Nihaad Book 1 Complete Hausa Novels Hausa Novels Online

107 5

Nihaad Book 1 Complete Hausa Novels

  • Mon 03, 2025
  • Love Stories

Description

πŸ’–πŸ’– *NIHAAD* πŸ’–πŸ’–


By Khaleesat HaiydarπŸ“–βœπŸ»


~
1


All thanks to Allah SWT for giving me the ability and privilege to present to you this book. My mother Hajiya Hajarah Allah ya karo farin ciki da kwanciyar hankali da arziki me amfani, Allah ya saka maki da gidan Aljanna, πŸ‘πŸ» my special greetings to my own Barrister KH, Allah ya jibanci lamarinka, ya kara bude hanyoyin arzikin da xa ayi ma addini hidimaπŸ’– and My lovely aunt Rukayya Allah ya raya su Lil Khaleesat ya kara maki kwanciyar hankali.. And then my fans, i am who i am as a result of u guys, i love you all for the support always, Allah ya baku farin cikin duniya da na kiyama.... As usual support ur writer and may God bless u.

 

Tun da ta ji furucin wan Abbanta na karshe ta sakar masu kuka me karfin gaske, ta kalli Mahaifiyarta dake goge hawayen dake sauka idonta, babu alamar dai xata ce komai, Ta kalli Abba da fuskarsa ke hade tamkar hadari, shi ma bata samu courage din ce masa komai ba, yayyinta maza biyu dake parlon babu wanda yace komai cikinsu, ta dinga kuka da shesheka ta kalli Umma warce tayi tagumi, kallon Kakarta dake girgiza kafa tayi cikin rawan murya ta kamo hannunta tace "Don girman Allah kice su yi hakuri sharrin shaidan ne, don Allah kice su yafe min, ni ban san wanda yayi min haka ba..." Kakar ta warce hannunta tace "Ja can, Ke har kinsan sharrin shaidan alhalin kece shaidaniyar Nihad, ai kafin ki dauko mana abun kunya gwara tun wuri mu kunyata ki, ki ce lalle ke sai kin xama mutuniyar banxa abinda kaf xuri'a babu? Me yake burgeki da rayuwar 'ya yan iska har wannan abu ya same ki haka?" Kuka kakar ta saki tace "Allah mun gode maka, ka haifi Ι—a ne kawai baka haifi halinsa ba, yanxu meye wannan kika mana Nihad" Mikewa Nihad tayi tana kuka sosai ta fice daga parlon, direct dakinta ta nufa don tasan ko me xata ce a parlon nan babu wanda xae saurareta, tunda har Umma ma ta ki cewa komai to babu wanda xai ce komai, bayan ta shiga daki ta sa makulli ta fada kan gado tana rusa kuka kamar ranta xai fita, is this actually happening to her? yanda ta ga rana haka ta ga dare, gashi ta kasa sallah ko da raka'a daya ne, gaba daya ta fice hayyacinta, she wish all this is nothing but a dream, she wish xata farka taga mummunan mafarki kawai take, da asuba aka murda kofar dakin ta daga idonta da suka kumbura tana kallon kofar amma bata da niyyar tashi ta bude, har aka gaji da Knocking aka bar wajen. Sai wajen karfe takwas na safe tana xaune saman darduma ta jawo wayarta da kyar, rabonta da wayar tun shekaranjiya, gaba daya bata son abinda xai hadata da wayar ma balle xuciyarta ya kara rauni, yanxun ma da ta dauko sim card dinta take son cirewa ta karya, missed calls da ta gani ya doshi hamsin, da messages da ya ninka calls din, ko wani message xance daya ne content dinsa, "Is that you on social media Nihad?" "Nihad what came over u?" "Nihad what is happening?" "Nihad something is wrong somewhere, ur Video is all over the internet" Fita tayi daga Inbox din hawaye me xafi na sauka idonta, ta bude WhatsApp shi ma dai duk messages din ne har da videos... Kashe wayar tayi ta ciro sim card din ta karya kamar yanda tayi niyya sannan ta jefar da wayar saman gado tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, wayyo ina ka xata farka taga mafarki kawai take da gaske, tun shekaranjiya take wish din nan, amma taki farkawa wanda hakan ke kara tabbatar mata da gaske ne duk abinda ke faruwa, babu wani xancen mafarki, Knocking din kofa aka yi, ta kalli kofar sai kuma ta mike a hankali ta nufi kofar ta bude, Umma ta gani tsaye, nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta, Umma ta shigo dakin ta kulle kofar, Nihad ta bi ta da kallo har ta xauna gefen gado, Nihad ta karasa inda take ta durkusa kasa cikin sanyin murya tace "Umma don girman Allah ku rufa min asiri kar ayi min haka, wllh xan iya mutuwa, talk to Abba plss" Umma ta sauke wani ajiyar xuciya tace "It's too late Nihad, tun da har Alhaji Abubakar ne ya yanke hukuncin nan kema kinsan babu me ja da wannan hukunci nasa, ke dai naki addu'a, mu ma kuma muna nan muna taya ki da shi, it's okay to make mistakes as long as we learn from them, so ki kwantar da hankalinki everything will be alright, kuma koma waye ya aikata maki haka sai dai mu ce Allah ya shiryesa" Ta rushe da wani kuka cikin tashin hankali take cewa "Na shiga uku Umma, yanxu baxa ki iya ce ma Abba komai ba? auren dole fa xa su min, Umma ya xan yi da raina idan hakan ya faru, na shiga uku na..." Mikewa Umma tayi ta nufi kofa ta fita ta kulle.  Compound Umma ta fita ta tarda Abba dake xaune shi kadai kana ganinsa kasan yayi nisa a tunanin da yake, ta nufesa ta ja daya daga kujerun dake wajen ta xauna tana kallonsa da damuwa karara fuskarta, he looks so disturbed also, ta kwantar da murya tace "Damuwa ba shi ne mafita ba Ranka shi dade, kayi hakuri ka sa ma ranka salama, Allah ne ya tsara haka, sai mu gode masa mu kara gode masa kawai" Abba ya numfasa yace "I think aurar da Nihad yanzu ba shi ne mafita ba Sumayyah, amma Engineer da Hajiya baxa su fahimci hakan ba, she is just 19, ga kuma wannan abu da ya faru, ta ina xata fara xaman aure bata gama mallakan hankalin kanta ba? da xa su sake shawara da ni da na ce masu gwara kawai ta tafi waje ta karasa karatun ta a can, ko da Uk ne...." Umma dake ta kallonsa tace "Wannan gaskiya ne, aurar da Nihad is not a way out, amma ni dai shawarata kar ka tofa naka a issue din nan Yallabai, duk yanda Yaya yayi da Nihad dai dai ne don 'er sa ce, kuma ran Hajiya xae 6aci idan ka bijiro da wannan batun na taje waje tayi karatu, gani kawai xa su yi kana ma goyon bayanta ne, naka kawai ido sannan kayi mata fatan alkhairi duk yanda suka yi da ita er su ce, kuma baxa su yi abinda xai cuceta ba, tunda suka ce aure mu xuba masu ido duk yanda suka yi dai dai ne, shawara ta biyu kuma kada ka kuskura Yaya yace xai hada Nihad da daya daga 'ya yansa balle ma bana tunanin xa ayi hakan kawai in case xa a bijiro da wannan gaskiya ka nuna a'a, don in har aka yi hakan zumunci xae tarwatse kasan su waye 'ya yan nasa da iyayensu, yara ne masu ji da kansu wa enda ba sa rayuwa a kasar, don haka kar ka soma yarda... don walakantattciya xasu mayar mana da er mu, ni yallabai yanda video din nan nata ya tafi viral gwara kawai a samo wani da ba kowa ba, bawan Allah wanda ba ma shi da abun duniya, shi kadai xai iya