inda nijlah take zauna yace"
Nijlah ki gayamata koke ba kanwat.... Be iya qarasawa ba sabida ganin nijlah kwance a qasa Yasmeen ta hau kanta tana Duka..

Bane ni zaka yaudara ko an gayama bansan sunan *'yar sadaka* nijlah ba,,zaka ha'inceni" to wallahi yau koni ko wannan tsinanniyar yarinyar,, Dama akan wannan kake wulaqantani...

Kukama nijlah kasawa tayi Banda Ido babu abinda take rabawa" ta ko ina Yasmeen ke dukanta har Saida numfashin nijlah yafara sarqewa..
Duk Yadda mashkur yayi Dan ganin ya kwaci nijlah ya kasa Dan ba ruqon Wasa Yasmeen tayi Mata ba,,tana dukanta tana surutai..
Rasa inda mashkur zesa ransa yayi Banda tashin hankali da firgice babu abinda yake ji" waiwaye ya riqayi koze Samu Wanda ze ceci nijlah ya Rasa,,sabida layin ba mutane indai ba lokacin sallah yayi kaga suna fitowa ba..
Dabarace ta fadowa mashkur yafara kwalama get man Kira Dan Shi kadai ze iya jinsu adaidai wannan lokacin..

Me gadi na zaune jikin get yasa radio a kunannsa Yana sauraran wani shiri inda yaji labarin governor ganduje ya tsige sarkin Kano Muhammad sinusi ya Dora hannu aka Yana salati,,hakan ne ya hanashi Jin kiranda mashkur ke masa.

Cikin zafin Rai mashkur yayi Kan Yasmeen da Duka ganin Yadda jini ke fita ta Baki ta hanci a jikin nijlah,,Amma Duk da haka yasmeen Bata dena Dukan taba haka Kuma bakinta beyi Shiru ba..
Wallahi Ko Zaka kasheni Saina fara kashe wannan abun tsiyar Idan yaso Sai kayi abinda zakayi..
Yana hawaye yace" shikenan Ai kin kasheta saiki dagata,,kaicona Ni mashkur Dana kasa riqe amanar Dana dauka Yasmeen baki kyautamin ba,,ki dagata Nace kafin nayi qasa qasa dake yanzu..

Ganin yadda hawaye Ke fita a idanshi yasa Yasmeen Tashi Akan nijlah bakinta Na rawa tace"
Baby kuka kake akan Na Daki wannan yarinyar" me Zan gani Ni Yasmeen Sai kuma ta fashe da kuka ta Shiga cikin gida da gudu tana yarfe hannu,,jikin rigarta da hannunta Duka jini ya Bata..
Tana Shiga me Gadi ya yarda radio yayi Kanta yana tambaya,,kallan waje yayi yaga motan mashkur,,dasauri ya fito Yana tambayan yallabai lafiya..

Chak numfashin mashkur ya tsaya ya Dena aiki,fa gudu yayi kan nijlah Yana kuka saikace qarami n yaro ya tattarota jikinsa Yana jinjigata tare da Kiran sunanta,,jikin Na kyarma ya saketa Yana salati..

Daidai lokacin get man ya qaraso Yana cewa yallabai lafiya" ganin mace kwance Bata numfashi yasa qarasawa Yana matsa hancinta..
Baba ta Mutu Ko,, shikenan Yasmeen kin gama da rayuwana,, nijlah naso ki girma naga yaranmu dake,,naso kema ki dandana rayuwa ta Jin Dadi Sai gashi kin rigamu gidan gaskiya" Sai kuma ya chakumi wayan rigar baba me Gadi Yana cewa,
Dan Allah ka dubamin ita Bata Mutu ba Ko??
Girgiza kai baba me Gadi yayi Dan yariga ya tabbata da mutuwar nijlah sedai Baze Iya gayaba sabida Shima mashkur yaga Hakan..

Baba me gadine yayi qoqarin Tashi Ze ciccibi nijlah yasata a Mota Domin aje ayi jana'izarta.

Mashkur yayi saurin Shan gabansa Yana cewa karka taba ta,,nizan sata a Mota da hannuna,,Allah yajiqanki Nijlah,,wayyo Ni mashkur wannan wacce irin ranace na riska..

