"Shaye shaye kika fara da har baki san when and where aka maki video din ba Nihad??" tace "Believe me yaya Farooq, wllh ban sani ba, yanda ku ka gansa haka nima na gansa" Yace "Na rabaki da bin kawaye barkatai Nihad, na rabaki da yawace yawace da xuwa parties, har night party nasan kina xuwa don Sadeeq saw u, na maki magana kika karyatasa kamar bai san me yake ba, u are just different from every other child in this house, just look at the disgrace u have caused to our family, u have tarnished the reputation of our home, how will i face my frnds da suka sanki, my own blood with such act? Oh no, Subhanallah" Ta dinga girgiza masa kai tace "Don Allah ku yi hakuri yaya, i wish my life can end now because of all this, i regret everything" Xaunawa yayi gefen gado ransa a dagule, ita dai ta dinga goge hawayen da ya ki tsaya mata tace "Yaya farooq i need one favor from u plss" Yace "U don't deserve that favor Nihad" tace "Plss yaya abu na karshe da xa ka iya min a rayuwa shine don Allah kar ka bari Abba su yi min auren dole, wllh xan iya mutuwa kaga har na gaya maka" Yace "What did ur boyfriend say about the video?" A hankali ta sunkuyar da kai tayi shiru, ya hade rai yace "Tambayarki nake" Cikin rawan murya tace "Yayi blocking dina...." Farooq ya gyada kai yace "Good" ta hade hannunta tace "Don Allah yaya, kasan consequences din auren dole kar ku bari ayi min, na yarda a min ko wani hukunci amma banda auren dole, idan ma xa a ce for the rest of my life baxan sake fita waje ba, sannan babu ni babu karatu har abada i agree but kar ayi min auren dole sbda wannan mistake din nawa, ka taimaka kayi ma Abba magana" Umma ce ta shigo dakin duk suka daga kai suna kallonta, tace "So kike ki kara tunxura Abbanki Nihad? Duk shirun da yayi maki bai isheki ba sai kin tunxurasa, Ba na baki shawaran kar ki ce komai a kan batun auren nan ba, so kike ki fusatar da Abbanki yayi maki abinda bai ta6a maki ba?" Faruq yace "Noo wannan ba magana bace Umma, we don't even know da wanda xa a hadata, ko ma me tayi ai da gatanta and she still have her right, su gani suke auren shine way out, whereas it's not" Umma tace "Toh tunda kai ka haifesu ai sai ka gaya masu way out" Ya girgiza kai yace "Umma idan ma auren ne ba sai a bari komai ya lafa ba, ta yaya abu na xafi xafi a shigo da maganar aure, waye xai aureta? Noo bata yi deserving wannan auren ba gaskiya" Umma tace "Ko ma wa xai aureta wannan ba damuwarka bane sai ka xuba ma iyayenka ido, su ai sun san abinda ya kamata, ko so kake ka nuna masu goyan bayan abinda tayi kake?" Ya dinga kallon Ummar tasa, Mikewa yayi ya fice daga dakin, ta bi bayansa, Nihad ta bi su da kallo, sai da suka sauka stairs Umma tace "Farooq" ya juyo yana kallonta, tace "Naga kamar so kake ka ja ma kanka bakin jini gun Kakarku da Engineer, sannan nima hakan ya shafeni, kawai so kake ka ja min maganan da ba shi da ranan mutuwa gun tsohuwar nan, don haka kar ka sake tofa komai a kan lamarin nan, ita kanta uwar da ta haifeta taki cewa komai har yanzu, me magana dama daga ni sai kai, kuma a hakan ma haushinmu ake, don Usman ma bai tsoma kansa ba balle a ga nasa, to ba Uba daya ba, ko ciki daya ku ka fito da Nihad ni dai nace ka janye bakinka daga issue din nan domin a samu masalha, daxu Abban naku ma ya kirani wai ya tafi karkara neman wanda xai hadata da, to idan ana son asiri ya rufu ai sai dai hakan dama, to wa xai yarda ya aureta a nan dai cikin gari? don haka nake kara gargadinka, kar ma ka fara cewa a fasa aure" Faruq yace "Karkara kuma?" Umma tace "Ehh nan fa, ko ka ga alamar Nihad xata samu miji cikin gari ba karkaran ba nace, da wannan mummunan abin da ta aikata wa xae yarda nasa ya aureta?" Yace "Ah haba, karkara kuma, noo ba dai karkara ba, waye ya ba Abba wnn muguwar shawaran? Karkara fa kike ce Umma" Strictly Umma tace "Farooq" ya daga kai ya kalleta tace "I am giving u this serious warning, kada ka kuskura ka sake tofa naka a wannan lamarin, kaji abinda nace maka??" Bai ce mata komai ba, tace "To na dai gaya maka" daga haka ta bar wajen ya bi ta da ido.

