yace "Haba Dad? Yanxu shi ka aura ma Nihad?" Farooq yace "No Abba, u should have given her a choice, bata yi deserving ayi mata dole ba sbda wannan kaddarar tata, but Abba...." Kasa cewa komai yayi ya koma ya xauna, shi ma ya rasa yanayin da yake ciki, but he don't think it's still bad after all, just dat.... Girgiza kai kawai yayi, Umma tace "Haba Alhaji...." Abba ya mike yana bin kowa da kallo yace "No one have the right to query my authority" Yana fadin haka ya bar masu parlon ya shiga bedroom dinsa, suka dinga kallon kallo a tsakaninsu a parlon, Usman ne ya fara mikewa ya fice daga parlon, Mumy ta mike ta bi bayansa ita ma tana share idonta, Umma ta sauke ajiyar xuciya tana kallon Farooq, ita gaba daya ma kanta fa ya kulle, Abba really took them unaware, jinginar da kanta tayi da kujera Farooq ya mike ya fice daga parlon shi ma. Ana idar da magrib yan kai amarya suka fara shirye shiryen kai ta, Nihad bata ta6a shiga irin tashin hankalin da take ciki ba a wannan moment din, ko video dinta bai tada hankalinta kamar yanxu ba, gashi nobody is there to console her, Nihal na schl, Husnah kuma taki xuwa gidan sbda Farooq, gashi bata da numberta a kai balle ta amshi wayar wani ta kirata, su kamila da Amina tamkar ma farin ciki da abinda ya sameta suke don uban kwalliya suka ci har da kashe dauri Hajiya Zuwaira ce ta kai ta gun Mumy tayi mata fada ta sa mata albarka, sbda takaici da bakin ciki Mumy ta ki cewa komai daga karshe da aka tilastata sae cewa tayi Allah ya tsare, Alhaji Abubakar ne kawai yayi mata fada, Abba kuwa tun da aka idar da magrib ya ki shigowa gidan dama, a haka dai aka tattara ta da akwatunan kayanta uku wanda Umma da Kamila suka hada mata wasu kayayyakinta a ciki, kuka take kamar xata shide, har addu'a ta dinga yi Allah ya dau ranta kafin a karasa da ita gidan, tana ganin an shiga gidan ta kara sautin kukan da take a haka har aka shigar da ita daki, gida ne bungalow madaidaici me dakuna uku, ko wani daki da bandaki, sae bandakin dake parlor sai kitchen, anyi furnishing gidan babu laifi sai dai furnitures din ba masu tsada bane, Nihad ta dinga kuka tana cewa ta shiga uku, masu bata bakin ma har sun gaji sun daina, karfe tara saura suka fara shirin tafiya, Nihad ta rike hannun Kamila cikin kuka tace "Aunty ynxu tafiya xa ku yi ku bar ni, don Allah kar kuyi min haka..." Kamila tayi dariya tace "Ae ko dole xa mu yi maki haka tunda mun kawo ki gidan mijinki kinga ni ynxu sae na koma xan dau jakata inyi driving xuwa gida, kawai kiyi hakuri ki bi mijinki ku xauna lafiya ko hakan xai goge wannan ta6on da kika ma kanki" Daga haka ta fice daga dakin don dama ita ce karshen fita, Nihad ta silalo kasa ta xauna tana kukan takaici, tana jin duk suka fice daga gidan ta daina jin