Allah ya tsine ma koma waye, Allah ya isa, shi ma sai an nemasa an rasa wataran yanda na rasa tsuntsaye nahhh" Juyawa Mumy tayi ta wuce cikin gida, Umma ta dagota tace "Ai ba Allah ya isa xa kiyi ba, koma uban wa yayi wannan aika aikan dole a ganosa a hukuntasa, ki bar komai a hannuna kawai" Nihad na shessheka tace "Umma wanda yayi mun haka ya tsaneni ne shi sa yayi haka kuma sai Allah ya tsine masa albarka ya daidaice, Allah ya isana" Nihal tace "Ki daina cewa haka baki san ko..." A fusace Nihad ta mike ta hankadeta har sai da ta kusa faduwa, tace "Shut up plss if have nothing good to say" Bude baki Umma tayi, sae kuma ta kalli Nihal tace "To wuce ciki" Nihal ta ta6e baki ta juya ta koma ciki, Umma ta juya ita ma ta bar wajen, Nihad ta hade rai ganin yanda ma'aikatan gidan ke kallonta, cikin tsawa tace "Uban meye kuke wani kallona munafukai yan iska, ai har da hadin bakin ku aka sakar min tsuntsaye suka bi duniya, to ku sani wllh daga yau sbda ku ni xan dinga shiga kitchen sai in ga d'an iskan da xai xubo maku abinci ya kawo maku, for one week ba ku da abinci wllh a gidan nan tunda har aka sakar min tsuntsu suka gudu" Tana fadin haka ta juya fuuuu ta wuce ciki. Da yammacin ranan Farooq ya shigo gidan daga Abuja, Nihad da abun duniya ya isheta don har sannan Aliyu isn't picking her calls, ga kuma har yanxu bata ga Driver ya bar gidan ba, kuma babu ma wata alamar da ta nuna xai bari, yana nan a xaune tare da mai gadi, ko makaranta bata je ba sbda damuwa gashi har test Husnah tace mata anyi, ta mike daga xaman da take ta yi a parlor ta fito compound jin motar Farooq, tamke fuska tayi ganin Khalil da Aminu sun nufi Farooq, Khalil ya fara basa hannu da ladabi, suka gaisa, farooq dai sai kallonsa yake, Aminu dake ta rawar kafa yana washe baki yace "Ae shine sabon dreban gidan tun bayan tafiyar Habibu, yau kwanansa biyar ina jin a gidan nan" Farooq ya kara kallon Khalil daga sama har kasa, sai kuma yace "Driver??" Sai kuma yayi saurin cewa "Ohk maa sha Allah, ya sunanka?" Khalil yace "Ibrahim" Farooq ya gyada kai yace "Maa sha Allah...." Tuni Mai gadi ya dau jakar Farooq ya nufi cikin gida da shi, Nihad dake tsaye balcony ta hade rai tace "Toh ajiye kayi tafiyarka ko ka aikesa ne??" Aminu ya ajiye jakar ya juya sui sui ya bar wajen, Farooq ya amsa gaisuwan da Nihal ke yi masa ya nufi Nihad yace "What happened Nihad?" Kamar jira take ta fashe da matsanancin kuka, yace "Meye haka?" Cikin kuka tace "Ya Farooq wani axxalumin da baya tsoron Allah ya bude ma tsuntsaye na cage duk sun gudu har parrot din" Bude baki Farooq yayi yace "Garin yaya?" Ta karasa ta rungumesa tana kuka sosai, ta gefen ido khalil ya kalleta kafin ya juya ya bar wajen, Farooq ya dago kanta yace "But how did it happen" Tace "Kawai yau da safe naje basu abinci naga ba komai cikin cage din" Yace "Ow that's bad, bari anjima sai mu je ki siyo wasu" Ta marairaice tace "But how will d parrot get to know me just as the old one?" Yace "Yanda wancan din ya sanki sabon ma haka xai san ki" Daga haka ya kama hannunta suka shiga gidan tana share idonta. Bayan ta amshi nata