💑'''
*JUST GIVE US FOLLOW.....*✔

*MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*

*WATPADD:HAFNANCY💞*

*IG:Hafsy___mustee*

✨✨

*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*

_please kindly touch the little star to vote me before you start reading_

🌼BABI NA TAKWAS🌼

*Page 21-23*

Kaina naji yana wani irin mugun sara min,babu shiri na tsaida kukana completely tamk'ar anyi ruwa an dauke.Daukar k'aramar filon wata two seater nayi,ahankali na sauko na kwanta ah k'asa tare da yin matashi da filon.Duk tunane-tunanen Mahmood ne yabi ya addabi xuciyata da kuma tsananin son sanin halin da yake ciki ahalin yanxu.

Ban wani jima da kwanciya ba wani nannauyar bacci yayi awon gaba dani.

_*"Fadima Zahra'u kinki ki rungumi kaddararki amatsayinki ta 'ya musulma kamar yadda aka koyar daku karban kaddara mai kyau ko mara kyau,amma ke kinki karbar taki kaddarar,nayi miki baiwa da kuma ni'imar da bah kowacce 'ya macece zata sami hakan ba,amma ke kin butulce min,kinci mutuncin mijinki tare da yi masa illa bayan kin san cewa babu abinda yakai Miji daraja agun duk wata d'iya mace,d'a namiji shine shugaba kuma shine jagoranki xuwa aljanna idan har yaso,adalilin sab'a masa da kikayi ya sanya na yanke miki hukuncin shiga wutar jahannama.......... "*_

Ah firgice na farka daga wannan mummunan mafarki tare da fashewa da kuka,atsoroce nake fadin"Yah Allah wallahi na tuba ka yafemin,Wlhy na k'arbi kaddarata,na haqura xan xauna da mijina,zamuyi zaman lafiya kuma xanyi masa biyayya har xuwa k'arshen rayuwata dashi aduniya,bazan sake ci masa mutunci ko kuma na sab'a masa ba,Yah Allah ka yafe min *'INA SON MIJINA'*

Ji nayi an d'an tab'oni ta baya,ai kuwa da k'arfi na sake ihu tare da waigowa babu b'ata lokaci,jikina sae karkarwa yake tamk'ar meh jin sanyi.Mahmood ne,banji shigowarsa ba sae de kawai naji saukar hannunsa ajikina.Shi kuwa ya dawo alokacin tana baccin mamakin nata,kafin yakai ga zama akan kujera yaji kawai ta tashi afirgice tana wannan sambatun nata,atake ya gane cewar mummunar mafarki tayi,kuma ze iya bugar k'irji yace bilhaqqi yaji dadin wannan mafarkin nata don kamar hakan ya sanya ta haqura ta rungumi *'MIJIN KADDARARTA'*.

"Haba my baby doll,da salati da kuma addu'a abaki ya kamata ki tashi dashi ba wai da ihu ba..... " ya fadi hakan ahankali kamar ze had'iyeta don so.

Sae ayanxu na tuna cewar salati da kuma addu'a ya kamata ace nayi ba wai ihu da kuma sambatu ba.Shi ya soma karanto min addu'oi,yana yi ina k'arba masa kamar wata meh koyon k'aratu koh tilawa.

Can hankalina ya dawo jikina,da hanzari na mik'e ina dubansa,cike da fuskar tausayi nace"Mahmood dina are you okay? Ka samu an wanke maka ciwon? "

Na fadi hakan ina dube-duben kan nasa,ina neman inda naji masa raunin don harna manta wurin,fes! idanuwana suka sauka kan k'atoton plaster din da aka lik'a masa awajen.

Wani d'an marayan kuka ne naji ya sub'uce min,hannu nakai na tab'a wurin,sannu ahankali na shiga shafa wajen,nace"Mijina don Allah ka yafe min hak'ika ko kadan ban k'yauta maka ba,amma ayanxu ina meh farin cikin shaida maka cewar Lallai na haqura xan xauna dakai amatsayin Mijina kuma ina sonka sosae Mahmudanah...... "

Shi kuwa wani irin dadi ne yaji ya tsikareshi tun daga tsakiyar kansa har xuwa babbar yatsar kafarsa,he can't juz believe wai Fadima ta haqura kuma zata xauna dashi har xuwa k'arshen rayuwarsu kafin meh duka ya raba.

