inyi ma mai aikin gidan magana in amso maka" Daga haka ya nufi backyard din gidan xuwa kofar kitchen dake baya, Drivern dai na xaune yana ta juya makullin motar hannunsa sai ga mai gadin ya dawo da plate din dankali da kwai da kofin shayi, ya amsa yace "Nagode sosai" slice din bread ne biyar a gefen irish din da kwai wanda aka matsa ketchup a gefe shi ma, irish din ya fara ci yana dangwalawa da ketchup din, Mai gadi yace "Amma xaka dinga tafiya ne da daddare ka dawo da safe ko gidan nan xaka tsaya?" ya kallesa yace "A ina xan tsaya a nan din?" Mai gadi yace "Ka ji ka, Yo ai har Habibu ya gama yayinsa a gidan nan kafin Alhaji ya bude masa shagon da ya bude masa na tayoyi a gidan nan yake komai nasa, duk tare muke, ga can boyis kwata, su Saminu da Shafi'u masu gyaran pulawa da sharan tsakar gida da Isiya me wanki da guga ai a nan suke duk" ya dau cup din shayin ya kurba yace "Dakin babba ne?" Mai gadin yayi dariya yace "Wai daki, to har parlor akwai a ginin, sannan dakuna uku ne ko wanne da bandaki, kai har ma da kitchen a nan din" yace "To shikenan" Aminu mai gadi yace "Kai ma kayi xamanka kawai a nan xa ka fi gane kan albashin naka, kaga babu xancen kashe kudin abun hawa xuwa da tafiya sannan xa a ciyar da kai a nan ba sae ka siya komai da neran ka ba, duk abinda yan gida suka ci a nan shi mu ma muke ci" Shi dai bai ce komai ba ya gama cinye irish din tass sannan yace "Toh xan xauna nan din in sha Allah, nagode da kulawa" Ganin ya ajiye plate din Aminu yace "Ya haka, naga baka ci kwan ba? Yanxun nan fa ta soya maka" Ya girgiza kai yace "Bana so" Aminu ya dau plate din yana kokarin cin kwan yace "Allah sarki, wasu haka suke basa cin kwai sai suce yana masu karni, mu dai kam ko danyensa ne baxa mu ki ci sha ba, wa yaƙi dadi" Sai da Aminu ya cinye kwan ya mike yace "Mu je ka ga Boyis kwatan" shi ma ya tashi, yana biye da shi, suka tafi far end of the main building in which stood a Beautiful Chalet, mai gadi ne ya fara shiga, shi ma ya cire takalminsa bakin kofar shiga Chalet din kamar yanda mai gadin yayi sannan ya shiga ciki, ba laifi parlon na da girma, sannan ga kujeru har ma da tv, kaya ne ko ta ina a parlon ga wani tashi da parlon yake, everywhere looks very untidy, isiya ne tsaye parlon yana ta faman guga a ironing board, Aminu yace "Ashe kana ta guga shi yasa baka fito ba, ina Saminu?" Isiya dake ta kallon wanda Mai gadin ya shigo da yace "Suna can daki" Aminu yace "To ga bako, kun samu karuwa a nan, shine ya maye madadin Habibu a gidan nan yanxu" Mutumin ya gaida isiya, isiya ya amsa yana ci gaba da gugansa, Aminu na kallonsa yace "Mu je ka xabi dakin da xaka xauna ko" Isiya yace "Ka dai san dakin dake daga dama ni ne a ciki, na hagu kuma Saminu, wanda ke jikin na hagun Shafi'u ne a ciki" Shi dai kallonsa kawai mutumin yake, Aminu dake kallon Isiya shi ma yace "To ya xa ayi kenan" Saminu da Shafi'u ne suka fito daga dakunan su, Isiya yace "Toh ai parlon ma na da girma sai kawai ya maida nan din wajen kwanansa ko" mutumin ya gyada kai yace "Ohk to shikenan" Isiya yace "Yauwa" Aminu ya kalli su Saminu yace "Sabon direban gidan ne shi ma kuma nan xai xauna, sunansa Ibrahim kun ga sunan Alhaji ne...." Saminu yace "To sannun sa da xuwa" Tuni ya juya ya fita daga parlon ya bar mai gadi, Aminu na ganin haka ya bi bayansa da