ta Tashi ta fita a Dakin cike da tashin hankali ta fita.

Tana fita mashkur yasa hannu ya goge hawayen tausan nijlah Dan ba'a San ranshi yayi Mata haka ba yayine kawai sabida mummy Taji Dadi ta Kuma barshi da nijlah Dan yasan Babu makawa mummy zata Iya cewa saiya saki nijlah adaidai wannan lokacin Duba da halin daya tsinceta a ciki..

Kallan Mummy mashkur yayi Yana cewa'
Mummy kiyi hakuri nizanyi maganinta,, yanzu ki Tashi Na kaiki hospital'

Cike dajin ciwo mummy tace ' Bazan Iya tashiba auta' ka Kira Dr kawai yazo ya dubani anan..

Beyi Magana ba yayi dealing number likitan..

Nijlah na fita ta zauna bakin kofa tana kuka tare da Dana sanin yadda da rabuwa da kaka Ashe dai talauci yafi Wani tashin hankalin sauqi,dama shirme nake danake ganin Zan Samu farin ciki Idan nayi aure ya Allah nijlah ta furta daqarfi tana yarfe hannu sabida Har yanzu bayanta be gama saisaita ba.

Hannu tasa ta shafa gurin aiko tana cirewa taga jini kwance a hannunta' wayyo Allah nijlah saita Tashi da gudu tana zagaye get din tana Kiran kaka da laman'

Dama haka aure a birni yake gashi Na kawo kaina inda za'a kashemini' wallahi Bazan zauna ba gida Zan tafi'

Bata qara neman shawaran zuciyantaba ta tashi,,Bata Ko dauki takalmi ba ta fita da gudu tayi titi' Sai da tayi tafiya mai Nisa kafin taga me napep ta tsayar dashi' .

Qoqarin tsayawa yake nijlah Tasha gabansa Aiko ya bigeta ta fadi gefe' tsoro da tashin hankali suka sa me napep ya gudu Sai wata matashiyar budurwa dake Bayan me napep dince ta tsaya kasan cewar layin ba mutane sosai ta nemi dauki Bata samu ba,,haka ta cire mayafinta ta dauka nijlah tasa a Mota tana mejin tausan yarinyar ta tafi asibiti da ita...


_________


Haba kawata yakamata ace munyi shagali a bikin nan gashi wannan corona tazo tayi kaka gida Har ansa dokan ta bashi a kowanne state kinga Ko Dole a Daga biki suwa Bayan Sallah..

Zaro Ido mubeena tayi tana cewa'haba kawata keda Zaki addu'a ayi bikin nan a gama saiki kawo wata magana' Naga Dai ba dolene ayi chasu a biki ba.

Ke kinga mubeena kibari kawai muyi a lokacin da zafi mana Dadi Ko bakisan ita Yasmeen'yar Gata bace Dan haka yakamata lokacin Duniya tasan da aurenta,, zee ta fada tana kallan yasmeen.

Yatsina fuska Yasmeen tayi tana hararan mubeena' Sai kuma ta Kalli Zainab tana cewa yauwa zee gayamata gaskiya to Idan ba'a Daga biki ba Sai ki gayamin ta inda abokan Abba zasu shigo qasar kinsan abbana bashida abokai dayawa anan yawancinsu ba 'yan qasa bane..

Gaskiya ne kawata suka tafa da zee'

Cikin rauni Yasmeen tace' zee nifa inaga kama mashkur Baze yadda da Hakan ba?

Dan Wallahi ya matsu da maganan auren nan'

Ai Toba Dole ya Daga qafa ba,,nifa Dama gani nake wannan mijin naki zee mugun takura Ke Allah yasa kin tsuma jiki sosai,,dariya suka sa zasu qara Magana mama ta shigo Dakin tana cewa'

Ku Kuma bakijin yinwane kuketa Hira haka Baku neman abinci Yasmeen..

Kuyi hakuri kwana biyu banajin dadi sosai.


