kalilan nijlah da kawayenta suka cika dandali da jama'a" sosai gurin ya cika yakuma kawatar nan fa dandali me kidan kagane yasaki kalanginsa tare da masu kidan kwarya,,masu Kayan saidawa Suma baa barsu Baya ba sun zo..

Kamar yadda akeyi a kowanne biki haka nijlah da kawayenta sukayi Dan sun cika dandali da jama'a anata wasa irin na Fulani,tare da al"Ada irin ta da..


Liman dake tsaye Suna Magana yace,malam kama kida nakeji a dandali" eh Liman Nima haka nakeji Kuma Dai yanzu ba lokacin zuwa dandali bane"

Suna cikin haka saiga wasu yammata Suna tafiya,,Malam ne yace ku yara Ina zuwa,, Malam muna wasan bikin nijlah ne,,tafada tana cigaba da tafiya.

Cike da mamaki yace Ina ita nijlah,,tana dandali tabasu amsa ,, murmushi Malam yayi Dan yasan nijlah zata aikata Duba da yadda takesan auren,,a Fili yace yaro yaro ne kajifa Liman bikin aure sukeyi a dandali.

Eh Ai ta birgeni kaga baza'ayi aure irin Na yaseer da fatima ba,,dariya suka sa,,Liman yace Aiko Yau dandali Ze dauki jama'a Nima baza'a barni Abaya ba..
Tinda suka fita aka zo aka Gaya yakumbo nijlah Na dandali,, murmushi yakumbo tayi ta Rasa inda zatasa Kanta,shin me zatayi farin ciki Ko me..
Ta tabbata Idan tayi baqin ciki ta yiwa Allah butulci Dan haka ta karkata zuwa farin ciki nan itama ta tafi dandali Dan Taya diyar Tata farin ciki..

Bayan tafiyarsu Liman Nasir be bisu dandali ba Dan yace saiyaje ya taho da ango.

Sosai ya riqa sauri harya kai Daki,,nan ya Shiga Yana Kiran mashkur,, mashkur dake zaune Yana Hada Kaya zuciyarsa na quna ya dago jajayen idanunsa ya zuba Nasir.
Dasauri Nasir ya qarasa kusa dashi ,hannunsa ya riqe yace,, mashkur lafiya naganka haka kama Wanda yayi jinya Na wata guda.

Kabari kawai nasir Ina cikin tashin hankali,,ban taba Shiga cikin matsala irin na yanzu ba,,Dana dauki abun da sauqi yanzu Ko magane shayi ruwane,,
Nasir adaidai lokacin da aka dauramin aure Sai gashi a lokacin iyayena da 'yan uwana sukesan rabani da wannan gari Nasir yaya zanyi..
Haba mashkur Kamar yaya, meyasa Zaka kayawa mummy wannan aure Bayan kasan halin mummy" cikin faduwar gaba mashkur yace.

Ban gayamata ba Nasir kafi kowa sanin yadda mummy take Sona take kaunata,,Na tabbata inda mutuwa zata zo daukana mummy zata Iya fansar Raina da nata" Amma kaga mummy tadau zafi Dani harta Kira manyan yayyena ta gayamusu..

Nasir Bani da yadda zanyi,,yazama Dole a Yau Dinan nabar garin nan indai inasan zaman lafiya.

What! Mashkur me kake nufi,,yaya zakayi da nijlah??

Nasir Zan dauki matata,da ita Zan tafi,,Iya wuya Ina tare da ita..

Niko Nace Kamar yadda muke Kenan lolxx....




Kudaure kuna sharing labarinan, Domin wasu su amfana.


Comments & share.



