tabe Baki tana cewa'

Kanina badai kafara nunamin banbanci ba,, yanzu sabida Allah sai kuje Shan ice cream ku dawo haka bako leda..

Murmushi mujaheed yayi yana sosa Kai ya zaunar da nijlah kusa da aunty husna shi kuma ya dawo kujeran dake kusa da daddyn Ayman ya zauna yana cewa'

Aunty ba laifina bane' kinganta nan itane tace' bata yadda abama kowa ba!

Zaro ido nijlah tayi aunty husna tayi saurin magana..

Murmushi husna tayi ta Dora hannunta kan nijlah tana cewa'
Kanwata Wai hakane?

Boye fuska nijlah tayi takasa magana ..

Mujaheed yace' to kingani' ba,,hakan kadai ya Isa ya tabbatar Miki,,sabida tace' na masoyane..

Kai kanina kadafa ka hada fada daddyn Ayman ya fada yana cigaba da latsa computer dake gabansa.

Da gudu nijlah ta tashi ta shiga daki tana dariya yayinda takejin tafi kowa sa'a Dan yanzu farin cikin datake ciki baza taba misaltuwa ba,,kan Dan qaramin gadonta ta fada ta rungume duka hannunta a qirji....


Dariya suka sa ganin yadda take gudu hips dinta sai juyi suke...

Kallan husna mujaheed yayi yace' Kai aunty yana ga kina kallemin mata yafada cikin hade fuska..

Eh lallaima yaran nan daddyn Ayman kaji abinda yake fada ko?

Kunfi kusa indai keda mujaheed ne,,nasan duk Wanda ya shiga shizeji kunya..

Kukan shagwaba husna ta saki tana cewa' Amma dai kana kallo ya shiganwa budurwanshi,,shine ni zakaqi shigan min ko..

Shikenan shikenan ya Isa haka indai ice cream ne ki shirya muma yanzu zamu fita saiki Sha ko..


Murna husna tayi tana cewa' to kagani dai,,dadin abin Nima inada miji..

Bazawar dariya mujaheed yayi yana cewa' Kai aunty kin cika kishi to bari kiji..

Mu babu inda mukaje' muna hanya nijlah ta rigime tace ita gaba daya ta fasa zuwa'

A tare husna da daddy Ayman suka ce sabida me?

Ajiyar zuciya mujaheed ya safke ya fara basu labarin yadda sukayi da nijlah'

Tin kafin ya gama husna tayi hamdala ga Allah sabida Dama ita burinta nijlah tayi karatu ta waye ta yadda ko sun maidata ga iyayenta.

Iyayen nata bazasuji haushi sosaima..



_______

Bangaren mashkur abin ba'a magana,,sedai duk da haka saida mashkur ya takura aka bashi sallama sabida yace maganinsa bana asibiti bane Dan haka a nemo masa nijlah a duk inda take ta hakane kadai hankali sa ze kwanta..





Kuyi hakuri da wannan,,yanzuma dakyar nasamu nayi,, nagode sosai da kaunarku gareni' ina alfahari daku masoyana a duk inda kuke.




Comment & share







*MOMN SULTAN CE*✍✍✍
💘💘 *YAR SADAKA..💘💘*


*STORY & WRITING...*
*BY*
*MOMN SULTAN.*


*DEDICATED TO...*
*MOMN AMATULLAH.*


*SPECIAL GIFT To...*
*💞 HUSSY❣...*



7⃣8⃣&7⃣9⃣


Kwance yake kan doguwar kujera' Banda juyi Babu abinda yake' jiyake inama mutuwa zata daukeshi koya huta da abinda yakeji'
Mashkur' mashkur yaji Daddy ba Kiran sunansa,,be iya amsawa ba ya yinqura da kyar ya iya Tashi' fitsari yakeji' Amma baze iya tashiba zaune sabida koya ya motsa jikinsa jiyake kama ze fadi' sosai yayi baki ya rame kallo daya zaka masa kagane Yana cikin tashin hankali mara misaltuwa.

Kallo daddy ya bisa dashi Yana cewa' auta menene ko Dai jikin ne?

