambaci sunayen culprits din nasa,shiru akayi na tsawon wani lokaci,shi kuwa ya baza kunnuwa yana bin kowa da kallo daya bayan daya,yana meh jiran yaji wani ya budi baki ya bashi amsar tambayarsa.    Runtse idanuwansa yayi yana meh tunano abinda Hanan ta gaya masa dazu,maganar tata ce take masa kuwwa akunne,ji yake kamar yanxu take masa maganar.     _*"Haba mijin hauwa'u yanxu har xuwa wannan lokacin baka cire Zahra aranka ba?aganina ya kamata ka shafeta acikin rayuwarka because I think Zahra ta maka nisa ba kadan ba........"*_    Karde hakan na nufin Zahra ta jima da mutuwa shine ta gaya masa hakan?kode dalilin daya saka dan'uwan nasa yake ta raina masa hankali kenan har kuma ya dena daga k'iransa kawai don kada atada masa hankali ko ya shiga cikin wani hali?     ** Seda muka soma biyawa gidanmu muka ajje akwatinmu sannan muka kamo hanya xuwa family house.seda kuma Mahmood yayi da gaske kafin ya samu na shiga gidan,ganin ransa ya soma bacewa ne ya saka kawai nayi shahada muka shige.     Gabana ne ya hau dukan chalugude asa'ilin da muka kusanto entrance door.Cak! na tsaya,naki gaba haka kuma naki baya,Mahmood ne ya juyo yana dubana,yace"Zahmood yadai?"     "Dear nah am not ready to face Mubeen,idan na shiga ince masa meh?ni matar wansa ce? Wallahi I can't........ " Axuciye yace"Shikenan Fadima tunda ban isa na saki abu kiyi ba,ba damuwa kina iya yin duk abinda ranki ya keso...... " ya shige ciki abinsa ya barta nan tsaye.           Da hanxari na take masa baya,adaidai lokacin kuma Mubeen ya bude idanuwansa yana fadin"No! No! No!!! Fadima Zahra tana nan araye bata mutu ba....... " Kowa ya bishi da kallon mamaki jin furucin daya fito daga bakinsa,jin shigowar mutane ne ya maida hankulansu ga kofar shigowa.    Babu wanda beji gabansa ya tsananta faduwa ba ah sa'ilin da kallonsa ya sauka kan halittun da suka shigo.Zumbur! Mubeen ya mik'e ya nufesu,cike da farin ciki yake fadin"I knew it,wallahi na fada zahrata bazata tab'a tafiya ta barni yanxu ba........ "      Rungumar Mahmood yayi yana murna,yace"Brother an k'ira an fada maka na dawo shine kayi min wannan big surprise din ta hanyar kawo min my Zahra ko?tank u very much amma meyasa ka dena daga call dina Idan na k'ira? " Shi kuwa Mahmood wani uban d'aci ne yaji aransa ah sa'ilin da mubeen ya k'ira Zahmood dinsa da 'Zahransa',ai yanxu Fadima tasa ce shi d'aya.    "Brother say something mana,wai meyasa Kowa ya maidani mahaukaci ne?tun dazu naketa tambaya amma Kowa ya maidani shashasha,wai meke faruwa ne da har ake b'oye min?" Cikashi yayi ya nufi Fadima wacce take tsaye bayan Mahmood dukkan ilahirin jikinsa rawa yake tamkar wacce ake kad'awa gangi.     "Zahrata nasan ke kadaice zaki iya fada min abinda ke faruwa,sabida irin son da kike min shi ze saka bazaki iya b'oye min komai ba,so now tell min wat's happening? "         Baba shine ya taso ya kamo hannun Mubeen ya mai dashi mazauninsa yace"Mubarak zauna ayi magana ta fahimta... " Ya dubi inda su Mahmood ke tsaye yace"Mahmooda kuma kuzo ku sami wuri ku zauna...... " suka bi umarninsa.     Baba ne yake gayawa Mubarak cewar ai gashi-gashi,be bari ya k'arashe ya mik'e zumbur!,idanuwansa sun canza launi xuwa pure hot red,ya dubi inda Mahmood ke zaune yace"Mahmood kaci amanata,ashe dama komawarka Zaria sabida ka samu kusanci da budurwata ne?ashe duk wani taimakon da kake ta ikrarin zaka min kanka kake tayiwa?Haba shiyasa Jiddan Mubarak ta canza min,kwata-kwata Idan mukayi waya bana gane kanta,koda na dawo mah Kowa beyi murnar dawowata ba sae mah tashin hankalin dana lura kowa ya shiga,atunaninku ni Mubarak ban yadda da kaddara bane ko menene da har za'a tara min mutane ana kuma min nasihu? Toh ku sani na yadda da ita,na yadda cewar abinda Allah ya rubuta cewar ba naka bane tofa komin tsiya bazaka tab'a samunsa ba,ni tun farko mah da'ace ka nuna min cewar kana son Zahra,toh wallahi ina iya bar maka ita sabida nima ina son naga kayi aure Yah Mahmood.......... " shiru yayi jin wani irin azababban ciwon kan dake nemar masa sallama.    Duk jikin kowa awurin seda yayi la'asar,masu hawaye nayi,masu shesshek'a suma ba'a barsu abaya ba,sosae Mahmood yayi dana sanin biyewa son xuciya,ahankali ya soma magana"Brother haqiqa ban k'yauta ba dana biyewa son xuciya,cin amana yana daga cikin halayen munafurci,cin amana yana daga cikin abubuwan da suke tauye imanin mutum,cin amana yana daga cikin abubuwan da suke qasqantar da darajar mutum awajen Allah,cin amana yana sanya mutum yayi baqin jini acikin al'umma,haka kuma zalika cin amana yana zama sanadiyyar dulmiyar da mutum acikin wutar jahannama.......... "    Mubarak baze iya jure ganin dan'uwansa na suffanta kansa da wa'ennan zantukan ba,da sauri ya isa inda Mahmood din yake ya rungumesa"No brother pls stop it,ka dena suffanta kanka da wa'ennan zantukan naka da babu dadin ji,wallahi ni baka ci amanata ba,dama can haka Allah ya rubuta cewar kai din Mijin Fadima ne bani ba,kawai ya tsara cewar ta sanadiyyata ce zaku had'e,come on brother wallahi ni na yadda da kaddara,dadina ayanxu kayi aure kamar yadda muka jima munata mafarkin faruwar hakan,and am assuring u dat Fadima Zahra will make a good home for you....... "    Kamar hadin baki,kowa ya dau tafi da hamdala ga ubangiji,basu taba tunanin cewar komai zaizo musu da sauqi haka ba.(ni kaina Hafnan da fans dina mun dauka za'a yi yakin duniya ta uku ne kafin adaidaita,sae gashi Mubeen ya tabbatar mana da cewar shi din cikakken Mumini ne meh yadda da kaddara meh k'yau ko mara k'yau).    Baba ya sake nasiha meh ratsa xuciya da gangar jiki,haka goggo Ladidi,da Mami da kuma Momi kowa seda ya tofa albarkacin bakinsa,daga bisani aka nemi gafarar juna da k'yau,sannan kowa ya watse.Washeqari seda muka sake cimma Mubarak agidansa,dayake aranar ya tattara iyalinsa suka koma gidansu,muka sake nemar gafararsa da k'yau,yace mana"Haba Yaya wannan wani irin abu ne?Nace maka wallahi baka min laifin komai ba,haka Allah ya tsara abinsa tun fil'azal,yanxu Idan nayi wani tashin hankali hakan na nufin ni din ban cika mumini meh kuma imani ba,tunda har na kasa yadda da kaddara,ina son ka sanya aranka cewar Fadima dama can ba tawa bace,Kila babu alheri ne acikin aurena da ita,da'ace na nace saina aureta,Kila bayan auran musifu kala-kala su kunno kai,don haka ni nama yi farin ciki da ban auretan ba,kaine alherinta shiyasa Allah ya hadaku,fatana ayanzu Allah ya yaye min sonta axuciya..... "    Haka muka baro gidan jikinmu asanyaye.Kwananmu biyu muka dawo Zaria.Bayan kwana biyu kuma Mahmood ya kaini ganin gida,toh agaban Mahmood dinne na fayyace musu abinda yayi ta faruwa.     "Ikon! Allah kenan,dama haka Allah ya tsara abinsa,Allah ya dada baku zaman lfy.... " shine abinda Abba da Umma suka fada. Su Ash dasu Leedar kowa mah yayi matuqar mamaki da farin cikin ganin komai yazo da sauqi.Suma suka qara mana addu'ar samun zaman lfy. *** _*BAYAN WATANNI BIYU*_ Hanan ta sauka lafiya tare da taimakon Mubarak,da kanta ta haihu wannan k'aron lfy qalau kuwa sabida ba k'aramin kulawace ta samu awannan cikin ba,sannan kuma addu'a baya faduwa Allah ya qarbi koke-kokensu ya sanya ta sauka lfy.Qatoton baby meh kosasshiyar lafiya ta haifo,yaro kamar Mubeen yayi kaki ya tofar.Ana gobe suna,Mahmood ya kaini kano,ah family house na kwana,washeqari da sassafe muka dunguma xuwa gidan suna,su Umma sun min kara ba kadan ba,ita,Ash,su Lubna da kuma Suhaima wanda Leedar ne ya bata izini suka zo.Ranar suna yaro yaci sunan Mahaifinsu Mubeen wato *MUSTAPHA*,se aka sakaya ana k'iranshi da *IRFAN*.,bayan kwana biyar da yin suna,Hanan ta shirya ta tafi maiduguri wajen iyayenta don kam ta dade bata je ba.se bayan 40days ta komo Kano.        *** _*AFTER NINE MONTHS*_      Allah ya saukeni lafiya,yayi min baiwar da ba kowacce 'ya mace yake yiwa ba,wato haihuwar ya'ya uku atake.Mahmood ya rasa inda zesa kansa don murna,tuni ya saka aka yada agidajen radio.Har kukan murna seda yayi,shi meh son 'ya'ya kamar meh sai gashi tashin farko Allah ya azurtashi da 'yan uku,maza biyu da mace daya,mazan duka suna matukar kama ne dashi,hasken fatata ce kawai suka dauka,macen ne kawai take kama dani kamar an tsaga kara an k'arya.Mahmood yayi barin naira da kuma rarraba kyaututtuka ah haihuwar 'yan uku,ni kuwa k'yautar wata sabuwar dalleliyar motace ya min,yanxu motocina sun zama biyu kenan,ga tasa daya ban,sannan kuma da nawa da nake hawa alokacin ina budurwa wanda Abba ne ya saka aka kawo min ita alokacin mun dawo daga kano sabo-sabon amarcina.    Ranar suna,yara suka ci sunan,baba mu'azzam ana k'iransa da Hassan,dayan kuma sunan Abbana aka saka masa wato Sa'ad,ana k'iransa da Hussain,macen kuma Zaynab aka saka mata,ana kiranta da Afra.Bayan suna na kira Ash na mika mata tsohuwar motata kyauta ko don zirga-zirgar school.Har kuka seda tayi min don murna,tana ta godiya da shima triplets albarqa.       **** Rayuwa ta mik'a,Mahmood na musamman ya samo min 'yan aikin da zasu dunga kula da triplets,har makaranta suke bina se su tsaya awaje harna fito lectures,sannan na karbesu na basu mama.watanninsu hudu-hudu da haihuwa amma idan ka gansu zakace sun kai 9months ne sabida yadda sukai bulbul dasu da wani irin k'yau sabida wadatacciyar kulawa da suke samu daga iyayensu da kakanninsu,kai infact kowa nason 'yan ukuna,babu wanda ze gansu beyi sha'awarsu ba.        Abangaren Mubeen kuwa,tuni ya manta da batun wata Zahra don Hanan ta zage damtse akan nada tana nuna masa tsantsar soyayya da kuma kulawa wanda ya zarce nada.wani irin soyayyace yake wa Hauwa'u Jiddah ayanxu wanda ko kadan beji hakan ba alokacin da yake tare da Zahra.Anan ya gane kuma ya tabbatar wa Kansa da cewar lallai _*SO_* na hakikanin gaskiya kwara _*DAYA_* ce tak!.kuma shi yakewa Hanan dinsa.       Bangaren Suhaileedar suma ba'a barsu abaya ba don rayuwar auransu mah abar kwatance ne,haihuwarta de shiru tukunna because planning sukai don ta samu nutsuwar karatunta wanda watanni kalilan ne ya rage mata ta kammala final year dinta.Tuni Leedar da Fresh suka soma bautar kasarsu ah federal high court dake nan zariar wadda justice ne ya shige musu gaba har suka Samu aka barsu anan,da zarar sun gama kuma zasuje law school na shekara guda ah Lagos before they will be call to bar.    *****       _*BAYAN SHEKARU UKU*_   Tuni Leedar suka soma aiki ah babban kotuna,shi Leedar an basshi ne anan federal high court tanan Zariar,ayayin da shi kuma Fresh akayi posting nashi ah can supreme court dake Abuja,ayanxu haka sunyi aure da Ashwairiyyarsa har tana mah dauke da juna biyu.ita kuwa Suhaima tana da d'a dan shekara daya meh sunan babansu leedar wato Ahmad,ana kiransa da 'Ammur'.     Fadima kuma tana dauke da tsohon ciki,haihuwa yau ko gobe,su triplets an girma sae uban wayau.Arzikin Mahmood se dada bunkasa take,Dr.Shamsu tsufa ta soma kamashi don haka yayi ritaya,seya mik'awa Mubarak mukaminsa.Ayanxu Mubeen ya koma _*Chief medical director Mubarak MUSTAPHA NAKOWA*_.      Kowa na tattalin matansa da 'ya'yansa,rayuwa dukkaninsu suke abar kwantace da sha'awa.Zancen jinns kuma babu labarinsu,babu wanda yafi karfin ubangiji sede idan baka kai kukanka gareshi ba.Itama Rukky tayi auranta.Usee kuwa Bayan ya kammala master dinsa,ya sami aiki ah 'GT bank' don accountancy ya karanta.dama suna soyayyarsu aboye da Hafeezah yar gidan baba Mu'azzam har asirinsu ya toni,bayan yayi settledown se aka daura musu aure gaba daya har Afreen da Arham dinta.ita kuwa auta Rafi'ah ita kadaice ta rage don ss2 mah take ahalin yanzu.       _*Tammat bihamdulillahi! anan na kawo k'arshen littafina SHIN SO DAYA NE?(Mijin kaddarata),mijin kaddararta ya zame mata alheri.*_ _*ba yawan litattafi shine fadakarwa ba,no sakon ciki kawai akeda buqata.wasu darussa kuka tsinta aciki?*_ _*Da fari de ku rage yiwa mutane wulaqanci sabida baku san baiwar da Allah yayiwa wannan ba,haka kuma baku san abinda ya taka ba,shi din mutum ne,aljan ne? Ko kuma wani jinsin daban? Ga example nan na abinda ya sami Rukky lema,ta wulaqanta samari Ashe abinda bata sani ba aljanu ne,su kuma suka shiga jikinta don daukar fansa,suka dunga cutar da ita ta hanyar sanyata aikata miyagun ababe*_ *sannan kuma amatsayinku na musulmai ku koyi yafiya,ga example nan ga Suhaima Sa'ad tana da riko da kuma kafiya wanda hakan ita kanta ya cutar da ita da shi kuma Leedar,if not becuz of Fadima sa'ad toh kuwa da basu kai inda suke ba ayau,ita kuwa taimako tayi wanda shima ina son kuyi koyi da taimakon,gashi adalilin hakan Allah ya kaddara auranta da Mahmood wanda daga baya auran ya zamo mata alheri.*_ _*Abu mafi Muhimmanci wanda nafi son kuyi koyi dashi shine,karbar kaddara meh k'yau ko mara kyau, don Allah bakuji Mubarak ya birgeku ba? Muna ta tsammanin za'ai tashin hankali ba kadan ba,amma se gashi ya shayar damu madarar mamaki.... Muma Allah ya sanya muci jarabobin ubangiji,wanda yake kan mana,wadda yayi mana da kuma wanda ze mana nan gaba... Amin Yah Allah!!!    Kuskuren dake cikin littafin nan Allah ka gafarta min,alherin dake cikinsa kuma Allah ka tabbatar min dashi,Allah ka albarkaci wanann farkon littafin nawa,Allah kasa na fadakar kuma na isar da sakon dana dade ina son isarwa.... Allahumma amin. 👏       Ku kasance dani acikin sabon littafina wanda ze fito nan gaba meh suna _*HIBBATULLAH (KYAUTA DAGA ALLAH)*_  find out about diz book Hibbatullah,karku sake abaku labari!!     I nid ur comments,idan kin san baki taba comment ba toh don Allah yau ki fito kiyi!!! Akullum kofata abude take na karban corrections da korafi.ku tuntunbeni tanan don korafi _*07065481260*_       Nagode.... *HAFNAN💞* *💘SHIN SO DAYA NE?💝* https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/           *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*                *{Onward together}* *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART  TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔        *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*         *WATPADD:HAFNANCY💞*         *IG:Hafsy___mustee*                      ✨✨✨ *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*         🌼BABI NA GOMA🌼   *page 26-29*     _*kuyi haquri da typing errors banyi editing ba don sauri,na tabbata sakon ciki kawai kuke da buqata ba spellings ba*_      Ummace ta cimma Abba adaki yana shirin xuwa wurin aikinsa.Hankali tashe ta shigo cikin dakin rik'e da wayarta ahannu.Kallo d'aya Abba yayi mata ya gano tsantsar damuwar dake shimfid'e akan fuskarta,dakatawa yayi daga sanya safarsa yace"Kareemata lafiya kike kuwa?meya faru kuma naga fuskarki dauke da damuwa....?"     Tace"Abba wlh tun dazu nake ta k'iran 'yar Kareematu amma taki ta daga,shine nake tunanin anya lafiya take kuwa? " Murmushi kawai Abba yayi,ya cigaba da sanya safarsa,can yace"Kareema kina da gajen haquri in dai akan 'ya'yanki ne,yanzu don Fadima taki daga wayar shine kika shiga cikin damuwa?don Allah kiyi mata uzuri mana kila bata kusa da wayar ne,in banda abinki mah ke kanki kinsan yadda kuke waya ada da yanxu bazai taba zama daya ba sabida yanzu ta koma k'arkashin wani ne,ma'ana mijinta wanda ayanxu ya fimu iko akanta,kuma ya zamar mata dole ta dunga masa bautar aure,don haka abinda nake so dake ki dan k'ara haquri nasan muddin idan tazo taga missed calls dinki dole zata nemeki....."      "A'ah ni dai hankalina zaifi kwanciya idan ka k'irawo mana mijinta muji daga gareshi.... " Yasan idan beyi mata abinda takeso ba toh tabbas ba zata shafa masa lafiya ba.Daukar wayarsa yayi ya latso shi Mahmood din.     Tafe suke acikin Mota duk ahankalinsu atashe,babu abinda Kakeji illa sautin kukan Fadima dake tashi ahankali,duk wani irin salon rarrashi babu wanda Mahmood beyi mata ba amma taki tayi shiru,haka ya haqura ya k'yaleta amma sosae yake jin kukan na dukan xuciyarsa.   Wayarsa ce yaji ta dauki kid'a,da hanzari ya lalubota ah aljihun wandonsa. *'ABBA'*,shine sunan daya gani yana rawa ajikin screen din wayar.Gabansa ne yaji ya bada rasss!.     Arud'e ya dubi Fadima yace"Baby wlh Abba ne ke k'irana,ko dai kin k'ira kin fad'a musu abinda ke faruwa ne? " Alokaci d'aya na tsaida kukana jin abinda ya fito daga bakinsa,wani mugun kallo na watsa masa,kana na had'iyi wani muyau mukut!      Nace"Tunda garin Allah ya waye ka ganni ne rik'e da waya balle kayi tunanin kona k'ira na fad'a musu ne?yanxun mah dubeni da k'yau babu wayar atare dani,tashin hankali ya sanya na mantar da ita agida...... " Wani sassanyar ajiyar xuciya ya sauke kafin ya daga k'iran wanda kiris ya rage ta katse.Bayan 'yan gaishe-gaishe Abba yace"Don Allah sirikina kayi haquri na takuraka da sassafen nan,wlh mahaifiyar Fadima ce take ta k'iranta awaya tun dazu amma bata daga ba,shine ta sanyani agaba akan dole saina k'iraka muji daga gareka koh lafiya? "     Oh! Allah yanxu ya zeyi?yanxu sae yai wa Sirikinsa k'arya agaban 'yarsa? Wani b'angaren xuciyarsa yace"Toya kuwa ka iya? Ai ya zame maka dole kayi masa k'aryar don kada ka tada hankalinsu musamman na mahaifiyarta.    Ahankali yace"Allah sarki Abba ni na dan fita ne,amma na barota agida tana bacci bata tashi ba,kuma wayarta ah silent take shiyasa kila bata ji ringing din wayar ba,amma na tabbata idan ta tashi xata nemeku da kanta...... "     "Ni kaina nayi tunanin hakan kuma nayi iya bakin k'ok'arina wajen fahimtar da uwar amma taki ta gane,madallah nagode d'ana,ah yini lafiya.... " Daga haka sukayi sallama.     Abba ya dubi Umma ya kora mata bayani.Tace"Ikon Allah! bacci sae kace baccin mutuwa?koda wayartata ah silent take ai taji vibration..... "     "Idan yana meeting mode kenan ko?don idan akace miki silent toh ai kin san wannan kwata-kwata ba'a jin k'ararsa,meeting mode ce kawai take bada vibration.... "    Shiru tayi masa bata k'ara cewa uffan ba don yanxu dai hankalinta ya d'an kwanta tunda 'yar tata nanan lafiya qalau.      *** "Meyasa zaka masa k'arya? Meyasa baka fad'a masa abinda ke faruwa ba idan yaso ya taho ya raba auran daya daura don kowa mah ya huta da tashin hankali....? "    Cike da mamaki yake kallonta,yace"Yanzu Babyna sae ki rabu dani akan abinda be taka k'ara ya k'arya ba?ina ce kece da bakinki ki fad'a min adaran jiya cewar you promised to withstand any obstacles that will come our way? Kuma kika ce min har kin soma jin sona aranki? Then why are you trying to go back to square one again? Inace mun wuce nan ko?" Afusace nace"Ai kaine kake kokarin sakani na koma square one din becuz you ain't helping matters at all,kace I shld be strong & bold to face ur family problems,I was trying to do such buh kwata-kwata u were not helping at all,ka tsaya kurum anata zagina har asiri akace nayi muku but u couldn't speak out,u were juz standing and looking kamar wani zararre..... "     "Baby am very sorry,abinda nakeson ki fahimta shine,idan babba yana magana be kamata ka katse masa hanzari ba becuz yin hakan na nufin rashin kunyace akai musu,balle mah Momi sam bata qaunar tana fad'a kaima kana fada,tafi son ace koda kana da gaskiyarka still kayi shiru da bakinka har ta gama kafin ka soma bayaninka,shiyasa ta qara fusata da kika tsoma baki kika katse mata hanzari.......... "      Sae ayanxu na fahimci dalilinsa na kin k'areni alokacin da aketa ci min mutunci,sae kuma naga da gaskiyarsa,be kamata ace na tsoma baki cikin xancen nan da nan ba.Da haka muka k'araso gidan baba Mu'azzam din,xuciyata sae harbawa take da sauri da sauri.     "Babyna relax,cool down & regain back ur confidence..... " ya fadi hakan alokacin da muka fito daga cikin motar.    * Acikin gidan Baba Mu'azzam kuwa,gidane ya kacame da rigima,ita Momi ruwan bala'i take ta zazzaga wa Baba Mu'azzam,tana yi,ya'yanta mah na tayata,su Afreen kuwa sun k'asa jurewa rashin kunyar dasu Khairat kewa mahaifin nasu,don haka gabaki dayansu ne suka taso suka shiga cikin fadan,gidan sae ya dada kacemewa da hayaniya.Goggo Ladidi kamar tasan za'ai rigima shine tazo da wannan safiyar,donsu Momi anan suka cimmata,hadda ita Goggon Momin ta hada aciki wai sun had'a kai sun munafurceta.     Sae da Kaka rigima ta dauko jibgegiyar dorinarta Sannan kowa ya shiga taitayinsa.Kallon Momi tayi wacce take tsaye sae girgize-girgizen jiki take,fuskar nan tata cike da b'acin rai k'arara.         Kaka rigima tace"Haba Binta da girmanki kike Abu kamar wata yarinya?abinda yara zasuyi kiyi musu fada shine ke kike yinsa da hankalinki da kuma wayonki?Ina wani amfanin tashin hankali anan?abune da idan an xauna toh kuwa tabbas za'a fahimci juna,amma kinzo kin tasa bayin Allah agaba kina haushi kamar kare kin hanasu mah suyi bayani sabida masifarki,wlh Binta ni mamakin wannan bak'on halin naki nake don sam ba haka kike ada ba,don Allah ina rokanki,idan har kinzo ne ki maida min da gida ya zamo filin yaki toh tun wuri ki hanxarta barin gidan nan don bazan tab'a bari ki raba min kan zuri'a ba,idan kuma ta maganar fahimta ce kika zo da ita,toh maza sami wuri ki zauna ayi maganar atsanake,idan kuwa d'ayar ne toh maza ki fuce min daga gani kafin na bud'e idanuwa........ "    Duk iya shegen mutum da kuma bala'insa toh kuwa abayan Kaka rigima yake,ko kadan bata d'aukar kaniya,hakan yasa Momi ta sassauta rigimarta,ta nemi gu ta xauna,adaidai lokacin su Mahmood suka shigo.Su Khairat sae aikawa Fadima da kallon banza suke don babu damar magana,Kaka rigima ta kasa ta tsare. Ni kuwa kallo daya nayiwa dukkan halittun dake cikin makeken falon,kana nayi saurin sadda kai k'asa sabida wani irin kallon banzar dasu Khairat ke jifana dashi.    Cike da murna su Afreen suka mik'e suka rungumota,"Oyoyo Anty Zahranmu sannu da xuwa.... " haka suka fada ah sa'ilin da suka cikata.Ni kuwa harga Allah naji dadin wannan tarbar tasu,atleast akwai masu sona acikin dangin mijina,kuma hakan da sukayi ze tabbatarwa Momi da cewar idan su sun k'ini,toh kuwa acikin zuri'arsu dakwai masu qaunata don Allah.     Daya bayan d'aya nabi manyan ina gaidasu suna k'arbawa,Momi ce kawai banyi kusa da ita ba don bana son ta min wani wulaqancin. Kaka rigima ce ta rik'e hab'a tace"Oh! ni Aishatu daga tarewar amarya jiya jiya shine har kin soma saka kafafu kina fita? Koda yake ko kadan banga laifinki ba,uwar mijinki ce ta tasoki agaba da tashin hankali...... "     Ta fadi hakan tare da nuna Momi.Ita kuwa Momin kawar da kai tayi gefe tana meh cike da jin haushin cin mutuncin da tsohuwar take ta mata agaban 'ya'yanta da kuma sirikartata. (Ai! ai kin yadda cewar Fadimar sirikar taki ce?😜) Wuri na samu akusa dasu Afreen na xauna,shi kuma uban gayyar kusa da Usee ya zauna.Ko'ina yayi tsit ana sauraron bayanin da ze fito daga bakin Baba.     Baba ne yayi gyaran murya ya soma magana ak'aron farko tunda muka shigo"Binta dama ina da niyyar k'iranki kizo ayi magana ta fahimta,sae gashi kinyi saurin ji tunda dama can ai aure ba abin b'oyuwa bane dole ajita daga bakin mutane."      Ya dan dakata,can ya cigaba"zancen kuma wai ita Fadimar budurwar Mubarak ne,shine ni ban san da wannan ba,abinda kawai na sani shine,yaro yazo ya sameni akan cewar yana son na shige masa gaba na nemar masa auranta ba tare da saninki ba,sosae nayi mamaki da jin wannan furucin nasa,ko dana tambayeshi ce min yayi wai don bakya qaunar yarinyar ne,amma bayan auran sae akiraki ah fahimtar dake,toh ni abinda ya saka na amince xan shige masa gaban shine,yarinyar daya samo 'yar babban gidace meh wadatacciyar tarbiya,'yar kuma wani aminina,shiyasa kai tsaye na shige masa gaba don bazanso yayi asarar mace ta gari ba,sau uku ina tambayarsa cewar da fatar sun daidaita kansu shida yarinyar?don bana son asami wata matsala,se yace min eh sun daidaita din,amma ni ban san cewar ita yarinyar budurwar Mubarak bace da banyi gangancin saka kaina cikin wannan al'amarin ba,kai Mahmood anyi hakan ko ba'ayi ba? "      Yayiwa Mahmood wannan tambayar yana meh jiran yaji ta cewarsa,ahankali Mahmood yace"Hakan akayi Baba.... " anan ya kwashe labarin komai tun farkon soma haduwarsa da Fadima akano,xuwa binsu da yayi,k'arban tayin aikin ABU da yayi sabida ya komo kusa da ita,dramar da suke tasha da Mubarak akanta,komai ya fada musu ba tare daya rage gishiri ko kadan ba.    wuri ya rud'e da tofe-tofen albarqacin bakunan mutane,wasu na cewa yaci amana ko kadan be k'yauta ba ayayin da wasu ke cewa haka Allah ya kaddara cewar ita din matarsa ce ba rabon Mubarak bace.     Anan kuwa Baba ya shiga zuba musu nasihu meh ratsa zukatu da kuma nuna musu cewar tun fil'azal haka Allah ya rubuta cewar Fadima ce matar Mahmood ba Mubarak ba,kuma ai ba abin tirr bane tunda akwai aure tsakaninsu.Yayi nasiha sosae wanda har hakan ya sanya Momi xubda makaman yakinta,daga ita har 'ya'yan nata.Hawaye ne keta shatato mata asaman kunci. Ni kuwa arayuwata babu abinda na tsana illa naga uwa tana xubda hawaye akan danta,babu zato babu tsammani sae kawai gani sukayi na mik'e na nufi wurinta.Tsugunnawa nayi tare da amfani da gefen mayafina na shiga goge mata hawaye ina cewa"No ummana pls don't cry akan abinda danki ya miki,kina da right din da zaki umarceshi daya sakeni idan har bakya son wannan auran...... "      Ban ida gama maganata kawai wani dan marayan kuka ya kufce min,ba tare da wani b'ata lokaci ba,Momi tayi saurin rungumoni tsam! ajikinta.Tace"Yata ba wannan ne ke damuna ayanxu ba,damuwata aynxu shine yadda Mubarak ze k'arbi zancen idan ya dawo,idan ba haka ba ni wlh na k'arbeki hannu bibbiyu amatsayin surukata....... " Gabana ne ya yanke ya fadi jin ta ambaci sunan 'Mubarak',na manta cewar akwai sauran rigima agaba.Ya salam! Wannan wacce irin sabuwar rayuwace na shiga? Cikata nayi alokacin dana ji Baba na k'ok'arin magana.   Yace"Fadima kina son Mahmood? "     Kallon shi Mahmood din nayi,naci sa'a kuwa Shima din kallona yake. "Amsa zaki ban ba cewa nayi ki kalleshi ba,kuma gaskiya zaki fada min karki cuci kanki,idan har bakya sonshi toh ki fito filli ki fada kowa yaji...... " Mahmood kuwa k'ura mata idanuwa yayi ayayin da xuciyarsa ke harbawa da sauri da sauri,karfa Fadima tace bata sonshi don agaskiya baze iya cigaba da rayuwa idan babu ita akusa dashi ba. "Eh baba ina sonsa kuma na amince xan zauna dashi har k'arshen rayuwata.... " Wata sassanyar ajiyar xuciya Mahmood ya sakar tare da yin hamdala acikin xuciyarsa.    Baba ya dan muskuta yace"Alhamdulillah! dama abinda nakeson naji daga gareki kenan,don haka abinda nakeso daku shine kada kowa acikinku ya sake ya k'ira Mubarak ya fesa masa zancen,ku jira har ya dawo,duk ranar daya diro garin nan don Allah Binta ki kirani zanzo na nutsar dashi tare da fahimtar dashi,itama matar tasa ku gargadeta dakyau,karta kuskura ta fada masa...... "      Kowa ya amsa da yaji kuma za'a kiyaye,anan aka shiga nemar gafarar juna,su Khairat suka nemi gafarar Fadima da Mahmood da kuma cousins din nasu.Mahmood ya nemi gafarar mahaifiyarsa Sannan aka soma watsewa.Se da Momi taja Haj.Fa'iza cikin daki,tace mata tasan irin abokan da zata dunga fadawa sirrinta don gashi-gashi abinda Haj.Rabi tace Haj.Nera ta gaya mata.(lol mata kenan da k'ananun magana,ance-ance baya tab'a kare mana😁).    Tayi mamaki kwarai da gaske don Haj.Nera har rantsuwa tayi mata akan babu wanda zeji,ashe sae data je ta karas mah haj. Rabi.Kwafa tayi tace zasu hade da Neran ne.Momi tace "A'ah ki barta kada abu ya zamar muku rigima,nide kawai na gaya miki ne don kisan irin k'awayen da kike tare dasu Sannan ki rage gaya musu komai naki......sae anjima.... "   Ta fice abunta,awaje mah seda ta sake nemar gafarar Fadima,Fadima tace"Haba Momina nifa baki tab'a min komai ba,idan kuwa har kinyi toni na riga na yafe miki tuntuni.... " Sosae Momi taji dadin zancenta,atake anan taji Fadimar ta sami wani gurbi acikin xuciyarta.        ***** Bayan sun kai gida kuwa,Mahmood ya rasa inda zai saka kansa don murna,yace da Fadima"Babyna ban tab'a tunanin cewar komai zaizo mana da sauki haka ba,na aza ko se anyi yankin duniya ta uku ne kafin komai ya lafa,sae gashi komai yazo mana da sauki,addu'a kenan baya tab'a faduwa akasa,yanzu sauran mana Mubeen,Allah yasa ya fahimcemu.... "     Ahankali na amsa da "Ameen" Yace"oya yi Maza ki k'irasu Umma amma don Allah na rokeki pls karki sanar dasu komai,ki koyi b'oye sirrin mijinki okay?"     