Yana kuka yasata a Mota ya nufi hospital da ita,,nan likitoci suka Hau Kan Dan ceto rayuwarta,,seda sukayi kusan 30 minutes akanta kafin Naga daya Daga cikinsu yajamata mayafi ya rufe fuskanta..
Jikinsu a sanyaye suka fito.

DA gudu mashkur yayi kansu Yana cewa likita Yaya Bata Mutu ba Ko?
Shafa kansa dr yayi Yana cewa kayi hakuri mashkur...


Be Bari yaqaraji ba ya fizge hannunsa ya Shiga Dakin,,direct Kan gadon da nijlah Ke kwance yace ya Bude ta..

Wani ihu ya saki ganin hancinta da kunnata rufe da adduga,, haryanzu jini bai Dena zuba ba..

Salati ta kurma Yana neman daidaita nutsuwarsa,,sedai be samu damar Hakan ba yayi Baya luuuuuuuu......




Idan kuka qara comments irin Na jiya,Bazan qara posting ba Sai Bayan Sallah Idan Allah yasa muna da raban gani..



Dan Allah ku riqa sharing danayi posting,,banaso ana damuna Akan Na turo,,abin dayawa Idan Na biyeku Bazan Samu lokacin kaina ba..



*Momn sultan ce*✍✍✍✍
💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*MMN FAREESAH....*



4⃣1⃣&4⃣2⃣


Yayi Baya luuuuuuuu,, dasauri sauran likitocin dake tsaye sukayi nasaran tare sa Suna salati..
Taimakon gaggawa suka Shiga bashi,,cikin Ikon Allah suka Sami damar dawa masa da numfashinsa,,sedai Yana farkawa ya dafe kai Yana hawaye..
Ruwan da aka dauramasa ya fizge tare da Tashi tsaye cikin tashin hankali,,jiyake Shima kama Ze Mutu sabida ya tsara yadda rayuwarsu zata kasance da irin soyayya da zasu gudanar a Duk lokacin da komai ya daidaita..

Daddy ne ya shigo ransa a bace,,Yana tafiya cikin sauri harya qaraso inda mashkur Ke tsaye" mashkur besan da zuwan daddy ba sabida yadda yake acikin tashin hankali.
Motsin dayaji a bayansa ne yasashi saurin zabura a gigice jikinsa Har tsuma yake tsabar tashin hankali Hade da Dana Sani mara musaltuwa ya Bude baki zeyi Magana daddy ya katseshi...

Bakin daddy Na rawa kama ze kifa sabida tashin hankali yace"mezaka gayamin auta,,Ashe Baka da hankali" yanzu mezamu Gaya iyayen yarinyarnan"Yama za'ayi ka dauki 'yar mutane ka kaita wannan gidan,,Bayan kasan halin mahaifin Yasmeen da Kishin tsiya,,gashi Shi bedauka mataki ba Yasmeen ta dauka,,sun kashe marainiyar Allah wanda bataji ba Bata gani ba..

Kuka me ciwo mashkur ya saki,,da gudu yafada jikin daddy,,cike da matsanancin tashin hankali mashkur yace" daddy Dan Allah kada ta Mutu wallahi banshirya rabuwa da itaba,,daddy inasanta Dan Allah daddy kace ta Tashi..
Ganin da daddy yayi ba'a cikin hayyacinsa yaje ba shiyasa ya rungumeshi Yana shafa bayansa..

Sedai yadau lokaci jikin daddy Yana kuka kafin yafara safke ajiyar zuciya" ganin haka yasa daddy fara Magana a hankali..
Garin Yaya ka tafi da yarinyar mutane Har akayimata irin wannan illar,,kana Ina Hakan ta faru daddy ya jera masa wadannan tambayayoyin?

Bakin mashkur Na rawa yace,,daddy kayi hakuri Nima bansan haka zata faru ba,,kasani cewar daddy tare da tsaresa da Ido" wallahi daddy bansani ba,,Dana sanina Hakan tafaru ba,,nayi nayi tabari Amma Duk da haka Saida ta kashemini ita mashkur yaqare maganar cikin gunjin kuka..
Wallahi inasanta banaso Na rasata,, kuskuren ne Yasmeen ta Riga ta aikata mana,,daddy bansan yazanyi da itaba..


