RUBUTU A KAN RUWA
 

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

FREE PAGE 1


Mafari...!

Zubewa take kokarin yi cikin gigitacciyar kukan dake ratsa duk wani me sauraro, da sauri jama'ar wurin suka yunkura da nufin taro ta gudun mugun faɗuwa amma inaaa basu samu nasara hakan ba, a kan gwiwowinta ta zube tana rero kukan dake fita daga ƙasan zuciyarta, kukan da duk me sauraro ke tabbatar da lallai an yiwa wannan yarinya rashi me girma, babu abunda ya kai rashin mahaifi ɗaci sbd dashi ne ake ado, yau babu majinginarta babu bangon ta ya rushe ba tare da ta tsammatar mishi mutuwa kwana kusa ba, ya tafi ba tare da sun yi cikakkiyar sallama ba, gabaɗaya ta hautsine ta hautsina kowa sbd kowa ya kwana ya tashi ya san da irin fitinanniyar ƙaunar da mahaifinta ke mata haka ita ma girman ƙaunarta gareshi ma'auni baya iya aunawa yau ya tafi ya barta, a gabaɗaya gidan kowa ya dawo bata baki sede wannan kuka ba na bari kwana kusa bane..

Kaman yadda mutuwa take da wani ɗabi'a, ta kan ɗanɗana maka ɗacinta ne ka gigice a lokaci ɗaya amma duk inda aka samu kwanaki dole ka rungumi hakuri ka fawwala Allah lamuransa, ka cigaba da bin wadda ka rasa da addu'a Dukda ze kasance chan Kasar zuciyarka amma dole ka koma rayuwarka kaman koda yaushe, haka ta kasance a rayuwar matshiyar budurwa Ayusher, yau kimanin kwana huɗu kenan da ta rasa baffanta me ƙaunarta, kaman kullum tun bayan rasuwar tana zaune ne cikin kayan saƙi na Fulanin usul farare ƙasan ɗan ficiciyar rigar sakin wani jan riga ne da mahaifinta ya saya mata a chan birni har kala uku take anfani dasu, zaninta ta ɗaura shine daga kan shafaffen cikinta da kaman ba'a sanya masa hatsi, idanunta sanye da farin gilashi me kyau wadda ya ainihin fito da kyaun fuskarta, kyakyawar gaske fara tas da ita daga ka ganta da yanayin sumanta da tayi kitso biyu duka baya ta kuntosu ɗaiɗai ta gefen kafadunta har suka sauka kirjinta zaka san eh lallai wannan yarinya cikakkiyar bafulatana ce.

Motsin Shigowar Nene be sa ta ɗauke idanunta daga inda ta kurawa ba tana ji dai ana ta hada hada da wasu baƙin masu gaisuwa sbd mahaifinta me jama'a ne har yau huɗu da rasuwarshi mutane basu daina tururuwar zuwa ba, amma hakan be sa ta motsa ba bare ta fito ayi gaisuwar da ita.

"Indo!"
Mahaifiyarta ta kirayi sunanta tana dafa kafaɗarta.
"Na san rashin baffanki babban rashi ne da har Abada ba ze daena miki ɗaci ƙasan rai ba sede ki sani, da rai da rayuwa duk na Allah ne bawa iyakarsa yayi hakuri dasu ya kuma rungumesu a duk halin da ya same su, baffanki ba abunda ya so miki ba kenan kin san illar da hawaye kan yiwa idanunki taya zaki cika mishi burinshi na zama kwararriyar likita me taimakon al'umma idan kika rasa idanun gabaɗaya mamana? Ki daure ki tashi kinji aminin baffanki ne yazo daga chan birnin shugaban ƙasa. (Habdu ummu a vurta un hifnindira a nani?) yi kokari ki tashi ki fito ku gaisa kinji?"

Kai ta gyaɗa kan cikin yanayin sanyin da ya aure ta a kwana huɗun wadda sam da ba haka take ba yarinya ce ta kwaramniya da magana, son mutane da yawan tambaya ga tausayi da iya mu'amala duk halinka Ayusher me iya zama da kai ne kuma ta san ta yadda zata bi baku batawa juna rai ba, bata taɓa shiga inda za'a wulakantata takalawa ne su futuk da suke rayuwa a jeji wadda gabaɗaya rugar nasu be haura gidaje ashirin da biyar ba, amma suna da matukar wadatar zuci, mahaifinta na matukar son mata karatun likitanci hakan yasa tun tashinta da kanshi yake kaita makarantar gomnati na kauyen dake gaba dasu in ta tashi ta dawo duk rugar daga ita se ƙaninta ne a makaranta wadda hakan ya janyo tsegumi masu yawa daga mutanen kauyen inda ake mata wani kallo na daban har a yanzu da take matakin aji na huɗu a sakandiri wato SS1.