sauri... Suna tafe mai gadi yace "Amma kasan da nauyi mu dinga kiran sunan Alhaji gatsau, baka da wani sunan ko inkiya da xa mu iya dinga kiranka da?" kallonsa yayi yace "Khalil Mahaifiyata ke kirana" Aminu yace "Allah sarki, to ai mu ma sai mu ce khalil din, suna me dadi kamar na larabawa wllh" Bayan sun koma mazaunin mai gadi sun zauna, Mai gadin ya kallesa yace "Yanxu kawai kayayyakin ka xaka je gida ka debo, aikin naka ma fa ba wani me wahala bane, kaga yan makaranta motar makaranta ce ke xuwa daukansu da safe, Yan matan nan biyu kuma daya a zaria ma take karatu, dayar ce ke karatu a nan, ita warce ke karatu a nan din sai ta kai karfe biyu ma bata tafi makarantar ba, Alhaji kadai xaka ajiye karfe tara gun aikinsa, ban ki ba dae Nihad don gantali gareta kamar ta ci kafar kare, kuma sae ta fake da makaranta, a takaice dai kai Alhaji wajen aikinsa da safe shine ainahin aikinka sauran duk masu sauki ne" Khalil da har ya gaji da surutun Aminu ya gyada masa kai kawai, for the next 30mins Aminu bai yi shiru ba, Khalil har ya daina tanka masa don ya ma yi nisa a tunanin da yake, dai dai nan Alhaji ya fito, Mai gadi yayi kasa da murya yace "Da alama yau baxai je motsa jikin ba kenan tunda har gashi sha daya ta yi" Sai kuma ya mike, Khalil ma ya mike yana kallon Alhajin a bit surprised at who is standing next to him, Khalil yayi kasa da murya yace "Yan makarantar har sun taso ne?" Mai gadi ya kalli Khalil da sauri yace "Ka je yana maka magana ne" Khalill ya nufi Alhajin da hanzari, Alhaji yace "Mu je xaka ajiye mu 3 streets away from this" Khalil yace "Toh" Motar da yayi parking bayan ya ajiye yan makaranta ya nufa, Abba yace "Wancan motar ba wannan ba" Khalil ya tafi gun motar da Abba ya nuna masa, Bayan sun fita gidan Mai gadi ya kulle gate, driving Khalil yake a hankali, lkci lkci yake kallon Nihad dake zaune bayan mota da Abbanta tana danna wayarta. Ganin Khalil a layin da Alhajin yace ya ajiye su, Alhaji Ibrahim yayi mamaki sosai, don shi ya ma mance ba Habibu bane ke jan sa, bai yi masa kwatancen inda xai kai su ba ya dai ce masa 3 streets.... Ganin yayi slow down Alhaji Ibrahim yace "Noo ci gaba da tafiya, gida na uku xaka tsaya" Dai dai gidan Khalil yayi parking, Alhaji yace "Kayi horn kawai" yana yin horn mai gadi ya leko ganin motar ya koma ya bude gate din da sauri, Khalil ya shiga ciki ya samu waje yayi parking , Alhaji Ibrahim yace "Maa sha Allah, kayi jirana har in fito" Khalil yace "To Alhaji" Nihad ta sauka ta daya side din wayarta kare a kunnenta, Alhaji Ibrahim ya sauka ya nufi entrance din gidan, Ta side mirror Khalil ke kallonta amma sai yaga kamar wannan fara ce ai, Nihad dake ta xagaye da waya a kunnenta da sunan she is making call, whereas she is not kawai bata son Abba yace su shiga ciki tare ne, tana ganin Abban nata ya shiga gidan ta turo baki ta tafi can karkashin wani Thatch dake compound din wanda aim dinsa wajen shan iska, xaunawa tayi a wajen. Khalil ya sauka daga cikin motar ya tafi gun mai gadin gidan suka gaisa, Mai gadin na kallonsa yace "Ko kai ne madadin Habibu" Khalil yace "Eh nine" Mai gadin yace "Maa sha Allah" Xaunawa khalil yayi yana bin compound din da kallo, wanda shi ma yayi haduwan karshe, ya d'an juya ya kalli Side din da Nihad take, she was so engrossed with what she is doing on her phone....