*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*N@DI@*



1⃣5⃣&1⃣6⃣


Wayyo Allah,,yau Naga ta kaina yanzu mezan Gaya iyayen yarinyarnan,,zagaye titi Bello ya riqayi Yana kallan Motan har Saida suka bacewa ganinsa kafin ya daga qafa yaname danasanin amincewa da rakiyan nijlah..
Yanzu mezan Gaya Kaka,,wanne dalili nake dashi Wanda ze tabbatar musu da maganata gaskiya ce,,sosai ya zurfafa cikin tunani Yana tafiya Yana hada hanya a haka harya Kai kauyen kankan,Yana zuwa dakin Nasir ya Shiga nan ya Samu Nasir ya zuba tagumi Yana tinanin rayuwar kadaicin dazeyi a wannan kauye Shi Daya ba abokinsa..
Ko sallama Bello beba yafara da masifa,,Kai Ashe wannan abokin naka bashida kunya,,miskilancin banza yakewa mutane"" dagowa Nasir yayi Yana kallan Bello da jajayen idanunsa yace" lafiya Bello,,Naganka anan?
To a ina zaka ganni Saida muka Shiga mota abokinka ya hankadoni waje,,yace wai ba inda Zan bishi daga Shi sai matarsa zasu tafi,,yanzu me kake tsammanin yakumbo ya dauka,,ni wallahi harna Fara tinanin mashkur Dan yankan Kaine..
Tinda Bello yafara magana Nasir yake dariya harya Kai Aya Nasir be dena dariya ba yanayi Yana kallan Bello,,haushine yakama Bello nan ya Fara hararan Nasir Yana cewa,,Ara ta kanni indai Yanke Kan nijlah zakuyi kaima bamu barinka Ka fita lafiya a wannan kauye..
Nasir be kulaba Saida yagama dariya kafin ya kama hannun Bello Yana cewa,, cool down abokina,,kaga niban iya yaran arna ba,,idan zaka gayamin da Hausa ko fulatanci Ka gayamin..
To shikenan zauna muyi magana,,wacce magana zamuyi alhalin an tafi da nijlah bamusan inda suke ba,,yanzu idan kaima kabi dare Ka gudu ina muka kama..
Haba Bello Ka kwantar da hankalinka nagayama babu wata matsala,,kuma ninasan abinda yasa mashkur yayi haka,,yanzu idan Kaine Ka tafi kiwan shanu sai Ka dawo gida da Mata,,wanne dalili zaka Gaya iyayenka" shiru Bello yayi Yana nazari kafin yace,,Zan gayamusu tsintota nayi a hanya,,to kagani kaima karya zaka Gaya iyayenka,,to tayaya kake tinanin mashkur ze tafi dakai ga kuma nijlah Wanda ya aure batare da Sanin iyayensa ko danginsaba..
Shiyasa akace yabarta anan yafara zuwa ya sanar da iyayensa kafin yakai musu ita,,yanzu ya zeyi Kenan,,Nima bansani ba cewan Nasir Yana qara cigaba da magana..
Inaga wani tinani yayi shiyasa yace Ka dawo shize tafi da nijlah,,Dan haka nakeso kace Kaine kafasa zuwa birni kace su tafi kawai sabida gani kuna ganina,,duk ranar dazan tafi saimu rankaya daku kuje can birni Kuga inda nijlah take,,koya kake gani za'ayi??
Amma Nasir tayaya kake tinanin yakumbo da Malam zasu yadda da wannan karyan,,zasu yadda sai kaqara da cewa dare ne yayi Baku samu mota ba,,dakyar aka samu guda shima gurin mutum dayane,,shine mashkur ya zauna ya Dora nijlah akan cinyensa suka tafi..
Eh to gwara wannan shawaran Amma bazan fita a dakin nan ba sai dare,,hakan yayi,,nan dai suka cigaba da tattaunawa Nasir Yana qara kwamtarwa sa Bello hankali.......