Comments & share






*Momn sultan ce*✍✍✍
💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘


*STORY & WRITING ...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*BABBAN YAYA' H_UMAR....*



6⃣8⃣&6⃣9⃣


Mama yanzu zamun fito suka fada cike da ladabi'' ku Tashi haka itama hiran ba Dadi takeba ana Jin yinwa.
Basu qara Magana ba suka Tashi sukafi Bayan mama data fita tana cewa' kudai 'yan Mata Baku da aiki Saina rawan kai Idan kukaji biki' kai ni nagaji da wannan shirye shiryen Baku daqi chi yaqi chinyewa.

Jummai' kina ina' banga kin Hada kayan abincin ba?
Hajiya nagama yanzu Zan kawo'

DA gudu jummai me aiki ta fara jera manyan kuloli Akan dining tana cewa'
Ranki ya dade Dama Yasmeen ce tace kada Na raqa aje kayan abinci Idan ba Zama akayi za'a Ciba.
Murmushi mama tayi taja daya Daga cikin kujerun ta zauna tana cewa kai ita Dai wannan yarinya ta fiye tsirfa' Amma bakomai kema kin kusa hutawa da jaraban yasmeen' dariya jummai tayi tace' eyyah hajiya aiba komai..

Bata fuska Yasmeen tayi tana cewa' to Idan kin gama gulman saiki Bani wuri Ko?
Sum sum jummai ta shige kitchen tana Bada hakuri.

Mama ta Kalli Yasmeen tayi Dan qaramin tsaki tana cewa' Wallahi Yasmeen ki gyara balinki,, shikenan Ke baki da aiki Saina tsanar tsalaka' shin Ke kikaba ubanki arziqin da kike tinqaho dashi? Shiru Yasmeen tayi mama ta qara daka Mata tsawa tana cewa' tambayanki nake? Bakin Yasmeen na rawa ta Bude baki zatayi da Magana sukaji gyaran muryan Abba dake shigowa cikin falon.

DA gudu Yasmeen tayi Kan Abba tana boyewa a bayanshi' hannu yasa ya riqeta sosai Yana murmushi,,nan da nan Yasmeen ta shagwabe masa tana cewa ita bazataci wannan abincin ba.

Indai wannan ne Karki damu kinji 'yar Lele, hannu Abba yasa a aljihunsa ya Ciro kudi masu yawa ya miqa mata' kinga amsa wannan kije Duk Wani restaurant dayamiki a fadin garin nan kici Duk abinda kikeso kinji 'yar lelen Abba.

Wani irin Dadi Yasmeen Taji Dan harga Allah abbanta Na nuna Mata kauna irin Wanda Bata taba gani ana nunama wasu ba' rungume hannun Abba tayi tana cewa' abbana nagode Allah yaqara Budi da wadata yarabaka da 'yan bakin ciki.

Ameen 'yarta Tashi kije kada yinwa ta kamamin Ke' dariya Yasmeen tayi tana cewa Abba Nida kawayena ne gasu can ma.

Sai yanzu Abba ya Kula dasu mubeena nan suka sunkuya Har qasa Suna gaidashi,,fuska sake ya amsa Yana tambayan Basu iyayen,,wasu kudi ya Ciro ya miqa Yasmeen Yana cewa'amsa wannan Ku qara aibansan kunada yawa haka ba..

Ah ah abba kabarshi wannan ma ya isa' kidai karba Dan bakisan dawa zaku hadu a gurin ba amsa Yasmeen tayi ta koma daki da gudu ta dauko mukullin Motan ta ta dawo tana cewa kuzo mu wuce.

Girgiza Kai mama tayi ta zuba nata abincin ta dauka tana kallan abba sedai batace komai ba ta shige daki tamejin takaicin lalata Mata yarinya dayayi' da Ido abba ya vita Yana cewa' hajiya yau kuma ba sannu da zuwa,kika wuceni kina harara..

