gangan danladi me gidan kagane Na tashi..

Tin Daga nesa su indo da Abu suke kallanta Har ta qarasa suka fara gaisawa,, nijlah Zaki Sai tuwan ruwa?turo baki nijlah tayi tace,,kinga niba ciye ciye ya kawoni ba,,kallo kawai zanyi Na Koma gida,kaka tace kada Na zauna,,Bata Ida rufe baki ba Taji an Kira sunanta" dasauri ta dago Ido tana duban Wanda ya Kira sunanta,,bazata taba manta wannan fuskan ba,,Dan shine mutum Na farko daya taba dukanta..

Murguda masa baki tayi tana cewa,,lafiya Zaka Kira sunana?

kiyi hakuri nijlah Bada niyya nayi Hakan ba,,kinji yarinya, Nasir ya fada Suna Hada Ido da mashkur dayayi kama besan abinda suke ba..

Yarinya Kuma,,nice ma yarinya,,to sannu babba,,dariya Nasir yayi Yana Kallan nijlah,,nidai Duk ba wannan ba,kin yafemin?

Karka damu Allah yanasan me yafiya nayafema,,Nima ka yafemin batama Mota danayi"

Nagode sosai Nasir ya fada Yana murmushi,,sedai Bani Zaki nema tafiyan Bata motor ba,kinga Wanda Zaki nema danba motana bane nashine,Nasir yafada Yana nuna Mata mashkur.

Har qasa nijlah ta sunkuya tana kallan fuskanshi tace,,Dan birni kayi hakuri Kaji, murmushi mashkur yayi,ya Bude baki a hankali yace,Tashi kinji kanwata,,maqale kafada nijlah nan yayi murmushi danya gane nufinta yace, shikenan Na hakura Amma Karki qara zana Mota kinji,,to nijlah tace ta Tashi da gudu zatabi kawayenta mashkur yace kinga nijlah zo..

Juyowa tayi da niyyan zuwa idanta ya safka Kan Na iro daya zuba Mata su alamun tambaya" lah iro yanzu nake dubanka anan,Hade Rai iro yayi Yana hararanta,,kai iro Daga tambaya Sai harara, nikaga tafiyana..

Ke nijlah Ina kikasan wadannan ya fada Yana nuna mashkur" cike da tsoro nijlah tace yayanane Daga birni suka zo" kin tabbata eh mana nijlah ta fada tana kallan mashkur" sosai mashkur ya cika da mamakin wayo irin Na yarinya sedai abinda yake tambayan kansa shin wanene wannan yaran da nijlah tayi Karya.

Nijlah Na ganin tafiyan iro ta qaraso kusa da mashkur tace gani" naira hamsin mashkur ya miqa nijlah Yana murmushi,amsa wannan Duk da Naji kince ba ciye ciye ya kawokiba,,

Nagode sedai kaka ta hanani amsar kudin samari indai ba iro ba,,wanene iro mashkur ya tsinci kansa da tambaya"

Iro yarone dabe wuci shekara 21 ba,,shine yake neman auren nijlah,, mashkur yaji Bello Na bashi amsa"

Kai Bello kana nufin kace wannan yarinya saurayi ne da ita??
Kwarai dagaske Bello ya bashi amsa,rufe fuska nijlah tayi tana dariya" mamaki sosai ya cika mashkur Nasir ne ya qara kallan nijlah yace yanzu Ke yarinya kinsan menene soyayya,,kasa Magana nijlah tayi ganin haka yasa Bello cewa..

Kinga nijlah amsa kije ki Sai abinda kikeso nizan Gaya yakumbo,,kasa amsa nijlah tayi Duk da tanasan siyan Abu a dandali,,qara miqa Mata kudin mashkur yayi,,Kanta a qasa tace Ni biyar Zaka Bani wannan yayi yawa ta fada Kanta a qasa..

Ki amsa wannan Bani da chanji,,wannan shine qaramin kudi a jikina,,Nasir Ko kanada Goma,,ta amsa wannan Nasir ya fada alamun Babu..

