ratsa gurin kafin Nasir yace,, to wai Kai mashkur dama ba soyayya kake da nizlah bah'' qayataccen murmushi mashkur yayi Yana Sosa Kai yace,,

Ai nizlah kanwace agareni,,ina kuma yimata so Wanda bansan irinsaba,, dan da ace ta isa aure nizan aureta na kaita can birni itama ta waye,,


Dariya suka sa suna kallan mashkur Wanda tinda aka ambaci sunan nizlah bakinsa yaqi rufuwa,,,

Koma dai menene munsan kana San nizlah,, Dan shaguwarku da ita abin dubawa ne, Nasir ya fada Yana kallan Bello..

Dariya Bello yayi shiko mashkur ya zuba musu Ido Yana kallansu,, be iya magana ba sabida Jin Kiran sallah da yayi..

Ni kunga tafiyana,, kafin kumin wani fassara na daban,, atare suka tashi suna qara jandada masa abinda ke zuciyarsa...

Sedai Shi Babu wannan a ransa soyayyar Yasmeen kawai yakeji,sedai Yana yiwa nijlah so irin Na tausayawa Amma Bada aure ba.

*******************

Uhmn uhmn,, Allah ni saikin Bani biyar naje dandali,, yaushe raban daki Bani biyar dinki,, kodan kinga Dan birni Yana Bani,,kayya nijlah,, Nima Bani dashine,da inadashi Babu abinda Ze Hana ni baki..

Turo baki nijlah tayi tana kuka tare da birgima a qasa,, kayya mezan gani haka sukaji Malam ya fada,,yakumbo kodai Wani Abu kikayiwa yarinyar nan..


Kai madai Malam Sai kace bakasan halin nijlah ba,, wannan kukan daka ga tanayi Bana komai bane illah Na naira biyar,, ita adole Saina Bata biyar ta kashe,Nace Bani dashi ta kwanta tana birgima,,kaga Idan kayan jikinta yayi datti Sai Muga inda Zan samu kudin sabulun wanki..

Girgiza kai malam yayi Bayan yagama Jin bayanin yakumbo,,nijlah Ko Bata daina birgima ba Dan Har tirken dabobi ta kai tanayi...


Ahankali Malam ya taka ya isa Har inda take ya kamo hannunta"ba musu ta tashi tana turo baki,,kiyi hakuri kinji nijlah ta,,gobe Idan Allah ya kaimu naira Goma Zan baki kije dandali kisai Duk abinda kikeso..

Kawu dagaske kake,,nijlah ta fada tana kallan bakinshi,, kai nijlah meyasa wayenki yayi yawa,,kin tabaji Malam yayi Karya??sukaji yakumbo na tambaya..


Shiru nizlah tayi tana girgiza kai,,Sai kuma tace,,Naga yataba cewa Nima za'a kaini birni nayi aiki irin na jummai,Amma haryanzu be kaini ba,,Kuma Naga hajiyar tana zuwa...

Bata rai Malam yayi yace,kinga nijlah banasan shirme,,kima ajiye wannan maganar Babu ita,,haba Malam ya zakayi haka,,zuwa aikin nizlah shine cigabanmu,,kana Dai kallo abinda zamu kai bakinmu,,wahala yake mana..

Yakumbo,,Malam ya Kira sunanata Har sau uku,,amsawa tayi tana kallansa,,kisani Daga Yau nafasa kai nijlah aiki,,auran da ita zanyi..

Zaro Ido yakumbo tayi tana kallan nijlah,da tinda aka Kira aure tafara rawa tana juyi,,bakin yakumbo na rawa tace Malam aure fa kace,nawa shekarun nijlah,,yake,saifa gambon wata take shekara Goma..


Ni wallahi nayi tinanin ka janye wannan maganar danaji kwana biyu Baka qara yiba.


Eh, nasani,Naga Dai ba haramun bane,,damu zauna da ita,cikin wahala Ai gwara taje can gidan mijinta Kota samu ladan aure,, wannan wanne irin ladane,,nijlah fa Ko wanke wanke Bata Iya sosaiba,,balle azo maganan gyaran gida,,nidai kayi hakuri a kaita gidan aiki hakan zefimin kwanciyarsa hankali...

