Wani sassanyar ajiyar xuciya ya sauke kafin ya daga k'iran wanda kiris ya rage ta katse.Bayan 'yan gaishe-gaishe Abba yace"Don Allah sirikina kayi haquri na takuraka da sassafen nan,wlh mahaifiyar Fadima ce take ta k'iranta awaya tun dazu amma bata daga ba,shine ta sanyani agaba akan dole saina k'iraka muji daga gareka koh lafiya? "
Oh! Allah yanxu ya zeyi?yanxu sae yai wa Sirikinsa k'arya agaban 'yarsa?
Wani b'angaren xuciyarsa yace"Toya kuwa ka iya? Ai ya zame maka dole kayi masa k'aryar don kada ka tada hankalinsu musamman na mahaifiyarta.
Ahankali yace"Allah sarki Abba ni na dan fita ne,amma na barota agida tana bacci bata tashi ba,kuma wayarta ah silent take shiyasa kila bata ji ringing din wayar ba,amma na tabbata idan ta tashi xata nemeku da kanta...... "
"Ni kaina nayi tunanin hakan kuma nayi iya bakin k'ok'arina wajen fahimtar da uwar amma taki ta gane,madallah nagode d'ana,ah yini lafiya.... "
Daga haka sukayi sallama.
Abba ya dubi Umma ya kora mata bayani.Tace"Ikon Allah! bacci sae kace baccin mutuwa?koda wayartata ah silent take ai taji vibration..... "
"Idan yana meeting mode kenan ko?don idan akace miki silent toh ai kin san wannan kwata-kwata ba'a jin k'ararsa,meeting mode ce kawai take bada vibration.... "
Shiru tayi masa bata k'ara cewa uffan ba don yanxu dai hankalinta ya d'an kwanta tunda 'yar tata nanan lafiya qalau.
***
"Meyasa zaka masa k'arya? Meyasa baka fad'a masa abinda ke faruwa ba idan yaso ya taho ya raba auran daya daura don kowa mah ya huta da tashin hankali....? "
Cike da mamaki yake kallonta,yace"Yanzu Babyna sae ki rabu dani akan abinda be taka k'ara ya k'arya ba?ina ce kece da bakinki ki fad'a min adaran jiya cewar you promised to withstand any obstacles that will come our way? Kuma kika ce min har kin soma jin sona aranki? Then why are you trying to go back to square one again? Inace mun wuce nan ko?"
Afusace nace"Ai kaine kake kokarin sakani na koma square one din becuz you ain't helping matters at all,kace I shld be strong & bold to face ur family problems,I was trying to do such buh kwata-kwata u were not helping at all,ka tsaya kurum anata zagina har asiri akace nayi muku but u couldn't speak out,u were juz standing and looking kamar wani zararre..... "
"Baby am very sorry,abinda nakeson ki fahimta shine,idan babba yana magana be kamata ka katse masa hanzari ba becuz yin hakan na nufin rashin kunyace akai musu,balle mah Momi sam bata qaunar tana fad'a kaima kana fada,tafi son ace koda kana da gaskiyarka still kayi shiru da bakinka har ta gama kafin ka soma bayaninka,shiyasa ta qara fusata da kika tsoma baki kika katse mata hanzari.......... "
Sae ayanxu na fahimci dalilinsa na kin k'areni alokacin da aketa ci min mutunci,sae kuma naga da gaskiyarsa,be kamata ace na tsoma baki cikin xancen nan da nan ba.Da haka muka k'araso gidan baba Mu'azzam din,xuciyata sae harbawa take da sauri da sauri.
"Babyna relax,cool down & regain back ur confidence..... " ya fadi hakan alokacin da muka fito daga cikin motar.
*
Acikin gidan Baba Mu'azzam kuwa,gidane ya kacame da rigima,ita Momi ruwan bala'i take ta zazzaga wa Baba Mu'azzam,tana yi,ya'yanta mah na tayata,su Afreen kuwa sun k'asa jurewa rashin kunyar dasu Khairat kewa mahaifin nasu,don haka gabaki dayansu ne suka taso suka shiga cikin fadan,gidan sae ya dada kacemewa da hayaniya.Goggo Ladidi kamar tasan za'ai rigima shine tazo da wannan safiyar,donsu Momi anan suka cimmata,hadda ita Goggon Momin ta hada aciki wai sun had'a kai sun munafurceta.