Kasa amsar kudin nijlah tayi,,kanwata ki amsa mana,kefa Naji yanzu kina Gaya Wani Ni yayankine kodama Karya kike,,Kunya ce ta kama nijlah nan ta miqa hannu ta amsa kudin,,
Nagode sosai Allah yasaka da alkairi,,Nima gobe Zan Baka fura da nono,,

Bata jira amsar Saba ta Shiga dandali tana murna,,

Bata Dade a gurin ba ta tafi,,tin Daga bakin kofa nijlah Ke Kiran kaka,,kaka!
Kai wannan yarinya Ni harna fara bacci Zaki tadani,,kaka kinga wannan Dan birnin ya Bani kudi harna Sai abin biyar kinga sauran,ta fada tana miqa kaka Chanjin..

Lalala nijlah waya baki wannan kudin kaddai kicemin Wanda ya dakeki dazu,,kaka bashi bane Wanda ya riqe Yana mishi fada,,Kuma Shima yabani hakuri,,to Duk Naji Amma Daga Yau Karki qara amsar kudi ahannun Wani koba na hanaki ba,,kaka Nima ban amsaba,Ina wannan bellon na gidan Liman,eh nagane cewan kaka,to shine yace Na amsa Ze gayamiki,,to Allah ya akaimu goben zansa Malam ya tambaya.



Washe gari karfe 10 na safe Malam yaje gidan liman anan sukayi magana da Bello ya tabbatarwa da Malam yaran bashida matsala,sannan hankali Malam ya kwanta.


Tin asuba mashkur yake Kiran mummy sedai network ya Hana wayan Shiga,,dafe Kai yayi Yana salati,,lafiya mashkur badai wani matsala bane?
Matsalane babba Nasir tin jiya nake Kiran mummy wayan yaqi Shiga gashi kasan halin mummy na tabbata yau bata rintsa ba.
Ni abinda ke damuna Kenan tinda muka zo ban samu kowa a waya ba,,ance semun fita wani Dan kauye anan kusa zamufi samun network,,kaga Nasir Kai kasan da haka Ka Bari nake ta kira,tashi da sauri muje na Kira mummy"
Dariya Nasir yayi yace Kai mashkur tinda muka zo banji Ka Kira Yasmeen ba sai mummy.

Murmushi mashkur yayi kafin yace, Nasir bana hada mummy da kowa na tabbata yanzu Yasmeen tana daki ko bacci taba tashi ba,,mummy ko bazata iya bacci ba Dan bataji lafiya naba.

Nasir be qara magana ba sabida yadda da maganan mashkur ya tashi suka fita,,

Bello suka gani yazo kawo musu kayan kari,,abokaina ina zuwa,,waya mukesanyi cewan mashkur Yana miqa masa hannu,,bayan sun gaisa Bello ya ajiye kayan abincin suka nufi kauyen..

Da Malam suka hadu a hanya nan Malam yake masa godiyan kudin Daya ba nijlah,,bayan Malam ya tafi mashkur ya juya Yana kallan bello..

Bello Naga wannan mutumin sai godiya yake akan naba nijlah naira hamsin,,nawa Raina 50 take daze Namin godiya har haka???


Hmmm Kai agurinka naira 50 bata da yawa Amma Banda gurin Malam da jikarsa nijlah" au dama ba shine mahaifinta ba"

Mahaifinta da maihaifiyarta sun rasu suke Kula da komai nata sedai Basu da karfi,, Dan ma suna San yarinyar kullum addu'a suke Allah ya kawo Mata mijin aure su auran da ita su huta"

Aure kuma nijlah har nawa take daga ganin yarinyar bata Ida shekara 11,, murmushi Bello yace yace ai nata Kai hakabama saura wata 4 ta cika shekara Goma.

Tashin hankali Amma akesan auran da ita cewan Nasir cike da mamaki,,to Nasir ya zasuyi Basu dashi kuma mu a wannan kauyen muna auradda yara shakara 13 zuwa 14..

Hira sosai suka riqa tafiya Bello Yana Basu akan labarin iyayen nijlah da rayuwarta,,tin daga nan mashkur yafara Jin tausan yarinyar jiyake dayana da yadda zeyi Daya taimaketa, akan auren da akesan yimata,,ahaka har suka Kai inda network ya hau Kan wayansu..