Kwatsam mutuwa ta ɗauke wannan gata nata taya burinsu ze cika? Taya zata taimaki al'umma idan aka gama watse wa aka barta da Nene wa ze hidimtawa karatunta? Wa ze iya kula da lafiyarta kaman Baffanta? Gashi jiya kanin mahaifinta da ze koma chan kudu ya ɗauke ƙaninta da take dan gani taji sanyi ya tafi dashi, mutuwa fa kenan! In ba mutuwa ba wa ya isa raba kan wannan gida me cike da tarin kaunar juna da sanin ciwon kai? Baffanta da ko yini a wani wuri se ya kama dolenshi suke yi amma daga rasuwarshi da kwana uku har an gangada ɗan shi kwalli ɗaya  namiji zuwa east.

Idanunta da ta soma gani dishi dishi sbd zub da hawaye ya sakata dakatawa ta cire glasses ɗin idanunta wadda atake duhu ya mamaye ganinta dishi dishi take kallo, hawayen ta share tana kokarin maida glasses din a lokaci ɗaya ta yunkura don yin gaba se taji ta Buge mutum wayoyin hannunsa gabaɗaya suka yi ƙasa, a razane ta ja baya tana shakar sassanyar kamshin da tun dazu take mamaki daga ina ne ashe na baƙin gaisuwa ne.

Da sauri ta duƙa ta ɗauko wayoyin tare da Miƙewa tsaye Allah ya sa babu abunda ya samesu, Z fold ɗin kawai ya karɓa bayan ya gama kare mata kallo ya zagaye ta ya wuce don bata gaisheshi ba bare ya tsaya amsawa kuma waya ce ya fito dashi me muhimmanci dole ya karbi Samsung din ya bar mata IPhone ɗin, daidaita kanta tayi tare da sallama ta shiga cikin falon na baffansu shimfide da jar babbar darduma irin na sarauta din nan, wata tsaleliyar macece zaune daga gefe sanye cikin rantsatsiyar lace da ya amsa sunansa ta yafe gyale, baƙa ce sede kyakyawa ce ba laifi se danna waya take tana ɗan murmusawa kaman ba gidan rasuwa ta zo ba.

Ɗauke idanunta tayi ta sauke kan ɗaya matashin me sanye da shadda ruwan ƙasa kansa ba hula se ɗan gashi da ya tara, bata raba ɗayan biyu tsara yake da wadda ta Buge awaje ko ma tace ze iya girmanshi don wanchan murjewar ƙashi da tsawo ne ze nunawa wannan da yake me ɗan kiba, ɗauke kanta tayi ta sake mayarwa kan ɗaya matashin shi kam sanye da kananun kaya bakin wando da farin riga, shi kam tsiriri ne kuma baƙi saɓanin wannan da wanchan da suke farare.

"Jam bandu mon na? On wari jam?"
(Ina kwananmu? Fatan kun zo lafiya?)

Duk ido suka zuba mata kaman sun ga nama ɗanya babu me jin yaren nata cikin su, Naina ta dubi Murad tace
"kaine Fulani se ka amsata ai"

Zaro idanu yayi yace
"Matar yaya ai nima a suna ne se kalar fata amma babu abunda na iya gwara dae Yaya suna yi sossai da Ammah da Abba"

Cikin hausar ta da be wani riƙe harshenta ba ta kara gaishesu suka amsa, amma Murad da aka ambata yafi bata kulawa da tausayawa ya ɗan mata nasiha, duban kakanta ta wurin uba tayi da wani kaninshi se amininshi ta gaishe su suka amsa cikin kulawa, yace cikin harshen fulatanci
"Na san baki rasa jin suna Emran daga bakin mahaifinki ba ko?"
"Eh malam ya kan ce min bashi da amini sama dashi babu sirrin juna da basu sani ba, sannan babu abunda ze iya nema daga wurinshi ya rasa a duniya, idan har na ganshi kaman na ga Baffa nane sbd shine amininsa guda ɗaya jal da ya zama jininshi, amma ban taɓa ganin shi ba in ze zo ya kan zo muna makaranta kuma be taɓa kwana ba kan a tashi mu dawo da yamma ya tafi"