Sae da Kaka rigima ta dauko jibgegiyar dorinarta Sannan kowa ya shiga taitayinsa.Kallon Momi tayi wacce take tsaye sae girgize-girgizen jiki take,fuskar nan tata cike da b'acin rai k'arara.
Kaka rigima tace"Haba Binta da girmanki kike Abu kamar wata yarinya?abinda yara zasuyi kiyi musu fada shine ke kike yinsa da hankalinki da kuma wayonki?Ina wani amfanin tashin hankali anan?abune da idan an xauna toh kuwa tabbas za'a fahimci juna,amma kinzo kin tasa bayin Allah agaba kina haushi kamar kare kin hanasu mah suyi bayani sabida masifarki,wlh Binta ni mamakin wannan bak'on halin naki nake don sam ba haka kike ada ba,don Allah ina rokanki,idan har kinzo ne ki maida min da gida ya zamo filin yaki toh tun wuri ki hanxarta barin gidan nan don bazan tab'a bari ki raba min kan zuri'a ba,idan kuma ta maganar fahimta ce kika zo da ita,toh maza sami wuri ki zauna ayi maganar atsanake,idan kuwa d'ayar ne toh maza ki fuce min daga gani kafin na bud'e idanuwa........ "
Duk iya shegen mutum da kuma bala'insa toh kuwa abayan Kaka rigima yake,ko kadan bata d'aukar kaniya,hakan yasa Momi ta sassauta rigimarta,ta nemi gu ta xauna,adaidai lokacin su Mahmood suka shigo.Su Khairat sae aikawa Fadima da kallon banza suke don babu damar magana,Kaka rigima ta kasa ta tsare.
Ni kuwa kallo daya nayiwa dukkan halittun dake cikin makeken falon,kana nayi saurin sadda kai k'asa sabida wani irin kallon banzar dasu Khairat ke jifana dashi.
Cike da murna su Afreen suka mik'e suka rungumota,"Oyoyo Anty Zahranmu sannu da xuwa.... " haka suka fada ah sa'ilin da suka cikata.Ni kuwa harga Allah naji dadin wannan tarbar tasu,atleast akwai masu sona acikin dangin mijina,kuma hakan da sukayi ze tabbatarwa Momi da cewar idan su sun k'ini,toh kuwa acikin zuri'arsu dakwai masu qaunata don Allah.
Daya bayan d'aya nabi manyan ina gaidasu suna k'arbawa,Momi ce kawai banyi kusa da ita ba don bana son ta min wani wulaqancin.
Kaka rigima ce ta rik'e hab'a tace"Oh! ni Aishatu daga tarewar amarya jiya jiya shine har kin soma saka kafafu kina fita? Koda yake ko kadan banga laifinki ba,uwar mijinki ce ta tasoki agaba da tashin hankali...... "
Ta fadi hakan tare da nuna Momi.Ita kuwa Momin kawar da kai tayi gefe tana meh cike da jin haushin cin mutuncin da tsohuwar take ta mata agaban 'ya'yanta da kuma sirikartata. (Ai! ai kin yadda cewar Fadimar sirikar taki ce?😜)
Wuri na samu akusa dasu Afreen na xauna,shi kuma uban gayyar kusa da Usee ya zauna.Ko'ina yayi tsit ana sauraron bayanin da ze fito daga bakin Baba.
Baba ne yayi gyaran murya ya soma magana ak'aron farko tunda muka shigo"Binta dama ina da niyyar k'iranki kizo ayi magana ta fahimta,sae gashi kinyi saurin ji tunda dama can ai aure ba abin b'oyuwa bane dole ajita daga bakin mutane."