Murmushi nayi nace"Haba! ai duk wata mace meh fallasa sirrin mijinta doluwace kuma da sauranta yasin... " Light kiss ya sakar min akan leb'ena yace"Thanks matata,I love you my *'Zahmood'*.     Cike da jindadin sunan daya ambato agareni nace"love you too my *'jannah'*................. 📝   A/N Wow! Congrats *'Zahmood💞'*.... Sauran muku rigimar Mijin jiddoh!!!         2episodes remaining,amma sai next week zaku gansu duka biyun atake don diz week Muna da biki,yanxu haka mah na kokarta nayi muku typing ne don kada kuji shirun yayi yawa.        *'HAFNAN'*            https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/     *💘SHIN SO DAYA NE?💝*        *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*               *{Onward together}* *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART  TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔          *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*        *WATPADD:HAFNANCY💞*         *IG:Hafsy___mustee*                        ✨✨✨ *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*         *🌼BABI NA SHA DAYA🌼*   *page 29-30*       Ummata na k'ira wacce muna gama gaisawa ta rufeni da fada,wai dole na ajje wannan baccin safen nan agefe wanda ya riga ya gama bi min jiki,tace idan ban kama jiki na watsar da kiwiya agefe na dunga kula da mijina ba,toh kuwa namiji shi babu ruwansa,idan yaga bakya masa abunda yakeso toh kuwa yana iya banka miki kishiya wacce zata zo ta dunga kula da bukatunsa da kuma tattalinsa,ke kuwa awatsar dake agefe ki koma 'yar kallo.Mun jima tana min nasihu meh ratsa xuciya,daga bisani mukayi sallama.Shima Abbana na k'irashi mun gaisa.Har yake labarta min irin yanayin da Umma ta shiga alokacin da take ta k'ira amma babu amsa.Dariya nayi sosae tare da jin wani irin soyayyar Ummata na ratsa jinin jikina.    Kai tsaye na latso _*My Ashwairiyya*_. Ita kuwa awannan lokacin ta fito wanka kenan,tana gaban madubi tana taje kanta,so take taje taga dakin Suhaima.Wayarta dake gaban madubi taji ya dauki kida,da hanzari takai hannu ta dauketa.     *'Fateenah'* shine sunan data gani yana rawa akan screen,gabanta ne taji ya bada rasss!.... Jefar da comb din hannunta tayi tare da mik'ewa da sauri har jikinta na dan rawa don tsananin tsoro da kuma fargabar abinda zataji daga sahibar tata. "Hel....lo... Fateenah'...... " haka ta fada cike da in-inna ah sa'ilin da tayi picking call din.     Bushewa da wani irin dariya nayi don nasan abinda take yiwa wannan rawar muryar,wato atunaninta tsantsar tashin hankali zata tsinta daga gareni shiyasa take cike da tsoro. Allah sarki my Ayush komai yayi chas-chas ahalin yanxu. Nace"Malama idan zaki daidaita muryarki toh tun wuri mah ki daidaita don ni yanxu babu abinda nakeso sama da mijin da kuka hana min saninsa da wuri sae akurarren lokaci...... "     Kwashe komai nayi na gaya mata tun wucewarsu,tarewata da kuma rigimarmu adaren farko,sae kuma sabuwar rigimarsu Momi da kuma xuwarmu gidan Baba Mu'azzam da kuma nasihunsa agaremu,sae kuma sulhun da aka nema. Wani wawan ajiyar xuciya Ash ta sauke,cike da murna tace"Wayyyo! Fateenah' ina zan saka kaina don murna? Agaskiya naji dadi ba kadan ba da har kika haqura kika rungumi mijin kaddararki,fateenah wlh believe me Mahmood shine kalarki ba Mubeen ba,wlh ni dama can ina ta miki kwadayin aurensa sae gashi lokaci daya Allah ya amsa addu'ata,ya zamo mallakinki,yanzu dai addu'armu shine Allah yasa Mubarak ya fahimceku ya kuma gane cewar wani baya taba auran matar wani,haka zalika wata bata taba auran mijin wata........ "     Cike da sanyin murya na amsa mata da "ameen." Tace min tana shirin xuwa gidan Suhaima ne,nace yanzu Muna gama waya ita zan kira.Mukayi sallama.     "Nima ahalin yanxu babu abinda nakeso kamar matata wacce naki bayyana kaina agareta sae akurarren lokaci..... " Da sauri na waiga tare da watsa masa wani Irin kallon soyayya,ware min hannayensa yayi.    Ahankali ya furta"Babyna I nid a warm hug...... " Babu b'ata lokaci na isa gareshi tare da fad'awa jikinsa,sannu ahankali ya maida hannayensa ya rufe yana meh dada kankameni.kunnuwana dake saman k'irjinsa ya sanya nake iya jin yadda xuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri.Ahankali na lumshe idanuwa ina meh jin wani irin sonsa na ratsa jinin jikina.     *** Ash cike da farin ciki ta Latso su Leedar da Fresh take labarta musu zancen Fadimar,suma din sosae sukai murna tare da musu fatar alheri da kuma addu'ar Allah yasa Mubeen ya fahimcesu.          * Cike da rawar jiki ta mik'e tana fadin" Momi kunnuwana sun kasa gasgata zancen da kike min? Taya za'ai Zahranmu ta rikid'e ta zamo matar Yah Mahmo?abu sae kace ah wasan kwaikwayo?"     "Toh wannan maganar da nake miki wasar zahiri ce bata kwaikwayo ba,Fadima de ayanxu matar Mahmood ce wacce ya b'oye mana auranta da yayi.... " acewar Momi. Cike da al'ajabi Hanan tace"Tabdijam! agaskia Momi Fadima da Yah Mahmo sunci amanarmu,Fadima ta manta cewar itace farin cikin mijina,shine don ta ruguza wannan farin cikin nasa shine ta tashi ta auri Yah Mahmo?dama can ni nasha fadawa Mubarak cewar nifa ina ganin kamar Fadimar bata qaunarsa kamar yadda shi yake hauka akanta,amma sam yaqi saurarona sabida makauniyar so daya rufe masa ido,yanxu ga irinta nan,ta tashi ta aure masa dan'uwa wanda na tabbatar ba k'aramin yaki za'ai ba kuwa idan ya dawo........ "     Ta rushe da kuka tare da ficewa da gudu tabar dakin,Momi kuwa sae Binta da kallon mamaki take,ahankali tace"Kai! kai! kai!!! Wayyo ni Bintu d'iyar hassan nide wallahi ban tab'a ganin shashasha marasa k'ishin mijinta kamar Hauwa'u ba,in banda abin sokuwan ai wannan al'amarin ah dadinta kenan tunda anyi nasarar raba mijinta da wacce yake fifitata akanta,amma jibi abinda wawiyar ke fada,yanxu duk suruntun da nake tayi ya tashi abanza kenan?tunda ta kasa fahimtar cewar ita Fadimar mah bata da masaniyar mijin da aka aura mata sae bayan an kawota....."     Taja tsaki tare da mik'ewa don gabatar da sallar la'asar.      ** Awannan daren mun gurji amarcinmu,Mahmood ya fanshi kudin sadakinsa ba kadan ba,ni kuwa nasha kuka har na baiwa uku lada,lallashi da sanya albarqa kuwa har Mahmood ya gaji da yinsu,sae cewa yake "Matata ubangiji Allah yayi miki albarqa,nagode kwarai da gaske da kika tsare min mutuncin kanki har kika kawoshi gidana.....*'Zahmood'* ina sonki matuk'a fiye da tsammaninki,Allah ya k'ara mana qaunar junanmu,Sannan kuma Allah ya azurtamu da 'ya'ya nagari....."     Cike da farin ciki na amsa da "Ameen ngd my *'Jannah'*.     Da safiyar ranar kuwa,sae ga Usee da kayan breakfast wai Momi ce tace akawo mana.Sosae abin ya bamu mamaki matuk'a tare da jinjina al'amarin,Mahmood ya k'arbi basket din yace"Usee kace mata muna godiya sosae sae mun shigo.... "    Da sauri Usee yace"A'ah tama ce suna nan tafe gobe duka dasu anty Meema.... " Gabana naji ya yanke ya fadi jin abinda ya fada,amma sae na kada baki nace"Allah ya kaimu kanin miji,sae mun gansu..... "    Murmushi ya sakar min yace"Toh!  matar Yayah,sae anjimanku.... " Muka had'a baki wajen cewa"Toh mu jima da yawa.... " ya fice.     Wani uban tsalle naga Mahmood ya daka yana fadin"Yessss! My family have accepted my Zahra da hannu bibbiyu........ Sauran mana kaninmu.... " Murmushi kawai nayi abina.Daga haka muka soma cin breakfast wanda ferfesun kan rago ce,sae kuma kayan tea.     Washeqari kuwa sun cika alqawari,sunzo din hadda 'yan gidan Baba Mu'azzam su Hafeezah da mominsu.Gida ya cika ya kacame da hayaniya,sae fira muke cikin raha da annashuwa.Dama tun safe nida Mahmood muka hada musu lafiyayyar girki kan suzo. Nace"Anty Meema waini ina Anty Hanan ne? " (Dayake mijina ya fada min cewar yanxu ta koma gidansu Momi da zama tunda mijinta ya tafi,shine nayi tunanin kila tare zasu zo amma kuma sae naga akasin hakan,babu ita aciki).    Momi ce ta kada baki tace"Hanan tana gida kinsan ciki yayi nauyi yanxu,don haka mah bata cika fita,amma tace tana gaidaki.... "    (Gaskiyar lamari kuwa shine,babu yadda Momi batayi da Hanan ba akan tazo suje amma taki,tace babu inda zata,akan dole Momi ta rabu da ita,Jasmin mah ta hanata binsu,ita kuwa yarinyar sae kuka taketa yi amma babu damar zuwa tunda uwarta ta hana). Nace"Allah sarki! Allah de ya raba lafiya... "    Ni nasan tabbas Momi tade k'are Hanan ne,amma ni xuciyata ta bani cewar haushina takeji sosae don na auri wan mijinta.Oho! Wallahi kome ze faru ya dade be faru ba donni dai yanxu harga Allah ina son mijina kuma bana danasanin aurensa,kuma babu wanda ya isa ya raba wannan auran sae Allah wanda shine ya hada abinsa.Su Momi da Khairat seda suka sake nemar gafarata akan cin mutuncin da suka min da kuma sharrin asirin da suka lik'a min.Nace"Laah! wallahi babu komai,ni wlhy ban rik'eku axuciya ba,Allah ya yafe mana duka... " Awa daya kacal su Momi sukayi,Sannan suka wuce,su Hafeezah kuwa sae da marece direban gidansu yazo ya daukesu wanda dama can shi dinne ya kawosu.'yan kudade na basu wanda Mahmood ne ya bani akan cewar idan sun tashi tafiya saina basu.    Nace"Afreen gashi ba yawa kwa siyi kayan kwalliya,naso baku acikin nawa ne amma kayan lefena nacan Zaria..... "    "Laaaaah! kuji anty sae kace wasu baki?mufa kannenki ne basai kin bamu wani abin ba,sada xumunci mukazo yi ba maula ba.... " Ah wasance nakai mata bugu ta goce,nace"kai Afreen yanxu yaya bazata iya baiwa kannenta kyauta ba? Shikenan idan ta basu ya zama maula ce suka yi? "       "Mude kome zaki fada bazamu k'arba ba,ki rik'e abarki bama so.... " tayi gaba su Rafi'ah suka take mata baya,har wajen Mota na bisu amma sam sunki k'arba,Afreen ce ta umarci direba daya tada motar,ya kuwa bi umarninta suka fice.Su Anty Meema mah haka suka min dana ce gashi sa baiwa 'ya'yana susha alawa,suka k'i k'arba. Asanyaye na koma ciki,gab da sallar magrib ogan nawa ya dawo.Ware min hannaye yayi wai nazo na rungumeshi,babu b'ata lokaci na isa gareshi ina dan bubbuga kafata akasa nace"Anki ah rungumekan,daga cewa zakaje kayiwa abokanka ban gajiya shine kayi zamarka acan ko? Kode sunyi maka wata matarce ban sani ba? "   "Lalalalaaaah! Sunma isa?kuma nima na isa na so wata bayan my Zahmood?wallahi babu ta biyunki acikin xuciyata my Zahra,ke kadai kin isheni rayuwa...... " "K'arya kake har yanxu kana son Zaynab,kuma itama din ai hakan ka fada mata,kace babu wata da zaka rab'a ko bayan ranta,sae gashi ayau ka k'arya alqawari...... " babu xato ba tsammani kawai naji hawaye ya soma ziraro min saman kunci,hawayen da ban san ko na menene ba? Kota kishin Zaynab dinne ko kuwa tausayin kaina na ganin na kamu da sonsa bayan nasan har yanxu yana qaunar Zeeynsa,kuma ko kusa nasan bazan taba samin irin matsayinta axuciyarsa ba,yafi sonta akaina nesa ba kusa ba.    Shima din idan yace ya manta Zeeynsa toh kuwa yayi k'arya,yasan yana mugun son Fadima,amma Zeeynsa ta dabance acikin xuciyarsa,yasan tabbas watarana Fadimar tana iya maye gurbin Zaynab din acikin xuciyarsa idan har ta iya bi dashi yadda ya kamata amatsayinta na wayayyiya. Rungumota yayi ya soma lallashinta,cike da kissarsa da kuma salonsa ya mantar da ita batun Zeey.Atake anan suka shiga farantawa juna rai,suna meh jin sabuwar qaunar junansu na ratsa dukkan wani gab'ar jikinsu.Ya tambayeta yadda sukayi da bak'in nata,anan ta bashi labarin yadda sukai dasu Afreen,sosae yayi dariya hadda k'yak'yatawa.     Yace"Ai nasan halin Afreen sarai bata son ana mata irin wannan k'yautar,sae tayi ta ganin kamar malauce tazo yi,yanxu mah idan ba sa'a kikaci ba,toh kuwa tana iya jera miki kwanaki kafin ki sake ganinta agidan nan.... " Waro idanuwa waje nayi nace"Akan nayi mata k'yautar kudin?"    "Naki wasane yarinyata,toh bari kiji akwai wani saurayinta Arham dake masifar sonta,toh wlh ko kwandala ya bata,toh shikenan daga ranar ta dena kulasa kenan har sae iyaye sun shiga cikin maganar,yanxu maganar da nake miki,babu wata k'yautar kudi da take k'arba daga gareshi,ita fa ta gwammace ayi mata k'yautar wani abin can daban amma bawai kudi ba,aurenta mah nan da wata uku masu xuwa insha Allah.... "    Ahankali nace"Allah ya nuna mana.... Agaskiya nide ta birgeni,sam abin duniya basu rufe mata idanuwa ba kamar wasu matan..... "      "Ai Aysha Afreen tayi ne,wallahi da'ace ni meh sha'awar auren dangi ne,toh kuwa wallahi da ita xan aura sabida halinta yayi ne... " ya fada tare da kashe min one eyes. Wani irin kishinta ne naji ya tokare min qahon xuciya,lokaci daya na sakar masa kukan shagwab'a,nace"Nasan kila auran mah dakai za'ayi,b'oye min kawai kake kamar yadda ka b'oye min aurena dakai...... "     Rik'e cikinsa yayi yana dariya yace"Babyna ji yadda kika koma lokaci guda,don't tell me kema kina da kishi sosae juz lyk Zee...... " B'ata fuskar da yaga nayi ne ya sakashi yin shiru,ya sosa k'eya tare da fadin"Am sorry my Zahmood bazan k'ara k'iran sunanta agabanki ba.... " sae kuma naji duk ya bani tausayi.Haka muka cigaba da wasanninmu na ma'aurata kafin daga bisani muka mik'e don gabatar da sallar magrib,bayan ya dawo daga masallaci kuma muka zauna cin abinci.       **** Kwanakin amarcin daya biyo baya kuwa ba'a magana don sosae nake samun kulawa da kuma daddadar soyayyar mijina agareni,nima ba laifi ina gwada masa tawa kulawar da soyayyar akoda yaushe.'Ya mace kenan,ko kuma nace xuciya ita de babu ruwanta,da zarar ta sami Wanda yake bata kulawa da kuma damuwa akanta,shike nan saita mace akan son wannan din,gashi ayau son da nake yiwa Mubarak ya zama tsuntsu ya koma kan Mahmood.Ayanxu Kam ina masifar son Mijina Wanda har nake jin bazan iya cigaba da rayuwa babu shi ba,tofa kullum muna mak'ale da juna baya fita,koda ace ya fitan ne,toh kuwa baya jimawa yake dawowa,dalilin daya sanya muka k'ara shaquwa dashi kenan.       Hakan yake gasu Suhaileedar,sun wani k'ara shaquwa da wani irin mugun son junansu daya qaru,sosae leedar ke tattalin Suhaima kamar wata sarauniya,haka mah iyayensa da kannensa ke masifar ji da ita.Rayuwa tayi mata fari kal,ga soyayyar miji ga kuma na family dinsa,agaskia Suhaima ko kadan bata da damuwa.      Ana gobe zamu koma Zaria,Mahmood ya kaini gidajen 'yan'uwansa,gidan goggo Ladidi muka soma zuwa,sae gidan Anty Meema,Anty Labeeba,anty Khairat,duk kuma sun rasa inda zasu sakani don murnar ganina,kuma bamu tashiwa sae mun dire musu abubuwan alheri.Akan hanya Mahmood ya tsaya daidai wani saloon.     Yace"Zahmood oya fito muje awanke miki kai,idan yaso Afreen ta miki kitso don ta iya sosae.... " Banyi wata gaddama ba na fito don ni Kaina Ina buqatar awanke min kan don jinsa nake kamar yana wari mah sabida ruwan da yake sha kullum😁(Kun gane Ai).     Mun cimma mutane ba laifi acikin saloon din,Mahmood ya narka musu uban kudi don kawai asamu ayi min da sauri,su kuwa sae washe haqora suke don ganin sun yaqi naira da safiyar nan,nan da nan suka wanke min kan sannan aka shigar dani dryer,retouching kawai nayi.Ana gama min ban wani b'ata lokaci ba na fito na sameshi zaune awaje yana jirana.Murmushi ya sakar min tare da mik'ewa daga inda yake,ya tako ya sameni ah inda nake tsaye.    Yace"Zahmood har an gama? " "Yo! ba dole agama ba tunda ka narka musu uban kudi kamar baka san zafin nemansu ba? retouching kawai da zanyi shine ka tashi ka zabga musu uban kudi..... "     "Can do more than that for you my Zahmood,wallahi kinfi karfin komai awurina,kudi kuwa yanxun mah na fara bararwa indai akanki ne... " Sosae kalamansa sukai min dadi,ya kamo hannuna yana fadin"Zahmood tunanin meh kike haka?taho mu tafi.... "       Na soma k'ok'arin kwatar hannuna"Haba my dear meye haka? Sakar min hannu kaga fa mutane na kallonmu..... " "Yo! toni ina ruwana da mutanen? Inace ko halali ta na rik'e? Idan kuma basu yadda ba toh suzo su duba foreheads dinmu zasu ga an rubuta *'MAHMOOD WEDS FADIMA'*"    Sosae abin yaban dariya,har muka iso gidan Baba Mu'azzam fira muke tayi da kuma wasanni.Acan suma rasa inda zasu sakani sukai don murna,ji suke tamkar su hadiyeni don so,mahmood ya tafi yace anjima zai dawo ya daukeni.      Afreen ta yaryara min kananun kitso meh k'yau,tace"Anty Zahra jan lallinki mah harta soma gogewa bari na aiki Rafi'ah ta dauko mana meh lalli anan bayan layinmu.... " Nace"Afreen wlh dama kin basshi kada ya dawo ya zauna zaman jirana don kinsan lalli bata saurin bushewa... "    "A'ah wallahi anty sae fa an miki don yayana ya gani ya kusan zaucewa,in banda abinki mah ai lalli itama adoce ga 'ya mace,nifa wlh mijin da xan aura idan har baya son lalli da k'amshi tofa bazan aureshi ba.... "    Da mamaki nace"Akan lallin?" "Anty naki wasane wlh....... " Ta kwalawa Rafi'ah k'ira tazo,ta aiketa gidan meh lallin,ba'a wani jima ba sae gashi sun dawo da meh lallin,zuwansu yayi daidai da gama kitsonmu.Aka zana min jan lalli meh k'yau,abinka da farar mace sae ya zauna das ajikina,abinci mah abaki Afreen tayi ta bani.Bayan an gama ta biya kudin lallin,inata cewa ta basshi zan biya amma taki.Kai agaskia nide ranar naga gata awurin wa'ennan bayin Allahn.Sae bayan sallar hudu Mahmood ya dawo daukata,yana ganina ya soma cewa"wowww! Afreen wlh nasan aikinki ne wannan,ngd sosae kin fitar min da amarya,yanxu ni wacce irin k'yautace zan maki daze nuna lallai naji dadin wannan gyaran.....?"    "Yanzu brother shikenan donna gyara anty Zahra shine sae an bani wata k'yauta?nasan da'ace Khairat ce ko Labeeba bazaka yi musu wannan maganar ba,don Allah ka bari bannaso,idan kana hakan sae nayi ta ganin kamar baka daukemu daya ba kamar yadda mu muka daukeku.... " Ahankali yace"okay am sorry kanwas bazan kuma ba.... "    Sun cikani da sha tara ta arziki,sukace insha Allah suna nan xuwa Zaria ganin gida,Kaka rigima sae tsiya take ta min waina kuke sae gyaran jiki nake,adole wai ina son na fita matsayi agun megidan namu,dariya ni take taban ba.Maminsu Afreen ita tata k'yautar ta tsimi ce,tace kada na kuskura nayi wasa da amfani da ita don mace sae da gyara.Akunyace na k'arba ina mata godia.     Amota kuwa Mahmood kamar ze hadiyeni don sha'awar lallina,yana tuki amma rabin hankalinsa na kaina ne,ya jawoni yana meh cusa kansa ajikina yana shak'ar kamshin jikina,hadda lallin kafata dana hannayena ya hau shafawa,ah rud'e nace"Haba dearnah tuki fa kake,pls concentrate on it.... "     "Ai ke dince Zahra kike nemar zautani da wannan adon taki,agaskia yau sai kwalliya ta biya kudin sabulu.... " ya kashe min ido daya,ni kuwa na gane nufinsa don haka sae nayi rau-rau da idanu kamar xan saki kuka,ganin hakan ya sakashi sakin dariya yace"Wallahi ayau babu zancen daga kafa,na fayi haquri kwana kusan uku kenan na zuba miki idanuwa ina kallonki amma yau babu daga kafa...... "    Tuni na sakar masa kukan shagwab'a,ya shiga lallashina har muka karaso Family house.Bansan meyasa nake jin faduwar gaba ba idan har akan komai daya shafi su hajiyar Mahmood ne,lfy lau muka baro gidan Baba Mu'azzam,banji wani faduwar gaba ba sanda mukaje amma gidansu Momi saina tsinci kaina da jin tsananin faduwar gaba.Kila kuma don wannan zuwan shine karona na biyu shiyasa.     Mahmood ya lura da yadda yanayina ya sauya,yace"Zahmood pls cool down,Momi has totally changed wlh believe me babu abinda Zata miki kinji matar Mahmood? " kai kawai na daga masa.      Ah main falon gidan muka tarar da Hanan da Usee suna hira.Muna hada idanuwa da ita sae naji gabana ya tsananta bugawa,ji nayi kamar Mubarak dinne nayi ido hudu dashi. "Oyoyo matar Yaya.... " Usee ya fada tare da mik'ewa,awasance Mahmood yace"Dakata malam ince dai ba shirin rungumar min mata kake ba? "    Dariya muka sakar,kafin Usee yayi magana na karba"Toh idan mah yayi haramun ne?shima din mijina ne fa... "     "Yauwa gaya masa matar Yaya.... " Tuni muka ga Mahmood ya hade rai sosae kamar be taba dariya ba wanda hakan ya bani tsoro har naji ina meh nadamar abinda na fada.    Yace"pls ki dena min irin wannan wasar bana so... " kan nayi magana ya shige dakin Momi.     Usee yace"Matar Yaya haquri zakiyi ki kuma dunga kula sosae don Yayah akwai zazzafar kishi akan duk wani abinda yake so..... " Nide jinsa kawai nake amma hankalina atashe yake na ganin na b'ata ran mijina.Tunawa nayi bamu gaisa da Hanan ba,juyowar da zanyi kawai naga inda take zaune wayam! bata awurin kuma.     Usee yace"Haquri zakiyi don dole daga ke har Yayah ku fuskanci hakan daga gareta,ita wai adole taya mijinta kishinki take..... " Murmushi kawai nayi nace"Ina Jasmin dita?" "Ina tsammanin bacci take.... " "Don Allah yi maza ka tadata baccin yamma Sam babu k'yau kada kanta yazo yana mata ciwo..... "     Murmushi yayi yace"An gama matar Yayah... " ya nufi wani daki can daban. Saukar da ajiyar xuciyata yayi daidai da fitowar Momi da Mahmood.    Da fara'arta tace"A'ah 'yata kune tafe da yamman nan? Sannu da xuwa... " Har kasa na russuna ina gaidata cike da kunya.Mahmood fuskarsa babu yabo ba fallasa yace"Hajiyata zan dawo na dauketa anjima kadan.... " kan tayi magana yayi gaba abinsa ba tare da ya sake kallon inda nake ba.     Axuciyata nace"Ashe haka Engr. yake da saurin daukar zafi akan abu?lallai kuwa ashe ina da aiki sosae agabana..... "         Acan daki kuwa rigima ce ta kaure tsakanin Usee da kuma Hanan,ta jiyo zancensu da Fadima afalo don lab'e tayi musu.Ta hanashi tada mata 'ya. Yace"Hauwa wai na tambayeki man? Yaushe kika fitsare kika koma haka ne?taurin kai agidan nan? Toh Wallahi baki Isa ba don Sam wannan dabi'ar ba tarbiyyar gidanmu bace,an baki haquri akan ki yadda da kaddara amma dayake ke din sokuwace marasa kishin mijinta dole kiki sauraran kowa.....    Da karfi tace"Usman ka fita daga cikin idona,Ai dama dole ka fadi hakan tunda kun hade kai wuri guda,kun nuna sam abinda Yah Mahmo yayi ba kuskure bane tunda ai shi cikinku daya dashi,ni kuwa nawa mijin tunda ba cikinku daya dashi ba ai dole ku nuna halin ko in kula akansa........ " Dariya yayi yace"Jibi inda wawiyar ta bullo kuma?"    Ya tamke fuska yace"Kuma yau ya zamo rana ta k'arshe agareki da har zaki sake daga min murya,don kina auran yayana bashi ze saka ki sakani agaba kina min fada kamar wani danki ba,ni dinma ba tsaranki bane,daga Khairat har Labeeba babu tsaranki acikinsu balle ni,don haka take note,idan kunni yaji toh gangar jiki ya tsira,idan kuma kikace zaki cigaba da min rashin kunya,toh kuwa watarana rufe ido zanyi,xan manta Cewar ke din matar yayana ce na baki kashi sosae,idan yaso zumuncinmu dashi ya tarwatse akanki..... Yarki kuma don Allah kada ki bari atasheta idan har don kada su gaisa da Fadimar ne,don Allah na rokeki ki dunga hada mata da sleeping pills aduk sanda kika ga ko kika ji Anty Zahra zato zo,wawiyar banza kawai..... "    Axuciye ya juya ze fita sae kuma yaci k'aro da Momi wacce hayaniyarsu ce ta janyo hankalinta,rab'awa ta gefenta yayi ya fice.       Yazo ze fice daga falon gabaki daya don har yama manta da wata Fadimar don tsananin b'acin rai. "Kanin miji haquri zamuyi duka kamar yadda ka fada dole ne duk mu fuskanci hakan daga garesu har mijin nata.... "    Allah sarki Usee sam be iya mah fushi ba arayuwarsa,duk cikinsu bayan maryam,shine na biyunsu ah haquri,komai ake mishi shanyewa yake,sam be iya maidawa babba magana ba,shiyasa abin na Hanan ya bashi haushi sosae. Murmushi ya sakar mata"Babu damuwa matar Yayah... "    "Toh ina kuma zaka bayan Muna hira meh dadi? " "Tsiren bakin titi zan siyowa amaryar tawa... " kafin nayi magana ya fice.Usee kenan sam bashi da matsala na ayyana hakan araina.     (U guys shld help ooo,am alrdy crushing on *'Dan rakiyar maza😁'*    Acan daki kuwa,Momi tas-tas tayiwa Hanan sannan ta fito don abin nata yakai mata wuya matuka,tayi lallashin,ta kuma nuna mata cewar tun fi'azal haka Allah ya rubuta cewar Fadimar matar Mahmood ce ba Mubarak ba,amma duk nasihun sun tashi abanza,shiyasa ta mata wankin babban riga.Babu abinda take illa kuka.Ita ba auran Fadima da Mahmood ne take jin haushi ba,A'ah ita damuwarta anan shine farin cikin mijinta da ake neman ruguzawa,bata burin ace yau mijinta ya shiga cikin wani mayuwacin hali akan Fadima,Zata cigaba da yi masa addu'ar Allah yasa ya haqura ya rungumi destiny dinsa,Allah ya sanyaya masa xuciya yaji kawai Fadimar ta fice aransa,wannan shine addu'arta akullum tun ranar data sami labarin auransu.    Kukanta shine ya tashi Jasmin,sae mutsissike idanuwa take don tabbatar da lallai kuka taga momin tata keyi.Ahankali ta saukar da kafafu daga saman gado,ta isa ga Mominta tace"Momina meya sameki kike kuka?kode kewar daddy kike ji ne? "    Uwar bata tankata ba sae aikin rera kukanta take ahankali,ganin hakan ya saka ta fice daga dakin xuwa falo,ta hango Usee da Fadima na cin tsirensu ah plate daya.Momi kuwa ta koma daki abinta bayan ta baiwa Fadima haquri akan cin fuskar da Hanan ta mata.   Usee na ganinta yace"Uwar taki taga damar kyaleki ki fito? " bata ma san yanayi ba,illa kurawa Fadima idanuwa da tayi tana meh son tunano inda ta taba ganinta.     "Jasmin taho nice wannan antin meh k'yau wacce har kike ta kokarin samo bulala azane ni rannan kin tuna? " Yaro baya mantuwa,ai kuwa ta tunata,da gudu taje ta rungumeta tana cewa"Anty meh k'yau nayi kewarki sosae,kullum idan kuna waya da abba nace ya bani sai yaki...."    Usee yace"Toh ai yanxu gashi ta dawo kusa dake,zaki gaji da ganinta har ki ture idan har uwarki ta yarda,yanxu anty meh k'yau matar daddynki Mahmood ce.... " Cike da murna tace"Laaah! anty da gaske?zaki Haifa min cousins kamarsu Ablan mum meema? "    Sosae maganarta ya bani kunya,lallai Jasmin akwai surutu,sae da Momi ta fito ta tsawatar mata sannan ta nutsu,na umarceta data zauna muci tsiren tare. Usee ya tsura mata idanuwa yace"Wai har bakin nan yasan wani abu waishi cousin,sae shegen surutun tsiya..... "    Dariya muka fashe dashi daga ni har momin,ita kuwa Jasmin turo baki gaba tayi alamun shagwaba.Muna haka ne fa sae ga uban gayyar yayi sallama ya shigo.Dago kai nayi na xuba masa ido,wani mugun kallo naga ya watso min,da sauri na sadda kai kasa xuciyata na cigaba da bugawa da sauri da sauri.Jasmin ce taje ta rungumeshi tana masa oyoyo.     Umma ita kuwa k'yautar turaren wuta kala-kala ta bani,sae kuma turamen zannuwa masu tsada biyu da leshi itama meh tsada,wai gudummawarta kenan agareni,ba yawa,sosae nayi mata godia,ta tabbatar min da cewar insha Allahu suna nan xuwa Susan gidanmu na can Zaria,wai adalilina Zata zo tasan inda dan nata ke zaune.      Haka muka baro gidan,ya tsaya awata eatery yayi mana take away,har muka iso gidan babu maganar data shiga tsakanina dashi,abincin mah ayau kowa ciyar da kansa yayi amma de ah plate daya mukaci,wanka mah yau daban daban akayi,da muka zo kwanciya bacci sae na kasa haquri ganin ya juya min baya.Mirginowa nayi tare da rungume bayansa,kana na fashe da kuka nace"Haba mijina wai har yanxu fushin kake dani?don Allah ka sassauta min walhi xuciyata bazata iya daukar wannan hukuncin ba,duk wani dak'ika dake tafiya tare suke wucewa da tsananin son da nake maka,pls my jannah don't turn ur back on me,Wallahi Zahmood bazata iya rayuwa ba tare da ganin walwalarka da kuma kulawarka agareta ba...... "     Wani sassanyar ajiyar xuciya ya sauke,yana meh jin wani irin mugun sonta da kuma qaunarta na kara shigar xuciyarsa dakyau.Ahankali ya juyo gareta har suna hada numfashi don sosae tsinin hancinsa ya manne da tata hancin. Yace"Zahmood abinda nake son ki sani shine,ni mutum ne meh zazzafar kishi akan duk wani abinda nakeso,nasan Usman kanina ne amma sam banso kikayi maganar runguma agabana ba,haka kuma banso ganinki kina cin abu ah plate daya dashi ba,sae naji haushinku duka alokacin,amma yanxu tunda kin gane kuskurenki sae ki kiyaye gaba.... "    "Dear nah bazan sake ba Wallahi... " Murmushi yayi yace"Yauwah dats my baby,I so much love you Zahmood.... "     Daga nan labarin ya soma sauya zani,ya cika alqawarinsa don seda kwalliya ta biya kudin sabulu kamar yadda ya fada.      *** Washeqari qarfe goma tayi mana ah garin Zaria.tsarin gidana yayi min ba kadan ba,gidan de gata madaidaiciya amma se shegen k'yau.Yace na shirya muje gidanmu.Har tsalle saida na doka don murna.Gidansu Ash muka soma zuwa,ba karamin murna tayi da ganina ba,donshi awaje ya tsaya ni kuma na shiga ciki.     