tsaraban da farooq ya kawo mata ta wuce sama xuwa dakinta, wayarta ta dauka ta sake kiran Inna, yana fara ring Inna ta daga, Nihad tace "Inna har yanxu fa driver din na nan babu inda ya tafi don ma in gaya maki" A fusace inna tace "Ke raba ni da wani shegen dreba an shigo an kwashe min yan canjina wai barin gidan da nayi jiya da magariba, kowa sai ce min yake ba shi bane, to ni na saci abina koko?" Nihad ta tabe baki ta katse wayarta, sai kuma ta ja tsaki tace "Dama ba a abun arxiki dake..." Da daddare tana dakin farooq dake kallonta yace "Toh sai in ce masa me idan na kirasa?" A hankali tace "Kawai hakuri xaka basa a kan abinda driver din yayi masa" Farooq yace "Ba kince layinsa a kulle yake ba?" Tace "Aa ya ta6a saving numberka a gabana ai, ka tuna sanda ya kiraka da baka da lafiya?" Yace "Oh, ohk" Daukar wayarsa yayi ta kira masa number Aliyu yayi dialing, a kashe suka ji wayar, yace "It's switch off" Shiru tayi bata ce komai ba, yace "Ki je kawai, gobe sai in kirasa" Mikewa tayi tace "To sai da safe yaya....."
Saura how many page free pages ya kare???
07087865788✍🏻
💖💖 *NIHAAD*💖💖
By _Khaleesat Haiydar_📖✍🏻
10......
Khalil na xaune yana waya a bakin gate mai gadi ya karaso wajen daga boys quarters, Khalil ya saka wayar a aljihunsa bayan ya gama, Aminu da har ya xauna ya mike yace "Aa bari in baka waje ka ci gaba da wayarka...." Khalil yace "Na gama" Aminu ya dawo ya xauna yana kallonsa yace "Na lura baka son kayi waya a gaban mutane saboda hayaniya ko?" khalil yace "Haka ne" Aminu yace "Ina can tare da su Saminu muna ta jajanta lamarin tsuntsayen nan da suka gudu, abun da mamaki da al'ajabi, sun kusa shekara daya da rabi fa a wajen ba a ta6a nemansu an rasa ba sai yau" Khalil yace "Ai gwara da suka gudu kar xunubanta ya dinga shafarsu su ma" Aminu ya kyalkyale da dariya yace "Wllh baka da dama, ni tashin hankalina abincin da tace xa a hanamu, in an hanamu abinci ya xa mu yi? Ba fa kanta kenan, duk da nasan uwarta baxata yarda da hakan ba, amma makira ce tana iya biyomu ta kwace idan an kawo mana" Khalil yayi murmushi kawai, Aminu yace "Amma fa kana bani tsoro da mamaki yanda kake nuna mata baka shakkarta, akwai wani littafi da na ta6a saurara a shafa labari, kaga yanda ta sa ka gaba haka? To haka ita ma yarinyar littafin ta sa mutumin gaba yana aiki a kampanin babanta ita kuma ita ce manaja a kampanin, tayi ta masa walakanci da rashin mutunci daga baya ta xurma sonsa in gaya maka, To sai...." Dakatar da shi khalil yayi yace "Me kake nufi?" Aminu ya gyara xama yana washe baki yace "Toh wa ya sani ko hakan xai iya faruwa wataran, barin taga sambalele me dogon hanci, ka fa san matan nan ba alkibla garesu ba...." Khalil yace "Ta wahala.... banda abun ka ina ita ina talaka? Sai dai kuma bata san wani talakan ma ko da kudi aka hadasa bazai saurareta ba, in dai kamar ni talakan yake wllh ko kallonta baxai yi ba" Aminu ya gwale ido, sai kuma ya tuntsire da dariya yace "Yanxu kana nufi misali yau ace maka gata nan ka aura baxa ka aura ba?" Khalil yace "Misalinka ba me yiwuwa bane har duniya ta nade, don kuwa da in aureta gwara na aura