take don tabbatar da lallai kuka taga momin tata keyi.Ahankali ta saukar da kafafu daga saman gado,ta isa ga Mominta tace"Momina meya sameki kike kuka?kode kewar daddy kike ji ne? "

   Uwar bata tankata ba sae aikin rera kukanta take ahankali,ganin hakan ya saka ta fice daga dakin xuwa falo,ta hango Usee da Fadima na cin tsirensu ah plate daya.Momi kuwa ta koma daki abinta bayan ta baiwa Fadima haquri akan cin fuskar da Hanan ta mata.

  Usee na ganinta yace"Uwar taki taga damar kyaleki ki fito? " bata ma san yanayi ba,illa kurawa Fadima idanuwa da tayi tana meh son tunano inda ta taba ganinta.

    "Jasmin taho nice wannan antin meh k'yau wacce har kike ta kokarin samo bulala azane ni rannan kin tuna? "

Yaro baya mantuwa,ai kuwa ta tunata,da gudu taje ta rungumeta tana cewa"Anty meh k'yau nayi kewarki sosae,kullum idan kuna waya da abba nace ya bani sai yaki...."

   Usee yace"Toh ai yanxu gashi ta dawo kusa dake,zaki gaji da ganinta har ki ture idan har uwarki ta yarda,yanxu anty meh k'yau matar daddynki Mahmood ce.... "

Cike da murna tace"Laaah! anty da gaske?zaki Haifa min cousins kamarsu Ablan mum meema? "

   Sosae maganarta ya bani kunya,lallai Jasmin akwai surutu,sae da Momi ta fito ta tsawatar mata sannan ta nutsu,na umarceta data zauna muci tsiren tare.

Usee ya tsura mata idanuwa yace"Wai har bakin nan yasan wani abu waishi cousin,sae shegen surutun tsiya..... "

   Dariya muka fashe dashi daga ni har momin,ita kuwa Jasmin turo baki gaba tayi alamun shagwaba.Muna haka ne fa sae ga uban gayyar yayi sallama ya shigo.Dago kai nayi na xuba masa ido,wani mugun kallo naga ya watso min,da sauri na sadda kai kasa xuciyata na cigaba da bugawa da sauri da sauri.Jasmin ce taje ta rungumeshi tana masa oyoyo.

    Umma ita kuwa k'yautar turaren wuta kala-kala ta bani,sae kuma turamen zannuwa masu tsada biyu da leshi itama meh tsada,wai gudummawarta kenan agareni,ba yawa,sosae nayi mata godia,ta tabbatar min da cewar insha Allahu suna nan xuwa Susan gidanmu na can Zaria,wai adalilina Zata zo tasan inda dan nata ke zaune.

     Haka muka baro gidan,ya tsaya awata eatery yayi mana take away,har muka iso gidan babu maganar data shiga tsakanina dashi,abincin mah ayau kowa ciyar da kansa yayi amma de ah plate daya mukaci,wanka mah yau daban daban akayi,da muka zo kwanciya bacci sae na kasa haquri ganin ya juya min baya.Mirginowa nayi tare da rungume bayansa,kana na fashe da kuka nace"Haba mijina wai har yanxu fushin kake dani?don Allah ka sassauta min walhi xuciyata bazata iya daukar wannan hukuncin ba,duk wani dak'ika dake tafiya tare suke wucewa da tsananin son da nake maka,pls my jannah don't turn ur back on me,Wallahi Zahmood bazata iya rayuwa ba tare da ganin walwalarka da kuma kulawarka agareta ba...... "

    Wani sassanyar ajiyar xuciya ya sauke,yana meh jin wani irin mugun sonta da kuma qaunarta na kara shigar xuciyarsa dakyau.Ahankali ya juyo gareta har suna hada numfashi don sosae tsinin hancinsa ya manne da tata hancin.

Yace"Zahmood abinda nake son ki sani shine,ni mutum ne meh zazzafar kishi akan duk wani abinda nakeso,nasan Usman kanina ne amma sam banso kikayi maganar runguma agabana ba,haka kuma banso ganinki kina cin abu ah plate daya dashi ba,sae naji haushinku duka alokacin,amma yanxu tunda kin gane kuskurenki sae ki kiyaye gaba.... "

   "Dear nah bazan sake ba Wallahi... "

Murmushi yayi yace"Yauwah dats my baby,I so much love you Zahmood.... "

    Daga nan labarin ya soma sauya zani,ya cika alqawarinsa don seda kwalliya ta biya kudin sabulu kamar yadda ya fada.