Tace"Fateenah kin gan yadda kika sauya kuwa?dama can ke meh k'yan ce sae kuma gashi kin kara akan nada,har wani mazaunai kika ajje fa,lallai agaida wannan Mahmood din agaskia yana kular mana dake yadda ya kamata,Masha Allah aure akwai dadi Muma Allah ya nuna mana tamu da Bash Dina.... "    Dundu na sakar mata abaya nace"Mara kunya kawai,ni tashi muje ki min rakiya kada ya gaji da jirana don har gida zamu.... " Muka fito nayiwa Maminta sallama tana ta shi min albarqa ina amsawa.     "Fateenah fatarmu de ayanxu Allah yasa Mubeen ya karbi kaddararsa..... " ta fadi hakan sanda muka fito daga cikin gidan. Ahankali nace"Ameen fa Sahibata.... "     Sun gaisa sosae da Mahmood dina,tace"Yallabai ngd kwarai da gaske gaskia aikinka na kyau don ga zahiri nan na gani ajikin Fateenah.... " Murmushi kawai mukayi daga ni har shi.Har gidansu Suhaima saida mukaje,muka tarar da Leedar agida,rasa inda Suhaima Zata sakani tayi don murna,shi kuwa Leedar wani kunyata yake ji,na nuna masa wlh babu komai don yanxu ni ina son mijina,har cikin gidan muka shiga muka gaida surukanta,suma din sun sanya mana albarqa sosai.Itama din Suhaimar irin Zancen Ash tamin wato Allah yasa idan Mubarak ya dawo ya karbi kaddararsa.     Daga k'arshe muka sauka can gidanmu,Umma na ganina tace"Saukar yaushe? "        Nace"safiyar yau dinnan wlh... " "Kedai wlh sam baki da hankali 'yar Kareematu,fisabilillahi yanxu sae da kika tasa bawan Allah agaba ya kawoki ganin gida daga dawowarku yau yau? "       "Ummana nasan dama ke kadai ce bakiyi kewata ba... " bata tankani ba  illa juyawa da tayi tana k'arbawa Mahmood gaisuwa wanda sae faman dariya yaketa mana.Abba mah sosai yayi farin cikin ganinmu don gabaki daya suna lambun shaqatawar gidan ne,kannena mah kamar zasu kada ni don murnar ganina.Sae yamma Mahmood ya dawo daukata,Umma ta tambeyeni babu matsala ko? Nace mata lafiya lau muke zaune amma ban gaya mata cewar ai Mahmood dan'uwan Mubarak bane balle na gaya mata abinda ke going,nafison Koda ace zasuji wani abin toh se bayan komai ya lafa idan Mubeen ya dawo.Abba yai mana nasihu sosai sannan muka baro gidan,Abba yace kannena nanan xuwa min weekend meh zuwa don washeqari Monday zamuyi resuming school.       *** wata irin shaquwace da kuma qaunar junanmu ya kara k'arfi atsakaninmu,rayuwar aure muke nida Mahmood abar kwatance da sha'awa.Tare muke tafiya makaranta kullum,idan na gama lectures sae naje office dinsa na jirashi har ya tashi.        ** **INA LABARIN MIJIN JIDDOH?**     Mubeen rayuwarsa yake babu yabo ba fallasa acan kasar Indiar,kwata-kwata mah ya dena nemar Mahmood awaya tunda idan ya k'ira baya dagawa,kuma ko kadan beyi gangancin gayawa wani nasa ba don baya son Mummy tasan cewar har yanxu yana tare da Fadima,amma kuma da Zarar ya dawo dole kuwa ta sani kuma dole ya auri Zahransa.Tunda Hanan taga Fadima amatsayin matar Mahmood,toh tun daga ranar duk wata walwalarta ta raqu wanda har hakan yasa Mubarak ya Dago cewar lallai matar tasa bata lafiya.Juyin duniyar nan yayi da ita akan ta fada masa abinda ke damunta amma se tace masa babu komai wallahi.Hakan ya kara sakashi cikin damuwa,ga rashin ji daga Zahransa,sannan yanxu kuma ga damuwar Hanan dinsa,duk yabi ya zama wani iri dashi don babu wani kwanciyar hankali atare dashi,abinda yaje yi mah sam baya wani concentrating akai,ganin hakan ya sanya abokan aikinsa k'iran CMD suka gaya masa halin da Mubarak din ke ciki tun ranar da suka sauka k'asar India.Dr.Shamsu sam beji dadin wannan al'amarin ba,aganinsa akan Hanan ne Mubeen din ya shiga cikin wannan damuwar,ya k'ira yace masa yana gama first 3months din kawai ya dawo gida,Mubeen ba karamin murna yayi da hakan ba,se yaki gayawa kowa nasa randa ze dawo.Tun asannan ne ya soma k'irgen ranakun daya rage masa ah Indiar.Ayanxu haka sati guda cur! kawai ya rage masa ya dawo.        **** watarana bayan mun gama morning lectures,sae kawai naji ina jin bak'on al'amari ajikina,zazzabi meh k'arfin gaske naji yana nemar rufeni,nayiwa Ash sallama na nufi office din Mahmood.Yana ganina ya taso arud'e yana fadin"My Zahmood yaya dai? Meya sameki?"   Amai shine ya biyo bayan tambayoyinsa,amai nake kamar zan amayo hanjin cikina,duk yabi ya rud'e.Students din da suke cikin office din sae ce min suke "Sorry ma,it shall be well with you.... "      Saida Mahmood ya wanke min fuska,wani student ya taimaka yayi clearing inda nayi amai.Ya daukeni kamar wata 'yar baby yana fadin"Dolene muje asibiti Zahmood jikinki yayi zafi sosai.... " cikin tashin hankali ya fice dani ahannunsa,ni kuwa babu damar kwatar kaina don gabaki daya jikina ya mutu.Ya umarce wani acikin students din daya rufe masa office,ya rufe ya mik'a masa makullan.    Yace dasu"Am sorry for the inconvenience..... Wen I get back I will attend to u all properly,buh for now I hav to take care of my wife... " . yayi gaba da sauri yana fadin"My Zahmood sannu kinji insha Allah it shall be well with you.Mutane kuwa sae binsu ake da kallo cike da shaawar wannan soyayyar tasu.     Babu bata lokaci ya Isa ga motarsa ya fice daga makarantar aguje,ahankali na furta"Dear nah I think am carrying ur baby........ " Cike da murna yace"Wayyyo Allah Zahmood are you serious? Da gaske kike na kusa zama uba? Yanxu nima an kusa kirana da baba kenan? "    Juyawa nayi ina kallon yadda yake zuba sambatu,hawaye na gangarowa Saman kuncinsa,abin gwanin ban tausayi,sae nima naji kawai hawaye ya ziraro min tare da jin sonsa na qaruwa acikin xuciyata. Asibitin mah haka aka kara tabbatar masa da lallai ina dauke da juna biyu na tsawon sati uku.Har k'yauta sae da Mahmood ya baiwa likita na wannan albishir daya masa.      Wani sabon tattalina yake daga ni har babyn tamu,na musamman ya dauki hutun sati guda yana kula dani,don rashin kunya Mahmood har kiran yan'uwansa yayi akan an samu karuwa,babu wanda yakai Momi murnar samun wannan karuwar,alast ta kusa ganin jikokinta daga bangaren babban danta.Bayan kwana biyu kuwa sae ga mutan kano anzo dubiyata hadda su 'yan gidan Baba mu'azzam,har gidanmu saida Mahmood yakaisu hadda Hajiyarsa don sada zumunci,ita kuwa Ummana Sau daya tazo da kannena,Suhaima mah haka,ita kuwa Ash tayi zuwa har sau hudu kenan.Aranar suka koma Kano.bayan sati guda na ware,na danji dan dama-dama har na soma zuwa makaranta,amma ko kadan Mahmood baya bari ina aiki,duk abinda nakeso shike tashiwa ya dauko min ita,wai shi baya son na wahalar masa da babynsa,nace ai kuwa idan baya bari ina dan motsa jiki toh kuwa haihuwar tana iya zuwar min da dan gaddama,shine fa yadan soma barina ina dan taba wani aikin amma ba sosai ba.       **** **BAYAN SATI GUDA**    Akace rana bata k'arya sede uwar diya taji kunya,sannu-sannu bata hana zuwa sede adade ba'a kai ba.Ayau misalin qarfe biyu Mubarak ya diro Nigeria,ta Lagos suka sauka,suka sake shiga jirgin da ze saukesu akano.Bayan 1hr 40mins suka iso Kano ta dabo tumbin giya.Be Sanar da kowa batun dawowarsa ba balle yasa ran za'a taho daukarsa,babu b'ata lokaci yayi shatar adaidaita.Har kofar gidan aka kawoshi.     Momi itace wacce ya soma hangowa ah tsakar gidan tana baiwa kajin da take kiwo abincinsu. "Assalamu alaykum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu..." Ya fadi hakan alokacin daya shigo cikin gidan sosai. Momi ce ta amsa sallamar tare da dago kanta,afirgice ta jefar da kwanon abincin kajin dake hannunta,tace"Wah nake gani haka agabana kamar d'ana Mubarak? "    Murmushin k'arfin halin ya sakar mata kana yace"Abin mamaki yanxu Momina dan naki ne kika kasa shaidawa kai tsaye?ko don na k'ara baki da kuma 'yar ramar danayi ne? " Da rawar murya tace"Eh fah hakane kam,ashe ba cewa kayi sae bayan watanni shidda zaka dawo ba? Ko kuwa bakada lafiya ne shine ka tashi ka kamo hanya ba tare da saninmu ba? "      "Momi hankalina zefi kwanciya idan ina kusa da Hauwa'u,idan ina ganinta zanfi jindadi,dama ko kadan banso wannan tafiyar ba sabida irin lalurarta ta laulayi meh tsanani,amma sabida matsa min da akayi shiyasa na tafi,koda naje can hankalina yaki kwanciya akanta shine oganmu yace kawai na dawo...... " Cike da fargaba Momi tace"Ai kuwa cikin nata da sauki sosae don bayan kwana bibbiyu Dr.Basira ke xuwa dubata,kuma ta tabbatar mana da cewar baby da mamanta lfy qalau suke,kuma she has about 70% assurance na cewar wannan k'aron da kanta zata haihu basai an barkata ba,eyyah Mubarak ai daka tsaya abinka ka gama abinda yakaika....... "    Murmushi kawai yayi yace"Bari na shiga ciki Momi... " kafin ta k'ara magana ya shige ciki jaye da trolley dinsa.Dif! duk wani network meh aiki ajikin Momi ya tsaya cak! ya dena aiki.Tana nan tsaya se tunane-tunane take,ahakan Usee ya shigo gidan yana cire earpiece akunnensa,cike da tashin hankali yace"Momi daga nesa na hango wani ya sauka daga cikin adaidaita har ya shigo cikin gidan nan kamar Yah Mubarak..... "     "Shine ba wai kama ba...... " Salati Usee ya saki tare da aza hannu duka biyun aka kamar wanda aka yiwa mutuwa.Wani irin zabura Momi tayi kamar wacce aka jonawa electric shock,tayi gaba da sauri sauri tana cewa"Usee taimaka ka kwashe min abincin kajin nan dana zubar,bari na kira Abbanku Mu'azzamu na fada masa cewar ya dawo....... "    "Toh" kawai ya iya cewa.Ta shige ciki,ada dakinta take da niyyar shiga don dauko wayarta amma se kuma ta Samu kanta da son yiwa su Mubarak lab'e.Da hanzari kuwa tayi dakin da aka sauki Hanan,ajikin kofar dakin ta lab'e tana sauraron maganarsu.    Kuka ta jiwo Hanan tana yi tare da rokansa"Haba mijin Hauwa'u yanxu har xuwa wannan lokacin baka cire Zahra aranka ba?aganina ya kamata ka shafeta daga cikin rayuwarka don I think Zahra ta maka nisa ba kadan ba...... " Wata uban tsawa ya doka mata,yace"Shut up! Jiddah..... Yanxu har ke kin isa kice na cire Zahra araina? Kin kuwa san yadda nake sonta kuwa?toh ayau ina son ki san cewar duk wani numfashi da nake shak'a tare nake shak'arsa da soyayyarta,bana tsammanin ko Momi mah wannan k'aron zata iya dakatar dani daga aurenta...."     Ya sassauta murya yace"Haba jiddan Mubarak ke kanki kin san nayi kokari sosae ba kadan ba da har nakai tsawon lokacin nan ah India ba tare da jin halin da Zahrata ke ciki ba,kullum idan munyi waya dake sae na gaya miki cewar har yanxu banji daga gareta ba,shine yanxu kike cewa na haqura da ita? Never! Wallahi,tashi ki dauko min makullin motata na kama hanyar Zaria yanxun nan kuwa...... "      "Haba Mubarak ko hutawa bakayi ba balle kasa koda ruwa ne acikinka shine kake tunanin kama hanyar Zaria ayanxu?ka bari ka huta mana..... "    Wani uban tsawa ya doka mata wanda hakan ba karamin firgitata yayi ba musamman mah Momi wacce har saida ta dan buge da k'ofa don tsananin firgici😁 Xuciyarsa ce ta bashi cewar kamar ana musu lab'e don haka da sauri ya nufi kofar yana fadin"Uban waye ne ke mana lab'e anan?" Azatonsa Usee ne don beyi tsammanin cewar Momi bace.     Ita kuwa Momi jin abinda ya fada ya sanyata hanzarin rugawa da gudu xuwa falo xuciyarta kamar zata fad'o waje don tsananin fargaba,tana iya cewa tunda take aduniyarta bata tab'a shiga irin wannan tashin hankalin ba kamar na yau. (Hahahah! Major general of soldiers ya dawo).😀😂 Ita kuwa Hanan har fitsari saida ta saki don tsananin tsoro.Koda ya lek'a sae yaga wayam!babu kowa,xuwa yayi ya lek'a falon,sae yayi ido hudu da Momi wacce sae faman sauke ajiyar xuciya take,jikinsa ne yayi sanyi qalau kamar kankara don jikinsa ya bashi cewar itace ta musu lab'en.       "Mubarak zoka zauna muyi magana..... " Gabansa ne yaji ya bada rass!,wato kenan Momi taji xantukansa da Hanan kenan?toh taji din mana shide walhi bata isa ta hana masa auran Zahra ba don ba itace ta haifeshi ba balle tace idan tayi masa baki yana iya kamashi.(Anya mubarak? Matar data raineka tsakaninta da Allah ne kake tunanin idan ta maka baki bazai kamaka ba? Ina ganin kawai ka zauna ka sake tunani).      "Ina son kadan bani aron juz 1hr acikin lokacinka so nake muyi magana.... " ta fadi da rawar murya don har ga Allah tsoron Mubarak din ma take. Arayuwarsa ta duniya momi ita kadai ce macen da baze ya musa mata magana ba,amma akan Zahra wannan k'aron sede ta nemi wani Mubarak din amma bashi ba.    "Toh" kawai ya iya cewa don kwarai yana son yaji ta bakinta kafin ya amayar da tasa.Samin gu yayi ya zauna,se alokacin Usee ya shigo suka gaisa da yayan nasa,har yake tambayarsa ya hanya? Ba yabo ba fallasa ya amsa masa. Hanan kuwa ta fito sae kuka take rik'e da key motarsa ahannunta,wuri guda ta tsaya cak! tama kasa karasa gareshi sae shesshek'a take,shi kuwa kallo daya yayi mata kana ya dauke kansa daga gareta.    Momi ce tayi mata ido,ai kuwa da hanzari ta shiga cikin taitayinta tare da samin hannun wata kujera ta zauna.Momi ta shige dakinta,da rawar hannu ta lalubo wayarta ta latso Baba Mu'azzam take gaya masa cewar ai Mubarak ya dawo,yace gashi nan tafe yanxun nan kuwa kada akuskura abari Mubarak din ya fita,ta de amsa masa da "insha Allahu" ne,don idan ya nemi fitar tasan ko ita ayanxu bata isa ta hana masa fita ba yadda idanuwansa suka rufe da tashin hankalin nan.Ta latso su Mahmood shima ta gaya masa,yace gasu nan tafe suma,duk 'ya'yanta mata saida ta kirasu suma Cike da tashin hankali sukace gasu nan tafe.Tace kada asake ataho da yara abarsu ahannun masu aikin gida,tama gode Jasmin na gidan Meema don haka komai zaizo musu da dan dama dama don bata qaunar yara su gigice da wannan tashin hankalin da suke shirin fuskata............... 📝    A/N Tofa! bilhaqqi yau ake yinta,fire on the mountain kadan-kadan,ku agaza musu da taimakon gaggawa ta yan fire service 😁     Last episode coming soon ending of diz week insha Allah!! Longest chapter so far!!        *HAFNAN CE💞*           *💘SHIN SO DAYA NE?💝* *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍* *{Onward together}* *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔ *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA* *WATPADD:HAFNANCY💞* *IG:Hafsy___mustee* ✨✨ *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE* _please kindly touch the little star to vote me before you start reading_ 🌼BABI NA TAKWAS🌼 *Page 21-23* Kaina naji yana wani irin mugun sara min,babu shiri na tsaida kukana completely tamk'ar anyi ruwa an dauke.Daukar k'aramar filon wata two seater nayi,ahankali na sauko na kwanta ah k'asa tare da yin matashi da filon.Duk tunane-tunanen Mahmood ne yabi ya addabi xuciyata da kuma tsananin son sanin halin da yake ciki ahalin yanxu. Ban wani jima da kwanciya ba wani nannauyar bacci yayi awon gaba dani. _*"Fadima Zahra'u kinki ki rungumi kaddararki amatsayinki ta 'ya musulma kamar yadda aka koyar daku karban kaddara mai kyau ko mara kyau,amma ke kinki karbar taki kaddarar,nayi miki baiwa da kuma ni'imar da bah kowacce 'ya macece zata sami hakan ba,amma ke kin butulce min,kinci mutuncin mijinki tare da yi masa illa bayan kin san cewa babu abinda yakai Miji daraja agun duk wata d'iya mace,d'a namiji shine shugaba kuma shine jagoranki xuwa aljanna idan har yaso,adalilin sab'a masa da kikayi ya sanya na yanke miki hukuncin shiga wutar jahannama.......... "*_ Ah firgice na farka daga wannan mummunan mafarki tare da fashewa da kuka,atsoroce nake fadin"Yah Allah wallahi na tuba ka yafemin,Wlhy na k'arbi kaddarata,na haqura xan xauna da mijina,zamuyi zaman lafiya kuma xanyi masa biyayya har xuwa k'arshen rayuwata dashi aduniya,bazan sake ci masa mutunci ko kuma na sab'a masa ba,Yah Allah ka yafe min *'INA SON MIJINA'* Ji nayi an d'an tab'oni ta baya,ai kuwa da k'arfi na sake ihu tare da waigowa babu b'ata lokaci,jikina sae karkarwa yake tamk'ar meh jin sanyi.Mahmood ne,banji shigowarsa ba sae de kawai naji saukar hannunsa ajikina.Shi kuwa ya dawo alokacin tana baccin mamakin nata,kafin yakai ga zama akan kujera yaji kawai ta tashi afirgice tana wannan sambatun nata,atake ya gane cewar mummunar mafarki tayi,kuma ze iya bugar k'irji yace bilhaqqi yaji dadin wannan mafarkin nata don kamar hakan ya sanya ta haqura ta rungumi *'MIJIN KADDARARTA'*. "Haba my baby doll,da salati da kuma addu'a abaki ya kamata ki tashi dashi ba wai da ihu ba..... " ya fadi hakan ahankali kamar ze had'iyeta don so. Sae ayanxu na tuna cewar salati da kuma addu'a ya kamata ace nayi ba wai ihu da kuma sambatu ba.Shi ya soma karanto min addu'oi,yana yi ina k'arba masa kamar wata meh koyon k'aratu koh tilawa. Can hankalina ya dawo jikina,da hanzari na mik'e ina dubansa,cike da fuskar tausayi nace"Mahmood dina are you okay? Ka samu an wanke maka ciwon? " Na fadi hakan ina dube-duben kan nasa,ina neman inda naji masa raunin don harna manta wurin,fes! idanuwana suka sauka kan k'atoton plaster din da aka lik'a masa awajen. Wani d'an marayan kuka ne naji ya sub'uce min,hannu nakai na tab'a wurin,sannu ahankali na shiga shafa wajen,nace"Mijina don Allah ka yafe min hak'ika ko kadan ban k'yauta maka ba,amma ayanxu ina meh farin cikin shaida maka cewar Lallai na haqura xan xauna dakai amatsayin Mijina kuma ina sonka sosae Mahmudanah...... " Shi kuwa wani irin dadi ne yaji ya tsikareshi tun daga tsakiyar kansa har xuwa babbar yatsar kafarsa,he can't juz believe wai Fadima ta haqura kuma zata xauna dashi har xuwa k'arshen rayuwarsu kafin meh duka ya raba. Beyi wata-wata ba ya rungumota yana meh jin wani irin sabuwar soyayyarta na kai masa mugun cafka acikin xuciyarsa. Ahankali yace"Babyna da gaske kin haqura?da gaske kike kin k'arbeni amatsayin mijin aurenki?sannan kuma da gaske kike kin soma jin sona aranki? " Tsagaitar da kukana nayi,na koma yin 'yar shesshek'a,cike da sanyin murya nace"Yes!!! Mahmood wallahi xan xauna dakai dear nah ina qaunarka har cikin raina.... " Cike da farin ciki ya cikani yana kallona eyes into eyes,kafin yace"Kenan hakan na nufin u will surely make me to feel being loved once again? " Gyad'a kai nayi ina meh xubar da 'yan kwalla cike da jindadin ganin tsantsar farin cikin daya shiga. Yace"And will u be strong,bold & face any family problem dat will be coming soon? " Cike da fargaba na daure na amsa da"Yeah I promise to be strong & bold for you & I also promise to withstand any obstacles dat will come our way...." Banyi aune ba kawai naji ya sunkuceni,ya soma yawo dani acikin makeken falon cike da murnar jin kalaman da suka fito daga bakina. "Dear nah saukeni mana kada kasa mu fama ciwonka.... " na fadi hakan ashagwab'ance,k'ok'arin sauka nake don awuyansa ya daurani,sae ji nayi na dad'a k'ankame kafafuwana. Yace"Baby ki bari na saukeki da kaina kada ki fad'o ki min asarar wani abin..... " Dundu na kai masa ta baya,ya b'ank'are bayar,yace"ouhhh!! wallahi dundun ya shiga sosae kuma asannu zan rama idan kika manta..... " Be direni ako'ina ba sae awani dakin bacci.Yace"Oya matata taso muje mu dauro alwala mu gabatar da sallah don nuna godiyarmu ga Ubangiji daya nuna mana wannan ranar ta kasancewa ma'aurata,ina rok'an Allah daya sanya mana albarqarsa acikin wannan auran,ya kauda duk wata fitintinu,rigingimu da kuma bala'i acikin rayuwar auranmu,ak'arshe kuma Allah ya axurtamu da 'ya'ya na gari,mahaddatan alqur'ani meh girma,masu tsananin tausayin iyayensu da al'ummar musulmi gabaki d'aya....... " Ahankali nace"Ameen Mijina..... " na fadi hakan sanda nake sharce dan guntun hawayen daya xubo min saman kunci.Tashiwa nayi don cika umarninsa,amma kafin nan sae daya kaini dakina yace na soma yin wanka sannan na dauro alwala nazo na sameshi anashi dakin inda muka baro kenan.Shi da kansa ya zab'o min wata night gown meh k'yau daga cikin wata sif,ya watsa minsu saman gado,riga da wando ce.Sannan shi ya koma dakin nasa don wanka da daura alwala. Ban dau wani tsawon lokaci ba na cimmasa adakin baccin nasa.Shi ya jamu sallar,Muna sallamewa,ya daga hannuwa sama ya shiga kwararo addu'o'i babu gaggautawa da kuma yiwa Allah k'irari,ban tab'a sanin cewar ilimin arabi ya ratsa Mahmood haka ba sae yau.Yadda yake wani lank'wasa harshe yana baiwa kowacce harafi hakkinta mah wani abin birgewa da sha'awa ne. Can kuma naga ya d'an juyo tare da dafa kaina,ya shiga kwararo min addu'o'i tare da shi min albarka mara iyaka wanda hakan ya sanya har se dana d'an xubda kwalla tare da jin wani soyayyarsa na fizgata.Yayi mana addu'ar samun zamar lafiya tare da samun zuria d'ayyaba. Muna idawarwa naji wani sabon bacci yayi min sallama,ashe Mahmood na lure da yadda naketa gyangyad'i tun awajen sallah,yace"Babyna goan sleep naga tun awurin sallah kike ta gyangyad'i kamar wata kaza,oya you ghatta sleep... " Ya manna min wata peck agoshi wanda na jishi har cikin jinin jikina.Bed dinsa ya nuna min alamun anan xan kwanta,shi kuma naga ya dau pillow ya kwanta ya akasa.ba tare da wata gaddama ba na isa kan gadon na kwanta. "Goodnite my lovely Wife.... " na tsinkayo maganarsa. Dan murmusawa nayi nace"Nite too dear nah..... " _*wayyooo!! Haba Zahmood💞 ya naku first night din ya banbanta dana sauran ma'aurata?*_ ** Suhaima ita kuma bayan an kaita b'angarenta,Reedah ce ta xauna da ita suke ta hira awannan yinin ranar,sae wuraren karfe goma na dare tayi mata sallama ta tafi,Shima din uban gayyar ne ya k'irata awaya yake ce mata"Toh! auta akyalemun amarya hakan ta huta da surutunki,ki tafi bangaranku don ina nan tafe yanxu da abokaina xuwa ga amarya..... " Murmushi kawai tayi kana tace"kai big brother wai zumudin meh kake haka bayan from now on you have the whole moments to spend together with *'SuhaiLeedar'*?" "Ni dai na gaya maki Karki sake na iso na iskeki anan.... " ya fadi hakan in a playful manner. Haka Reedah tabar b'angaren Suhaima wacce dakyar ta barta ta tafi,wai hadda cewa ta kwana. Dariya sosae Reedah tayi tace"Iyyeh! ashe so kike Yah Haidar ya min dan iskan duka yau acikin gidan nan kenan sabida yadda mah naga yake rawar k'afa akanki,toh kuwa idan aka kuskura aka kawo masa wargi ze iya lallatsa mutum,am so sorry bestie kiyi haquri ki bari ku durje first night dinku don hakan shi ake k'ira da *'AURAN'*...... Bye gudnite..... " Tayi gaba tabar Suhaima da binta da kallo.Ansha barkwanci da wasanni daga angwaye,daga k'arshe sukayi musu addu'ar samun zaman lafiya da kuma samun zuri'a d'ayyaba,sannan sukayi musu sallama suka fito.Har wajen motocinsu Leedar ya rakosu yana dad'a musu godiya. Fresh ne ya jawoshi gefe bayan sauran duk sun shiga cikin motar,ya d'an daki kafadarsa yace"Shege abokina yau an zama babban mutum,dan iska kuma kabi yarinyar mutane asannu sabida yadda naga kake rawar kafa akanta kar ka...... " Dunkule hannu yayi ze kai masa dundu abaya,da sauri Fresh yayi wajen motarsu yana dariya,Leedar yace"Bakai wai dan iska ba? Dont worry zaka ci ubanka ne.... " Haka de aka rabu cike da farin ciki da wasanni.Shima juz lyk kamar yadda su Mahmood sukayi,haka suma din sukayi.Wato gabatar da sallah don nuna godiyarsu ga Allah da kuma addu'ar samun zaman lfy da zuria ta gari.Sae de su nasu kwanciyar ya banbanta,don tare suka kwanta,ni kuwa ganin lamarin nasu na nemar sauya zani ya saka nayi saurin barin dakin don kam naga kamar suna matuk'ar buqatar sirri. _*Nice one SuhaiLeedar💞... Asubahi ta gari....*_ *** *4:30am* _*"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha...."*_....... Wannan k'aron da salati na farka da ita bayan wani mummunar mafarkin danayi akan Suhaima da Leedar,wai jinns dinsu Rukky sun halak'asu kamar yadda suka dau alqawari. Kuka na fashe dashi wanda hakan ya sanya Mahmood farkawa agigice,ambaton sunan Allah ya soma yi kafin ya nufo inda nake,ya kunna dim light,haske yadan bayyana kadan adakin. "Baby doll wat happened? Mummunar mafarki kikai ko? " Agigice nace"Eh.... Dama.... " Da sauri ya katseni yace"No baby doll ba'a bada labarin mafarki,kawai addu'a ya kamata kiyi kinji ko? " Ahankali nace"okay nagode dear nah.... " addu'o'i na soma xubawa acikin xuciyata babu gaggautawa,ji nake kamar na latso su Leedar din amma kuma bana son Mahmood yasan halin da ake ciki. (Hahahah! Fadima ta sanya abin aranta ne shiyasa tayi mafarki da hakan! If not *'SuhaiLeedar'* nanan lafiya qalau,sharar baccinsu mah suke ahalin yanxu,shi Leedar dinma ya manta da batunsu don ya rik'e addu'a sosae). Daga ni har shi bamu sake komawa bacci ba,Muna nan xaune kamar wasu kurame har aka soma k'iraye-k'irayen sallar asubahi.Ya umarceni dana tashi mu gabatar da sallah.Koda muka idar mun dad'e zaune yana zuba mana addu'o'i,can muka shafa,komawa gado nayi na kwanta don wani bacci-bacci ke idanuwana.babu b'ata lokaci baccin yayi awon gaba dani. Mahmood kuwa sae daya dan karanci alqur'ani,shidda tana yi ya mik'e ya shiga kitchen don had'a musu abinda zasu ji.Arish ya soya musu da kwai,sannan yayi warming ragowar pizza din jiya da kuma garnished chicken.sae kuma ruwan zafin daya dafa ya zuba aflask wanda zasu sha shayi da ita. 6:58am ya kammala komai don ba wuya,still de magajiyar tana nan kwance tana sharar baccinta,kuma ko kadan baya da niyyar tashinta,hasalima wankansa ya shige. ** Khairat yar bala'i tun shidda da rabi ta iso family house,Labeeba kuwa sae 7:15,Anty Meema ita kuwa sae data b'ata musu lokaci sosae don sae takwas Saura ta iso gidan,Momi kamar zata kifeta da duka don haushi. Haka suka fito suka dunguma gidan Mahmood tare da taimakon Usee (usman) as the driver. (Hahaha! Inyi muku irinta momi,tace"*Dan rakiyar Maza"*😀. Hanan taso binsu amma se ta tuna cewar yau Dr.Basira zatazo dubata kuma da sassafe take dako sammako................ 📝 A/N *Ohh! My God!! Mahmood Nakowa kayi ne! Ka cika jarumin jarumai,rana daya,tashin farko Kasan yadda kayi ka cusawa Fadima sonka harta haqura ta xauna dakai,koda yake dama can ta soma sonka amma ita bata san da hakan bane.... Job Weldon to you M.Nakowa....First mission completed & succeeded,now let's watch & see if you will succeed in ur second mission (The family problem). Ohhh! My God! Nakowa's family are on their way..... Ghen!ghen!ghen!! Fire on the mountain🔥🔥🔥🔥🔥 *sorry guys nasan da yawanku sun aza ko awannan episode din za'ai bala'in,sorry dearies I want to follow each step one by one without skipping!! *HAFNAN CE💞* *💘SHIN SO DAYA NE?💝*        *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*        *WATPADD:HAFNANCY*        *IG:Hafsy__mustee*                      💥 *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*           🌼BABI NA UKU🌼 *Page 6-9*         "Mama bara naje nima na kimtsa kada su wuce wajen reception d'in nan bani..." acewar Anty Hajaar wacce tana gama fad'ar hakan ta mik'e tabar dakin xuwa sashin da aka saukesu. Kaka rigima ta rakata da "Toh! adawo lafiya Hajara,Allah sarki an girma ba'a san an girma ba,yanxu fisabilillahi taron k'ananun yara mah sae sunje.... Koda yake Allah ne ya kawo mu xamani..."     Ai dole ne Anty Hajar tama je wannan reception din ko don taje tayi ciye-ciye ta kuma nunawa duniya cewar ita din fah uwar amarya ce.Maminsu Hafeezah mah zataje don ita da Mahmood suna mugun d'asawa da k'yau. Ash ce xaune tare da Zuzu ah barandar sashin da aka saukesu.Hirar Khaleed Zuzu ke bata wanda ga dukkan alamu ya nuna cewar gayen ya gama tafiya da imaninta.Ita Ash din mah da akewa hirar amsawa kawai take da "uhmm" ko kuwa "a'ah",don kusan xan iya cewa gabaki daya hankalinta ya tafi ne ga su Fadima.Sae ayanxu ne take ganin wautarta na k'iran shi Mahmood d'in daya zo ya lallashi Fadimar bayan tasan muddin Fatin nata na had'a idanuwa dashi amatsayin mijin da aka aura mata,toh kuwa komai na iya k'wab'ewa,anything can happen!.     Oh! Allah!! akace dana sani yakan zo ne bayan ka aikata ba daidai bah,akan k'irashi da *'dana sani mara amfani'*,data sani kawai ta lallab'ata ta saka kayan don tasan Fatinta komin fad'arsu de tana jin maganarta,kuma tasan xata sauko ne har ta haqura taje reception din,amma da yake iyayi yayi mata yawa,kai tsaye ta k'ira Mahmood din da yaxo gareta,iyayinta ya janyo tana neman haifar da tashin hankali acikin jama'a wanda ta fison ace sae an kai Fadimar gidansa,asannan kowa ya kama gabansa kafin tasan wanene mijinta,tasan duk wani tashin hankali da ze biyo baya alokacin zai iya xuwa da sauki.Wurin reception mah ba lalle ne Fadimar ta gane Mahmood din ba tunda duk'ar da kai zatayi tayi,balle mah tasan halin Fadimar sarai da alkunya,zaiyi matuk'ar wuya ta masa kallon tsaf acikin jama'a.Koda ace tama gane shi,tasan Fadimar baxata tab'a kunyatar dashi idanuwan mutane ba har sae sun k'ebe.      