tace "Kawai yaje ya sha kwayoyinsa jiya in gaya maki yayi assaulting dina" Nihad ta xaro ido tace "Really?" Husnah tace "Wllh ke dai in gaya maki, ban da abunsa ai i wouldn't have denied him" Nihad tace "Where was Nafee then?" Husnah tace "Ita suna tare da saurayinta, kin san shi ma ya zo" Da mamaki Nihad tace "Yaks??" Husnah tace "Ai kuwa baki ga yanda ya dinga tambayarki ba, nace kina hanya duk ya damu baki iso ba, ke gwara ma da baki xo ba din, kilan rashin xuwanki ya sa haka ya faru," Nihad tayi shiru, can tace "Tabdi, kuma a Tahir guest palace din?" Husnah tace "Wane Tahir, ai ba a can muka yi birthday din ba, ke kinga haduwar birthday din nan kuwa Nihad?? Gaskiya na jima ban ga birthday da yayi haduwar na Maska ba, it was light" Nihad tace "Ni xancen yaks ne ya tsaya min a rai, Shi yasa fa kike ganin bana kula clique dinsu, bana harka da maza marasu aji" Husnah tayi dariya tace "Ni kawai way of approach dinsa ne ya kona min rai, amma what's there? norms ne ai, someone that i have been crushing on from day one" Nihad tace "To karfe nawa ku ka bar wajen?" Husnah tace "Kai dare yayi fa sosai, ke ni fa wllh gwara ma da Allah ya hanaki xuwa nace maki, don da ban san ya xan yi da ke ba a wajen ga uban daren da muka yi, cabb to wa ma xai saurareki, gaskiya birthday din nan yayi armashi, ai da naga daren yayi sosai shine na fasa komawa hostel kawai muka kama daki a nan ni da Surayya, ita Naf fa sai yau da safe ta xo nan ta same mu" Nihad ta kyabe baki ta ajiye handbag dinta tace "I am jet hungry banyi breakfast ba, me suke siyarwa a nan?" Husnah tace "Ke bamu dade da waya da Ayman ba xai taho mana da abinci yanxu, bari in kirasa ince plate uku xai kawo, shi ma jiya ya dawo daga Egypt" Daga haka Husnah ta kirasa ta sanar masa ya dado wani plate din, bayan ta ajiye wayar tana kallon Nihad tace "Amma jiyan me ya hanaki xuwa don Allah?" Nihad ta sauke wani ajiyar xuciya irin na takaici tace "Husnah in gaya maki wani sabon driver Abba ya dauka, kin san ai ya bude ma Habibu Shago" Husnah ta gwalo ido tace "Don Allah, kina nufin yanxu babu Habibu? Allah sarki, kai amma xaki yi kewan Habibu, sau da yawa fa da shi kike hada baki, gashi duk inda kika ce ya kai ki kai tsaye yake kai ki, har ma ya jira ki" Nihad ta marairaice tace "Ke dai bari, ai ni aka yi ma da Habibu ya bar driving, sau nawa yake kai ni Tahir ko Bristol or prince hotel, kuma ya jirani komin dadewar da xa mu yi, sau nawa xa mu fita in amshi mota a hannunsa shi ya tafi harkar gabansa nima inyi tafiyata, sai na gama xan kirasa mu hadu a busstop mu koma gida, Yawanci ba shi nake aika ya siyo min duk abinda nake bukata ba, ai har kuka sai da nayi da naji Abba ya bude masa shago, Habibu ai mutum ne" Husnah tace "Amma fa ya ci kudinki ba karya" Nihad tace "I wish Allah xai ta6a xuciyar Abba ya dawo mana da Habibu kawai" Husnah tace "Toh shi sabon da aka dauka fa?" Nihad ta gyara xama tace "Ai shi xan baki labari yanxu, wato wani tatattcen d'an iska, mara kunya Abba ya dauko mana as driver Husnah, kinsan jiya a kansa sai da Mumy ta mareni har sau biyu a titi cikin jama'a? Husnah as i