U can contact me directly via👇🏻


07087865788✍🏻

4
💖💖 *NIHAAD*💖💖




By _Khaleesat Haiydar_✍🏻




~~~~

Gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga manya manyan fans dina irinsu.. Fatima Arebia, Aisha Abubakar, Maman Shukrah (Banatsapparel and more) Khadijah Dutse, mu'azatu😂, infact da duk wani member na Khaleesats palace da ban ambato ba a nan ku sani ina son ku har raina, ina yin ku, ina maku fatan alkhairi Allah ya dafa maku a duk lamuranku, My respect to many of my fans da suka fara patronizing Nihad without even waiting for the end of free pages, yawancin ku ba biyan littafin ku ka yi ba kyauta ce kawai kuke min, kuma ina alfahari da ku, ina maku fatan alkhairi da Zuri'a dayyiba. Allah ya bar xuminci, ya saka da Alkhairi ya karo maku yalwataccen arxiki, na kuma sadaukar da page din nan gare ku.



Bayan minti talatin da biyar Nihad ta gaji da jiran Abbanta don har sannan bai fito daga gidan ba, ga kiran da Husnah ke ta yi mata taki dagawa don bata son tace mata bata gida tasan baxata jira ta ba, kallon agogon dake makale hannunta tayi ganin sha biyu har da minti goma ta tashi daga kan kujerar da take ta nufi khalil, Babu yabo babu fallasa tace "Hey xan koma gida kayi dropping dina yanxu" Sai da ya fara kallon mai gadi dake gefensa kamar dai da mai gadin take, ta daure fuska tace "Malam da kai fa nake?" Sai a sannan ya kalleta ya d'an kara kunnensa gaba yace "Na'am" Rasa ma me zata ce masa tayi saboda bakin ciki, har sannan fuskarta a daure tace "Ina ga dai kana da matsalar ji, dalla malam ka tashi ka maida ni gida" Yace "Naga ai Alhajin bai fito ba" Tana masa wani kallo tace "Eh na fi ka sanin bai fito ba" Yace "To kar ya fito ya tarar bana nan" Ta rike kugu cike da masifa tace "Sai ka maida ni, idan ka maida ni xaka iya dawowa idan ka ga dama" Ya dauke kai yayi shiru bai ce komai ba, shi dai mai gadi sai mazurai yake da ido babu damar ya kwaba ma khalil, shi tsoronsa ma kada wnn ɗan abin ya sa ya rasa aikinsa, yana ga kamar Khalil bai ta6a aiki gidan masu hannu da shuni bane shi yasa har ya tsaya suna ja in ja da Hajiya karama banda haka ina shi ina biyeta, ai duk abinda tace haka xa ayi, tsawar Nihad ne ya dawo da mai gadin reality don sai da ya tsorata, "Dalla Malam kana bata min lkci, are you even okay, how dare u query my order? Ko dai kana shaye shaye ne???" Khalil ya ɗan kalleta, sae kuma ya mike ya nufi motar, ta ja wani dogon tsaki ta bi bayansa kamar xata tashi sama tana harararsa, duk sai taji ranta yayi mugun baci, bayan mota ta bude ta shiga, tuni mai gadi har ya wangale gate yana daga mata hannu alamar Allah ya tsare, Khalil yayi reverse ya fita daga compound din, cikin mintuna kadan ya isa gida da ita, yana parking dai dai gate ta ja tsaki ta bude motar ta fice without closing the door, da ido ya bi ta har ta shiga gate din gidan, ya fi minti biyar tsaye da motar, daga bisanni ya sauka ya kulle door din motar, sannan ya shiga yyi