     ***
Washeqari qarfe goma tayi mana ah garin Zaria.tsarin gidana yayi min ba kadan ba,gidan de gata madaidaiciya amma se shegen k'yau.Yace na shirya muje gidanmu.Har tsalle saida na doka don murna.Gidansu Ash muka soma zuwa,ba karamin murna tayi da ganina ba,donshi awaje ya tsaya ni kuma na shiga ciki.

    Tace"Fateenah kin gan yadda kika sauya kuwa?dama can ke meh k'yan ce sae kuma gashi kin kara akan nada,har wani mazaunai kika ajje fa,lallai agaida wannan Mahmood din agaskia yana kular mana dake yadda ya kamata,Masha Allah aure akwai dadi Muma Allah ya nuna mana tamu da Bash Dina.... "

   Dundu na sakar mata abaya nace"Mara kunya kawai,ni tashi muje ki min rakiya kada ya gaji da jirana don har gida zamu.... "

Muka fito nayiwa Maminta sallama tana ta shi min albarqa ina amsawa.

    "Fateenah fatarmu de ayanxu Allah yasa Mubeen ya karbi kaddararsa..... " ta fadi hakan sanda muka fito daga cikin gidan.

Ahankali nace"Ameen fa Sahibata.... "

    Sun gaisa sosae da Mahmood dina,tace"Yallabai ngd kwarai da gaske gaskia aikinka na kyau don ga zahiri nan na gani ajikin Fateenah.... "

Murmushi kawai mukayi daga ni har shi.Har gidansu Suhaima saida mukaje,muka tarar da Leedar agida,rasa inda Suhaima Zata sakani tayi don murna,shi kuwa Leedar wani kunyata yake ji,na nuna masa wlh babu komai don yanxu ni ina son mijina,har cikin gidan muka shiga muka gaida surukanta,suma din sun sanya mana albarqa sosai.Itama din Suhaimar irin Zancen Ash tamin wato Allah yasa idan Mubarak ya dawo ya karbi kaddararsa.

    Daga k'arshe muka sauka can gidanmu,Umma na ganina tace"Saukar yaushe? "

       Nace"safiyar yau dinnan wlh... "

"Kedai wlh sam baki da hankali 'yar Kareematu,fisabilillahi yanxu sae da kika tasa bawan Allah agaba ya kawoki ganin gida daga dawowarku yau yau? "

      "Ummana nasan dama ke kadai ce bakiyi kewata ba... " bata tankani ba  illa juyawa da tayi tana k'arbawa Mahmood gaisuwa wanda sae faman dariya yaketa mana.Abba mah sosai yayi farin cikin ganinmu don gabaki daya suna lambun shaqatawar gidan ne,kannena mah kamar zasu kada ni don murnar ganina.Sae yamma Mahmood ya dawo daukata,Umma ta tambeyeni babu matsala ko? Nace mata lafiya lau muke zaune amma ban gaya mata cewar ai Mahmood dan'uwan Mubarak bane balle na gaya mata abinda ke going,nafison Koda ace zasuji wani abin toh se bayan komai ya lafa idan Mubeen ya dawo.Abba yai mana nasihu sosai sannan muka baro gidan,Abba yace kannena nanan xuwa min weekend meh zuwa don washeqari Monday zamuyi resuming school.

      ***
wata irin shaquwace da kuma qaunar junanmu ya kara k'arfi atsakaninmu,rayuwar aure muke nida Mahmood abar kwatance da sha'awa.Tare muke tafiya makaranta kullum,idan na gama lectures sae naje office dinsa na jirashi har ya tashi.

       **

**INA LABARIN MIJIN JIDDOH?**

    Mubeen rayuwarsa yake babu yabo ba fallasa acan kasar Indiar,kwata-kwata mah ya dena nemar Mahmood awaya tunda idan ya k'ira baya dagawa,kuma ko kadan beyi gangancin gayawa wani nasa ba don baya son Mummy tasan cewar har yanxu yana tare da Fadima,amma kuma da Zarar ya dawo dole kuwa ta sani kuma dole ya auri Zahransa.Tunda Hanan taga Fadima amatsayin matar Mahmood,toh tun daga ranar duk wata walwalarta ta raqu wanda har hakan yasa Mubarak ya Dago cewar lallai matar tasa bata lafiya.Juyin duniyar nan yayi da ita akan ta fada masa abinda ke damunta amma se tace masa babu komai wallahi.Hakan ya kara sakashi cikin damuwa,ga rashin ji daga Zahransa,sannan yanxu kuma ga damuwar Hanan dinsa,duk yabi ya zama wani iri dashi don babu wani kwanciyar hankali atare dashi,abinda yaje yi mah sam baya wani concentrating akai,ganin hakan ya sanya abokan aikinsa k'iran CMD suka gaya masa halin da Mubarak din ke ciki tun ranar da suka sauka k'asar India.Dr.Shamsu sam beji dadin wannan al'amarin ba,aganinsa akan Hanan ne Mubeen din ya shiga cikin wannan damuwar,ya k'ira yace masa yana gama first 3months din kawai ya dawo gida,Mubeen ba karamin murna yayi da hakan ba,se yaki gayawa kowa nasa randa ze dawo.Tun asannan ne ya soma k'irgen ranakun daya rage masa ah Indiar.Ayanxu haka sati guda cur! kawai ya rage masa ya dawo.