aurenta ya rufa mata asiri su xauna lafiya ba tare da ya goranta mata wataran ba, bai kuma walakanta mana ita ba, kyau ace ma a karkara yake rayuwarsa yallabai" Abba ya daga kai yana mata wani kallo babu ko kiftawa, tace "Atoh Allah ya baka hakuri, ka samo wani d'an senator ko Attajiri ka hadasu kawai, hakan ma dai dai ne...." Tana kai wa nan ta mike ta ce "Allah ya rufa asiri, ya tsare yan baya" Daga haka ta bar wajen, Abba ya dafe kansa. Umma ta saka Abba tunani iri iri bayan ta bar sa a wajen, ta wani bangaren she is damn right, abinda ta fada gaskiya ne, babu wanda xai yi ma tayin Nihad ya amsa da farin ciki ko dadin rai, Nihad is nothing but a disappointment to him, bai taba xaton hakan daga gareta ba kuma yayi da ya sanin fifitata da yayi cikin duk 'ya yansa, yayi da ya sanin nuna mata so karara da yayi kan sauran 'ya yan sa, amma Alhmdlh tunda abinda tayi ya tsaya iya haka, shawaran da Umma ta basa kuma shi xai yi amfani da... Mai gadi ne ya bude gate jin ana horn, Abba ya bi motar da ta shigo compound din da ido har yayi parking, yana xaune aka samesa cikin ladabi ya mika masa ledan dake hannunsa yace "Ga aiken Alhaji" mikewa Abba yayi yace "Mu je can parlor daga nan ka kwashi takalman da xa ayi min polish ka ba mai gadi" Abba na gaba yana biye da shi a baya har suka shiga cikin babban parlon gidan, sannan main parlor din Abba, Abba ya xauna yace "Ka Ι—an jira xan yi waya, xan sake aikenka ne"  Mai gadi ne xaune a position dinsa tare da driver, mai gadin yayi kasa da murya yace "Ka ko ji abinda ke faruwa kuwa??" Drivern yace "Me ke faruwa?" Mai gadi ya bi compound din da ido kafin cikin rada yace "Daxu Saminu ya xo ya nuna min nima a waya, wllh na gani.." Driver yace "Me ka ga?" Mai gadi ya kai baki kunnensa cikin rada sosai yace "Wllh hoton tsaraicin fitsararriyar yarinyar nan ne duk ya baxu yanar gizo, da idona na gani a wayar Saminu, kai baka ganin duk gidan kamar anyi mutuwa ba, ai duk gidan alhini suke, Da yake baka da babban waya baxa ka gani ba" Driver ya kallesa da kyau yace "Tsaraici?" Mai gadi ya kwashe da dariya yace "Yo tsaraici mana, yar kamfai da rigar mama kawai ne a jikinta kuma hoto me motsi aka mata, duk halittar jikinta babu wanda bai fito ba malam, abun dai ba a cewa komai, ni Alhaji ne ma ke ban tausayi don ya shiga damuwa sosai" Yana kallon mai gadin yace "Kai a ina ka gani??" Mai gadi yace "Toh jira ka ga ikon Allah" yana fadin haka ya nufi boys quarters da sauri, ba a dau lkci ba sai gashi ya dawo rike da wayar saminu, ya mika masa, amsa yayi ya danna play a video din, ko second goma bai yi da kallon ba ya ajiye wayar gefensa yana kallon Mai gadin, Mai gadin ya kwashe da dariya yace "Toh dada, muma duk haka muka gani, Allah kadai yasan iyakar inda abun nan yaje, shi ma a wani gruf ya gani wai, har fesbook yace min ya gani, kaga daga yanxu sai dai ta daga ma wasu kai ba mu ba kuma" Dariya mai gadin ya kyalkyale da, Driver ya mike yace "Ga takalma in ji Alhaji a ba shoe shiner" Daga haka ya tafi boys quarters. Nihad na kwance edge din gadonta ta kafa ma agogon dake manne bangon dakinta ido, xuwa yanxu kam ta hakura da kukan da take, but she is so weak, har ta mance rabonta da wani abinci, babu wanda ke bin ta kanta a gidan banda Umma dake shigowa dakin nata lkci lkci, she still don't have the courage to go to her mother, Bude kofar dakin aka yi ta daga kai da sauri, Husnah ce ta shigo dakin da sallama fuskarta dauke da damuwa, ta karasa kusa da ita ta xauna gefen ta amma ta kasa cewa komai, Nihad din ma dai bata ce mata komai ba, Husnah ta sauke ajiyar xuciya tace "Kar ki sa ma kanki wani ciwon kawata, duk abinda ya faru da mutum a rayuwa dama Allah ya tsara hakan, kiyi hakuri da kaddaranki, kiyi hakuri kiyi accepting with good faith" Lkci daya hawaye ya kawo idon Nihad, Husnah da ita ma har hawayen ya cika idonta tace "Pls have faith don Allah Nihad, koma waye yayi maki wannan abun Allah baxai bar sa haka ba, tun a duniya Allah xai bi maki hakkinki, ya saka maki" Nihad ta mike xaune ta fashe da kuka tace "Ji nake kamar in kashe kaina Husnah" Husnah ta rufe bakinta da sauri tace "Kiyi istigifari, who are u not to be tested by Allah?? Kar ki kuma fadin hakan, kowa da irin tasa kaddaran a rayuwa, ki dau naki with good faith nace maki, in sha Allah xaki cinye wannan jarabawan, muna nan muna maki addu'a, Allah ya rufe abun cikin gaggawa a daina yawo da shi a media" Nihad ta share idonta a hankali tace "How will i mend this damage?" Husnah tace "Allah will, ke dai ki ci gaba da addu'a, wllh kawata tunda naga abun nan Allah ya sani baccin kirki for the pass 3 days ban yi ba, amma koma waye yayi mana haka xai ga sakkaya daga wajen Allah, sai Allah ya saka mana" Nihad ta sunkuyar da kai a hankali tace "Kuma fa wai aure Uncle dina da Inna suka ce xa ayi min" Husnah ta xaro ido tace "What?? Aure?? Which of ur uncle are u talking about? Abbansu Hamid??" Nihad ta gyada mata kai, Husnah ta rike ha6a tace "But sorry to say Nihad yanxu duk rashin jin da su Zeenat da Pinky ke yi bai gani ba sai naki? Duk runz din da suke yi babu wanda ya hango nasu sai naki? Lallai kam ance laifi tudu ne, Kawai sbda wani axxalumin yaje yayi posting dinki halve naked shine xa ace xa a maki aure? Wa enda ma aka saki hotunansu fully naked ba ace xa a masu aure ba sai ke da naki nafila ne, Tabdi... to wai wa suka ce xa su aura maki?" Nihad tace "I don't even know, but i am thinking of running away" Husnah tace "Nima nayi wannan tunanin, kada ki wani tsaya a cuceki a...." Bude kofa aka yi duk suka yi shiru suka juya suna kallon kofar, Yaya Farooq ne ya shigo dakin, Nihad sai da zuciyarta ya kusa shigewa cikinta don bata mance dukan tsiyan da yayi mata shekaranjiya ba, banda ma Umma ta masa jan ido ta kwaceta a hannunsa, Ya wani murtuke fuska yana kallon Husnah cikin daga murya yace "Ke, Uban wa ya baki permission din shigowa gidan nan, ta ina ma kika shigo don uwarki??" Husnah ta mike tana sissinne kai jikinta na 6ari, Ita dai Nihad banda faduwa babu abinda gabanta yake har ta fara kallon bandaki ko can xata shige ta kulle, Ya daka ma Husnah wani raxanannen tsawa yace "Xo ki fita kar in karya ki in karya banza" Jakarta ta dauka ta nufi kofa da sauri har tana tuntube, Tana fita ya doka ma Nihad wata harara yace "Kin ga result din bin ire iren kawayen nan ai..." Cikin rawar murya tace "Yaya ita Husnah ai babu ruwan..." Haureta ya kai kafa xai yi ta kauce, ta fashe da matsanancin kuka dai dai shigowar Umma, Umma na ganinsa, tana tafe hannu tace "Wato duk warning din da