hayaniyar kowa, nan kuma tunanin ta ya tafi gun wanda xata gani a matsayin mijinta, tsoho ne, yaro ne, baki ne, fari ne, kato ne, siriri ne, mummuna ne, kyakkyawa ne, infact duk wannan tunanin ne suka baibaye ranta gabanta ya dinga faduwa hankalinta ya kara tashi, daga karshe ma daina kukan tayi banda bugawa babu abinda xuciyarta yake, ta fi minti ashirin a haka taji an bude gate, da sauri ta mike ta tafi gun window ta bude labule amma sai taga ba ta nan gate din ma yake ba balle taga me shigowa, komawa tayi ta xauna can karshen gado tana jin yanda kirjinta ke heaving, to waye wannan da ko mota ba shi da, bayan wasu mintuna taji an shigo parlor, daga karshe ta ji kamar an bude wani daki an shiga, mikewa tayi ta jingina da window with so much fear, har ta gaji da tsayuwa bata ga alamar xa a shigo dakin ba, komawa tayi ta xauna gefen gado, a kan idonta karfe sha daya tayi, bacci take ji amma taki kwanciya sbda fargaba, kafin sha biyu bacci barawo ya saceta. Ba ita ta bude ido ba sae da hasken rana ya sauka saman fuskarta washegari da safe, a firgice ta mike xaune, sae kuma ta sauka daga saman gadon ta shige bandaki da sauri, bayan ta idar da sallah ta mike a hankali ta nufi kofar dakin ta bude ta fita xuwa parlor, ta dinga bin ko ina da kallo xuciyarta na bugawa, kofar da take tunanin kitchen ne ta nufa ta bude kofar a hankali, wani kara ta saki ba tare da ta shirya ba ganin mutum a tsaye yayi backing kofar kitchen din ga ruwa ya daura saman gas, juyowa yayi suka yi ido hudu da ita, wani irin shock ne ya bayyana a fuskarta ta dinga komawa baya tana kallonsa bakinta ya kasa furta komai, can ta nunasa da yatsa nan ma words suka yi failing dinta, juyawa yayi ya kashe gas din don ruwan ya fara tafasa ya juye cikin mug sannan ya bi gefenta ya fice daga kitchen din ba tare da ya sake kallonta ba, makalkalewa tayi jikin kofa jikinta na 6ari tana ganin abun kamar a mafarki, sae a sannan bakinta ya bude ta fasa wani raxanannen ihu, sai kuma ta fara ganin kitchen din na juya mata lkci daya ta sulale kasa....




_8 months earlier_


Contact me directly via👇🏻 to gain access to the book

07087865788 ✍🏻

3
💖💖 NIHAAD💖💖




By _Khaleesat Haiydar_✍🏻



~~~


Gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga sauran membobi yan gurmin Khaleesats Palace, don gurminsu ya hana in saka sunansu jiya inga ta tsiya, Su Hajiya Aisha Bela, Hajiya Suwaiba, Hajiya Safiyya Usman😂 Hajiya Mardiyya mandy rice😜, Hajiya Sadiya uwar Hanan, Uwar Sa'eed, Hajiya Farida me kayan en gayu, Amzaj, Hajiya Zaarah, Wata ana ce mata me kayi nayi, Hajiya Aisha Macika, Hajiya Billy, Uwar Habee, har dai da wata me gawayin dare, duk na gaisheku kyauta... Sauran da basu ga sunansu ba a tsakiyar rubutu xa su gani😁



8months earlier...