Beyi wata-wata ba ya rungumota yana meh jin wani irin sabuwar soyayyarta na kai masa mugun cafka acikin xuciyarsa.

Ahankali yace"Babyna da gaske kin haqura?da gaske kike kin k'arbeni amatsayin mijin aurenki?sannan kuma da gaske kike kin soma jin sona aranki? "

Tsagaitar da kukana nayi,na koma yin 'yar shesshek'a,cike da sanyin murya nace"Yes!!! Mahmood wallahi xan xauna dakai dear nah ina qaunarka har cikin raina.... "

Cike da farin ciki ya cikani yana kallona eyes into eyes,kafin yace"Kenan hakan na nufin u will surely make me to feel being loved once again? "

Gyad'a kai nayi ina meh xubar da 'yan kwalla cike da jindadin ganin tsantsar farin cikin daya shiga.

Yace"And will u be strong,bold & face any family problem dat will be coming soon? "

Cike da fargaba na daure na amsa da"Yeah I promise to be strong & bold for you & I also promise to withstand any obstacles dat will come our way...."

Banyi aune ba kawai naji ya sunkuceni,ya soma yawo dani acikin makeken falon cike da murnar jin kalaman da suka fito daga bakina.

"Dear nah saukeni mana kada kasa mu fama ciwonka.... " na fadi hakan ashagwab'ance,k'ok'arin sauka nake don awuyansa ya daurani,sae ji nayi na dad'a k'ankame kafafuwana.

Yace"Baby ki bari na saukeki da kaina kada ki fad'o ki min asarar wani abin..... "

Dundu na kai masa ta baya,ya b'ank'are bayar,yace"ouhhh!! wallahi dundun ya shiga sosae kuma asannu zan rama idan kika manta..... "

Be direni ako'ina ba sae awani dakin bacci.Yace"Oya matata taso muje mu dauro alwala mu gabatar da sallah don nuna godiyarmu ga Ubangiji daya nuna mana wannan ranar ta kasancewa ma'aurata,ina rok'an Allah daya sanya mana albarqarsa acikin wannan auran,ya kauda duk wata fitintinu,rigingimu da kuma bala'i acikin rayuwar auranmu,ak'arshe kuma Allah ya axurtamu da 'ya'ya na gari,mahaddatan alqur'ani meh girma,masu tsananin tausayin iyayensu da al'ummar musulmi gabaki d'aya....... "

Ahankali nace"Ameen Mijina..... " na fadi hakan sanda nake sharce dan guntun hawayen daya xubo min saman kunci.Tashiwa nayi don cika umarninsa,amma kafin nan sae daya kaini dakina yace na soma yin wanka sannan na dauro alwala nazo na sameshi anashi dakin inda muka baro kenan.Shi da kansa ya zab'o min wata night gown meh k'yau daga cikin wata sif,ya watsa minsu saman gado,riga da wando ce.Sannan shi ya koma dakin nasa don wanka da daura alwala.

Ban dau wani tsawon lokaci ba na cimmasa adakin baccin nasa.Shi ya jamu sallar,Muna sallamewa,ya daga hannuwa sama ya shiga kwararo addu'o'i babu gaggautawa da kuma yiwa Allah k'irari,ban tab'a sanin cewar ilimin arabi ya ratsa Mahmood haka ba sae yau.Yadda yake wani lank'wasa harshe yana baiwa kowacce harafi hakkinta mah wani abin birgewa da sha'awa ne.

Can kuma naga ya d'an juyo tare da dafa kaina,ya shiga kwararo min addu'o'i tare da shi min albarka mara iyaka wanda hakan ya sanya har se dana d'an xubda kwalla tare da jin wani soyayyarsa na fizgata.Yayi mana addu'ar samun zamar lafiya tare da samun zuria d'ayyaba.