Krista, ko kuma in dauwama ba auren, kai kasan darajan da Allah yayi ma ɗan Adam kuwa? To bari kaji ko da kudi wannan yarinyar baxata tsaya inda budurwata take ba, ga ta dai yar talakawa kamar ni amma ita wannan fitsararriyar baxata tsaya inda xata tsaya ba wllh...." Aminu yace "Aa dole xaka ji haushinta wllh, nima kuma ina taya ka jin haushinta kullum, ji tijaran fa da tayi maka daxu, banda yanayin rayuwa a ina xata ganka har ta cakume kwalar rigarka tana dungure kanka tana maka munanan xagi, a ƙalla ai xaka bata kusan shekara goma na sani, amma ta maka wnn cin mutunci da tijara gaban Nihal da kawarta, ba ma wannan ba ji yanda ta dau bahon ruwa gaba daya ta juye maka a cikin jama'a" Khalil yayi wani Murmushi bai dai ce komai ba, Aminu yace "Ni dai yau ace min ga ta in aura xan yarda in aureta ko don kudin babanta da kuma halaccinsa, sai kuma in saita mata xama...." Daga sama har kasa khalil ya kalli Aminu, bai san sanda yayi dariya ba yace "Kai ta kudin kake kenan" Aminu ya washe hakora, Khalil ya girgiza kai yana Murmushi, Aminu yace "Wllh ni fa naji dadin bude kejin nan da aka yi tsuntsayen suka gudu, Allah ne ya bi min hakki na abinda ta min jiya a kan su" Khalil yace "Ku kuka bar mata tsuntsayen suka kai har warhaka a gidan ai" Daga haka ya mike ya bar Aminu a wajen xai je yayi alwala kafin a kira isha'i. Nihad na komawa dakinta taga missed calls din Husnah da yawa, ta xauna gefen gado ta kirata, yana fara ringing Husnah ta daga, Nihad ta dinga jin hayaniya tace "Kina ina haka?" Husnah tace "Mozida suite" Nihad tace "Me ake yi a nan?" Husnah tace "Wllh na manta ban gaya maki ba shekaranjiya a schl, Abokin saurayin Naf ne ke birthday, nayi ta kiranki tun daxu baki daga ba dama wai in gaya maki" Nihad tace "Toh ai tun jiya ya kamata ku gaya min, kuma yanxu kinga dare yayi" Husnah tace "Kashhh, kinga ke matsalarki kenan Nihad, karfe takwas din ne dare?" Nihad tace "Toh ta yaya ma xa ayi in taho babu me kai ni, kinsan wawan nan har yanzu Abbanmu bai koresa ba wa yasani ma ko asiri yayi ma yan gidan duk suke supporting dinsa, Umma ce kadai ke bayana a ko da yaushe, throughout na xuba ido yau in ga ko xai tafi ban ga ya tafi ba" Husnah tace "Kinsan abinda zai faru?" Nihad tace "Aa" Husnah tace "Yanxu xa mu fita mu karo wasu wine, kawai ki san duk yanda xa ayi ki fito mu hadu a wannan katon supermarket din na anguwarku" Nihad tace "Kar fa ku bar ni inyi ta jira Husnah" Husnah tace "Haba wani jira, bayan gashi nan yanxu ni da Naff da Sumy za mu fito" Nihad tace "Okay, bari a shiga masallaci sbda yan sa ido, sai in fito" Husnah tace "Sai mun hade, kar kuma kice ban gaya maki ba, A abokan celebrant din har da 'ya yan gwamnoni, shiga ce ta kece raini xa ki yi, duk da nasan ki ba wasa" daga haka Husnah ta katse wayar. Nihad ta mike ta shiga bandaki tayi wanka a gurguje jin ana kiran isha'i, ta dauro alwala ta fito da sauri, tada sallah tayi bayan ta idar ta fito da wani ubansun gown dinta ja wanda Aliyu ne ya siyo mata daga kasar waje ta saka, ko make up bata yi ba duk ta harhada kayan make up din da turarruka a wani babban jakarta