reverse ya bar layin ya koma can gidan da Abba yake. Nihad na shiga gida bangaren Umma ta nufa, jefar da jakarta tayi saman kujeran parlon tana kallon Umma tace "Umma wani irin driver ne wannan Abba yayi employing, who even linked them? wllh yaron bai da kunya ko kadan Umma, kinga abinda yayi min kuwa??" Umma ta ajiye kayan hannunta tana kallonta tace "Me yayi maki?" Nihad tace "Wllh rashin kunya yayi min, ni babu wani wanda ya ta6a min haka ma tun da nake, wai yaron ya maida ni gida yaki fa" Umma tace "Aa abu me sauki sae ayi ma Abban naku magana ya sallamesa, halan d'an kauye ne?" Nihad tace "Toh ae dama su ne masu wannan tsagerancin da rashin ta idon, wllh Umma wannan idan yayi wata daya a gidan nan daina kai mu duk inda xa mu xae yi, Allah cewa xai dinga yi baxae je ba kansa tsaye idan ma bai hada mana da zagi ba, gwara kawai Abba ya dawo ya sallamesa a samo wani dama ni bai min ba from the start, irinsu ne idan an shigo da su inuwa su maida mutum rana, wai kinga me yayi min ne, jayayya fa muka tsaya muna yi da shi" Daga haka ta fice daga parlon ta tafi dakinta don ta shirya xuwa inda xa su hadu da Husnah, sae dae tana tsaka da shiryawa ta dinga kiran wayar Husnah ta ji a kashe, lkci daya ranta ya baci, kaddai har tayi tafiyarta, ta zauna gefen gado tana ta trying din layin amma ya ki connecting. Ana kiran sllhn Azahar Abba ya fito daga gidan tare da wata tsohuwa, Khalil ya mike tsaye ganinsu, suna karasowa inda yake Abba yace "Sabon drivern da na dauka kenan Hajiya, yau ya fara aiki..." Tsohuwar ta kallesa daga sama har kasa tace "To ba laifi, kuma da ganinsa xae fi Habibu kwazo duba da halittarsa, kawai dae sai mu yi fatan Allah ya sa ya fi Habibu nutsuwa, don Habibu ni kadai nasan ɗan iska" Khalil yayi kasa da kai tare da risinawa yace "Ina yini Hajiya" da fara'a tace "Lafiya lau, amma kai buzu ne koh?" Ya murmusa yana girgiza kai, Tsohuwar tace "Toh a dai kula da dukiyar mutane ka ji, kai ma sai kaga Allah ya kula da kai, baka ga motar da Habibu ya ajiye kafin ya tafi ba, duk ta fita hayyacinta daga karshe konden konden aka siyar ma, su ma din dai a walakance suka siya, ya sunanka?" Yace "Ibrahim" Buda baki tayi tace "Ikon Allah, Kai ae kawai ka zama d'an gida abun ka daga yau ka ji, babu me raina ka ko waye shi, kanka tsaye kar ka yarda da hakan, ae sunan Uban gidan naka kenan, kuma ni na haifesa, Allah yayi maku albarka gaba daya" yana murmushi yace "Ameen" Abba yace "Toh ki koma haka Hajiya, ni xan tafi" Tace "To Allah ya tsare, idan Habubakar din ya dawo xan tattauna da shi" Yace "Ba laifi, sae anjima" daga haka ya nufi motar, Khalil na biye da shi a baya. Yana ajiye Abba a gida, Abba yace "Ka tafi islamiyya ka dauko yara nasan sun tashi ynxu" Khalil yace "Toh in sha Allah" hanyar makarantar ya nufa, yana parking bakin gate sae ga Nihal, sannan Fadil da Sudais, Amina ce karshen fitowa duk suka shige bayan motar, ita kuma ta xauna gaba, ta madubi yake