Zaune yake saman farar kujera dake kusa da dakin mai gadi, ya fi awa daya xaune wajen, lkci lkci yake goge zufan fuskarsa da handkerchief din hannunsa, karamar waya ya fiddo aljihunsa yana duba agogo dake nuni da karfe biyar da rabi, ya juya ya kalli mai gadi dake xaune gefensa da radionsa a hannu, xai yi magana aka danna horn, da sauri mai gadin ya ajiye radion ya mike ya isa bakin gate din gidan ya bude, wata rantsantsiyar mota ce ta shigo compound din, mutumin dake xaune ya bi motar da ido har ta isa kantamemen space da aka tanadar don parking a compound din, mai gadin ya dawo bayan ya maida gate din ya rufe yace "Bari in sanar masa kana ta jira kar ya shige ciki kuma" Daga haka ya nufi parking lot din ya jira har dattijon dake cikin motar ya sauko yana gyara babban rigar jikinsa, da ladabi me gadin ya risina yace "Barka da isowa Alhaji" Alhaji Ibrahim yace "Yauwa Aminu... " Mai gadin yace "Alhaji dama Habibu ya taho da baƙon tun daxu, shi har ya ma tafi yace yau xai koma, baƙon kuma gashi can yana jiranka tun karfe biyu" Alhaji Ibrahim ya kulle motar tasa yace "Ohk, to ya karaso" Mai gadi ya koma gun mutumin dake xaune saman farar kujera da sauri yace "Kaje nayi masa magana" Tashi mutumin yayi ya nufi parking space din, yana isa ya duka har kasa yana kallon Alhaji Ibrahim yace "Barka da yamma Alhaji" Alhaji Ibrahim na kallonsa yace "Yauwa kai ne wanda Habibun ya kawo kenan?" Mutumin yace "Eh ni ne" Alhaji yace "Ya sunanka?" Mutumin ya sauke idonsa daga kallonsa yace "Sunana Ibrahim" Alhaji Ibrahim ya jinjina kai yace "To madallah, amma ya ku ke da Habibun?" Mutumin yace "Garinmu daya da shi, ga gidanmu ga gidansu, babana aminin mahaifinsa ne" Alhaji Ibrahim yace "To ba laifi, ai har garin naku naje watanni da suka wuce" Shi dai mutumin bai ce komai ba, Alhaji Ibrahim yace "Shkkn babu damuwa, amma kayi karatu ne?" Mutumin ya girgiza kai yace "Aa iyakata sakandari, shi ma ban zana waec ba" Alhaji Ibrahim ya daga kafada yace "Ohk, xuwa kake ganin xaka dinga yi kullum ko kuma yaya tsarin naka yake?" yayi kasa da kai yace "Duk yanda ka tsara haka xa ayi Alhaji" Alhaji Ibrahim yace "Kaje dai gobe da safe ka dawo, ni yanxu xan shiga ciki in huta ne, dawowata daga aiki kenan..." yace "Toh nagode kwarai Alhaji, Allah ya kara girma" Tuni Alhaji Ibrahim ya nufi main entrance din shiga gidan nasa, ya mike ya bi sa da kallo, sannan ya kalli building din gidan wanda duplex ce gari guda, juyawa yayi ya koma gun mai gadi, mai gadin na ganinsa yace "Ya ake ciki?" yace "Yace in dawo da safe" Mai gadi yace "Ahaf ai ka ma samu, tunda ta hannun Habibu ka biyo, ai Alhaji sun fi shekara goma sha biyar da Habibu, har kauyensu ya je daurin aurensa kwanaki, in dai baka da rawan kai sannan uwa uba ace kana da nutsuwa gun aikinka to wllh tuni Alhaji xai ja ka jiki ka xama kamar d'an gida, ba ga mu ba duk mun dawo kamar yan gidan banda dai ba halinsu daya da wasu daga ahalin gidan nasa ba, to ya sunan naka?" Mutumin yace "Sunana Ibrahim" Mai gadi ya rufe baki yace "Yo ai sunan Alhajin kenan" yace "Allah sarki, Sai goben in sha Allah, xan tafi ynxu" Mai gadi yace "Allah ya kai mu" Gate ya nufa ya fita daga gidan. Alhaji Ibrahim ne xaune parlonsa, daga gefensa matarsa kuma amaryarsa Hajiya Maryam, Wasu yan mata ne biyu xaune daga kasa saman lallausan carpet dake malale parlon, Hajiya Maryam tace "Ayi hakuri Alhaji in sha Allah hakan ma baxai sake faruwa ba, ita ma Hajiya nasan bata fahimce su bane, amma xa