Girgiza kai mashkur yayi ya bude baki a hankali yace' daddy fitsari nakeji'
A hankali daddy ya kama hannunsa ya Shiga dashi cikin toilet nan ya sakeshi Yana cewa'kayi fitsari nizan jiraka a waje daka Gama saika kirani kaji?

Juyawan daddy kenan mashkur ya fara qoqarin cire wandonta' beyi aune ba yaji kafansa ya dau karkarwa nan yayi saurin riqe kan famfo Yana Kiran daddy.

Dasauri daddy ya shigo Yana tambayansa' menene auta kayi fitsarin ko Yaya.

Cikin kuka mashkur yace daddy bazan iyaba' Sai ya dafe saitin zuciyarsa Yana cewa'daddy zuciyana zata buga Dan Allah daddy ka taimakeni nijlah ta dawo gareni,, wallahi zaku iya rasani ya qare maganar Yana rungume daddy..

Hannu daddy yasa Yana shafa bayansa alamun rarrashin' ganin yayi shiru ya Dena kukan yasa daddy tambayansa'
Auta kayi fitsarin?

Bazan iyaba Babu abinda Zan iya matuqar nijlah Bata dawo gareni' ba,,meyasa zatayimin haka menayi Mata daddy Dan Allah ka gayamin?

Yawu me daci daddy ya hadiye batare dayayi Magana ba yafara qoqarin taimaka masa nan yayi fitsarin daddy ya bashi ruwa ya wanke tare suka fito mashkur Na jikin daddy Yana fidda numfashi dakyar dakyar..

Dakinsa daddy ya wuce dashi nan ya kwantar dashi kan dagonsa Yana cewa'
Mashkur kayi hakuri' kana kallo nayi iyakar qoqarina Akan batan yarinyarnan Amma duk da haka ba'a gantaba,, inaso ka dauka batan nijlah daga Allah ne'' yayi Hakan sabida ya jarraba imaninka' Na tabbata idan kayi hakuri wata Rana nijlah zata dawo gareka..

A firgice mashkur ya Tashi zaune Yana cewa'
Daddy wata Rana fa kace' yaushe Kenan? Yau ko gobe? Jibi ko gata?

Daddy bazan iya jurewa ba bansan a hannun da take ba,,ina tsoran kada a cutar da marainiyar Allah,,nasan duk a inda take hankalinta yafi nawa Tashi daddy ka taimakeni tinda ni ka hanani fita nemanta..

Hannunsa daddy ya riqe Yana cewa' Amma Dai kana kallo Na zagaye gidajen radio da television Na Bada sanarwan cikiyanta kai har gidan jaridu Sai da nakai cikiya Amma kake Abu kama Wanda kaga Na rumgeme hannuna Na zuba ido banyi komai ba?

Dan Allah daddy karka bari mafarkina ya zama gaskiya' ko kana so na rasata?

Wallahi daddy Zan iya Zama mara amfani da mamora na kare rayuwana cikin qunci da tashin hankali,, daddy Zan iya Zama mutum mutumi idan har Na rasata.


Kafin daddy yayi Magana mummy dake shigowa dakin tace'
Wallahi karyane auta,,zaka samu farin ciki irin wanda nake fata,,Nina sani' wannan duk abinda kake Na Dan lokacine da an daura aurenka da Yasmeen shikenan zata mantar da kai wancan jakar.

To waini Dan Allah uban wa yace ta fita' ina ita Da kanta ta fita tabar gidan?
Ita Bata damu da Hakan ba Sai kai zaka tadamana hankali.
Duba kaga yadda ka rame ka Zama kwaran gwal Sai hanci.

To wallahi ka kiyayeni' kai Banda Allah yasa an rufe fita ko ina sabida wannan cuta da Allah yakawo ai da tini ka dade da barin qasar nan dan ni bazan iya zuba ido kana wannan abun kunyar ba,,yarinyar dako nonon kirki Babu a qirjinta kake wannan haukan..

Toka sani nijlah ta tafi tafiya ta har abada' kaini ina fata nijlah ta hadu da....


