"Shi ma din sai an dinga basa abincin a nan? Waye yace haka?" Daga mai aiki har mai gadin suka yi shiru, tace "Ohh kawai ku kuka tsara hakan sbda ku ke siyan kayan abinci?? To Abba bai ce haka ba, ni ma kuma bance ba, saboda haka ajiye abincin nan dake hannunki baxa a kai ba, kai kuma Aminu ka kama gabanka, ba shi da portion din abinci a gidan nan" juyawa Aminu yayi ya bar wajen a sanyaye, Hafsah ta nemi plate ta rufe abincin ita ma a sanyaye, tsaki Nihad tayi ta dau plate ta debi abinda xata deba ta cika nama sannan ta fita, tana fita Nihal ta shigo kitchen din ita ma xata xuba abinci, ganin wanda Hafsah ta rufe tace "Hafsah wannan wa ya ci ya rage?" Hafsah dake wanke wanke tace "Aa ban dade da xubawa ba, Aminu ne ya xo amsar ma sabon dreba abinci Aunty Nihad ta hana" Nihal tayi shiru da mamaki, can tace "To saboda me?" Hafsah tace "Nima ban sani ba wllh" Nihal ta buɗe abincin tana kallo, can ta rufe ta kalli Hafsah tace "Ki kai masa" Hafsah ta xaro ido tace "Ta fa hana Aunty Nihal" Nihal bata kuma cewa komai ba ta dau spoon ta daura saman abincin ta fita daga kitchen, xaune ta tadda Khalil bakin gate da mai gadin, mai gadin ya dauko masa wani guntun bread dake ta ajiye dakinsa da pure water ya basa, kallonta suke gaba daya, shi dai Khalil yana kokarin gane wacece, don kamarsu ta ɓaci da Nihad, sai da ta karaso ya gane ba Nihad bace don Nihad ta fi ta haske har ma da tsayin hanci, amma both suna da dimple, ta mika masa abincin tace "Ga abincin" Amsa yayi ya d'an yi murmushi wanda iyakarsa Lips yace "Nagode" Juyawa tayi ta koma ciki, Mai gadi yace "Kaga er albarka, muna ganin abubuwan al'ajabi fa a gidan nan, halaye iri iri in gaya maka, kaga Nihal din nan da kake gani, ko kadan bata yi halin uwarta Hajiya ba, yarinya ce nutsatssiya ga sanin ya kamata, uwa uba ga girmama d'an adam ko da kuwa almajiri ne, ba dai ka ganta da kawaye ba kuma, uwarta kuwa ban ta6a ganin mace mara kirki mara mutunci irinta ba duk nan hakuri muke da ita, gashi bata da aiki sai shige ma matan manya manyan kasar nan, sannan ita kadai ce bata yarda Habibu ya ja ta a mota ba, duk sanda xata fita sai ta bari Alhaji ya fita sannan ta ja mota ita ma, bata dawowa kuma sai dab da magariba motar nan kaga duk yayi butu butu da laka malam, tana dawowa kuma xata sa Habibu ya wanke motar, ita kuma wancan Ja'irar da ta hanaka abinci ban ta6a ganin me kirki irin uwarta ba, wato matar Alhaji ta biyu kenan, ga dai ita ce ta fari gun uwarta, tsakaninsu da Nihal kwana daya tak, shi sa xaka gansu kamar yan biyu, sai kuma Allah ya basu kama daya, komai nasu iri daya ne, to wllh Hajiya Mumy uwar Nihad mace ce me mutunta mutum babu ruwan baiwar Allahn nan da duniya, sai gashi Allah ya hadata da shaidaniyar yarinya, bata da aiki sai na bitar kawaye da rashin daraja ɗan adam, to haka Allah yayi ikonsa a gidan nan, kyansa ace Nihad uwarta Umma, ita kuma Nihal uwarta Mumy kaga dai dai kenan, amma Allah bai tsara hakan ba, ni fa da rana daya aka haifesu sai muce canja su