na maka bai isheka ba ko Farooq? Duk jan kunnen da nayi maka kar ka sake dawowa hanyar dakin nan watsi kayi da shi sbda ban isa ba ko?? To uban naku ma da ya ga abun nan ko nunata da yatsa bai yi ba balle ya kai mata hannu, kai ko zagi bai hadasa da ita ba, to wai shin ma ina ruwanka farooq? Meye naka? To wllh ka shiga hankalinka ka fita harkarta a gidan nan, ka shiga hankalinka nace, Shi Usman da yake ba mahaukaci bane ai nasiha kadai ya hadasa da ita, tun daga sannan ma a ina ta sake saka sa a ido, abun nan dai naga ba yaki bane, kai iskancin da kake sani ake yi balle a tsawatar maka?? To ahir dinka farooq kar ka kuskura in nuna maka bacin rai na wllh" Ita dai Nihad shessheka kawai take, shi kam banda kallon mahaifiyarsa babu abinda yake, ji yake kamar ya karya Nihad ko xai ji sauki a ransa, juyawa yayi ya fice daga dakin kamar xai tashi sama, Umma ta bi sa da harara, sai kuma ta ja tsaki tace "Rabu da shi, ba kanki farau ba ai" Daga haka ita ma ta fice daga dakin. Bayan magrib Nihad ta dake ta fita dakinta for the first time tun da gari ya waye, part din mum dinta ta nufa, duk gaba daya jikinta a sanyaye yake, ta bude kofar parlon a hankali Mumy na xaune parlon da sisters dinta biyu, tun jiya suke gidan amma ko bin ta kanta su ma basa yi, abun duniya duk ya ishesu barin da suka ga damuwar da yayarsu ta shiga, Nihad dai tunda Umma ta kwace ta a hannun Aunty Jamila rabonta da su sai kuma yanxu, banda faduwa babu abinda xuciyarta ke yi, Mumy ta nuna mata kofa alamar ta fita, kuka ta sakar mata ta xube nan bakin kofar cikin rawan murya tace "Don Allah Mumy kiyi hakuri ki yafe min, wllh i don't know how all this happen, i don't know who did this to me, mumy ba halina bane don Allah ki saurareni" Mumy tace "Fita nace Nihad" Kallon Aunties dinta tayi tana girgiza kai wasu sabbin hawayen na sauko mata tace "Aunty Jamila don Allah ku ce Mumy ta yafe min" Ganin Mumy ta mike, ta tashi da sauri ta fice daga parlon xuciyarta na bugawa, kuka take sosai bata da option ta nufi dakin yayanta farooq, bata tadda shi a dakin ba ta rakube jikin kofa tana shessheka, ba a dau lkci ba ya shigo dakin daga masallaci, yana kokarin kulle kofar ya ganta, kan yace komai ta hade hannunta with tears tace "Ya farooq don Allah ka saurareni, only u will understand and listen to me, wllh i knew nothing about that video, ban san wa yayi min ba, ban san yaushe aka min ba, ban kuma san wanda ya fitar ba" Kuka take sosai, ya daure fuska yace "Shaye shaye kika fara da har baki san when and where aka maki video din ba Nihad??" tace "Believe me yaya Farooq, wllh ban sani ba, yanda ku ka gansa haka nima na gansa" Yace "Na rabaki da bin kawaye barkatai Nihad, na rabaki da yawace yawace da xuwa parties, har night party nasan kina xuwa don Sadeeq saw u, na maki magana kika karyatasa kamar bai san me yake ba, u are just different from every other child in this house, just look at the disgrace u have caused to our family, u have tarnished the reputation of our home, how will i face my frnds da suka sanki, my own blood with such act? Oh no, Subhanallah" Ta dinga girgiza masa kai tace "Don Allah ku yi hakuri yaya, i wish my life can end now because of all this, i regret everything" Xaunawa yayi gefen gado ransa a dagule, ita dai ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "Yaya farooq i need one favor from u plss" Yace "U don't deserve that favor Nihad" tace "Plss yaya abu na karshe da xa ka iya min a rayuwa shine don Allah kar ka bari Abba su yi min auren dole, wllh xan iya mutuwa kaga har na gaya maka" Yace "What did ur boyfriend say about the video?" A hankali ta sunkuyar da kai tayi shiru, ya hade rai yace "Tambayarki nake" Cikin rawan murya tace "Yayi blocking dina...." Farooq ya gyada kai yace "Good" ta hade hannunta tace "Don Allah yaya, kasan consequences din auren dole kar ku bari ayi min, na yarda a min ko wani hukunci amma banda auren dole, idan ma xa a ce for the rest of my life baxan sake fita waje ba, sannan babu ni babu karatu har abada i agree but kar ayi min auren dole sbda wannan mistake din nawa, ka taimaka kayi ma Abba magana"  Umma ce ta shigo dakin duk suka daga kai suna kallonta, tace "So kike ki kara tunxura Abbanki Nihad? Duk shirun da yayi maki bai isheki ba sai kin tunxurasa, Ba na baki shawaran kar ki ce komai a kan batun auren nan ba, so kike ki fusatar da Abbanki yayi maki abinda bai ta6a maki ba?" Faruq yace "Noo wannan ba magana bace Umma, we don't even know da wanda xa a hadata, ko ma me tayi ai da gatanta and she still have her right, su gani suke auren shine way out, whereas it's not" Umma tace "Toh tunda kai ka haifesu ai sai ka gaya masu way out" Ya girgiza kai yace "Umma idan ma auren ne ba sai a bari komai ya lafa ba, ta yaya abu na xafi xafi a shigo da maganar aure, waye xai aureta? Noo bata yi deserving wannan auren ba gaskiya" Umma tace "Ko ma wa xai aureta wannan ba damuwarka bane sai ka xuba ma iyayenka ido, su ai sun san abinda ya kamata, ko so kake ka nuna masu goyan bayan abinda tayi kake?" Ya dinga kallon Ummar tasa, Mikewa yayi ya fice daga dakin, ta bi bayansa, Nihad ta bi su da kallo, sai da suka sauka stairs Umma tace "Farooq" ya juyo yana kallonta, tace "Naga kamar so kake ka ja ma kanka bakin jini gun Kakarku da Engineer, sannan nima hakan ya shafeni, kawai so kake ka ja min maganan da ba shi da ranan mutuwa gun tsohuwar nan, don haka kar ka sake tofa komai a kan lamarin nan, ita kanta uwar da ta haifeta taki cewa komai har yanzu, me magana dama daga ni sai kai, kuma a hakan ma haushinmu ake, don Usman ma bai tsoma kansa ba balle a ga nasa, to ba Uba daya ba, ko ciki daya ku ka fito da Nihad ni dai nace ka janye bakinka daga issue din nan domin a samu masalha, daxu Abban naku ma ya kirani wai ya tafi karkara neman wanda xai hadata da, to idan ana son asiri ya rufu ai sai dai hakan dama, to wa xai yarda ya aureta a nan dai cikin gari? don haka nake kara gargadinka, kar ma ka fara cewa a fasa aure" Faruq yace "Karkara kuma?" Umma tace "Ehh nan fa, ko ka ga alamar Nihad xata samu miji cikin gari ba karkaran ba nace, da wannan mummunan abin da ta aikata wa xae yarda nasa ya aureta?" Yace "Ah haba, karkara kuma, noo ba dai karkara ba, waye ya ba Abba wnn muguwar shawaran? Karkara fa kike ce Umma" Strictly Umma tace "Farooq" ya daga kai ya kalleta tace "I am giving u this serious warning, kada ka kuskura ka sake tofa naka a wannan lamarin, kaji abinda nace maka??" Bai ce mata komai ba, tace "To na dai gaya maka" daga haka ta bar wajen ya bi ta da ido.