Ya isa haka''' mummy taji daddy ya daka Mata tsawan daya hanata qarasa abinda takesan fadi..

Cike da tashin hankali,, mashkur ya maida kallansa ga daddy Yana cewa'
Dan Allah daddy karka bari maganganun mummy su tabbata inaso ta dawo gareni wallahi idan maganarta ta Zama gaskiya Zan iya rayuwa cikin kunci da bakin ciki..

Sai ya maida kallansa gaa mummy Yana cewa' mummy Dan Allah kidena mummy namiki biyayya a matsayinki Na mahaifiya! Yakamata ace kema kinso abinda nake so!

Ko kinaso maganganunki su Zama sanadin ajalina,,tashin hankali Na bakin ciki na,a qarshe na mutu ban haifamiki yaran da kikeso daga gareni ba?


Kasa jure sauraran maganganunsa mummy tayi ta juya da sauri ta fita a dakin tana mejin takaicin yadda autan nata yafada tarko da kogin soyayyar jinin mutanan datafi tsana a rayuwanta..
Tabbas idan Na tsaya Na cigaba da sauraran maganganinsa zeyi galaba akaina sabida bazan iya jure ganin tashin hankali autana ba,,dakinta ta shige ta fada kan bed tunanin ta inda zata bullowa al'amarin..

Tinda mummy ta fita mashkur ya rungume daddy Yana cewa' daddy nima Zan tafi yawan Duniya tinda mummy Bata San abinda nakeso,,ko Allah ze hadani da nijlah a can,,Amma kafin nan daddy inaso a daura aurena da Yasmeen..

Shiru daddy yayi ya zuba masa ido harya Gama Magana.

Ganin daddy yayi shiru mashkur ya bude baki a hankali yace'
Dan girman Allah daddy kada kace ah ah ka barni nabi zabin zuciya ta..


Nannauyar ajiyar zuciya daddy ya safke kafin yace' shikenan auta Na yadda za'a daura aurenka da Yasmeen sabida kaima ka samu me kula dakai tinda Naga itama kana santa.

Eh daddy inasanta da Yasmeen nafara soyayya inamata so irin wanda nakema nijlah sedai Hakan baze taba Mantar Dani Abar kaunata nijlah ba sedai ze ragemin radadi da zugin rashinta idan har ina tare da Yasmeen..

Amma inaso ka sani Babu inda zaka,,koda anyi aurenka sedai ka zauna anan damu sabida muma hankalinmu zefi kwanciya idan muna ganinka' batin tafiya Duniya Kuma ka ajiyeshi a gefe Dan Babu inda zakaje..

Bude baki mashkur yayi da niyyan Magana daddy ya katseshi,,kaga banasan dogon bayani ka kwanta ka huta nizanje Naga mahaifin ita Yasmeen..

Kwanciya mashkur yayi ya rungume hannunsa Yana tinanin Yasmeen..

Be jima da kwanciyaba Nasir ya fadomasa' waya ya dauka ya kirashi nan yake gayamasa tashin hankalin daya faru..

Sosai hankali Nasir ya Tashi Dan yafi kowa sanin halinda kaka da Malam ke ciki kai harma da mutanan kauyen garin kankan..

Ran Nasir a bace ya hau mashkur da fada ta inda yake Shiga Bata nan yake fita ba,,Yana cewa' yanzu shikenan kajamin bala'i Dan wallahi bazasu taba Bari Nabar garin nan batare dasu ba..

Jikin mashkur a sanyaye yace' nima ba haka naso ba,,Nasir dakaga halin Dana Shiga bazaka gayamin haka ba Amma bakomai haka Allah ya tsaramin..

Haka Dai Allah ya tsara mana cewar Nasir cikin fada.

Kayi hakuri Nasir insha Allahu za'a ganta' to naji Amma ni haka Zan zauna nawa iyayen nasan ganina Babu dama?

Shiru mashkur yayi Yana tunani kafin yace yauwa Nasir kasan me zakayi?

Saika fada ni Kawai ka gayamin Dan wallahi kaina ya kulle.