       ****
watarana bayan mun gama morning lectures,sae kawai naji ina jin bak'on al'amari ajikina,zazzabi meh k'arfin gaske naji yana nemar rufeni,nayiwa Ash sallama na nufi office din Mahmood.Yana ganina ya taso arud'e yana fadin"My Zahmood yaya dai? Meya sameki?"

  Amai shine ya biyo bayan tambayoyinsa,amai nake kamar zan amayo hanjin cikina,duk yabi ya rud'e.Students din da suke cikin office din sae ce min suke "Sorry ma,it shall be well with you.... "

     Saida Mahmood ya wanke min fuska,wani student ya taimaka yayi clearing inda nayi amai.Ya daukeni kamar wata 'yar baby yana fadin"Dolene muje asibiti Zahmood jikinki yayi zafi sosai.... " cikin tashin hankali ya fice dani ahannunsa,ni kuwa babu damar kwatar kaina don gabaki daya jikina ya mutu.Ya umarce wani acikin students din daya rufe masa office,ya rufe ya mik'a masa makullan.

   Yace dasu"Am sorry for the inconvenience..... Wen I get back I will attend to u all properly,buh for now I hav to take care of my wife... "

. yayi gaba da sauri yana fadin"My Zahmood sannu kinji insha Allah it shall be well with you.Mutane kuwa sae binsu ake da kallo cike da shaawar wannan soyayyar tasu.

    Babu bata lokaci ya Isa ga motarsa ya fice daga makarantar aguje,ahankali na furta"Dear nah I think am carrying ur baby........ "

Cike da murna yace"Wayyyo Allah Zahmood are you serious? Da gaske kike na kusa zama uba? Yanxu nima an kusa kirana da baba kenan? "

   Juyawa nayi ina kallon yadda yake zuba sambatu,hawaye na gangarowa Saman kuncinsa,abin gwanin ban tausayi,sae nima naji kawai hawaye ya ziraro min tare da jin sonsa na qaruwa acikin xuciyata.

Asibitin mah haka aka kara tabbatar masa da lallai ina dauke da juna biyu na tsawon sati uku.Har k'yauta sae da Mahmood ya baiwa likita na wannan albishir daya masa.
 

   Wani sabon tattalina yake daga ni har babyn tamu,na musamman ya dauki hutun sati guda yana kula dani,don rashin kunya Mahmood har kiran yan'uwansa yayi akan an samu karuwa,babu wanda yakai Momi murnar samun wannan karuwar,alast ta kusa ganin jikokinta daga bangaren babban danta.Bayan kwana biyu kuwa sae ga mutan kano anzo dubiyata hadda su 'yan gidan Baba mu'azzam,har gidanmu saida Mahmood yakaisu hadda Hajiyarsa don sada zumunci,ita kuwa Ummana Sau daya tazo da kannena,Suhaima mah haka,ita kuwa Ash tayi zuwa har sau hudu kenan.Aranar suka koma Kano.bayan sati guda na ware,na danji dan dama-dama har na soma zuwa makaranta,amma ko kadan Mahmood baya bari ina aiki,duk abinda nakeso shike tashiwa ya dauko min ita,wai shi baya son na wahalar masa da babynsa,nace ai kuwa idan baya bari ina dan motsa jiki toh kuwa haihuwar tana iya zuwar min da dan gaddama,shine fa yadan soma barina ina dan taba wani aikin amma ba sosai ba.

      ****
**BAYAN SATI GUDA**

   Akace rana bata k'arya sede uwar diya taji kunya,sannu-sannu bata hana zuwa sede adade ba'a kai ba.Ayau misalin qarfe biyu Mubarak ya diro Nigeria,ta Lagos suka sauka,suka sake shiga jirgin da ze saukesu akano.Bayan 1hr 40mins suka iso Kano ta dabo tumbin giya.Be Sanar da kowa batun dawowarsa ba balle yasa ran za'a taho daukarsa,babu b'ata lokaci yayi shatar adaidaita.Har kofar gidan aka kawoshi.