Mama na zaune a falo tana kallo Taji fadowar Abu akanta" dasauri ta dago tana kallan yasmeen,, cike da tashin hankali tafara jera Mata tambayoyi"
Yasmeen meya sameki" accident kukayi,,Ko Yan bindiga dadine suka tareku,, Yasmeen Bata Iya amsa mama ba, Saima kukanta data qara saki tana qara shiga jikin mama..
Tureta mama tayi tana cewa" Dan gidanku ki gayamin,,gaba daya kin Tashi hankali to kodai Yan garkuwane suka tareku a hanya..
Qin Magana Yasmeen tayi sabida batajin zata Iya furta Koda Kalma dayane sabida bakin Kishin dake Cin zuciyarta,,jitake inama ta Mutu kota Dena Jin abinda takeji a jikin zuciyarta..
Ganin tayi Shiru taqi Magana yasa mama Tashi tsaye tana cewa to Ina Shi mashkur din yake?
Ni 'yan nan inazansa kaina,,ya Allah ka kawomin dauki" Ke Yasmeen kodai kurma Kika Zama mama ta fada tana kai Mata Duk..
Yasmeen ki Duba jikinki yadda Duk ya baci da jini indai wannan jinin mutum ne to Babu shakka hadari kuka Samu,,da yaushe kuka fita a gidannan baki gayamin ba,,Ina kukaje?

Duk tambayoyin da mama tayi babu Wanda ta Samu amsa,,ita kadai tayi burarinta ta gama,, ganin datayi Yasmeen taqi kulata yasata sakin kuka tare da fitowa waje da gudu tana cewa..
Me Gadi wakaga ya ajiye Yasmeen?
Cikin tashin hankali hankali baba me Gadi yace' hajiya Ai Yasmeen ce ta kashe wata yarinya da wannan alhajin mashkur yazo da ita,,Nima ina nan inajin radio banji abun ba Sai Daga Baya..

Cike da matsanancin tashin hankali da fargaba mama ta dafe qirji tana cewa" kisa fa kace Malam Audu?

Kwarai kuwa Dan gaskiya yarinya ta Mutu sabida Nida kaina nadubata Kuma kinsan ninake sallar gawa a garinmu kafin Na Samu wannan aiki..

Mama taba idajiba ta Koma ciki da gudu ta dauka waya ta Kira Abba"
Tana kuka tace" Alhaji kayi sauri kazo gida ba lafiya"
What!!!
Hajiya Karki gayamin Wani Abu ya faru da 'yar Lele,,Dan Allah ba yadda zanyiba,,kowaye ya tabata Sai inda qarfina ya qare..

Mama batasan lokacin data saki tsaki ba,tana cewa"
To ai shikenan yanzu saika zo kaga abinda kudi da shagwabawa game da sanka suka jama"
Murmushi Abba yayi Yana cewa kedai kullum bakida abokin Kishi Sama da Yasmeen,,yanzu fisabilillahi Idan ban shagwaba lelena ba wazan shagwaba,,da Allah kidena yimin irin haka..

Hawaye masu zafi mama ta goge tana cewa" to ai gashinan abinda gata Yaja Mata" ta kashe "Yar mutane..
Cikin firgice Abba yace" ehhhh hajiya kinko San abinda kike fada,,kisa fa kikace"

A hasale mama tace eh,,abinda Kaji Shi nake fada,,Dan haka yanzu ka dawo gida musan halin da yarinya take ciki,,tana gama fada ta katse Kiran tana zagaye faloon...

Zuwa yanzu ita Kanta Yasmeen hankalinta yatara Tashi Amma Idan ta Tinan ta rabu da damuwanta Sai Taji hankalinta ya kwanta,,Babu abinda Ke Daga Mata hankali illah kukan mama data zauna Kan kujera tanayi tana salati tare da neman dauki gurin Allah.

Ahankali Yasmeen ta matso kusa da mama tana cewa,,pls mama kidena zubda hawayenki Akan wannan banzar,,hawayenki yadena zuba Akan 'yar sadaka mara Gata..
Tasss tasss tasss mama ta dauke Yasmeen da Mari tana nunata da yatsa'
Yasmeen Karki Bari bakina ya fadi mummunar Kalma akanki" Kuda kuke da kudin ki Kuka ba kanku" to wallah ki Sani Idan Har wannan yarinya ta Mutu Bazan Bari ki zauna a gida kinajin dadiba,,wallahi kema Sai an daureki,,shashasha kawai..