Ko juyowa mama batayi ba ta,,ganin haka yasa abba bin bayanta Yace' wai bakiji ina magana ba?

Dagowa mama tayi ranta a bace tace' eh banji ba.

Hmmm nasan kinjini sarai' da dai kince sarautankine ya motsa zanfi yadda.

Cike da takaici da mama ta bude baki ahankali tafara magana' haba abban Yasmeen sai yaushe zaka dena Dora yarinyarnan a keken bera' kafa kusa kaita dakin miji Amma bazaka dena Nuna Mata wannan gatan ba' sai kuma ta sassauta murya tana cigaba da mama' wallahi ina tsoran auran da Yasmeen sabida babu namijin daze iya Nuna Mata gatan dakake bata Dan wannan ya wuci gata sai dai barna.

A kul bakinki ya qara furta irin wannan maganar' wai shin saunawa Zan gayamiki kidena samana Ido' kodan ke Baki tashi cikin irin wannan gatan ba',,shiyasa kikesan yiwa yarinya baqin ciki?

Dafe qirji mama tayi tana kallan abba,,bakinta na rawa tace'bakin ciki fa kace?

Eh shine mana' aiban ganekiba sai yanzu dazan auran da 'yar Lele Naga har wani qiba kika qara sabida farin Zata tafi tabar Miki gidan ko?

Wasu hawaye masu zafi suka fara bin quncinta nan tasa hannu ta gogesu' bata qara cewa komai ba ta fita tabar masa dakin' yinin ranar ki abinci mama bata iya ciba...


Dr na dauka mashkur ya gayamasa abinda ke faruwa' nan da nan Dr Ahmad ya harhada takaddun gabansa ya da fita da sauri ya nufi gidan mummy' da zuwansa yafara dubata,,ya Jima Yana 'yan gwaje gwajensa kafin ya dago Kai Yana kallan mashkur'

Dr lafiya dai Naga kana kallona' Dan Allah Kada kace da matsala' gyara zaman glass dinsa yayi Yana cewa'ba wani matsala' bane sedai mummy ta Samu buguwa sosai shiyasa takasa takawa Amma nan da hour daya Zata iya Jin daidai.

Ajiyar zuciya mummy ta safke daga ita har mashkur suna godema Allah dayasa bata qarye ko taji ciwo me yawa ba' tashi Dr Ahmad yayi Yana cewa'abokina nizan wuce sabida nabar patients suna jirana.

Tashi mashkur yayi Yana masa godiya ya rakashi har jikin mota' anan ne Dr Ahmad yake cewa kaga na manta da Allah ayimata ruwan dumi yanzu sabida taji dadin gurin.

Yanzu ki zansa ayimata Dana Shiga ciki' dariya Dr Ahmad yayi Yana cewa'
Mijin kwaila angon Yasmeen ina Ka boye nijlah bangantaba?

Rasa Rasa gaban mashkur ya Fadi sedai ya danne Yana cewa' Kai niwai narasa meyasa kuka samin ido' to indai nijlah ce babu me sake ganemin ita.

Dariya Ahmad yayi Yana cewa ango ango nan ya tada mota ya tafi mashkur na daga masa hannu.

Dr Ahmad na tafiya mashkur yafara zagaye gida Yana Neman nijlah,sedai duk inda ya duba be gantaba hankalinsa yafara tashi' nan yafara kwala Mata kiran..
Nijlah nijlah nijlah' ya Kira sunanta yafi sau burin masaqi ganin bata amsaba yayi tinanin ko bacci tayi tana wannan rigiman nata..

Nan ya yaci gaba da nemanta sedai duk inda yakesa ran zeganta ya duba bata nan' dasauri ya dawo bakin get Yana cewa'

Malam Musa Kai malam musa' da gudu malam musa' ya fito Yana karkarwa yace
ranka ya Dade gani'

Dan Allah Dan annabi kayimin Rai Kada Ka koreni daga wannan gidan' wallahi bazan qaraba'

Kai malam musa' niba wannan ba' Baka ga wannan yarinya ba?