da xae iya daukan hijab da takalmi da tarkace da yawa, tana jin an tada sllh sae da ta jira aka yi raka'a daya snn ta fita da sauri bayan ta sa ma dakinta makulli, tayi surveying parlor don tabbatar da babu kowa a ciki, ko wa na dakinsa, dama kuma gidan ana magrib kowa ke shigewa daki babu me shiga privacy din wani, sai kuma washegari idan an hadu wajen breakfast, yawanci da yake a bangaren Umma dakinta yake, Umma kan shigo taga ko tana waya kuma da wa take wayar, to dai ta sa ma dakin makulli ko taje xata shiga xata ji sa a kulle, da sauri da sauri ta fito compound nan ma ta ci sa'a babu kowa, duk suna masallaci, kan kace me ta bar compound din ta kama hanyar inda supermarket din da Husnah tace ta jirasu yake, tana isa wajen ko minti biyar ba ayi ba sai ga motarsu Husnah suka dauketa suka wuce, Husnah tace "Yanxu da Habibu na nan nasan da kansa zai xo ya daukeki idan aka gama partyn ko karfe sha biyun dare ne, yanxu dole kinga sai mun ajiye ki a nan after the party in ba dai saurayi kika yi a can ba" Nihad dai ta xuge jakarta ta fara gyara fuskarta xata yi light make up. Wajen partyn ya hadu iya haduwa kamar yanda Husnah ta fada ai kam ya yan manya ne suka cika wajen, very dim light ne kunne a inda suke birthday din, babu abincin da babu da abun sha tun daga ruwa, lemo, wine, alcoholic drinks, kai komai da akwai a wajen, gasassun rago biyu aka bankare wajen, ga manya manyan pepper chicken... cake din da budurwarsa tayi masa ma kadai abun kallo ne... duk hayakin cigarette ya turnike wajen, an sha shagali iya shagali a birthday din nan, abinda Nihad bata yarda da shi ba shine ta sake ma maza fuska a wajen, xata dai shige cikin kawayenta mata amma bata xama cikin maza, ko da kana ta shisshige mata ma banxa xata yi da kai tayi ta danna waya, Husnah ta kwankwade glass din wani alcoholic wine, glass na biyu kenan ta sha, su Naf da sauran yan matan wajen su ma duk wine din suke sha, Husnah na kallon Nihad dake rike da cinyar kaza da wani can drink a gabanta tace "Wllh ki ɗan dana wine din nan ya fi na wancan ranan dadi sannan shi wannan babu abinda xa ki ji idan kika sha, wllh soo cool" Nihad tace "Aa baxan sha ba drink din nan ya isheni" Zully tace "Ke dadina dake kwabsin ki yayi yawa, don Allah ki ɗan kurba idan bai maki ba sai ki bari kar ki sha, nima kinsan ai ban fiye son wines haka ba, amma tunda kika ga ina shan wannan ya kamata kisan ba karya" Nan duk suka mata caaa akan cewa ta ɗandana idan bata ji dadinsa ba sai ta bari, Husnah ta cika mata glass din gabanta tace "Kiyi sipping first ki ji" Nihad ta dauka ta kai baki ta kurbi kadan, bayan few seconds ta wara ido tana kallonsu tace "Waow its really nyc, it tastes good" Husnah ta kyalkyale da dariya tace "Ba na gaya maki ba da kin tsaya kin kwabsawa" Nan Nihad ta kwankwade wine din, Husnah ta kara cika mata glass nan ma ta shanye, Naff sai dariya take tana cewa "Wllh ki bar ta haka Husnah tam ni dai na gaya maki" Husnah tace "Toh meye a ciki ai baya wani bugarwa" Haka dai Nihad ta sha wine tayi nak, party din da ba a karasa da ita ba kenan tayi ta masu layi a wajen, banda