Muna idawarwa naji wani sabon bacci yayi min sallama,ashe Mahmood na lure da yadda naketa gyangyad'i tun awajen sallah,yace"Babyna goan sleep naga tun awurin sallah kike ta gyangyad'i kamar wata kaza,oya you ghatta sleep... "

Ya manna min wata peck agoshi wanda na jishi har cikin jinin jikina.Bed dinsa ya nuna min alamun anan xan kwanta,shi kuma naga ya dau pillow ya kwanta ya akasa.ba tare da wata gaddama ba na isa kan gadon na kwanta.

"Goodnite my lovely Wife.... " na tsinkayo maganarsa.

Dan murmusawa nayi nace"Nite too dear nah..... "

_*wayyooo!! Haba Zahmood💞 ya naku first night din ya banbanta dana sauran ma'aurata?*_

**
Suhaima ita kuma bayan an kaita b'angarenta,Reedah ce ta xauna da ita suke ta hira awannan yinin ranar,sae wuraren karfe goma na dare tayi mata sallama ta tafi,Shima din uban gayyar ne ya k'irata awaya yake ce mata"Toh! auta akyalemun amarya hakan ta huta da surutunki,ki tafi bangaranku don ina nan tafe yanxu da abokaina xuwa ga amarya..... "

Murmushi kawai tayi kana tace"kai big brother wai zumudin meh kake haka bayan from now on you have the whole moments to spend together with *'SuhaiLeedar'*?"

"Ni dai na gaya maki Karki sake na iso na iskeki anan.... " ya fadi hakan in a playful manner.

Haka Reedah tabar b'angaren Suhaima wacce dakyar ta barta ta tafi,wai hadda cewa ta kwana.

Dariya sosae Reedah tayi tace"Iyyeh! ashe so kike Yah Haidar ya min dan iskan duka yau acikin gidan nan kenan sabida yadda mah naga yake rawar k'afa akanki,toh kuwa idan aka kuskura aka kawo masa wargi ze iya lallatsa mutum,am so sorry bestie kiyi haquri ki bari ku durje first night dinku don hakan shi ake k'ira da *'AURAN'*...... Bye gudnite..... "

Tayi gaba tabar Suhaima da binta da kallo.Ansha barkwanci da wasanni daga angwaye,daga k'arshe sukayi musu addu'ar samun zaman lafiya da kuma samun zuri'a d'ayyaba,sannan sukayi musu sallama suka fito.Har wajen motocinsu Leedar ya rakosu yana dad'a musu godiya.

Fresh ne ya jawoshi gefe bayan sauran duk sun shiga cikin motar,ya d'an daki kafadarsa yace"Shege abokina yau an zama babban mutum,dan iska kuma kabi yarinyar mutane asannu sabida yadda naga kake rawar kafa akanta kar ka...... "

Dunkule hannu yayi ze kai masa dundu abaya,da sauri Fresh yayi wajen motarsu yana dariya,Leedar yace"Bakai wai dan iska ba? Dont worry zaka ci ubanka ne.... "

Haka de aka rabu cike da farin ciki da wasanni.Shima juz lyk kamar yadda su Mahmood sukayi,haka suma din sukayi.Wato gabatar da sallah don nuna godiyarsu ga Allah da kuma addu'ar samun zaman lfy da zuria ta gari.Sae de su nasu kwanciyar ya banbanta,don tare suka kwanta,ni kuwa ganin lamarin nasu na nemar sauya zani ya saka nayi saurin barin dakin don kam naga kamar suna matuk'ar buqatar sirri.

_*Nice one SuhaiLeedar💞... Asubahi ta gari....*_

***

*4:30am*
_*"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,Allahumma ajirni fi musibati wa akhlifni khairan minha...."*_....... Wannan k'aron da salati na farka da ita bayan wani mummunar mafarkin danayi akan Suhaima da Leedar,wai jinns dinsu Rukky sun halak'asu kamar yadda suka dau alqawari.