Hmm Ni kinga tafiyana,, Naji an tada Sallah,,fita Malam yayi yabar nijlah Na rawa tana cewa yakumbo Nima Zaki saimin wannan abun da Ake dafa tuwo..


Ke dallah rufemin baki,ki Kuma Dena wannan rawan kan,,Ko an gayamiki auren Cin tuwo ne,, fari nijlah tayima yakumbo tana cewa,,eh mana nidai gwara akaini gidana,,nasan Ko Goma Zan riqa samu Ina zuwa dandali,,


Acan masallaci Bayan an idar da Sallah Malam ya matsa kusa da Liman ya gayamasa Magana a hankali,, murmushi Liman yayi Yana cewa,,kayi daidai Malam hukuncin daka yanke yayimin Dadi..

Har mutane sun fara bita akace su dawo za'ayi wata Magana,, lah mashkur zo muje naga mutane na koma cikin masallaci,, jeka kawai nizan jiraka ana,,sabida sanin hali yasa Nasir da Bello suka barshi anan su suka dawo cikin masallacin..

Liman ne yafara magana,,to jama'a Allah ya kashe Yaba Wani,,game dukiyar aure Kuma yake sha'awar qarawa mace yazo gata,, Ko saurayin daya shirya,, charaf,,Wani tsoho yayi saurin Daga hannu..

Malam ne ya katse Liman ta hanyar cewa,, *'YAR SADAKA CE* to kunji abinda Malam yace,,yarinya sadaka ce..


Yauwa ga Wani Chan ansamu Liman ya fada Yana nuna tsohon mutumin dake rankwafe Yana murmushi,,yauwa Ala gafatta Malam matso kusa Liman yace da wannan tsoho,,matsowa tsoho yayi kafin Liman ya tambayeshi.

Menene sunanka,,sunana laman ya'u,,to Malam ya'u,,ita wannan yarinya da kace kanaso sunanta nizlah..

Nijlah,, Nasir ya maimaita Sunan tare da fita aguje Yana Kiran mashkur,,

Mashkur mashkur,Dan Allah mashkur kazo ka cece yarinyarnan indai soyayya na gaskiya kake yimata,,kai lafiya wacce yarinya kake Magana,,bakin Nasir Na rawa yace nijlah ce,,gata can za'a Bada sadakanta..

What kana nufin aurenta za'a Bada,,eh wallahi kayi sauri muje Kar a daura auren,,da gudu suka nufi masallacin mashkur Na tinani a cikin zuciyarsa...


Yanzu Idan na Karbi auren nijlah ya zanyi da Mummy,,Waze yadda temakonta,nayi,tayaya Zan fahimtar da iyayena,, Daga zuwa bautar qasa na biqe da aure,,auren ma Na qaramar yarinya Wanda Bata wuci shekara Goma ba!!!

Da wannan tinani suka Shiga cikin masallaci,sunyi sa'a baa daura auren ba,,sedai ana gab da daura wa,,ku dakata Nasir ya fada Yana nuna mashkur,, wannan shiyafi dacewa da auren nijlah indai sabida Allah za'a Bada sadakanta..

Wannan gaskiya ne, mutane suka amsa Suna goyan Bayan mashkur"" Malam ya'u Najin haka yace Sam be yadda ba..

Akan me nasamu Mata zakumin bakin ciki,, hakuri Liman ya Shiga ba Malam ya'u Amma Duk da haka ya dage Shi saiya auri nijlah..

Nasir ne yace kaga tsoho karka damu,,wannan Ze Baka naira dubu Goma kabar masa ita..

Kai yaro kalla idona Malam ya'u ya fada Yana zaro Ido waje..
Atare Nasir da mashkur suka zuba Alhaji ya'u Ido Suna sauraransa.
Nan alhaji ya'u yacigaba da Magana,,wallahi Ko naira dubu hamsin zaku Bani Bazan hakura da auren nijlah ba,,Har Sai kun auramin budurwa me suffa irin ta nijlah,,

What? What me kace tsoho,,to wallahi Ko ka amsa dubu Goma Ko kayi asara gaba daya,,nan Nasir ya juya inda liman Ke zaune yace..

Liman kaga wannan abokina ne dashi mukeso adaura wannan aure indai Malam ya amince.


