a wajensa, a nakada masa shegen duka" Nihad tace "Husnah bari in je gida ko xan ji saukin abinda ke damuna, i can't endure anymore" Husnah ta ta6e baki tace "Wllh kina da sa ma kai damuwa, duk ki bada space din da lamarin driver xai dinga damunki haka, to wai shi wannan driver din daga ina ya xo yake abu isa isa da gadara haka?" Mikewa Nihad tayi tace "Duk yanda ake ciki xan kiraki da wayar Nihal ai tana da number ki" Daga haka ta fice daga hall din, tun da ta fara school din bata ta6a trekking da kafafuwanta har bakin titi ba sai yau, haka nan ta tsayar da adaidaita shi ma xata iya kirga iya sau nawa ta hau sa a rayuwarta, suna isa gida ta sauka ta bude jakarta ta basa kudi sannan ta shiga gidan, Aminu ne kawai bakin gate, ta ɗan bi compound din da kallo sai kuma tayi kasa da murya tace "Aminu baka tambayar min driver din can ko ya ga jakata ba kuma?" Aminu yace "Anya, don ina da yakini da ya gani xai nuna min, ai shi mutum ne me gaskiya da amana" Ta wani galla masa harara tace "Dallah Malam rufe min baki, duka duka kwananku nawa tare xaka san yana da gaskiya da amana, ashe kai dolo ne ma ban sani ba? To bari ka ji wayata ce ta kusan miliyan daya da rabi a jakar nan" Driver ya gwalo ido yace "Subhanallahi, subhanallahi...." Nihad ta saci kallon wanda ke tahowa ganin driver din ne ta daure fuska ta juya ta nufi cikin gida da sauri, xaunawa Khalil yayi gefen Aminu ganin yanda yake zaro ido kamar mara gaskiya yace "Me ya faru kake buda ido haka" Aminu yace "Ba nace maka ta yarda jakarta ba daxu har tana tambayata ko na gani, to wllh wai har da wayarta na miliyan biyu da rabi a cikin jakar" Khalil ya ciro karamar wayarsa yace "To ta huta..." Aminu yace "Atoh dai, Ta kuwa huta wllh, don yau tana sa uban a gaba ya siya mata sabo wallahi sai ya siya, sai dai uwarta ta hana amma tsaf in dai ita ce xai siya mata, kai kaji waya har miliyan uku, ni yanxu na samu irin kudin nan ai kauye xan koma in tada gini malam, inci me kyau in sha me kyau, sannan in kara mata biyu...." Khalil na kallonsa yace "Haba?" Aminu yace "Wllh tllh, albashin namu fa Hajiya ke amsowa a wajensa ta bamu, Ni dai ban san ko nawa yake bata ba amma dubu 50 50 take bamu, kuma da farkon xuwana akwai wani lkcn da ya ta6a bani da kansa wllh dubu 70 ya bani, to kilan dai har da kyautatawa ce irin tasa ban dae sani ba" Khalil dae bai ce masa komai ba. Nihad na shiga cikin parlor ta tafi dakinta direct, xaunawa tayi gefen gado ta rafka tagumi abun duniya ya isheta, tun da shegen mutumin nan ya xo gidan nan bata da kwanciyar hankali, bude kofar dakin aka yi Nihal ta shigo da sallama, Nihad ta daga kai tana kallonta, Nihal ta karaso ta xauna gefenta tace "Amma ba ki jira ku gama lectures din yau ba kika taho ko" Nihad ta yatsine fuska tace "I am tired, kawai shine na dawo" Nihal tace "Toh ki kwanta ki huta, xuwa yamma sai ki rakani shopping din, kinsan gobe sunday xan tafi fa" Nihad tace "Wa xai kai ki shopping din??" Nihal tace "Khalil" Nihad ta juya ido tace "Waye haka?" Nihal tace "Driver..." Nihad ta bude baki ta rike ha6a tace "Wai khalil? Shi uban wa ya basa wannan suna yana driver? Ni fa na xata kinyi wani saurayi ne Khalil ban sani ba, shi driver din ne yace maki sunansa khalil?" Nihal dai kallonta kawai take, Nihad ta gyada kai tace "Tabdi, ana iskanci a duniya, shi yasan ma'anar Khalil din ma kuwa?? Yau naga mutumi da karfin hali, ke kuma wawuya shine kika yarda sunansa Khalil, to wllh karya yake ba abinda ya hadasa da wannan sunan" Nihal tace "To ko ma dai meye sunan Abbanmu garesa, ko so kike in kira sunan Abba gatsau?" Nihad tace "Toh meye don kin kira tunda ba sunan Abban kika kira ba? Meye don kin ce masa Ibrahim ba shine sunan nasa ba? Wato dai ke kika makala masa khalil din kenan?" Nihal tace "Aa, yace haka ake kiransa dama, ni bani na sa masa ba" Nihad ta bude baki tace "Ji shegen karya, to karya yake munafuki, uban wa ke ce masa haka? Amma fa mutumin nan yayi mugun raina maki wayo ma dai, a kauye wa yasan wani khalil, dama Halilu yace shine xan yarda, to wai tsaya ma tukun, fira ku ke har yake gaya maki sunansa khalil??" Mikewa Nihal tayi tace "Woo na gaji da question and answer din nan, Ko ma meye sunansa ba abu bane da za mu tsaya muna bata lkci akai, ni dai anjima ki shirya mu