    Momi itace wacce ya soma hangowa ah tsakar gidan tana baiwa kajin da take kiwo abincinsu.

"Assalamu alaykum warahmatullahi ta'ala wa barakatuhu..." Ya fadi hakan alokacin daya shigo cikin gidan sosai.

Momi ce ta amsa sallamar tare da dago kanta,afirgice ta jefar da kwanon abincin kajin dake hannunta,tace"Wah nake gani haka agabana kamar d'ana Mubarak? "

   Murmushin k'arfin halin ya sakar mata kana yace"Abin mamaki yanxu Momina dan naki ne kika kasa shaidawa kai tsaye?ko don na k'ara baki da kuma 'yar ramar danayi ne? "

Da rawar murya tace"Eh fah hakane kam,ashe ba cewa kayi sae bayan watanni shidda zaka dawo ba? Ko kuwa bakada lafiya ne shine ka tashi ka kamo hanya ba tare da saninmu ba? "

     "Momi hankalina zefi kwanciya idan ina kusa da Hauwa'u,idan ina ganinta zanfi jindadi,dama ko kadan banso wannan tafiyar ba sabida irin lalurarta ta laulayi meh tsanani,amma sabida matsa min da akayi shiyasa na tafi,koda naje can hankalina yaki kwanciya akanta shine oganmu yace kawai na dawo...... "

Cike da fargaba Momi tace"Ai kuwa cikin nata da sauki sosae don bayan kwana bibbiyu Dr.Basira ke xuwa dubata,kuma ta tabbatar mana da cewar baby da mamanta lfy qalau suke,kuma she has about 70% assurance na cewar wannan k'aron da kanta zata haihu basai an barkata ba,eyyah Mubarak ai daka tsaya abinka ka gama abinda yakaika....... "

   Murmushi kawai yayi yace"Bari na shiga ciki Momi... " kafin ta k'ara magana ya shige ciki jaye da trolley dinsa.Dif! duk wani network meh aiki ajikin Momi ya tsaya cak! ya dena aiki.Tana nan tsaya se tunane-tunane take,ahakan Usee ya shigo gidan yana cire earpiece akunnensa,cike da tashin hankali yace"Momi daga nesa na hango wani ya sauka daga cikin adaidaita har ya shigo cikin gidan nan kamar Yah Mubarak..... "

    "Shine ba wai kama ba...... "

Salati Usee ya saki tare da aza hannu duka biyun aka kamar wanda aka yiwa mutuwa.Wani irin zabura Momi tayi kamar wacce aka jonawa electric shock,tayi gaba da sauri sauri tana cewa"Usee taimaka ka kwashe min abincin kajin nan dana zubar,bari na kira Abbanku Mu'azzamu na fada masa cewar ya dawo....... "

   "Toh" kawai ya iya cewa.Ta shige ciki,ada dakinta take da niyyar shiga don dauko wayarta amma se kuma ta Samu kanta da son yiwa su Mubarak lab'e.Da hanzari kuwa tayi dakin da aka sauki Hanan,ajikin kofar dakin ta lab'e tana sauraron maganarsu.

   Kuka ta jiwo Hanan tana yi tare da rokansa"Haba mijin Hauwa'u yanxu har xuwa wannan lokacin baka cire Zahra aranka ba?aganina ya kamata ka shafeta daga cikin rayuwarka don I think Zahra ta maka nisa ba kadan ba...... "

Wata uban tsawa ya doka mata,yace"Shut up! Jiddah..... Yanxu har ke kin isa kice na cire Zahra araina? Kin kuwa san yadda nake sonta kuwa?toh ayau ina son ki san cewar duk wani numfashi da nake shak'a tare nake shak'arsa da soyayyarta,bana tsammanin ko Momi mah wannan k'aron zata iya dakatar dani daga aurenta...."

    Ya sassauta murya yace"Haba jiddan Mubarak ke kanki kin san nayi kokari sosae ba kadan ba da har nakai tsawon lokacin nan ah India ba tare da jin halin da Zahrata ke ciki ba,kullum idan munyi waya dake sae na gaya miki cewar har yanxu banji daga gareta ba,shine yanxu kike cewa na haqura da ita? Never! Wallahi,tashi ki dauko min makullin motata na kama hanyar Zaria yanxun nan kuwa...... "

     "Haba Mubarak ko hutawa bakayi ba balle kasa koda ruwa ne acikinka shine kake tunanin kama hanyar Zaria ayanxu?ka bari ka huta mana..... "

   Wani uban tsawa ya doka mata wanda hakan ba karamin firgitata yayi ba musamman mah Momi wacce har saida ta dan buge da k'ofa don tsananin firgici😁

Xuciyarsa ce ta bashi cewar kamar ana musu lab'e don haka da sauri ya nufi kofar yana fadin"Uban waye ne ke mana lab'e anan?" Azatonsa Usee ne don beyi tsammanin cewar Momi bace.