Ya dan dakata,can ya cigaba"zancen kuma wai ita Fadimar budurwar Mubarak ne,shine ni ban san da wannan ba,abinda kawai na sani shine,yaro yazo ya sameni akan cewar yana son na shige masa gaba na nemar masa auranta ba tare da saninki ba,sosae nayi mamaki da jin wannan furucin nasa,ko dana tambayeshi ce min yayi wai don bakya qaunar yarinyar ne,amma bayan auran sae akiraki ah fahimtar dake,toh ni abinda ya saka na amince xan shige masa gaban shine,yarinyar daya samo 'yar babban gidace meh wadatacciyar tarbiya,'yar kuma wani aminina,shiyasa kai tsaye na shige masa gaba don bazanso yayi asarar mace ta gari ba,sau uku ina tambayarsa cewar da fatar sun daidaita kansu shida yarinyar?don bana son asami wata matsala,se yace min eh sun daidaita din,amma ni ban san cewar ita yarinyar budurwar Mubarak bace da banyi gangancin saka kaina cikin wannan al'amarin ba,kai Mahmood anyi hakan ko ba'ayi ba? "
Yayiwa Mahmood wannan tambayar yana meh jiran yaji ta cewarsa,ahankali Mahmood yace"Hakan akayi Baba.... " anan ya kwashe labarin komai tun farkon soma haduwarsa da Fadima akano,xuwa binsu da yayi,k'arban tayin aikin ABU da yayi sabida ya komo kusa da ita,dramar da suke tasha da Mubarak akanta,komai ya fada musu ba tare daya rage gishiri ko kadan ba.
wuri ya rud'e da tofe-tofen albarqacin bakunan mutane,wasu na cewa yaci amana ko kadan be k'yauta ba ayayin da wasu ke cewa haka Allah ya kaddara cewar ita din matarsa ce ba rabon Mubarak bace.
Anan kuwa Baba ya shiga zuba musu nasihu meh ratsa zukatu da kuma nuna musu cewar tun fil'azal haka Allah ya rubuta cewar Fadima ce matar Mahmood ba Mubarak ba,kuma ai ba abin tirr bane tunda akwai aure tsakaninsu.Yayi nasiha sosae wanda har hakan ya sanya Momi xubda makaman yakinta,daga ita har 'ya'yan nata.Hawaye ne keta shatato mata asaman kunci.
Ni kuwa arayuwata babu abinda na tsana illa naga uwa tana xubda hawaye akan danta,babu zato babu tsammani sae kawai gani sukayi na mik'e na nufi wurinta.Tsugunnawa nayi tare da amfani da gefen mayafina na shiga goge mata hawaye ina cewa"No ummana pls don't cry akan abinda danki ya miki,kina da right din da zaki umarceshi daya sakeni idan har bakya son wannan auran...... "
Ban ida gama maganata kawai wani dan marayan kuka ya kufce min,ba tare da wani b'ata lokaci ba,Momi tayi saurin rungumoni tsam! ajikinta.Tace"Yata ba wannan ne ke damuna ayanxu ba,damuwata aynxu shine yadda Mubarak ze k'arbi zancen idan ya dawo,idan ba haka ba ni wlh na k'arbeki hannu bibbiyu amatsayin surukata....... "
Gabana ne ya yanke ya fadi jin ta ambaci sunan 'Mubarak',na manta cewar akwai sauran rigima agaba.Ya salam! Wannan wacce irin sabuwar rayuwace na shiga?
Cikata nayi alokacin dana ji Baba na k'ok'arin magana.
Yace"Fadima kina son Mahmood? "
Kallon shi Mahmood din nayi,naci sa'a kuwa Shima din kallona yake.
"Amsa zaki ban ba cewa nayi ki kalleshi ba,kuma gaskiya zaki fada min karki cuci kanki,idan har bakya sonshi toh ki fito filli ki fada kowa yaji...... "
Mahmood kuwa k'ura mata idanuwa yayi ayayin da xuciyarsa ke harbawa da sauri da sauri,karfa Fadima tace bata sonshi don agaskiya baze iya cigaba da rayuwa idan babu ita akusa dashi ba.
"Eh baba ina sonsa kuma na amince xan zauna dashi har k'arshen rayuwata.... "
Wata sassanyar ajiyar xuciya Mahmood ya sakar tare da yin hamdala acikin xuciyarsa.