su je su bata hakuri" Alhaji Ibrahim na kallon yan matan yace "Ku tashi ku bani waje" Duk a tare suka ce kayi hakuri Abba, yace "Ku fita nace..." Mikewa suka yi a tare suka fita daga parlon, daya daga cikin yan matan tace "Gaskiya ni ki daina ja min Nihad, ko me kika yi sai a hada mu a mana fada, da na sani da ban biki ba jiya, haba don Allah" Tsaki er uwar tayi mata ta bi wani corridor tayi gaba abunta irin ko damunta abun bai yi ba. Wata mata ce da baxata haura hamsin da bakwai ba xaune wani lafiyayyen parlor da ba a cika da kaya masu hayaniya ba, cike da ɓacin rai tace "Toh banda ma fitina da neman magana irin naku dole ne sai kun je? Me yasa baxa ku xauna inda Allah ya ijiye ku ba, maganinku kenan" Nihad tace "Ae wllh daga yau ko Abban ne yace mu je ni dai sai dai in fita inyi using opportunity din in xaga gari in sha iska in dawo abu na, i don't care... baxan sake xuwa ba gaskiya" tana kai wa nan ta mike ta dau wayarta dake caji ta fita daga parlon, Hajiya Sumayyah tace "Atoh dai, da ya fi maku, don dama magana ta ce kawai bakwa ji banda haka na hanaku xuwa tun ba yau ba" Ita dai er uwar Nihad na kwance saman kujera bata ce komai ba, Hajiya Sumayyah ta bude kofar bedroom dinta ta shiga ta kulle. Washegari asabar kasancewar yan matan gidan basu da lectures duk suka yi shirin tafiya islamiyya amma banda Nihad dake kwance parlon step mum dinta tana aikin danna waya, Hajiya Sumayyah da suke kira da Umma da tace "Ke Nihad kina kallon lkci kuwa, ko baxa ki islamiyyan bane yau ma?" Nihad tace "Umma sai gobe i have something important to do" Umma tace "To ita Nihal ma cewa tayi ba xata ba?" Bata rufe baki ba sai ga Nihal ta shigo har ta gama shiryawa, Umma ta kalli Nihad bata dae ce komai ba ta ci gaba da abinda take, Nihal tace "Hope u are been cautious of time Nihad?" Tashi Nihad tayi ta fita daga parlon tana cewa "Ni sai gobe" Mai gadi ne tsaye tare da mutumin da ya xo jiya, bayan sun gaisa mai gadin yace "Yanxu xaka ga Alhajin ya fito xai tafi gun motsa jiki, don ma yau bai fito da wuri ba, amma dai bari in sanar masu a ciki kar kuma ka yi ta jira haka babu dadi" mutumin yace "To nagode" Xaunawa yayi kan farar kujera yana bin compound din da kallo don ya kayatu da kyawawan shukoki na flowers har ma da artificial flowers, daga can wani gefe wani karamin water fall ne me ban sha'awa ruwa na ta xuba ga artificial crocodiles da kifaye a ciki, ba a dau lkci ba mai gadin ya dawo yace "Ka ga wancan yar barandar?" ya kalli inda yake nuna masa yace "Eh na gani" Mai gadin yace "Toh kaje can kayi jiran alhajin, akwai kujeru ma a wajen" Tashi yayi ya tafi wajen yana bin ko ina da kallo, bayan kujeru masu kyau har da carpet grass malale a kasa daga gefe, ga artificial flowers da ya kawata wajen, ya xauna saman daya daga kujerun wajen surveying everywhere with his eyes, bayan kusan minti sha biyar aka bude kofar parlon, tsaye tayi tana kallonsa daga sama har kasa a bit flabbergasted, ya kalleta yayi kasa da kai yace "Ina kwana" tace "Wa kake nema Malam? Daga ina haka?" Yace "Mai gidan nake jira" ta fi minti daya tana masa kallon sama har kasa, ta ma rasa me xata ce, sai kuma ta sauka kasa xuwa compound din ta tafi gun mai gadi da sauri, yana gaisheta ta ki amsawa tace "Aminu waye wancan aka bar sa xaune a kofar shiga parlor? Waye wannan?" Yace "Ranki shi dade baƙon Alhaji ne wanda Habibu ya kawo jiya, shine sabon...." Ta gwalo ido ta dakatar da shi da sauri tace "Haba Aminu, Haba Aminu, yanxu kai