Yaba da Kyan nijlah gami da nutuwarta nan ta Nuna mashkur wasu a tamfofi dake maqale jikin shagon tana saidawa..
Ranka ya Dade gafa Kaya irin Baku Na manya" nasan zasuyiwa ' yar Kanwar tamu kyau?

Murmushi mashkur yayi Yana Duba kayan nan Shima ya Yaba da kyansu" bakomai ki bazamin set 50 a ki gwadata a Dinka,,Amma fa kaloli nakeso less da atamfa da material,,hadda shadda Idan ansamu Daga Sai a qaramin wasu"
Sosai aunty zee tayi godiya tafara zabar kayan tana nuna masa,, nijlah Ko sabida Dadi batasan lokacin data rungumeshi ba tana cewa yeeee Nima Na Zama Yar birni" hannu yasa ya lakuce Mata hanci Yana cewa wuce muje kafin kimin halin naki anan..

Suna fita ya Wani sakon ya qara shigowa cikin wayarsa' Yana karantawa Yana murmushi harya gama"
Allah ya Sani Yana mugun San Yasmeen Har besan yadda Ze kwatantawa me karatu ba,,Duk Da itama nijlah Yana jinta Har a cikin jininsa tana ninqaya..

Sosai yaji kewar Yasmeen ta kamashi musamman Idan ya Tina kwalliyar data yimasa ranar da abin Ze faru" hakanan ya riqa tuqi Yana murmushi.

Nijlah Ko Bata Wani Kula dashi ba,,Banda murnar an Sai Mata Kaya Babu abinda take, a haka harya kawota gidan mummy,,a Dakin Shi ya ajiyeta Yana shafa bayanta,

Ki kwanta nan ki huta nizanje Wani guri Na dawo" to tace tana gyara kwanciyarsa Dan Dama cikinta ciwo yafara tin a saloon,,daurewa kawai take..

Mashkur be Koma Dakin mummy ba ya fita Yana murna,,Wani katafaren gurin Saida kayan ciye ciye ya shiga,,nan ya Saima Yar Lele Kaya iri iri,, be je gurin Yasmeen ba Saida yasai Mata kayan da Duk yasan Yana burgeta kafin ya qarasa kofar gidansu Yana mejin dadi..

Waya ya dauka yayi dealing number ta" Yasmeen Na kwance abin Duniya Duk yabi ya isheta musamman Idan ta Tina rabanta da Jin muryar mashkur,,Sai Taji Duk Babu Dadi a jikinta ga Wani irin faduwa da gabanta yake Idan ta Tina da Sunan nijlah,, Taji wayanta Na ringin dasauri ta dauka ta karata a kunne tana murna tana komai..

Saida ya saita nutuwarsa kafin yace' ki fito Ina waje" shagwabe fuska tayi tana cewa' pls baby kashigo ciki,,kaida gidanku..

No a hanya nake akwai abinda ya kawoni Zan gayamiki ba Zama nazo ba.

Rasss rasss gaban Yasmeen ya fadi Har Saida tasa hannu ta dafe" mashkur beyi Aune ba yaji ta sakar masa kuka tana bashi hakuri..

Dan Allah bebi kayi hakuri ka shigo,,kwalliya nasan nayima shiyasa'
Cikin tsawa mashkur yace Ke niba ba kwalliya nazo gani ba,,sabida yanzu Na dawo Daga kai matata gurin kwalliya........................





Comments & share







*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SMALL GIFT TO...*
*MY DALAπŸ€ͺ.....*



5⃣2⃣&5⃣3⃣


Cike da mamaki Yasmeen ta Bude baki a hankali tana maimaita Kalmar matata' matata.
Yanzu nadawo Daga kai matata gurin kwalliya' Yasmeen ta maimaita maganar a fili"
Eh haka nace daidai kikaji' kinga kidena batamin lokaci Idan bazaki fitoba nizan wuce' mashkur ya Bata amsa sedai wannan Karan cikin sanyin murya ya fada ganin yadda ta Shiga Wani Hali Dan kawai ya Kira nijlah da matarsa...