Anan ta dakata tana kallon matasan biyu har ma na wajen da ya dawo yanzu ya zauna ya ɗan kalli wayan shi da ta ajiye chan nesa da ita duk basu yi kama da waenda zata ce sun yi tsara da mahaifinta ba.
"Aisha?"
Ya kira sunan yana kallonta da oily eyes ɗin sa lumsassu.
Da sauri ta amsa tana gaishe shi da harshen fulatanci, da turanci ya amsa yana mata gaisuwa sede sam bata ma fahimci me yake cewa ba sbd irin slang  ɗin shi ko wurin malamansu na sakandiri bata taɓa ji ba, shiru tayi abin ta.
Sun ɗan jima sossai kan ya dubi Baba yace
"Baba ina da wata alfarma da nake son roƙo, wannan yarinya mahaifinta na da buri me girma a kanta kuma idan har kaji Isma'il na maimaita min abu to tabbas so yake nayi wani hubassa a kai ne, duk nazari da tunani da nayi akan rayuwarta ba zan iya taimakonta a cikin wannan ruga ba, idan ba damuwa ina so a bani riƙonta in shaa Allah zaku sameni me riƙe amanarta har Allah yayi cikon burin mahaifinta"

A razane take kallonshi da idanunta dake zub da ruwa zuciyarta na tsitsinkewa tunanin ta na kasuwa kashi biyu zuwa uku, taya zata fara barin mahaifanta ta bi mutumin da a yau ta soma kallonshi a rayuwarta? Taya zata iya rabuwa da mahaifiyarta a wannan gaɓar da take bukatar abokin kuka? Amma kuma burinta da na mahaifinta fa? Idan tana so ta kasance yadda mahaifinta ke so dole se ta bar rugar nan amma....

"Ai Emran baka buƙatar shawara da mu akan ɗiyar Isma'il duk abunda kaga ya dace se ayi"
Da sauri ta kalli kakan nata ta ɓangaren uba dake magana, hawaye ne ya wanke mata fuska tana tunanin yadda zata tsallake ahalinta zuwa inda bata saba ba, mutuwa mai tonon asiri kuka ne ya kwace mata.

Da kallo Naina ta bita tana tunanin abunda su Emran suka tattauna da wannan tsohon bororon har ya saka yarinyar kuka, ta san Emran ba wani faɗa mata zai yi ba hakan yasa ta taɓe baki, tsakani da Allah ma ta gaji da rugar se ƙarnin nono yake mata... Kaman Emran yaji kuwa yace su fara haramar tafiya.

Shi ya fara Miƙewa ya isa gabanta ya ɗauki wayarshi kan cikin dattako irin tashi da sanin darajar na gaba duk talaucinsa ya duƙa gaban baba ya fiddo bundles na dubu daidai har guda uku ya ajiye ya miƙe ya fice baban na ta mishi adu'o'insu na tsoffi da godiya bayan duk tarin kayan abincin da ya zube.

A jikin mota ya ɗan jingina yana amsa waya ɗayar hannunshi kuwa na daddana ɗayar cikin sauri da kwarewa, su Naina da suka gaji da tsayuwa ta kalleshi mijinta mai kyau ne, a kullum kara godiya take da ta sameshi ji take tayiwa mata dayawa zarra domin shi ɗin zaki ne a cikin maza, komai nashi cike da charisma da class yake aiwatarwa yanayin magananshi da tafiyar shi cike da ginshira shi ke kara burgeta dashi a ko yaushe, babu abunda ke bakanta mata rai irin miskilancinshi da har ita be bari ba, gyaran murya tayi tace
"Dear me muke jira ne? Naga Murad da Nameer duk suna mota"

"Aisha"
Ya faɗa bayan tsawon minti ɗaya da maganar ta ba tare da ya kalleta ba.

Yanke tsamannin jin wani kalma daga bakinshi tayi bayan ta tsura mishi idanu na sama da mintuna uku tana jiran jin cikakken bayani tace
"ban gane ba Emran? Aisha muke jira? Me zamu yi mata?"