aka yi a asibiti, amma Nihal aka fara haifa er baka da ita washegari aka haifi Nihad ita kuma fara tass, kaga ko ai ba ayi canje ba" Khalil dake kallonsa yana sauraronsa attentively yace "Ita Umman yaranta nawa?" Mai gadi ya gyara xama irin abun nema ya samu din nan, yana kirga su da yatsa yace "Kaga Farouq shine ɗan ta na fari, a Habuja yake aiki, ya kan yi wata biyu ma bai leko gidan nan ba, ba laifi yana da kirki da faram faram da jama'a, shi ma kuma bai yo halin uwarsa ba gaskiya, sai Usman shi kuma kadaran kadahan, shi ba a ma gane alkibilarsa, yana da kirki oho, bashi da kirki oho, atoh a haka na san sa gaskiya, sai Kamila warce tayi aure shekara biyu kenan, wani shegen mai kudi Umman tasan yanda tayi ta hadata da ta aura, sai Nihal sannan autarsu Amina, amma fa ta fi ji da Nihal din don ita ma auta take kiranta, ita wannan Aminar ma mara kunya ce gaskiya amma fa akwai son karatun addini, tana ajin karshe na sakandari, Nihal kuma ABU Zaria take, ita Nihad makarantarta ance yayi Miliyan biyu xuwa uku, haka naji su Saminu ke cewa, Maryam Abatcha naji suka ce sunan makarantar" Khalil yace "Toh ita me xuwa Maryam Abatcha din su nawa ne gun Mamarta" Mai gadi yace "Ai ita ce ta fari, sai kanninta biyu duk maza, Sudess da Fadil" Khalil bai ce komai ba ya bude abincin hannunsa ya dau spoon ya fara ci. Nihad na gama cin abinci ta tafi bangaren Mum dinta, shiryawa ta sameta tana yi hankalinta a d'an tashe, Nihad tace "Mumy me ya faru?" Mumy tace "Yanxu Jamila ta kirani wai kanwar mijinta ta rasu" Nihad ta dafe kirji tace "Kaddai Aunty Salma?" Mumy tace "Ita" Salati Nihad ta saki tace "Allah sarki, Allah ya ji kanta, Mumy in sa Hijab mu je" Mumy tace "Ki sameni a waje, drivern bai fita ba dai ko?" Nihad tace "Mumy kiyi driving din mana ko kuma ni inyi" ko tanka ta Mumy bata yi ba ta dau handbag dinta ta fita, bangaren Umma ta fara shiga ta sanar mata rasuwan, Umma tace "Allah Ubangiji ya ji kanta, in sha Allah idan xaki koma gobe sai mu je muyi gaisuwa mu ma, Allah ya ji kan musulmi" Mumy tace "Ameen, Allah ya kai mu goben" Part din Abba ta nufa, shi ma ta sanar masa rasuwan daga haka ta fita compound, Mai gadi yayi kasa da murya yana ma Khalil magana yace "Yauwa kaga Hajiya Mumyn ita ce uwar Nihad, ina ga fita xata yi" Muryar Mumy suka ji tana cewa "Aminu Drivern ya fita ne?" Mai gadi ya mike da sauri yace "Aa gashi nan Hajiya a kusa da ni" Khalil ya mike ya gaisheta da ladabi, Mumy ta amsa cikin mutuntawa tana kallonsa daga sama har kasa, sai kuma tace "Shi ne Drivern?" Khalil yace "Ni ne Hajiya" Mumy tace "Don Allah xaka ajiye ni nan Hotoro ne idan ba damuwa" yace "Toh Hajiya" Makullin motarta ta mika masa, ya amsa da ladabi Aminu ya nuna masa motar Mumy, gun motar ya nufa, Mumy ta daga wayarta dake ringing ta kai kunne, Nihad ce ta fito ita ma sanye da Hijab har kasa, tana ganinsa cikin motar Mumy ta wani daure fuska, bayan yayi warming motar ya karaso da motar har inda Mumy take ya tsaya, Mumy ta bude bayan motar ta