Yasmeen Bata qara Magana ba ta saki wayar ta fadi qasa' nan take wayar ta ragargaje"
Bata bi takantaba ta kife a gurin tana sakin kuka'
Tajima tanayi kafin Daga bisani ta Tashi ta fada toilet.

Tinda mashkur yaji tsinkewar wayar yasan abinda yafaru sedai beyi mamakin Hakan ba sabida yasan Kishin Yasmeen tin kafin kaddaran auren nijlah ta fada masa,,dafe kansa yayi yanamejin haushin Hakan dayayi mata' Dan Ko ba'a gayamasa yasan Yau Yasmeen bazata Iya Cin komai ba' Idan kuwa Hakan tafaru to tabbas ya cika Maci Amana Kamar yadda ta kirashi da Sunan.
Rasa mafita yayi Dan haka ya yanke shawaran Shiga ciki koze Iya shawo Kan masoyiyar tasa' dasauri ya kunna Mota yayiwa get man horn, Yana Bude masa ya Shiga ciki Ko kallan inda baba Mai Gadi yake be Kalla ba haka ya tsayar da motan ya fito Yana tafiyansa me daukar hankali.

Tabe Baki get man yayi Yana cewa' oh ikon Allah kuduba yadda nake gaisheda mutuminnan yayi kama be gani ba,,kodan ba abin mamaki bane tinda Yana tare da wannan'yar girman Kan Yasmeen yaqare maganar Yana waiwaye alamun rashin gaskiya.

Masha na Shiga yafara qoqarin Kiran layin Yasmeen sedai wannan Karan wayar a kashe ake gayamasa" Rasa yadda zeyi yayi Dan haka ya qarasa kofan falon Yana sallama"
Mama na daki ta fito da sauri tana cewa'wanene?

Mama nine mashkur'
Murmushi mama tayi tana cewa sannu da zuwa Ka shigomana Ka tsaya a waje' Kan mashkur a qasa ya shiga' be zauna akan kujera ba ya risina Yana gaida mama,,

Mama ina kwana?

Lafiya qlau mashkur' yame jiki?
Dasauri harta Samu lafiya an sallamemu'
Kai alhamdulillah naji dadi sosai,,Allah ya kiyaye gaba.

Ameen mama' mama bata tashiba Saida taqara ba mashkur hakuri akan abinda yafaru nan ta tashi tana cewa ina ita Yasmeen?
Ka Kira wayanta mana' sosai kai mashkur ya shigayi Yana cewa ai mama wayan ne akashe shiyasa ma na shigo..

Dakin Yasmeen mama ta tafi tana Kiran sunanta sedai mama bata iya cigaba da Kiran ba sabida Jin kukanta" dasauri ta Shiga tana cewa ke Yasmeen lafiya me aka Miki?
Cikin kuka Yasmeen tace' mama shine wallahi yadena Sona nijlah yakeso.

Girgiza Kai mama tayi tana cewa inji waye? Waya gayamiki?
Allah mama Baya Sona shikenan nayi asaran dakon soyayyarsa danayi shekara da shekaru' sai yanzu wata Kula baqa Zata zo muyi kasan soyayyarsa da ita.
Ai kinji matsalarki mama ta fada tana Zama a gefen bed tare da janyota a jikinta' kinga Yasmeen ki tashi ki goge wannan hawayen' indai mashkur ne gashican Yana jiranki a falo..

Dan Allah mama da gaske?
Kinci gidanku ina Miki karyane?
Dariya Yasmeen tayi tana goge hawayen fuskanta ta tashi ta fada toilet,,tana Shiga mama ta fito tana cewa gatanan zuwa tana can tana shirmen nata.

Murmushi mashkur yayi yakasa amsawa' har mama takai qofa ta dawo tana cewa'kaga munata magana ban tambaya su mummy ba?

Murmushi mashkur yayi Yana cewa'suna lafiya tace a gaisheki

To alhmdllh mama ta fada tana Shiga daki.