Toh! yanxu gashi ta janyo k'ebewar tasu da wuri tun mutane basu gama watsewa ba,kuma tasan anything shitty can happen. Axuciyarta tace"Ohh! ni Ayshatu wat have I done? meya kaini k'iransa? "    Xuciyarta babu abinda yake yi illa bugawa da sauri da sauri,kasa kunnuwa tayi tana meh jiran ta jiyo hayaniyarsu Fadimar sannan tayi ciki wuf!.Zuzu de data ga sam hankalin Ash din baya gareta,sae kawai taja bakinta tayi shiru,ita Allah-Allah mah take su Fadimar suyi su gama soyayyarsu kamar yadda take tunani sannan ta shiga taje ta tsalawa Khaleed dinta kwalliya. Anty Hajaar ce tazo shiga sashin,da hanxari Ash ta mik'e tare da shan gabanta.      Wani irin kallon banza ta jefawa Ash din,kana tace"marasa kunya meye kuma haka? Ko de wata sabuwar salon rashin kunyarce ta motso miki shine hadda wani shan gabana?" Dan murmusawa kawai Ash tayi,kana tace"Yana de gab da motsowa.... So nake kawai nace miki ki d'an dakata,ango na ganawa da amaryarsa aciki........ "     Hab'a Anty Hajaar ta rik'e,kana tace"ikon Allah!... nide tunda na budi ido nayi wayau ban tab'a ganin rashin kunya da da'a irin wannan ba,Muido da wannan angon nata sam basu da alk'unya ko kadan musamman mah angon nata,ai sae ya bari iyayenta su tafi kafin ya shiga wurinta suyi shashancin nasu son ransu........ " Wani kallo ta watsawa Anty Hajaar,ta dubi inda Zuzu take taga mah sam hankalinta baya garesu,hasalima wayarta take daga can d'an nesa da inda suke tsaye.      Ahankali Ash tace"Dad'ina dake Anty akwai ki da iya jan k'aramar magana tayi tsayi da kuma janyowa kanki raini awajen kananan yara,ina ruwanki da koma meye ya shiga yi? Ina ce ko matarsa ce ba dadironsa ba? Don Allah Anty Hajaar ki dunga kama girmanki kada ya gama xubewa ah idanuwanmu mu yara..... " Tana gama fad'ar hakan ta koma mazauninta,sae duba agogo take awayarta,yanxu haka takwas ta wuce da mintuna goma,akalla Mahmood ya shafe kusan mintuna ashirin aciki yanxu.Ita kuwa Anty Hajaar jikinta ne yayi sanyi qalau don bata tab'a jin k'unyar kwab'o ba arayuwarta sae yau da Ash ta mata.Sae taga rashin dacewar maganar daya fito daga bakinta.Jan jikinta tayi xuwa ga wani k'aramar kujera ta tsakar gida ta xauna.(lol maganin irinku kenan Anty Hajaar... Ash kin biyani....)      *** Idanuwana dani k'aran kaina mun kasa gasgata cewar wai *'ENGR. MAHMOOD MUSTAPHA'* dan'uwan Mubarak ne tsaye agabana amatsayin *'MIJIN KADDARATA'*     Sake kai yatsu nayi ina murza idanuwana akaro na uku don tabbatarwa kaina cewar mafarki nake kuma wanda ke tsaye agabana ba 'ENGR.MAHMOOD' my brother inlaw bane.Harda mitsilin kaina nayi wai ko mafarki nake na farka,amma uban Zafin dana ji ne ya saka nasan ba mafarkin nake ba,this is reality!!!.    Da rawar murya nace"Don Allah meh kake yi anan?" Gaban Engr.ne ya buga wata irin ganga,fargaba da kuma tsoron actions din da Fadima xatayi taking duk ya cika masa xuciya fal! amma da yake shi din namijin duniya ne,sae be bari ta gano weakness dinsa ba.      Fuskar mamaki ya shimfid'a mata,kana yace"Ban gane meh nakeyi anan ba? all what I know is dat wajen matata nazo...... "      "Wacece kuma matar taka? " na fadi hakan sanda naji xuciyata na wani min mugun zogi.   "Of cours! Fadima Sa'ad Mainasara amaryar Engr.Mahmood Mustapha...... " Da hanzari na katseshi"k'arya kake mak'aryacin banza,mak'aryacin wofi,you can never be my husband ko amafarki,ni bah kai na aura ba,ni *'MAHMOOD NAKOWA'* na aura not *'ENGR.MAHMOOD MUSTAPHA'* because am very pretty sure dat brother inlaw bazaka taba cin amanar d'an'uwanka ba,bazaka tab'a yaudararsa ba,haka kuma nasan bazaka tab'a bin bayansa ka k'wace masa ni ba...... "     Wani irin mugun d'aci ne Mahmood keji aransa na jin irin wannan kalaman da Fadima take jefarsa dashi,yab'onsa take ko kuwa maganace mara dad'i take jefa masa?   sassauta muryata nayi,da rawar murya meh had'e da kuka na cigaba da magana"pls brother inlaw meya kawoka gidan surukaina?ko kuwa kaima kana cikin abokan ango ne? kuma ina mijina yake da har ya barka ka shigo har inda matarsa take?okay yanxu na gane,ka samu labarin cewar nayi aure shine kazo kaci min mutunci don na yaudari d'an'uwanka ban aureshi ba..... "    Had'a hannuwa wuri guda nayi kana nace"pls na rokeku don Allah kuyi haquri ba laifina bane nima din biyayya kurum nayi,don Allah kacewa d'an'uwan naka daya gafarceni ba laifina bane,albarqan iyayena nake nema shiyasa na amince da xab'insu.... Pls brother inlaw ka tafi kada mijina ko wani ya shigo ya ganka anan....... " Wasu 'yan kwalla ne yaji sun ziraro masa saman kunci na tausayin kansu daga shi har Fadimar,da hanzari ya juya ya fice daga dakin kamar yadda ta buqata.k'aron farko daya soma ganin rashin dacewar auren Fadima da yayi gashi yanxu tana denying dinsa akan bashi ne wanda aka aura mata ba don baze iya cin amanar dan'uwansa ba.        Maganar 'cin amanar' data ambato shi yafi tsaya masa arai.Anya kuwa ya k'yautawa Mubarak kuwa? Taya kuma xasuyi zaman aure da Fadima bayan Mubarak dan'uwansa ne,his blood brother,ai kuwa kusan koda yaushe Ze dunga haduwa da Fadimar musamman ah family house. And anything bad can happen!. Shi fa bema taba tunanin hakan ba,burinsa kawai ya mallaki Fadima shikenan an gama komai.Gashi yanxu ya mallaketa din ba tare da sanin mahaifiyarsa ba,yan'uwansa da kuma shi uban gayyar wato Mubarak.wani irin yakine za'ayi idan Mubarak din ya dawo? amsar da be sani ba kenan.Amma shi de abinda ya sani shine,*'MATAR MUTUM KABARINSA'*.... Dama can Allah ya riga ya rubuta cewar Fadima matarsa ce shiyasa lamarin aurensu yazo da hakan.Shi de addu'arsa Allah yasa Fadima ta fahimci dalilinsa na aurenta sannan kuma ta soshi su xauna lafiya.      Koda ya fita daga dakin,wurin Haj.Faiza ya nufa wato maminsu Hafeezah don gaya mata cewar anyi cancelling xuwa reception din,don baze so ya matsawa Fadimar mah azo ayi tashin hankali yadda mah yaga yau idanuwan nan nata atsattsaye suke na shirin sauke kwandon bala'i.baze so ace komai ya k'wab'e musu agaban jama'a ba don su karan kansu Baba Mu'azzam da iyalensa basu san Fadimar bata san cewar Engr. ne mijinta ba,all their taught ta sani kuma tana sonsa shiyasa ya shige masa gaba wajen neman aurenta.        "Haba Mahmood wannan wani iri xance ne kake yi wai an fasa xuwa reception? Kasan fa abokanka baza suji dadi ba don ba k'aramin kudi suka barnatar ba....... " Mami ce ke wannan maganar alokacin da 'yarta Afreen yayar Hafeezah ke sak'ala mata abin wuya da 'yan kunne.     Mahmood dake tsaye da hularsa ahannu yace"Mum Fadimarce bata jindadi,she's sick........ " Akid'ime ta mik'e tana fadin"What?? Bata da lafiya? Meke damunta??      "Zazzab'i ce,pls kada ki d'aga hankalinki Mami dama tun acan gidansu ne ta soma rashin lafiyar amma yanzu da sauki,zafin jiki ne da dan ciwon kai kawai...... " Saukar da ajiyar xuciya Mami tayi,kana tace"Mahmood ina ganin kawai ka kaita asibiti Doc.ya dubata...... "       Cike da faduwar gaba yace"A'ah Mami ba sae an kaita asibiti ba,nace miki da sauki kije mah ki dubata da kanki ki gani...... " Kafin ya sake magana tayi wuf! ta fice,Afreen da Hafeezah dake tsantsara makeup suka take mata baya.     Shi kuwa Mahmood ajiyar xuciya ya sauke,ahankali ya furta"Ya salam! Wannan wani irin aure ne nayi? Wani irin tashin hankali da bala'i ne nake nemar jajibowa rayuwata?" Ficewa yayi daga dakin,ya nufi waje,Su Ash na ganinsa suka mik'e,so take ta masa magana amma sae kuma taga ya daga mata hannu yayi gaba da sauri-sauri.Da hanzari Ash sukayi ciki gabanta na meh cigaba da dukan tara-tara.tabbas tasan wani abin ne ya faru don yadda taga Mahmood ya fita babu walwala akan fuskarsa.Toh koma meye ya faru Fatin ta birgeta,don basu ji wata hayaniyarsu ba,komai silently sukayi shi.     ** Ina ganin ficewarsa naja jikina dakyar na xauna agefen gado da k'arfi tare da rik'e kaina dake barazanar fashewa don azabar ciwon kai.Hawayena sun kafe sunki zuba,abubuwan daya faru yanxu tsakanina da Engr. sun girmi k'wak'walwata don so nake nayi tunani da kuma nazarin kalamansa amma brain dina ya gaza yin hakan,k'wak'walwar tawa ta kasa bani damar tunanin komai.      Ina cikin wannan halin ne naji muryar Mamin Hafeezah tun kan ta k'araso dakin tana fadin"Fadima d'iyata kina ina? " Axuciyata nace"Ban gane ina ina ba? ya wuce dakin da kuka saukeni....? "    Ganinta nayi ta shigo arud'e tare dasu Hafeezah biye da ita,sae ayanzu hankalina ya tashi kar de ace sunga fitar Engr. daga cikin d'akina??     "Fadima yah kike jin jikin naki yanxu da sauki de koh? Idan babu tun wuri muje asibiti... " Sae ayanzu hankalina ya dan kwanta ganin ba abinda nake tunani akai bane,kafin nayi magana naji sallamarsu Ash,biye dasu Anty Hajaar ce dasu Mama Jamila wanda ga dukkan alamu dawowarsu kenan.     "A'ah kaina ne kawai ke ciwo Mami.... " na bata amsa cikin sanyin murya. Tace"Toh bari na kawo miki maganin ciwon kan.... "     Da sauri nace"A'ah Mami karki damu akwai ah purse dina.... " Da hanzari na dauko purse din na ballo paracetamol,na dibi dan ruwa ah jug na hadiye maganin.Sae sannu ake ta min.Su mama Jamila mah sae duk suka ji ba dadi da kuma tausayina,duk aganinsu zazzabin bankwana dasu nake don lafiyata qalau sae yanxu dana soma jin jikina ba dadi.     So nake nayiwa Ash wasu yan tambayoyi amma presence din su mama jamila da dangin mijina ya hanani k'eb'ewa da ita.Agaskia naga gata sosae awurin dangin mijin,nan da nan suke tayi dani kamar wata kwai da ba'a son ta fashe.     Ina ke miki ciwo? Meh kike son kici?duk tambayoyin kenan wanda rana ta farko kenan dana ji na soma qaunar wannan auren. Amma shi mijin nawa ina yake ne da har yanxu banga ko inuwarsa ba?        ** Shi kuwa Mahmood yana fita,sae da aka kai ruwa rana kafin abokansa su haqura da xancen reception din.    Ce musu yayi"Idan ta kudin da kuka barnatar ne shine kuke jinsa ajiki,toh kuyi haquri xan biyaku amma ni lafiyar matata ya fiye min komai...... " Sae kuma suka ji duk jikinsu yayi sanyi da maganarsa.Haka de kowa ya kama gabansa duk rai babu dadi.k'iran wasu abokansu sukayi wa'enda suke venue din already suka sanar dasu cewar an fasa,Suma din sunyi d'an korafi amma da sukaji dalili se kuma suka dan sassauta. Shima Mahmood din wucewa gidansa yayi dake 'court road' don baze iya sake komawa cikin gidan ba.Gobe mah sae dare ze taho d'aukarta,don zasuyi kusan sati uku akano kafin su koma Zaria.       Washegari wajen qarfe goma akayi walima acikin filin gidan,ba wasu jama'an Kirki ne suka zo ba kamar namu ba,kuma ba laifi malamar tayi nasiha meh ratsa xuciya wanda nayi kuka sosae. Itama Suhaima anata b'angaren,qarfe goma akayi walima ah k'ayatacciyar filin gidan,ana gamawa direct akayi da ita b'angaren da xata zauna,sannan jama'a suka watse,tayi kuka sosae sanda kawayenta da wasu mamamninta suka zo wucewa wa'enda suka kwana.Dakyar ta bari suka wuce tana kuka wasu mah suna kuka.Yanzu ya rage ita kadai acikin dakinta,sae angonta da xata jira.     Su Mama Jamila ne suke ce min zasu wuce,ai kuwa kuka na sakar musu ina cewa nima binsu xanyi. Mama Sadiya ce tace"Yau ga sakarya,Yo! ai wannan itace ake kira da auren ai,gashi mun kawoki gidan mijinki inda kike ta mararin xuwa..... kinga ni cika min gyale..... "     Haka su Mama Sadiya mah suka min,suka tureni suka fice har su Ash. Sae kuka nake wiwi kamar wata k'armar yarinya,su Mami kuwa sae aikin rarrashina suke. Sae bayan isha'i akace min nazo mu tafi ga angona ya taho daukata,mamaki nake tayi wai ace da daddaran nan ne xamu kama hanyar Zaria? Kamar na tambayi su mami ko Zariar ce zamu tafi da daddaran nan amma sae naji na kasa.      Falon Baba kamar yadda naji ake k'iran mahaifinsu Hafeezah aka kaini,anan naga angon nawa Xaune akasa yana sauraron jawabin Baba. Kun san wanene mijin nawa?? Its still Engr. Mahmood Mustapha dai nake gani zaune agabana,sae ayanzu na tabbatar da cewar Yes! shi din ne de mijina.      Tuni naji wani irin tashin hankali ya min sallama,taya akai ya sami aurena? meh yayi wa mahaifina har ya bashi aurena? Dama ze iya cin amanar Mubarak ban sani ba? Inasu mummy da sauran kannansa don ga dukkan alamu ya nuna cewar basu da masaniyar auren,kamar b'oye musu yayi,sannan kuma su waye Baba Mu'azzam da kuma Mamin Hafeezah agareshi? Anya ba hayar iyaye yayi ba  don su tsaya masa akan wannan aure ba kuwa?     Wani murmushin takaici nayi ina meh raya wasu al'amura araina,ni kadai kurum nasan tashin hankalin da zan haifar muddin muka sanya kafa muka bar nan gidan.Ni kadai nasan tanadin dana yiwa Engr. Mahmood bayan ya gama labarta min dalilinsa na auren *'BUDURWAR KANINSA'*..................... 📝     A/N Tofa my people mun fa iso gun.... Wani kudiri ne kuma ke ah cikin ran Fadima? Meh take shirin yiwa Engr. Mahmood? Ku dai biyoni.      *IT'S HAFNAN*                  *💘SHIN SO DAYA NE?💝*        *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*        *WATPADD:HAFNANCY*        *IG:Hafsy__mustee*                      💥 *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*           🌼BABI NA UKU🌼 *Page 6-9*         "Mama bara naje nima na kimtsa kada su wuce wajen reception d'in nan bani..." acewar Anty Hajaar wacce tana gama fad'ar hakan ta mik'e tabar dakin xuwa sashin da aka saukesu. Kaka rigima ta rakata da "Toh! adawo lafiya Hajara,Allah sarki an girma ba'a san an girma ba,yanxu fisabilillahi taron k'ananun yara mah sae sunje.... Koda yake Allah ne ya kawo mu xamani..."     Ai dole ne Anty Hajar tama je wannan reception din ko don taje tayi ciye-ciye ta kuma nunawa duniya cewar ita din fah uwar amarya ce.Maminsu Hafeezah mah zataje don ita da Mahmood suna mugun d'asawa da k'yau. Ash ce xaune tare da Zuzu ah barandar sashin da aka saukesu.Hirar Khaleed Zuzu ke bata wanda ga dukkan alamu ya nuna cewar gayen ya gama tafiya da imaninta.Ita Ash din mah da akewa hirar amsawa kawai take da "uhmm" ko kuwa "a'ah",don kusan xan iya cewa gabaki daya hankalinta ya tafi ne ga su Fadima.Sae ayanxu ne take ganin wautarta na k'iran shi Mahmood d'in daya zo ya lallashi Fadimar bayan tasan muddin Fatin nata na had'a idanuwa dashi amatsayin mijin da aka aura mata,toh kuwa komai na iya k'wab'ewa,anything can happen!.     Oh! Allah!! akace dana sani yakan zo ne bayan ka aikata ba daidai bah,akan k'irashi da *'dana sani mara amfani'*,data sani kawai ta lallab'ata ta saka kayan don tasan Fatinta komin fad'arsu de tana jin maganarta,kuma tasan xata sauko ne har ta haqura taje reception din,amma da yake iyayi yayi mata yawa,kai tsaye ta k'ira Mahmood din da yaxo gareta,iyayinta ya janyo tana neman haifar da tashin hankali acikin jama'a wanda ta fison ace sae an kai Fadimar gidansa,asannan kowa ya kama gabansa kafin tasan wanene mijinta,tasan duk wani tashin hankali da ze biyo baya alokacin zai iya xuwa da sauki.Wurin reception mah ba lalle ne Fadimar ta gane Mahmood din ba tunda duk'ar da kai zatayi tayi,balle mah tasan halin Fadimar sarai da alkunya,zaiyi matuk'ar wuya ta masa kallon tsaf acikin jama'a.Koda ace tama gane shi,tasan Fadimar baxata tab'a kunyatar dashi idanuwan mutane ba har sae sun k'ebe.      Toh! yanxu gashi ta janyo k'ebewar tasu da wuri tun mutane basu gama watsewa ba,kuma tasan anything shitty can happen. Axuciyarta tace"Ohh! ni Ayshatu wat have I done? meya kaini k'iransa? "    Xuciyarta babu abinda yake yi illa bugawa da sauri da sauri,kasa kunnuwa tayi tana meh jiran ta jiyo hayaniyarsu Fadimar sannan tayi ciki wuf!.Zuzu de data ga sam hankalin Ash din baya gareta,sae kawai taja bakinta tayi shiru,ita Allah-Allah mah take su Fadimar suyi su gama soyayyarsu kamar yadda take tunani sannan ta shiga taje ta tsalawa Khaleed dinta kwalliya. Anty Hajaar ce tazo shiga sashin,da hanxari Ash ta mik'e tare da shan gabanta.      Wani irin kallon banza ta jefawa Ash din,kana tace"marasa kunya meye kuma haka? Ko de wata sabuwar salon rashin kunyarce ta motso miki shine hadda wani shan gabana?" Dan murmusawa kawai Ash tayi,kana tace"Yana de gab da motsowa.... So nake kawai nace miki ki d'an dakata,ango na ganawa da amaryarsa aciki........ "     Hab'a Anty Hajaar ta rik'e,kana tace"ikon Allah!... nide tunda na budi ido nayi wayau ban tab'a ganin rashin kunya da da'a irin wannan ba,Muido da wannan angon nata sam basu da alk'unya ko kadan musamman mah angon nata,ai sae ya bari iyayenta su tafi kafin ya shiga wurinta suyi shashancin nasu son ransu........ " Wani kallo ta watsawa Anty Hajaar,ta dubi inda Zuzu take taga mah sam hankalinta baya garesu,hasalima wayarta take daga can d'an nesa da inda suke tsaye.      Ahankali Ash tace"Dad'ina dake Anty akwai ki da iya jan k'aramar magana tayi tsayi da kuma janyowa kanki raini awajen kananan yara,ina ruwanki da koma meye ya shiga yi? Ina ce ko matarsa ce ba dadironsa ba? Don Allah Anty Hajaar ki dunga kama girmanki kada ya gama xubewa ah idanuwanmu mu yara..... " Tana gama fad'ar hakan ta koma mazauninta,sae duba agogo take awayarta,yanxu haka takwas ta wuce da mintuna goma,akalla Mahmood ya shafe kusan mintuna ashirin aciki yanxu.Ita kuwa Anty Hajaar jikinta ne yayi sanyi qalau don bata tab'a jin k'unyar kwab'o ba arayuwarta sae yau da Ash ta mata.Sae taga rashin dacewar maganar daya fito daga bakinta.Jan jikinta tayi xuwa ga wani k'aramar kujera ta tsakar gida ta xauna.(lol maganin irinku kenan Anty Hajaar... Ash kin biyani....)      *** Idanuwana dani k'aran kaina mun kasa gasgata cewar wai *'ENGR. MAHMOOD MUSTAPHA'* dan'uwan Mubarak ne tsaye agabana amatsayin *'MIJIN KADDARATA'*     Sake kai yatsu nayi ina murza idanuwana akaro na uku don tabbatarwa kaina cewar mafarki nake kuma wanda ke tsaye agabana ba 'ENGR.MAHMOOD' my brother inlaw bane.Harda mitsilin kaina nayi wai ko mafarki nake na farka,amma uban Zafin dana ji ne ya saka nasan ba mafarkin nake ba,this is reality!!!.    Da rawar murya nace"Don Allah meh kake yi anan?" Gaban Engr.ne ya buga wata irin ganga,fargaba da kuma tsoron actions din da Fadima xatayi taking duk ya cika masa xuciya fal! amma da yake shi din namijin duniya ne,sae be bari ta gano weakness dinsa ba.      Fuskar mamaki ya shimfid'a mata,kana yace"Ban gane meh nakeyi anan ba? all what I know is dat wajen matata nazo...... "      "Wacece kuma matar taka? " na fadi hakan sanda naji xuciyata na wani min mugun zogi.   "Of cours! Fadima Sa'ad Mainasara amaryar Engr.Mahmood Mustapha...... " Da hanzari na katseshi"k'arya kake mak'aryacin banza,mak'aryacin wofi,you can never be my husband ko amafarki,ni bah kai na aura ba,ni *'MAHMOOD NAKOWA'* na aura not *'ENGR.MAHMOOD MUSTAPHA'* because am very pretty sure dat brother inlaw bazaka taba cin amanar d'an'uwanka ba,bazaka tab'a yaudararsa ba,haka kuma nasan bazaka tab'a bin bayansa ka k'wace masa ni ba...... "     Wani irin mugun d'aci ne Mahmood keji aransa na jin irin wannan kalaman da Fadima take jefarsa dashi,yab'onsa take ko kuwa maganace mara dad'i take jefa masa?   sassauta muryata nayi,da rawar murya meh had'e da kuka na cigaba da magana"pls brother inlaw meya kawoka gidan surukaina?ko kuwa kaima kana cikin abokan ango ne? kuma ina mijina yake da har ya barka ka shigo har inda matarsa take?okay yanxu na gane,ka samu labarin cewar nayi aure shine kazo kaci min mutunci don na yaudari d'an'uwanka ban aureshi ba..... "    Had'a hannuwa wuri guda nayi kana nace"pls na rokeku don Allah kuyi haquri ba laifina bane nima din biyayya kurum nayi,don Allah kacewa d'an'uwan naka daya gafarceni ba laifina bane,albarqan iyayena nake nema shiyasa na amince da xab'insu.... Pls brother inlaw ka tafi kada mijina ko wani ya shigo ya ganka anan....... " Wasu 'yan kwalla ne yaji sun ziraro masa saman kunci na tausayin kansu daga shi har Fadimar,da hanzari ya juya ya fice daga dakin kamar yadda ta buqata.k'aron farko daya soma ganin rashin dacewar auren Fadima da yayi gashi yanxu tana denying dinsa akan bashi ne wanda aka aura mata ba don baze iya cin amanar dan'uwansa ba.        Maganar 'cin amanar' data ambato shi yafi tsaya masa arai.Anya kuwa ya k'yautawa Mubarak kuwa? Taya kuma xasuyi zaman aure da Fadima bayan Mubarak dan'uwansa ne,his blood brother,ai kuwa kusan koda yaushe Ze dunga haduwa da Fadimar musamman ah family house. And anything bad can happen!. Shi fa bema taba tunanin hakan ba,burinsa kawai ya mallaki Fadima shikenan an gama komai.Gashi yanxu ya mallaketa din ba tare da sanin mahaifiyarsa ba,yan'uwansa da kuma shi uban gayyar wato Mubarak.wani irin yakine za'ayi idan Mubarak din ya dawo? amsar da be sani ba kenan.Amma shi de abinda ya sani shine,*'MATAR MUTUM KABARINSA'*.... Dama can Allah ya riga ya rubuta cewar Fadima matarsa ce shiyasa lamarin aurensu yazo da hakan.Shi de addu'arsa Allah yasa Fadima ta fahimci dalilinsa na aurenta sannan kuma ta soshi su xauna lafiya.      Koda ya fita daga dakin,wurin Haj.Faiza ya nufa wato maminsu Hafeezah don gaya mata cewar anyi cancelling xuwa reception din,don baze so ya matsawa Fadimar mah azo ayi tashin hankali yadda mah yaga yau idanuwan nan nata atsattsaye suke na shirin sauke kwandon bala'i.baze so ace komai ya k'wab'e musu agaban jama'a ba don su karan kansu Baba Mu'azzam da iyalensa basu san Fadimar bata san cewar Engr. ne mijinta ba,all their taught ta sani kuma tana sonsa shiyasa ya shige masa gaba wajen neman aurenta.        "Haba Mahmood wannan wani iri xance ne kake yi wai an fasa xuwa reception? Kasan fa abokanka baza suji dadi ba don ba k'aramin kudi suka barnatar ba....... " Mami ce ke wannan maganar alokacin da 'yarta Afreen yayar Hafeezah ke sak'ala mata abin wuya da 'yan kunne.     Mahmood dake tsaye da hularsa ahannu yace"Mum Fadimarce bata jindadi,she's sick........ " Akid'ime ta mik'e tana fadin"What?? Bata da lafiya? Meke damunta??      "Zazzab'i ce,pls kada ki d'aga hankalinki Mami dama tun acan gidansu ne ta soma rashin lafiyar amma yanzu da sauki,zafin jiki ne da dan ciwon kai kawai...... " Saukar da ajiyar xuciya Mami tayi,kana tace"Mahmood ina ganin kawai ka kaita asibiti Doc.ya dubata...... "       Cike da faduwar gaba yace"A'ah Mami ba sae an kaita asibiti ba,nace miki da sauki kije mah ki dubata da kanki ki gani...... " Kafin ya sake magana tayi wuf! ta fice,Afreen da Hafeezah dake tsantsara makeup suka take mata baya.     Shi kuwa Mahmood ajiyar xuciya ya sauke,ahankali ya furta"Ya salam! Wannan wani irin aure ne nayi? Wani irin tashin hankali da bala'i ne nake nemar jajibowa rayuwata?" Ficewa yayi daga dakin,ya nufi waje,Su Ash na ganinsa suka mik'e,so take ta masa magana amma sae kuma taga ya daga mata hannu yayi gaba da sauri-sauri.Da hanzari Ash sukayi ciki gabanta na meh cigaba da dukan tara-tara.tabbas tasan wani abin ne ya faru don yadda taga Mahmood ya fita babu walwala akan fuskarsa.Toh koma meye ya faru Fatin ta birgeta,don basu ji wata hayaniyarsu ba,komai silently sukayi shi.     ** Ina ganin ficewarsa naja jikina dakyar na xauna agefen gado da k'arfi tare da rik'e kaina dake barazanar fashewa don azabar ciwon kai.Hawayena sun kafe sunki zuba,abubuwan daya faru yanxu tsakanina da Engr. sun girmi k'wak'walwata don so nake nayi tunani da kuma nazarin kalamansa amma brain dina ya gaza yin hakan,k'wak'walwar tawa ta kasa bani damar tunanin komai.      Ina cikin wannan halin ne naji muryar Mamin Hafeezah tun kan ta k'araso dakin tana fadin"Fadima d'iyata kina ina? " Axuciyata nace"Ban gane ina ina ba? ya wuce dakin da kuka saukeni....? "    Ganinta nayi ta shigo arud'e tare dasu Hafeezah biye da ita,sae ayanzu hankalina ya tashi kar de ace sunga fitar Engr. daga cikin d'akina??     "Fadima yah kike jin jikin naki yanxu da sauki de koh? Idan babu tun wuri muje asibiti... " Sae ayanzu hankalina ya dan kwanta ganin ba abinda nake tunani akai bane,kafin nayi magana naji sallamarsu Ash,biye dasu Anty Hajaar ce dasu Mama Jamila wanda ga dukkan alamu dawowarsu kenan.     "A'ah kaina ne kawai ke ciwo Mami.... " na bata amsa cikin sanyin murya. Tace"Toh bari na kawo miki maganin ciwon kan.... "     Da sauri nace"A'ah Mami karki damu akwai ah purse dina.... " Da hanzari na dauko purse din na ballo paracetamol,na dibi dan ruwa ah jug na hadiye maganin.Sae sannu ake ta min.Su mama Jamila mah sae duk suka ji ba dadi da kuma tausayina,duk aganinsu zazzabin bankwana dasu nake don lafiyata qalau sae yanxu dana soma jin jikina ba dadi.     So nake nayiwa Ash wasu yan tambayoyi amma presence din su mama jamila da dangin mijina ya hanani k'eb'ewa da ita.Agaskia naga gata sosae awurin dangin mijin,nan da nan suke tayi dani kamar wata kwai da ba'a son ta fashe.     Ina ke miki ciwo? Meh kike son kici?duk tambayoyin kenan wanda rana ta farko kenan dana ji na soma qaunar wannan auren. Amma shi mijin nawa ina yake ne da har yanxu banga ko inuwarsa ba?        ** Shi kuwa Mahmood yana fita,sae da aka kai ruwa rana kafin abokansa su haqura da xancen reception din.    Ce musu yayi"Idan ta kudin da kuka barnatar ne shine kuke jinsa ajiki,toh kuyi haquri xan biyaku amma ni lafiyar matata ya fiye min komai...... " Sae kuma suka ji duk jikinsu yayi sanyi da maganarsa.Haka de kowa ya kama gabansa duk rai babu dadi.k'iran wasu abokansu sukayi wa'enda suke venue din already suka sanar dasu cewar an fasa,Suma din sunyi d'an korafi amma da sukaji dalili se kuma suka dan sassauta. Shima Mahmood din wucewa gidansa yayi dake 'court road' don baze iya sake komawa cikin gidan ba.Gobe mah sae dare ze taho d'aukarta,don zasuyi kusan sati uku akano kafin su koma Zaria.       Washegari wajen qarfe goma akayi walima acikin filin gidan,ba wasu jama'an Kirki ne suka zo ba kamar namu ba,kuma ba laifi malamar tayi nasiha meh ratsa xuciya wanda nayi kuka sosae. Itama Suhaima anata b'angaren,qarfe goma akayi walima ah k'ayatacciyar filin gidan,ana gamawa direct akayi da ita b'angaren da xata zauna,sannan jama'a suka watse,tayi kuka sosae sanda kawayenta da wasu mamamninta suka zo wucewa wa'enda suka kwana.Dakyar ta bari suka wuce tana kuka wasu mah suna kuka.Yanzu ya rage ita kadai acikin dakinta,sae angonta da xata jira.     Su Mama Jamila ne suke ce min zasu wuce,ai kuwa kuka na sakar musu ina cewa nima binsu xanyi. Mama Sadiya ce tace"Yau ga sakarya,Yo! ai wannan itace ake kira da auren ai,gashi mun kawoki gidan mijinki inda kike ta mararin xuwa..... kinga ni cika min gyale..... "     Haka su Mama Sadiya mah suka min,suka tureni suka fice har su Ash. Sae kuka nake wiwi kamar wata k'armar yarinya,su Mami kuwa sae aikin rarrashina suke. Sae bayan isha'i akace min nazo mu tafi ga angona ya taho daukata,mamaki nake tayi wai ace da daddaran nan ne xamu kama hanyar Zaria? Kamar na tambayi su mami ko Zariar ce zamu tafi da daddaran nan amma sae naji na kasa.      Falon Baba kamar yadda naji ake k'iran mahaifinsu Hafeezah aka kaini,anan naga angon nawa Xaune akasa yana sauraron jawabin Baba. Kun san wanene mijin nawa?? Its still Engr. Mahmood Mustapha dai nake gani zaune agabana,sae ayanzu na tabbatar da cewar Yes! shi din ne de mijina.      Tuni naji wani irin tashin hankali ya min sallama,taya akai ya sami aurena? meh yayi wa mahaifina har ya bashi aurena? Dama ze iya cin amanar Mubarak ban sani ba? Inasu mummy da sauran kannansa don ga dukkan alamu ya nuna cewar basu da masaniyar auren,kamar b'oye musu yayi,sannan kuma su waye Baba Mu'azzam da kuma Mamin Hafeezah agareshi? Anya ba hayar iyaye yayi ba  don su tsaya masa akan wannan aure ba kuwa?     Wani murmushin takaici nayi ina meh raya wasu al'amura araina,ni kadai kurum nasan tashin hankalin da zan haifar muddin muka sanya kafa muka bar nan gidan.Ni kadai nasan tanadin dana yiwa Engr. Mahmood bayan ya gama labarta min dalilinsa na auren *'BUDURWAR KANINSA'*..................... 📝     A/N Tofa my people mun fa iso gun.... Wani kudiri ne kuma ke ah cikin ran Fadima? Meh take shirin yiwa Engr. Mahmood? Ku dai biyoni.      *IT'S HAFNAN*                  *💘SHIN SO DAYA NE?