am talking to u now i am boiling inside, tun shekaranjiya nake cikin ɓacin rai da bakin cikin mutumin nan, daga fara aiki shekaranjiya har ya raina ni baya girmama ni, ina masa magana sai yayi min banxa ko kuma ya kalle wanda ke kusa da shi irin dai kamar ba da shi nake ba da na kusa da shi nake, ko kuma ya kara min sheggun kunnuwansa gaba, irin dai na raini da tantiranci, Husnah yayi mugun raina ni wllh, yanxu maganar da nake maki motar ya Farooq Umma ta bani makulli na fito da shi, baxan juri xama a mota ni da shi yana driving dina ba...." Tuni har hawaye ya cika idonta, Husnah dake ta sauraronta da mugun mamaki ta gyara xama tace "What?? Shi ordinary driver din yake duk wannan abinda kika lissafo min kuma kika kyalesa? Ta yaya kika basa wannan fuskar ya rainaki daga fara aikinsa Nihad? Waye shi haka, kuma a ina Abba ya samo sa?? Wai ma garin yaya kika yi creating room for this bullshit" Nihad na shessheka tace "Baxa ki gane ba, wllh irin yan iskan nan ne yaron, cikin ruwan sanyi yake raininsa da rashin mutunci, idan kin gansa ma xa kiyi xaton baya magana nan ko katon ɗan iska ne, yanda fa kika san motarsa haka yake jin kansa daga fara aiki" Husnah ta rike ha6a tace "Tabdi... to kuwa xa mu yi maganinsa, but what did Abba say about it? Ko baki kai kararsa ba har yanxu?" Nihad tace "Babu wani action da Abba ya dauka tunda Mumy ta zuzzuga sa, har Umma ma ta saka baki amma Abba yaki daukan kwakkwaran action, the painful part of it is that Mumy supporting dinsa take kamar ta ta6a saninsa, kinsan yanda take abubuwanta dai, to wllh a kansa ta gaggaura min mari jiya a tsakiyar Hotoro dalilin da yasa na fasa xuwa Tahir palace kenan, to wannan ne har xan dinga basa kudi yana kai ni duk inda nake so ba tare da yayi casting dina ba wataran? Ina ai baxai yiwu ba, bana harka da fitsararrun yara ni...." Husnah tace "Calm down besty, shi karamin kwaro ne wllh, kuma xa mu yi maganinsa, Clique dinmu kadai mun ishesa" Naf dake ta sauraronsu ta kyabe baki tace "Lallai wnn ɗan iska ne number 1, daga wani kauyen aka samo maku shi halan? Shi a yan kauyen ma shege ne fa" Nihad tace "How will i even know, wlh d'an rainin wayo ne na karshe, gashi baya wani magana nake gaya maku, yanda kuka san kurma, cikin ruwan sanyi yake rashin mutunci da raini, ga wani ji da kai, to kana aiki karkashin mutane kana driving ina wani ji da kai??" Kwankwasa kofar aka yi, Husnah tace "Ayman is here..." Naf ta nufi kofar ta bude, wani matashi ya shigo dakin rike da takeaway uku with many drinks da bottle water, Ya ajiye ledan yana kallon Nihad yace "Manyan mata, ashe dai kina kasar nan Nihad?" Nihad tace "To an zuga Abbana ya ki kai ni UK karatu ba dole a gan ni a kasar ba" Dariya yayi yace "Gaskiya ne, to ya kwana da yawa, kinsan ku manya ne ba kowa ku ke replying ma chat ba both WhatsApp and IG" Nihad tace "Not at all" Husnah ta mike ta dauko takeaway daya ta ajiye ma Nihad, Ayman na kallon Husnah yace "I think bari in kama wani dakin kawai" Husnah tace "Ohk then" Daga haka ya fita daga dakin, Naf ta ja tsaki tace "Sai shegen girman kai, wato jira yake in fara masa magana