Sosai Yasmeen ta zauna ta tsara kwalliya tare da saka wasu Kaya masu shegen kyau turaruka ta feshe jikinta dasu kafin ta fito tana taku cikin nutsuwa Dan Yasmeen badaga nan ba gurin iya daukar wanka da kalamai masu dadi shiyasa ko sun Sami sabani da mashkur bata Shan wahala gurin janye hankalinsa har yaji ya hakura..

Tinda ta fito ya zuba Mata Ido Yana Yaba kyan surarta' a haka harta qaraso kusa dashi'
Jitayi kama ta rungumeshi sedai bazata iya hakan ba nan ta zauna Kan hannun kujeran da mashkur ke zaune tana kashe masa ido' a hankali tasa hannu ta zagaye jikin kujeran tare da kwantar da kanta Kan hannun kujeran daidai inda hannunsa ke Kai.

Ido ya zuba Mata Yana zancen zuci' wai me yarinyarnan take nufi kadafa ta susutani sabida alokacin yafara Jin wani irin Abu na tsirgawa a cikin jikinshi..

Baby fishi kake dani?

Kallanta mashkur yayi Yana girgiza mata Mai Yana kallanta cike da soyayya' to Amma shine zaka sani kuka,,yanzu Dana hadiye zuciya na mutu ya zakayi?

Hakan ma baze taba faruwa ba,,sedai yanzu kema kin chanza Hali shiyasa Nima nakesan chanza nawa kema kiji inda dadi.

Baby ni kuma me nayi?

Au Bama ki sani ba' ko?

To kayi hakuri bazan qaraba'
Kallanta kawai yake Yana mamakin shagwabanta,,da kyar ya bude baki Yana magana Yana kallanta"

Allah yasa'

Da ameen Yasmeen ta amsa tana qara narke masa.

Babu Wanda ya qara magana kusan minti guda daga Baya Yasmeen tace'
Baby wai har lokacin biki yayi? Ni gaskiya sonake adan qara lokaci kaga'
Kinga dakata banasan wannan shirmen zancen naki,,sai ana magana na arziqi saiki tsiro da shirme, wanne irin daga biki?

Nan fa mashkur ya rikice Mata Yana fada a cikin nutsuwa tare da Nuna Mata bacin ransa.

Murmushi Yasmeen tayi tana dariya tare da yimasa gwalo tace' yeeeeee naji ta bakinsa,,Dama sonake naji kadena dokin bikinmu ko haryanzu kanayi?

Ba qaramin sanyi mashkur yaji ba Dan yau har saida yakai hannu da niyyan bigeta ta goce,,daganan suka cigaba da hira,, mashkur be bar gidansu Yasmeen ba sai bayan sallar magrib yamata sallama ya tafi gidan abokinsa jabeer....

Tinda nijlah ta kwanta bacci ya gagara daukanta Banda juyi babu abinda take,,tin tanajin ciwo kadan kadan harta fara riqe cikinta tana yamutsa fuska,, ahankali a hankali ciwon ya riqa sauka a cikinta tare da riqemata bayanta da mara,,tin tana kuka a hankali harta fara me sauti tana Kiran sunan Allah..

A haka bacci yadan fara daukanta,,tana cikin bacci taji fitsari me shegen zafi na damunta' dakyar nijlah ta tashi zaune tanasan Shiga toilet sedai wani abun mamaki qafan yaqi daguwa ga wani irin ciwo dake damunta'Banda kuka tana kallan kofa babu abinda nijlah take..
Dakyar ta iya safka da rarrafe ta sauko akan gadon tana kuka ta rarrafa ta Shiga toilet..

Mummy dake zaune a falo tana kallo yayinda Maryam me aiki ke tsaye a kitchen tana fere doya taji suka ji kukan nijlah' tsaki mummy tayi tana kwana Kiran Maryam"
Maryam ke Maryam kina ina zoki budemin dakin wannan shegiyar yarinyar Naga abinda take,,aini bansan tana gidanba nake zaune a falo,,to Allah ya kareni daga daukan Corona virus a jikinta,,nasan babu inda qafanta be kaiba' dariya Maryam ta gumtse tana tsoran Kada tayi mummy ta hauta da fada...