Baba ya dan muskuta yace"Alhamdulillah! dama abinda nakeson naji daga gareki kenan,don haka abinda nakeso daku shine kada kowa acikinku ya sake ya k'ira Mubarak ya fesa masa zancen,ku jira har ya dawo,duk ranar daya diro garin nan don Allah Binta ki kirani zanzo na nutsar dashi tare da fahimtar dashi,itama matar tasa ku gargadeta dakyau,karta kuskura ta fada masa...... "
Kowa ya amsa da yaji kuma za'a kiyaye,anan aka shiga nemar gafarar juna,su Khairat suka nemi gafarar Fadima da Mahmood da kuma cousins din nasu.Mahmood ya nemi gafarar mahaifiyarsa Sannan aka soma watsewa.Se da Momi taja Haj.Fa'iza cikin daki,tace mata tasan irin abokan da zata dunga fadawa sirrinta don gashi-gashi abinda Haj.Rabi tace Haj.Nera ta gaya mata.(lol mata kenan da k'ananun magana,ance-ance baya tab'a kare mana😁).
Tayi mamaki kwarai da gaske don Haj.Nera har rantsuwa tayi mata akan babu wanda zeji,ashe sae data je ta karas mah haj. Rabi.Kwafa tayi tace zasu hade da Neran ne.Momi tace "A'ah ki barta kada abu ya zamar muku rigima,nide kawai na gaya miki ne don kisan irin k'awayen da kike tare dasu Sannan ki rage gaya musu komai naki......sae anjima.... "
Ta fice abunta,awaje mah seda ta sake nemar gafarar Fadima,Fadima tace"Haba Momina nifa baki tab'a min komai ba,idan kuwa har kinyi toni na riga na yafe miki tuntuni.... "
Sosae Momi taji dadin zancenta,atake anan taji Fadimar ta sami wani gurbi acikin xuciyarta.
*****
Bayan sun kai gida kuwa,Mahmood ya rasa inda zai saka kansa don murna,yace da Fadima"Babyna ban tab'a tunanin cewar komai zaizo mana da sauki haka ba,na aza ko se anyi yankin duniya ta uku ne kafin komai ya lafa,sae gashi komai yazo mana da sauki,addu'a kenan baya tab'a faduwa akasa,yanzu sauran mana Mubeen,Allah yasa ya fahimcemu.... "
Ahankali na amsa da "Ameen"
Yace"oya yi Maza ki k'irasu Umma amma don Allah na rokeki pls karki sanar dasu komai,ki koyi b'oye sirrin mijinki okay?"
Murmushi nayi nace"Haba! ai duk wata mace meh fallasa sirrin mijinta doluwace kuma da sauranta yasin... "
Light kiss ya sakar min akan leb'ena yace"Thanks matata,I love you my *'Zahmood'*.
Cike da jindadin sunan daya ambato agareni nace"love you too my *'jannah'*................. 📝
2episodes remaining,amma sai next week zaku gansu duka biyun atake don diz week Muna da biki,yanxu haka mah na kokarta nayi muku typing ne don kada kuji shirun yayi yawa.
*{Onward together}*
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*
*WATPADD:HAFNANCY💞*
*IG:Hafsy___mustee*
✨✨✨
*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*
*🌼BABI NA SHA DAYA🌼*
*page 29-30*
Ummata na k'ira wacce muna gama gaisawa ta rufeni da fada,wai dole na ajje wannan baccin safen nan agefe wanda ya riga ya gama bi min jiki,tace idan ban kama jiki na watsar da kiwiya agefe na dunga kula da mijina ba,toh kuwa namiji shi babu ruwansa,idan yaga bakya masa abunda yakeso toh kuwa yana iya banka miki kishiya wacce zata zo ta dunga kula da bukatunsa da kuma tattalinsa,ke kuwa awatsar dake agefe ki koma 'yar kallo.Mun jima tana min nasihu meh ratsa xuciya,daga bisani mukayi sallama.Shima Abbana na k'irashi mun gaisa.Har yake labarta min irin yanayin da Umma ta shiga alokacin da take ta k'ira amma babu amsa.Dariya nayi sosae tare da jin wani irin soyayyar Ummata na ratsa jinin jikina.
Kai tsaye na latso _*My Ashwairiyya*_.
Ita kuwa awannan lokacin ta fito wanka kenan,tana gaban madubi tana taje kanta,so take taje taga dakin Suhaima.Wayarta dake gaban madubi taji ya dauki kida,da hanzari takai hannu ta dauketa.