ko" Husnah tace "Ke dai kowa sai kice yana da girman kai bayan kema kina fama da naki, duk fa Salman ne ya hura maki kunne ki daina kula kowa sai ki dinga fakewa da ana maki girman kai" Naf tace "Ni fita ma xan xo in yi yanxu, amma xan dawo later" Husnah tace "Ina xa ki? Baxa ki ci abincin ba?" Tace "Idan na dawo xan ci" Husnah tace "Kar fa ki ki dawowa Naf, saboda ke naki gayyato Zully nan fa" Naf tace "Ke wllh xan dawo, wani Alhaji ne ke ta damuna da kira ya shigo kano, to yayi min alkawarin waya dama, shine xan je" Husnah tace "Ahh, to maza ki je, Allah ya sa mu ga latest iphone" Naf ta dau figigin gyalenta tace "Toh Allah ya sa bari in je, Nihad idan na dawo xa mu tsara yanda xa ayi da ɗan kauyen can shi kuma" Nihad tace "Toh sai kin dawo" Daga haka Naf ta fita daga dakin, Husnah tace "Tabdi, yau ni naga karfin hali wai barawo da sallama, wannan idan yayi wata daya a gidan ai sai dai kuma ya koma rayuwa cikin main building ya bar boys quarters kawai" Nihad tace "Sai yanzu rashin barina in xauna a hostel da Mumy tayi ke kara damuna sosai, kinsan da na hakura amma tun da aka kawo wannan drivern damuwan ya dawo sabo" Husnah tace "To ko xaki kara gwada yi ma Abba magana?" Nihad tace "Babu yanda Umma bata yi da shi ba, amma da yake Mumy da ya farooq sun hure masa kunne ya ki amincewa, sae dae kawai yayi ta bani hakuri wai there is time for everything" Husnah tace "Gaskiya in har ba sallaman driver din nan aka yi ba xaki takura sosai, gashi Abba baxai baki mota ba ko" Nihad tace "Ba fa ruwan Abba, Mumy ce matsalar gidan nan sae yaya Farooq, amma ae Umma tayi kokarin ganin an bani motar kwanaki hakan bai yiwu ba" Husnah xata yi magana wayarta ya fara ring, tana dubawa taga Ayman ne, dagawa tayi tace "Ya? Wani room number kake?" Yace "102... Pls Nihad ta bani minti goma mu yi magana mana" Husnah tace "Ohk over there?" Yace "Yeah" katse wayar tayi tana kallon Nihad tace "Ayman wants to speak to you" Nihad tace "Ohk kin katse wayar kuma" Husnah tace "No, yana room 102" Nihad tace "Ina ga ya sha kwaya, nice xan bi sa dakin??" Husnah tace "C'mon, minti nawa xa kiyi ki fito, he said just 10 mins, behave like the big girl u are mana" Nihad tace "Look, ya bar ni ma inji da damuwata i don't have that strength to talk" Husnah tace "Don Allah kiyi hakuri ki je Nihad, minti goman nayi ko bai gama magana ba ki fito kawai, ko albarkacina ya ci mana, yana ganin idan na gaya maki xaki ji shi yasa ya biyo ta wajena, ki je ki dawo ki ji yanda xa mu yi da wancan ɗan kauyen shi kuma" Nihad ta d'an kyabe baki, sai kuma ta mike tana gyara veil din abayanta tace "Wani room ma kika ce?" Husnah ta gaya mata, daga nan ta fita xuwa dakin. Kwankwasa kofar dakin tayi, sai gashi ya bude yana kallonta da murmushi fuskarsa yace "Welcome Nihad" gefensa ta bi ta shiga dakin ta xauna saman one seater dake dakin tana kallonsa har ya dawo ya xauna gefen gado sannan tace "I am all ears" shiru yayi yana kallonta, ta langwabar da kai tace "Kayi shiru" Ɗan murmushi yayi yace "Donno where to start from, kinsan kina da wani kwarjini na daban Nihad" Ta kalli agogon dake wrist