Ranka ya Dade wacce yarinya?

Cikin fada mashkur yace' waiya ina tambayanka kana dawomin da tambayana'

Nijlah nake nufi tana ina mashkur yafada cikin tashin hankali.

Bakin Musa na rawa yace' ranka ya Dade ai tinda kuka Shiga ciki Naga ta fito da gudu ta fita wace.

What!
What,, me kakesan gayamin' kana nufin nijlah ta fita?

Eh ranka ya Dade ai tafi hour da fita a gidan nan.

Hannu mashkur ya Dora akai Yana cewa'shikenan malam musa' Ka kasheni'

Wata wawar chakuma mashkur yakaiwa Musa hankalinsa a tashi ya matse masa wuya Yana haqi Yana cewa' wallahi saika nemomin matata nan da nan tari ya tirniqe mashkur Amma duk da haka be saki Musa me gadi ba..

Tin Musa na qoqarin kwatar kanshi harya kasa yafara kakari Yana riqe da hannun mashkur.

Jin ihun yayi yawa yasa masu aikin ban ruwan fulawa suka fito da gudu suna kallan tashin hankalin dake faruwa'

Sunyi iya Kar qoqarin su akan suga sun kwaci musa a hannun mashkur sun kasa hakan yasa suka Shiga ciki da gudu suna Kiran mummy'

Mummy dake zaune ta kasa tashi' taji hayaniya yayi yawa a kofan falon' nan ta Kira Maryam tana cewa' Maryam jeki duba kiga abinda ke faruwa' nasan koma menene baze wuci wannan aljanar ta hadashiba.


Dasauri Maryam ta fita itama sai gata ta dawo tana cewa mummy mashkur, mashkur ne zeyi kisa.

Ai mummy mantawa dayi da ciwan kafanta sai gata ta tashi tana dingisawa tare da bin bango ta fito tana salati, daidai lokacin daddy yayi horn, Maryam ce ta iya budema daddy Aida gudu daddy yayi Kan mashkur Yana cewa.

Kai mashkur Baka da hankali Meka sha' Ka sakeshi nace saika kashesa?

Sabida zuwa yanzu Musa yagama galabaita harshensa harya zazzago sabida azaba.

Mashkur be iya magana ba sabida yadda yake jinsa,,haka majiya karfi suka taru suka banbare mashkur a jikin musa' nan take Musa ya zube qasa sumamme..

Lafiyayyun Mari daddy ya safkewa mashkur Yana cewa'Baka da hankali kisan Kai zakayi kome' mashkur be damu da Marin daya Shaba Saima qoqarin kwato Musa yake daga hannun jama'a Yana cewa.

Karku fita dashi wallahi Saiya dawomin da matata,, ganin abun na mashkur ya wuci qima daddy yafara tofa masa adduoi.

Banda kuka babu abinda mummy take gashi an tambaya mashkur abinda ya hadashi da Musa yaqi fada ko ince yakasa magana' matata kawai yake kira,, ganin babu alamun nijlah yasa mashkur fasa wani irin ihu ya zube a qasa..

Nan da nan jini yafara bin hancinsa sabida ya riqa ya sallamawa samun farin ciki yakuma San nijlah bazata iya dawowa da qafantaba....


Cike da tashin hankali daddy yasa mashkur a mota ya tashi hospital dashi' nan mummy ta zauna tana tsinewa nijlah.


_____________


Cikin bacci yakumbo tafara surutai tana Kiran nijlah tare da shiru Shure da qafanta'

A hankali malam yafara tashin ta ta hanyar taba hannunta Yana cewa' yakumbo, yakumbo.

Firgigit ta Farka tana salati.

Haba yakumbo sai yaushe zaki dena mafarkin nijlah idan ban mantaba tinda nijlah ta tafi saikinyi mafarkinta' mafarkin dare be ishekiba saikin hada Dana Rana?