πŸ’– *Bitter Rivalries*πŸ’–


And i came really prepared...... πŸ€—


Contact me directly viaπŸ‘‡πŸ»

07087865788✍🏻

πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–

 


By _Khaleesat Haiydar_πŸ“–βœπŸ»

 

~~
2

 

Dumbin gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga iyayen gidan Khaleesat's Palace, my die hard fansπŸ₯°πŸ˜ Su Hajjaju Chamo me gwala-gwalai duk da jarin ya karye amma take ta bobboye mana, Hajiya Aunty Zahra mai siyar da harawa, Hajiya Nafisa Mom twins, Su Hajiya Aunty Maryam, Uwar Nabeela, Mrs Jay, Hajiya Inna, Hajiya Deejah, Hajiya Zeenaru, Nanisa Zero Zero, Hajiya Bilkisu, Hajiya Rabia, Damsel, Uwar Yusrah, Ummu Zainab, Uwar gidan Barrister wato Khaleesat me siyar da tayoyi, kai duk wanda bai ga sunansa a nan ba ya biyo ni da sunan xai gansa a next page😜 amma fa ko kun ki ko kun so sai nayi sharing link dinku, ku tanadar ma sabbin fans ruwa da cin cin ehe.πŸ€“

 


Da daddare Abba na xaune parlonsa tare da Yayansa Alhaji Abubakar.... Alhaji Abubakar yace "Ae duk ba sai ka sanar masu komai ba, kawai gobe idan an daura auren kowa ma sai ya sani, i don't think u owe anybody explanation to this" Abba ya numfasa yace "Toh shikenan" Alhaji Abubakar yace "Yea i think that's okay ba sai kace ma kowa komai ba for now, a ina kace xa su xauna? I mean which of ur houses are they staying?" Abba yace "I don't think i can keep her where she will in any way feel comfy, i wish xai koma can karkarar tasu su xauna in basa enough jari, idan noma xai yi ma yayi employing workers su yi masa a can ko ni xan dinga biya, cause i want her to learn a bitter lesson of her life, ina son ta san wata rayuwar bayan rayuwa cikin daula" Alhaji Abubakar ya girgiza kai yace "No... There is no need for all that, duk abinda ya kamata kayi kar ka fasa, ka basu inda xa su xauna comfortably" Bayan Alhaji Abubakar ya bar gidan, Umma ta shigo parlon Abba, ganin basu ta6a abincin da ta ajiye masu ba tace "Haba yallabai, ko abincin baka ci ba har yanxu?" Abba yace "Kawai ayi min black tea" Umma tace "Toh shkkn" Tashi tayi ta dau abincin ta fita, ba a dau lkci da fitarta ba Farooq ya shigo parlon, waya ya tadda Abbansa ke yi, wanda da jin yanda yake amsa wayar kasan magana ce aka kirasa a kan Nihad kuma abokinsa ne me kiran nasa, Farooq ya sunkuyar da kansa duk jikinsa yayi sanyi, har Abba ya gama wayar ya jinginar da kai da kujera bai ce masa komai ba, a hankali Farooq ya dago yace "Barka da dare Abba" Abba ya amsa, Farooq yace "Throughout ina ta kiranka but couldn't reach u on phone" Abba yace "Ehh wata er tafiya nayi, is there any problem?" Farooq yace "Ya gajiyan hanya" Abba yace "Alhamdulillah" Farooq yayi kasa da murya yace "Abba magana ce dama a kan Nihad?" Dai dai nan Umma ta shigo da mug din black tea dake ta kamshi, Da hannu Abba yayi masa alamar ya aka yi, Farooq yayi shiru, Abba yace "Maganar me a kan Nihad Umar?" Farooq ya d'an fara kame kame, sai kuma dai kawai yace "Abba a kan auren nan da aka ce ne, is it not better a yi hakuri a janye, idan ya so..." Dakatar da shi Abba yayi yace "Idan wannan maganar ce ta kawo ka, ka je kawai i need rest Umar, kaga ban dade da shigowa gidan ba" Umma dai na xaune kan one sitter, pleadingly Farooq yace "Pls ka saurareni Abba" Abba yace "I said i need rest...." Umma tace "ka je yace xai huta ko kuwa?" Mikewa Farooq yayi ya fice daga parlon, Umma ta kalli Abba tace "Kayi hakuri Yallabai, xan so ka cire wannan damuwar a ranka, in sha Allah everything will be alright, kar kaje ka sa ma kanka wani ciwon bayan hawan jinin da kake fama da" Abba yayi sigh yana girgiza kai yace "A kalla ba a kirani a rana ba xa a kirani sau goma a kan Nihad, the video is trending day by day.... Me yafi wannan bakin ciki Sumayyah? A reputable person like me, noo Nihad tayi tarnishing image din gida na" Da damuwa Umma tace "To ya xa ayi Yallabai haka Allah ya kaddaro mana, sai dai kawai mu rungumi kaddara, amma akwai wani malami bawan Allah, tun ranan da abun ya faru Hajiya Sukhaina tace ko shi xa ayi ma magana yayi addu'a Allah ya kawo karshen trending din abun, shiru xaka ji kamar ba ayi ba wllh, neman video din ma xa ayi a rasa" Abba ya mata wani kallo yace "Malami? Wani irin malami?" Umma ta gyara xama tace "Ba boka fa nace ba Alhaji, amma dai shkkn kawai, ina ce akwai malamai bayin Allah wa enda..." Mikewa Abba yayi bayan ya dau mug din black tea dinsa ya wuce daki ya kulle kofa. Washegari friday ana sauka sallan juma'a, Abba ya tafi tare da yayansa da cousins dinsa biyu xuwa garin da aka daura ma Nihad aure, a kan sadaki dubu hamsin wanda shi ya bayar. Sai kusan la'asar suka dawo gida, nan kuma ya sanar ma Umma su fara shirye shiryen kai ta, Umma tayi shiru cike da jimami, sai kuma ta sauke ajiyar xuciya tace "To wani gidan kenan xa a kai ta yallabai?" Abba yace "Wannan gidan da aka gama na Rijiyar zaki, it's already furnished" Umma tace "Allah sarki, ina laifin wannan gidan na kusa da mu yallabai, ai xa su fi sakewa a nan..." Abba yace "Ban yi niyya ba" Umma tace "Rijiyar zakin ma yayi ai, Allah ya saka da alkhairi" mikewa tayi ta fita don xuwa sanar ma Mum din Nihad da Yan uwanta dake can bangarenta abinda Abba ya ce, nata side din ta fara shiga, first daughter dinta Kamila na xaune parlon sai second daughter dinta Amina, sannan kanninta mata biyu da suka xo daga Jigawa daxu, Umma tace "To duk ku shirya kai amarya an daura mata auren yau dai" Kamila ta riΖ™e ha6a tace "Har an daura?? yanxu Umma Abba bai fada maku da wa aka yi auren ba, ni kawai sai xuciyata ke bani Hamid ne ko Saif" Umma ta saki baki tace "Hamid? Ita uwar Hamid din karen hauka ya cijeta xata yarda a hada shi da Nihad? Ko kuma shi Hamid din mahaukaciya ne da zai amince da auren Nihad, Kai har shi Uban Hamid din da ya kirkiro auren ba yarda xai yi ayi auren da Ι—an sa ba karewa kenan, haka ita ma Innar, wani can dai Abban naku ya samo a karkara, hakan kuma kadai ne rufin asirinta a dai abin nan da ya faru" Amina ta mika ma Umma wayarta dake ring, Umma ta amsa ganin autarta ce ke kira ta daga ta kai kunne da murmushi tace "Hello auta, duk yau kin ji ni shiru ko" lkci daya ta hade rai tace "Ki zo kiyi me kina karatun ki Nihal? A kan wani dalili xaki taho kuna tsaka da karatu? To wllh kar ki fara idan ba haka ba yanxun nan in kira Farooq in gaya masa, me xuwanki xai sa a fasa, bayan har an daura auren ma, duk sanda ku ka yi hutu idan kin dawo sai kije ki ga dakin er uwar taki ba shikenan ba, amma ki wani ce xaki kamo hanya kamar ana yaki" a kufule Umma da ta gama sauraronta tace "To wai uban meye na wannan kukan da kike, so kike ki ja ma kanki wani ciwo ne ko ko? Bata da waya yanxu a hannu, idan na fita yanxu xan bata sai ku yi magana, amma ta ina xaki baro Zaria da yamman nan ba hutu ku ka yi ba, kuma dama kin ta6a dawowa gida ke kadai ne banda gulma da daura ma kai wahala Nihal?? Ni dai sai anjima ban san shashanci" Katse wayar Umma tayi, Aunty Laraba tace "Wai tahowa xata yi daga Zarian?" Umma tace "Ehh wai, kinji wata gulma dai, ko uban me xata xo tayi oho" Aunty Laraba tace "To wai ita tace ma Abban nasu bata son Maryam Abatcan da er uwar ke xuwa ne?" Umma tayi murmushi tace "Aa haka dai yayi niyya ita ya turata federal dai dai ita, ita kuma Nihad dama Private ne dai dai da ita inji uban, wato Maryam Abatcha, option ma ya bata ta xabi Private uni da take so shine ta xabi Maryam Abatcha" Aunty Maimuna tace "Ai ko ga Maryam Abatcha ana ta gani a soshiyal media" Umma dai bata ce komai ba, sai kuma tace "Allah dai ya shirya mana zuri'a kawai" daga haka ta fita xuwa bangaren mum din Nihad, a corridor ta hadu da matan Alhaji Abubakar su biyu sun shigo gidan, suka gaisa da fara'a ana kara jajanta lamarin da ya faru, Hajiya fatima tace "Daxu Abbansu Hamid ya dawo gida yake sanar mana ai har an daura aure, nace shine babu labari ko daga gare ku Hajiya" Umma tace "Wllh abun ne ya xo a haka Hajajju, kinsan muna ta tunanin xa su hakura a fasa auren a nemo wani solution, to kin san halin mazan namu da kafiya, wllh sun ki, kawai fatan Allah ya basu xaman lafiya da ko ma waye mijin" Hajiya Zuwaira tace "Shikenan addu'ar, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi a gareta, Allah kuma ya duba yan baya" Duk suka amsa da Ameen, Umma tace "Mu je dama bangaren Maryam din xan je" a tare suka tafi part din Mumy, bayan an gaisa an kara jajantawa, Mumy dai bin su kawai take da kallo bata cewa komai, Umma ta sanar mata abinda Abba yace sannan ta fita daga dakin. Bayan magrib xa a kai Nihad, kafin Magrib din Abba ya tara gaba daya matan nasa da 'ya yansa, Usman, Farooq, Kamila, Amina, Nihal ce kawai bata nan a yaran Umma, yaran Mumy kuwa Nihad da kanninta biyu wa enda duk maza ne, daya me shekara tara da kuma me shekara shidda duk basa parlon, Bayan duk sun hallara a parlon Abba ya nisa yace "Ina fatan duk kun ga abinda ya faru da yar uwarku Nihad, Nihad is nothing but a disappointment to the family, kar ku ga Nihad tayi wannan mummunan laifin na bada ita ga wanda nayi niyya without bothering ko ya cancanceta ko bai yi ba, to wllh wllh if anything of such should happen again in my family infact ko wanda bai yi kusa da hakan ba idan ya faru a family dina wllh i will prefer to shoot that person" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah Ubangiji ya tsare, ya kare mana zuri'a Alhaji" Abba ya kalli Mumy da bata cewa komai tun faruwan abun, amma kana ganinta kasan she is heartbroken, her first child, habaa ko bacci bata iya yi tunda wannan lamari ya faru, da tasan Nihad xata girma ta yi irin wnn rashin jin da Allah bai raya mata ita ba, tun faruwan hakan ita ma ta kashe wayarta sbda kiran yan uwa da abokan arziki da suka san Nihad, Abba yayi gyaran murya yace "Ban ga laifinki ba Maryam don ni nasan kinyi iya bakin kokarin ki na ganin kin ba ma Nihad tarbiya yanda ya kamata, u tried ur best, matsalar kawai u didn't make Nihad ur frnd aside mothering her, amma dai babu komai, kawai dai kafin Nihad ta dauko mana abinda xuciyarmu xai kasa dauka nan gaba tun wuri ni da yayana da yan uwana mun mikata, kusan xance na bada sadakarta" Abba na fadin haka ya ciro sadakinta dake aljihunsa ya mika ma Umma yace "Sai ki damka mata ku da xa ku kai ta" Umma ta amsa cikin sanyin murya tace "Yanxu Yallabai mun yi deserving a bada er mu ba tare da mun san wanda aka ba ma ba? Ai hankalinmu baxai taba kwanciya ba, tun jiya nake bin ka kaki gaya min, ai yana da kyau a sanar mana mu sani don muna da hakkin sani, idan ma ni bani da hakkin in sani mahaifiyarta fa?" Abba ya Ι—an yi shiru, sai kuma ya dau wayarsa yayi dialing number snn ya kai kunne, ana dagawa yace "Ka shigo nan parlor ka sameni yanzu" daga haka ya katse wayar, duk kowa yayi shiru ya xuba ido ya ga wanda xai shigo parlon barin Farooq da Umma. Da sallama ya bude kofar parlon, ganin su Umma ya dakata daga bakin kofar bai shigo ba, Abba na kallonsa yace "Karaso" ya karasa shiga cikin parlon kansa a kasa, duk occupant din parlon kallonsa suke with full shock, Abba ya nunasa yace "Shi na ba auren Nihad, shine mijinta" Mikewa Farooq yayi yana kallon Abba baki bude, Mumy ta hadiyi wani kullutu da taji ya tokareta a makogwaro, Umma kuwa sae kallonsa take daga sama har kasa babu ko kiftawa, ta ma rasa yanayin da take ciki ita, Kowa na parlon ya kasa cewa komai, tsabar silence din parlon da allura xai fadi xa a ji karar faduwarsa, shi kam dai yana ta tsaye ya sunkui da kai har sannan, Abba yayi breaking silent din yace "Je ka" Juyawa yayi ya fita daga parlon, Usman ya kalli Abba yace "Haba Dad? Yanxu shi ka aura ma Nihad?" Farooq yace "No Abba, u should have given her a choice, bata yi deserving ayi mata dole ba sbda wannan kaddarar tata, but Abba...." Kasa cewa komai yayi ya koma ya xauna, shi ma ya rasa yanayin da yake ciki, but he don't think it's still bad after all, just dat.... Girgiza kai kawai yayi, Umma tace "Haba Alhaji...." Abba ya mike yana bin kowa da kallo yace "No one have the right to query my authority" Yana fadin haka ya bar masu parlon ya shiga bedroom dinsa, suka dinga kallon kallo a tsakaninsu a parlon, Usman ne ya fara mikewa ya fice daga parlon, Mumy ta mike ta bi bayansa ita ma tana share idonta, Umma ta sauke ajiyar xuciya tana kallon Farooq, ita gaba daya ma kanta fa ya kulle, Abba really took them unaware, jinginar da kanta tayi da kujera Farooq ya mike ya fice daga parlon shi ma. Ana idar da magrib yan kai amarya suka fara shirye shiryen kai ta, Nihad bata ta6a shiga irin tashin hankalin da take ciki ba a wannan moment din, ko video dinta bai tada hankalinta kamar yanxu ba, gashi nobody is there to console her, Nihal na schl, Husnah kuma taki xuwa gidan sbda Farooq, gashi bata da numberta a kai balle ta amshi wayar wani ta kirata, su kamila da Amina tamkar ma farin ciki da abinda ya sameta suke don uban kwalliya suka ci har da kashe dauri Hajiya Zuwaira ce ta kai ta gun Mumy tayi mata fada ta sa mata albarka, sbda takaici da bakin ciki Mumy ta ki cewa komai daga karshe da aka tilastata sae cewa tayi Allah ya tsare, Alhaji Abubakar ne kawai yayi mata fada, Abba kuwa tun da aka idar da magrib ya ki shigowa gidan dama, a haka dai aka tattara ta da akwatunan kayanta uku wanda Umma da Kamila suka hada mata wasu kayayyakinta a ciki, kuka take kamar xata shide, har addu'a ta dinga yi Allah ya dau ranta kafin a karasa da ita gidan, tana ganin an shiga gidan ta kara sautin kukan da take a haka har aka shigar da ita daki, gida ne bungalow madaidaici me dakuna uku, ko wani daki da bandaki, sae bandakin dake parlor sai kitchen, anyi furnishing gidan babu laifi sai dai furnitures din ba masu tsada bane, Nihad ta dinga kuka tana cewa ta shiga uku, masu bata bakin ma har sun gaji sun daina, karfe tara saura suka fara shirin tafiya, Nihad ta rike hannun Kamila cikin kuka tace "Aunty ynxu tafiya xa ku yi ku bar ni, don Allah kar kuyi min haka..." Kamila tayi dariya tace "Ae ko dole xa mu yi maki haka tunda mun kawo ki gidan mijinki kinga ni ynxu sae na koma xan dau jakata inyi driving xuwa gida, kawai kiyi hakuri ki bi mijinki ku xauna lafiya ko hakan xai goge wannan ta6on da kika ma kanki" Daga haka ta fice daga dakin don dama ita ce karshen fita, Nihad ta silalo kasa ta xauna tana kukan takaici, tana jin duk suka fice daga gidan ta daina jin hayaniyar kowa, nan kuma tunanin ta ya tafi gun wanda xata gani a matsayin mijinta, tsoho ne, yaro ne, baki ne, fari ne, kato ne, siriri ne, mummuna ne, kyakkyawa ne, infact duk wannan tunanin ne suka baibaye ranta gabanta ya dinga faduwa hankalinta ya kara tashi, daga karshe ma daina kukan tayi banda bugawa babu abinda xuciyarta yake, ta fi minti ashirin a haka taji an bude gate, da sauri ta mike ta tafi gun window ta bude labule amma sai taga ba ta nan gate din ma yake ba balle taga me shigowa, komawa tayi ta xauna can karshen gado tana jin yanda kirjinta ke heaving, to waye wannan da ko mota ba shi da, bayan wasu mintuna taji an shigo parlor, daga karshe ta ji kamar an bude wani daki an shiga, mikewa tayi ta jingina da window with so much fear, har ta gaji da tsayuwa bata ga alamar xa a shigo dakin ba, komawa tayi ta xauna gefen gado, a kan idonta karfe sha daya tayi, bacci take ji amma taki kwanciya sbda fargaba, kafin sha biyu bacci barawo ya saceta. Ba ita ta bude ido ba sae da hasken rana ya sauka saman fuskarta washegari da safe, a firgice ta mike xaune, sae kuma ta sauka daga saman gadon ta shige bandaki da sauri, bayan ta idar da sallah ta mike a hankali ta nufi kofar dakin ta bude ta fita xuwa parlor, ta dinga bin ko ina da kallo xuciyarta na bugawa, kofar da take tunanin kitchen ne ta nufa ta bude kofar a hankali, wani kara ta saki ba tare da ta shirya ba ganin mutum a tsaye yayi backing kofar kitchen din ga ruwa ya daura saman gas, juyowa yayi suka yi ido hudu da ita, wani irin shock ne ya bayyana a fuskarta ta dinga komawa baya tana kallonsa bakinta ya kasa furta komai, can ta nunasa da yatsa nan ma words suka yi failing dinta, juyawa yayi ya kashe gas din don ruwan ya fara tafasa ya juye cikin mug sannan ya bi gefenta ya fice daga kitchen din ba tare da ya sake kallonta ba, makalkalewa tayi jikin kofa jikinta na 6ari tana ganin abun kamar a mafarki, sae a sannan bakinta ya bude ta fasa wani raxanannen ihu, sai kuma ta fara ganin kitchen din na juya mata lkci daya ta sulale kasa....