shiga, Nihad ma ta bude baya xata shiga mumy tace "Baxa ki xauna a gaba ba" Without looking at her mum tace "No, i will be more comfortable at the back" Kulle motar tayi ta bude handbag dinta ta ciro tsadadden shade dinta ta saka, Khalil ya ja motar Mai gadi na daga masu hannu har suka fita compound din ya kulle gate, cike da nutsuwa Khalil ke driving din xuwa hotoro da Mumy tace daga Nasarawa GRA. Suna isa dai dai family house din mijin kanwarta Jamila ta sa yayi parking, Mumy ta fara sauka daga motar tana kallonsa tace "Ko xaka je ka dawo xuwa bayan magrib ka daukemu, kar a bar ka kayi ta jira a nan" Yace "Aa babu komai xan jira daga can tsallaken in sha Allah" Jin haka Mumy tace "Toh shkkn" Daga haka ta juya ta shiga gidan rasuwar Nihad na biye da ita a baya. Nihad bata yarda ta xauna cikin jama'a da suka fara taruwa gidan ba ana koke koke, ta nemi waje at the far end of the compound ta inda generator din gidan yake ta xauna ita daya a wajen, Iphone dinta ta ciro a jakarta, taga missed calls din Husnah da Naf, da sauri tayi dialing Number Husnah, yana fara ring Husnah ta daga tace "Ina kika shiga ne babe" Nihad tace "Wllh mun fita tare da Abba ne, and i left my phone at home, what's up kun fitan ne?" Husnah tace "Tun yaushe, ke in gaya maki akwai labari wllh" Nihad tace "Yanxu dai kuna ina?" Husnah tace "Tahir guest palace, kiyi kokari ki taho yanxu kar ayi ba ke" Nihad tace "Husnah Hijab fa ne a jikina, mun xo wani gaisuwa da Mumy a hotoro" Naf ta amshe wayar don a handsfree Husnah ta sa, tace "Haba dai minti nawa kin shiga boutique Nihad" Nihad tace "Toh shkkn bari in amshi makullin motar Mumy a hannun driver in taho kawai, nasan before magrib xata koma gida kafin nan na dawo" Naf tace "Shkkn xa mu jira ki a Tahir din be fast pls" Katse wayar Nihad tayi tana bin compound din da ido trying to figure out where her mum is, har ta kare xaga tsakar gidan da idanuwanta bata ga mumy ba alamar dai ta shiga cikin gidan, tashi tayi da sauri ta nufi gate ta bude ta fita, nan ma ta dinga waige waigen inda xata hango drivern, tun da ta fito ya ganta, don yana xaune daga tsallaken bakin titi wajen mai siyar da Fruits, hada ido suka yi ta tsallaka da sauri ta nufesa babu yabo babu fallasa tace "Hey ka bani makullin mota xan mika sako in dawo yanxu" Kallon me siyar da fruits din yayi kamar dai da shi take, nan da nan Nihad ta harxuka cikin tsawa tace "Malam da kai nake fa kake kallon wani" Ya kalleta sai kuma ya kara kunnensa gaba yace "Na'am?" Nihad was soo mad at him, xuciyarta ya dinga tafarfasa ta rasa abun ce masa, shi ma kuma bai kuma cewa komai ba sae ma dauke kansa da yayi, ruwan da ta gani cikin roba gun me siyar da fruits din ta fixgo a fusace ta juye masa gaba daya tun daga saman kansa, duk mutanen dake wajen suka kame a inda suke baki bude suna kallonta da mamaki, Tana huci cikin bacin rai tace "Kai din banzaaa kana driver din gidanmu har xan dinga maka magana kana mayar ni mahaukaciya, who do u think u are?? Waye kai??"