To shikenan Kawai Kabi dare ka gudu idan yaso daga Baya Sai mu koma abasu hakuri Na tabbata lokacin nijlah ta dawo gareni..

What mashkur kana haukane,,sokake kayi sanadiyyar mutuwar kaka da Malam kaga nidai Kawai ka sake tunani.

Hmmm Nasir Kenan Hakan danayi shine kawai mafita ka gudo cikin dare Dan wallahi idan kaka taji batan nijlah zata iya hadiyen zuciya ta mutu kaga Kenan anyi ba ai ba..

Shiru Nasir yayi kafin yace to shikenan Bari yanzu Na fito tin kafin tsare ya tsala...

Sallama sukayi mashkur yayi murmushi Yana cewa' Na gama da matsala guda...


Basu jima da Gama waya ba mummy ta shigo da plate shaqe da abinci' kauda kai mashkur yayi Yana cewa'mummy ni a koshe nake..

Zama mummy tayi tana rararshinsa Amma duk da haka mashkur yaqi amsa a dole mummy ta hakura ta fita a dakin tana buga tsaki..

Tana fita bacci ya dauke mashkur..


_______



Karfe 9 na dare Yasmeen ta farka fuskannan Tata ta kumbura tayi jajur da ita,, dasauri mubeena ta fara tambayanta tana cewa'

Kawata menene ki haryanzu baki dawo daidai ba.

Uhmn mubeena Kenan tayaya kike tinanin Zan iya dawowa cikin hayyacina alhalin kina gani wata banza kuchaka 'yar kauye Wanda Bata da galihu tayi nasaran Shiga cikin gonata har tayi shuka a ciki.

To shine me?karki manta haryanzu mashkur nasanki menene abin damuwa?

Akwai mana ke Bari ingayamiki wallahi ko' mutuwa nayi bazan taba kaunar mashkur yayi wani auren ba balle yanzu danake a raye..

Riqe baki mubeena tayi tana cewa' to GA abinci nan saikici..

Bazan iya Ciba,, ki daukesa kawai..

Kai yasmeen kinada matsala idan maganar aurenkune anfa Gama Magana domin kuwa daddyn mashkur yazo har gida sunyi Magana da Abba akan maganar daurin aurenki gobe.

Bayan Sallah Sai ayi duk wani shagali da kike so.

Zaro ido Yasmeen tayi tana cewa' ke mubeena banasan Karya?

dagaske fa cewar mubeena tana cewa'

Wallahi kina bacci akayi komai aka gama,,nidai fatana kada kice baki amince ba..

Murmushi Yasmeen tayi ta ce' Na amince mubeena nima fatana daya nakasance tare da mashkur' idan bana tare dashi hankalina baze taba kwanciya ba..

Dama Abu guda nakeso ayi chasu a raqashe a lokacin aurena' yanzu Kuma an amince daga Baya za'ayi kinga shikenan Sai a daura auren kona samu damar mallake zuciyar baby'' ya cire wancan shegiyar daga cikinta..

Dariya mubeena tayi tana cewa to yanzu saikici abinci muje ko gyaran gashi ayimiki da kunshi.

Tashi Yasmeen tayi ta dauka mayafinta tare da sa takalmi tana cewa' Tashi muje Nina koshi..

Tashi mubeena tayi suka fita,,karfe 9 :20 suka isa wani katafaren saloon,, anan aka gyarawa Yasmeen gashi tare da kunshi irin Na amare' gyaran be tsaya anan ba saida aka Mata dilka da Halawa,,idan Mai karatu be mantaba,, Abaya mun fadi irin magunguna Na gyara' da Yasmeen ke amfani dasu tin daga lokacin da akasa aurensu har zuwa yanzu.

Dan haka Bata da wani matsala Na gyaran jiki daga ciki har waje lolxx..


Basu suka dawo gida ba Sai karfe 11 Na dare,,Suna zuwa mama zata fara fada Abba ya hanata nan itama tayi shiru sabida tafara jimamin rabuwanta da tilon diyar Tata..