*         *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*        *WATPADD:HAFNANCY💞*         *IG:Hafsy____mustee*                      ✨✨ *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*            🌼BABI NA SHIDDA🌼     *page 15-18*          Can de na cije na sanya 'yar yatsa na sharce hawayen da har xuwa wannan lokacin sunki daina zuba,sae mah dad'a gangarowa suke kamar ana korosu ko kuma nace tamk'ar ruwan famfo. "Brother inlaw har kayi round up na labarinka banji ka ambaci kalmar *'NAKOWA'* ba wanda abinda nafi k'osawar naji inda ka sami wannan sunan kenan.... " Na kafeshi da jikakkun idanuwana ina meh jiran naji bayanin da ze biyo baya.      Saukar da wata wahalalliyar ajiyar xuciya naji yayi,kana yace"Fadima da fari dai don Allah ina son kiyi cancelling wannan *'Brother inlaw'* din da kike k'irana da ita,pls stop it banaso,am now ur husband so pls kindly upgrade my name to a romantic one,I want to feel being love again..... " Wata uwar harara na watsa matsa,amsa nayi niyyar bashi amma kuma se na tuna cewar ban gama jin duk abinda nakeson naji daga gareshi ba,don haka se nayi ladab tare da maida wuk'ar.      "Naji dear nah daga yau na sauya maka suna .... " na fad'a in a very romantic way.Har cikin xuciyarsa yaji dadin wannan sunar,ji yayi kamar Zeeynsa ce ta fada masa hakan don haka take k'iransa da *'Dear nah'*. Ni kuwa da gangan nace *'Dear nah'* don na sosa masa xuciya yaji kamar Zaynab din ce agabansa.     Axuciyata nace"Kaji dan malohon har ya wani susuce don na k'irashi kawai da 'Dear nah',lallai na yadda mace de shed'aniyace,ko shaid'an din mah yana Sara mata,tasan ta yadda zatayi ta zautar da d'a namiji,kissa da kisissina da duk wani salon yaudara duk atafin hannun mace suke...... " Ji nayi ya katse min tunanina,yace"Nakowa de da kike taji ana fada family name dinmu ne,tun asali mahaifinmu ne ya sami wannan sunan daga bakin jama'a,sabida shi din mutumin mutane ne,kowa nasa ne,haka kuma yana da tausayi da kuma taimakon na k'asa dashi,dalilin daya saka mutane ke k'iransa da *'NAKOWA'* kenan,ba dukanmu muke amfani da sunan ba,ina daya daga cikin wa'enda basa amfani da sunan acikinmu,shima Mubarak din baya amfani da ita,we're juz bearing *'Mustapha'*,ta siyasa na tambayi Mubarak ko ya tab'a fad'a miki family name dinmu? Sae yace wallahi be tab'a ba,so yake idan yazo gabatar da Kansa awajen mutanenki,sae asannan ne ze bada cikakken sunansa,sosae nayi murna da hakan da kuma ganin wautarsa,shiyasa na bada wannan sunan awajen mutanenki don nasan tabbas bazakiyi saurin d'agowa ba....... "      Tafa hannaye na soma yi kamar wata 'yar coci,shi kuwa kallo ya bini dashi,k'wayar idanuwan nan nasa dauke suke da tsananin tsoron actions din da xanyi taking. Nace"Wow!wow!bravo!!... so smart & intelligent being.... Hmm! Nakowa's family..... "      Sake maimaita sunan nayi cike da alhini"Nakowa's family........ " "Nakowa's family wallahi babu wani mahaluk'in daya kama kafarku wajen iya tsara takun basaja,believe me wallahi kune sahun gaba ah iya tafiyar da takun basaja very smoothly ba tare da an sami wata tagargad'a ba,Ni Fadima sa'ad wai *'Wa'* da *'K'ani'* suka ta yawo da hankalina da kaifin tunanina.Da fari de,*'K'ani'* ya b'oye min cewar yana da mata hadda 'ya,sae matarsa tayi takun basaja axuwan ita k'anwarsa ce don de kawai kada na d'ago cewar ita din matarsa ce,sannan kuma wai don kada nayi zargin cewar al'akar soyayyata dashi is secret,family dinsa basu da masaniya,don haka idan har ita ta tarb'eni axuwan fiancee dinsa,toh tabbas xanyi tunanin cewar ai sauran mah sun sani,kawai kawaici suke nuna min,sae kuma aka sami matsala,takun nasu ya sami d'an targad'e,mahaifiyarsa da 'yarsa suka b'ata musu shirinsu wanda hakan ya saka na d'ago cewar tabbas akwai wata ak'asa,wai hakan da matar tasa tayi aganinta son miji ne ya saka ta biye mishi ko menene? Idan kuwa hakane xan iya cewa ita din k'atuwar dak'ik'iyace,raina mata hankali kawai akai awannan shirin,shirin *'DR. MUBARAK MUSTAPHA NAKOWA'* itace '*BASAJA TAKUN FARKO'*............."      Dan murmushin takaici nayi,kana na cigaba"Bayan komai ya d'an lafa,sae kuma *'Wa'* ya kunno mana da tasa k'alar takun basajar wanda ya shallak'e tunanin duk wani meh tunani,friends dina sunsha fad'a min cewar kamar brother inlaw dina is having a crush on me!,amma kasan meh? Saurin k'wab'arsu nayi akan karsu sake min wannan zancen banzar,and do you know why I said so? Sabida aganina brother inlaw dina baze tab'a tunanin cin amanar dan'uwansa ba,kawai de k'yautatawace da kuma kulawa kake nuna min amatsayina na budurwan k'aninka,sae gashi tashi daya ka shayar dani madaran mamaki,sae da kasan ta yadda kayi ka aureni,ayau gani ga *'ENGR.MAHMOOD MUSTAPHA NAKOWA'* wan *'DR.MUBARAK MUSTAPHA NAKOWA'* amatsayin mijin auran '*FADIMA SA'AD MAINASARA'*... gaya min,isn't dat a shameful thing to us? Sannan kuma mutane sun sami abin fada cewar ai 'wa' ya auri budurwar 'k'aninsa,kaga wannan shirin taka itace *'BASAJA TAKUN K'ARSHE'* don daga kai,wallahi insha Allahu babu wani d'a namiji da xan yarda ya sake tsara wata takun basajar akaina......never wallahi........ "      "Fadima please listen....... " ya fada awahalce. Da sauri na daga masa hannu"Malam saurara min nan!.... lokacin zancen soki burutsunka ya riga da yayi expire,yanxu kuwa lokacin maganata ne,it's my turn to speak out and take actions,lokacin zartar da hukunci yayi......... "      "Bayan igiyoyin auren na rataye ah wuyana shine kike tunanin zartar da hukunci da kanki?taya zaki zartar da wannan hukuncin baby doll? ko kuwa atunaninki ni Mahmood xan tab'a furta kalmar '*SAKI'* ne agareki?toh kuwa idan hakan kike tunani,toh ina son ki sani,Ni Mahmood baxan tab'a sakin matata Fadima sa'ad ba,Mahmood ba ragon namiji bane ko kuma wani sok'on ba da har zeyi tunanin rushe ginin daya dad'e yana ginata ba,baxan tab'a gangancin sakinki ba don na dad'e ina jiran zuwan wannan ranar ta mallakarki amatsayin matar aurena,Fadima ina son kisa aranki cewar ni dake aurenmu mutu ka raba ne takalmin kaza,don haka baxan tab'a sakinki ba,ruwan daya tafasa ya dad'e be k'one ba...... "     Gabana ne naji ya yanke ya fadi da jin maganganunsa,amma kuma se na d'aure nace"Mahmood wallahi se ka sakeni adaran nan ba sae an kai gobe ba,don banzo da shirin fuskantar tashin hankalin dake shirin kunno kai acikin family dinka asanadin aurena ba,baxan tab'a yadda Mubarak ya min kallon 'maciya amana' ba balle har na lamunci tsaya jin yana jifana da wannan kalmar ba,never! wallahi I'll never permit dat..... "     Cikin d'aga murya nace"Mahmood ina meh umartarka daka gaggauta sauke igiyoyin aurena duka ukun dake rataye ah wuyanka don bazan tab'a so ayi mah tunanin gyara wannan auran nan gaba ba....... " Cike da takaicinta Mahmood yace"Ban tab'a tunanin cewar ke din dak'ik'iya bace sae yau,atunanina ilimin arabi ya gama ratsa k'wak'walwarki,ashe abinda ban sani ba da sauranki,kin kuwa san girman laifin duk wata matar data buk'aci saki da bakinta daga wurin mijinta? Nasan kin fini sanin abinda Allah (SWT) ya tanadar mata,amma shine ke don toshewar basira da kuma tsananin b'acin ran da kike ciki yasa har ke kike nemar mah ayi miki sakin da manzon Allah (SAW) yayi mana hani da yinta,wato saki uku!!,,wa'iyazubillah!! wallahi Fadima ki gaggauta yin istigfari ga ubangiji,sannan kuma ki nemi tsari daga shed'an don duk shine ke neman sakaki ki k'auce hanya,Fadima ina son ki rungumi kaddararki da hannu bibbiyu,ina son ki sanya aranki dama can Allah ya rubuta cewar ni din mijinki ne,ke kuma matata,saki de kamar yadda na fada,kinji nace wallahi bazan tab'a sakinki ba,aurena dake mutu ka raba ne,zaman auranmu daram!,,ni dake kamar magnet da k'arfe haka zamu kasance,am fully ready to face any problem coming soon............ "      Wasu hawayen bakin ciki ne suka soma shatato min saman kunci,xuciyata ta sauya zuwa xuciyar kafirai marasa imani,idanuwana sun rikid'e sun koma na tsantsar bala'i.ko daya daga cikin karatun daya karanto min babu wanda yayi nasarar shiga cikin k'wak'walwata. Cike da isa da gadara nace"Mahmood ga shawara idan har zaka k'arbeta.... Ka sakeni ta ruwan sanyi tun muna shaida juna,idan kuwa kaki,toh ina meh tabbatar maka da cewar lallai kuwa za'a ji kanmu don ta tashin hankali da kuma k'eta za'a rabu,now its left to you to choose one of conditions listed........."     Murmushin leb'en baki kawai Mahmood yayi,kana yace"All of the conditions listed sunyi tsauri da yawa matar Mahmood,don haka none of the conditions listed will be picked up...... " Da sauri nace"Haka kace ko? "     "Ba wai haka nace ba,hakan de take.... " ya fada tare da kashe min one eyes. Gani nayi yana nema ya kawo min taurin kai,ni kuwa xuciyata sae ingizani take,tana meh raya min wasu al'amura araina,ai kuwa da hanxari nayi kitchen ina waigensa,shi kuwa sae murmushi yaketa wulla min.     Ahankali nace"Dan iska yanzun nan kuwa zaka yi abinda nakeso.... " Shi kuwa Mahmood he wonder wat Fadima is upto,atunaninsa wani abin take da buqata shiyasa taje kitchen din.Babu zato babu tsammani sae ganinta yayi ta fito daga kitchen rik'e da wata sharb'ebiyar wuk'a ahannunta.wata irin zabura yayi tare da mik'ewa da sauri.    Cike da tashin hankali yace"Fadima meye haka? Meh kenan kika rik'e ahannunki?" Ni kuwa ganin tashin hankali da kuma zallar tsoron dake shimfid'e akan fuskarsa ya sakani bushewa da wata dariyar shekiyanci.     Axuciyata nace"Wow! Plan dina yayi aiki,nasan tabbas baxan sha wata bak'ar wahala ba kafin na sami takaddar saki nah... "      "Fadima nace meye wannan ahannunki?" Ya sake tambaya. Mur! nasha,nace"Ai! wai tambayata mah kake?okay cokalin cin abinci ne....."      Na fadi hakan tare da tunkaran inda yake,jaa da baya ya soma yi yana fadin"A'ah Fadima wuk'ace fa nake gani ahannunki,meh zakiyi da ita? " "Au! na aza koh idanuwan mijin nawa sun dena aiki ne,ashe tunanina was wrong,the two eyes are still working tunda har ya gano wuk'a ce ahannuna...."     Dad'a tamke fuska nayi kamar ba Fadima meh sanyin xuciya da imani ba,nace"zancen kuma abinda xanyi da ita,so nake nayi gunduwa gunduwa da namomin jikinka idan har kaki bani takaddar saki nah......" Da tsawa yace"Ke Fadima! kinyi hauka ne? Kisan kai fa kike shirin aikatawa? Wai ni Fadima meya shiga cikin k'wak'walwarki ne?Dama ashe haka kike ban sani ba? Musa ah fuska sannan fir'auna azuci?"     Ni kaina nasan baxan iya aikata abinda nace ba,barazana ce kawai nake son na masa. Ban tankashi ba,kawai na nufi inda yake tsaye,da sauri naji yace"Tsaya Fadima karki k'araso don naga abin naki da gaske ne,kina iya aikata abinda kika fada,xan baki takaddar sakinki donni lafiyar jikina ya fiye min komai..... "      Ajiyar xuciya na sake,kana nace"Da kuwa ka shafawa kanka lafiya.... " Yace"Muje daki na rubuta miki don takadda da biro na ciki..... "     "Oya! shige gaba muje..... " na fad'a da k'arfi.Da hanxari yayi gaba yana meh daga hannayensa duka biyun asama kamar wani barawon da dan sanda yayi arresting.(hohoho! Fadima the seargent). Na take masa baya ina meh nuna wuk'ar adaidai saitin bayansa,shi kuwa lokaci xuwa lokaci yake dan waigowa yana dan dubana.     Babu zato babu tsammani naji kawai ya juyo yana k'ok'arin warce wuk'ar ahannuna,kokuwa muka soma yi,dayake k'arfin d'a namiji da 'ya mace ba daya bane,sae kawai yayi nasarar k'arbeta ahannuna.Ni kuwa ganin hakan yasa na sake kwasa aguje nayi kitchen din.        Wata kwalbace da ban san kota mecece ba na gani saman wata cabinet,wawurarta nayi,na nufi waje,adaidai Kofar kitchen din muka jame. Ba tare da wani b'ata lokaci ba na daga hannu na rotsa masa wannan kwalbar aka,ai kuwa ta sameshi agoshi.      Ji kake "Ahhhhhhhhh! Wayyo Allah,innalillahi wa'inna ilaihi raji'un Fadima kin kasheni......." Agigice na cillar da sauran fasasshen kwalbar daya saura ahannuna.     Fashewa da kuka nayi,nace"Wayyo! Allah na shiga uku na kashe mijina... " na fadi hakan ina meh k'ok'arin kai hannu na tab'a inda jini keta bulbulowa. Ture hannunta gefe yayi,da hanxari ya shige kitchen din ya kunna famfo,ya wanke fuskarsa gabaki daya har inda jinin ke bulbulowa,kana ya koma falo duk ina biye dashi ina kuka sae cewa nake ya yafe min,amma k'ala bece min ba.Keys din motarsa ya kwasa da wayoyinsa,yayi waje,nabi bayansa.       Kafin na k'arasa ga k'ofar naga kawai ya rufota tare da kulleta da padlock. Mahmood na fita waje,ya duba agogonsa,its to eleven.     Daga murya yayi yace"Mal.Bello yi sauri ka bud'e min gate...... " Da hanxari ya nufi motarsa,sae daya k'ira wani abokinsa dake aiki ah Aminu kano teaching hospital,yaci sa'a kuwa yana kan aiki ne,babu b'ata lokaci ya tada motarsa,yayi reverse,yana jin sanda Fadima keta girgiza kofa kamar xata ballata.     Ah 360 yabar gidan,Mal.Bello ya rakashi da "Yallabai ashe bakace bazaka sake fita ba? " Ina!! Mahmood ya riga ya masa nisa,maida Kallonsa yayi ga b'angaren su Fadimar,ahankali yace"Anya lafiya kuwa? Kai ban tsammani komai sumul yake ba don yadda Yallabai ya fice acikin mota atsiyace dole akwai ayar tambaya anan,Allah de ya kyauta.............. 📝      *HAFNAN*💞 *💘SHIN SO DAYA NE?💝* *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA* *WATPADD:HAFNANCY💞* *IG:Hafsy___mustee* ✨✨ *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE* 🌼BABI NA BIYAR🌼 *page 12-15* "Fadima I have to take us back,sabida yana da matuk'ar muhimmanci kiji labarin Zeey Maleek d'ita,jin labarin ne ze saka kisan yadda akai naji sha'awar son na aureki,amma kafin na cigaba da baki labarin pls let's eat first don yunwa nakeji sosae...." Ya fadi hakan tare da rik'e cikinsa kamar da gaske,so yake kawai ta d'an tab'a wani abin. "Ni bana jin yunwa,kaci abinka kawai,kuma ka min sauri........ " na fada atakaice ina meh hura hanci.Da mamaki naga ya bini da kallo,kana yace"Saurin meh kike ne baby doll? Remember from now on,we hav the whole moment to spend together for the rest of our lives,Fadima ina son ki sani cewar aurena dake Insha Allah mutu ka raba ne...... " Naso tanka masa amma kuma se naga idan na biye mishi zamu ta jan magana ne gwara kawai nayi shiru na bishi ahankali donna samu ya warware min zaren daya sak'a. "Ki sakko muci idan ba haka ba nima baxan ci ba kuma bazan baki labarin komai ba,kinji nace wallahi... " yanayinsa ya nuna sam babu alamun wasa atattare dashi,hakan ya sa ba tare da na tsaya wani dogon tunani ba na sakko sabida na k'osa naji takun basajar daya k'ulla.Shi da kansa ya firfito mana da abubuwan dake shak'e cikin k'atuwar ledar daya shigo da ita. "Baby doll wanne zakici aciki? Pizza ko garnished chicken🐓? Or u will like to take all?? " "Lallai guy din nan ya mugun raina min wayau ba kadan ba,wai ni yakeso ya yaudara da salon soyayyarsa ko meh?hadda wani *'Baby doll'*? ba damuwa duk kayi ka gama xan bika asannu don mu wanye lafiya." Hura min idanuwa naji yayi wanda hakan ya maidoni daga duniyar tunanin dana lula xuwa duniyar da muke ciki. "Matar Mahmood ya naga kinyi shiru? Ko so kike na baki abaki? Iyyeh fada min karki ji kunyata am ur husband.... " ya fadi hakan tare da kashe min one eyes. Dan guntun tsaki naja,nace"Bannaso ai nima ina da hannun da xan iya ciyar da kaina,garnished chicken🐓 din kawai xan iya ci.... " Murmushi naga yayi yace"An gama my all,bari na dauko plate" ya mik'e tsaye,naga ya nufi b'angaren dinning,ata gefen dining din naga ya bud'e wata kofa ya shige ciki,atake na gano nan ne kicin din gidan.Ji nayi kamar na arta aguje nabar gidan kafin ya fito,amma se kuma naga rashin dacewar hakan,sam yin hakan ba class dina bane,kuma ai ina son nasan ta yadda akai ya sami aurena,don haka be kamata na gudu ba,xan bari mu wanye ta salun-alum idan yaso hakan,idan kuma ta tashin hankali da kuma k'eta yakeso arabu,then Fadima Sa'ad is ever ready for that. Murmushin yaudara na sak'ar masa sanda naga ya nufo inda nake da plate ahannunsa.Cike da kissa da kisissina na mik'e na k'arbi plate din hadda wani duk'awa wanda hakan ba k'aramin mamaki ya bashi ba. "Dear ya naga plate daya kawai ka dauko? " na fadi hakan ahankali tare da lank'wasa murya. "Ah plate daya xamuci.... " ya fada yana kallonta cike da mamakin wannan sudden sauyawar tata,daga shiga kicin ya dawo har ta canza ta koma Fadimarta daya sani? Ko dai tunani tayi taga rashin dacewar abinda take masa da kuma maganganun da take ta kwakkwab'a masa? Ko ta haqura ta rungumi kaddararta ne? Axuciyarsa yace"No Fadima am not getting you at all... I guess you are upto something freakish & very mean... " Ni kuwa axuciyata nace"Dan iska mamakin canzawata yake,besan cewa so nake na lallab'ashi ya gayan komai sannan nasan nayi ba,hadda wani wai ah plate daya xamuci abinci,shege daga yau sae de kaci abinci ah kwano daya da uwarka ba dai da Fadima Sa'ad kuma ba.... " Sosae na sake jiki mukaci mukayi Kat! damu,mafi yawanci shi da Kansa yaketa feeding dina,ni kuwa sau uku kawai na bashi abaki ina meh cike da takaicin kaina. Bayan mun k'are cin abincin,naga ya kasa haqura yace"Baby doll wat happened? Wannan sudden change din nan taki am suprised fa?kodai u're upto something ne? " Murmushi meh ciwo na sakar masa,kana nace"No ba komai wallahi,ni de kawai kaban labari.... " Saukar da ajiyar xuciya yayi,kana ya soma bani labarin rayuwar soyayyarsu shida tsohuwar matarsa *Zaynab Maleek*,mace meh tsananin sonsa da tattalinsa,mace meh gudun b'acin ransa da son kowa nashi,wani abin nasu da idan ya fadi sae muyi dariya,wani kuma na abin atausaya musu ne yanda wai matar babanta ta sanyata agaba,ashe wai tun tana 'yar karamarta mahaifiyarta ta rasu.Ta taso ne ahannun matar babanta wanda sam ko kadan bata qaunarta,har tayi aure wani lokutan mah takan zo har gida idan baya nan ta lakadawa ita Zaynab din dukan tsiya ita da 'ya'yanta mata,yayun Zeey din.Dakyar da sudin goshi ya taka musu birki ya kuma sanya aka masu iyaka da gidansu.Gashi ita Zeey din tana da haqurin gaske,komai aka mata sae kaji tace"wallahi dear nah na yafe musu har cikin xuciyata. " Hakan ya saka Zaynab ta sake samun gurbi acikin xuciyarsa,sae ji yake kamar duk duniya babu ta biyun Zeeynsa,baya jin ze iya rayuwa da wata 'ya mace face Zaynab dinsa ko bayan ranta. "Sae gashi rana daya na k'aryawa Zeey dita alkawarin dana daukar mata,yau gani ga wata 'ya macen amatsayin *'Matata'*, *'Matar Mahmood din Zaynab Maleek'*... Fadima ranar dana soma ganinki alokacin da kuka kawo ta'aziyya kano,aranar se dana danyi jinyar xuciyata,don ganinki ya tuno min da Zaynab dita,everything about you was juz lyk hers,infact! hatta kamanninki da nata yanaso yayi iri daya.Ah yinin ranar na lura sosae na kamu da matsananciyar sonki,why? Because gani nake kamar Zeey dita ce ta dawo. "Titsitseyar Hanan nayi,na sakata dole ta bayyana min alak'ar dake tsakaninki da Mubarak wanda ko kusa banso hakan ba,naso ace babu alak'ar soyayya atsakaninku,kuma wallahi banso kika bishi wani gun ba,Fadima sam be kamata ace amatsayinki ta 'ya mace musulma, kuma kamilalla kiyi trusting namijin da baki taba sanin halayyarsa,ki yadda dashi kai tsaye har ki bishi for only Allah knows inda zai kaiki ba,wannan abin ba k'aramin sosa xuciyata yayi ba,amma se na batsar nace toh wai ni miye nawa da damuwa akanki? Ai ke kika kai kanki,duk da cewar na yadda da kanina sam ba mazinaci bane,amma ban san meyasa na kasa sakewa da fitarku tare ku biyu kadai ba,ashe de sonki nake ban sani ba,koda naje gida kasa xama nayi,naji kamar na sanya k'iransa na rufeshi da fada akan ya maido dake gida,amma se naga zagewar zatayi yawa and he might get to suspect something." Jan gwauron numfashi yayi kana yace "Na takaice miki labari,dawowa nayi na xauna jiran dawowarku awaje,ita Hanan duk ta tsure duk aganinta tashin hankali xan haifar sanin da tayi na cewar mahaifiyarmu bata qaunar wani acikinmu yayi tunanin qara matar aure,aganin ita Hanan din xan taya Mummy hukunta Mubarak ne,na nuna mata cewar karta damu ba wani tashin hankali xan haifar ba kawai Fadimar ta min kama da wata wacce na sani ne.Kamawa daga wulaqancin da mummy tayi wa 'yan'uwanki,da korosu waje da tayi duk akan idanuwana ne,koda naje ina bata haquri zageni tayi tass! ta ajje agefe wai har ni ina da bakin magana? Ai gwara Mubarak din tunda shi yayi tunanin qaro aure amma ni fa? dayar mah na gagara ajjewa ina nan kamar wanda aljana ta aure,sae kace kaina farau aka soma yiwa mutuwa. Maganarta daya fi sosa min rai har ya saka na dan zubda kwalla shine wai,da alamu haka xan k'arashe rayuwata babu magaji,wanda ze dunga daga hannu sama yana min addu'ar samun rahamar ubangiji,sae de nata daukar 'ya'yan abokaina ina sha'awarsu,hakan data fada shi ya k'ara min kaimi da kuma k'warin gwiwar gwada sa'ata awurinki,ban damu da cewar ke din budurwar kanina bace,burina kawai nasan ta yadda xan bullo miki har na samu shiga awajenki,because nima ina buqatar asake sona,I want to share dat love again with someone,Fadima I really want to see my own children,kuma ke kadai ce naga kamar Kinfi dacewa da rayuwata shiyasa nayi tunanin xuwa gareki,nabi bayanku don nasan gidanku,koda naga motarku ta lalace,sae na samu wuri nayi parking adan nesa daku don Kar nayi saurin tunkaranku ku d'ago wani abin.Sae dana dan ja lokaci kuma na tabbatarwa Kaina lallai bazaku dago ba sannan na tunkareku." Anan Mahmood ya baiwa Fadima labarin komai na yadda akai yata fama da xuciyarsa da kuma kokarin son ya yakice soyayyarta acikin xuciyarsa,amma hakan ya faskara,akan dole yabi son xuciyarsa,ya kudura aransa cewar dolene ya baiwa xuciyar abinta takeso. Yace"A.B.U Zaria ta dade tana aiko min da request akan suna matuk'ar buqatar nazo na dunga aiki dasu,don suna da labarina yadda nake da basira da kuma fasahar sarrafa na'ura meh k'wak'walwa,I hav turned down their requests on several occasion,ganinki ya saka ni da kaina na aika musu da sak'on amincewata da offer dinsu,wanda tsananin murnar hakan ya saka suka bani k'yautar wata madaidaiciyar gida don nuna godiyarsu agareni.Ni kuwa gani nayi rayuwata xata dawo sabuwa dal kamar an ciro daga kwali,xuciyata fes! raina yayi haske ganin nayi close dake,wani abin dadin dadawar kuma,wai kema A.B.U kike schooling, hakan yasa naci alwashin bazan tab'a wahala wajen shigar da kaina gareki ba,xanyi kokari naga na koya miki yadda zaki soni,sannan daga baya na aureki kota halin k'ak'a. " Ya bata labarin yadda sukai tayi da Mubeen,yadda Mubeen din keta nemarta awaya baya samunta da kuma yadda yayi masa karyar wai sabuwar wayace take jira,da kuma hana masa xuwa Zaria da yayi don dubata,da kuma wucewarsa India da dramar da kullum suke sha awaya. Yace"Wallahi ko jiya mah se daya k'ira amma naki dagawa.... " Afusace na mik'e nace"Agaskia Mahmood kaci amanar Mubarak ba kadan ba,Allah sarki bawan Allah inata tunanin kila dama can yaudarata yake baya qaunata shiyasa be damu yasan halin da nake ciki ba,ashe abinda ban sani ba,kai kana can kana shuka masa bishiyar k'arya har tayi nasarar tasiri da kuma girma acikin xuciyarsa,why? Because ya yadda dakai,yasan bazaka tab'a masa k'arya ba,Mahmood meyasa zaka ci amanar Mubarak? Why? Meh yayi maka arayuwa da har zakayi tunanin ramuwar gayya irin wannan? Kamar yadda kake ikrarin kana sona,toh wallahi Mubarak ya fika sona sau dubun dubanni,ka kuwa san irin tashin hankalin da kake kokarin haifarwa acikin zuri'arku? Ka tab'a tunanin cewar anya xuciyarka ta maka adalci wajen sona kuwa? Tukunna mah de gaya min wanene *'BABA MU'AZZAM'* agareka,sannan kuma ina family dinka suke da akayi wannan auran?" Jikin Mahmood ne yayi sanyi qalau kamar kankara,ahankali ya bud'i baki ya cigaba da mata bayani"Baba Mu'azzam shima family dina ne ba hayarsa nayi ba kamar yadda kike tunani,k'anin mahaifina ne,shak'ikinsa kuwa,ma'ana ciki daya suka fito da mahaifina,matarsa daya itace Haj.Fa'iza wacce akafi sani da 'Mami',ya'yansu biyar kuma duk mata,Zaliha itace ta farko wacce take kusan sa'ar Maryam (Meema) qanwata,nasan kin ganeta don da aka kawoki mah tana gidan,tana auran wani dan sanda ne anan kanon,sae Zaineema meh bi mata,ita kuwa sa'ar Usman kaninmu ne,ita kuwa tana aurene ah katsina,ita bata zo bikin ba amma nasan yan'uwanta sun gaya mata,sae meh sunan Kaka rigima wacce ake k'ira da 'Afreen',ita kuwa sa'arki ce,sae Hafeezah sa'ar Suhaima,sannan auta Rafi'ah.Sanda kika fada min cewar ai mahaifinki shine chief justice ta yankin federal high court Zaria,sosae nayi murna don na sanshi da dadewa,Baba Mu'azzam ya tab'a zuwa dani wurinsa sau daya ah office dinsa,mahaifinki abokin baba ne sosae don ta sanadiyyarsa ya samu aikin alk'alanci,lokaci daya sukaje nemar aikin,se akace mutum daya kawai za'a dauka,anso daukar Baba ne amma se kuma yaga kamar abokinsa Sa'ad ya fishi buqatar aikin,se ya haqura ya bar masa,shi kuma ya tafi ya soma kasuwancinsa kadan da kadan har Allah ya sanya albarqa,ya tallafa masa ya habbak'a kasuwancin nasa ta man fetur.Sosae justice ke ganin mutunci da kuma darajar Baba don aganinsa ya taimaki rayuwarsa ba kadan ba,sati daya da soma aikina ah A.B.U naje office din mahaifinki,sosae yayi murnar ganina don ya shaidani,bayan yan gaishe-gaishe,na gabatar masa da kaina amatsayin meh sonki da aure,dan Jim yayi yana tunani." (Alokacin tunani yake akan Haidar kada ya watsa musu k'asa ah ido don bazai iya hana dan Baba Mu'azzam auran 'yarsa ba,kawai zeyi tunani akan hakan) "Ni kuwa gani nayi kamar bazan samu abinda nakeso ba,atake anan naji gwiwowina sunyi kasa,can ya karbi lambar wayata tare da ce min zeyi tunani akai. " (Bayan kwana uku da ganawarsa da Mahmood,shine al'amarin su Fadima ya bullo,ya danyi murna da hakan,kenan ai Haidar bazai ce an watsa mishi kasa ah ido ba,yanxu yana da damar baiwa dan Alh. Mu'azzam auren Fadimar don kwarai ya yaba da hankalin Mahmood). "Bayan kwana biyu sae ga k'iran Baba Mu'azzam wai yana son ganina,koda naje sosae ya nuna min murnarsa na samo 'yar gidan mutunci da tarbiyya amatsayin wacce nakeson na aura,wai justice na musamman ya kirashi ya labarta masa komai tare da bada go ahead din aturo,toh anan ne na rokeshi kan don Allah kada asanar da mahaifiyata don bata qaunar yarinyar,sannan kuma kada ayi wata gayyata don kada maganar ta bazu har ya isa kunnanta,sosae yayi mamaki da zancena har yace shi baze goya min baya nayin auran nan ba har se naje na nemo izinin mahaifiyata da kaina,rok'ansa nake tayi harda kuka akan ya taimaka ya shige min gaba na samu na aureki Insha Allah bayan auran sae asanar da mahaifiyar tawa,dakyar da sudin goshi ya amince ya shige min gaba don shi kansa yana bala'in son wannan hadin har ransa,toh kinji-kinji yadda akai na sami auranki,sannan ko daya acikin yan'uwana babu wanda yasan da wannan auran hatta shi Mubarak din........ " Kallonsa nake cike da tsanarsa da kuma k'yamar hanyar daya bi ya aurena ba tare da samun albarqan mahaifiya akan wannan auran ba,hawaye sae bulbulowa suke saman kuncina babu gaggautawa,kuma ko kadan ban damu nasa hannu na sharce su ba...............📝 A/N Ga alqawarinku nan na cika,Insha Allah zaku dunga ganin update kullum as frm now on!!! *HAFNAN*💞 *💘SHIN SO DAYA NE?