Hamdala mashkur yayi ya Kira layin Mummy,,bugu Daya biyu ta dauka muryanta a sanyaye" Assalamu alaikum mummy na kin tashi lafiya??
Kaima kasani ko lafiya ko akasin haka,,yanzu abinda kayi Ka kyautamin Kenan kodan kaga na damu dakai ko auta.

Kiyi hakuri Mummy wallahi ba laifina bane garin me ba network yanzuma seda mukayi tattaki zuwa wani guri me nisa aka samu network.

What mashkur kana nufin bazan riqa samunka a waya ba,,to wallahi kayi gaggawan baro wannan kauyen kafin naci mutumcinka,,Kako San a zaune na kwana.

Pls mummy kiyi hakuri iya yaune Insha Allahu za'a gyara,,yafada haka danya kwantar Mata da hankali"

Nidai nagayama kadawo kafin na Gaya daddynka tinda ni Ka rainani,,inyaso Shi yafada kaji" kiyi hakuri bata amashi ba ta katse Kiran ranta a mugun bace" yasan koya Kira ba dauka zatayi ba Dan haka ya tura Mata text massage.

Layin Yasmeen ya Kira dake zaune kusa abbansu tana Shan ice cream" murmushi tayi tace lah abba kaga mashkur ya kira.

Murmushi abba yayi yace dama na gayamiki ze Kira saiki dauka kafin ya katse,, dasauri ta dauka ta tashi ta koma dakinta,,hello hubby nah!

Na'am baby kin tashi lafiya,,lafiya qlau sai kewanka,,baby daga tafiya harkin Fara kewa da wuri haka,,karki manta shekara guda zanyi,,

Narke masa tayi tana kukan shagwaba tace,,Dan Allah Kada kayimana haka kaface 1 month zakayi Ka dawo" ah ah baby garin da nisa bazan iya wannan sintirin ba,,keya kamata kizo mu gaisa.

Bata fuska Yasmeen tayi tana turo Baki,,kaima kasan bazan iya rayuwa a irin wannan gurin ba,,Kai dai dakaga zaka iya saika zauna"

To ai shikenan kinga Kenan bakisan gani,,Allah hubby inaso Kaine Ka zabamana wannan rayuwa ta nisanta juna,,

Hira Sosai sukayi har Saida Nasir ya kasheshi kafin suyi sallama su koma kauyen,,bayan kwana biyu kowa aka kaishi gurin aikinsa inda mashkur ze riqa koya yara karatu a makarantar primary ta gari.

Sosai yayi mamaki da ganin ko ajujuwan babu gaba daya sun lalace birbiri ya Gama lalata sauran,,a haka yake koya musu duk da ba zuwa sukeba,,watarana sedai yaje Shi Daya yagama abinda zeyi ya dawo...

Nasir yayi sa'a kauyen da aka Kashi a kusa yake sedai Shi ana samun lalbai Dan Har headmaster garesu..

Wasa wasa Shakuwa me karfi Na qara Shiga tsakanin nijlah da mashkur,kullum saita kawo masa warar Fulani shiko yanasan taimaka musu Amma Malam ya Hana yace indai ba auren nijlah yakeso ba Baze amsa kudinsaba,,ba yadda mashkur ya Iya haka ya hakura sedai kullum Yana ba nijlah naira Goma Ko biyar tana zuwa dandali.


Yau tin safe Malam ya tashi bashi da Ko naira biyar balle su Sami abinda zasu sa a bakinsu.

Tinda nijlah ta Tashi take kuka ita yinwa takeji gashi Har karfe 12 Na safe Basu Sami abinda zasu sa a bakinsu ba.

Dan Allah Malam kabar yarinyarnan ta Shiga Ko gidansu Indo ne tasa Wani Abu a cikinta kaga yaro besan Babu ba" Ni kaina abinda nake tinanin kenan sedai Bazan bar yarinya tana zuwa kwadayi gidan mutane ba,,tinda su Basu tausaya sun bamu ba..

Malam me zakayi Kar ka cemin Baka fasa Bada sadakan nijlah ba,,Dan Allah kabari kaqarasa Ko shakara Goma sha biyu ne" kinga yakumbo ki rufemin baki,,Ina yanzu nijlah ta cika shekara Goma.
Dan Allah ba shawaranki nake nemaba..