*************

Karfe 1 na Rana a garin Kano yama aunty lateefah,tinda ta Shiga gidan tafara Kiran mummy,,duk ta inda tabi ma'aikatane ke gaisheta sedai ba Wanda ta amsa tana tafiya tana Kiran mummy harta isa dakinta..
Kwance ta Sami mummy ta zuba tagumi tana Kiran layin mashkur,,mummy na ganin lateefah tayi cilli da wayan tana cewa,, shikenan mashkur,, shikenan tinda bayana kakesan gani,,da gudu lateefah ta qarasa kusa da mummy tana tambayanta?
Mummy meya faru da mashkur menene kuma,,ko haryanzu be dawo gida ba?
Ina ze dawo lateefah yafiso saina mutu ze dawo gidannan,, wannan wanne irin karatu yarannan take da Har yazabi bacin raina..
Hannu ladeefah tasa tana gogewa mummy hawaye,,kiyi hakuri Mummy kina kallo nabar aikina Na dawo Nigeria sabida abinda yarannan ya aikata,,duk Da yace Ke Kika amince Amma banji dadin yadda Kika Tashi Hankalinki ba,mummy mashkur ba yaro bane Duk inda yake Ze Iya Kula da kansa,,Kuma shikenan seya tafi cikin matsiyata masu yawo a Jeje wadanda Basu da Wani abinci Sai nono,, wallahi Bazan lamuntaba koya dawo Ko hankalin kowa ya Tashi a gidannan..
Kiyi hakuri Mummy nasan Duk inda mashkur yake Yana hanya"Koda yazo Baze shigomin gida ba Sai an kaishi hospital an Duba lafiyarsa,,nasan zuwa yanzu yaci abubuwa marasa kyau da zasu Iya taba lafiyarsa,,Kuma inaso kufara kaishi toilet Na Baya yayi wankan kafin ya shigomin Daki...
Shikenan mummy za'ayi yadda kikace,,Abu daya nakeso ki kwantar da Hankalinki,,haba lateefa tayaya hankali Ze kwanta Ina zaune cikin Jin Dadi auta Yana cikin wahala kinga lateefa Idan Baze zoba kuje ku daukomin Shi Dan wallahi Na tsani Zama da wadannan mutanan,,shiyasa kikaga Ko nono Bana sha..
Ajiyar zuciya lateefah ta safke tana kallan mummy tana girgiza kai tace,,Dan Allah mummy ki rage wannan damuwan kinsani Idan daddy yaji Baze tabajin Dadi ba,,cike da fada mummy tace.
To yaji man Idan yaji saime dukana zeyi,,Koshi yayi irin wannan rayuwar ne,,Amma mummy Amma me Dan ubanki,,karfa ki batamin Rai.
Kiyi hakuri Mummy Naga Dai daddy Shima bafulatani ne,,kidena nuna kyamarsu a Fili Hakan Ze riqa sosamasa Rai..
Badai kema kina Bayan wadannan mutanan ba mutanan da saisu shekara Goma basuci Nama ba,,mummy kinsan nafiki tsanar Zama a irin wannan guri kawai Dai banaso kina fada agaban daddy..
Sallama Yaya yayi suka amsa nan ya Samu guri kusa da mummy ya zauna Yana gaisheta,,dauke kai mummy tayi taqi amsawa dan a ganinta basuyiwa mashkur Magana ba shiyasa be dawo ba..
Lateefah ce tayiwa Yaya sannu da zuwa nan ya amsa Yana cewa Ina mashkur yake?
Yaya be dawo ba Nima tinda nazo nake zuba idansa gashi Har 4 Na yamma be qaraso ba,,Anya Ko ya taho?
Eh Yana hanya dazu munyi Magana dashi yace nan da 2 hours ze Iya qarasowa..
lateefah meya Samu mummy Ko Bata da lafiya?
Bansani ba,,kaida Nace kagayamasa ya dawo da wuri shine harka samu damar zuwa shibe qarasoba,,kiyi hakuri Mummy kinsan yanayin haryarsu Sai ya hau Mota biyu kafin su zo,,Nace driver zeyi daukansa yace harya kama hanya" karyane wallahi kunsan Allah Idan be dawo Yau ba Saina Saba muku a cikin gidannan..
Tinda daddy ya shigo yafara Jin hayaniya harya shigo falo ya Samesu zaune sun sa mummy tsakiya Suna Bata hakuri..
Daya Bayan daya ya riqa kallansu Yana mamakin zuwansu,,sannu da zuwa sukayi masa ya amsa tare da neman guri ya zauna Yana Kallan mummy yace..