Numfashi Kaka ta safke tana cewa' kayya malam' wallahi hankalina yakasa kwanciya' gani nake kama munyi gangancin bashi yarinyar nan ya tafi da ita'

Babu wani Kaka Insha Allah nijlah na cikin kwanciyar hankali.

Hakane Amma gaskiya wannan mafarkin danayi na yanzu ya firgitani' nidai kawai kaje kayimana sadaka ko hankalina ze kwanta.

Yakumbo sadaka kuma' Nima dazan Samu me Bani wallahi so nake' nan yafara zaro aljihun wandansa Yana cewa' duba nan ki gani' wallahi Banda naira Goma nan Bani da ko biyar..

Malam kaje ko kuli kuli Ka siyama yara inyaso saika rarrabashi kanana Ka bayar na tabbata Allah ze dubi marainiya da idan rahama koma a wanne Hali take taji dadi'

Idan kuma ba haka ba nizan tafi Gona ko kanya na debo sainayi sadakanta Kaka ta fada tana qoqarin tashi tsaye..

Riqeta malam yayi Yana cewa keda Baki da cikakkiyar lafiya ina zakije' ki zauna kawai ninasan abinda zanyi..

Hawaye Kaka ta share tana cewa' malam Ka taimaka ninasan abinda nagani a cikin mafarkina' sai kuma ta daga hannu tana addu'a..






Yawan comments yawan typing


Pls share.





*Momn sultan ce*✍✍✍
💘💘 *'YAR SADAKA..*💘💘


*STORY & WRITING ...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*QUEEN MARYAM....*



7⃣0⃣&7⃣1⃣


Addu'a sosai yakumbo ta riqa yima nijlah tana qara tuba ga Allah Dan ita gani take kama laifinsune da suka kasa bata farin ciki gashi yanzu ta tafi ta barsu,,Basu San halin da take ciki'
Fita malam yayi ya sai kuli na naira goman data rage cikin aljihunsa ya raba yara' abinka da rugan kauye nan da nan yara suka zagayeshi sedai befi mutum goma suka samu ba sauran sai hakura wasu suka koma gida suna kuka..

Dakin Nasir malam ya wuce acan ya sameshi' bayan sun gaisa ya Shiga yimasa tambayoyi kama yadda ya saba' a koda yaushe'
Nasir nidai hankalina yaqi kwanciya dan haka nakeso Ka shirya muje can birni Naga marainiya'

Gaban Nasir ne ya yanke ya badi Amma Saiya dake Yana cewa' ah ah malam kayi hakuri Dan ko jiya munyi waya da mashkur harya hadani da nijlah mun gaisa,, kaga tamace a gaisheku kuma nan da 'yan kwanaki zasu kawo muku ziyara.

Washe Baki malam yayi Yana cewa Kai alhamdulillah naji dadin wannan labarin' Bari na koma gida da sauri na Sami yakumbo itama nasan zatayi farin ciki ba kadan ba'

Sosai ma kuwa Nasir yafada Yana Allah Allah malam ya tafi Dan Shima zuwa yanzu yafara tsorata da lamarin mashkur gashi lokacin tafiyansa gida yayi Yana tsoran cewa zeje Kaka tace bata yadda ba..

Har malam yayi nisa ya juyo Yana magana' Kaga Nasir duk da haka kayi qoqari idan mashkur din ya Kira saika kirani mu gaisa'
To malam zakajini in Allah ya yarda.

Malam na tafiya Nasir ya dafe Kai Yana cewa'Kai gaskiya na hada kaina da aiki' ni dai fatana daya' Allah yasa mashkur ya riqe Amana'
Tashi yayi ya tafi inda suke waya ya Kira layin mashkur sedai Yana ringing ba'a dauka ba,,gajiya Nasir yayi ya dawo gida ranshi babu dadi..


Sosai matashiyar matar ke gudu akan titi' kafin ta qarasa hospital harta Kira babban likitansu' nan ta sanar masa tana da mara lafiya gatanan zuwa asibitin.