πŸ’– *Bitter Rivalries*πŸ’–


And i came really prepared...... πŸ€—


Contact me directly viaπŸ‘‡πŸ»

07087865788✍🏻

πŸ’–πŸ’– *NIHAAD*πŸ’–πŸ’–




By _Khaleesat Haiydar_πŸ“–βœπŸ»



~~
2



Dumbin gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga iyayen gidan Khaleesat's Palace, my die hard fansπŸ₯°πŸ˜ Su Hajjaju Chamo me gwala-gwalai duk da jarin ya karye amma take ta bobboye mana, Hajiya Aunty Zahra mai siyar da harawa, Hajiya Nafisa Mom twins, Su Hajiya Aunty Maryam, Uwar Nabeela, Mrs Jay, Hajiya Inna, Hajiya Deejah, Hajiya Zeenaru, Nanisa Zero Zero, Hajiya Bilkisu, Hajiya Rabia, Damsel, Uwar Yusrah, Ummu Zainab, Uwar gidan Barrister wato Khaleesat me siyar da tayoyi, kai duk wanda bai ga sunansa a nan ba ya biyo ni da sunan xai gansa a next page😜 amma fa ko kun ki ko kun so sai nayi sharing link dinku, ku tanadar ma sabbin fans ruwa da cin cin ehe.πŸ€“