Yanzu abinda kikeyi ya dace Kenan agaban yaranki kina zauna kina koya musu dabi'a mara kyau ta rashin sanin darajar Dan Adam,,to Wallahi kisani kowa da Kika gani da baiwar da Allah yayi masa dan haka kibi Duniya a sannu" turo baki mummy tayi ta budeshi a hankali tace,,to Ni menayi kawai Dan Nace yarona ya dawo gareni Sai ka kama fada kana fishi Dani"
Ki rufemin baki,,kosu Fulanin ba Allah ya haliccesu ba,kinsan bakisan Fulani Kika auri jininsu,,Maryam a gidana Kika Zama abinda Kika Zama shine yanzu Har Kika Iya ....." Daddy kayi hakuri Kasan halin mummy tinba yanzu ba,,kasani Ko kauyensu Inna wuro batasan zuwa Har Allah yamata rasuwa,,daddy Mun girma hadda yara bazamu so ganin haka Yana faruwa a tsakaninka da mummy ba,,munsani daddy kaima ka Sani,,baku taba yin fada da mummy Sai a Kan maganar zuwa ruga lokaci gudu kaika Kadena zuwa daganan bamu sake ganin bacin ranku ba Sai yanzu da mashkur Yaja..

Kallan yaya daddy yayi yace meya dawo dakai kasar nan yanzu,,bakinsa Na rawa yace daddy Wani aiki nazo Yi,,Ke Kuma fa daddy yafada Yana nuna lateefah da cikinta ya duru ruwa harta fara karkarwa..
Ba tambayanki nayi ba,,Ina Kika Baro mijinki?
Nina kirata,,Shima Sadiq Nina kirashi tinda kai bazaka Sashi ya dawo gidaba su zasu Sashi yadawo,,to ai shikenan Idan ya dawo saiki jiqashi ki yanshe Ko,,be jira amsar mummy ba ya fita a falon..
Hira suka cigaba dayi ita Dai mummy jinsu kawai take tana Kalle kalle tare da.neman ta hanyar da mashkur Ze shigo,,Har akafara Kiran Sallar magrib Basu qaraso ba haka Dai kowanne su ya daura alwala sukayi sallah,,Suna cigaba da Zaman jiransa...

Tinda nijlah Taji warin Mai zuciyanta yafara Tashi nan ta fara toshe hanci tana kallan mashkur,,a hankali yake Mata Magana Yana Kallan yadda idanunta sukayi zuru zuru,,
Menene Naga kina toshe baki da hanci,,
Banasan warin Mai ka saukeni cikina juyawa yake tafada tana yinqurin Amai,,kafin motan ta tsaya tafara Kwara Amai a jikin mashkur Har Saida ta Bata gaban rigarsa,,be damu da Hakan ba Saima shafa bayanta ya riqayi Yana Mata sannu,,Seda ta gama me motan ya Basu ruwa a jarka suka wanke jikinsu,,nan suka cigaba da tafiya hancinta a toshe ,,karfe 7 Na dare Suka sauka a cikin garin Kano,,me napep ya tare suka Shiga nan yayi masa kwantancen gidansu kasancewar mashkur be taba Hawa nape ba,,dariya me nape yayi Yana cewa Malam haka kai bakone,,mu ba address Ake bamu ba,unguwa kawai Zaka fada Idan mukaje saika nuna gidanka,,ok kawia mashkur yace yacigaba da jera nijlah sannu,,tinda suka Hau napep bacci ya dauketa Har suka kai gidansu mashkur Bata Sani ba.
Bayan ya sallami me napep ya tsaya tinanin ta yadda zefara tashinta Sai kawai ya dauketa ya kwankwasa get..
Waye ne Ze balle mana kofa qara bugawa mashkur yayi Yana cewa nine baba zoka Bude..
DA gudu baba me Gadi ya Bude kofan Yana yiwa mashkur sannu da zuwa..
Ahankali mashkur yace,,baba ga kayana Dan Allah ka temaka ashigomin dasu,,to ranka ya Dade,,nan baba yafara rufe qofan,,qaran qofa yasa nijlah Bude Ido tana Kalle kalle..
Ahankali mashkur ya safketa Yana jera Mata sannu,,Ina kayana nijlah tafada cike da sanyin kuka.
Kingansu can Karki faramin halin naki,,dasauri ta dauko kullin dankwalinta ta Dora akai tana Kalle kallen gidan..
Hannunta ya kama Yana cewa 'yar kauye Sai Wani Kalle kalle kike,,lah kado kaga wannan abun da Ake nunawa,,lah kado Kalli kaza haka nijlah ta riqa fada Har suka isa qofan falon..
Da sallama mashkur ya Shiga zuciyarsa na harbawa tare da matsanancin faduwar gaba..
Mummy dake zaune tasa abinci agaba Taji sallamar mashkur,,dasauri ta dago ido Aiko tayi sa'a idanta be safka Kan Na mashkur ba saiya sauka Akan santaleliyar surukarta..
Zabura tayi ta Tashi tana nuna nijlah da yatsa bakinta yakasa magana...
Aunty lateefah ce tayi qoqarin Bude baki tace mashkur Kaine haka,,ita Kuma wannan Daga ina,,Ina Zaka kaita..
Mashkur be Iya Magana ba illah zuba musu shanyenyun idanunsa dayayi Yana cigaba da tafiya,,,har Saida yakai jikin kujera Ze zauna hannunsa riqe Dana nijlah yaji muryar mummy tana Magana..
Karka fara Zama min Kan kujera ka Kuma ficemin da wannan aljanar yarinyar"waima a gidan ubanwa ka samota Sai kuma tasa kuka tana cewa.
Kunga irin jajibe jajiben nasa,,ya kamomin wannan qazantar Har gida...