Amma Malam...!Amma me kinfisu yinwa ya kashe yarinya muna kallo,,Idan Ko Na auradda ita Na tabbata bazata Rasa abinda zata Ciba...

To Malam wazata aura kasan Dai iro bashi da kudin aure Kuma Koda ka bashi sadaka Baze Iya ciyar da nijlah ba sabida Shima dakyar take samu yaci..


Bashi zanba auren taba sedai inaso kisani a kwana kusa Zan auran da ita,,kai malam kafa Duba lamarin nan,

Nijlah Najin batin aure ta tashi tana me Jin Dadi tace,,Malam ka gyale maganan kaka kayimin aure Nima Na riqa tuqa tuwo da kaina mijina Na siyomin tsire inaci...

Yauwa Yar albarka,Allah yasa asamu Wanda Ze Iya riqemana Ke ya Kula da maraicinki,,hawaye kaka ta goge da zanin jikinta tace..

To a gaskiya koka auran da nijlah sedai mijin ya biyota gidannan Dan gaskiya banga Wanda Ze Iya juran rigiman nijlah ba" Idan kinga ana haka Sai kiyi,kinga Nina fita karbomana bashi Ko gari musamu Musa a cikinmu..

Adawo lafiya yakumbo tayiwa Malam kafin ta janyo nijlah ta rungume tana rera kuka" Kaji kaka da baqin ciki,,bakiso Nima mijina ya riqa saimin kayan dadi ..



Yawan comments yawan typing,Dan Allah ku rage godiya ki riqa sharshi Ta hakane zan gane sakon danake San isarwa Yana zuwa muku




Comments & Share😍






*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*HUSSAIN 80k*



7⃣&8⃣


Kujimin kaka da baqin ciki,baki Nima mijina ya riqa saimin kayan dadi iron na abu, nijlah ta fada cike da yarinta!.
Cikin kuka yakumbo tace!uhmn nijlah Kenan angayamiki kayan Dadi shine aure,,me Kika Sani game da Zaman takewar aure"
Allah kaka Na Sani,,badai ruwa Ake zubawa a buta na alwala ba,Sai kuma ka zauna Idan anyi tuwo a cikin gida ka dauka Langa a zuba masa tuwo..

Nijlah Kenan babu abinda Kika sani"Allah kaka Na Sani Niki Dena kirana yarinya Kuma Naga Abu tayi zamanta a gidan Musa Ai Dai Nima Zan zauna" Allah ya kyauta cewan kaka tana Jin quna cikin zuciyanta..

Tana nan zaune Har Malam ya dawo dauke da Leda a hannunsa,,
Wai haryanzu kina zaune kina tunani Akan abinda bashida mafita Sai wacce na fada" uhmn uhmn fa Malam wallahi nijlah bazata Iya Zaman aure ba,,ka Duba qanqantar shekarunta?

Yakumbo Kenan tin yaushe muke neman mafita bamu samu ba,,se yanzu Dana samu Zaki kawo matsala,,kiyi tinani Dan Allah.

Shiru yakumbo tayi tana nazari kafin tayi iya Bude baki tace" yanzu Malam Idan muka auran da ita akazo haihuwa ta kamu da jajjan fitsari ya zamuyi,, murmushi Malam yayi Dan ya gano abinda yakumbo Ke tsoro..

Indai wannan ne ki kwantar da Hankalinki,na tabbata nijlah bazata samu wannan matsalan ba,,to Malam kasan Wanda Ze aureta??

Kinga yakumbo Idan bakisan ayi aurennan kawai ki fada ni Kuma Zan zuba Miki Ido Naga yadda Zaki Iya Kula da ci da Shan nijlah,, yakumbo kinfi kowa sanin halin nijlah,,yinwa kawai Idan Taji ta riqa surfafa Miki kuka Ke Akan kudin dandali Sai nijlah ta kusan kwana tana ihu,,Ina Sai yanzu da Allah ya kawo mashkur wannan kauye nijlah ta Dan samu gata,,Idan ba haka bane Sai gayamin..