je Sahad store din" Nihad tace "Allah ya kiyaye in dai can xaki wllh baxan je ba, ga wajaje irinsu wellcare kice min Sahad, ai kowa da kowa ke xuwa Sahad" Nihal ta juya ta kalleta, sai kuma ta girgiza kai kawai ta fita daga dakin. Nihad ta rike ha6a tace "Ji maye wai khalil, shi a lallai ya xo gidan masu kudi bari ya maida sunansa irin na yan gayu wai khalil, aa Khalo ba khalil ba" Ta ja tsaki ta mike ta shige bandaki. Ta a fitowa ta koma gefen gado da take xaune ta xauna, tunani ta shiga yi a ranta, to ko dai taje can chalet din da kanta ta duba jakarta ne? Ta kalli agogo lkci daya ta mike ta fito main parlor Umma tace "Aa har kin dawo er baba" Nihad ta gaisheta sannan ta fita balcony har sannan taga yana xaune tare da Aminu a bakin gate, komawa ciki tayi ta shiga kitchen sannan ta bude kofar kitchen din da xai sada ka da back yard din gidan wanda ta nan ma xaka iya xagawa har xuwa Chalet, ganin yanda Hafsah ke kallonta ta sha kunu tace "Ya dai da kallo haka ke kuma?" Hafsah ta kauda kanta, Nihad ta fita da sauri ta xaga ta baya sai Chalet, bata ga takalmin kowa a bakin kofar ba alamar su Isiyan ma duk basa nan kenan, a hankali ta bude kofar tana leka parlon sannan ta shiga, da sauri sauri ta fara dudduba parlon, har xuwa dining area bata ga alamar jakarta ba, har bandakin dake parlon sai da ta bude, wanda sai da ta kusa amai, ta kullo da sauri tana yatsina fuska ta yi hanyar dakunan chalet din, duk dakuna biyun dake a bude sai da shiga tana tottoshe hancinta tsabar tsami da doyi, na ta bincika kaf Ghana must go da ta gani a dakunan amma bata ga jakarta ba, dakin da khalil ke ciki ta murda ta ji a kulle, to ko dai nan dakin aka ajiye jakar nata shine har da kullewa da makulli, tunanin inda xata fara nemo spare key ta shiga yi, can ta zare key din dake jikin kofar su Isiya ta juya ta fita da sauri ta xaga ta koma kitchen, sai da ta wanke hannunta da morning fresh ta hada har key din tana yatsina fuska sannan ta shigo parlor, har wani tashi taji xuciyarta ke yi sbda warin da ta dinga inhaling, kazami irin wannan har shi xai takura mata a gidan nan ya dinga shiga gonarta, dubi wajen da suke kwana wanda ita ko pig take rearing baxata bari yayi rayuwa a irin wannan kazantaccen wajen ba, tana wannan tunanin ta faki idon Umma dake waya ta shige bangaren Abbanta, direct dakinsa ta wuce bayan ta shiga parlor, nan ta hau bude duk wani drawer da ke dakin, a bedside drawer ne ta ga bunches of spare keys na gidan, tayi murmushi ta kalli na hannunta sannan ta hau duba irinsa, kaf irinsu guda uku dake wajen duk sai da ta dauka incase of necessity sannan ta mayar da drawer din ta kulle ta mike ta fice daga dakin, kitchen ta sake bi ta xaga xuwa Chalet din, da sauri ta shiga ciki ta nufi hanyar rooms din, dakin dake kulle tayi facing, ta hau gwada makullen hannunta da sauri da sauri, lkci daya ta bude dakin, wani farin ciki ne ya lullubeta, ta shige ciki ta kulle tana bin ko ina da kallo gabanta na faduwa? Banda kamshi babu abinda ke tashi a dakin, rigarsa da ta gani saman gado ya sa ta gane shine a dakin, rike ha6a tayi.... to gidan uban wa ya samo wannan turaren da ya xuba a dakin haka, bata daina bin dakin da kallo ba ta karasa middle of the room, the room look so different kamar ba a chalet din ba, babu tarkace da kaya kamar irin na su isiya sannan everywhere looks so neat and tidy, ta kyabe baki without bothering ta hau yin abinda ya kai ta dakin, Duvet ta gani kamar an rufe abu da shi ta tafi da sauri ta daga sai ga jakarta a ajiye saman gadon, xaro ido tayi wani farin ciki ya lullubeta, ta bude jakar tana bincikawa da sauri, banda abubuwan da Husnah ta xuba mata a jakan sai nata tarkacen bata ga alamar wayarta a ciki ba, nan kuma ta marairaice tana bin dakin da kallo, a ina to ya ajiye mata wayar?? Sake jakar tayi ta nufi tasa jakar kayan dake dakin, sai bin jakan take da kallo kafin ta durkusa ta xuge zip din, ko karasa bude zip din bata yi ba tayi ido hudu da wayarta, babu bata lkci ta dauka, dai dai nan kuma aka bude kofar dakin, tsabar rudewa da tsorata da tayi bata san sanda ta mike ta saki wayar jikinta na rawa tace "Wayyoo... Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"



07087865788 ✍🏻

Showing 36001 words to 37658 words out of 37658 words