*'Fateenah'* shine sunan data gani yana rawa akan screen,gabanta ne taji ya bada rasss!.... Jefar da comb din hannunta tayi tare da mik'ewa da sauri har jikinta na dan rawa don tsananin tsoro da kuma fargabar abinda zataji daga sahibar tata.
"Hel....lo... Fateenah'...... " haka ta fada cike da in-inna ah sa'ilin da tayi picking call din.
Bushewa da wani irin dariya nayi don nasan abinda take yiwa wannan rawar muryar,wato atunaninta tsantsar tashin hankali zata tsinta daga gareni shiyasa take cike da tsoro. Allah sarki my Ayush komai yayi chas-chas ahalin yanxu.
Nace"Malama idan zaki daidaita muryarki toh tun wuri mah ki daidaita don ni yanxu babu abinda nakeso sama da mijin da kuka hana min saninsa da wuri sae akurarren lokaci...... "
Kwashe komai nayi na gaya mata tun wucewarsu,tarewata da kuma rigimarmu adaren farko,sae kuma sabuwar rigimarsu Momi da kuma xuwarmu gidan Baba Mu'azzam da kuma nasihunsa agaremu,sae kuma sulhun da aka nema.
Wani wawan ajiyar xuciya Ash ta sauke,cike da murna tace"Wayyyo! Fateenah' ina zan saka kaina don murna? Agaskiya naji dadi ba kadan ba da har kika haqura kika rungumi mijin kaddararki,fateenah wlh believe me Mahmood shine kalarki ba Mubeen ba,wlh ni dama can ina ta miki kwadayin aurensa sae gashi lokaci daya Allah ya amsa addu'ata,ya zamo mallakinki,yanzu dai addu'armu shine Allah yasa Mubarak ya fahimceku ya kuma gane cewar wani baya taba auran matar wani,haka zalika wata bata taba auran mijin wata........ "
Cike da sanyin murya na amsa mata da "ameen." Tace min tana shirin xuwa gidan Suhaima ne,nace yanzu Muna gama waya ita zan kira.Mukayi sallama.
Da sauri na waiga tare da watsa masa wani Irin kallon soyayya,ware min hannayensa yayi.
Ahankali ya furta"Babyna I nid a warm hug...... "
Babu b'ata lokaci na isa gareshi tare da fad'awa jikinsa,sannu ahankali ya maida hannayensa ya rufe yana meh dada kankameni.kunnuwana dake saman k'irjinsa ya sanya nake iya jin yadda xuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri.Ahankali na lumshe idanuwa ina meh jin wani irin sonsa na ratsa jinin jikina.
***
Ash cike da farin ciki ta Latso su Leedar da Fresh take labarta musu zancen Fadimar,suma din sosae sukai murna tare da musu fatar alheri da kuma addu'ar Allah yasa Mubeen ya fahimcesu.
*
Cike da rawar jiki ta mik'e tana fadin" Momi kunnuwana sun kasa gasgata zancen da kike min? Taya za'ai Zahranmu ta rikid'e ta zamo matar Yah Mahmo?abu sae kace ah wasan kwaikwayo?"
"Toh wannan maganar da nake miki wasar zahiri ce bata kwaikwayo ba,Fadima de ayanxu matar Mahmood ce wacce ya b'oye mana auranta da yayi.... " acewar Momi.
Cike da al'ajabi Hanan tace"Tabdijam! agaskia Momi Fadima da Yah Mahmo sunci amanarmu,Fadima ta manta cewar itace farin cikin mijina,shine don ta ruguza wannan farin cikin nasa shine ta tashi ta auri Yah Mahmo?dama can ni nasha fadawa Mubarak cewar nifa ina ganin kamar Fadimar bata qaunarsa kamar yadda shi yake hauka akanta,amma sam yaqi saurarona sabida makauniyar so daya rufe masa ido,yanxu ga irinta nan,ta tashi ta aure masa dan'uwa wanda na tabbatar ba k'aramin yaki za'ai ba kuwa idan ya dawo........ "
Ta rushe da kuka tare da ficewa da gudu tabar dakin,Momi kuwa sae Binta da kallon mamaki take,ahankali tace"Kai! kai! kai!!! Wayyo ni Bintu d'iyar hassan nide wallahi ban tab'a ganin shashasha marasa k'ishin mijinta kamar Hauwa'u ba,in banda abin sokuwan ai wannan al'amarin ah dadinta kenan tunda anyi nasarar raba mijinta da wacce yake fifitata akanta,amma jibi abinda wawiyar ke fada,yanxu duk suruntun da nake tayi ya tashi abanza kenan?tunda ta kasa fahimtar cewar ita Fadimar mah bata da masaniyar mijin da aka aura mata sae bayan an kawota....."