💝*       *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION🖊* *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART  TORCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔      *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*         *WATPADD:HAFNANCY💞*           *IG:Hafsy___mustee*                             ✨✨ *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*            🌼BABI NA BAKWAI🌼 _*please kindly show me some love by voting & commenting to let me know dat u guys are really enjoying the novel*_       *page 18-20* _"Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla,wa anta taj alal hazna iza shi'ita sahla...... "_addu'ar da nake ta nanatawa kenan babu gaggautawa sabida wani irin radadi da naji xuciyata ke min.Ina addu'ar ina hadawa da dukan kofa,alokaci daya kuma ina meh rera kuka kamar raina ze fita.Xuciyata cike take da nadamar abinda ta aikata. "Mahmood don Allah karka tuka mota da kanka acikin irin wannan halin daka fita,don Allah ka bari ni da kaina nazo na kaika asibiti,pls dear nah am really sorry forgive me...... " Na sake rushewa da wani sabon kuka ina meh cike da jin haushin kaina na abinda na aikata.Ina jin sanda ya tada motarsa ya fice atsiyace daga gidan. Shi kuwa Mal.Bello k'asa kunnuwa yayi yana sauraro don yaji kamar bugun k'ofar cikin gidan ake da k'arfin gaske kamar za'a ballata.Da hanxari yayi ciki yana fadin"Oh! ni Bello dan Abu wai meke faruwa ne? " Koda Mal.Bello ya iso sae gani yayi an garkame k'ofar da k'aton kwado,windunan dama arurrufe suke ta ciki,kuma labulayen asauke suke,don haka duk wani kukan kuran da Fadima take ba'a jin komai. Mal.Bello dai ya tabbatarwa kansa da lallai babu lafiya yau agidan,daga kawo sabuwar amarya kuma sae tashin hankali tun ba'a kwan ba?ina kuma uban gidan nashi zaya je acikin daren nan da har ya rufe wannan baiwar Allahn aciki sannan yayi ficewarsa cikin mota atsiyace kamar ze tashi sama? Toh kodai wani laifin ne ta masa da har ya kasa hak'uri har gari ya waye shine ya tafi kai k'ararta gidan iyayenta? k'ara k'arfin girgiza k'ofar da tayi ne ya dawo dashi daga duniyar tunane-tunanen daya lula ciki. Duk da cewar yasan ba wai jinsa zatayi ba,amma still ya daure yace"Hajiyata hak'uri fa zakiyi ya dawo ya bud'eki da kansa,addu'ata agareku shine Allah yayi muku tsari da shed'an,ya kauda fitina atsakaninku,sannan kuma ya baku zaman lafiya.... " Ya juya ya koma bakin aikinsa yana d'an raye-rayen wakokinmu na gargajiya yana meh cike da al'ajabin wannan al'amarin. Fadima meh kika aikata?kin kuwa san idan wani abin ya sameshi you will definitely be held responsible?meyasa ke bazaki rungumi kaddararki ba kamar yadda kowa keta baki shawarwari akan hakan?shi kansa idan kin lura dashi cike yake da nadamar hanyar daya bi ya sami auranki ba tare da saninki ba,amma duk da hakan ya yadda da kaddararsa,maganarsa gaskiyace dayace *'MATAR MUTUM KABARINSA'*,kenan wani baya tab'a auran matar wani,haka mah wata bata tab'a auran mijin wata se dai idan har Allah ya kaddara. Toh ita wacece da har bazata rungumi kaddararta ba?wace 'ya macece mah da har zata ga *'MAHMOOD NAKOWA'* bata ji sha'awar son ya kasance mijinta ba sabida haduwarsa da kuma iya tattalin mace?komansa ah ilimance yake yinsa,ji bi yadda yake ta ankarar da ita idan ta nemi k'auce hanya,kenan bayan ilimin boko,na arabi mah ya gama ratsashi? Wani irin zazzafar soyayyarsa ce taji ya soma kai mata cafka acikin xuciyarta,da sauri ta kai hannu ta danne daidai saitin xuciyarta,ahankali tace"Mahmood wallahi na haqura ka dawo wallahi xan gaya maka cewar na haqura xan xauna dakai,zan fada maka cewar na soma jin sonka araina,kuma xan gaya maka cewar am also fully ready to face any problem coming soon frm both Mubarak & the rest of ur family members....... " Wani kuka ne naji ya kufce min,ina yi ina cigaba da sambatuna,kaina naji yayi min wani irin girma,ga wani ciwon da yake min alamun kukan da nake ne ya haifar min da hakan.Sassauta kukan nayi don kada na janyowa kaina wani sabon ciwon don ban gama warkewa ba.Idan naji wani motsi awaje saurin mik'ewa nake na nufi Kofa wai azatona ko Mahmood ne ya dawo. Ji nayi kamar na sanya k'iran Umma na fada mata halin da nake ciki amma kuma se naga dare ya lula,ayanxu haka duk inda take tana tare da Abba,kuma bazanso yasan halin da nake ciki ba,yanke shawarar k'iran Ash nayi wacce ko dan flashing bata min ba tunda suka koma. (Dayake aranar da za'a kaita Abbanta ya maida mata da wayarta tare da zuba mata sabbin layuka biyu aciki). Bugun farko akace min switched off,ba tare da b'ata lokaci ba na latso dayar layinta wanda acikin wata k'aramar wayarta ta saka wannan layin,shima switched off aka ce min.Ji nayi kamar na aza hannuwana duka biyun aka na kurma uban ihu,can baya ada,rayuwata nake cike da jindadi da walwala,sam ban san wata rayuwar kunci da damuwa ba,amma shigowar Dr.Mubarak Nakowa da kuma Engr.Mahmood Nakowa ya kawo min canjin rayuwa,suka sauya min rayuwa xuwa zallar damuwa da kuma kuncin rayuwa. *** Ita kuwa Ash tasan tabbas Fadima ta riga tasan Mahmood shine mijinta tun kafin mah su baro kanon,kawai tasan taki tada wata rigima ne acikin jama'a,tafi son sae sun keb'e,toh tasan muddin idan suka rage su biyu dole Fadimar zata nemeta awaya,dalilin daya sanya ta kashe wayoyinta gabaki daya kenan tunda suka dira Zaria. Zuciyarta cike yake da damuwa da kuma tsananin son tasan halin da Fatin tata ke ciki. Ahankali ta furta"Yah Allah ka sanyaya xuciyar Fateenah aduk halin da xata tsinci kanta,kasa ta haqura ta rungumi *'MIJIN KADDARARTA'*,ya Allah na rokeka,ka wanzar da zaman lafiya tsakanin Fadima,mijinta da kuma danginsa....... " Haka de ta cigaba da kwararo addu'o'i wa Fadimar tata,daga bisani ta shafa,dama nafila raka'a biyu tayi,sannan ta zauna tana zubawa Fadima addu'ar samun zaman lafiya da mijinta da kuma danginsa.Can ta mike tana duban agogon dake manne asaman bango,taga 10:35pm,zuciyarta ce ta soma ingizata akan ta latso Fadima,amma sae ta danne taki kunna wayar,tabi lafiyar gado ta kwanta,ba'a dau wani tsawon lokaci ba,wani nannauyar bacci yayi awon gaba da ita. _Ashwairiyyar Bash asubahi ta gari_ *** *✨AMINU KANO TEACHING HOSPITAL✨* *11:10pm* "Subhanallah!!... wai ni babban mutum meya ji maka wannan raunin ne haka? Wallahi karka so kaga yadda ciwon yayi rami sosae.... " Dr.Jabir ne yayi wannan maganar sanda yake wanke wa Mahmood rauninsa da spirit. "Kaga Jabir,idan har zaka wanke min abu toka maida hankali ka wanke bana son neman jin ba'asi,nace maka tsautsayi ce kawai ko kunnuwanka sun toshe ne? " yayi masa wannan tambayar cikin hargowa. Kwantar da murya Dr.Jabir yayi yace"Allah ya huci xuciyarka abokina, ni damuwa nayi da wannan situation din naka amma tunda baka son tambaya,kayi haquri bazan sake ba.. " Sae duk Mahmood yaji ba dadi,amma kuma kala bece masa ba har ya gama wankin,ya lik'a masa k'aton cotton wool awajen,sannan ya manna plaster asama don ya agaza ya rik'e wool din. Yace"Allah sarki da'ace Dr.Mubarak nanan da shine ze k'arbi wannan aikin don nasan baze tab'a bari wani yayi in bashi ba.... " Gaban Mahmood ne ya bada ras!! jin an ambaci sunan 'Mubarak'. Axuciyarsa yace"Kode ze mah k'ara lalata abin? Kila mah ciwon ze dada caccakawa da kwalbar daga bisani ya aika dani barzau in har akan Fadima ne...... " Azahiri kuma ignoring dinsa yayi,yace"Malam kana da damuwa wallahi ka cika hayaniya,pls nawa ne kudin aikinka? " Dr.Jabir ya bushe da wani irin dariya yace"seriously yanzu sae na karbi kudi daga hannun babban mutum kamarka?haba idan nayi hakan ai na cika babban butulu mara tunani,kai dai jeka kawai fatana Allah ya baka lfy ya kuma kiyaye tsautsayin gaba.... " *'BABBAN MUTUM'* sunan da Dr.Jabir ke kiransa dashi kenan,wai don Mahmood din akwai kirki sosae,tausayi,mutumci,iya mu'amala da mutane,da sauransu,shiyasa ya cancanci da ah kirashi da *'BABBAN MUTUM'*, sae de ance dan'adam tara yake be cika goma ba,matsalar Mahmood daya,wato miskilin k'arshe ne na gidan gaba kuwa,sam baya wani cika son hayaniya,idan kaga ya zage yana hira,toh kuwa tabbas da Zeeynsa ce,gashi yanxu itama Fadima tana kokarin samin wannan matsayin na Zeey.gashi da shegen zurfin ciki,sam bashi da abokin shawara,kai tsaye yake aikata duk abinda ransa yaso,shiyasa acikin duka friends nashi mah babu wanda yasan ta yadda akai ya auri Fadima,su de kawai zancen auren ne suka ji daga bakinsa. Murmushin jindadin xancen Dr.Jabir yayi,kana yace"Shikenan nagode Jabir,bari naje dare na k'ara lulawa,sae da safe.... " Ya kwashi keys da kuma wayoyinsa daya xuba saman wani table,adaidai lokacin kuma Dr.Jabir ya mik'o masa wata 'yar farar leda. Cike da rashin fahimta yace"And wat is in? " "Maganin pain reliever ce ke aciki.... " B'ata fuska yayi sosae yace"Amma kasan de tun ina karamina na tsani shan tablets ko? Shine don iskanci zaka wani xuba min aleda? Gaskia ka barshi bazan sha ba,tunda ka wanke raunin its okay kawai..... " Babu yadda Dr.Jabir beyi da Mahmood ba,juyin duniya yaki karba don shi arayuwarsa ya tsani ace yasha magani,gara-gara na gargajiya yana iya sha,amma na bature sam baya sonta,haka mah idan baya da lafiya ya gwammace ayi masa allura da ace masa yasha magani. Sallama yayi wa Dr.Jabir ya fice,shi kuma ya rakashi da"Ace wa amarya muna nan xuwa mu kwashi girki.... " Ai! tuni ya b'ace masa amma ya tabbata yaji abinda ya fada. Murmusawa yayi yace"Kai Mahmood wallahi wani irin bahagon mutum ne meh dan wuyar sha'ani,idan baka xauna ka fahimci rayuwarsa ba,kana iya zaton ko sam baya ganin darajar dan'adam,amma abin ba haka yake ba,he's juz too simple but difficult to understand..... " ✨✨✨✨ Wata k'awar mominsu Mahmood wacce take zaune unguwa d'aya dasu Baba Mu'azzam ce ta k'ira ita Momin awaya take kala mata xancen auren Mahmood wanda shi Baba Mu'azzamun ne ya shige masa gaba. Wata irin zabura ce Momi tayi kamar wacce aka manna mata shocking tare da dafe k'irji da k'arfi,tace"Dakata Rabi..... wannan wacce, irin xancen banza ce kike min haka?taya za'ai Mahmooda nah yayi aure ba tare da sanina ba?taya mah za'ai Mu'azzam ya shige masa gaba ba tare da nemar izinina ba?" Haj.Rabi tace"Haba Binta meh zan tsinta acikin k'arya face zubda girma,daraja da kuma mutunci?kin tuna da wannan kawar tawa Haj.Nera?"       "Eh eh na ganeta...... " momi ta fada tana meh daga kai da sauri-sauri kamar Haj.Rabin na gabanta ne. "Toh ai k'awar haj. Fa'iza matar Mu'azzamun ce,aminai ne sosae,kuma komai na haj.Fa'iza ita Haj.Nera ta sani,toh ita Neran ce tazo har gidana take fada min donni ban mah sani ba,wai daga wurin walimar auran take wanda akai acikin gidan Alh.Mu'azzam,toh anan take kala min gashi-gashi,wlh da farko na k'aryata xancen akan cewa babu ta yadda za'ai ah b'oye miki xancen auran,rantse-rantsen da take tayi ne ya sanya na yadda da ita don Haj.Nera idan har kaga ta kuke da rantse-rantse toh kuwa xancen gaskiyace take gaya maka,shine nace bara na k'iraki na d'an fesa miki zancen,amma don Allah karkice ah bakina kika ji............. "     Da hanxari Momi ta tari numfashinta"Dalla can rufemin baki anan,munafukai kawai masu bacci da ido daya,ana ruwan sama suna k'irgawa,'yan adawa da kuma hana ruwa gudu,wato yadda kuke ganin d'ana ke samun cigaba arayuwarsa shine kuke bakin ciki,kuke masa hadassa da k'yashi,soyayyar dake tsakanina da dana shine kuke bakin ciki,kuke kokarin so ku shiga tsakaninmu,toh kuwa da sakel,Haj.Rabi kin shayar dani madaran mamaki,da har kika shiga sahun masu mini hassada..... "     Cike da mamaki haj.Rabi tace"Haba Binta wannan wacce irin maganace kike haka?taya zan shiga tsakaninki da danki?taya zan masa hassada kan cigaban da yake ta samu arayuwarsa? Nifa na gaya miki babu abinda zan tsinta acikin k'arya face zubda girma da daraja,idan har baki yadda ba toh kiyi bincike,Haj.Fa'iza tace zasuyi kusan sati uku agidansa nanan kanon kafin su koma Zaria inda yake aiki,ita kuma take karatunta,don haka kije kiyi bincike da kanki,amma don Allah idan har kika ga zancena ya tabbata gaskia,na hadaki da Allah karkice ah bakina kika ji...... "     Bata jira taji ta cewarta ba tayi saurin datse call din cike da jin haushin zazzafar kalaman da Haj.Binta ta jefeta dasu. Haj.Rabi kenan akwai shegen gulmace-gulmace nakin karawa kuwa,sae da Haj.Nera ta rok'eta akan tayi shiru da bakinta,har ta dau mata alqawarin cewar babu wanda ze ji zancen,har da ce mata ah inda ta gaya mata toh anan wurin zata watsar da batun.Taso din tabar wa cikinta zancen,amma dayake meh hali baya fasa halinsa,zancen har tsingulinta yake tayi shiyasa ta yanke shawarar fesawa Haj.Binta.     Haj.Binta kuwa jiki ah sab'ule ta koma da baya ta zauna agefen gado,alokaci d'aya ta rasa abinda ke mata dadi acikin duniyarta.Taya mah za'ai Mahmood yaje kai tsaye yayi auransa ba tare da saninta ba? Taya kuma za'ai Baba Mu'azzam ya shige masa gaba ba tare da an nemi izini daga gareta amatsayin mahaifiyarsa meh kuma iko akansa ba? Idan kuwa zancen Haj.Rabi ya kasance gaskia,tabbas zataso jin dalilin b'oye mata zancen auran kafin ta dauki duk wani mataki daga baya.Taso latso Mahmood din taji daga bakinsa amma kuma tafi son taje masa abazata ta gano gaskiyar lamari da ganta.     Da rawar hannu ta lalub'o wayarta ta latso babbar d'iyarta Maryam (Meema).Ta kora mata zancen nasu da Haj.Rabi. Dama duk acikin 'ya'yanta Meema tafisu sanyi da kuma kauda kai kan abubuwan da basu taka k'ara sun k'arya ba.     Cikin sanyinta tace"Hajiyata nasan idan mah hakan ta kasance gaskia,toh tabbas Yah Mahmo bazai tab'a rasa dalilin b'oye miki ba,don Allah hajiyata ki masa uzuri ki kuma fahimci dalilinsa if dat happened to be true..... " "Ke dallah rufe min baki marasa tunani kawai,ai duk daga ke har shi din halinku daya,matacciyar xuciya gareku sam bakwa da kawa zucina kamar yadda nake dashi akanku,har ke kin isa kice kada na dauki mataki idan har hakan ta kasance gaskiya? Toh! sannu Haj.Hafsatu uwata.... "    "Haba! Hajiyata ki baiwa zancen nawa k'yakk'yawar fahimta..... " Da sauri tace"Saurara min nan kafin inci ubanki,gobe k'arfe bakwai ta muku anan gidan sannan mu dunguma xuwa gidan nasa muje mu ganowa idanuwan namu,kuma kada wata ta sake acikinku ta k'irashi ko baba Mu'azzam din har se munje mun ganowa idanuwanmu,kina jina ko? "     "Ehh! naji bayananki duka.... " Bata sake wata magana ba ta katse call din,kai tsaye ta latso autarta Khairat ta kora mata zancen itama.     Dama Khairat sam bata haquri kamar zawo take,duk acikinsu tafisu d'aukar Zafi da abu sosae. Cewa tayi"Kan babban burauba,Momi shine baki soma ci mana ubanta awaya ba kafin ku had'e?Fisabilillahi Momi taya za'ai Yah Mahmo yayi aure ba tare da saninmu ba har Babansu Zali ya shige masa gaba duk bamu sani ba? Kawai so ake ashiga tsakaninmu dashi,karki damu gobe kafin bakwai mah na iso gidan sae muje mu binciko kamar yadda tace,amma idan har zancenta ya kasance k'arya ne toh wlh Momi har gida zamuje muci mata mutunci....."    Cike da farin cikin zancen 'yar tata tace"Nagode 'yata nasan ke da Labeebah ne kawai zaku iya goyar min baya..... "      Haka ta k'ira Labeebah,itama din kamar Khairat din tayi,ta lailayowa wani uban ashar ta gundumawa Haj.Rabi,tare da tabbatarwa Momin da cewar itama din kafin bakwai tana family house. Sae kai komo kawai momi ke tayi adakin baccinta,kallon agogo tayi taga 10:45pm,ji tayi kamar ta sanya hannu ta tura sandar agogon xuwa karfe bakwai na safe............. 📝     A/N Ghen!Ghen!!Ghen!!!.... Nakowa's family fire on the mountain in a bit🔥🔥🔥     Can't wait. *wait! Karku ce min har kun manta da batunsu mal.Gaddafi? Jinns din Rukky Lema? *Ina labarin daren Farkon *Suhaileedar?* *Ina labarin Mubeen mijin Hauwa'u Jiddoh?     step-by-step zamu bisu,ku dai ku cigaba da kasancewa dani.           *IT'S*                  *YOUR* ❤❤                     *LADY*       *HAFNAN💞* ,    *💘SHIN SO DAYA NE?💝*     *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*       *WATTPAD:HAFNANCY💞*        *IG:Hafsy___mustee*                        🌠🌠 *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*            🌼BABI NA HUDU🌼    *Page 9-12*          Har Baba ya kare jawabinsa da nasiharsa agaremu kan zaman aure da haquri da juna,ban tsinci komai ba don gaba daya hankalina ya tafi ne ga tsananin mamakin yadda akai Engr. Mahmood ya aureni,da kuma sunan k'aryar da yayi amfani da ita wajen aurena wato *'MAHMOOD NAKOWA'*.         Taya mah xan soma tunanin xaman aure da wan saurayina? Taya kuma xan soma tunanin had'a idanuwa da Mubarak axuwan k'anin mijina?shi kuma ya dunga min kallon  matar wansa?Sannan wani irin tashin hankali ne xa'ayi idan har Mubarak yasan cewar wansa ya aureni? Nasan tabbas zeyi tunanin cin amanarsa nayi bayan ko kadan bani da masaniya akan faruwar hakan.Wallahi wallahi da'ace nasan cewar Engr. ne wanda mahaifina keta burin aura min da wallahi baxan tab'a bari ayi wannan auran ba,na gwammace koma meh ze faru ya faru amma baxan taba cin amanar Mubarak ba. Se de kuma hausawa sunce *'RASHIN SANI YAFI DARE DUHU'*.... Aikin gama ya riga da ya gama,baxan iya maida hannun agogo baya ba,amma nasan ta yadda xanyi na raba auran nan bayan na gama jin dalilinsa na aurena.........      Allah-Allah kawai nake wannan munafikin tsohon kilakin ya gama xancen soki burutsunshi sannan mu saka kafa mubar gidan don na samu na aiwatar da kudirin dake cina arai. "Fadima tunanin meh kike?tashi ku je dare nayi Allah yayi muku albarqa.... "      Maganar Baba ne ya dawo dani daga duniyar tunanin dana Lula.Da hanxari na mik'e donna k'osa mu bar gidan.Su Mami ne suka mana rak'iya.Hafeezah ce rungumeni dani har muka isa waje inda yayi parking motarsa.        "Fadima Allah ya tsare,sae munzo ganin dakin amarya.... " Mami ce ta fadi hakan sanda na daidaita xamana ah kujerar meh xaman banza.Hakan ya bani tabbacin Lallai Zariar zamu tafi da daddaran nan.       (Ni kuwa nace sorry Fadima xakuyi 3weeks agidanki na nan Kanon dake 'court road').     Axuciyata nace"kafin kuzo ganin gida Fadima ta ware don baxan tab'a iya xaman aure da wan saurayina ba..... " Har muka bar unguwar muka haye saman titi babu maganar data shiga tsakanina dashi.Xuciyata se tafarfasa take tare da min wani mugun zogi.     Shi kuwa Engr. Sam ya kasa sakewa da wannan shirun da Fadimar ta masa,yasan tabbas shirun nata bata banxa bace,dole akwai abinda take shiryawa aranta.Sae daya tsaya kan hanya ya siya musu gasasshiyar kaza,pizza da kuma youghourt masu sanyi na roba. Sun kusa da 'court road' yaga shi de ya kasa haquri da wannan shirun nata,yana son ko 'yar zagi ce ta masa ko ze dan sami sassaucin abinda ke damunsa aransa.      Ahankali yace"Fadima pls speak for Allah's sake,kiyi magana don tabbas na b'ata miki,ki zageni,ki mareni idan hakan ze saka ki huce kan abinda aka miki..... Zahra'u cry out loud idan har hakan ze saka ki samu sassauci na abinda kike ji agame da cin amanar da nayi muku....... " Ni kuwa kamar dama jira nake abani umarni,kawai sae ji nayi na rushe da wani irin kuka meh tsuma xuciya.     Cike da rawar murya yace"Fadima weep weep,ki kara da dukana wallahi I won't stop you idan har hakan ze saka ki yafe min abinda nayi miki............" K'ara volume din kukan nayi,amma K'ala bance masa ba.Shi kuwa har cikin ransa yake jin wannan kukan nata,ji yake kamar ana caccaka masa allura adaidai saitin xuciyarsa na wannan kukan da takeyi,sae ayanxu yake jin haushin kansa na kuntata mata da yayi.    Beyi yunk'urin hanata kukan ba har suka iso gidan. Mamaki ne ya kusan kasheni ganin  ya shigo damu wata unguwa instead of Zaria da nake ta saka ran can muka nufa.Ban gama shanye mamakina ba kawai naga yana xuba uban horn awani tangamemen gida.Ba'a dau wani tsawon lokaci ba naga an wangame mana gate din gidan,da hanzari naga ya danna hancin motar ciki.       Tsaida kukana nayi ina dubarsa cike da mamaki,ahankali nace"Ina ne nan kuma ka kawo ni? Ina aza ko Zaria muka nufa ah daran nan? " "Nan din mah gidanki ne,kuma aciki zaki xauna harna tsawon sati uku kafin mu koma can Zariar...... Kuma kada ki samu wata damuwa akan kayar sawarki don komai da zaki buqata yana nan gidan already....."     Ad'an tsiwace nace"What?? Ka dauka cewar xanyi xaman aurene dakai? toh idan mah hakan kake tunani toh tun wuri ka canza tunaninka,idan kuwa mafarkin hakan kake toh tun wuri mah ka farka don Fadima Sa'ad bazata tab'a xaman cin amana ba da wan saurayinta,bazan tab'a goya maka baya muyi kazamar rayuwar nan ba,abin tirr! da kuma Allah ya wadai...!!!....... " Kuka yaci k'arfina.Ji kake kiiiiiiii!!! yaci wani wawan birki awurin parking lot.     Idanuwansa sun kada sunyi jajur dasu kamar jan gauta,maganganun Fadima sun sosa masa rai ba kadan ba.        Axuciye ya nunata da 'yar yatsa"Karki sake bakinki ya kuma gangancin kazanta aurena dake,zan iya juren komai da xaki min amma bazan juri tsaya kallonki kina kazanta aure sunnar ma'aiki ba...idan ke baki yadda da kaddara ba,toh ni as a good Muslim na yadda da ita,shi de aure nufi ne na ubangiji,matar wani bata tab'a auran mijin wata,haka zalika mijin wata baya tab'a auren matar wani..... Kenan 'matar mutum kabarinsa',dama can Allah ya riga ya kaddara cewar dole sae kinyi soyayya da 'kani' kafin daga baya ki auri 'Wansa'......."        Axuciye nima nace"Amma hanyar daka bi ka samu aurena sam bata dace ba,wannan sam ban yadda wai kaddara bace,kawai son xuciyace aka bi...... " Baki bud'e yake kallona,kana yace"Subhanallah! Fadima kada b'acin rai ya saka kiyi babban sab'o! kada ki bari ki tauna maganganun da zaki saka Allah SWT yayi fushi dake... "      Sabon kuka na fashe dashi nace"Mahmood idan hakan ta faru waya jawo?........ " Da hanzari naga ya katseni ta hanyar sanyar 'yar yatsarsa akan lips dinsa"Shhhh! My all pls ki addana duka kalamanki,idan muka shiga ciki kina da damar amayo min da duk abinda ke ranki,amma for now pls juz pretend as if everything is alryt,bana son baba Maigadi yayi zargin wani abin...... "        K'ok'arin magana nake sae ji kawai nayi ya sanya hannunsa ya rufe min baki,cikin wata sassanyar murya wanda aganina ta yaudara ce yace"pls *My all* juz do diz for ur dear husband...... " Sanya hannu nayi na saukar da hannun nasa da k'arfi tare da furta"Karka sake ka kuma tab'a min jiki....... "     Murnushi naga yayi kafin yace"U are my wife,halal dita,infact! U are all dat I hav got,kinga kuwa dole ne nayi duk yadda naso dake...... " Ji nayi kamar na kwasheshi da mari ko zan samu dan sassaucin abinda nakeji axuciyata agame dashi.Alokaci d'aya muka fito daga motar,na hangi Maigadi ta b'angaren Mahmood din yana masa barka da zuwa.   Ji nayi shi Mahmood din yace"Mal.Bello gaka ga *'MATAR MAHMOOD*',, Fadima Sa'ad Mainasara....... " Washe baki Mal.Bello yayi yace"Ikon! Allah ashe de uban gidana ne ya auri baiwar Allahn nan,ai naji sanarwar auransu ita da k'anwarta ah radio,amma se de ba'a fadi sunayen mazajen ba shiyasa ban san cewa uban gidan nawa ne ze aureta ba,amarya ina miki maraba da xuwa Allah ya sanya albarqa awannan auran naku,ina meh tabbatar miki da cewar insha Allahu zakiji dadin xama da boss dina idan har kika bishi ahankali...... "     Duk da uban duhu daya k'arade wurin amma hakan be hanani wurga masa uban harara da murgud'e murgud'en baki ba.Wai mah xanji dadin xama dashi idan na bishi ahankali,an gaya maka ni xaman aure nazo yi?toka sani ayau ba gobe ba Zaria zata ganni. (Duk acikin xuciya ta fadi wannan maganar). Da alamu akwai shi da xuba,don sake cewa yayi"Amma yallabai aure babu gayyata?ko de ban kai matsayin da za'a gayyaceni xuwa bikin babban mutum bane? "     Ji nayi kamar nace"Ya kuwa ze gayyaceka?bayan shi kadai da iyayen daya hayo ne kawai suka san da munafikin kudirinsu? " Shi kuwa uban gayyar adaidai lokacin ya karashe fito da abubuwan daya tsaya kan hanya ya siya tare da rufe k'ofar motar.Ni duk azatona baze tankashi ba,don daga ni har Mal.Bello din mun fidda rai.     "Yi haquri yallabai na cikaka da surutu sae da safe... " haka naji Mal.Bello ya fada cike da sanyin murya wanda har ya saka naji dan tausayinsa,har ya juya ze tafi,sae asannan ne muka ji yace"Mal.Bello kaima kayi haquri hayaniyarka ce tayi yawa,auren ne yaxo ba wani shiri shiyasa banyi wata gayyata ba.... " "Ba damuwa yallabai Allah ya sanya alheri.... " ya fada tare da juyawa ya koma bakin aikinsa.    Mahmood ya rakashi da"Ameen mungode,ka rufe gate din babu inda zani kuma.... " Wuceni yayi abinsa ba tare da ya min tayin binsa ba,ba k'aramin shaka nayi da hakan ba,amma se kawai na cije don tunowa da kudirina da nayi.Da hanxari nabi bayansa,hadda hadawa da d'an gudu-gudu donna cin masa don tuni yayi min nisa kamar wanda ake jansa da igiya.    Yana gama bud'e entrance door din,ya juyo yana kallona dauke da murmushin yaudara akan fuskarsa,yace"Welcome to your matrimonial home *'Matar Mahmood Nakowa'*.......bismillah kina iya shigowa..... " Be jira ta cewata ba ya shige abinsa,nima take masa baya nayi kamar wata jela.Wurin yayi duhu sosae,can naga ya kunna hasken lantarki,nan da nan kuwa sae ga haske ya gauraye tafkeken falon.Hakan ya bani damar k'arewa dukkan ilahirin falon kallo cikin dakikun da basu wuce goma ba.Duk wani kayan alatu na more rayuwa babu wanda wannan makeken falon be mallaka ba,tsaya kwatanta muku tsaruwar wannan falon baya daya daga cikin kudirin dake raina,xan de barku da kissima haduwarsa aranku.    Cike da zafin rai na isa inda yake tsaye,babu zato babu tsammani yaga kawai na cakumo kwalar rigarsa.Nace"Brother inlaw can u pls tell me dalilinka na cin amanar dan'uwanka?meyasa ka rabani da farin cikina? Kuma wani suna ne *'NAKOWA'* da kayi amfani dashi wajen aurena?? Huh?? Kayi magana......... " Da mamaki yace"Subhanallah!! Fadima kin kuwa san girman laifin dake shirin sauka akanki da kika cakumi kwalar rigar mijinki da niyyar ci masa mutunci?pls baby doll take ur hands off me don sam bana son Allah ya kamaki da wannan laifin.... "     Axuciye na cikashi ina huci,nace"Da fari dai....._Sister inlaw komai naki sun min,k'yawunki,halayyarki,kamun kanki,uwa-uba da kuma nagartacciyar tarbiyar dana lura ya gama ratsaki,bilhaqqi dan'uwana yayi dace da mace ta gari,xanyi kokari na shawo kan mahaifiyarmu don baxan tab'a bari kanina yayi losing mace ta gari ba....._Brother inlaw ina fatar duk ka tuna da wannan Kalaman naka? " Fesar da wata iska naga yayi,kana yace"I could still remember everything my baby doll..... "       "Ashe duk kanka kake tayi wa campaign ban sani ba,ni kuwa shashashar sae na dad'a sake jiki dakai har ina gaya maka komai nawa wanda wani abin mah sam be kamata ace na gaya maka ba,amma yadda ce ta haifar da hakan,ni aganina dole na k'yautatawa duk meh sona da Mubeen,balle kana mah dan'uwansa wanda mah yaci alwashin taimaka mana don cimma burinmu ta mallakar juna,kaga kuwa dole na k'yautatamakar,ashe abinda ban sani ba shine,kana da naka mak'arkashiyar akasan kafirar xuciyarka,ashe kana nan kana gina wani dogon buri ne aranka..... Brother inlaw ka yadda dani wallahi ban tab'a ganin maci amana ta lamba d'aya kamarka ba..............."      Da k'arfi yace"Fadima enough..... " Sannu ahankali ya tako har xuwa inda nake tsaye,yanayinsa ya saka har na soma tsorata don ban taba ganinsa yayi fushi kamar haka ba,gani yayi kamar ina shirin soma taka rawar mazari,se naga ya dan sassauta,ya shimfid'a min pretty smile asaman fuskarsa,hakan da yayi ya saka na saki 'yar ajiyar xuciya araina don atunanina so yayi ya lakada min na jaki.    Ahankali yace"Matar Mahmood ki dena jefan mijinki da munanan kalamai haka,nasan nayi laifi amma ban cancanci kiyi amfani da wannan munanan kalaman agareni ba,kiyi haquri ki saurari abinda xance....... "      "Pls have a sit,sannan ki natsu ki bani hankalinki anan..... " Alokaci daya kowannenmu ya sami wuri ya zauna. Ahankali ya soma da"Zaynab Abdulmaleek 'ya ce ga wani tsohon comissioner of land & housing tanan Kanon,ni da ita mun had'e ne ah *'Federal University of Nigeria,Nsukka,Enugu state'*,, ah inda nake karantar 'computer engineering' ita kuma take karantar 'pharmacy'.Mun dau tsawon lokaci muna soyayya nida ita wanda ashe mah gari daya muke da ita,soyayyarmu abar kwatance ne da sha'awa acikin campus,bamu dau tsawon lokaci ba mukai aure bayan mun k'are karatunmu da bautar kasa duka,nima kuma alokacin na samu aiki awata shahararriyar 'Electronic company' anan Kanon.shekarunmu daya cif-cif Zaynab ta koma ga mahallicinta bayan tayi wata 'yar gajeriyar jinya ta typhoid...... "     Kuka yaci k'arfinsa wanda har hakan ya jawo na dan ji birbishin tausayinsa araina,amma dana tuna laifinsa agareni,sae kuma nan da nan nasha mur!! nace"Ba labarin soyayyarka da tsohuwar matarka nake son ji ba,labarin yadda akai ka samu aurena nake son ji,we are talking about the presence,so pls stop taking us back Mr.young man................... 📝"    A/N Pls kuyi manage nayi busy ne,buh next episode will be ready tmrrw Insha Allah.      *HAFNAN*💞 *💘SHIN SO DAYA NE?💝       *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*        *{Onward together}* *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE😘 HEART  TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔         *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*          *WATPADD:HAFNANCY💞*           *IG:Hafsy____mustee*                         ✨✨✨ _*wannan page din taki ce ke daya my Janaf💞,don haka kiyi yadda kike so da ita,Allah yabar qauna da zumunci*_                           💥💥 *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*          🌼BABI NA TARA🌼 *page 23-26*     Wuraren 7:10 Fadima ta farka daga nannauyar baccinta,k'arar ruwan wankan Mahmood dake zuba ak'asa ne ya tasheta.Ahankali nake bin dakin da kallo,dakin namiji kenan babu ruwansa da tara kayan k'warmasai,komai tsaf-tsaf dashi,dakin dan gayu kenan,sae wani daddad'ar kamshin turaren daki ne ke tashiwa,gaskia Mahmood akwai tsafta da kuma son gayu.lalubo wayata nayi dake ajje gefen filon da nayi matashi dashi,niyyata na latso Suhaima don ranar da Abba ya maida min da wayata,toh ita kuma aranar ya damk'a mata sabuwar dalleliyar waya.     