Bani wayarki,,hannun Yasmeen na rawa taba mama wayar' Cilla Mata wayar mama tayi tana cewa" ubankine Ze budemin day Zaki Bani ita ahaka,,wallahi kikayi wasa kema Saina lakada Miki Dukan mutuwa kinga Sai ayi biyu...

Hannun Yasmeen Na rawa ta dauka wayan ta cire password ta miqa mama"
Number mashkur mama ta Duba ta danne Kiran..

Mashkur dake kwance jikin daddy Yana kuka yaji wayarsa Na ringin kasa dauka yayi Sai daddyne ya amsa Kiran..

Assalamu alaikum,, daddy ya amsa yanasan sanin wacece,,Dan ba Suna yagani jiki ba,,

Bakin mama Na rawa tace,,nice mahaifiyar Yasmeen" Dan Allah a wanne asibiti kuke?

Seda daddy ya rintse Ido kafin yace,, muna standard hospital,,dan Allah yame jikin,,mama ta tambaya cike da Kunya..

Zuwa yanzu bamusan halin datake ciki ba,,dazu Dai harsun fito da ita Sai kuma aka Koma ciki,,Suna qara Duba lafiyanta..

Wani irin dadi mama Taji Dan harga Allah Idan nijlah ta rasu batasan inda zata sa kantaba..

Bata saurari Yasmeen Ko Abba ba ta dauka mayafi ta fita da saurin gaske Har tana hadawa da gudu..

Yau mama da Kanta tayi drive sabida tsabar zauri da yadda zuciyarta Ke azalzata.



Comments & share





*Momn sultan ce*✍✍✍✍
💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*SHAFA'ATU UMAR.....*



4⃣3⃣&4⃣5⃣


Mama na fita Abba ya sanyo matarsa gidan Yana tuqi cikin kwanciyar hankali"
Guri me kyau yasamu yayi parking,,nan da nan ma'aikatan gidan suka zubewa Suna kwasar gaisuwa,,sedai yau uban gidan nasu be Iya amsasuba sabida saurin dayake ya Shiga ciki yaga 'yar lelensa..
Cikin sauri ya Bude qofar falon,,bakinsa da sallama ya Shiga ciki Yana 'yan Kalle kalle..
Gefe daya Daga cikin kujerun ya hango Yasmeen zaune ta Hada kai da qafa tana kuka a hankali.
Dasauri Abba ya qarasa inda take yana tambaya..

Ke Yar Lele waya tabamin Ke,, zonan ki gayamin kodan kin Daki wancan 'yar masu yawan jejen kike kuka"
Girgiza kai Yasmeen tayi tana fadawa jikin Abba tare da sakin matsanancin kuka Wanda ita Kanta batasan kona Mene ba..
Hankalin Abba ba qaramin Tashi yayi ba,,nan ya Shiga jera Mata tambayoyi sedai Yasmeen ta gagara amsa Koda guda dayane..

Tashi Abba yayi ya Bude fridge"
Ruwa me sanyi ya dauko tare da cup ya zuba ruwan ciki" Da kansa ya Shiga Bata Yana shafa Kanta..
Yasmeen Bata Wani sha dayawaba ta janye fuskanta tana turo baki..
Yaya Dai 'yar Lele kigayamin kodai Wani ya tabamin Ke.
Cike da shagwaba Yasmeen
Tace"
Ba mama bane hadda cewa zata dakeni" Kuma Shima mashkur tureni ya riqayi Yana min tsawa..

Hmmmm kinga abinda nake gayamiki Ko 'yar Lele Amma Duk Da haka kin Nace kince Sai Shi Zaki aura,,Bayan Yana nuna banbanci tsakaninki da 'yar sadaka.
Cike da sangarta da shagwaba Yasmeen tace" Ni Ni fa Nina sanshi,,Kuma nasan daya aureni Ze hakura da ita..

To ai shikenan ita Kuma mama ki barni da ita,,tana ma Ina banji duriyartaba tinda Na shigo?
Abba naji ta Kira mashkur Daga nan ta fita,,inaga asibiti taje Duba wannan shegiyar..