Taja tsaki tare da mik'ewa don gabatar da sallar la'asar.
**
Awannan daren mun gurji amarcinmu,Mahmood ya fanshi kudin sadakinsa ba kadan ba,ni kuwa nasha kuka har na baiwa uku lada,lallashi da sanya albarqa kuwa har Mahmood ya gaji da yinsu,sae cewa yake "Matata ubangiji Allah yayi miki albarqa,nagode kwarai
Showing 9001 words to 12000 words out of 43707 words

A/N
Wow! Congrats *'Zahmood💞'*.... Sauran muku rigimar Mijin jiddoh!!!
2episodes remaining,amma sai next week zaku gansu duka biyun atake don diz week Muna da biki,yanxu haka mah na kokarta nayi muku typing ne don kada kuji shirun yayi yawa.
*'HAFNAN'*
https://mobile.facebook.com/Intelligent-Writers-Association-1194933670662901/
*💘SHIN SO DAYA NE?💝*
*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*
*{Onward together}*
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOUCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINGS 💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔
*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*
*WATPADD:HAFNANCY💞*
*IG:Hafsy___mustee*
✨✨✨
*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*
*🌼BABI NA SHA DAYA🌼*
*page 29-30*
Ummata na k'ira wacce muna gama gaisawa ta rufeni da fada,wai dole na ajje wannan baccin safen nan agefe wanda ya riga ya gama bi min jiki,tace idan ban kama jiki na watsar da kiwiya agefe na dunga kula da mijina ba,toh kuwa namiji shi babu ruwansa,idan yaga bakya masa abunda yakeso toh kuwa yana iya banka miki kishiya wacce zata zo ta dunga kula da bukatunsa da kuma tattalinsa,ke kuwa awatsar dake agefe ki koma 'yar kallo.Mun jima tana min nasihu meh ratsa xuciya,daga bisani mukayi sallama.Shima Abbana na k'irashi mun gaisa.Har yake labarta min irin yanayin da Umma ta shiga alokacin da take ta k'ira amma babu amsa.Dariya nayi sosae tare da jin wani irin soyayyar Ummata na ratsa jinin jikina.
Kai tsaye na latso _*My Ashwairiyya*_.
Ita kuwa awannan lokacin ta fito wanka kenan,tana gaban madubi tana taje kanta,so take taje taga dakin Suhaima.Wayarta dake gaban madubi taji ya dauki kida,da hanzari takai hannu ta dauketa.
*'Fateenah'* shine sunan data gani yana rawa akan screen,gabanta ne taji ya bada rasss!.... Jefar da comb din hannunta tayi tare da mik'ewa da sauri har jikinta na dan rawa don tsananin tsoro da kuma fargabar abinda zataji daga sahibar tata.
"Hel....lo... Fateenah'...... " haka ta fada cike da in-inna ah sa'ilin da tayi picking call din.
Bushewa da wani irin dariya nayi don nasan abinda take yiwa wannan rawar muryar,wato atunaninta tsantsar tashin hankali zata tsinta daga gareni shiyasa take cike da tsoro. Allah sarki my Ayush komai yayi chas-chas ahalin yanxu.
Nace"Malama idan zaki daidaita muryarki toh tun wuri mah ki daidaita don ni yanxu babu abinda nakeso sama da mijin da kuka hana min saninsa da wuri sae akurarren lokaci...... "
Kwashe komai nayi na gaya mata tun wucewarsu,tarewata da kuma rigimarmu adaren farko,sae kuma sabuwar rigimarsu Momi da kuma xuwarmu gidan Baba Mu'azzam da kuma nasihunsa agaremu,sae kuma sulhun da aka nema.