Kuka na fashe dashi wanda hakan ya sanya Mahmood farkawa agigice,ambaton sunan Allah ya soma yi kafin ya nufo inda nake,ya kunna dim light,haske yadan bayyana kadan adakin.

"Baby doll wat happened? Mummunar mafarki kikai ko? "

Agigice nace"Eh.... Dama.... "

Da sauri ya katseni yace"No baby doll ba'a bada labarin mafarki,kawai addu'a ya kamata kiyi kinji ko? "

Ahankali nace"okay nagode dear nah.... " addu'o'i na soma xubawa acikin xuciyata babu gaggautawa,ji nake kamar na latso su Leedar din amma kuma bana son Mahmood yasan halin da ake ciki.

(Hahahah! Fadima ta sanya abin aranta ne shiyasa tayi mafarki da hakan! If not *'SuhaiLeedar'* nanan lafiya qalau,sharar baccinsu mah suke ahalin yanxu,shi Leedar dinma ya manta da batunsu don ya rik'e addu'a sosae).

Daga ni har shi bamu sake komawa bacci ba,Muna nan xaune kamar wasu kurame har aka soma k'iraye-k'irayen sallar asubahi.Ya umarceni dana tashi mu gabatar da sallah.Koda muka idar mun dad'e zaune yana zuba mana addu'o'i,can muka shafa,komawa gado nayi na kwanta don wani bacci-bacci ke idanuwana.babu b'ata lokaci baccin yayi awon gaba dani.

Mahmood kuwa sae daya dan karanci alqur'ani,shidda tana yi ya mik'e ya shiga kitchen don had'a musu abinda zasu ji.Arish ya soya musu da kwai,sannan yayi warming ragowar pizza din jiya da kuma garnished chicken.sae kuma ruwan zafin daya dafa ya zuba aflask wanda zasu sha shayi da ita.

6:58am ya kammala komai don ba wuya,still de magajiyar tana nan kwance tana sharar baccinta,kuma ko kadan baya da niyyar tashinta,hasalima wankansa ya shige.

**
Khairat yar bala'i tun shidda da rabi ta iso family house,Labeeba kuwa sae 7:15,Anty Meema ita kuwa sae data b'ata musu lokaci sosae don sae takwas Saura ta iso gidan,Momi kamar zata kifeta da duka don haushi. Haka suka fito suka dunguma gidan Mahmood tare da taimakon Usee (usman) as the driver. (Hahaha! Inyi muku irinta momi,tace"*Dan rakiyar Maza"*😀.

Hanan taso binsu amma se ta tuna cewar yau Dr.Basira zatazo dubata kuma da sassafe take dako sammako................ 📝

A/N

*Ohh! My God!! Mahmood Nakowa kayi ne! Ka cika jarumin jarumai,rana daya,tashin farko Kasan yadda kayi ka cusawa Fadima sonka harta haqura ta xauna dakai,koda yake dama can ta soma sonka amma ita bata san da hakan bane.... Job Weldon to you M.Nakowa....First mission completed & succeeded,now let's watch & see if you will succeed in ur second mission (The family problem).

Ohhh! My God! Nakowa's family are on their way..... Ghen!ghen!ghen!! Fire on the mountain🔥🔥🔥🔥🔥

*sorry guys nasan da yawanku sun aza ko awannan episode din za'ai bala'in,sorry dearies I want to follow each step one by one without skipping!!

*HAFNAN CE💞*
*💘SHIN SO DAYA NE?💝*

       *MALLAKAR:HAFSAT ALMUSTAPHA*

       *WATPADD:HAFNANCY*
       *IG:Hafsy__mustee*

                     💥

*KASHI NA BIYU:RIKICIN K'ARSHE*

          🌼BABI NA UKU🌼

*Page 6-9*

        "Mama bara naje nima na kimtsa kada su wuce wajen reception d'in nan bani..." acewar Anty Hajaar wacce tana gama fad'ar hakan ta mik'e tabar dakin xuwa sashin da aka saukesu.