Mashkur wacece wannan Daga ina ka daukota??

Kafin mashkur yayi Magana yaji tsincin muryar nijlah..

Sunana nijlah kawu Daga garin kankan ya daukoni Kuma ni matarsace Ko kado?????????????????????



*Kuyi hakuri wayana ya Samu matsala ba lallai ku qara Jina a 'yan kwanakinan ba,,sedai kuyi fatan Allah yasa ta gyaru da wuri,,Nima ba haka naso ba,,zanyi missig zafafan comments dinku😍😍😍*




*Comments & share*




*momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*DALA.....*



1⃣7⃣&1⃣8⃣


Kallan kallo aka riqayi a falon yayin da mummy ta riqajin Dakin Yana juya mata,,sedai Wani bangare na zuciyanta Yana gayamata Karya yarinyar take,,kallan mashkur nijlah tayi tana murmushi tace..
Dan birni kayi Shiru Baka Basu amsa ba,, mashkur be Iya kallan inda nijlah take ba yacigaba da qoqarin Zama Kan kujera..binshi nijlah tayi tana kallan mummy dake binta da Wani irin kallo Wanda batasan kona menene ba.
Marin da aunty ladeefah tayiwa mashkur ne ya dawo dashi Daga duniyar suman tsaye dayayi..
Dan iyayenka ba tambayanka akeba,,Yaya kaduba yadda ya maida mu mahaukata,,
Kinga lateefah abi komai a hankali shida kanshi zeyi bayani cewan yayan Yana mamakin abinda mashkur ya aikata duk da yasan halin mahaifiyar tasu..
Mummy Bata Iya Magana ba Dan a yadda take Bata Jin abinda suke fada kallansu kawai take sabida gaba daya komai nata ya tsaya ya Dena aiki...
Kallan aunty lateefah mashkur yayi kafin ya safke kansa kasa nan take idanunsa ya kada yayi jajur ga Wani tuquqin bakin ciki daya tokare masa zuciya,,kasa hadiye yawu yayi Yana Kallan kafet..
Lah lah lah,,Amma dai kado anyi mugu,,Babu abinda mijina yamiki Zaki mareshi,,aradu Kaci sa'a kai babbane Dana sheqeka da Sanda,,ka zube anan..
Ke Dan ubanki bamasan hauka kai mashkur ka Bude baki kayimana magana,,a Ina ka samo wannan aljanar yarinyar??
Dakyar mashkur ya Iya tsayar da nutsuwarsa ya dago kanshi dake saramasa Yana kallan yaya,,kafin ya Bude bakinsa Wanda zuwa yanzu yayi masa nauyi yace,,
Dan Allah Yaya kubani lokaci saina yi bayani Amma Daga zuwana kun tsareni da tambayoyi..
Au Allah lallai yaran nan ka samu sake yaya kake Gaya haka,,mummy kingani Duk soyayyar da Kika nuna masa ce tajamana haka,,gashi muna magana Yana mayar mana sabida be daukemu da qima ba,,aunty lateefah ta qare maganan tana huci,,mummy ko Ido ta zuba musu,,zuwa yanzu tana fatan maganan nijlah ya Zama karya Kai inda halima ace nijlah ba cikakkiyar me hankali bace..
Aunty kiyi hakuri niba haka nake nufi ba,,da hakane bazan tabajin magananku a daidai lokacin da kuka buqaci na dawo gida ba,,