Wani wawan ajiyar xuciya Ash ta sauke,cike da murna tace"Wayyyo! Fateenah' ina zan saka kaina don murna? Agaskiya naji dadi ba kadan ba da har kika haqura kika rungumi mijin kaddararki,fateenah wlh believe me Mahmood shine kalarki ba Mubeen ba,wlh ni dama can ina ta miki kwadayin aurensa sae gashi lokaci daya Allah ya amsa addu'ata,ya zamo mallakinki,yanzu dai addu'armu shine Allah yasa Mubarak ya fahimceku ya kuma gane cewar wani baya taba auran matar wani,haka zalika wata bata taba auran mijin wata........ "
Cike da sanyin murya na amsa mata da "ameen." Tace min tana shirin xuwa gidan Suhaima ne,nace yanzu Muna gama waya ita zan kira.Mukayi sallama.
"Nima ahalin yanxu babu abinda nakeso kamar matata wacce naki bayyana kaina agareta sae akurarren lokaci..... "
Da sauri na waiga tare da watsa masa wani Irin kallon soyayya,ware min hannayensa yayi.
Ahankali ya furta"Babyna I nid a warm hug...... "
Babu b'ata lokaci na isa gareshi tare da fad'awa jikinsa,sannu ahankali ya maida hannayensa ya rufe yana meh dada kankameni.kunnuwana dake saman k'irjinsa ya sanya nake iya jin yadda xuciyarsa ke bugawa da sauri da sauri.Ahankali na lumshe idanuwa ina meh jin wani irin sonsa na ratsa jinin jikina.
***
Ash cike da farin ciki ta Latso su Leedar da Fresh take labarta musu zancen Fadimar,suma din sosae sukai murna tare da musu fatar alheri da kuma addu'ar Allah yasa Mubeen ya fahimcesu.
*
Cike da rawar jiki ta mik'e tana fadin" Momi kunnuwana sun kasa gasgata zancen da kike min? Taya za'ai Zahranmu ta rikid'e ta zamo matar Yah Mahmo?abu sae kace ah wasan kwaikwayo?"
"Toh wannan maganar da nake miki wasar zahiri ce bata kwaikwayo ba,Fadima de ayanxu matar Mahmood ce wacce ya b'oye mana auranta da yayi.... " acewar Momi.
Cike da al'ajabi Hanan tace"Tabdijam! agaskia Momi Fadima da Yah Mahmo sunci amanarmu,Fadima ta manta cewar itace farin cikin mijina,shine don ta ruguza wannan farin cikin nasa shine ta tashi ta auri Yah Mahmo?dama can ni nasha fadawa Mubarak cewar nifa ina ganin kamar Fadimar bata qaunarsa kamar yadda shi yake hauka akanta,amma sam yaqi saurarona sabida makauniyar so daya rufe masa ido,yanxu ga irinta nan,ta tashi ta aure masa dan'uwa wanda na tabbatar ba k'aramin yaki za'ai ba kuwa idan ya dawo........ "
Ta rushe da kuka tare da ficewa da gudu tabar dakin,Momi kuwa sae Binta da kallon mamaki take,ahankali tace"Kai! kai! kai!!! Wayyo ni Bintu d'iyar hassan nide wallahi ban tab'a ganin shashasha marasa k'ishin mijinta kamar Hauwa'u ba,in banda abin sokuwan ai wannan al'amarin ah dadinta kenan tunda anyi nasarar raba mijinta da wacce yake fifitata akanta,amma jibi abinda wawiyar ke fada,yanxu duk suruntun da nake tayi ya tashi abanza kenan?tunda ta kasa fahimtar cewar ita Fadimar mah bata da masaniyar mijin da aka aura mata sae bayan an kawota....."
Taja tsaki tare da mik'ewa don gabatar da sallar la'asar.
**
Awannan daren mun gurji amarcinmu,Mahmood ya fanshi kudin sadakinsa ba kadan ba,ni kuwa nasha kuka har na baiwa uku lada,lallashi da sanya albarqa kuwa har Mahmood ya gaji da yinsu,sae cewa yake "Matata ubangiji Allah yayi miki albarqa,nagode kwarai
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4 Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15