Matsowa nijlah tayi jikin Malam tana murna tace,,Malam kawai kayimin aure ka kyale kaka tayi ta abunta,,Nima Na riqa Cin tsire da kosai irin Na birni Ko,,dungurinta Malam yayi Yana cewa eh Zan Miki aure Amma sekin Dena yiwa mutane kukan dare"
Dasauri nijlah tace Allah nadena,,kaka aidai Na Dade banayi Ko?

Shiru kaka tayi tana sauraran shirme nijlah kafin tayi qoqarin cewa,,Hakane Malam Nima Na yadda Na Kuma amince da auren nijlah sedai inaso ka zaba Mata mijin daze Iya Kula da ita!

Haba yakumbo muda zamu Bada sadakanta mune zamu zaba Wanda zamu aura Mata" to ai abin ne' kinga kedai kawai kiyiwa yarinya addu'a.

Kinga dauki wannan kanzon ki jiqamana Musa a cikinmu" Ni Allah gari kwaki nakeso ba kanzo ba nijlah ta fada cike da shagwaba,,rarrashinta Malam yayi yayinda yakumbo ta tafara jiqa qanzon,,bako Mai haka ta zuba kuli suka ci.

Suna gamawa Malam ya tafi gidan kakannin nijlah Na wurin uwa,,anan ya samesu da magana nan,Basu Bada matsala ba Dan kowa ya amince,nan ya dawo gida cike da farin ciki Na samun nasara Dan a ganinsa auran da nijlah shine Abu mafi sauqi daze Bata farin cikin dasuka kasa Sama Mata Shi a matsayinta Na marainiya Kuma jika a gurin su..


*******

Zaune take ta hannu biyu Akan kumatu da alama tayi zurfi cikin tinanin,,a hankali ta cire hannu ta dauko wayanta dake Kan center table ta qara Danna Kiran layinsa.
Abu daya Ake gayamata Dan haka tayi cilli da wayan tana Tashi tsaye,,Saida Nace karkayi tafiyan nan Amma ka dage Saida kayi gashinan wayama ya gagaremu sedai kayi kasamu lokaci ka Kira,,Anya kuwa mashkur be samu matsala ba..

Girgiza kai daddy yayi Yana qarasowa kusa da mummy, nan ya zauna kusa da ita Yana kallanta cike da kulawa yace,,

Haba Khadija Se yaushe Zan gayamiki kidena sa damuwa a ranki,girma fa ya kamaki,,Karki sa ciwo yamiki illah Akan abinda bashida Wani illah..

Haba Alhaji Taya kake tinanin hankalina Ze kwanta Akan tafiyan mashkur,kako je kauyen kaga inda yake zaune,, toyaya kikeso ayimasa, mashkur Dai ba yarone qarami ba,da inyaji wahala Baze dawo gida ba,Kuma kina kallo nasama masa admission a UK Amma fur yaran nan yace bayaso ga idda yake muradi Toba seki barshi yaje yayi ba..

Cikin kuka mummy tace haba Alhaji kana nufin haka zamu zuba ido mashkur ya zauna cikin matsiyatan mutane dako Nama Sai su shekara Basu Ciba,,to wallahi Bazan taba yadda ba gwara tin farko kasan yadda zakayi da danka..

Girgiza kai daddy yayi Yana Kallan mummy yace" yanzu Ke Khadija Harkin isa ki aibata Fulani kokin manta Nima bafulatani ne,, dasauri mummy tace Amma Dai ba irinsu ba.

Cikin fishi daddy yace,Koma Dai menene jinin fulani kike aure Dan haka ki kyale yaro ya qarasa karatunsa Koma menene saikiyi Daga Baya,,

Turo baki mummy tayi ta Tashi dasauri ta Koma daki tana Kiran babban danta..

Hello mummyna barka da yamma,,yauwa Ibrahim,,mummy lafiya Naji muryanki haka,, mummy Ko baki da lafiya ne,,kuka mummy tasa tana cewa..

Ibrahim ka Kira wannan yaran ka gayamasa ya dawo gida, mashkur Yana neman doramin hawan jini.