__________


Kwance take a daki ta hada kai da gwiwa tana tinanin rayuwa' Babu shakka mutane Kala Kala ne wasu Na da kirki wasu akasin haka' dafe qirji tayi tana cewa'
Yanzu me nayi'shin nima Na Shiga cikin mutanan kwarai ko kuwa?

Lumshe ido tayi tana tinanin rayuwar datayi da mashkur' murmushi Mai ciwo tayi data Tina lokacin da Yasmeen ta hau kanta tana duka iwa jaka agaban mashkur batare daya dauki wani mataki ba,,Sai Kumar ta Tina dukan daya Mata a daidai lokacin data barmasu gidansu ta fito neman inda zata hau Mota ta koma gurin kaka..

Kuka ta saki tana cewa' kado Baka Sona Dan haka nima Na hakura dakai kaje can ka zauna da Yasmeen tinda itace zabin Raina.

Sai ta tsagaita da kukan tana cewa' Anya ko Na kyauta' idan Na Manta alkairin da kayimin Sai Kuma ta bude ido tana cewa' tabbas mashkur ba kaunata kake ba kana Dai San zamana a kusa dakai kodan ka riqa matsani ta inda kakeso' tinawa tayi da irin kukan da take masa idan Yana shafa qananun nononta kafin zuji wahala su Girma Dan yanzu qirjin nijlah cike yake da kayan yaqi lolxx..

Tana nan zaune Mujaheed ya shigo Yana cewa' ke wai Haryanzu me kike da bazaki fito kici abinci ba?

Dasauri nijlah ta rufe Ido tana sauke numfashi a hankali'

Jikin gadon ya qaraso Yana cewa' badai bacci kikayi ba?

Leqata yayi yaga idonta a rufe alaman bacci a tare take,,nan ya zauna yasa hannu Yana buga katifan tare da Kiran sunanta.

Sweety, sweety na ki tashi haka kafin yinwa ya illatamin ke' shiru nijlah tayi taqi motsawa ganin haka yasa Mujaheed sauka Akan gadon ya bude fridge.

Ruwa me sanyi ya dauko Ya fara shafa Mata a fuska Yana Kiran sunan.

Dasauri ta riqe hannunsa tana dariya..
Sallamar husna ya hanata Magana ta safke qafanta a qasa tana cewa' aunty sannu da zuwa.
Ran husna a bace ta amsa tana cewa' muje daki nah''inasan ganinki'

Sum sum Mujaheed ya fita a dakin Yana turo baki ,,ranshi a mugun bace..

Mujaheed na fita' husna tasama kofa key ta zuba nijlah ido..

Sosai nijlah Tasha jinin jikinta ta safke kanta qasa lokaci guda jikinta ya dauka karkarwa sabida tsoran aunty husna da taji ya ratsa dukkan jikinta..




Comments & share









*MOMN SULTAN CE*✍✍✍
💘💘 *YAR SADAKA..💘💘*

*STORY & WRITING...*
*BY*
*MOMN SULTAN.*


*DEDICATED TO...*
*MOMN AMATULLAH.*


*SPECIAL GIFT To...*
*ALL MY FAN'S...*


🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


*KARSHEN 'YAR SADAKA BOOK 1....*

*COMING SOON*

*YAR SADAKA BOOK 2...*

*Bayan sallah in Allah ya aramana Rai da lafiya...*



8⃣0⃣...



Kallan Nijlah aunty husna takeyi da tsananin mamaki,, Bata damu da yadda jikin nijlah ke karkarwa ba ta Sami guri kusa da ita ta zauna' cikin dauriya husna ta kama hannun nijlah duka biyu ta riqesu cikin nata,,ta Kuma kafeta da Ido tana kallanta.

A hankali nijlah ta Dago tana satar kallan husna take kwayar idonsu ta sarqe Dana juna' dasauri nijlah ta dauke kanta tana zumburo baki gaba.

Murmushi husna tayi ta saki daya hannun nijlah ta Dago kanta dashi tana cewa'
Kina Jin kunyan kika Bari wani qato Yana tabamiki jiki?

Saurin zaro ido nijlah tayi' cike da shagwaba,dajin kunya tace wallahi aunty...
Karki qarasa nijlah' nafa gani da idona,, ashe baki da wayo?