rashin hankalin naka ya kai haka, a tunaninka ya kamata a bar sa yaje har can ya jira Abbanmu, privacy din mu ne can din fa? ga dai kujeru a compound amma har sai yaje balcony kamar xai shiga parlor, a ina aka ta6a haka?" Aminu yayi kasa da murya yace "Wannan gaskiya ne Hajiya, ayi hakuri anyi kuskure kam, ayi hakuri" Tace "To tun wuri ka tafi kace ya dawo nan kusa da kai ya xauna ya jira Abban" Aminu yace "Toh Hajiya" tabe baki tace "Ni dama tambayarka xanyi hope jiya baku mance feeding din tsuntsaye na ba?" Ya washe baki yace "Haba dai Hajiya, ai kullum safe rana da dare sai Saminu ya basu, yau ma da asuba ina kallo yaje ya xuba masu" tace "Yauwa toh nagode, bari in je in duba su, shekaranjiya da jiya duk bama nan ban gansu ba" Yace "Da yake sai dare ku ka dawo jiya din ma" Tace "Eh fa" daga haka ta wuce ta xaga ta inda tsuntsayen suke a backyard din gidan wanda nan dinma duk shuke shuke ne, ta fi minti bakwai tana kallon kyawawan tsadaddun birds din nata ko wani breeds a cage dinsu daban, birds din iri hudu ne ko wanne me kyau har kuma da Aku a ciki, ta tafi gun akun da aka yi Seperating da sauran tace "Hello cutie" The bird was only chirping and flying around the little cage alamar he appreciates seeing her, bayan wani lkci ta bar wajen xata koma cikin gida, tsaye taga Abba a balcony bakon nasa kuma ya sauka daga saman kujera ya durkusa kasa yana sauraren Abba, kallonta kawai Abba yake da mamaki yace "Nihad ke baxa ki islamiyyan bane?" Tayi gathering courage tayi kasa da murya tace "Abba assignment nake typing anjima xan yi submitting via...." Abba ya dakatar da ita yace "Why are u skipping Islamiyya this days Nihad, last week ma na ga baki je ba ko, hakan ba dai dai bane dear" Sunkuyar da kanta tayi bayan few seconds ta dago, kallon mutumin dake kallonsu ita da Abba tayi, ta wani daure fuska wondering why he was looking at them, tana tafiya a hankali ta shiga parlor ta kullo kofar, bayan minti shidda aka sake bude kofar, har sannan Abba na tsaye speaking with the man, su uku ne duk sanye da hijab din islamiyya har kasa, Abba ya kallesu, sai kuma yace "Ke xaki yi driving din?" Tace "Eh Abba ga makullin" Amsa yayi ya mika ma mutumin dake durkushe gabansa yace "Ka ajiyesu a makaranta, xan jira ka har ka dawo" Ya amsa da ladabi yace "Toh Alhaji" shi ya fara sauka Balcony din, Autan Mumyn Nihad da ake kira da Sudais yace "Abba is he our new driver" Abba yace "Yes he is sweetheart" Duk suka yi ma Abbansu sallama suka sauka xuwa parking lot, sai da suka tsaya dai dai motar xuwa makarantarsu sannan drivern ya nufi motar shi ma, bayan ya bude duk suka shiga back seat, ya shiga ya tada motar yana warming, shi dai Abba na tsaye balcony har sannan yana kallonsu, Drivern na warming motar yaji ance "Ina kwana" ya daga kai yana kallonta ta madubi da mamaki, sai kuma yace "Ina kwana" Bayan wasu yan mintuna ya ja motar suka bar gidan xuwa islamiyyan nasu with Fadil and Sudais directing him. Parking yayi bakin gate din islamiyyan, Nihal ta bude motar ta sauka su Fadil ma duk suka sauka, bayan ta kulle motar ta kallesa tace "Sai anjima" Yace "Sai anjima Hajiya" Suka shiga makarantar, reverse yayi ya bar wajen har sannan bai daina mamaki ba. Yana isa gidan bayan mai gadi ya bude masa gate ya shiga yayi parking ya kashe motar ya sauka, gun mai gadin ya nufa ya xauna, Mai gadin yace "Inji ka yi kumallo dai?" Driver yace "Aa" Mai gadin yace "Toh bari
Showing 6001 words to 9000 words out of 37658 words