Da daddare Abba na xaune parlonsa tare da Yayansa Alhaji Abubakar.... Alhaji Abubakar yace "Ae duk ba sai ka sanar masu komai ba, kawai gobe idan an daura auren kowa ma sai ya sani, i don't think u owe anybody explanation to this" Abba ya numfasa yace "Toh shikenan" Alhaji Abubakar yace "Yea i think that's okay ba sai kace ma kowa komai ba for now, a ina kace xa su xauna? I mean which of ur houses are they staying?" Abba yace "I don't think i can keep her where she will in any way feel comfy, i wish xai koma can karkarar tasu su xauna in basa enough jari, idan noma xai yi ma yayi employing workers su yi masa a can ko ni xan dinga biya, cause i want her to learn a bitter lesson of her life, ina son ta san wata rayuwar bayan rayuwa cikin daula" Alhaji Abubakar ya girgiza kai yace "No... There is no need for all that, duk abinda ya kamata kayi kar ka fasa, ka basu inda xa su xauna comfortably" Bayan Alhaji Abubakar ya bar gidan, Umma ta shigo parlon Abba, ganin basu ta6a abincin da ta ajiye masu ba tace "Haba yallabai, ko abincin baka ci ba har yanxu?" Abba yace "Kawai ayi min black tea" Umma tace "Toh shkkn" Tashi tayi ta dau abincin ta fita, ba a dau lkci da fitarta ba Farooq ya shigo parlon, waya ya tadda Abbansa ke yi, wanda da jin yanda yake amsa wayar kasan magana ce aka kirasa a kan Nihad kuma abokinsa ne me kiran nasa, Farooq ya sunkuyar da kansa duk jikinsa yayi sanyi, har Abba ya gama wayar ya jinginar da kai da kujera bai ce masa komai ba, a hankali Farooq ya dago yace "Barka da dare Abba" Abba ya amsa, Farooq yace "Throughout ina ta kiranka but couldn't reach u on phone" Abba yace "Ehh wata er tafiya nayi, is there any problem?" Farooq yace "Ya gajiyan hanya" Abba yace "Alhamdulillah" Farooq yayi kasa da murya yace "Abba magana ce dama a kan Nihad?" Dai dai nan Umma ta shigo da mug din black tea dake ta kamshi, Da hannu Abba yayi masa alamar ya aka yi, Farooq yayi shiru, Abba yace "Maganar me a kan Nihad Umar?" Farooq ya d'an fara kame kame, sai kuma dai kawai yace "Abba a kan auren nan da aka ce ne, is it not better a yi hakuri a janye, idan ya so..." Dakatar da shi Abba yayi yace "Idan wannan maganar ce ta kawo ka, ka je kawai i need rest Umar, kaga ban dade da shigowa gidan ba" Umma dai na xaune kan one sitter, pleadingly Farooq yace "Pls ka saurareni Abba" Abba yace "I said i need rest...." Umma tace "ka je yace xai huta ko kuwa?" Mikewa Farooq yayi ya fice daga parlon, Umma ta kalli Abba tace "Kayi hakuri Yallabai, xan so ka cire wannan damuwar a ranka, in sha Allah everything will be alright, kar kaje ka sa ma kanka wani ciwon bayan hawan jinin da kake fama da" Abba yayi sigh yana girgiza kai yace "A kalla ba a kirani a rana ba xa a kirani sau goma a kan Nihad, the video is trending day by day.... Me yafi wannan bakin ciki Sumayyah? A reputable person like me, noo Nihad tayi tarnishing image din gida na" Da damuwa Umma tace "To ya xa ayi Yallabai haka Allah ya kaddaro mana, sai dai kawai mu rungumi kaddara, amma akwai wani malami bawan Allah, tun ranan da abun ya faru Hajiya Sukhaina tace ko shi xa ayi ma magana yayi addu'a Allah ya kawo karshen trending din abun, shiru xaka ji kamar ba ayi ba wllh, neman video din ma xa ayi a rasa" Abba ya mata wani kallo yace "Malami? Wani irin malami?" Umma ta gyara xama tace "Ba boka fa nace ba Alhaji, amma dai shkkn kawai, ina ce akwai malamai bayin Allah wa enda..." Mikewa Abba yayi bayan ya dau mug din black tea dinsa ya wuce daki ya kulle kofa. Washegari friday ana sauka sallan juma'a, Abba