To Malam Kaji abinda yaro yace,,Liman yafada Yana Kallan Malam,,

Sassanyan ajiyar zuciya Malam ya safke kafin yace,,Liman Bani da zabi kawai kayi Mata zabin daya dace,,to shikenan Liman ya fada tare da gyaran murya.

A matsayina na limamanin wannan kauye Zan auran auren nijlah da wannan yaro,kai yaro Mene sunanka"" kasa Magana mashkur yayi nasir yayi saurin cewa mashkur Hussain.

To Masha Allah, mashkur ka amince Zaka auri nijlah,, mashkur besan lokacin daya Daga kai alaman eh ba.

Ba'a Wani bata lokaci ba aka daura auren nijlah abbakar tare da zankadeden angonta..

Nan Alhaji ya'u ya riqa zagege zagege Yana cewa an nuna bare yafisu,, ya qara da cewa Allah yasa Dan birni ya siyar da nijlah kowa ya huta,,maganganu marasa kai da gindi ya riqayi Har Saida manyan 'ya'yansa suka fiddashi a masallacin.

Mashkur Na fito yaji Wani irin tashin hankali ya ziyarci zuciyarshi nan ya barsu Nasir Suna tattaunawa da Malam Dan koya tsaya Baze Iya cewa komai ba sabida tsantsar tashin hankali..

Jiyayi Idan beyi waya da mummy ba Baze samu kwanciyar hankali ba, Dan haka ya nufi inda suke waya,, Da zuwashi ya fara Kiran layin mummy sedai wayar Na Shiga mummy taqi amsawa tana me Jin haushinsa.

Karin ya qara Kira wayar yaya ta shigo,,nan yayi saurin kai hannu ya dauka Yana Kiran hello yayan mashkur,,ba Wani yayan mashkur da Zaka kirani,,kasa mana uwa a tashin hankali sabida bakasan me kake ba Ko mashkur???

Kayi hakuri yaya wallahi ban tafi da fishin mummy ba Har Saida ta amince Na tafi"
Karya kake mutumin banza da wufi,ahaka kakeso karatun yayima albarka?
Kayi hakuri yaya mashkur yafada zuciyansa Na halbawa day sauri da sauri.


Inaso ka Bude kunnanka da kyau ka saurarani" bakin mashkur Na rawa ya amsa da to yaya.

Kaje yanzu ka Hada kayanka ka dawo gida Idan Har bakasan bacin ranmu" Wani irin Abu mashkur yaji ya buqi zuciyarsa Har Sai da ya dafe da hannunsa yace ,yaya Yau fa kace?

Eh Yau Nace Ko bazaka iyaba Ni a gobe Na dawo qasar nazo Har inda kake,,ah ah yaya kayi hakuri Zan dawo yafada yanajin kuka Na zuwa masa,,yadau Fi kyau yaya ya fada Yana katse Kiran.

Hannu mashkur ya Dora akai Yana cewa Na Shiga uku Ni mashkur meya kaini auren nijlah gashi Ina neman sa kaina a 100,yanzu yaya zanyi?

Be Iya samun amsa ba yaji Wani Kiran Na shigowa cikin wayarsa" Yana dubawa Yana aunty ladefa,zaro Ido yayi waje Yana tinanin fadan da aunty ladeefah zata masa,sedai Baze Iya Qin daukaba sabida yasan abinda Ze biyo baya,hannunsa Na rawa ya dauka Yana Kara wayar a kunne aunty ladeefah tafara da...................





Dan Allah Dan annabi Idan kinsan bazaki Iya comments ba Karki soma karantawa.



Comments &share😍



*Momn sultan takuce*
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*HAJJA FATI...*



1⃣1⃣&1⃣2⃣


Ashe Baka da kirki mashkur,mahaifiyar tamu kakesan kashewa" Anya ko kanasan albarka a karatun naka"
Aunty me kuma nayi,uwarka kayi Dan bantan ubanka,, mashkur ni kake tambaya abinda kayi Dan qaniyanka???
Sanin halin aunty ladeefah da fada yasashi cewa ah ah,,Amma aunty" Amma me Ka rufemin Baki, ko kanaso kagayamin karatunka da zuwa wannan mugun kauyen yafi mummy daraja,,dasauri ya Shiga girgiza Kai kama tana kallanshi...
Au rainin hankalin naka harya Kai ina magana kayimin shiru"
Haba aunty bafa Nina Kai kaina wannan rigar ba,kaini akayi kuma wallahi bantafi ba Saida Mummy ta amince yafada cikin sanyin murya.
To yanzu tace bataso Dan haka Ka tattara kayanka Ka dawo kafin nazo har garin naci maka"