dinta, sannan tace "Then just start from d end" Dariya yayi sannan yace "Ohk, a takaice kawai ina son ki bani dama let date" Tace "Sorry but i don't double date Ayman" Yace "What's d big deal about double dating Nihad?" Ta girgiza kai tace "Tsari na kenan, i have my boyfriend, and yana sona kamar yanda nima nake son sa, so what's d need of dating else where?" Shiru Ayman yayi, can ya mike ya koma kan kujerar da take ya xauna a hannun kujeran xai kama hannunta ta fixge ta matsa gefe sannan tace "I am sorry Ayman, ina da saurayina kuma duk kun sani" Yayi kasa da murya yace "Yeah i know, but pls Nihad... even if it's once a while, i will always provide u with all ur needs, i am not talking about petty needs" Da mamaki tace "What's that u are talking about?" The way he was looking at her directly in the eyes yasa ta mike tana kallonsa da kyau tace "Seems Husnah bata ta6a baka labarina ba ko?? Kawai kana ganin mu tare, duk inda take xaka gan ni, Ohk get this Ayman, my obstinacy have limit, it hasn't attain to this extent, sorry" Daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin ta kullo masa kofar. Tana komawa wajen Husnah, Husnah ta katse wayar da take ta ajiye, Nihad tace "Baki ta6a gaya ma Ayman wacece ni ba ko?" Husnah bata ce mata komai ba, Nihad ta nemi waje ta xauna, Husnah tace "Toh wai meye a ciki, kawai kin bi kin makale ma Aliyu da definitely kinsan yana da yan mata iri iri shi ma, ni wllh Aliyun nan haushi yake bani, ga shegen ji da kai kamar ɗan jinin sarauta, duk abinda ya daura ki a kai shi kike yi, ga samari iri iri ko wanne na sonki amma kince ke sai Aliyu, to Aliyun me" Nan da nan Nihad ta hade rai tana kallon Husnah, can ta ja tsaki ta dau jakarta ta mike ta nufi kofa, Husnah tace "Tun da an ta6a numfashin ki ba dole ki nufi kofa ba, to baxa ki tsaya ki ji yanda xa mu yi da sabon drivern naku ba" Ko sauraronta Nihad bata yi ba har ta fice daga dakin, Husnah ta ta6e baki tace "Kawai ki makale ma mutumin da yan mata ke rububi a kansa, ki dauki son duniya ki dora masa, shi kuma yayi ta yin kamar bai san kina yi ba, da ma yana baki lokacinsa yanda ya kamata ne abun baxai dameni ba" Husnah ta ja tsaki ta jawo abincin gabanta ta bude.....
Contact me directly via👇🏻
07087865788 WhatsApp only.
7️⃣
💖💖 *NIHAAD*💖💖
By _Khaleesat Haiydar_✍🏻
~~~~~~~
Sai bayan la'asar Nihad ta iso gida, bayan ta fito daga wajen Husnah school kawai ta wuce tayi attending lectures daya, mai gadi na bude gate ta shiga gidan ba tare da ta saurari gaisheta da yake ba, tayi parking dai dai inda motar take ta kashe, sauka tayi ta kulle motar tana kallon inda mai gadin ke xama ko xata ga Khalil, ai ko yana xaune, ko da wasa bai kalli inda take ba, sai ma danna torchlight phone dake hannunsa da yake with full concentration, nan da nan taji har ranta ya fara baci, wai wa yayi ma wannan mutumin hanyar xuwa neman aiki a gidansu? har ta juya xata wuce ciki sai kuma ta dawo, fuskarta daure ta nufesu, Mai gadi na ganin ta doso inda suke ya mike daga xaunen da yake yana gaisheta, Babu yabo babu fallasa ta amsa sannan tace "Aminu kuna canza ma tsuntsaye na abinci