dariya babu abinda suke mata, Husnah tace "Kaii amma jininta ma bai da karfi wllh, ɗan wannan wine din shine xai bugar da ita" Nan suka ci gaba da shagulgulansu, Nihad kuwa ta kife kai a wajen sai bacci, ba a tashi birthday din nan ba sai karfe dayan dare, Husnah ba irin tashin da bata yi ma Nihad ba amma ta ki tashi, da ta dagota xata koma ta kife kai, wani abokin celebrant din yace "Na kama daki a nan why not kawai ku barta ta kwanta ta huta" Husnah tace "Aa nasan halinta tana farkawa xa mu samu matsala da ita, kawai dai kamata yayi mu ma a kama mana dakin dama dare yayi ba lallai a bari mu shiga schl ba yanxu, idan ya so duk sai mu kwana a nan" Ba don ransa ya so ba haka nan ya kama masu dakin, suka ciccibi Nihad sai dakin suka kwantar da ita saman gado, Husnah dai na ta kaffa kaffa da Iphone din Nihad a wajen tunda ta san halin wasu daga yan matan dake wajen. Sai kusan biyu suka kwanta a dakin bayan duk sun yi wanka.
Karfe hudu da rabi Nihad ta farka da wani axababben ciwon kai, da kyar ta mike xaune tana bin dakin da kallo, sai kuma ta sauka tana layi ta nufi kofar dake dakin wanda bandaki ne, ta kuma sani tunda sun saba lodging a wajen ita da su Husnah, tana shiga bayin bayan tayi fitsari taji wani amai ya taho mata, nan ta dinga kwarara aman tana rike da cikinta dake juya mata, da kyar ta wanke bakinta bayan ya lafa mata ta fito, bata sake komawa baccin ba sbda ciwon kai me tsanani da ya takurata, ganin biyar ya kusa ta ta6a Husnah da kyar, ta fi minti goma tana tada Husnah dake xuba minshari kamar wani kato, kafin ta bude ido cikin magagin bacci tace "Wai ya aka yi Nihad?" Da kyar Nihad tace "Don Allah wa xai yi dropping dina gida kafin yan gidanmu suyi noticing bana nan, asuba ya riga yayi" Husnah ta ja tsaki tace "Tsakar daren nan wa xai wani kai ki gida kowa na bacci, ki bari gobe kawai" Nihad tace "Ke asuba fa yayi ki duba agogo ki ga, wllh na manta yayanmu na gida zai iya xuwa bedroom dina yace xai tasheni inyi sallah, idan yana gari duk yana tashin mu...." Husnah tace "Ohh God Nihad ki barni inyi bacci mana, haba" Daga haka ta juya ta ci gaba da baccinta, tashi Nihad tayi da kyar ta bude jakarta ta dau Hijab dinta ta saka sannan ta bude kofar dakin ta fita, babu kowa reception din hotel din sai tv dake aiki, ta fita haraban wajen, wani mutumi ta gani xaune yana ta xukar ta6a a waje, ganinta ya kashe ta6ar, ta nufesa tana kallonsa ganin bahaushe ne tace "Bawan Allah idan babu damuwa ina son taimako wajenka don Allah" Daga sama har kasa yake kallonta yace "Taimakon me?" Tace "Nasarawa GRA nake son ka ajiyeni pls, kawayena da muke tare da su bacci suke ni kuma ban xo da motata ba" Yace "Ohk babu damuwa, bari in dauko makullin motata" Tace "Toh Nagode, nima xan dauko jakata" Daga haka duk suka koma ciki, ta shiga dakinsu, shi ma ya shiga nasa, ta tattara komai nata a jakarta, wayarta ne kawai bata gani ba, zaro ido tayi lkci daya hankalinta ya tashi ta fara tashin Husnah a rikice tace "Husnah
Showing 30001 words to 33000 words out of 37658 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11 Chapter 12Chapter 13