Ban kai ga latso layin nata ba kawai naji Mahmood na kiciniyar bud'e kofar bathroom.Da sauri na maida wayar na ajje don bana son yaji duk wani abinda zamuyi discussing da ita.idanuwana fes akansa sanda ya fito,daga shi sae 'yar gajeriyar wando wato 'boxers',hannunsa rik'e da wani k'aramin towel yana tsane kansa dashi.Da sauri na runtse idanuwana tare da dauke kallona daga gareshi don tunda nayi wayau ni de ban tab'a ganin namiji balagi ahakan ba. shi kuwa ya lura da yanayin data shiga,wato dai bata ji dadin ganinsa ahakan ba kenan.Murmushi ya saki tare da jefar da jikakken towel din agefe,Sannu ahankali ya taka sadaf-sadaf cikin sanda xuwa gareta ba tare da ta sani ba don har yanxu idanuwan nata arufe suke.Cak! ya dauketa kamar wata 'yar baby.      Ni kuwa saurin bud'e idanuwa nayi jin wani bak'on al'amari ajikina wato ayau jikina yayi gogayya dana baligin namiji,don sosae ya rungumeni ak'irjinsa kamar wanda baya son ak'wace masa ni. "Please dear nah meye haka? don Allah ni ka saukeni.... " na fadi hakan kamar xan saki kuka.     Murmushi meh sauti naji ya sake kawai ba tare da yace min uffan ba.Be direni ako'ina ba sae acikin bath tub. Yace"oya Maza ga ruwan wanka nan na hada miki kiyi,idan kuma so kike ni na miki toh shikenan.... "     Zaro idanuwa waje nayi"sae kace wata 'yar baby? No ka fita pls xanyi da kaina.... " Ahankali yace"Ai ke din babyn tawa ce.... " ya kashe min ido daya,kana ya juya ya lakuto min maclean akan brush sannan ya miko min,ya janyo min wani dan babban towel dake rataye akan kofar bathroom din tare da azawa saman wata igiya,yace"Ga towel nan idan kin gama sae ki dauro.... "      Kafin nayi wata magana ya fice tare da rufo min kofar,ni kuma mamakinsa nake,taya za'ai nama fita da wannan dan towel din ya ganni ahakan?gaskia nifa bazan iya ba       Wani b'angaran xuciyata yace"Toh wai ba mijinki bane? Idan bazaki iya fitowa ya ganki ahakan ba toh ai se ki kwan aciki..... "    Ah sanyaye na soma wanke bakina ba.Shi kuwa yana fita,dakinta yayi,yaje ya zab'o mata wata 'yar atampa meh red pattern da adon flowers blue,daya daga cikin kayan daya bada aka dindinka mata su kenan anan kanon.Doguwar rigace 'A shape' wacce gabaki dayan gaban an mata kwalliya ne da shining stones.      Komowa dakin yayi ya dire mata shi asaman gado,kayan kuwa yasha guga har wani fidda kyalli yake.Shi kuwa diban kayansa yayi ya nufi dakinta don jin alamun kamar ta gama wankan amma fitowace ya gagareta.Acan yayi shirinsa cikin kananan kaya as usual,kayan sun k'arbeshi sosae. Ni kuwa na gama wankan harna daura towel din amma fitowace ta gagareni don kunyar had'a idanuwa dashi nake ahakan,towel din ko gwiwata bata gama kaiwa ba.Can de nayi shahada na murd'a kofar bathroom din na bud'e ina dan lek'e-lek'e.Ai kuwa naci sa'a ban ganshi adakin ba.Da sauri-sauri gudu-gudu na fito naje na sanyawa kofar dakin key wato na rufeta don kada ya shigo.    Man shafawa,powder,lipstick,turare,kwalli,underwear,bra da kuma kayan sawa na gani zube asaman gado.Cikin zafin nama na sarrafa komai,na shafa komai ah inda ya kamata na shafa.Can na saka innerwears dina,sannan na warware kayan da zan saka,doguwar rigace meh k'yau sosae kuma kayan ya bani sha'awa.Da sauri na zura,nayi mamaki sosae yadda kayan ya zauna ajikina kuma ya amsheni.Nayi daurin dankwalina meh k'yau,kana na feffeshe duk wani lungu da sako na jikina.     Ni kaina na tsorata da haduwar da nayi,sae jifar kaina nake da Murmushi ta madubi don nasan muddin oga yayi ido hudu da wannan wankan toh tabbas yana iya zaucewa.Zuwa nayi na bud'e kofar dakin,amaimakon na fita waje,a'ah sae dawowa nayi na zauna agefen gado ina wasu 'yan kame-kame kamar wata bak'uwa.Ni da gidana amma na kasa sakewa.     Shi kuwa ya bata lokacine donta shirya dakyau,after like twenty minutes ya nufi kitchen,ya had'o kayan breakfast akan wani tray sannan ya nufo dakin. Da sallama ya shigo,da sauri na dago kai na zuba masa idanuwa.    "Wowwww! yanxu Mijina ne wannan hadaddan? " na fadi hakan araina,sannu ahankali idanuwana suka sauka akan abinda yake rik'e dashi. Da hanzari na mik'e na nufeshi,shi kuwa daskarewa yayi awaje d'aya yana kallona ya k'asa furta ko da kalma d'ayace agareni,sae yi yake kamar ze hadiyeni.K'arban tray din hannunsa nayi nazo na ajja ak'asa.     "Wowwww! seriously is diz M.Nakowa's wife?Babyna kinga yadda kika fito sharr! dake kuwa?agaskia ba don za'ace nayi son kai ba toh da kuwa nace matata is the most beautiful creature in this world..... "     Xancen nasa sosae yayi min dadi,kokarin magana nake sae gani nayi ya katse min hanzari ta hanyar sanya 'yar yatsarsa akan leb'ensa"Shhhh! matata pls don't deny,juz believe me ke din k'yakk'yawace.... "     Ahankali na furta"mijina kaima din k'yakk'yawan ne ai.... " Cike da farin ciki ya furta"Allah da gaske kike matata ina da k'yau?"    "Har mah ka fini,fari ne de kawai xan nuna maka.... " B'ata fuska yayi sosae yace"Ki dena cewa na fiki k'yau don ba gaskia kika fada ba.... "      Zan musa masa yace"Shhhh! it's okay let's have breakfast am hungry my wife.... " Nace"shine baka tadani na hada mana ba kai kayi da kanka? " na fadi hakan ina d'an bubbuga kafafuwana akasa.Kallona yake dauke da sha'awata ak'wayar idanuwansa.     Yace"Yanzu shikenan saina tada sarauniya tana baccinta meh dadi? Ni idan mah zaki yadda zan fison ace na dunga miki bauta,naki kawai kici,kisha,kiyi ibada,kwanciya,ki kula da mijinki ta b'angaren hakkinsa,sannan kuma sae haifa mana k'yakk'yawan 'ya'ya kamarki,naki kenan...... " Cike da kunyar jin maganganunsa na duk'ar da kai kasa,russunawa nayi har kasa nace"Mijina ina kwana? Ya jikin naka? "     Matsowa kusa dani yayi,ya russuna kamar yadda nayi yace"Bazan amsa ba,yanxu ne gari ya waye mana har kika ganni? " "Kayi haquri don............... "     Wani irin k'arar bubbuga kofa muka jiyo,kofar da zata sadaka da sashin namu.Bugu ake bana wasa ba wanda hakan ba k'aramin razanamu yayi ba musamman ni wacce saurin mik'ewa nayi jiki na karkarwa kamar wacce ruwan Sama yai wa dan banzar duka.     Ji mukayi ance"Mahmooda kana iya?Maza ka hanzarta bud'e mana k'ofa..... " da k'arfi aka fadi hakan. Arayuwata na duniya harna mutu baxan tab'a manta meh muryar nan ba,muryar *'HAJIYARSU MAHMOOD'* kenan.    Atsorace nace"Mahmood ba muryar hajiyarka nake ji ba? " Cike da tashin hankali yace"Wallahi kuwa itace..... "     Kuka na fashe dashi nace"Mahmood kaga abinda nake ta jiye mana amma kai kaki ka gane ko? Yanxu na tabbata taji labarin auranmu ne shine tazo da wannan tashin hankalin,wai kai azatonka zancen aure yana b'oyuwa ne?toh ni dai gaskia banzo da shirin fuskantar tashin hankali agidan aurena ba,dududu mah yau kwanana daya rak! da tarewa shine har zan soma fuskantar.......... "     Karar girgiza k'ofar da ake ne ya katse min maganata,can aka ce"wai Mahmood baya jina ne ko kuwa so kake na sanya spare key na shigo? " Agigice nace"Look Mahmood dear u juz hav to do something Cuz am not going out there to face her & her humiliations..... "     Yace"okay abinda nake so dake kawai ki tsaya anan,ina fita kiyi saurin sanya key ki rufe k'ofar..... "    "Okay" kawai na furta.Ya juya ya fice,ni kuwa fadawa kan gado nayi,wani dan marayan kuka ne naji yana nemar kufce min,ai kuwa da sauri na sanya hannu na rufe bakina har da matseshi sosai wai don kada kukan yayi nasarar kufcewa.     Ahankali na furta"Yah salam! meke shirin faruwa dani ne?" Shi kuwa Mahmood yana bud'e kofa,babu b'ata lokaci Momi ta tureshi gefe,suka samu suka shige ciki gaba d'ayansu.   Cike da fargaba Mahmood yace"Momi........... " Da sauri ta daga hannunta tace"You are not allowed to utter any word,you hav the right to remain silent till am done with my investigation........ "     Da k'arfi tace"Khairat wai meh kuke jira ne? Let the investigation commence immediately,ku bincika min duk wani lungu da sako na cikin dakunan gidannan,idan har kuka ga wani abinda be dace ba toh ina son ku hanxarta fitar min dashi nan,ina fatar kun gane abinda nake nufi? "    Khairat da Labeebah ne kawai suka amsa mata da "Mun gane Momi.... " Ita kuwa Meema samun wuri tayi ta xauna,dama shi Usee tuni ya nemi gu ya zauna.Khairat ce ta nufi hanyar ainihin dakin Fadima,ita kuwa Labeebah dakin Mahmood ta nufa inda anan ne Fadimar take. Dundu Momi ta saukarwa Meema agadon baya tana fadin"Shegia zaki tashi ne kiyi abinda nace ko kuwa sae naci ubanki? Banza kawai mara kishin uwarta..... "     Da sauri Meema ta mik'e tana turo baki gaba cike da haushin wannan bak'on halin na uwarta.hanyar wani daki ita kuma ta nufo don yin bincikenta. "A'ah Labee dakata anan,karki kuskura ki shiga wannan dakin,na yarje muku da ku binciki kowanne amma banda wannan duk da cewar ban san abinda kuke bincike akai ba amma karde ashiga wannan...... "    Haka suka ji Mahmood ya fad'a babu alamun wasa atattare dashi.       "Dan kutumar ubanka har kai ka isa na bada umarni sannan kai ka take ka hana?yaushe aka haifeka? Ko mantawa ne kayi da wacce take tsaye agabanka take kuma bada wannan umarnin?idan kuwa mantuwar ce kayi toh ina meh tunatar dakai cewar Haj.Fatima Binta Mu'azu mahaifiyarka ce........." Ta juya ga Labeebah wacce duk ta gama tsorata da yanayin yayan nata shiyasa taki gaba"Maza Labeebah shige ciki ki min bincike ko kuma ni nazo nayi da kaina...... "    Saukar da ajiyar xuciya yayi bayan ya tuna cewar ai ya sanya Fadima ta rufe k'ofar. Ni kuwa ina daki ina jin duk wani abin dake wakana afalon,jikina sae rawa yake don tsananin tsoro,xuciyata kuma kamar zata fasa k'irjina ta fad'o waje don fargaba.Ina jin umarnin da aka baiwa Labeebah,da zafin nama na mik'e don tunawa nayi da cewar ban rufe k'ofar ba kamar yadda ya umarceni da nayi.      Ban kai ka isa k'ofar ba sae gani nayi ta fad'o dakin,fuska sam babu ko digon annuri akansa.Da mamaki take nuna ni tace"Fadima you?budurwar Yah Mubarak? Meh kike anan? " Cike da fargaba na daure nace"Ni ba budurwar Mubarak bace.... Am *'FADIMA SA'AD MAINASARA'* matar *'MAHMOOD NAKOWA'* Cike da tashin hankali tace"Shut the hell up!! karya kike,taya za'ai ki zama matar Yah Mahmo?kuma....."    "Malama investigation aka sanyaki kiyi ba interrogation ba,don haka you have no right to question me,nice nan abinda be dace ba abincikenku,so kindly arrest me,tambayoyi kuma oganki ce keda right ta min bake ba.... Let's go...... " Na lura sosai jikinta yayi sanyi da kalamaina,shige gaba nayi na batta tsaye kamar gunki tana bina da kallo.      Shi kuwa Mahmood yana ganin Labeebah tayi nasarar shigewa dakin,ya furta "Yah salami! Shikenan ta faru ta k'are,ruwa ya k'arewa dan kada...... " Wuf! Momi tayi ta Mik'e ah sa'ilin da tayi ido hudu da Fadima sa'ad,ita kuwa Fadimar 'yar kissa sae jifar Momin take da Murmushi.     Russunawa har k'asa nayi nace"Momi kune da sassafe haka? Sannunku da xuwa,ina kwana? " Cike da mamaki Momi tace"Ke saurara min nan!!.... Meya kawoki gidan nan kuma meh kikeyi acikinsa? "     Fuskar mamaki nima na shimfid'a mata kana nace"Momi Kamar ya meh nake yi agidan nan? mace da gidan mijinta kuma har sae an tambayeta abinda take acikinsa?....... " Kafin Momi tayi wata magana Khairat ta k'arbe wacce fitowarta kenan daga dakin Fadima kuma duk taji abinda ake fada tace"Wai ni ban gane xancen da ake ba anan,dodon kunnuwana sunki su yadda cewar wai Fadima budurwar Yah Mubarak ce matar Yah Mahmoh..... " (duk sun shaidata don gabaki dayansu an kaita wajensu sun gaisa alokacin da suka kai ta'aziyyar rasuwar mahaifinsu).    Momi ce tace"Ban san meh yarinyar nan tayiwa ya'yana Maza ba da har suke rawar kafa akanta,Mubarak ya wulakanta 'yan'uwansa akanta,yanxun kuma wansa ya aure masa wacce yake haukar akanta,wannan cin amanar da meh yayi kama?" Juyawa tayi ga Mahmood tace"Munafiki,ashe da gaske din ne kayi aure shine ka b'oye min har baban Zali ya shige maka gaba,Mahmood meh na maka da har ka zab'i ka b'oye min al'amari meh girma haka?"    Murmushin takaici tayi,kana ta cigaba"Koda yake da gani ba yin kanka bane,asiri ce tayi tasiri akanku daga kai har dan'uwan naka...... " Afusace nace"Mahmood why are u silent?why can't u open ur mouth and defend me? Meyasa bazaka fad'a musu ta yadda akayi ka aureni ba? Ka tsaya kurum ana zagina alhalin am innocent?shin haka mukayi dakai?..... "     Khairat tace"Labeebah wai meh muke jira ne da bazamu soma cin ubanta ba? " "Ahir dinku! kada wata 'yar iska acikinku tayi gangancin tab'a matata,idan kuwa hakan ta faru toh wallahi sae na lahira yafi yarinya jindadi.... "    Tasss! Kakeji Momi ta wanke masa fuska da mari,tace"Ai dole ka fadi hakan tunda asiri ya gama cinka,Shima baba Mu'azzam din yanzun nan zanje naji dalilin daya saka ya shige maka gaba Sannan naci masa mutunci daga shi har zuri'arsa,ku kuma ku jira dawowata akaro na biyu don ban gama daku ba....... "    Ta juya gasu Khairat tace"Ku taho mu tafi..... " Ta fice abinta,Khairat tace"U are welcome to Nakowa's family,duk wani tashin hankali is awaiting you in diz family..... "     Labeebah kuwa cewa tayi"will soon be coming back for you,a betrayer kawai..... " Mahmood yayi wani mahaukacin taku biyu zai damkosu,ai kuwa da hanzari suka fice da gudu.Ita kuwa Meema meh k'aryayyan xuciya kamarni nan Hafnan har ta soma xubar da kwalla.    Tace"Yah Mahmo,Anty Fadima don Allah kuyi haquri,ga shawara idan zaku k'arbeta,kawai ku biyomu gidan Baba Mu'azzam din ayita ta k'are... "     "Nifa idan zasu bi ta tawa kawai subar garin if not wallahi yanzu kuwa suka soma ganin tashin hankali"acewar Usee.Wani uban harara Meema ta kwasheshi dashi tace"Kai dai wallahi baka da correct thinking of a man,shiyasa Momi ke kiranka da *'DAN RAKIYAR MAZA'*.... 😀"     Kafin yakai ga bata amsa kawai yaji Momi na kwala masa k'ira,da sauri ya fice yana meh cike da jin haushin abinda yayar tasa ta fad'a masa.   Mahmood ya saukar da ajiyar xuciya yace"Meema jeki gamu nan tahowa.... " Da gudu-gudu ta fice don kada taci ubanta ahannun Momi.    Ni kuwa kuka nake sosae kamar raina ze fita,yanxu atunaninsu asiri nayiwa Mahmood kenan ya aureni ko meh? "Fadimata pls tashi mubi bayansu... " haka naji ya fad'a yana meh kokarin yafa min mayafi ajiki.    Axuciye nace"babu inda zani,ni kawai ka bani takaddar sakina...." Dakyar da sudin goshi da kuma wasu 'yan dabaru nasa ya samu ya lallasheta har ta haqura ta yarda zata bishi gidansu baba Mu'azzam din................ 📝   A/N Yanzu meh kuma ze faru gidan baba Mu'azzam? Ku biyo    Sorry for the late post,wallahi was kinda busy ne yau!!    *HAFNAN CE💞*                                https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/     *💘SHIN SO DAYA NE?💝*        *INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*               *{Onward together}* *{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}* '''THE PEN OF LOVE 😘 HEART  TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑''' *JUST GIVE US FOLLOW.....*✔          *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*        *WATPADD:HAFNANCY💞*         *IG:Hafsy___mustee*                        ✨✨✨ *KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*         *🌼BABI NA SHA DAYA🌼*   *page 29-30*       Ummata na k'ira wacce muna gama gaisawa ta rufeni da fada,wai dole na ajje wannan baccin safen nan agefe wanda ya riga ya gama bi min jiki,tace idan ban kama jiki na watsar da kiwiya agefe na dunga kula da mijina ba,toh kuwa namiji shi babu ruwansa,idan yaga bakya masa abunda yakeso toh kuwa yana iya banka miki kishiya wacce zata zo ta dunga kula da bukatunsa da kuma tattalinsa,ke kuwa awatsar dake agefe ki koma 'yar kallo.Mun jima tana min nasihu meh ratsa xuciya,daga bisani mukayi sallama.Shima Abbana na k'irashi mun gaisa.Har yake labarta min irin yanayin da Umma ta shiga alokacin da take ta k'ira amma babu amsa.Dariya nayi sosae tare da jin wani irin soyayyar Ummata na ratsa jinin jikina.    Kai tsaye na latso _*My Ashwairiyya*_. Ita kuwa awannan lokacin ta fito wanka kenan,tana gaban madubi tana taje kanta,so take taje taga dakin Suhaima.Wayarta dake gaban madubi taji ya dauki kida,da hanzari takai hannu ta dauketa.     *'Fateenah'* shine sunan data gani yana rawa akan screen,gabanta ne taji ya bada rasss!.... Jefar da comb din hannunta tayi tare da mik'ewa da sauri har jikinta na dan rawa don tsananin tsoro da kuma fargabar abinda zataji daga sahibar tata. "Hel....lo... Fateenah'...... " haka ta fada cike da in-inna ah sa'ilin da tayi picking call din.     Bushewa da wani irin dariya nayi don nasan abinda take yiwa wannan rawar muryar,wato atunaninta tsantsar tashin hankali zata tsinta daga gareni shiyasa take cike da tsoro. Allah sarki my Ayush komai yayi chas-chas ahalin yanxu. Nace"Malama idan zaki daidaita muryarki toh tun wuri mah ki daidaita don ni yanxu babu abinda nakeso sama da mijin da kuka hana min saninsa da wuri sae akurarren lokaci...... "     Kwashe komai nayi na gaya mata tun wucewarsu,tarewata da kuma rigimarmu adaren farko,sae kuma sabuwar rigimarsu Momi da kuma xuwarmu gidan Baba Mu'azzam da kuma nasihunsa agaremu,sae kuma sulhun da aka nema. Wani wawan ajiyar xuciya Ash ta sauke,cike da murna tace"Wayyyo! Fateenah' ina zan saka kaina don murna? Agaskiya naji dadi ba kadan ba da har kika haqura kika rungumi mijin kaddararki,fateenah wlh believe me Mahmood shine kalarki ba Mubeen ba,wlh ni dama can ina ta miki kwadayin aurensa sae gashi lokaci daya Allah ya amsa addu'ata,ya zamo mallakinki,yanzu dai addu'armu shine Allah yasa Mubarak ya fahimceku ya kuma gane cewar wani baya taba auran matar wani,haka zalika wata bata taba auran mijin wata........ "     Cike da sanyin murya na amsa mata da "ameen." Tace min tana shirin xuwa gidan Suhaima ne,nace yanzu Muna gama waya ita zan kira.Mukayi sallama.     "Nima ahalin yanxu babu abinda nakeso kamar matata wacce naki bayyana kaina agareta sae akurarren lokaci..... " Da sauri na waiga tare da watsa masa wani Irin kallon soyayya,ware min hannayensa yayi.    Ahankali ya furta"Babyna I nid a warm hug...... " Babu b'ata lokaci na isa gareshi tare da fad'awa jikinsa,sannu ahankali ya maida hannayensa ya rufe yana meh dada kankameni.kunnuwana dake saman k'irjinsa ya sanya nake iya jin yadda xuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri.Ahankali na lumshe idanuwa ina meh jin wani irin sonsa na ratsa jinin jikina.     *** Ash cike da farin ciki ta Latso su Leedar da Fresh take labarta musu zancen Fadimar,suma din sosae sukai murna tare da musu fatar alheri da kuma addu'ar Allah yasa Mubeen ya fahimcesu.          * Cike da rawar jiki ta mik'e tana fadin" Momi kunnuwana sun kasa gasgata zancen da kike min? Taya za'ai Zahranmu ta rikid'e ta zamo matar Yah Mahmo?abu sae kace ah wasan kwaikwayo?"     "Toh wannan maganar da nake miki wasar zahiri ce bata kwaikwayo ba,Fadima de ayanxu matar Mahmood ce wacce ya b'oye mana auranta da yayi.... " acewar Momi. Cike da al'ajabi Hanan tace"Tabdijam! agaskia Momi Fadima da Yah Mahmo sunci amanarmu,Fadima ta manta cewar itace farin cikin mijina,shine don ta ruguza wannan farin cikin nasa shine ta tashi ta auri Yah Mahmo?dama can ni nasha fadawa Mubarak cewar nifa ina ganin kamar Fadimar bata qaunarsa kamar yadda shi yake hauka akanta,amma sam yaqi saurarona sabida makauniyar so daya rufe masa ido,yanxu ga irinta nan,ta tashi ta aure masa dan'uwa wanda na tabbatar ba k'aramin yaki za'ai ba kuwa idan ya dawo........ "     Ta rushe da kuka tare da ficewa da gudu tabar dakin,Momi kuwa sae Binta da kallon mamaki take,ahankali tace"Kai! kai! kai!!! Wayyo ni Bintu d'iyar hassan nide wallahi ban tab'a ganin shashasha marasa k'ishin mijinta kamar Hauwa'u ba,in banda abin sokuwan ai wannan al'amarin ah dadinta kenan tunda anyi nasarar raba mijinta da wacce yake fifitata akanta,amma jibi abinda wawiyar ke fada,yanxu duk suruntun da nake tayi ya tashi abanza kenan?tunda ta kasa fahimtar cewar ita Fadimar mah bata da masaniyar mijin da aka aura mata sae bayan an kawota....."     Taja tsaki tare da mik'ewa don gabatar da sallar la'asar.      ** Awannan daren mun gurji amarcinmu,Mahmood ya fanshi kudin sadakinsa ba kadan ba,ni kuwa nasha kuka har na baiwa uku lada,lallashi da sanya albarqa kuwa har Mahmood ya gaji da yinsu,sae cewa yake "Matata ubangiji Allah yayi miki albarqa,nagode kwarai da gaske da kika tsare min mutuncin kanki har kika kawoshi gidana.....*'Zahmood'* ina sonki matuk'a fiye da tsammaninki,Allah ya k'ara mana qaunar junanmu,Sannan kuma Allah ya azurtamu da 'ya'ya nagari....."     Cike da farin ciki na amsa da "Ameen ngd my *'Jannah'*.     Da safiyar ranar kuwa,sae ga Usee da kayan breakfast wai Momi ce tace akawo mana.Sosae abin ya bamu mamaki matuk'a tare da jinjina al'amarin,Mahmood ya k'arbi basket din yace"Usee kace mata muna godiya sosae sae mun shigo.... "    Da sauri Usee yace"A'ah tama ce suna nan tafe gobe duka dasu anty Meema.... " Gabana naji ya yanke ya fadi jin abinda ya fada,amma sae na kada baki nace"Allah ya kaimu kanin miji,sae mun gansu..... "    Murmushi ya sakar min yace"Toh!  matar Yayah,sae anjimanku.... " Muka had'a baki wajen cewa"Toh mu jima da yawa.... " ya fice.     Wani uban tsalle naga Mahmood ya daka yana fadin"Yessss! My family have accepted my Zahra da hannu bibbiyu........ Sauran mana kaninmu.... " Murmushi kawai nayi abina.Daga haka muka soma cin breakfast wanda ferfesun kan rago ce,sae kuma kayan tea.     Washeqari kuwa sun cika alqawari,sunzo din hadda 'yan gidan Baba Mu'azzam su Hafeezah da mominsu.Gida ya cika ya kacame da hayaniya,sae fira muke cikin raha da annashuwa.Dama tun safe nida Mahmood muka hada musu lafiyayyar girki kan suzo. Nace"Anty Meema waini ina Anty Hanan ne? " (Dayake mijina ya fada min cewar yanxu ta koma gidansu Momi da zama tunda mijinta ya tafi,shine nayi tunanin kila tare zasu zo amma kuma sae naga akasin hakan,babu ita aciki).    Momi ce ta kada baki tace"Hanan tana gida kinsan ciki yayi nauyi yanxu,don haka mah bata cika fita,amma tace tana gaidaki.... "    (Gaskiyar lamari kuwa shine,babu yadda Momi batayi da Hanan ba akan tazo suje amma taki,tace babu inda zata,akan dole Momi ta rabu da ita,Jasmin mah ta hanata binsu,ita kuwa yarinyar sae kuka taketa yi amma babu damar zuwa tunda uwarta ta hana). Nace"Allah sarki! Allah de ya raba lafiya... "    Ni nasan tabbas Momi tade k'are Hanan ne,amma ni xuciyata ta bani cewar haushina takeji sosae don na auri wan mijinta.Oho! Wallahi kome ze faru ya dade be faru ba donni dai yanxu harga Allah ina son mijina kuma bana danasanin aurensa,kuma babu wanda ya isa ya raba wannan auran sae Allah wanda shine ya hada abinsa.Su Momi da Khairat seda suka sake nemar gafarata akan cin mutuncin da suka min da kuma sharrin asirin da suka lik'a min.Nace"Laah! wallahi babu komai,ni wlhy ban rik'eku axuciya ba,Allah ya yafe mana duka... " Awa daya kacal su Momi sukayi,Sannan suka wuce,su Hafeezah kuwa sae da marece direban gidansu yazo ya daukesu wanda dama can shi dinne ya kawosu.'yan kudade na basu wanda Mahmood ne ya bani akan cewar idan sun tashi tafiya saina basu.    Nace"Afreen gashi ba yawa kwa siyi kayan kwalliya,naso baku acikin nawa ne amma kayan lefena nacan Zaria..... "    "Laaaaah! kuji anty sae kace wasu baki?mufa kannenki ne basai kin bamu wani abin ba,sada xumunci mukazo yi ba maula ba.... " Ah wasance nakai mata bugu ta goce,nace"kai Afreen yanxu yaya bazata iya baiwa kannenta kyauta ba? Shikenan idan ta basu ya zama maula ce suka yi? "       "Mude kome zaki fada bazamu k'arba ba,ki rik'e abarki bama so.... " tayi gaba su Rafi'ah suka take mata baya,har wajen Mota na bisu amma sam sunki k'arba,Afreen ce ta umarci direba daya tada motar,ya kuwa bi umarninta suka fice.Su Anty Meema mah haka suka min dana ce gashi sa baiwa 'ya'yana susha alawa,suka k'i k'arba. Asanyaye na koma ciki,gab da sallar magrib ogan nawa ya dawo.Ware min hannaye yayi wai nazo na rungumeshi,babu b'ata lokaci na isa gareshi ina dan bubbuga kafata akasa nace"Anki ah rungumekan,daga cewa zakaje kayiwa abokanka ban gajiya shine kayi zamarka acan ko? Kode sunyi maka wata matarce ban sani ba? "   "Lalalalaaaah! Sunma isa?kuma nima na isa na so wata bayan my Zahmood?wallahi babu ta biyunki acikin xuciyata my Zahra,ke kadai kin isheni rayuwa...... " "K'arya kake har yanxu kana son Zaynab,kuma itama din ai hakan ka fada mata,kace babu wata da zaka rab'a ko bayan ranta,sae gashi ayau ka k'arya alqawari...... " babu xato ba tsammani kawai naji hawaye ya soma ziraro min saman kunci,hawayen da ban san ko na menene ba? Kota kishin Zaynab dinne ko kuwa tausayin kaina na ganin na kamu da sonsa bayan nasan har yanxu yana qaunar Zeeynsa,kuma ko kusa nasan bazan taba samin irin matsayinta axuciyarsa ba,yafi sonta akaina nesa ba kusa ba.    Shima din idan yace ya manta Zeeynsa toh kuwa yayi k'arya,yasan yana mugun son Fadima,amma Zeeynsa ta dabance acikin xuciyarsa,yasan tabbas watarana Fadimar tana iya maye gurbin Zaynab din acikin xuciyarsa idan har ta iya bi dashi yadda ya kamata amatsayinta na wayayyiya. Rungumota yayi ya soma lallashinta,cike da kissarsa da kuma salonsa ya mantar da ita batun Zeey.Atake anan suka shiga farantawa juna rai,suna meh jin sabuwar qaunar junansu na ratsa dukkan wani gab'ar jikinsu.Ya tambayeta yadda sukayi da bak'in nata,anan ta bashi labarin yadda sukai dasu Afreen,sosae yayi dariya hadda k'yak'yatawa.     Yace"Ai nasan halin Afreen sarai bata son ana mata irin wannan k'yautar,sae tayi ta ganin kamar malauce tazo yi,yanxu mah idan ba sa'a kikaci ba,toh kuwa tana iya jera miki kwanaki kafin ki sake ganinta agidan nan.... " Waro idanuwa waje nayi nace"Akan nayi mata k'yautar kudin?"    "Naki wasane yarinyata,toh bari kiji akwai wani saurayinta Arham dake masifar sonta,toh wlh ko kwandala ya bata,toh shikenan daga ranar ta dena kulasa kenan har sae iyaye sun shiga cikin maganar,yanxu maganar da nake miki,babu wata k'yautar kudi da take k'arba daga gareshi,ita fa ta gwammace ayi mata k'yautar wani abin can daban amma bawai kudi ba,aurenta mah nan da wata uku masu xuwa insha Allah.... "    Ahankali nace"Allah ya nuna mana.... Agaskiya nide ta birgeni,sam abin duniya basu rufe mata idanuwa ba kamar wasu matan..... "      "Ai Aysha Afreen tayi ne,wallahi da'ace ni meh sha'awar auren dangi ne,toh kuwa wallahi da ita xan aura sabida halinta yayi ne... " ya fada tare da kashe min one eyes. Wani irin kishinta ne naji ya tokare min qahon xuciya,lokaci daya na sakar masa kukan shagwab'a,nace"Nasan kila auran mah dakai za'ayi,b'oye min kawai kake kamar yadda ka b'oye min aurena dakai...... "     Rik'e cikinsa yayi yana dariya yace"Babyna ji yadda kika koma lokaci guda,don't tell me kema kina da kishi sosae juz lyk Zee...... " B'ata fuskar da yaga nayi ne ya sakashi yin shiru,ya sosa k'eya tare da fadin"Am sorry my Zahmood bazan k'ara k'iran sunanta agabanki ba.... " sae kuma naji duk ya bani tausayi.Haka muka cigaba da wasanninmu na ma'aurata kafin daga bisani muka mik'e don gabatar da sallar magrib,bayan ya dawo daga masallaci kuma muka zauna cin abinci.       **** Kwanakin amarcin daya biyo baya kuwa ba'a magana don sosae nake samun kulawa da kuma daddadar soyayyar mijina agareni,nima ba laifi ina gwada masa tawa kulawar da soyayyar akoda yaushe.'Ya mace kenan,ko kuma nace xuciya ita de babu ruwanta,da zarar ta sami Wanda yake bata kulawa da kuma damuwa akanta,shike nan saita mace akan son wannan din,gashi ayau son da nake yiwa Mubarak ya zama tsuntsu ya koma kan Mahmood.Ayanxu Kam ina masifar son Mijina Wanda har nake jin bazan iya cigaba da rayuwa babu shi ba,tofa kullum muna mak'ale da juna baya fita,koda ace ya fitan ne,toh kuwa baya jimawa yake dawowa,dalilin daya sanya muka k'ara shaquwa dashi kenan.       