Kaka rigima ta rakata da "Toh! adawo lafiya Hajara,Allah sarki an girma ba'a san an girma ba,yanxu fisabilillahi taron k'ananun yara mah sae sunje.... Koda yake Allah ne ya kawo mu xamani..."

    Ai dole ne Anty Hajar tama je wannan reception din ko don taje tayi ciye-ciye ta kuma nunawa duniya cewar ita din fah uwar amarya ce.Maminsu Hafeezah mah zataje don ita da Mahmood suna mugun d'asawa da k'yau.

Ash ce xaune tare da Zuzu ah barandar sashin da aka saukesu.Hirar Khaleed Zuzu ke bata wanda ga dukkan alamu ya nuna cewar gayen ya gama tafiya da imaninta.Ita Ash din mah da akewa hirar amsawa kawai take da "uhmm" ko kuwa "a'ah",don kusan xan iya cewa gabaki daya hankalinta ya tafi ne ga su Fadima.Sae ayanxu ne take ganin wautarta na k'iran shi Mahmood d'in daya zo ya lallashi Fadimar bayan tasan muddin Fatin nata na had'a idanuwa dashi amatsayin mijin da aka aura mata,toh kuwa komai na iya k'wab'ewa,anything can happen!.

    Oh! Allah!! akace dana sani yakan zo ne bayan ka aikata ba daidai bah,akan k'irashi da *'dana sani mara amfani'*,data sani kawai ta lallab'ata ta saka kayan don tasan Fatinta komin fad'arsu de tana jin maganarta,kuma tasan xata sauko ne har ta haqura taje reception din,amma da yake iyayi yayi mata yawa,kai tsaye ta k'ira Mahmood din da yaxo gareta,iyayinta ya janyo tana neman haifar da tashin hankali acikin jama'a wanda ta fison ace sae an kai Fadimar gidansa,asannan kowa ya kama gabansa kafin tasan wanene mijinta,tasan duk wani tashin hankali da ze biyo baya alokacin zai iya xuwa da sauki.Wurin reception mah ba lalle ne Fadimar ta gane Mahmood din ba tunda duk'ar da kai zatayi tayi,balle mah tasan halin Fadimar sarai da alkunya,zaiyi matuk'ar wuya ta masa kallon tsaf acikin jama'a.Koda ace tama gane shi,tasan Fadimar baxata tab'a kunyatar dashi idanuwan mutane ba har sae sun k'ebe.

     Toh! yanxu gashi ta janyo k'ebewar tasu da wuri tun mutane basu gama watsewa ba,kuma tasan anything shitty can happen.

Axuciyarta tace"Ohh! ni Ayshatu wat have I done? meya kaini k'iransa? "

   Xuciyarta babu abinda yake yi illa bugawa da sauri da sauri,kasa kunnuwa tayi tana meh jiran ta jiyo hayaniyarsu Fadimar sannan tayi ciki wuf!.Zuzu de data ga sam hankalin Ash din baya gareta,sae kawai taja bakinta tayi shiru,ita Allah-Allah mah take su Fadimar suyi su gama soyayyarsu kamar yadda take tunani sannan ta shiga taje ta tsalawa Khaleed dinta kwalliya.

Anty Hajaar ce tazo shiga sashin,da hanxari Ash ta mik'e tare da shan gabanta.

     Wani irin kallon banza ta jefawa Ash din,kana tace"marasa kunya meye kuma haka? Ko de wata sabuwar salon rashin kunyarce ta motso miki shine hadda wani shan gabana?"

Dan murmusawa kawai Ash tayi,kana tace"Yana de gab da motsowa.... So nake kawai nace miki ki d'an dakata,ango na ganawa da amaryarsa aciki........ "

    Hab'a Anty Hajaar ta rik'e,kana tace"ikon Allah!... nide tunda na budi ido nayi wayau ban tab'a ganin rashin kunya da da'a irin wannan ba,Muido da wannan angon nata sam basu da alk'unya ko kadan musamman mah angon nata,ai sae ya bari iyayenta su tafi kafin ya shiga wurinta suyi shashancin nasu son ransu........ "

Wani kallo ta watsawa Anty Hajaar,ta dubi inda Zuzu take taga mah sam hankalinta baya garesu,hasalima wayarta take daga can d'an nesa da inda suke tsaye.