da ruwa kuwa??" Yace "Ehh Hajiya ko daxu da kaina naje wajen na basu abinci da ruwan" Mai gadi ne ke mata magana amma banda hararan khalil babu abinda take with hatred, how dare him baxai gaisheta ba ma, wani dogon tsaki ta ja tace "Aminu ka sameni wajen tsuntsayen" Daga haka ta wuce fuuu xuwa bayan gidan inda cage din birds din nata suke, Aminu ya kalli khalil sannan ya bi bayanta da sauri, sai a snn Khalil ya daga kai ya bi su da kallo, suna isa wajen tsuntsayen tace "Aminu in tambayeka mana" Yayi kasa da kai yace "Toh Hajiya" Tace "Wai waye ya kawo wancan yaron gidan nan da sunan ya nemi aikin driving?" Aminu yace "Hajiya Habibu ne ya kawosa ae" Da mamaki tace "Habibu??? Habibu dai?" Aminu yace "Kwarai Hajiya" Juyawa tayi ta wuce ta bar sa tsaye a wajen, gida ta shige, Aminu ya dawo bakin gate ya xauna yana kallon khalil dake kallonsa shi ma, yayi kasa da murya yace "Wai tambaya take wa ya kawoka, to ban san ko na kwabsa ba da nace Habibu, kasan fa Habibu mutuminta ne, har makudan kudi tana basa, to duk inda xata kai tsaye yake kai ta har ya jirata, ya sha gaya min maganganu amma yace kar in gaya ma kowa" Khalil yace "Wani magana?" Aminu ya gyara xama yace "Ae otal daddaya ne a garin nan da wajen shakatawa irin ta manya bai ta6a ajiyeta ba... Kai duk dai wani otal dake kano da ya amsa sunansa otal xuwa take, wani lkcn tun safe sae dare xae je ya daukota, Khalil dake ta kallonsa da mamaki yace "Hotel?? Me ke kai ta can?" Aminu yace "Ahaf ka ji ka da wani xance, me ake zuwa yi otal, kuma kaf babu wanda ya sani a gidan nan sae Habibu sae kuma ni da yake gaya ma, kai wani lkcn har Habuja tana xuwa kuma ta dawo a ranan, kasan sha'anin jirgi, peee ta tafi peee ta dawo ita da kawayenta, babu wanda xae sani, duk kowa tunaninsa tana makaranta, ita ce Kaduna, Ita ce legas, patacot.....kai manyan garuruwan kasar nan dai da ka sani babu inda yarinyar nan bata xuwa, babu abinda Habibu bai sani ba game da ita ai, ina ga shi yasa taji haushin barin dreba da yayi" Khalil dai yayi shiru, Mai gadi yace "Atoh ni kallonta kawai nake kyar" Khalil yace "Allah ya kiyaye" Mai gadi yace "Ameen dae" Nihad na shiga bedroom dinta ta ajiye jakarta da mayafi ta dau wayarta tayi dialing number Habibu, yana fara ringing ta nemi gefen gado ta xauna babu bata lkci ya daga hade da sallama yace "Hajjaju Hajjaju ina yini" Tace "Lafiya lau Habibu" Yace "Ya kwana biyu kuma?" Tace "Lafiya lau, Kana ji na?" Yace "Ina ji Hajiya" Tace "Wannan drivern da ka kawo ma Abba, a ina ka san sa?" Habibu yace "Wani abu ya faru ne Hajiya?" Tace "Tambayarka nake kana tambayata" Yace "Ehh Hajiya na san sa, d'an uwa na ne, garinmu daya" Nihad tace "Bana son karya ta ina ya xama ɗan uwanka kana baƙi yana fari??" Habibu yace "Ayya Hajiya ai in dai ka fito kauye daya da mutum ku ka shigo maraya dan uwanka xaka kirasa, haka abun yake ki tambayi kowa ma" Ta kyabe baki tace "Toh abu daya nake so da kai yanxu" Yace "Toh ina ji Hajiya"
Showing 18001 words to 21000 words out of 37658 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7 Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13