Hakan yake gasu Suhaileedar,sun wani k'ara shaquwa da wani irin mugun son junansu daya qaru,sosae leedar ke tattalin Suhaima kamar wata sarauniya,haka mah iyayensa da kannensa ke masifar ji da ita.Rayuwa tayi mata fari kal,ga soyayyar miji ga kuma na family dinsa,agaskia Suhaima ko kadan bata da damuwa.      Ana gobe zamu koma Zaria,Mahmood ya kaini gidajen 'yan'uwansa,gidan goggo Ladidi muka soma zuwa,sae gidan Anty Meema,Anty Labeeba,anty Khairat,duk kuma sun rasa inda zasu sakani don murnar ganina,kuma bamu tashiwa sae mun dire musu abubuwan alheri.Akan hanya Mahmood ya tsaya daidai wani saloon.     Yace"Zahmood oya fito muje awanke miki kai,idan yaso Afreen ta miki kitso don ta iya sosae.... " Banyi wata gaddama ba na fito don ni Kaina Ina buqatar awanke min kan don jinsa nake kamar yana wari mah sabida ruwan da yake sha kullum😁(Kun gane Ai).     Mun cimma mutane ba laifi acikin saloon din,Mahmood ya narka musu uban kudi don kawai asamu ayi min da sauri,su kuwa sae washe haqora suke don ganin sun yaqi naira da safiyar nan,nan da nan suka wanke min kan sannan aka shigar dani dryer,retouching kawai nayi.Ana gama min ban wani b'ata lokaci ba na fito na sameshi zaune awaje yana jirana.Murmushi ya sakar min tare da mik'ewa daga inda yake,ya tako ya sameni ah inda nake tsaye.    Yace"Zahmood har an gama? " "Yo! ba dole agama ba tunda ka narka musu uban kudi kamar baka san zafin nemansu ba? retouching kawai da zanyi shine ka tashi ka zabga musu uban kudi..... "     "Can do more than that for you my Zahmood,wallahi kinfi karfin komai awurina,kudi kuwa yanxun mah na fara bararwa indai akanki ne... " Sosae kalamansa sukai min dadi,ya kamo hannuna yana fadin"Zahmood tunanin meh kike haka?taho mu tafi.... "       Na soma k'ok'arin kwatar hannuna"Haba my dear meye haka? Sakar min hannu kaga fa mutane na kallonmu..... " "Yo! toni ina ruwana da mutanen? Inace ko halali ta na rik'e? Idan kuma basu yadda ba toh suzo su duba foreheads dinmu zasu ga an rubuta *'MAHMOOD WEDS FADIMA'*"    Sosae abin yaban dariya,har muka iso gidan Baba Mu'azzam fira muke tayi da kuma wasanni.Acan suma rasa inda zasu sakani sukai don murna,ji suke tamkar su hadiyeni don so,mahmood ya tafi yace anjima zai dawo ya daukeni.      Afreen ta yaryara min kananun kitso meh k'yau,tace"Anty Zahra jan lallinki mah harta soma gogewa bari na aiki Rafi'ah ta dauko mana meh lalli anan bayan layinmu.... " Nace"Afreen wlh dama kin basshi kada ya dawo ya zauna zaman jirana don kinsan lalli bata saurin bushewa... "    "A'ah wallahi anty sae fa an miki don yayana ya gani ya kusan zaucewa,in banda abinki mah ai lalli itama adoce ga 'ya mace,nifa wlh mijin da xan aura idan har baya son lalli da k'amshi tofa bazan aureshi ba.... "    Da mamaki nace"Akan lallin?" "Anty naki wasane wlh....... " Ta kwalawa Rafi'ah k'ira tazo,ta aiketa gidan meh lallin,ba'a wani jima ba sae gashi sun dawo da meh lallin,zuwansu yayi daidai da gama kitsonmu.Aka zana min jan lalli meh k'yau,abinka da farar mace sae ya zauna das ajikina,abinci mah abaki Afreen tayi ta bani.Bayan an gama ta biya kudin lallin,inata cewa ta basshi zan biya amma taki.Kai agaskia nide ranar naga gata awurin wa'ennan bayin Allahn.Sae bayan sallar hudu Mahmood ya dawo daukata,yana ganina ya soma cewa"wowww! Afreen wlh nasan aikinki ne wannan,ngd sosae kin fitar min da amarya,yanxu ni wacce irin k'yautace zan maki daze nuna lallai naji dadin wannan gyaran.....?"    "Yanzu brother shikenan donna gyara anty Zahra shine sae an bani wata k'yauta?nasan da'ace Khairat ce ko Labeeba bazaka yi musu wannan maganar ba,don Allah ka bari bannaso,idan kana hakan sae nayi ta ganin kamar baka daukemu daya ba kamar yadda mu muka daukeku.... " Ahankali yace"okay am sorry kanwas bazan kuma ba.... "    Sun cikani da sha tara ta arziki,sukace insha Allah suna nan xuwa Zaria ganin gida,Kaka rigima sae tsiya take ta min waina kuke sae gyaran jiki nake,adole wai ina son na fita matsayi agun megidan namu,dariya ni take taban ba.Maminsu Afreen ita tata k'yautar ta tsimi ce,tace kada na kuskura nayi wasa da amfani da ita don mace sae da gyara.Akunyace na k'arba ina mata godia.     Amota kuwa Mahmood kamar ze hadiyeni don sha'awar lallina,yana tuki amma rabin hankalinsa na kaina ne,ya jawoni yana meh cusa kansa ajikina yana shak'ar kamshin jikina,hadda lallin kafata dana hannayena ya hau shafawa,ah rud'e nace"Haba dearnah tuki fa kake,pls concentrate on it.... "     "Ai ke dince Zahra kike nemar zautani da wannan adon taki,agaskia yau sai kwalliya ta biya kudin sabulu.... " ya kashe min ido daya,ni kuwa na gane nufinsa don haka sae nayi rau-rau da idanu kamar xan saki kuka,ganin hakan ya sakashi sakin dariya yace"Wallahi ayau babu zancen daga kafa,na fayi haquri kwana kusan uku kenan na zuba miki idanuwa ina kallonki amma yau babu daga kafa...... "    Tuni na sakar masa kukan shagwab'a,ya shiga lallashina har muka karaso Family house.Bansan meyasa nake jin faduwar gaba ba idan har akan komai daya shafi su hajiyar Mahmood ne,lfy lau muka baro gidan Baba Mu'azzam,banji wani faduwar gaba ba sanda mukaje amma gidansu Momi saina tsinci kaina da jin tsananin faduwar gaba.Kila kuma don wannan zuwan shine karona na biyu shiyasa.     Mahmood ya lura da yadda yanayina ya sauya,yace"Zahmood pls cool down,Momi has totally changed wlh believe me babu abinda Zata miki kinji matar Mahmood? " kai kawai na daga masa.      Ah main falon gidan muka tarar da Hanan da Usee suna hira.Muna hada idanuwa da ita sae naji gabana ya tsananta bugawa,ji nayi kamar Mubarak dinne nayi ido hudu dashi. "Oyoyo matar Yaya.... " Usee ya fada tare da mik'ewa,awasance Mahmood yace"Dakata malam ince dai ba shirin rungumar min mata kake ba? "    Dariya muka sakar,kafin Usee yayi magana na karba"Toh idan mah yayi haramun ne?shima din mijina ne fa... "     "Yauwa gaya masa matar Yaya.... " Tuni muka ga Mahmood ya hade rai sosae kamar be taba dariya ba wanda hakan ya bani tsoro har naji ina meh nadamar abinda na fada.    Yace"pls ki dena min irin wannan wasar bana so... " kan nayi magana ya shige dakin Momi.     Usee yace"Matar Yaya haquri zakiyi ki kuma dunga kula sosae don Yayah akwai zazzafar kishi akan duk wani abinda yake so..... " Nide jinsa kawai nake amma hankalina atashe yake na ganin na b'ata ran mijina.Tunawa nayi bamu gaisa da Hanan ba,juyowar da zanyi kawai naga inda take zaune wayam! bata awurin kuma.     Usee yace"Haquri zakiyi don dole daga ke har Yayah ku fuskanci hakan daga gareta,ita wai adole taya mijinta kishinki take..... " Murmushi kawai nayi nace"Ina Jasmin dita?" "Ina tsammanin bacci take.... " "Don Allah yi maza ka tadata baccin yamma Sam babu k'yau kada kanta yazo yana mata ciwo..... "     Murmushi yayi yace"An gama matar Yayah... " ya nufi wani daki can daban. Saukar da ajiyar xuciyata yayi daidai da fitowar Momi da Mahmood.    Da fara'arta tace"A'ah 'yata kune tafe da yamman nan? Sannu da xuwa... " Har kasa na russuna ina gaidata cike da kunya.Mahmood fuskarsa babu yabo ba fallasa yace"Hajiyata zan dawo na dauketa anjima kadan.... " kan tayi magana yayi gaba abinsa ba tare da ya sake kallon inda nake ba.     Axuciyata nace"Ashe haka Engr. yake da saurin daukar zafi akan abu?lallai kuwa ashe ina da aiki sosae agabana..... "         Acan daki kuwa rigima ce ta kaure tsakanin Usee da kuma Hanan,ta jiyo zancensu da Fadima afalo don lab'e tayi musu.Ta hanashi tada mata 'ya. Yace"Hauwa wai na tambayeki man? Yaushe kika fitsare kika koma haka ne?taurin kai agidan nan? Toh Wallahi baki Isa ba don Sam wannan dabi'ar ba tarbiyyar gidanmu bace,an baki haquri akan ki yadda da kaddara amma dayake ke din sokuwace marasa kishin mijinta dole kiki sauraran kowa.....    Da karfi tace"Usman ka fita daga cikin idona,Ai dama dole ka fadi hakan tunda kun hade kai wuri guda,kun nuna sam abinda Yah Mahmo yayi ba kuskure bane tunda ai shi cikinku daya dashi,ni kuwa nawa mijin tunda ba cikinku daya dashi ba ai dole ku nuna halin ko in kula akansa........ " Dariya yayi yace"Jibi inda wawiyar ta bullo kuma?"    Ya tamke fuska yace"Kuma yau ya zamo rana ta k'arshe agareki da har zaki sake daga min murya,don kina auran yayana bashi ze saka ki sakani agaba kina min fada kamar wani danki ba,ni dinma ba tsaranki bane,daga Khairat har Labeeba babu tsaranki acikinsu balle ni,don haka take note,idan kunni yaji toh gangar jiki ya tsira,idan kuma kikace zaki cigaba da min rashin kunya,toh kuwa watarana rufe ido zanyi,xan manta Cewar ke din matar yayana ce na baki kashi sosae,idan yaso zumuncinmu dashi ya tarwatse akanki..... Yarki kuma don Allah kada ki bari atasheta idan har don kada su gaisa da Fadimar ne,don Allah na rokeki ki dunga hada mata da sleeping pills aduk sanda kika ga ko kika ji Anty Zahra zato zo,wawiyar banza kawai..... "    Axuciye ya juya ze fita sae kuma yaci k'aro da Momi wacce hayaniyarsu ce ta janyo hankalinta,rab'awa ta gefenta yayi ya fice.       Yazo ze fice daga falon gabaki daya don har yama manta da wata Fadimar don tsananin b'acin rai. "Kanin miji haquri zamuyi duka kamar yadda ka fada dole ne duk mu fuskanci hakan daga garesu har mijin nata.... "    Allah sarki Usee sam be iya mah fushi ba arayuwarsa,duk cikinsu bayan maryam,shine na biyunsu ah haquri,komai ake mishi shanyewa yake,sam be iya maidawa babba magana ba,shiyasa abin na Hanan ya bashi haushi sosae. Murmushi ya sakar mata"Babu damuwa matar Yayah... "    "Toh ina kuma zaka bayan Muna hira meh dadi? " "Tsiren bakin titi zan siyowa amaryar tawa... " kafin nayi magana ya fice.Usee kenan sam bashi da matsala na ayyana hakan araina.     (U guys shld help ooo,am alrdy crushing on *'Dan rakiyar maza😁'*    Acan daki kuwa,Momi tas-tas tayiwa Hanan sannan ta fito don abin nata yakai mata wuya matuka,tayi lallashin,ta kuma nuna mata cewar tun fi'azal haka Allah ya rubuta cewar Fadimar matar Mahmood ce ba Mubarak ba,amma duk nasihun sun tashi abanza,shiyasa ta mata wankin babban riga.Babu abinda take illa kuka.Ita ba auran Fadima da Mahmood ne take jin haushi ba,A'ah ita damuwarta anan shine farin cikin mijinta da ake neman ruguzawa,bata burin ace yau mijinta ya shiga cikin wani mayuwacin hali akan Fadima,Zata cigaba da yi masa addu'ar Allah yasa ya haqura ya rungumi destiny dinsa,Allah ya sanyaya masa xuciya yaji kawai Fadimar ta fice aransa,wannan shine addu'arta akullum tun ranar data sami labarin auransu.    Kukanta shine ya tashi Jasmin,sae mutsissike idanuwa take don tabbatar da lallai kuka taga momin tata keyi.Ahankali ta saukar da kafafu daga saman gado,ta isa ga Mominta tace"Momina meya sameki kike kuka?kode kewar daddy kike ji ne? "    Uwar bata tankata ba sae aikin rera kukanta take ahankali,ganin hakan ya saka ta fice daga dakin xuwa falo,ta hango Usee da Fadima na cin tsirensu ah plate daya.Momi kuwa ta koma daki abinta bayan ta baiwa Fadima haquri akan cin fuskar da Hanan ta mata.   Usee na ganinta yace"Uwar taki taga damar kyaleki ki fito? " bata ma san yanayi ba,illa kurawa Fadima idanuwa da tayi tana meh son tunano inda ta taba ganinta.     "Jasmin taho nice wannan antin meh k'yau wacce har kike ta kokarin samo bulala azane ni rannan kin tuna? " Yaro baya mantuwa,ai kuwa ta tunata,da gudu taje ta rungumeta tana cewa"Anty meh k'yau nayi kewarki sosae,kullum idan kuna waya da abba nace ya bani sai yaki...."    Usee yace"Toh ai yanxu gashi ta dawo kusa dake,zaki gaji da ganinta har ki ture idan har uwarki ta yarda,yanxu anty meh k'yau matar daddynki Mahmood ce.... " Cike da murna tace"Laaah! anty da gaske?zaki Haifa min cousins kamarsu Ablan mum meema? "    Sosae maganarta ya bani kunya,lallai Jasmin akwai surutu,sae da Momi ta fito ta tsawatar mata sannan ta nutsu,na umarceta data zauna muci tsiren tare. Usee ya tsura mata idanuwa yace"Wai har bakin nan yasan wani abu waishi cousin,sae shegen surutun tsiya..... "    Dariya muka fashe dashi daga ni har momin,ita kuwa Jasmin turo baki gaba tayi alamun shagwaba.Muna haka ne fa sae ga uban gayyar yayi sallama ya shigo.Dago kai nayi na xuba masa ido,wani mugun kallo naga ya watso min,da sauri na sadda kai kasa xuciyata na cigaba da bugawa da sauri da sauri.Jasmin ce taje ta rungumeshi tana masa oyoyo.     Umma ita kuwa k'yautar turaren wuta kala-kala ta bani,sae kuma turamen zannuwa masu tsada biyu da leshi itama meh tsada,wai gudummawarta kenan agareni,ba yawa,sosae nayi mata godia,ta tabbatar min da cewar insha Allahu suna nan xuwa Susan gidanmu na can Zaria,wai adalilina Zata zo tasan inda dan nata ke zaune.      Haka muka baro gidan,ya tsaya awata eatery yayi mana take away,har muka iso gidan babu maganar data shiga tsakanina dashi,abincin mah ayau kowa ciyar da kansa yayi amma de ah plate daya mukaci,wanka mah yau daban daban akayi,da muka zo kwanciya bacci sae na kasa haquri ganin ya juya min baya.Mirginowa nayi tare da rungume bayansa,kana na fashe da kuka nace"Haba mijina wai har yanxu fushin kake dani?don Allah ka sassauta min walhi xuciyata bazata iya daukar wannan hukuncin ba,duk wani dak'ika dake tafiya tare suke wucewa da tsananin son da nake maka,pls my jannah don't turn ur back on me,Wallahi Zahmood bazata iya rayuwa ba tare da ganin walwalarka da kuma kulawarka agareta ba...... "     Wani sassanyar ajiyar xuciya ya sauke,yana meh jin wani irin mugun sonta da kuma qaunarta na kara shigar xuciyarsa dakyau.Ahankali ya juyo gareta har suna hada numfashi don sosae tsinin hancinsa ya manne da tata hancin. Yace"Zahmood abinda nake son ki sani shine,ni mutum ne meh zazzafar kishi akan duk wani abinda nakeso,nasan Usman kanina ne amma sam banso kikayi maganar runguma agabana ba,haka kuma banso ganinki kina cin abu ah plate daya dashi ba,sae naji haushinku duka alokacin,amma yanxu tunda kin gane kuskurenki sae ki kiyaye gaba.... "    "Dear nah bazan sake ba Wallahi... " Murmushi yayi yace"Yauwah dats my baby,I so much love you Zahmood.... "     Daga nan labarin ya soma sauya zani,ya cika alqawarinsa don seda kwalliya ta biya kudin sabulu kamar yadda ya fada.      *** Washeqari qarfe goma tayi mana ah garin Zaria.tsarin gidana yayi min ba kadan ba,gidan de gata madaidaiciya amma se shegen k'yau.Yace na shirya muje gidanmu.Har tsalle saida na doka don murna.Gidansu Ash muka soma zuwa,ba karamin murna tayi da ganina ba,donshi awaje ya tsaya ni kuma na shiga ciki.     Tace"Fateenah kin gan yadda kika sauya kuwa?dama can ke meh k'yan ce sae kuma gashi kin kara akan nada,har wani mazaunai kika ajje fa,lallai agaida wannan Mahmood din agaskia yana kular mana dake yadda ya kamata,Masha Allah aure akwai dadi Muma Allah ya nuna mana tamu da Bash Dina.... "    Dundu na sakar mata abaya nace"Mara kunya kawai,ni tashi muje ki min rakiya kada ya gaji da jirana don har gida zamu.... " Muka fito nayiwa Maminta sallama tana ta shi min albarqa ina amsawa.     "Fateenah fatarmu de ayanxu Allah yasa Mubeen ya karbi kaddararsa..... " ta fadi hakan sanda muka fito daga cikin gidan. Ahankali nace"Ameen fa Sahibata.... "     Sun gaisa sosae da Mahmood dina,tace"Yallabai ngd kwarai da gaske gaskia aikinka na kyau don ga zahiri nan na gani ajikin Fateenah.... " Murmushi kawai mukayi daga ni har shi.Har gidansu Suhaima saida mukaje,muka tarar da Leedar agida,rasa inda Suhaima Zata sakani tayi don murna,shi kuwa Leedar wani kunyata yake ji,na nuna masa wlh babu komai don yanxu ni ina son mijina,har cikin gidan muka shiga muka gaida surukanta,suma din sun sanya mana albarqa sosai.Itama din Suhaimar irin Zancen Ash tamin wato Allah yasa idan Mubarak ya dawo ya karbi kaddararsa.     Daga k'arshe muka sauka can gidanmu,Umma na ganina tace"Saukar yaushe? "        Nace"safiyar yau dinnan wlh... " "Kedai wlh sam baki da hankali 'yar Kareematu,fisabilillahi yanxu sae da kika tasa bawan Allah agaba ya kawoki ganin gida daga dawowarku yau yau? "       "Ummana nasan dama ke kadai ce bakiyi kewata ba... " bata tankani ba  illa juyawa da tayi tana k'arbawa Mahmood gaisuwa wanda sae faman dariya yaketa mana.Abba mah sosai yayi farin cikin ganinmu don gabaki daya suna lambun shaqatawar gidan ne,kannena mah kamar zasu kada ni don murnar ganina.Sae yamma Mahmood ya dawo daukata,Umma ta tambeyeni babu matsala ko? Nace mata lafiya lau muke zaune amma ban gaya mata cewar ai Mahmood dan'uwan Mubarak bane balle na gaya mata abinda ke going,nafison Koda ace zasuji wani abin toh se bayan komai ya lafa idan Mubeen ya dawo.Abba yai mana nasihu sosai sannan muka baro gidan,Abba yace kannena nanan xuwa min weekend meh zuwa don washeqari Monday zamuyi resuming school.       *** wata irin shaquwace da kuma qaunar junanmu ya kara k'arfi atsakaninmu,rayuwar aure muke nida Mahmood abar kwatance da sha'awa.Tare muke tafiya makaranta kullum,idan na gama lectures sae naje office dinsa na jirashi har ya tashi.        ** **INA LABARIN MIJIN JIDDOH?**     Mubeen rayuwarsa yake babu yabo ba fallasa acan kasar Indiar,kwata-kwata mah ya dena nemar Mahmood awaya tunda idan ya k'ira baya dagawa,kuma ko kadan beyi gangancin gayawa wani nasa ba don baya son Mummy tasan cewar har yanxu yana tare da Fadima,amma kuma da Zarar ya dawo dole kuwa ta sani kuma dole ya auri Zahransa.Tunda Hanan taga Fadima amatsayin matar Mahmood,toh tun daga ranar duk wata walwalarta ta raqu wanda har hakan yasa Mubarak ya Dago cewar lallai matar tasa bata lafiya.Juyin duniyar nan yayi da ita akan ta fada masa abinda ke damunta amma se tace masa babu komai wallahi.Hakan ya kara sakashi cikin damuwa,ga rashin ji daga Zahransa,sannan yanxu kuma ga damuwar Hanan dinsa,duk yabi ya zama wani iri dashi don babu wani kwanciyar hankali atare dashi,abinda yaje yi mah sam baya wani concentrating akai,ganin hakan ya sanya abokan aikinsa k'iran CMD suka gaya masa halin da Mubarak din ke ciki tun ranar da suka sauka k'asar India.Dr.Shamsu sam beji dadin wannan al'amarin ba,aganinsa akan Hanan ne Mubeen din ya shiga cikin wannan damuwar,ya k'ira yace masa yana gama first 3months din kawai ya dawo gida,Mubeen ba karamin murna yayi da hakan ba,se yaki gayawa kowa nasa randa ze dawo.Tun asannan ne ya soma k'irgen ranakun daya rage masa ah Indiar.Ayanxu haka sati guda cur! kawai ya rage masa ya dawo.        **** watarana bayan mun gama morning lectures,sae kawai naji ina jin bak'on al'amari ajikina,zazzabi meh k'arfin gaske naji yana nemar rufeni,nayiwa Ash sallama na nufi office din Mahmood.Yana ganina ya taso arud'e yana fadin"My Zahmood yaya dai? Meya sameki?"   Amai shine ya biyo bayan tambayoyinsa,amai nake kamar zan amayo hanjin cikina,duk yabi ya rud'e.Students din da suke cikin office din sae ce min suke "Sorry ma,it shall be well with you.... "      Saida Mahmood ya wanke min fuska,wani student ya taimaka yayi clearing inda nayi amai.Ya daukeni kamar wata 'yar baby yana fadin"Dolene muje asibiti Zahmood jikinki yayi zafi sosai.... " cikin tashin hankali ya fice dani ahannunsa,ni kuwa babu damar kwatar kaina don gabaki daya jikina ya mutu.Ya umarce wani acikin students din daya rufe masa office,ya rufe ya mik'a masa makullan.    Yace dasu"Am sorry for the inconvenience..... Wen I get back I will attend to u all properly,buh for now I hav to take care of my wife... " . yayi gaba da sauri yana fadin"My Zahmood sannu kinji insha Allah it shall be well with you.Mutane kuwa sae binsu ake da kallo cike da shaawar wannan soyayyar tasu.     Babu bata lokaci ya Isa ga motarsa ya fice daga makarantar aguje,ahankali na furta"Dear nah I think am carrying ur baby........ " Cike da murna yace"Wayyyo Allah Zahmood are you serious? Da gaske kike na kusa zama uba? Yanxu nima an kusa kirana da baba kenan? "    Juyawa nayi ina kallon yadda yake zuba sambatu,hawaye na gangarowa Saman kuncinsa,abin gwanin ban tausayi,sae nima naji kawai hawaye ya ziraro min tare da jin sonsa na qaruwa acikin xuciyata. Asibitin mah haka aka kara tabbatar masa da lallai ina dauke da juna biyu na tsawon sati uku.Har k'yauta sae da Mahmood ya baiwa likita na wannan albishir daya masa.      Wani sabon tattalina yake daga ni har babyn tamu,na musamman ya dauki hutun sati guda yana kula dani,don rashin kunya Mahmood har kiran yan'uwansa yayi akan an samu karuwa,babu wanda yakai Momi murnar samun wannan karuwar,alast ta kusa ganin jikokinta daga bangaren babban danta.Bayan kwana biyu kuwa sae ga mutan kano anzo dubiyata hadda su 'yan gidan Baba mu'azzam,har gidanmu saida Mahmood yakaisu hadda Hajiyarsa don sada zumunci,ita kuwa Ummana Sau daya tazo da kannena,Suhaima mah haka,ita kuwa Ash tayi zuwa har sau hudu kenan.Aranar suka koma Kano.bayan sati guda na ware,na danji dan dama-dama har na soma zuwa makaranta,amma ko kadan Mahmood baya bari ina aiki,duk abinda nakeso shike tashiwa ya dauko min ita,wai shi baya son na wahalar masa da babynsa,nace ai kuwa idan baya bari ina dan motsa jiki toh kuwa haihuwar tana iya zuwar min da dan gaddama,shine fa yadan soma barina ina dan taba wani aikin amma ba sosai ba.       **** **BAYAN SATI GUDA**    Akace rana bata k'arya sede uwar diya taji kunya,sannu-sannu bata hana zuwa sede adade ba'a kai ba.Ayau misalin qarfe biyu Mubarak ya diro Nigeria,ta Lagos suka sauka,suka sake shiga jirgin da ze saukesu akano.Bayan 1hr 40mins suka iso Kano ta dabo tumbin giya.Be Sanar da kowa batun dawowarsa ba balle yasa ran za'a taho daukarsa,babu b'ata lokaci yayi shatar adaidaita.Har kofar gidan aka kawoshi.     Momi itace wacce ya soma hangowa ah tsakar gidan tana baiwa kajin da take kiwo abincinsu. "Assalamu alaykum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu..." Ya fadi hakan alokacin daya shigo cikin gidan sosai. Momi ce ta amsa sallamar tare da dago kanta,afirgice ta jefar da kwanon abincin kajin dake hannunta,tace"Wah nake gani haka agabana kamar d'ana Mubarak? "    Murmushin k'arfin halin ya sakar mata kana yace"Abin mamaki yanxu Momina dan naki ne kika kasa shaidawa kai tsaye?ko don na k'ara baki da kuma 'yar ramar danayi ne? " Da rawar murya tace"Eh fah hakane kam,ashe ba cewa kayi sae bayan watanni shidda zaka dawo ba? Ko kuwa bakada lafiya ne shine ka tashi ka kamo hanya ba tare da saninmu ba? "      "Momi hankalina zefi kwanciya idan ina kusa da Hauwa'u,idan ina ganinta zanfi jindadi,dama ko kadan banso wannan tafiyar ba sabida irin lalurarta ta laulayi meh tsanani,amma sabida matsa min da akayi shiyasa na tafi,koda naje can hankalina yaki kwanciya akanta shine oganmu yace kawai na dawo...... " Cike da fargaba Momi tace"Ai kuwa cikin nata da sauki sosae don bayan kwana bibbiyu Dr.Basira ke xuwa dubata,kuma ta tabbatar mana da cewar baby da mamanta lfy qalau suke,kuma she has about 70% assurance na cewar wannan k'aron da kanta zata haihu basai an barkata ba,eyyah Mubarak ai daka tsaya abinka ka gama abinda yakaika....... "    Murmushi kawai yayi yace"Bari na shiga ciki Momi... " kafin ta k'ara magana ya shige ciki jaye da trolley dinsa.Dif! duk wani network meh aiki ajikin Momi ya tsaya cak! ya dena aiki.Tana nan tsaya se tunane-tunane take,ahakan Usee ya shigo gidan yana cire earpiece akunnensa,cike da tashin hankali yace"Momi daga nesa na hango wani ya sauka daga cikin adaidaita har ya shigo cikin gidan nan kamar Yah Mubarak..... "     "Shine ba wai kama ba...... " Salati Usee ya saki tare da aza hannu duka biyun aka kamar wanda aka yiwa mutuwa.Wani irin zabura Momi tayi kamar wacce aka jonawa electric shock,tayi gaba da sauri sauri tana cewa"Usee taimaka ka kwashe min abincin kajin nan dana zubar,bari na kira Abbanku Mu'azzamu na fada masa cewar ya dawo....... "    "Toh" kawai ya iya cewa.Ta shige ciki,ada dakinta take da niyyar shiga don dauko wayarta amma se kuma ta Samu kanta da son yiwa su Mubarak lab'e.Da hanzari kuwa tayi dakin da aka sauki Hanan,ajikin kofar dakin ta lab'e tana sauraron maganarsu.    Kuka ta jiwo Hanan tana yi tare da rokansa"Haba mijin Hauwa'u yanxu har xuwa wannan lokacin baka cire Zahra aranka ba?aganina ya kamata ka shafeta daga cikin rayuwarka don I think Zahra ta maka nisa ba kadan ba...... " Wata uban tsawa ya doka mata,yace"Shut up! Jiddah..... Yanxu har ke kin isa kice na cire Zahra araina? Kin kuwa san yadda nake sonta kuwa?toh ayau ina son ki san cewar duk wani numfashi da nake shak'a tare nake shak'arsa da soyayyarta,bana tsammanin ko Momi mah wannan k'aron zata iya dakatar dani daga aurenta...."     Ya sassauta murya yace"Haba jiddan Mubarak ke kanki kin san nayi kokari sosae ba kadan ba da har nakai tsawon lokacin nan ah India ba tare da jin halin da Zahrata ke ciki ba,kullum idan munyi waya dake sae na gaya miki cewar har yanxu banji daga gareta ba,shine yanxu kike cewa na haqura da ita? Never! Wallahi,tashi ki dauko min makullin motata na kama hanyar Zaria yanxun nan kuwa...... "      "Haba Mubarak ko hutawa bakayi ba balle kasa koda ruwa ne acikinka shine kake tunanin kama hanyar Zaria ayanxu?ka bari ka huta mana..... "    Wani uban tsawa ya doka mata wanda hakan ba karamin firgitata yayi ba musamman mah Momi wacce har saida ta dan buge da k'ofa don tsananin firgici😁 Xuciyarsa ce ta bashi cewar kamar ana musu lab'e don haka da sauri ya nufi kofar yana fadin"Uban waye ne ke mana lab'e anan?" Azatonsa Usee ne don beyi tsammanin cewar Momi bace.     Ita kuwa Momi jin abinda ya fada ya sanyata hanzarin rugawa da gudu xuwa falo xuciyarta kamar zata fad'o waje don tsananin fargaba,tana iya cewa tunda take aduniyarta bata tab'a shiga irin wannan tashin hankalin ba kamar na yau. (Hahahah! Major general of soldiers ya dawo).😀😂 Ita kuwa Hanan har fitsari saida ta saki don tsananin tsoro.Koda ya lek'a sae yaga wayam!babu kowa,xuwa yayi ya lek'a falon,sae yayi ido hudu da Momi wacce sae faman sauke ajiyar xuciya take,jikinsa ne yayi sanyi qalau kamar kankara don jikinsa ya bashi cewar itace ta musu lab'en.       "Mubarak zoka zauna muyi magana..... " Gabansa ne yaji ya bada rass!,wato kenan Momi taji xantukansa da Hanan kenan?toh taji din mana shide walhi bata isa ta hana masa auran Zahra ba don ba itace ta haifeshi ba balle tace idan tayi masa baki yana iya kamashi.(Anya mubarak? Matar data raineka tsakaninta da Allah ne kake tunanin idan ta maka baki bazai kamaka ba? Ina ganin kawai ka zauna ka sake tunani).      "Ina son kadan bani aron juz 1hr acikin lokacinka so nake muyi magana.... " ta fadi da rawar murya don har ga Allah tsoron Mubarak din ma take. Arayuwarsa ta duniya momi ita kadai ce macen da baze ya musa mata magana ba,amma akan Zahra wannan k'aron sede ta nemi wani Mubarak din amma bashi ba.    "Toh" kawai ya iya cewa don kwarai yana son yaji ta bakinta kafin ya amayar da tasa.Samin gu yayi ya zauna,se alokacin Usee ya shigo suka gaisa da yayan nasa,har yake tambayarsa ya hanya? Ba yabo ba fallasa ya amsa masa. Hanan kuwa ta fito sae kuka take rik'e da key motarsa ahannunta,wuri guda ta tsaya cak! tama kasa karasa gareshi sae shesshek'a take,shi kuwa kallo daya yayi mata kana ya dauke kansa daga gareta.    Momi ce tayi mata ido,ai kuwa da hanzari ta shiga cikin taitayinta tare da samin hannun wata kujera ta zauna.Momi ta shige dakinta,da rawar hannu ta lalubo wayarta ta latso Baba Mu'azzam take gaya masa cewar ai Mubarak ya dawo,yace gashi nan tafe yanxun nan kuwa kada akuskura abari Mubarak din ya fita,ta de amsa masa da "insha Allahu" ne,don idan ya nemi fitar tasan ko ita ayanxu bata isa ta hana masa fita ba yadda idanuwansa suka rufe da tashin hankalin nan.Ta latso su Mahmood shima ta gaya masa,yace gasu nan tafe suma,duk 'ya'yanta mata saida ta kirasu suma Cike da tashin hankali sukace gasu nan tafe.Tace kada asake ataho da yara abarsu ahannun masu aikin gida,tama gode Jasmin na gidan Meema don haka komai zaizo musu da dan dama dama don bata qaunar yara su gigice da wannan tashin hankalin da suke shirin fuskata............... 📝    A/N Tofa! bilhaqqi yau ake yinta,fire on the mountain kadan-kadan,ku agaza musu da taimakon gaggawa ta yan fire service 😁     Last episode coming soon ending of diz week insha Allah!! Longest chapter so far!!        *HAFNAN CE💞*