Eyyah Mummy meya Samu mashkur din,, mummy Ko jiya munyi waya dashi yace Yana zaune lafiya a garin dayake" toka gayamasa ya dawo gida banasan zamansa cikin wadannan mutanan indai yanasan zamana dashi lafiya.

Shikenan mummy kiyi hakuri zanyi Magana dashi,,eh ka gayamasa yayi saurin neman transfer yadawo cikin gari,,to mummy kiyi hakuri insha Allahu Ze dawo,,kashe wayan mummy tayi tare da sakin tsaki..

*******

Tinda Malam ya Tashi yasa a ransa Yau Ze Bada auren nijlah gako wanne irin mutum ne indai yanada kamala Kuma Ze Iya riqe nijlah..

Yakumbo ya Samu da maganan yayi sa'a Bata bashi matsala ba ta Kuma amince tare da Tarin adduointa ga auren jikar Tata.



Comments &share





*Momn sultan ce*✍✍✍
πŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA..*πŸ’˜πŸ’˜


*STORY & WRITING BY...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*DEDICATED TO.....*
*MMN AMATULLAH*


*SPECIAL GIFT TO...*
*MMN MUHAMMAD*



9⃣&1⃣0⃣



Tinda Malam ya fita be qara yiwa yakumbo maganar auren nijlah ba,gashi Yau Har anyi wata guda, Dan haka yakumbo ta garzaya zuwa gidan jummai dillaliya Akan tanaso Akai nijlah birni itama tayi aikatau kosa Samu su rage zafi.

Dakyar jummai ta yadda Dan acewarta nijlah 'yar shagwabace su Kuma alhazan birni Basu San shagwababbun yara indai ba nasu bane,,Seda yakumbo ta Hada da ban hakuri tare da cewa zata jama nijlah kunne..

Nijlah Najin batin aiki tayi murna tare da cewa bazata yimusu rigima ba,,nan yakumbo ta Maida hankali gurin tafiyan nijlah birni aikatau..

Yau nijlah da farin ciki ta Tashi sabida ana bikin yayar kawarta,tinda safe ta tafi Suna party, yayinda Ake al'adu irin Na Fulani.

Ke kikace kinaso amarya,,da bakyaso da ba'a Baki shiba,,haka 'yammata suka riqa wucewa suna rera waqa,,gefe guda manyan matane dauke da wata yarinya 'yar qarama bisa doki,,kawunan kowacce su dauke da kwalla da fanteka sai 'yan komatsan Kaya!!!
Ta ko ina suke shigewa,, wasu gada cikinsu suna rangada guda ...


Tsaki mashkur yaja Yana kallan abokan nasa da sukabi tawagar Yan Kai amarya da kallo,,, washe Baki Bello yayi Yana cewa kagani fa,, aure ya tabbata,, Allah yasanya alkairi,,duka sauran Suka amsa,da ameen Banda mashkur Daya hade giran Sama data qasa...

Kai dallah Malam ware,idan zaka zabo yarinya a karkaran nan ka zaba,bamusan wannan miskilancin naka,, daba kaiwa zuci yayi ba..

Allah ya sawaqe,,ni duk garin nan babu yarinya data isa aura agurina,,Dan wallahi Basu Kai Mata ba,,Zan so kuje birni Kuga inda Mata suke,, hhhhh Bello ya fada Yana kallan mashkur..

Kai kujimin Dan rainin hankalin nan to idan ba Mata bane suwaye""' yauwa tambaya mana Shi cewan Nasir dake zuwa gurin...

Kwailayene,, ko nayi karya,, gaba daya suka amsa da cewa kwarai ma kuwa..


Tabe Baki mashkur yayi Yana cewa,,Ku duba yarinyar nan indo, dududu shekaranta nawa Amma har Malam ya'u ya auran da ita?

eh mana kuma Ka zuba ido nan da wata Tara zata iya haihuwa,, ai mu matanmu na karkara da iya zaman aure suke ba irin naku na birni ba..


Dariya mashkur yayi Yana Sosa Dan yafisu Sanin abinda yake Gaya,,sedai su bazasu gane hakan ba,,sabida nasu al'adan suka sani...

Shirune ya
Showing 3001 words to 6000 words out of 65025 words