ya tafi tare da yayansa da cousins dinsa biyu xuwa garin da aka daura ma Nihad aure, a kan sadaki dubu hamsin wanda shi ya bayar. Sai kusan la'asar suka dawo gida, nan kuma ya sanar ma Umma su fara shirye shiryen kai ta, Umma tayi shiru cike da jimami, sai kuma ta sauke ajiyar xuciya tace "To wani gidan kenan xa a kai ta yallabai?" Abba yace "Wannan gidan da aka gama na Rijiyar zaki, it's already furnished" Umma tace "Allah sarki, ina laifin wannan gidan na kusa da mu yallabai, ai xa su fi sakewa a nan..." Abba yace "Ban yi niyya ba" Umma tace "Rijiyar zakin ma yayi ai, Allah ya saka da alkhairi" mikewa tayi ta fita don xuwa sanar ma Mum din Nihad da Yan uwanta dake can bangarenta abinda Abba ya ce, nata side din ta fara shiga, first daughter dinta Kamila na xaune parlon sai second daughter dinta Amina, sannan kanninta mata biyu da suka xo daga Jigawa daxu, Umma tace "To duk ku shirya kai amarya an daura mata auren yau dai" Kamila ta riΖ™e ha6a tace "Har an daura?? yanxu Umma Abba bai fada maku da wa aka yi auren ba, ni kawai sai xuciyata ke bani Hamid ne ko Saif" Umma ta saki baki tace "Hamid? Ita uwar Hamid din karen hauka ya cijeta xata yarda a hada shi da Nihad? Ko kuma shi Hamid din mahaukaciya ne da zai amince da auren Nihad, Kai har shi Uban Hamid din da ya kirkiro auren ba yarda xai yi ayi auren da Ι—an sa ba karewa kenan, haka ita ma Innar, wani can dai Abban naku ya samo a karkara, hakan kuma kadai ne rufin asirinta a dai abin nan da ya faru" Amina ta mika ma Umma wayarta dake ring, Umma ta amsa ganin autarta ce ke kira ta daga ta kai kunne da murmushi tace "Hello auta, duk yau kin ji ni shiru ko" lkci daya ta hade rai tace "Ki zo kiyi me kina karatun ki Nihal? A kan wani dalili xaki taho kuna tsaka da karatu? To wllh kar ki fara idan ba haka ba yanxun nan in kira Farooq in gaya masa, me xuwanki xai sa a fasa, bayan har an daura auren ma, duk sanda ku ka yi hutu idan kin dawo sai kije ki ga dakin er uwar taki ba shikenan ba, amma ki wani ce xaki kamo hanya kamar ana yaki" a kufule Umma da ta gama sauraronta tace "To wai uban meye na wannan kukan da kike, so kike ki ja ma kanki wani ciwo ne ko ko? Bata da waya yanxu a hannu, idan na fita yanxu xan bata sai ku yi magana, amma ta ina xaki baro Zaria da yamman nan ba hutu ku ka yi ba, kuma dama kin ta6a dawowa gida ke kadai ne banda gulma da daura ma kai wahala Nihal?? Ni dai sai anjima ban san shashanci" Katse wayar Umma tayi, Aunty Laraba tace "Wai tahowa xata yi daga Zarian?" Umma tace "Ehh wai, kinji wata gulma dai, ko uban me xata xo tayi oho" Aunty Laraba tace "To wai ita tace ma Abban nasu bata son Maryam Abatcan da er uwar ke xuwa ne?" Umma tayi murmushi tace "Aa haka dai yayi niyya ita ya turata federal dai dai ita, ita kuma Nihad dama Private ne dai dai da ita inji uban, wato Maryam Abatcha, option ma ya bata ta xabi Private uni da take so shine ta xabi Maryam Abatcha" Aunty Maimuna tace "Ai ko ga Maryam Abatcha ana ta gani a soshiyal media" Umma dai bata ce komai ba, sai kuma tace "Allah dai ya shirya mana zuri'a kawai" daga haka ta fita xuwa bangaren mum din Nihad, a corridor ta hadu da matan Alhaji Abubakar su biyu sun shigo gidan, suka gaisa da fara'a ana kara jajanta lamarin da ya faru, Hajiya fatima tace "Daxu Abbansu Hamid ya dawo gida yake sanar mana ai har an daura aure, nace shine babu labari ko daga gare ku Hajiya" Umma tace "Wllh abun ne ya xo a haka Hajajju, kinsan muna ta tunanin xa su hakura a fasa auren a nemo wani solution, to kin san halin mazan namu da kafiya, wllh