 


_8 months earlier_


Contact me directly viaπŸ‘‡πŸ» to gain access to the book

07087865788 ✍🏻

3
πŸ’–πŸ’– NIHAADπŸ’–πŸ’–

 


By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 

~~~


Gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga sauran membobi yan gurmin Khaleesats Palace, don gurminsu ya hana in saka sunansu jiya inga ta tsiya, Su Hajiya Aisha Bela, Hajiya Suwaiba, Hajiya Safiyya UsmanπŸ˜‚ Hajiya Mardiyya mandy rice😜, Hajiya Sadiya uwar Hanan, Uwar Sa'eed, Hajiya Farida me kayan en gayu, Amzaj, Hajiya Zaarah, Wata ana ce mata me kayi nayi, Hajiya Aisha Macika, Hajiya Billy, Uwar Habee, har dai da wata me gawayin dare, duk na gaisheku kyauta... Sauran da basu ga sunansu ba a tsakiyar rubutu xa su gani😁

 

8months earlier...

 

Zaune yake saman farar kujera dake kusa da dakin mai gadi, ya fi awa daya xaune wajen, lkci lkci yake goge zufan fuskarsa da handkerchief din hannunsa, karamar waya ya fiddo aljihunsa yana duba agogo dake nuni da karfe biyar da rabi, ya juya ya kalli mai gadi dake xaune gefensa da radionsa a hannu, xai yi magana aka danna horn, da sauri mai gadin ya ajiye radion ya mike ya isa bakin gate din gidan ya bude, wata rantsantsiyar mota ce ta shigo compound din, mutumin dake xaune ya bi motar da ido har ta isa kantamemen space da aka tanadar don parking a compound din, mai gadin ya dawo bayan ya maida gate din ya rufe yace "Bari in sanar masa kana ta jira kar ya shige ciki kuma" Daga haka ya nufi parking lot din ya jira har dattijon dake cikin motar ya sauko yana gyara babban rigar jikinsa, da ladabi me gadin ya risina yace "Barka da isowa Alhaji" Alhaji Ibrahim yace "Yauwa Aminu... " Mai gadin yace "Alhaji dama Habibu ya taho da baΖ™on tun daxu, shi har ya ma tafi yace yau xai koma, baΖ™on kuma gashi can yana jiranka tun karfe biyu" Alhaji Ibrahim ya kulle motar tasa yace "Ohk, to ya karaso" Mai gadi ya koma gun mutumin dake xaune saman farar kujera da sauri yace "Kaje nayi masa magana" Tashi mutumin yayi ya nufi parking space din, yana isa ya duka har kasa yana kallon Alhaji Ibrahim yace "Barka da yamma Alhaji" Alhaji Ibrahim na kallonsa yace "Yauwa kai ne wanda Habibun ya kawo kenan?" Mutumin yace "Eh ni ne" Alhaji yace "Ya sunanka?" Mutumin ya sauke idonsa daga kallonsa yace "Sunana Ibrahim" Alhaji Ibrahim ya jinjina kai yace "To madallah, amma ya ku ke da Habibun?" Mutumin yace "Garinmu daya da shi, ga gidanmu ga gidansu, babana aminin mahaifinsa ne" Alhaji Ibrahim yace "To ba laifi, ai har garin naku naje watanni da suka wuce" Shi dai mutumin bai ce komai ba, Alhaji Ibrahim yace "Shkkn babu damuwa, amma kayi karatu ne?" Mutumin ya girgiza kai yace "Aa iyakata sakandari, shi ma ban zana waec ba" Alhaji Ibrahim ya daga kafada yace "Ohk, xuwa kake ganin xaka dinga yi kullum ko kuma yaya tsarin naka yake?" yayi kasa da kai yace "Duk yanda ka tsara haka xa ayi Alhaji" Alhaji Ibrahim yace "Kaje dai gobe da safe ka dawo, ni yanxu xan shiga ciki in huta ne, dawowata daga aiki kenan..." yace "Toh nagode kwarai Alhaji, Allah ya kara girma" Tuni Alhaji Ibrahim ya nufi main entrance din shiga gidan nasa, ya mike ya bi sa da kallo, sannan ya kalli building din gidan wanda duplex ce gari guda, juyawa yayi ya koma gun mai gadi, mai gadin na ganinsa yace "Ya ake ciki?" yace "Yace in dawo da safe" Mai gadi yace "Ahaf ai ka ma samu, tunda ta hannun Habibu ka biyo, ai Alhaji sun fi shekara goma sha biyar da Habibu, har kauyensu ya je daurin aurensa kwanaki, in dai baka da rawan kai sannan uwa uba ace kana da nutsuwa gun aikinka to wllh tuni Alhaji xai ja ka jiki ka xama kamar d'an gida, ba ga mu ba duk mun dawo kamar yan gidan banda dai ba halinsu daya da wasu daga ahalin gidan nasa ba, to ya sunan naka?" Mutumin yace "Sunana Ibrahim" Mai gadi ya rufe baki yace "Yo ai sunan Alhajin kenan" yace "Allah sarki, Sai goben in sha Allah, xan tafi ynxu" Mai gadi yace "Allah ya kai mu" Gate ya nufa ya fita daga gidan. Alhaji Ibrahim ne xaune parlonsa, daga gefensa matarsa kuma amaryarsa Hajiya Maryam, Wasu yan mata ne biyu xaune daga kasa saman lallausan carpet dake malale parlon, Hajiya Maryam tace "Ayi hakuri Alhaji in sha Allah hakan ma baxai sake faruwa ba, ita ma Hajiya nasan bata fahimce su bane, amma xa su je su bata hakuri" Alhaji Ibrahim na kallon yan matan yace "Ku tashi ku bani waje" Duk a tare suka ce kayi hakuri Abba, yace "Ku fita nace..." Mikewa suka yi a tare suka fita daga parlon, daya daga cikin yan matan tace "Gaskiya ni ki daina ja min Nihad, ko me kika yi sai a hada mu a mana fada, da na sani da ban biki ba jiya, haba don Allah" Tsaki er uwar tayi mata ta bi wani corridor tayi gaba abunta irin ko damunta abun bai yi ba. Wata mata ce da baxata haura hamsin da bakwai ba xaune wani lafiyayyen parlor da ba a cika da kaya masu hayaniya ba, cike da Ι“acin rai tace "Toh banda ma fitina da neman magana irin naku dole ne sai kun je? Me yasa baxa ku xauna inda Allah ya ijiye ku ba, maganinku kenan" Nihad tace "Ae wllh daga yau ko Abban ne yace mu je ni dai sai dai in fita inyi using opportunity din in xaga gari in sha iska in dawo abu na, i don't care... baxan sake xuwa ba gaskiya" tana kai wa nan ta mike ta dau wayarta dake caji ta fita daga parlon, Hajiya Sumayyah tace "Atoh dai, da ya fi maku, don dama magana ta ce kawai bakwa ji banda haka na hanaku xuwa tun ba yau ba" Ita dai er uwar Nihad na kwance saman kujera bata ce komai ba, Hajiya Sumayyah ta bude kofar bedroom dinta ta shiga ta kulle. Washegari asabar kasancewar yan matan gidan basu da lectures duk suka yi shirin tafiya islamiyya amma banda Nihad dake kwance parlon step mum dinta tana aikin danna waya, Hajiya Sumayyah da suke kira da Umma da  tace "Ke Nihad kina kallon lkci kuwa, ko baxa ki islamiyyan bane yau ma?" Nihad tace "Umma sai gobe i have something important to do" Umma tace "To ita Nihal ma cewa tayi ba xata ba?" Bata rufe baki ba sai ga Nihal ta shigo har ta gama shiryawa, Umma ta kalli Nihad bata dae ce komai ba ta ci gaba da abinda take, Nihal tace "Hope u are been cautious of time Nihad?" Tashi Nihad tayi ta fita daga parlon tana cewa "Ni sai gobe" Mai gadi ne tsaye tare da mutumin da ya xo jiya, bayan sun gaisa mai gadin yace "Yanxu xaka ga Alhajin ya fito xai tafi gun motsa jiki, don ma yau bai fito da wuri ba, amma dai bari in sanar masu a ciki kar kuma ka yi ta jira haka babu dadi" mutumin yace "To nagode" Xaunawa yayi kan farar kujera yana bin compound din da kallo don ya kayatu da kyawawan shukoki na flowers har ma da artificial flowers, daga can wani gefe wani karamin water fall ne me ban sha'awa ruwa na ta xuba ga artificial crocodiles da kifaye a ciki, ba a dau lkci ba mai gadin ya dawo yace "Ka ga wancan yar barandar?" ya kalli inda yake nuna masa yace "Eh na gani" Mai gadin yace "Toh kaje can kayi jiran alhajin, akwai kujeru ma a wajen" Tashi yayi ya tafi wajen yana bin ko ina da kallo, bayan kujeru masu kyau har da carpet grass malale a kasa daga gefe, ga artificial flowers da ya kawata wajen, ya xauna saman daya daga kujerun wajen surveying everywhere with his eyes, bayan kusan minti sha biyar aka bude kofar parlon, tsaye tayi tana kallonsa daga sama har kasa a bit flabbergasted, ya kalleta yayi kasa da kai yace "Ina kwana" tace "Wa kake nema Malam? Daga ina haka?" Yace "Mai gidan nake jira" ta fi minti daya tana masa kallon sama har kasa, ta ma rasa me xata ce, sai kuma ta sauka kasa xuwa compound din ta tafi gun mai gadi da sauri, yana gaisheta ta ki amsawa tace "Aminu waye wancan aka bar sa xaune a kofar shiga parlor? Waye wannan?" Yace "Ranki shi dade baΖ™on Alhaji ne wanda Habibu ya kawo jiya, shine sabon...." Ta gwalo ido ta dakatar da shi da sauri tace "Haba Aminu, Haba Aminu, yanxu kai rashin hankalin naka ya kai haka, a tunaninka ya kamata a bar sa yaje har can ya jira Abbanmu, privacy din mu ne can din fa? ga dai kujeru a compound amma har sai yaje balcony kamar xai shiga parlor, a ina aka ta6a haka?" Aminu yayi kasa da murya yace "Wannan gaskiya ne Hajiya, ayi hakuri anyi kuskure kam, ayi hakuri" Tace "To tun wuri ka tafi kace ya dawo nan kusa da kai ya xauna ya jira Abban" Aminu yace "Toh Hajiya" tabe baki tace "Ni dama tambayarka xanyi hope jiya baku mance feeding din tsuntsaye na ba?" Ya washe baki yace "Haba dai Hajiya, ai kullum safe rana da dare sai Saminu ya basu, yau ma da asuba ina kallo yaje ya xuba masu" tace "Yauwa toh nagode, bari in je in duba su, shekaranjiya da jiya duk bama nan ban gansu ba" Yace "Da yake sai dare ku ka dawo jiya din ma" Tace "Eh fa" daga haka ta wuce ta xaga ta inda tsuntsayen suke a backyard din gidan wanda nan dinma duk shuke shuke ne, ta fi minti bakwai tana kallon kyawawan tsadaddun birds din nata ko wani breeds a cage dinsu daban, birds din iri hudu ne ko wanne me kyau har kuma da Aku a ciki, ta tafi gun akun da aka yi Seperating da sauran tace "Hello cutie" The bird was only chirping and flying around the little cage alamar he appreciates seeing