    Ita kuwa Momi jin abinda ya fada ya sanyata hanzarin rugawa da gudu xuwa falo xuciyarta kamar zata fad'o waje don tsananin fargaba,tana iya cewa tunda take aduniyarta bata tab'a shiga irin wannan tashin hankalin ba kamar na yau. (Hahahah! Major general of soldiers ya dawo).😀😂

Ita kuwa Hanan har fitsari saida ta saki don tsananin tsoro.Koda ya lek'a sae yaga wayam!babu kowa,xuwa yayi ya lek'a falon,sae yayi ido hudu da Momi wacce sae faman sauke ajiyar xuciya take,jikinsa ne yayi sanyi qalau kamar kankara don jikinsa ya bashi cewar itace ta musu lab'en.

      "Mubarak zoka zauna muyi magana..... "

Gabansa ne yaji ya bada rass!,wato kenan Momi taji xantukansa da Hanan kenan?toh taji din mana shide walhi bata isa ta hana masa auran Zahra ba don ba itace ta haifeshi ba balle tace idan tayi masa baki yana iya kamashi.(Anya mubarak? Matar data raineka tsakaninta da Allah ne kake tunanin idan ta maka baki bazai kamaka ba? Ina ganin kawai ka zauna ka sake tunani).

     "Ina son kadan bani aron juz 1hr acikin lokacinka so nake muyi magana.... " ta fadi da rawar murya don har ga Allah tsoron Mubarak din ma take.

Arayuwarsa ta duniya momi ita kadai ce macen da baze ya musa mata magana ba,amma akan Zahra wannan k'aron sede ta nemi wani Mubarak din amma bashi ba.

   "Toh" kawai ya iya cewa don kwarai yana son yaji ta bakinta kafin ya amayar da tasa.Samin gu yayi ya zauna,se alokacin Usee ya shigo suka gaisa da yayan nasa,har yake tambayarsa ya hanya? Ba yabo ba fallasa ya amsa masa.

Hanan kuwa ta fito sae kuka take rik'e da key motarsa ahannunta,wuri guda ta tsaya cak! tama kasa karasa gareshi sae shesshek'a take,shi kuwa kallo daya yayi mata kana ya dauke kansa daga gareta.

   Momi ce tayi mata ido,ai kuwa da hanzari ta shiga cikin taitayinta tare da samin hannun wata kujera ta zauna.Momi ta shige dakinta,da rawar hannu ta lalubo wayarta ta latso Baba Mu'azzam take gaya masa cewar ai Mubarak ya dawo,yace gashi nan tafe yanxun nan kuwa kada akuskura abari Mubarak din ya fita,ta de amsa masa da "insha Allahu" ne,don idan ya nemi fitar tasan ko ita ayanxu bata isa ta hana masa fita ba yadda idanuwansa suka rufe da tashin hankalin nan.Ta latso su Mahmood shima ta gaya masa,yace gasu nan tafe suma,duk 'ya'yanta mata saida ta kirasu suma Cike da tashin hankali sukace gasu nan tafe.Tace kada asake ataho da yara abarsu ahannun masu aikin gida,tama gode Jasmin na gidan Meema don haka komai zaizo musu da dan dama dama don bata qaunar yara su gigice da wannan tashin hankalin da suke shirin fuskata............... 📝

   A/N
Tofa! bilhaqqi yau ake yinta,fire on the mountain kadan-kadan,ku agaza musu da taimakon gaggawa ta yan fire service 😁

    Last episode coming soon ending of diz week insha Allah!!

Longest chapter so far!!

       *HAFNAN CE💞*

    
    
*💘SHIN SO DAYA NE?💝*

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION📖✍*

*{Onward together}*
*{ we give the reader's of ours the best out of the best's,, our inks are melodious And dropping a kinda light's to reader's}*
'''THE PEN OF LOVE 😘 HEART TOCHING ❤ TEARS OF SORROWS 😭 CURDLES 😊 GIGGLES 😁 AND MARRIAGE THINK
Showing 15001 words to 18000 words out of 43707 words