Amma aunty kinsan ko rabi banyi a aikin nan ba,, sai dagamin hankali kuke"inye mashkur nikake gayama haka,,ba laifinka bane laifin mummy ne datake daure maka gindi"
Kiyi hakuri aunty amma"Amma me to wallahi Ka sani a yau nakeso Ka dawo gida kafin gobe, Nima a gobe Zan zo qasar nida yaya saika gayamana dalilin dayasa kakesan dorawa uwarmu hawan jini??

Aunty yanzu yamma yayi bazan iya tafiyan dare ba,,kaika sani nidai magayama karka Bari mu riga zuwa qasar Dan jirgin asuba zamu hau..! Shiru yayi Yana sauraranta batare daya iya magana ba..

Cigaba da magana aunty ladeefah tayi tana cewa, Banda shashanci irin naka mashkur kafi kowa Sanin halin mummy tinda Kai kake zaune da ita Amma Ka take Sanin Ka tafi gurin da tafi tsana a zuciyanta" kana kallo tin muna yara mummy batasan zuwa kauye balle harta rabi Fulani,,kodan lokacin bakada wayo...

Zuciyarsa na quna tare da tilin Dana Sanin zuwanshi wannan kauye yace aunty kiyi Insha Allahu goben Zan zo kafin kuzo,,ni inaga dakun hakura da zuwa nizan ba Mummy hakuri..

Bazamu fasa zuwa ba,,ok kanaso kaje ta lallabeta taqi nuna damuwanta akai bayan Ka dagamata hankali muma Ka dagamana''cikin sanyin jiki da tinanin irin tashin hankalin daze tarar a gida yace shikenan aunty..kit ta katse Kiran tanajan dogon tsaki tare da cewa yaro besan komai ba sai bin talakawa kaskantantu wulaqantantu wadanda Basu San komai ba sai yawo a jeji da shanaye..


Tinda mashkur ya Gama waya ya zauna a gindin bishiyar dafe da kansa Yana ji kama ze fado qasa sabida sarawan dayake masa" dakyar ya iya daga qafafunsa yafara tafiya Yana hada hanya harya Kai dakinsu"
Kan katifanshi ya kwanta hannunsa dafe da kansa yanajin zuciyarsa na azalzalasa akan abubuwa da dama,,rintse idonsa yayi yanasan bacci ya daukeshi sedai abin ya gagara Dan a yadda yakeji bacci baze taba daukansa duk kuwa da irin sunan dayayi gurin satar mutane,,runtse Ido yayi Yana hango kyankyawar fuskar nijlah,, qirjinta yake hanqe yaga Babu komai a jikinta danko qirgan danqi Bata fara ba,,sedai nijlah akwai iyaye dasan ado da kwalliya Duk da Bata da kayan kirki Amma kullum saita chanza Koda Bata samu sabulun wanki ba,,sosai ya zurfafa cikin tinanin yarinyar tare da yaban halayenta,,abu daya yakeji tare da ita shine rigima,,yasani Idan tafara rigima bataji Bata gani saita kwana tana kuka" oh Allah ya fada a Fili,,yanzu Idan nijlah tafara wannan kukan yaya zeyi da ita,,wanne irin mataki mummy zata dauka akansu gaba daya,,Rasa amsa dayayine yasashi saurin Tashi ya fita.
Alwala ya daura nan ya dawo Daki ya shinfida Sallaya..
Sallah yayi Har raka'a biyu nan ya dungura kanshi a qasa Yana neman dauki a gurin Allah..


Bayan an fidda Alhaji ya'u,,Liman yafara Magana kama haka" Malam inaga yakamata mu qarasa gida Domin ayiwa yakumbo bayanin abinda Ke faruwa tare da gayamata wannan aurin aure..

Hakane Liman sedai Ina tsoran yadda yakumbo zata riski wannan labari,,bansan yadda zata dauki rabuwa da nijlah ba,,Malam yaqare maganar da cikin kuka Wanda baza'a kirashi Na bakin ciki ba,,Sai Dai Ko farin ciki..
Haba Malam yaya da kuka,kaida zakayi farin ciki gashi yarinya tayi dacen Miji bame San hayaniya ba..