To gain access to the book, contact me directly via👇🏻
07087865788✍🏻
5️⃣💖💖 *NIHAAD* 💖💖
By _Khaleesat Haiydar_✍🏻
~~~~~
Tun da Nihad ta kwara masa ruwan bai dago kansa da ya sunkuyar ba, lkci daya kamanninsa suka sauya, sae kuma dai ya daga kai ya kalleta, Tana hararansa tace "To wllh kaji ka sani, ka rasa aikinka a karkashin mu daga wannan moment din, yau ba sai gobe ba xan sa Abbana ya dau wani sabon driver din ya sallameka, baka yi deserving aiki a gidanmu ba..." Mai fruit din na girgiza kai rai bace yace "Amma baki da mutunci, baki da kirki, baki san darajan da Allah yayi ma d'an Adam ba, kuma uwa uba baki da tarbiya wllh..." Tayi masa wani matsiyacin kallo tace "Kai kuma wa ya sako da kai Malam? Kai a wa xaka sako min bakinka cikin lamarina? Ina ruwanka? Ko xaka tilasta ni in san darajan d'an Adam din ne??" Wani tsaki ta ja tana harararsa, Wani mutumi a wajen ya karbe a fusace yace "Xa ki samu dai dai dake a duniya wllh, ke yanxu irin tarbiyar da aka maki a gidanku kenan? Tir kuwa da tarbiyan gidan nan naku, tir da tarbiyan da iyayenki suka maki, idan haka arxikin ke sa mutane a hanyar halaka Allah ya hanamu..." Nan kowa na wajen yayi mata caaa, ko wanne na gasa mata magana son ransa har da masu xaginta, abun da tayi ya basu mamaki sosai ya kuma ta6a su, barin yanda suka ga khalil yayi shiru yaki ce mata komai, har da masu ce mata arxikin ma sai sun nemesa sun rasa, da surutunsu ya isheta ta ja dogon tsaki tace "Duk ku ji da abinda ya dame ku malamai, bani da ikon hukunta driver din gidanmu aka ce maku, ina ruwanku da abinda na masa banda sa ido irin na mutane" Tana fadin haka ta juya, sai ta kara jin ranta ya wani baci, yanxu ya xata yi da xuwa wajensu Husnah, kwata kwata bata son hawa adaidaita, duk k'uran duniya ya kare ma mutum, kuma ma ai ba girmanta bane taje Tahir guest palace a adaidaita Sahu, bata sake bi ta kan mutanen wajen ba ta tsallaka titi abun ta, bin ta da kallo kawai Khalil ke yi, mutanen wajen sai hakuri suke basa, wani dattijo dake tsaye shi ma wajen a kan idonsa aka yi komai ya dafa khalil cike da jimami yace "Kayi hakuri yaro, rayuwa ce, amma bari in baka shawara wannan aiki ba shine xai kai ka aljanna ba balle ka ji shakkun barinsa, ka ajiye masu makullinsu, da dai wannan axababben walakancin gwara ko dako ne kayi ka ci abinci, balle siffarka bai yi kama da ta rago ba, ga ka namiji har namiji, ka nemi wata sana'ar sai Allah ya dubeka, ni ko duk arxikin duniyar nan xa a tattara min amma a hada min da walakanci to wllh na hakura da arxikin gwara inyi ta xama da talauci na, balle irin wannan walakanci da cin fuskar da yarinyar da aƙalla xaka bata shekaru sha uku ko sha hudu tayi maka a kan titi a bainar nasi babu kunya babu tsoron Allah, sannan babu ladama a tattare da ita, aa gaskiya ka sake duba lamarin nan dai, Allah Ubangiji ya saka maka wannan cin xarafi da cin mutuncin da tayi maka" Wani matashi ne da gidansu ke nan bakin titin ya fito da wata jallabiyarsa yana kallon khalil yace "Ga wannan mu shiga wancan shagon sai ka canxa, Allah ya saka maka abinda tayi maka" Mikewa Khalil yayi ya amshi rigar yana kallon mutumin yace "Nagode sosai" shagon da ya gwada masa ya nufa, duk mutanen wajen suka bi sa da kallo cike da tausayi barin ma da suka ga ya ki cewa komai, ya shiga shagon, me shagon ya basa waje ya canxa