Jinjina kai Abba yayi Yana cewa' kinga Tashi kije kiyi wannan ki cire wannan kayan da suka baci da jini Ko baki gani ba"
Sai yanzu Yasmeen taga jinin dake jikinta.
Cike da kyankyami ta Tashi tana tafiya kama batasan taka qasa ta Shiga dakinta..

Toilet ta shiga ta cire kayan jikinta ta Hada ruwa me dumi ta fada cikin bahun wankan tana ninqaya a ciki" ta jima tana wanke jikinta kafin ta fito,,Bayan tashafe jikinta da Mai tare da turaruka masu kamshi ta Bude wardrobe,,dugawar rigar ta dauka Na material green colour me tsarin orange..

Bayan ta gama shiryawa ta dauka waya ta Hau Kan bed ta fara karanta Daga cikin littattafan momn sultan..


Ahankali mama take tuqi gabanta Na tsanan ta faduwa,,ahaka harta kai hospital,,tana zuwa ta Kira mashkur daddy yasake dauka..

Na qaraso abinda mama tace cikin sanyin murya da kunya'
Nan daddy yayi Mata kwatancen inda suke..
Bata Wani sha wahala ba ta ISA inda suke tana kallan mashkur dake kwance a cinyar daddy,,Har yanzu bai Dena kuka sedai zuwa yanzu ya rage kukan Sai ajiyar zuciya yake safkewa Akai Akai..

Kasa Magana mama tayi ta nemi gefensu ta tsaya tare da rungume hannunta a qirji tana addu'a"

Har wurin karfe 4 na yamma likitoci Basu fito ba,,ganin haka yasa daddy daukan waya ya Kira mummy Yana San sanar da ita..

Mummy na Daki zaune Kan bed yayinda lateefah Ke dauke Kan carpet tana shirya kayanta cikin akwati Dan gobe da sassafe jirginsu Ze Tashi,,mummy Taji wayarta Na ringin..
Mummy daddyne Dan Allah Idan kin dauka kibashi hakuri kigayamasa gobe da safe Zan tafi,,nasan Idan yadawo ya ganni Allah fada zeyimun..

Keni da Allah Bani waya kada ya tsinke,,mummy Na Daga wayan daddy yace,,hajiya Bazan Samu dawowa da wuri ba"
Ok,,Amma lafiya kace haka,,kaida kake dawowa da wuri?
Nan daddy ya kwashe Duk abinda ya faru ya Gaya mummy,,ai be Ida zancen ba,,mummy ta tuntsire da dariya tare da tafa hannu tana cewa..

Kai Amma Yasmeen ta birgeni"toku me kuke a hospital tinda ance ta rasu Ai shikenan kaga Nima Na yadda kwallan mangwaro Na huta da Kuda..

Ran daddy a mugun bace ya daka mummy tsawa Wanda tasa mashkur firgita ya Tashi zaune,,kafin ya tambaya daddy abinda Ke faruwa sukaga Dr ya fito Yana goge gumin fuskansa,,

Tsaki daddy ya ja tare da katse Kiran suka bi Bayan Dr..
Yana Shiga office daddy yabi bayansa mama da mashkur suka tsaya a tsaye Suna sauraran abinda dr Ke Gaya daddy..

Mashkur Najin dr yace,, nijlah Na buqatar jini ya saki murmushi tare da yin sujjada a qasa Yana godewa Allah'

Be jira fitowan daddy ba ya dawo Dakin da aka kwantar da nijlah ya faki idon likitocin ya fada dasaurin gaske..
Yana Shiga ya tafi bakin gadon dasauri,,fuskanshi dauke da murmushi"
Kallan yadda take bacci ya Shiga yi Yana murmushi,, ahankali ya kai hannunsa Kan lallausan gashinta ya Shiga shafawa ahankali ahankali tare lumshe idansa,Wani irin yana Mai wuyar misaltuwa ya ziyarci zuciyarsa,,tare da farin ciki na ratsashi tako Ina ajikinsa.