Tuni babban likitan yafara hada manyan likitocin dake asibitin yana sanar musu nan suka tsaya zaman jiran qarasowarsu,,yayinda nurses suka qarasa bakin get dauke da gadon tura mara lafiya.

A guje motar ta qaraso cikin asibitin' matashiyar duk ta hada zufa ta gigice,,hankalinta a tashe, hadda ita suka fara qoqarin fito da nijlah a cikin mota, Kan gadon marasa lafiya aka dorata' likitoci da Kansu suka Shiga tura gadon da gudu aka Shiga da ita dakin duba marasa lafiya.

Nan take likitoci suka Shiga dubata tare da bata taimakon gaggawa' Basu jimaba suka samu nasaran dawo da numfashinta daidai'

Da kuka nijlah tafara tana Kiran Kaka tare da birgima akan gadon tana niyyan faduwa qasa'
Daya daga cikin likitocin ya leqa waje Yana cewa'

Bismillah husna zaki iya shigowa'

Cike da rawan jiki matashiyar matar da aka Kira da husna ta Shiga tana yiwa Dr godiya'

Kan gadon da nijlah ke kwance ta qarasa tana yimata sannu' kallanta kawai nijlah keyi sedai zuwa yanzu ta dena kuka Dan ba wani ciwo taji ba illah tsorata da tayi ganin yadda napep din yayi kanta..

Hannu husna tasa da niyyan taba nijlah' dasauri nijlah ta janye tana turo baki' tare da cewa ni ah ah.

Murmushi husna tayi Wanda ya bayyanar da kyawun fuskanta tana magana cike da tausasawa kiyi hakuri yarinya nice na kawoki nan bayan hadarin da kika samu' sunana husna.

Fita likitocin sukayi suka bar dakin husna na qoqarin Jan nijlah da jikinta'

Kanwata ki gayamin sunanki Saina Kira gidanku Azo a tafi dake?

A hankali nijlah ta bude baki tace' sunana nijlah,, sedai Bani da kowa inda nake basa Sona kullum Duka na suke suna zagina' saita sauko qasa tana kuka ta kuma riqe qafan husna'
Aunty Dan Allah ki tafi Dani ki kaini gurin kaka' zasu kasheni..

Tinda nijlah tafara magana husna ta lumshe ido tana mejin tausan nijlah duk da batasan wacece itaba' hannu tasa ta janyo nijlah jikinta tasa hannu biyu ta rungumeta tana shafa bayanta'
Kiyi hakuri kinji nijlah Insha Allahu Zan Kula dake har zuwa lokacin dazan hadaki da iyayenki..

Aunty Bani da iyaye ance sun mutu' indai ba lahira zaki kaini ba' dariya husna tayi tace ah ah Niba lahira Zan Kai 'yar kanwataba,itama nijlah murmushi tayi tana boye fuska tare da goge hawayenta..

Hannu husna tasa ta riqa goge Mata tana cewa'kidena kuka' Insha Allahu kukanki ya qare kinji kanwata.

Wani irin murmushi nijlah tayi tana kallan husna tace'aunty dagaske' dagamata Kai husna tayi Dan ita ba qaramin dadi taji na haduwa da nijlah' koba komai Zata Debe Mata kewa kafin ta kaita gidan iyayenta..

Suna cikin haka nurse tazo yiwa nijlah allura' nan fa nijlah taqi tsayawa Saida husna ta bude jakanta ta dauko wasu chocolate ta riqe a hannunta tana cewa' ki tsaya ayimiki Saina Baki wannan.

Duk da nijlah batasan menene ciki ba Amma haka ta qanqame husna aka yimata alluran' sallama aka Basu suka tattara suka tafi gida...

Tin kafin ta qarasa wayanta ya fara ringing' dauka husna tayi ta Kara a kunne' daga daya bangaren aka
Showing 51001 words to 54000 words out of 65025 words