Dagowa mummy tayi taga Maryam tsaye tana sunne Kai'

Ke kuma ya haka zaki tsayamin aka saikace mara hankali'
Dasauri Maryam tayi qasa da Kai tana cewa mummy kiyi hakuri..

Niba wannan na tambayeki ba,,jeki duba dakin auta kiga me wannan yarinyar takewa kuka Kada muna nan zaune ta hadamana gobara bamu sani ba,,kafin mummy ta qarasa magana nijlah ta saki wani wahalallan ihu tana Kiran Kaka..

Da gudu Maryam ta qarasa dakin tana cewa ke kina ina'

Nijlah da qarasawanta toilet kenan ta cire pant da niyyan zatayi fitsari taga jini nabin jikinta pant dinta yayi kaca kaca da jini gashi jinin hadda guda guda..

Wayyo Allah na jama'a Ku taimakamin wallahi Bari nake.

Dasauri Maryam ta Shiga toilet tana janyo nijlah jikinta,,jinin data gani ne yasata sakin salati tana cewa' ke dama cikine dake?

Eh wallahi Dan Allah ki taimakamin Bari nake nijlah ta fada a galabaice Dan zuwa yanzu magana ma a hankali takeyinta.

Mummy dake zaune taji nijlah na ambatar bari' bata Ida tsinkewa ba Saida taji Maryam na cewa Dama ciki gareki?mummy bata jira Jin amsar da nijlah Zata ba Maryam ba ta miqe tsaye tana tafa hannu tare da sakin kuka tana cewa.......




Kuyi hakuri inada mara lafiya shiyasa kukaji Shiru...



Comment & share






*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*MMN MUHMUD...*



5⃣4⃣&5⃣5⃣


Cikin kuka da tashin hankali mummy ke magana"Shikenan auta kajamana abun kunya' mezan gani a gidana ni hauwa?
Da gudu ta qarasa dakin mashkur Bako sallama tana surutai marasa Kan gado.ita ta manta da ciwan kafanta sabida tsabar tashin hankali datake ciki.

Maryam ko ta duqufa gurin yiwa nijlah sannu tare da qoqarin yadda Zata gyara Mata jiki,,sedai duk yadda maryam taso taba nijlah' nijlah taqi bata dama..
Banda kuka da Kiran Kaka babu abinda nijlah take tana riqe mara yayinda taqi Bari Maryam ta taimaka Mata.

Mummy na zuwa ta fara bin jikin nijlah da kallo tana hawaye' turus tayi ganin jinin dake bin kafan nijlah" haushine ya kama mummy tayi kukan kura ta chafki wuyanta tare da zubamata rankwashi akai'
Dan ubanki haka Ake Bari zaki dagamin hankali,shegiyar yarinyar kawai me suffar aljanu.

Turo Baki nijlah tayi,,cikin kuka tafara magana,Allah Baba Bari nayi ki tambaya kado ai dai yace Nima Zan haihu gashi kuma cikin ya zube ta fada tana sakin wani kuka danma zuwa yanzu ciwan maran yafara sakinta.

Saketa mummy tayi tana tsaki' aikin banza yarinya qarama dako kanta bata Gama sani ba yaje ya daukowa mutane wahala,,to wallahi zanga me gyara Miki jiki a gidan nan sedai ki rufe a haka,,Nina godema Allah dayasa bakimin wannan qazantar a falo ba..

Kuka nijlah tasa tana cewa" Dan Baba ki wankemin wallahi bazan iyaba.

Ke Maryam tashi kifita anan kije ki cigaba da aikin Dana saki'
Maryam da karkarwa tace to mummy'
Nan ta fita tana tausan nijlah sedai bata da yadda zatayi,,tana fita ta fada kitchen ta cigaba da aikin ta..