Cike da shauqin kaunarta yakai bakinsa yayi kissing lips dinta Yana cewa" raguwa daka Dan tabaki Sai langwabewa mutane kama wacce ta Mutu" Sai kuma yayi murmushi Yana shafa lips dinta..
Yana cikin haka yaji an Tura qofan dasauri ya janye hannunsa a Kanta Yana Kallan kofan,,daddyne Sai mama suka shigo Dakin..
Sallamarsu ya amsa tare da Tashi tsaye ya Tura mama kujeran,,mama Bata Iya Zama ba ta tako Har zuwa bakin gadon tana kallan yadda nijlah Ke Jan numfashi ahankali..

Girgiza kai mama tayi ganin kankantan nijlah Amma Duk Da haka Yasmeen ta Iya zage kwanjinta Akan Yar karamar yarinyar"
Addu'a mama ta Shiga tofa nijlah Bayan ta gama ta juyo tana kallan mashkur,, ahankali mama ta Bude baki tana cewa..

Dan Alhaji kuyi hakuri Da abinda ya faru" yarone yanzu ka haifeshi Baka haifi bakinsaba...

Babu komai cewan daddy Yana murmushi" Sai Dai mu godema Allah tinda gashi yarinya da sauran kwananta a gaba"

Hakane sedai Duk da haka Ina Mai Baku hakuri musamman ma kai mashkur sabida kai akayima" Kuma nizan jamata kunne,,Na tabbata Hakan Baze qara faruwa ba..

A ciki ciki Mashkur ya amsa Yana Kallan gefe Dan tinda suka shigo be Daga kai ya Kalli kowa ba..

Idan akwai abinda Ake buqata Sai a gayamin,,inaso zanje gida Na dawo,,inyaso Saina kwana a gurinta basai kun Gaya iyayen yarinyarba???

Bakomai Nima nijlah kyatace zanyi duk abinda ya dace cewar..

Dan risinawa mama tayi tana yiwa daddy godiya tare da cewa nizan wuce tea Na taho dashi Idan ta farka Sai a Bata..

Dasauri mashkur yace" ah ah kibarshi kawai mama hakama Mun gode basai kin dawo ba..

Jikin mama a sanyaye tace kana ganin ba matsala mashkur' kai tsaye mashkur yace eh babu..

Sallama mama tayi musu ta fita a Dakin jikinta Duk a sanyaye Duba da yadda mashkur yake amsata kama bayaso,,taso ace yabarta ta zauna da nijlah Dan tana ganin zatafi kowa Bata kulawa..

Tana fita daddy ya Hau Kan mashkur da fada ta inda yake Shiga batanan yake fitaba" shidai mashkur be Iya cewa komai ba Banda baqin ciki Babu abinda kecin ransa..

Kaima kanasan Zama mara Kunya kenan' Koka manta yarta kakesan aure" Amma tana Magana kana sa baki,,kokai Zaka zabi yadda za'a Kula da nijlah..
Ahankali mashkur ya girgiza kai Yana Kallan daddy,,Sai da daddy ya gama kafin mashkur ya Bude baki a hankali yace"
Daddy nibanqi mama ta zauna da nijlah ba sedai daddy abinda Baze taba yiwuwa Kenan ba,,Ina tsoro Kar cikin dare Yasmeen ta qara zuwa inda nijlah take ta illatamin ita"

Gafara can ka rufemin baki,,soqoqon banza kawai,,Ina da Rana tsaka ita Yasmeen tayimata haka,,Kuma a gabanka Baka Iya tsinana komai ba Sai aikin kuka,,ka kirani kagayamin kuna hospital Baka Iya ba Sai dr Jamil ne yagayamin yaganka anan kafin Na baro office nazo..

Turo baki mashkur yayi kama qaramin yaro yace' to daddy Yaya zanyi da ita nayi nayi ta dagata taqi"

Kuma kake mana kazauna da ita anan Bayan bakasan yadda zakayi da itaba ita ta sake kawomata Hari?

Daddy ya tambaya"

Sosa kai mashkur yayi Yana cewa Hakan Bama zata sake faruwa ba insha Allah"

To Allah yasa yanzu Sai muje a gwada jininka day nawa Dan likita yace da yiwuwar a qara Mata jini danta zubda jini sosai..

To mashkur yace yana me tausayawa nijlah
Showing 30001 words to 33000 words out of 65025 words