Shiru nijlah tayi tana qoqarin fara hawaye aunty husna ta zare Mata ido tana cewa' idan kikamin Kuka saina batar miki'

Hadiye kukan nijlah tayi ta sunke da kanta qasa gabanta Na tsananta faduwa' jitayi inama kasa zata tsage ta shige ciki Dan kunya' cigaba da Magana aunty husna tayi''

Haba nijlah banyi tsammanin haka daga gareki ba,,nayi tinanin kece Zaki tayani kare.kanki,,Amma kina kallo kinyi shiru kin zuba ido Saima dariya kike,,kinasa Rai ni husna nizan tsawatar kome?

Shiru nijlah tayi,,husna tace' Magana nake.

Bakin nijlah Na rawa tace ah ah.

Tam yayi kyau aunty husna ta fada tana cigaba da magana'
Nijlah Mujaheed da kike gani kanin daddyn Ayman ne uwa daya uba daya,,duk da baki da shakaru nasan Zaki gane irin soyayyar da Dan uwansa yake nuna masa' ko rantsuwa nayi bazan kaffara ba Akan soyayya daddyn Ayman Akan Mujaheed tafi Wanda yakemin' kema shaidace sabida a gabanki yayi wasu abubuwan.

Duk da Mujaheed ya girmeni Amma Hakan be hanasa girmamani a matsayina Na matar wansa ba,, Kuma Nina riqe Mujaheed tin Bayan da mahaifansu suka rasu.

Nijlah nasan halinsa idan yanasanki Babu abinda baze Miki ba' Mujaheed betaba soyayya da wata 'ya mace ba Sai akanki,,Mata da yawo Suna kawo masa Hari da tayin kansu Amma yaqi amsasu gaba daya hankalinmu a tashe yake sabida rashin aurensa..

Kwatsam Allah ya kawoki cikinmu ya Kuma Yaba dake harya zabeki a matsayin Wanda zai aura,,
To meyasa Zaki saki jiki dashi Yana tabaki yadda yakeso?

Dasauri nijlah ta Dago tana kallan husna sedai wannan Karan batayi yinqurin Magana ba tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.

Amsa Zaki bani bawai kisani a gaba kina kallo ba..

Ko kinaso nayi Magana Dan uwansa yaji haushina koma yayi tinanin bana kaunar Dan uwansa?

Girgiza kai nijlah tayi tace' aunty kiyi hakuri wallahi ba wani Abu Yamin ba,,fuskana Kawai ya taba..

Cikin zafi husna tace' dan gidanku fuska Kawai ne' Ko Hakan ya dace?

Bazan qaraba nijlah tafada tana turo baki' Dan ita zuwa yanzu tafara gajiya da maganganun aunty husna duba D yadda takejin dadin kasan cewa da Mujaheed' Dan Yana Bata kula sosai da sosai har Yana Sawa tana mantawa da ita din wacece..

Shikenan cewan aunty husna tana kallan Nijlah' a hankali Kuma tace'

Nijlah Niko inasan Jin labarinki' a ina kike meya fito dake daga gida a irin wannan lokacin?

Rass Rass gaban nijlah ya fadi lokaci guda bakinta ya fara karkarwa tafara qoqarin janye jikinta ana husna..

Riqeta husna tayi tana cewa' Dan Allah ki gayamin banaso wani Abu mara kyau yafaru' idan haka ta kasance nice sila,,gashi a yanzu bani da damar maidaki gurin iyayenki..

Amma idan baki gayamin ba,, ayau Zan fita dake a gidannan dan....



Dakata' dakata''sukaji daddyn Ayman yafada cikin wata irin murya Wanda ita Kanta husna Bata tabajin yayi irin taba.

A tare suka Kalli kofan jikin husna Na Bari ta Tashi da sauri tana rufe bakinta..
Baya ta riqayi tanasan boyewa sabida yanayin da taga mijin nata a ciki baze Bari ta iya Magana ko bashi hakuri
Showing 60001 words to 63000 words out of 65025 words