Maryam na fita mummy ta maida hankalinta ga nijlah tana cewa' to ke kuma me Bari saiki jira Wanda yamiki cikin yadawo kinga Saiya wanke miki,, kafin nijlah tayi magana mummy ta fita tana murmushi.

Falo ta dawo ta zauna Kan kujera ta dora qafa daya Kan daya tana dariya Saida tayi me isarta kafin tace' hmmmm gaskiya yaro yarone Banda haka ina wannan yarinyar ta isa ciki har zatayi bari' Banda hauka irin nata' to nidai me aikina bazata taba wannan jinin me shegen qarni ba we dai ta jira idan ya dawo yasan yadda zeyi da ita.

Tinda mummy ta fita nijlah ta kife cikin jinin tana kuka,,Banda karkarwa babu abinda jikinta yake' hakoranta sai haduwa suke da juna suna bada qara kaf kaf kaf,,lokaci guda zazzabi ya sauka a jikinta me zafin gaske....


Gyara Zama mashkur yayi cike da San Jin shawaran da jabeer ze bashi yace' Uhmn jabeer kenan bazaka gane ba'
Haba mashkur kaima kasani dole ran mummy ya baci kama ci sa'a mummy na Sanka na tabbata da kB ne da tintini mummy ta koreshi a gidanta gaba daya..

Ajiyar zuciya mashkur ya safke Yana cewa' jabeer nasan da haka Amma yakamata ace kaima Ka fuskanceni' be kamata mummy tariqayin haka ba duba da yanayin nijlah' yarinyace qarama idan tana Abu zaka fuskanci batasan komai na raguwa ba Amma duk da rashin wayanta Saida ta gane irin qiyayyar da mummy take Mata' wallahi jabeer ina tsaran girman nijlah batare da mummy ta chanza Hali ba, ya qare maganar idansa cike da hawaye..

Ido jabeer ya zuba mashkur Yana nazarinsa kafin ya bude baki a hankali yace' dadina dakai wallahi ragwanta kama mace' Dan Allah duba yadda Ka bude baki kana kuka saikace mace' nifa bawai bangane abinda kake nufiba,,na gane sosai sedai in tambayeka?

Inajinka cewar mashkur' yafada cike dasan tsayar da kukansa!

Yanzu Dama Kai Baka shirya daukar irin wannan tashin hankali ba kaje Ka auro jinsin dakasan mahaifiyarka bata so?

Oh God' jabeer nasani dole mummy tayi fishi Amma yakamata ta sauko haka sabida nabata hakuri' to shikenan kacigaba da rarrashinta Zata hakura cewan jabeer.

Ajiyar zuciya mashkur ya safke Yana cewa' jabeer nifa ba wannan me damuna ba!

Menene kuma cewan jabeer Yana kallan mashkur cike da tausayawa?
Jabeer Yasmeen ce' narasa yadda zanyi na ajiye soyayyanta na hukuntata akan abinda ta aikata' dariya jabeer yasa Yana cewa ai bazaka iyaba,,abokina nasankafa dasan Yasmeen har tinani nake akan soyayyarku' sedai yanzu na kama bakina na rufe tinda gashi kayimata kafi kishiya' Duka mashkur yakai masa Yana cewa' pls jabeer muyi magana Ka ajiye zancen wasa' wallahi Nima banso hakan ba naso raguwa da Yasmeen ita daya kamar yadda take a cikin gidansu sedai kash qaddara ta Riga fata..

Dariya jabeer yayi Yana cewa hhhhhh daga Baya kenan angon nijlah' murmushi mashkur yayi bece komaiba jabeer ya cigaba da magana" abokina abinda kayi kayi daidai Dan be kamata Ka hukunta Yasmeen da hukunci me tsauri ba,,duba da yadda akayimata kishiya tinkafin ta shigo Dan ma kishiyar kwailace.

Murmushi mashkur yayi Yana cewa eh nidai nace yanzu ya zaayi da maganar nijlah?