kallon Nihal, tace "Barka da rana" xai amsa Sudais da Fadil suka gaishesa su ma, amsa masu yayi gaba daya sannan ya maida hankalinsa kan driving din da yake. Nihad na tsaye bakin parlon Abba tana jiran ya amsa sallamar da tayi, yana amsawa ta shiga, ta karasa parlon ta xauna saman kujera tace "Abba ina yini" yace "Nihad me yasa kika ki shiga ku gaisa da inna da mutanen gidan?" Ta langwabar da kai bata ce komai ba, glasses dinsa ya saka yana maida dubansa kan laptop din gabansa, tace "Abba i came to report this new driver to you" Sake kallonta yayi yace "What about him?" Tace "Abba kawai don nace ya maida ni gida i am press shine mutumin nan ya ki, infact yi yayi kamar bai ji abinda nake cewa ba ya bar ni a tsaye" Abba yace "Is that so?" Tace "Wllh Abba, and it's not as if i was rude to him, kawai cewa nayi don Allah ka maida ni gida ina son xan koma, kawai sai yayi min banxa, wllh Sagir mai gadi ne shaidata" Abba dai yayi shiru yana kallonta, bude kofar parlon Abba aka yi sai ga su Sudais da Fadil sun shigo gaida Abban nasu ganin motarsa a gida, Nihal ce ta shigo bayansu, Abba yace "Welcome Nihal, tell the driver to wait me at the balcony...." Juyawa tayi ta fita, ba a wani dau lkci ba sai ga ta ta dawo tace "Abba na gaya masa" Abba ya ajiye laptop din kafarsa ya mike ya nufi kofa, Nihad taji wani dadi har cikin ranta dama babu abinda xata ce ma Abbanta tana so da baya yi, mikewa tayi da sauri ta bi bayansa Nihal ta bi ta da kallo, Abba na kallon Khalil bayan ya zauna saman daya daga kujerun dake wajen yace "Ibrahim me yasa tace ka maido ta gida ka ki?" Khalil ya durkusa kasa yace "Yallabai ban ki ba, ce mata nayi kar ka fito ka tarar bana nan kace inyi jiranka, amma daga karshe na daukota na dawo da ita gidan" Nihad dake jikin kofa ta hade rai jin abinda yace, Abba ya juya ya kalleta yace "Is that so?" Tace "To Abba sae fa da ya ja min rai, maimakon ina gaya masa kawai ya tashi ya kai ni gida" Abba ya kalli khalil yace "Je ka" Mikewa Khalil yayi yana kallonta yace "Kiyi hakuri, ban san haƙan xai bata maki rai ba" Wani shegen kallo tayi masa ta juya tayi wucewarta ciki. Bangaren Umma Nihad ta koma, Kamar xata fashe da kuka tace "Umma kin ga Abba bai dauki ko wani action ba dai ko?" Umma tace "Sai yace masa me?" Tace "Ba abinda yace masa, ni wllh sai dai duk abinda xai faru ya faru, da kaina xan dinga driving kaina, gashi gobe ina da lectures karfe goma a haka xai kai ni schl din? Nooo i will prefer to drive my sef" Umma tace "To idan kika tafi da motar da wanne xa a dauko kannenki daga makaranta?" Tace "Ba ga motar yaya Farooq ba ko yaya Usman" Bata jira me umma xata ce ba ta fita daga parlon xuwa kitchen, Aminu mai gadi ta gani a windown kitchen din ta baya, mai aikinsu Hafsah tana xuba wani abinci a plate, kallonta tayi tace "Abincin waye wannan?" Kafin tayi magana Aminu yace "Na sabon dreba ne" Buda baki tayi tace
Showing 9001 words to 12000 words out of 37658 words