Kwarai dagaske cewan Nasir,, Ai Liman Idan kaga mashkur yayi Magana to ba qaramin Abu akeyi ba,,bashida San hayaniya,wallahi tinda muka taso da mashkur bantaba ganin abokin fadan Saba kowa yabansa yake,,shiyasa nazabawa nijlah Shi Duk da nasan wasu zasuyi tambaya Shin Ni meya hanani aurenta nasa abokina yayi?
Nan mutane sukafara surutu Suna fito da tambayan dankuwa sunga lokacin da Nasir Ke gayawa mashkur yazo ya taimaki nijlah" wasu nacewa shimeya hanashi taimakonta indai Dan Allah take..

Kuyi hakuri yanzu Zan Baku amsar tambayoyinku" wallahi Ni Nasir Zan Iya auren nijlah Duk da Babu shaguwa tsakanina da ita Kamar yadda ta Shaqu Na mashkur,,sedai banqi amsar aurenta sabida komai ba sedai, Ni inada zafi Bani da rigima sannan abu kadan Ke batamin Rai nayita jibgar yara,,Idan Ko sa'anane Daga lokacin Ina Iya Dena abota dashi..
Nan ya numfasa yace mashkur kadai Ke Iya Zama Dani sabida miskilanci irin nashi da hakuri Wanda Koda nayi Abu sedai yace Allah ya shiryeka koya girgiza kai,,Idan Ko fada Na tsokalo shike Bada hakuri Har adawo daidai.
Natabbata wannan dalili nawa ya isa kugane nijlah ba sa'ar aurena bace Duba da yanayin rigimarta ta Babu gaira Babu dalili..

Sosai Yan gurin sukasa dariya,Bello yace ainaga alama shiyasa Daga zuwanka garinnan kafara Dukan yaran gari" Aina nasan haka halinka yake da rufdugu zamuma" nan ma dariya akayi kafin Liman yace.
Babu shakka Nasir munji dadin kalamanta akan abokinka Kuma muna fada abinda ka fada ya Zama gaskiya" insha Allahu Nasir yafada kanshi a qasa.

To Malam yakamata mu tafi Ko,,nan suka Tashi suka tafi gidan Malam.
Yakumbo dake zaune nijlah nakan cinyanta tana rigima Taji sallamar Malam,,amsawa yakumbo tayi tana kallan nijlah tace.
Toga malam yazo Naga Yana murmushi ga dukkan alamu yayi samuwa inaga Yau zakici shinkafa da miyar dakiketa mafarki"turo baki nijlah tayi tana kallan Malam kafin ta kurma uban ihu tana cewa.

Wallahi yakumbo Babu abinda yakawo bakiga hannunsa Babu komai ba,,nidai Allah saikin siyamin burodi...
Qarasawa Malam yayi ya cewa kinga Yar albarka Tashi kizo kiji Abu Wani Na tabbata Zakiyi farin ciki kinji Yar gidan kaka..

Maqe kafada tayi tana birgima a qasa,,nan Malam ya Kalli yakumbo yace,,kinga yakumbo dauko tabarma ki shinfida a rumfa ya fada Yana nuna yaloluwar rumfar Kara dake maqale jikin Dakin daba lallai ya wuci damuna ba,,
Shinfida tabarma yakumbo tayi tana cewa Ikon Allah suwa muka Samu,,Malam kodai Yau zakka ta biyo ta gidanmu.
Kedai ki shinfida kafin nayimiki albishir,,nan Malam ya juya Yana cewa ku shigo Daga ciki..


Liman ne a gaba Sai Nasir da Bello tare da sauran mutane dake tayasu murna,,wasu Ko yan uwan mahaifiyar nijlah ne...
Tinda suka shigo yakumbo tabisu da kallo tana mamakin abinda ya kawosu adaidai wannan lokaci Kuma gaba dayansu,,kowanne ta Kalla fuskanshi dauke da annuri,,nan ta zauna Kan buhun dawa tana binsu da kallo..
Kinga yakumbo ruwa Zaki Basu ba wannan kallanba,,gaba daya suka Hada baki gurin cewa ah ah alhamdulillah ta zauna kawai muyi abinda ya kawomu..