her, bayan wani lkci ta bar wajen xata koma cikin gida, tsaye taga Abba a balcony bakon nasa kuma ya sauka daga saman kujera ya durkusa kasa yana sauraren Abba, kallonta kawai Abba yake da mamaki yace "Nihad ke baxa ki islamiyyan bane?" Tayi gathering courage tayi kasa da murya tace "Abba assignment nake typing anjima xan yi submitting via...." Abba ya dakatar da ita yace "Why are u skipping Islamiyya this days Nihad, last week ma na ga baki je ba ko, hakan ba dai dai bane dear" Sunkuyar da kanta tayi bayan few seconds ta dago, kallon mutumin dake kallonsu ita da Abba tayi, ta wani daure fuska wondering why he was looking at them, tana tafiya a hankali ta shiga parlor ta kullo kofar, bayan minti shidda aka sake bude kofar, har sannan Abba na tsaye speaking with the man, su uku ne duk sanye da hijab din islamiyya har kasa, Abba ya kallesu, sai kuma yace "Ke xaki yi driving din?" Tace "Eh Abba ga makullin" Amsa yayi ya mika ma mutumin dake durkushe gabansa yace "Ka ajiyesu a makaranta, xan jira ka har ka dawo" Ya amsa da ladabi yace "Toh Alhaji" shi ya fara sauka Balcony din, Autan Mumyn Nihad da ake kira da Sudais yace "Abba is he our new driver" Abba yace "Yes he is sweetheart" Duk suka yi ma Abbansu sallama suka sauka xuwa parking lot, sai da suka tsaya dai dai motar xuwa makarantarsu sannan drivern ya nufi motar shi ma, bayan ya bude duk suka shiga back seat, ya shiga ya tada motar yana warming, shi dai Abba na tsaye balcony har sannan yana kallonsu, Drivern na warming motar yaji ance "Ina kwana" ya daga kai yana kallonta ta madubi da mamaki, sai kuma yace "Ina kwana" Bayan wasu yan mintuna ya ja motar suka bar gidan xuwa islamiyyan nasu with Fadil and Sudais directing him. Parking yayi bakin gate din islamiyyan, Nihal ta bude motar ta sauka su Fadil ma duk suka sauka, bayan ta kulle motar ta kallesa tace "Sai anjima" Yace "Sai anjima Hajiya" Suka shiga makarantar, reverse yayi ya bar wajen har sannan bai daina mamaki ba. Yana isa gidan bayan mai gadi ya bude masa gate ya shiga yayi parking ya kashe motar ya sauka, gun mai gadin ya nufa ya xauna, Mai gadin yace "Inji ka yi kumallo dai?" Driver  yace "Aa" Mai gadin yace "Toh bari inyi ma mai aikin gidan magana in amso maka" Daga haka ya nufi backyard din gidan xuwa kofar kitchen dake baya, Drivern dai na xaune yana ta juya makullin motar hannunsa sai ga mai gadin ya dawo da plate din dankali da kwai da kofin shayi, ya amsa yace "Nagode sosai" slice din bread ne biyar a gefen irish din da kwai wanda aka matsa ketchup a gefe shi ma, irish din ya fara ci yana dangwalawa da ketchup din, Mai gadi yace "Amma xaka dinga tafiya ne da daddare ka dawo da safe ko gidan nan xaka tsaya?" ya kallesa yace "A ina xan tsaya a nan din?" Mai gadi yace "Ka ji ka, Yo ai har Habibu ya gama yayinsa a gidan nan kafin Alhaji ya bude masa shagon da ya bude masa na tayoyi a gidan nan yake komai nasa, duk tare muke, ga can boyis kwata, su Saminu da Shafi'u masu gyaran pulawa da sharan tsakar gida da Isiya me wanki da guga ai a nan suke duk" ya dau cup din shayin ya kurba yace "Dakin babba ne?" Mai gadin yayi dariya yace "Wai daki, to har parlor akwai a ginin, sannan dakuna uku ne ko wanne da bandaki, kai har ma da kitchen a nan din" yace "To shikenan" Aminu mai gadi yace "Kai ma kayi xamanka kawai a nan xa ka fi gane kan albashin naka, kaga babu xancen kashe kudin abun hawa xuwa da tafiya sannan xa a ciyar da kai a nan ba sae ka siya komai da neran ka ba, duk abinda yan gida suka ci a nan shi mu ma muke ci" Shi dai bai ce komai ba ya gama cinye irish din tass sannan yace "Toh xan xauna nan din in sha Allah, nagode da kulawa" Ganin ya ajiye plate din Aminu yace "Ya haka, naga baka ci kwan ba? Yanxun nan fa ta soya maka" Ya girgiza kai yace "Bana so" Aminu ya dau plate din yana kokarin cin kwan yace "Allah sarki, wasu haka suke basa cin kwai sai suce yana masu karni, mu dai kam ko danyensa ne baxa mu ki ci sha ba, wa yaΖ™i dadi" Sai da Aminu ya cinye kwan ya mike yace "Mu je ka ga Boyis kwatan" shi ma ya tashi, yana biye da shi, suka tafi far end of the main building in which stood a Beautiful Chalet, mai gadi ne ya fara shiga, shi ma ya cire takalminsa bakin kofar shiga Chalet din kamar yanda mai gadin yayi sannan ya shiga ciki, ba laifi parlon na da girma, sannan ga kujeru har ma da tv, kaya ne ko ta ina a parlon ga wani tashi da parlon yake, everywhere looks very untidy, isiya ne tsaye parlon yana ta faman guga a ironing board, Aminu yace "Ashe kana ta guga shi yasa baka fito ba, ina Saminu?" Isiya dake ta kallon wanda Mai gadin ya shigo da yace "Suna can daki" Aminu yace "To ga bako, kun samu karuwa a nan, shine ya maye madadin Habibu a gidan nan yanxu" Mutumin ya gaida isiya, isiya ya amsa yana ci gaba da gugansa, Aminu na kallonsa yace "Mu je ka xabi dakin da xaka xauna ko" Isiya yace "Ka dai san dakin dake daga dama ni ne a ciki, na hagu kuma Saminu, wanda ke jikin na hagun Shafi'u ne a ciki" Shi dai kallonsa kawai mutumin yake, Aminu dake kallon Isiya shi ma yace "To ya xa ayi kenan" Saminu da Shafi'u ne suka fito daga dakunan su, Isiya yace "Toh ai parlon ma na da girma sai kawai ya maida nan din wajen kwanansa ko" mutumin ya gyada kai yace "Ohk to shikenan" Isiya yace "Yauwa" Aminu ya kalli su Saminu yace "Sabon direban gidan ne shi ma kuma nan xai xauna, sunansa Ibrahim kun ga sunan Alhaji ne...." Saminu yace "To sannun sa da xuwa" Tuni ya juya ya fita daga parlon ya bar mai gadi, Aminu na ganin haka ya bi bayansa da sauri... Suna tafe mai gadi yace "Amma kasan da nauyi mu dinga kiran sunan Alhaji gatsau, baka da wani sunan ko inkiya da xa mu iya dinga kiranka da?" kallonsa yayi yace "Khalil Mahaifiyata ke kirana" Aminu yace "Allah sarki, to ai mu ma sai mu ce khalil din, suna me dadi kamar na larabawa wllh" Bayan sun koma mazaunin mai gadi sun zauna, Mai gadin ya kallesa yace "Yanxu kawai kayayyakin ka xaka je gida ka debo, aikin naka ma fa ba wani me wahala bane, kaga yan makaranta motar makaranta ce ke xuwa daukansu da safe, Yan matan nan biyu kuma daya a zaria ma take karatu, dayar ce ke karatu a nan, ita warce ke karatu a nan din sai ta kai karfe biyu ma bata tafi makarantar ba, Alhaji kadai xaka ajiye karfe tara gun aikinsa, ban ki ba dae Nihad don gantali gareta kamar ta ci kafar kare, kuma sae ta fake da makaranta, a takaice dai kai Alhaji wajen aikinsa da safe shine ainahin aikinka sauran duk masu sauki ne" Khalil da har ya gaji da surutun Aminu ya gyada masa kai kawai, for the next 30mins Aminu bai yi shiru ba, Khalil har ya daina tanka masa don ya ma yi nisa a tunanin da yake, dai dai nan Alhaji ya fito, Mai gadi yayi kasa da murya yace "Da alama yau baxai je motsa jikin ba kenan tunda har gashi sha daya ta yi" Sai kuma ya mike, Khalil ma ya mike yana kallon Alhajin a bit surprised at who is standing next to him, Khalil yayi kasa da murya yace "Yan makarantar har sun taso ne?" Mai gadi ya kalli Khalil da sauri yace "Ka je yana maka magana ne" Khalill ya nufi Alhajin da hanzari, Alhaji yace "Mu je xaka ajiye mu 3 streets away from this" Khalil yace "Toh" Motar da yayi parking bayan ya ajiye yan makaranta ya nufa, Abba yace "Wancan motar ba wannan ba" Khalil ya tafi gun motar da Abba ya nuna masa, Bayan sun fita gidan Mai gadi ya kulle gate, driving Khalil yake a hankali, lkci lkci yake kallon Nihad dake zaune bayan mota da Abbanta tana danna wayarta. Ganin Khalil a layin da Alhajin yace ya ajiye su, Alhaji Ibrahim yayi mamaki sosai, don shi ya ma mance ba Habibu bane ke jan sa, bai yi masa kwatancen inda xai kai su ba ya dai ce masa 3 streets.... Ganin yayi slow down Alhaji Ibrahim yace "Noo ci gaba da tafiya, gida na uku xaka tsaya" Dai dai gidan Khalil yayi parking, Alhaji yace "Kayi horn kawai" yana yin horn mai gadi ya leko ganin motar ya koma ya bude gate din da sauri, Khalil ya shiga ciki ya samu waje yayi parking , Alhaji Ibrahim yace "Maa sha Allah, kayi jirana har in fito" Khalil yace "To Alhaji" Nihad ta sauka ta daya side din wayarta kare a kunnenta, Alhaji Ibrahim ya sauka ya nufi entrance din gidan, Ta side mirror Khalil ke kallonta amma sai yaga kamar wannan fara ce ai, Nihad dake ta xagaye da waya a kunnenta da sunan she is making call, whereas she is not kawai bata son Abba yace su shiga ciki tare ne, tana ganin Abban nata ya shiga gidan ta turo baki ta tafi can karkashin wani Thatch dake compound din wanda aim dinsa wajen shan iska, xaunawa tayi a wajen. Khalil ya sauka daga cikin motar ya tafi gun mai gadin gidan suka gaisa, Mai gadin na kallonsa yace "Ko kai ne madadin Habibu" Khalil yace "Eh nine" Mai gadin yace "Maa sha Allah" Xaunawa khalil yayi yana bin compound din da kallo, wanda shi ma yayi haduwan karshe, ya d'an juya ya kalli Side din da Nihad take, she was so engrossed with what she is doing on her phone....


U can contact me directly viaπŸ‘‡πŸ»


07087865788✍🏻

4
πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–

 


By _Khaleesat Haiydar_✍🏻

 