     Ahankali Ash tace"Dad'ina dake Anty akwai ki da iya jan k'aramar magana tayi tsayi da kuma janyowa kanki raini awajen kananan yara,ina ruwanki da koma meye ya shiga yi? Ina ce ko matarsa ce ba dadironsa ba? Don Allah Anty Hajaar ki dunga kama girmanki kada ya gama xubewa ah idanuwanmu mu yara..... "

Tana gama fad'ar hakan ta koma mazauninta,sae duba agogo take awayarta,yanxu haka takwas ta wuce da mintuna goma,akalla Mahmood ya shafe kusan mintuna ashirin aciki yanxu.Ita kuwa Anty Hajaar jikinta ne yayi sanyi qalau don bata tab'a jin k'unyar kwab'o ba arayuwarta sae yau da Ash ta mata.Sae taga rashin dacewar maganar daya fito daga bakinta.Jan jikinta tayi xuwa ga wani k'aramar kujera ta tsakar gida ta xauna.(lol maganin irinku kenan Anty Hajaar... Ash kin biyani....)

     ***
Idanuwana dani k'aran kaina mun kasa gasgata cewar wai *'ENGR. MAHMOOD MUSTAPHA'* dan'uwan Mubarak ne tsaye agabana amatsayin *'MIJIN KADDARATA'*

    Sake kai yatsu nayi ina murza idanuwana akaro na uku don tabbatarwa kaina cewar mafarki nake kuma wanda ke tsaye agabana ba 'ENGR.MAHMOOD' my brother inlaw bane.Harda mitsilin kaina nayi wai ko mafarki nake na farka,amma uban Zafin dana ji ne ya saka nasan ba mafarkin nake ba,this is reality!!!.

   Da rawar murya nace"Don Allah meh kake yi anan?"

Gaban Engr.ne ya buga wata irin ganga,fargaba da kuma tsoron actions din da Fadima xatayi taking duk ya cika masa xuciya fal! amma da yake shi din namijin duniya ne,sae be bari ta gano weakness dinsa ba.

     Fuskar mamaki ya shimfid'a mata,kana yace"Ban gane meh nakeyi anan ba? all what I know is dat wajen matata nazo...... "

     "Wacece kuma matar taka? " na fadi hakan sanda naji xuciyata na wani min mugun zogi.

  "Of cours! Fadima Sa'ad Mainasara amaryar Engr.Mahmood Mustapha...... "

Da hanzari na katseshi"k'arya kake mak'aryacin banza,mak'aryacin wofi,you can never be my husband ko amafarki,ni bah kai na aura ba,ni *'MAHMOOD NAKOWA'* na aura not *'ENGR.MAHMOOD MUSTAPHA'* because am very pretty sure dat brother inlaw bazaka taba cin amanar d'an'uwanka ba,bazaka tab'a yaudararsa ba,haka kuma nasan bazaka tab'a bin bayansa ka k'wace masa ni ba...... "

    Wani irin mugun d'aci ne Mahmood keji aransa na jin irin wannan kalaman da Fadima take jefarsa dashi,yab'onsa take ko kuwa maganace mara dad'i take jefa masa?

  sassauta muryata nayi,da rawar murya meh had'e da kuka na cigaba da magana"pls brother inlaw meya kawoka gidan surukaina?ko kuwa kaima kana cikin abokan ango ne? kuma ina mijina yake da har ya barka ka shigo har inda matarsa take?okay yanxu na gane,ka samu labarin cewar nayi aure shine kazo kaci min mutunci don na yaudari d'an'uwanka ban aureshi ba..... "

  
Showing 18001 words to 21000 words out of 43707 words