sun ki, kawai fatan Allah ya basu xaman lafiya da ko ma waye mijin" Hajiya Zuwaira tace "Shikenan addu'ar, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi a gareta, Allah kuma ya duba yan baya" Duk suka amsa da Ameen, Umma tace "Mu je dama bangaren Maryam din xan je" a tare suka tafi part din Mumy, bayan an gaisa an kara jajantawa, Mumy dai bin su kawai take da kallo bata cewa komai, Umma ta sanar mata abinda Abba yace sannan ta fita daga dakin. Bayan magrib xa a kai Nihad, kafin Magrib din Abba ya tara gaba daya matan nasa da 'ya yansa, Usman, Farooq, Kamila, Amina, Nihal ce kawai bata nan a yaran Umma, yaran Mumy kuwa Nihad da kanninta biyu wa enda duk maza ne, daya me shekara tara da kuma me shekara shidda duk basa parlon, Bayan duk sun hallara a parlon Abba ya nisa yace "Ina fatan duk kun ga abinda ya faru da yar uwarku Nihad, Nihad is nothing but a disappointment to the family, kar ku ga Nihad tayi wannan mummunan laifin na bada ita ga wanda nayi niyya without bothering ko ya cancanceta ko bai yi ba, to wllh wllh if anything of such should happen again in my family infact ko wanda bai yi kusa da hakan ba idan ya faru a family dina wllh i will prefer to shoot that person" Umma ta sauke ajiyar xuciya tace "Allah Ubangiji ya tsare, ya kare mana zuri'a Alhaji" Abba ya kalli Mumy da bata cewa komai tun faruwan abun, amma kana ganinta kasan she is heartbroken, her first child, habaa ko bacci bata iya yi tunda wannan lamari ya faru, da tasan Nihad xata girma ta yi irin wnn rashin jin da Allah bai raya mata ita ba, tun faruwan hakan ita ma ta kashe wayarta sbda kiran yan uwa da abokan arziki da suka san Nihad, Abba yayi gyaran murya yace "Ban ga laifinki ba Maryam don ni nasan kinyi iya bakin kokarin ki na ganin kin ba ma Nihad tarbiya yanda ya kamata, u tried ur best, matsalar kawai u didn't make Nihad ur frnd aside mothering her, amma dai babu komai, kawai dai kafin Nihad ta dauko mana abinda xuciyarmu xai kasa dauka nan gaba tun wuri ni da yayana da yan uwana mun mikata, kusan xance na bada sadakarta" Abba na fadin haka ya ciro sadakinta dake aljihunsa ya mika ma Umma yace "Sai ki damka mata ku da xa ku kai ta" Umma ta amsa cikin sanyin murya tace "Yanxu Yallabai mun yi deserving a bada er mu ba tare da mun san wanda aka ba ma ba? Ai hankalinmu baxai taba kwanciya ba, tun jiya nake bin ka kaki gaya min, ai yana da kyau a sanar mana mu sani don muna da hakkin sani, idan ma ni bani da hakkin in sani mahaifiyarta fa?" Abba ya Ι—an yi shiru, sai kuma ya dau wayarsa yayi dialing number snn ya kai kunne, ana dagawa yace "Ka shigo nan parlor ka sameni yanzu" daga haka ya katse wayar, duk kowa yayi shiru ya xuba ido ya ga wanda xai shigo parlon barin Farooq da Umma. Da sallama ya bude kofar parlon, ganin su Umma ya dakata daga bakin kofar bai shigo ba, Abba na kallonsa yace "Karaso" ya karasa shiga cikin parlon kansa a kasa, duk occupant din parlon kallonsa suke with full shock, Abba ya nunasa yace "Shi na ba auren Nihad, shine mijinta" Mikewa Farooq yayi yana kallon Abba baki bude, Mumy ta hadiyi wani kullutu da taji ya tokareta a makogwaro, Umma kuwa sae kallonsa take daga sama har kasa babu ko kiftawa, ta ma rasa yanayin da take ciki ita, Kowa na parlon ya kasa cewa komai, tsabar silence din parlon da allura xai fadi xa a ji karar faduwarsa, shi kam dai yana ta tsaye ya sunkui da kai har sannan, Abba yayi breaking silent din yace "Je ka" Juyawa yayi ya fita daga parlon, Usman ya kalli Abba
Showing 3001 words to 6000 words out of 37658 words