~~~~

Gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga manya manyan fans dina irinsu.. Fatima Arebia, Aisha Abubakar, Maman Shukrah (Banatsapparel and more) Khadijah Dutse, mu'azatuπŸ˜‚, infact da duk wani member na Khaleesats palace da ban ambato ba a nan ku sani ina son ku har raina, ina yin ku, ina maku fatan alkhairi Allah ya dafa maku a duk lamuranku, My respect to many of my fans da suka fara patronizing Nihad without even waiting for the end of free pages, yawancin ku ba biyan littafin ku ka yi ba kyauta ce kawai kuke min, kuma ina alfahari da ku, ina maku fatan alkhairi da Zuri'a dayyiba. Allah ya bar xuminci, ya saka da Alkhairi ya karo maku yalwataccen arxiki, na kuma sadaukar da page din nan gare ku. 

 

Bayan minti talatin da biyar Nihad ta gaji da jiran Abbanta don har sannan bai fito daga gidan ba, ga kiran da Husnah ke ta yi mata taki dagawa don bata son tace mata bata gida tasan baxata jira ta ba, kallon agogon dake makale hannunta tayi ganin sha biyu har da minti goma ta tashi daga kan kujerar da take ta nufi khalil, Babu yabo babu fallasa tace "Hey xan koma gida kayi dropping dina yanxu" Sai da ya fara kallon mai gadi dake gefensa kamar dai da mai gadin take, ta daure fuska tace "Malam da kai fa nake?" Sai a sannan ya kalleta ya d'an kara kunnensa gaba yace "Na'am" Rasa ma me zata ce masa tayi saboda bakin ciki, har sannan fuskarta a daure tace "Ina ga dai kana da matsalar ji, dalla malam ka tashi ka maida ni gida" Yace "Naga ai Alhajin bai fito ba" Tana masa wani kallo tace "Eh na fi ka sanin bai fito ba" Yace "To kar ya fito ya tarar bana nan" Ta rike kugu cike da masifa tace "Sai ka maida ni, idan ka maida ni xaka iya dawowa idan ka ga dama" Ya dauke kai yayi shiru bai ce komai ba, shi dai mai gadi sai mazurai yake da ido babu damar ya kwaba ma khalil, shi tsoronsa ma kada wnn Ι—an abin ya sa ya rasa aikinsa, yana ga kamar Khalil bai ta6a aiki gidan masu hannu da shuni bane shi yasa har ya tsaya suna ja in ja da Hajiya karama banda haka ina shi ina biyeta, ai duk abinda tace haka xa ayi, tsawar Nihad ne ya dawo da mai gadin reality don sai da ya tsorata, "Dalla Malam kana bata min lkci, are you even okay, how dare u query my order? Ko dai kana shaye shaye ne???" Khalil ya Ι—an kalleta, sae kuma ya mike ya nufi motar, ta ja wani dogon tsaki ta bi bayansa kamar xata tashi sama tana harararsa, duk sai taji ranta yayi mugun baci, bayan mota ta bude ta shiga, tuni mai gadi har ya wangale gate yana daga mata hannu alamar Allah ya tsare, Khalil yayi reverse ya fita daga compound din, cikin mintuna kadan ya isa gida da ita, yana parking dai dai gate ta ja tsaki ta bude motar ta fice without closing the door, da ido ya bi ta har ta shiga gate din gidan, ya fi minti biyar tsaye da motar, daga bisanni ya sauka ya kulle door din motar, sannan ya shiga yyi reverse ya bar layin ya koma can gidan da Abba yake. Nihad na shiga gida bangaren Umma ta nufa, jefar da jakarta tayi saman kujeran parlon tana kallon Umma tace "Umma wani irin driver ne wannan Abba yayi employing, who even linked them? wllh yaron bai da kunya ko kadan Umma, kinga abinda yayi min kuwa??" Umma ta ajiye kayan hannunta tana kallonta tace "Me yayi maki?" Nihad tace "Wllh rashin kunya yayi min, ni babu wani wanda ya ta6a min haka ma tun da nake, wai yaron ya maida ni gida yaki fa" Umma tace "Aa abu me sauki sae ayi ma Abban naku magana ya sallamesa, halan d'an kauye ne?" Nihad tace "Toh ae dama su ne masu wannan tsagerancin da rashin ta idon, wllh Umma wannan idan yayi wata daya a gidan nan daina kai mu duk inda xa mu xae yi, Allah cewa xai dinga yi baxae je ba kansa tsaye idan ma bai hada mana da zagi ba, gwara kawai Abba ya dawo ya sallamesa a samo wani dama ni bai min ba from the start, irinsu ne idan an shigo da su inuwa su maida mutum rana, wai kinga me yayi min ne, jayayya fa muka tsaya muna yi da shi" Daga haka ta fice daga parlon ta tafi dakinta don ta shirya xuwa inda xa su hadu da Husnah, sae dae tana tsaka da shiryawa ta dinga kiran wayar Husnah ta ji a kashe, lkci daya ranta ya baci, kaddai har tayi tafiyarta, ta zauna gefen gado tana ta trying din layin amma ya ki connecting. Ana kiran sllhn Azahar Abba ya fito daga gidan tare da wata tsohuwa, Khalil ya mike tsaye ganinsu, suna karasowa inda yake Abba yace "Sabon drivern da na dauka kenan Hajiya, yau ya fara aiki..." Tsohuwar ta kallesa daga sama har kasa tace "To ba laifi, kuma da ganinsa xae fi Habibu kwazo duba da halittarsa, kawai dae sai mu yi fatan Allah ya sa ya fi Habibu nutsuwa, don Habibu ni kadai nasan Ι—an iska" Khalil yayi kasa da kai tare da risinawa yace "Ina yini Hajiya" da fara'a tace "Lafiya lau, amma kai buzu ne koh?" Ya murmusa yana girgiza kai, Tsohuwar tace "Toh a dai kula da dukiyar mutane ka ji, kai ma sai kaga Allah ya kula da kai, baka ga motar da Habibu ya ajiye kafin ya tafi ba, duk ta fita hayyacinta daga karshe konden konden aka siyar ma, su ma din dai a walakance suka siya, ya sunanka?" Yace "Ibrahim" Buda baki tayi tace "Ikon Allah, Kai ae kawai ka zama d'an gida abun ka daga yau ka ji, babu me raina ka ko waye shi, kanka tsaye kar ka yarda da hakan, ae sunan Uban gidan naka kenan, kuma ni na haifesa, Allah yayi maku albarka gaba daya" yana murmushi yace "Ameen" Abba yace "Toh ki koma haka Hajiya, ni xan tafi" Tace "To Allah ya tsare, idan Habubakar din ya dawo xan tattauna da shi" Yace "Ba laifi, sae anjima" daga haka ya nufi motar, Khalil na biye da shi a baya. Yana ajiye Abba a gida, Abba yace "Ka tafi islamiyya ka dauko yara nasan sun tashi ynxu" Khalil yace "Toh in sha Allah" hanyar makarantar ya nufa, yana parking bakin gate sae ga Nihal, sannan Fadil da Sudais, Amina ce karshen fitowa duk suka shige bayan motar, ita kuma ta xauna gaba, ta madubi yake kallon Nihal, tace "Barka da rana" xai amsa Sudais da Fadil suka gaishesa su ma, amsa masu yayi gaba daya sannan ya maida hankalinsa kan driving din da yake. Nihad na tsaye bakin parlon Abba tana jiran ya amsa sallamar da tayi, yana amsawa ta shiga, ta karasa parlon ta xauna saman kujera tace "Abba ina yini" yace "Nihad me yasa kika ki shiga ku gaisa da inna da mutanen gidan?" Ta langwabar da kai bata ce komai ba, glasses dinsa ya saka yana maida dubansa kan laptop din gabansa, tace "Abba i came to report this new driver to you" Sake kallonta yayi yace "What about him?" Tace "Abba kawai don nace ya maida ni gida i am press shine mutumin nan ya ki, infact yi yayi kamar bai ji abinda nake cewa ba ya bar ni a tsaye" Abba yace "Is that so?" Tace "Wllh Abba, and it's not as if i was rude to him, kawai cewa nayi don Allah ka maida ni gida ina son xan koma, kawai sai yayi min banxa, wllh Sagir mai gadi ne shaidata" Abba dai yayi shiru yana kallonta, bude kofar parlon Abba aka yi sai ga su Sudais da Fadil sun shigo gaida Abban nasu ganin motarsa a gida, Nihal ce ta shigo bayansu, Abba yace "Welcome Nihal, tell the driver to wait me at the balcony...." Juyawa tayi ta fita, ba a wani dau lkci ba sai ga ta ta dawo tace "Abba na gaya masa" Abba ya ajiye laptop din kafarsa ya mike ya nufi kofa, Nihad taji wani dadi har cikin ranta dama babu abinda xata ce ma Abbanta tana so da baya yi, mikewa tayi da sauri ta bi bayansa Nihal ta bi ta da kallo, Abba na kallon Khalil bayan ya zauna saman daya daga kujerun dake wajen yace "Ibrahim me yasa tace ka maido ta gida ka ki?" Khalil ya durkusa kasa yace "Yallabai ban ki ba, ce mata nayi kar ka fito ka tarar bana nan kace inyi jiranka, amma daga karshe na daukota na dawo da ita gidan" Nihad dake jikin kofa ta hade rai jin abinda yace, Abba ya juya ya kalleta yace "Is that so?" Tace "To Abba sae fa da ya ja min rai, maimakon ina gaya masa kawai ya tashi ya kai ni gida" Abba ya kalli khalil yace "Je ka" Mikewa Khalil yayi yana kallonta yace "Kiyi hakuri, ban san haΖ™an xai bata maki rai ba" Wani shegen kallo tayi masa ta juya tayi wucewarta ciki. Bangaren Umma Nihad ta koma, Kamar xata fashe da kuka tace "Umma kin ga Abba bai dauki ko wani action ba dai ko?" Umma tace "Sai yace masa me?" Tace "Ba abinda yace masa, ni wllh sai dai duk abinda xai faru ya faru, da kaina xan dinga driving kaina, gashi gobe ina da lectures karfe