Shiru jabeer yayi Yana tinani kafin yace' mashkur inaga kawai a nemi makaranta me kyau asakata ciki islamiyya da boko..
Girgiza Kai mashkur yayi' nan jabeer ya Tabe Baki Yana cewa Kai nifa banasan iskanci yazaayi muna magana ta Riga Bani amsa da Kai,, sorry jabeer a gaskiya banasan nijlah tafara haduwa da wasu kawaye tana cikin wannan hali,,nafiso saita fara wayewa kafin ta Shiga cikin mutane'
Sabida me mashkur jabeer ya tambaya?
Sabida ina gudun su hure Mata kunne..

To shikenan kaima kayi magana' toga shawara ta biyu' meze Hana mu kaita makarantar matan aure taje can ta koya Zama da mutane tare da wayewa da girki Kai hadda Kula da miji za'akoyamata a ciki.

Murmushi mashkur yayi yace hakan yayi Amma kafin nan Nima inasanta akusa Dani sedai bayan kwana biyu Zata iya tafiya kaga lokacin Nima na Samu sai kuma yakasa qarasawa.

Baki jabeer ya riqe Yana cewa wai kana nufin har rage zafi kake da wannan yar yarinyar' dasauri mashkur ya zaro Ido waje' Yana cewa' ah haba kaga niba haka nake nufiba nafi so Ka samamin malama dazata riqa zuwa har gida tana koyamata kafin biki kaga da an Gama biki saita wuce makaranta.

Murmushi jabeer yayi Dan ya Riga ya harbo jirgin mashkur yace' to shikenan kwana nawane biki.

3 weeks ya rage Insha Allah' Allah ya kaimu jabeer yafada Yana tsokalan mashkur.

Harsun Gama hira mashkur yace' kaga abokina wai kuwa ina Shi Nasir Ka Bani wayansa inasan magana dashi?

Hannu biyu mashkur yasa ya dafe kansa Yana cewa' Kai Amma ban kyautaba' wallahi jabeer tin bayan dawowana ban qara waya da Nasir ba.
Nasan yanzu hankalinsa a tashe yake'

Tab Amma wannan iyayenta ba qaramin kasada sukayi ba,,wai kana nufin daga Kai sai nijlah kuka Baro kauyen kankan?
Dariya mashkur yayi Yana cewa da Bello suka hadoni Niko na korashi sabida banaso yazo yaga tashin hankalin da mummy Zata man,,Amma yanzu Zan dauko SIM card Dina nasan Nasir duk inda yake hankalinsa a tashe yake'.

Gaskiya Ka gaggauta kiransa Dan Baka kyautaba' hakane jabeer Nima banso daukan lokaci me tsayi har hakaba,,abubuwane kawai da suka sha kaina gashi itama yarinyar ta cika rigima' Kai wallahi har kash.....sai kuma yakasa qarasawa Yana Sosa Kai..

Daga nan suka Dan taba hira mashkur yace' nizan wuce kaga lokaci Yaja gashi nabar nijlah a daki,,sabida nasan Zan Dade shiyasa ban kaita saban gidaba na kaita gidan mummy...

Gidan mummy fa kace mashkur?
Eh wallahi jabeer can na kaita shiyasa kaga inata sauri ban saki jiki na zauna ba ,,yanzu ma sabida dolene zuwan.

Hakane yanzu dai kayi saurin tafiya sauran bayanin Zan Kira Ka sai muyi a waya.
To shikenan jabeer nagode nan ya miqa masa hannu sukayi musabaha,, har mota jabeer ya raka mashkur Yana daga masa hannu...

Sosai Mashkur ya saki gudu a mota Yana yi Yana adduan samun ta lafiya sedai tindaga bakin get yake jiyo hayaniyar mummy..
Dasauri ya fito a motan ko parking ne Ida gyarawaba ya Shiga ciki,,

Assalamu alaikum

Yauwa sannu da zuwa' angon nijlah saika qarasa Shiga ciki,ga matarkacan tayi Bari.

Bari kuma mummy mashkur ya tambaya?

Dan gidanku tambayana kakeyi' Ka wuce kaje Ka gyaramin gida kafin nayi Baki
Showing 39001 words to 42000 words out of 65025 words