Gaisu yakumbo tafara nan Taji suna yimata Allah ya Sanya alkairi" Seda suka gama ta juyo tana kallan Liman tace,,Liman me Kuma ya faru Naji ana yimin addu'a..
Eh yakumbo Yau Dai Allah yayi an daura auren yarinyarki" wacce yarinya Liman??, yakumbo ta tambaya mejin faduwar gaba,, nijlah dake kwance a qasa tana sharar hawaye tayi Shiru tana sauraransu tasan Dai ita dayace yarinyar yakumbo Dan haka ta Maida hankalinta gaba daya Kan Liman tanajin amsar dayake bawa yakumbo..

Yakumbo yarki nijlah,yanzun nan,Bayan idar da salla malam yabada aurenta ga.....Ai nijlah Bata jira Jin wane angon ba ta Tashi da gudu sabida Jin Kunya ya kamata,,Daki ta Shiga ta dauko dakalmin Danko Wanda yasha dinki da zare da allura tasa ta fita da gudu ta Bayan gidan,,kasan cewar gidan bashi da danga Babu Wanda ya Ganta.

Mashkur" zabura yakumbo tayi ta miqe tsaye cikin rashin hankali da dimuwa tace,,badai wannan yaran mashkur ba,da naira hamsin bashi masa wahalan badawa???
Eh shifa Malam ya fada Yana Kallan yadda yakumbo ta haukace ta tubure masa..

To Wallahi Baze taba yiwuwa ba ,Akan me Zaka auran da nijlah ga Bako Wanda bamusan asalinsa ba,hasalina karatun arnane ya kawoshi ruga...

Haba yakumbo be kamata kina fadar hakaba,,kinga Nasir yabamu labarin mashkur bashida Wani matsala ki kwantar da Hankalinki.

Cikin kuka yakumbo tace haba Liman yanzu shikenan nijlah zata tafi ta barni" Bazan iyaba,kugayamasa wallahi ki warware wannan aure aba Dan gari yadda koya na juya zanga marainiya,,Anya Ko Malam ka riqe amanar da danmu yabari,,kaico mutuwa kinyiwa yarinyar shigar sauri,wayyo niya Allah Na,,nan fa yakumbo ta juya tana fillanci Niko nayi zugun tare sauraranta sedai banji abinda take gayaba,,ta jima tana kuka kafin Daga bisani sukayi nasaran shawo hankalinta..
Haba yakumbo meyasa Zaki haka,,kinsan bakisan auren Kika yadda naje naba,,kaga Malam niba aureni Bani so Wanda Kaba auren nijlah Baze taba Zama kusa damu ba nijlah zatayi nesa damu bamusan rayuwar dazatayi ba.

Insha Allahu nijlah zatayi rayuwa me kyau ku kwantar da Hankalinku cewar nasir cike da tausayin yakumbo..

To Amma Dai ba yanzu Ze tafi da itaba ko??eh saimun gama service nan da wata 9 insha Allah" gaskiya yayi wuri yadai Yi hakuri Sai nijlah ta qara wayo nan shekara biyu saiya dauketa,,cewan yakumbo tana hawaye.
Shiru Nasir yayi ganin yadda tsohuwan ta Shiga Wani Hali yace to shikenan,,nan sukayi Mata sallama kowa ya tafi gida..

Nasir da Malam Sai Liman suka tsaya Suna tattaunawa..


Tinda nijlah ta fita da gudu ta Shiga gidan kawayenta tana Kiran su daya Bayan dayan,,bayan sun gama hallara ta fara rawa tana cewa Yau ranar auren nijlah Dan haka kowa ya shirya za'ayi wasa Na kece Raini Yau Yar gidan kaka da Malam zata Hada wasa a dandali..

Yeeeeeeee Yau akwai wasa,,ihu suka sa irin na murna suka sukafara zagaye Dan garin Suna waqa..

*'yan wasa ku fito wasa,Idan baku zoba samarinku suzo Bani Na fadaba angon nijlah ne,,angon nijlah ne me jan baki....*


Haka suka riqa waqa Suna wasa Suna Tara jama'a,,cikin lokaci
Showing 6001 words to 9000 words out of 65025 words