kayansa, wayarsa dake aljihunsa ya fara cirowa ya dinga jujjuya wayar kafin ya ajiye gently a saman bench, canxa kayan yayi, me shagon ya taho masa da babban leda don ya linke tasa kayan ya sa a ciki, amsa yayi ya masa godiya sannan ya linke ya saka a ledar yana rike da ledar ya fito shagon, mai shagon ya kalli wayarsa da ya bari kan bench, ya d'an bude ido yana sake kallon wayar sannan ya kalli khalil da har ya wuce, da sauri yace "Malam ka bar wayarka" Dawowa Khalil yayi da sauri ya dau wayar, ya zira a aljihun jallabiyar, yana ɗan murmushi yace "Nagode kwarai" daga haka ya fita me shagon ya bi sa da kallo kamar me naxari. Mumy ce tsaye bakin gate ta dalilin kiranta da aka yi ganin Nihad can tsallake ga jama'a a tsattsaye sun taru an sa ta a tsakiya, Mumy na kallon Nihad tace "Lafiya Nihad, me ke faruwa?" Nihad ta rungume hannunta tace "Mumy ko ba wancan driver din bane, wllh bashi da kunya ko kadan" Mumy tace "Me yayi maki?" Nihad tace "Wai fa Sajida ce tace min tana anguwan nan, dama akwai wani textbook da nake son amsa a wajenta, shine nace ya d'an ajiye ni, can gaba ne ba nisa, shine fa yake gaya min maganar banxa, shi wai baxai je ba" Mumy tace "Sai aka yi yaya?" Nihad na yatsina fuska tace "Shikenan, su kuma wa encan bansan me yasa suka taru haka ba" Mumy tace "Ina drivern?" Nihad ta kalli tsallaken titin ta ga ya fito wani shigo da jallabiya, Kafin ta ce komai Mumy tace "Mu je wajen nasa" Da sauri Nihad tace "Aa Mumy kyalesa kawai, ni ai ban biyesa ba, haka yayi min daxu ma a gidan Baffa, aa kawai dai ki bar sa" Mumy tace "Tsallaka mu je nace, bana son surutu" Nihad tayi shiru ganin Mumy ta tsallaka ta bi bayanta, amma gaba daya she isn't comfortable, Mumy ta nufi driver, yana ganinta yace "Hajiya har kin fito?" Tace "Aa ya sunanka?" Yace "Ibrahim" Tace "Ohk, ya ku ka yi da Nihad?" Gaba daya mutanen wajen kallonsu suke, Nihad dai na tsaye ta ki karasowa ta wani sha kunu, Mumy ta kalleta tace "To karaso mana Nihad" tana tafiya a hankali ta karasa inda suke tsaye da Umma ce baxa ta ji wani shakku ba xata biyo amma Mumy bata da tabbas, Mumy na kallon khalil tace "Ina jin ka" Nihad ta amshe tace "Na fa gaya maki abinda ya faru Mumy, nan nan wajen Sajida xai ajiye ni in amso textbook shine yake min maganar banxa har sa zagina, ni ko biyesa ban yi ba" Mai fruit dake tsaye shi ma ya saki salati yace "Wllh karya take Hajiya, ba haka aka yi ba, ai ina nan a xaune, bokiti guda na ruwa ta dauka ta kwara masa kawai ba laifin tsaye balle na xaune, baki ga ya canxa kaya ba, duk a kan idonmu aka yi komai" Mumy bata bari me fruit ya rufe baki ba ta tsinka ma Nihad mari, Nihad bata gama recover ba ta kuma sauke mata wani, wanda hakan ya ba mutane da yawa dake wajen mamaki, dama ashe ana hukunta 'ya yan masu kudi, hakan ya kuma mugun burgesu, fuska daure Mumy tace "Wuce ki basa hakuri" Nihad da tunda aka haifeta tana jin ba a ta6a marinta ba ta dinga ganin dishi dishi, ta dafe kuncinta, wani tsawa da Mumy tayi mata sai da ya dada hargitsa ta, Mumy tace "Tafi ki basa hakuri nace kar 6allaki a nan" Bata san sanda ta nufesa ba ta tsaya a gabansa hawaye cike idonta cikin rawan murya tace
Showing 12001 words to 15000 words out of 37658 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5 Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13