Karyar banza cewar aunty lateefah tana nuna nijlah,,wacece wannan?
Hade fuska mashkur yayi,,Zan gayamusu yanzu nagaji da yawa saina huta,,mummy kinajin abinda yake fada kinyi shiru??
Mummy bata iya motsawaba Saida lateefah tayi saurin girgiza ta kafin ta safke nannauyan ajiyar zuciya tana kallan mashkur Daya kafeta da Ido Yana mamakin halinda mummy ta shiga..
Dasauri yayi gurinta Yana cewa,,lafiya sweet mom,,waya tabamana ke"" dasauri ta daga masa hannu alamun karya qaraso inda take,,chak ya tsaya tare da hadiye yawun Daya taru a bakinta,,tinda yake mummy bata taba yimasa irin wannan karbar ba to kodai shima ya shafo abinda take kyama tattare da Fulani,,yayiwa kanshi wannan tambayan..
Bakin mummy na rawa tace,,auta wacece wannan?
Shiru mashkur yayi Yana tinanin amsar dazeba mummy sai ya maida kallansa ga nijlah yanasan yimata magana da ido,,aiko nijlah ta washe Baki tana tinanin amsa mashkur yakesan tabada..
Tace ehhh,,a kankan ya dauko ni kuma Malam ya daura mana" tsawa mashkur ya Daka Mata Yana hararanta tini nijlah ta rufe Baki tana karkarwa tare da komawa bayan aunty lateefah tana boyewa,, da mugun gudu lateefah ta dawo bayan yaya tare da Dora hannu aka..
Dan ubanka kabani amsa kafin yanzu na Saba ma,,yaushe kazama haka mashkur ni nake ma tambaya kana kallona,,,to kodai na chanza ma,, dasauri yace ah ah mummy dama dama.
Dama me,, gaskiya zaka gayamin ko angayama idan zakayi taimako saika kawomin irin jaraba har gidana,,Bama ta tsaya iya get ba shine saida Ka kawomin ita har cikin falona..
Zuciyarsa na dokawa yace mummy kiyi hakuri tare zamu zata zauna da ita"
A ina?mummy ta tambaya..
Batare da fargaba ba mashkur yace anan gidan,,sedai Ka zauna da ita Amma badai mummy ba" shima baze zauna da wannan annobar ba mummy taba lateefah amsa..
Kai Dan birni me suke fada,,Allah dai yasa badani suke ba,,cewan nijlah tana kallan mummy sai kuma ta sunkuya tace sannu ina yini..
Ke tashi anan kafin kimin barbaren kudin cizo Naga alama a wannan jikin naki babu abinda bazaa samu,,Kai mashkur Ka fitamin da ita a falo Ka kuma dawo kayimin bayanin inda Ka daukota..
Mummy marainice shiyasa na kawota ta riqa tayaki aiki,,mummy yarinyar bata da matsala Dan Allah karkice ah ah yafada Yana hada hannu alamun roqo.
A tare mummy da lateefah har ma da yaya suka sa salati suna tafa hannu" lateefah ce tace cewa akayi mummy na buwatar 'yan aiki,,to koma ina buqata saina rasa Wanda Zan dauka sai wannan..
Duk da yarinta da shirme irin na nijlah saida tagane kyamarta suke gashi taji Dan birni Yana maganar aiki zata tayasu,,to wai me suke nufi?
Wanne irin kallo suke min nijlah ta tambayeni kanta,bata dawo daga tinanin ba taji mashkur Yana cewa..
Mummy Dan Allah kiyi hakuri ki tayani riqe amanar da Allah ya doramin,,yarinyarnan marainiyace bata da gata shiyasa na kawomiki ita,,
Karya kake mashkur
Showing 9001 words to 12000 words out of 65025 words