Tsaki yaja yana Miƙewa daga jinginen da yake kaman ze ce wani abu kuma se ya fasa daidai lokacin da kunnuwansu suka soma jiyo musu kukan Ayusher kaman zata tsaga gidan, lumshe idanun shi yayi ya buɗe kn ya sake jn tsaki, baki sake Naina ke kallon Ayusher da mutanen da suka rakota da kullin kayanta cikin zani ta kalleshi
"Emran ina zamu kai yarinyar?"

"Shes staying with us from now on"

"what????"
Ta yi exclaiming ranta na dugunzuma wani bala'i na kunno mata, ya fa san yadda ta tsani ganin wata kusa dasu taya zata fara rayuwa da wannan bagidajiyar kauyen da ko hausa bata iya ba ita da bata ma jituwa da Ƴan aiki bare wannan kazamar? Daga mutuwan uba se a lika mishi wata yarinya?

"Emran ni ce matar gidan kuma dole idan yarinyar nan ta bimu a gidana zata zauna don haka ni ban amince ba"

Kallon gargadi yayi mata kan ya maida kanshi cikin harshen fulatanci yace ta shiga, se kuka take haka tana ji tana gani aka sanya ta a jibgegiyar motar ya zagaye ya shiga, Naina da bala'i ke cin ta ranta a ƙone cike da kyamar Aisha ta shiga tana wani manne wa da kofa, turaren ta ta fiddo daga handbag ta feffesa a motar ba wadda yace mata ci kanki wadda hakan da tayin kuwa yasa Aisha sake tsinkewa da sabon hawaye, wallahi mutuwa be yi ba...

A hankali take sauke ajiyar zuciya idanunta na bisa bishiyoyi zuwa dabbobi da suke wucewa jefi jefi har suka bar rugar su zuwa karamar hukumar garin har suka dangana da cikin birnin yola zuwa jimeta duk ta san wuraren sbd jigilar asibiti da mahaifinta kasancewar an haife ta da matsalar ido wadda likitoci suka tsayar kan Fatar jikinta ne ke affecting idanun.

A hankali motar su ta shiga Airport, bayan ɗan zirga-zirga se gata a gaban jirgi taka kafa tayi don shiga se ta koma baya da gudu tana zazzare idanu, ta gwada haka ya kai sau uku kan na huɗun ta saki kuka tana kokarin komawa da gudu hakan yasa mutanen da hankalinsu ke kanta kwashewa da dariya ciki har da Murad, Naina kam takaicin ace tare ma da ita suka zo yasa tayi ciki abin ta tunda mijinta ya jima a ciki Nameer ma bayan gama dariyar wannan kauyanci ciki yayi Murad ne ya tsaya yana kwaɓa mata hausa da ɗan abinda yake ji cikin fulatanci.

Se da yayi da gasken gaske ganin kowa ya shiga ana shirin rufe kofa kan ya kamata kamar wata tsohuwa tana takawa da kyar tana hawa suna shiga tayi turus daga bakin kofa ganin yawan fasinjojin cikin jirgin kuma dayawa hanaklinsu na kanta ganin bororuwa da kayan saƙi cikin jirgi wadda hakan ya firgitata ta kwasa da gudu ta koma kasa me za'a yi in ba dariya ba wasu har suna kokarin yi mata video.

Goshi Murad ya dafe ganin yayanshi ya ja tsaki ya miƙe ya fice daga jirgin cikin takunsa na ƙasaita da ginshira, yarinyar nan kar tayi yayansu ya wanke mata fuska da mari sbd saurin fushinshi da zuciya irin tashi don har shi yanzu da girman shi be gami yayan nasu tsinka mishi mari ba in har ya kai shi kololuwa bare ita wannan da ya karɓa amanarta a matsayin ɗiyarshi dole tayi hankali da Ya Emran saukinta ma ba sossai yake zaman Nijeriya ba..

"Ke!" Dakakkiyar muryarsa ta ratsa dodon kunnenta wadda yayi sanadiyar kara mata tsoron ta a firgice ta miƙe tana ja baya a kuma tsananin tsorace ganin ya nufo ta gadan gadan...


*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba
6039380652
Keystone bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰




                       🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA
 

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

FREE PAGE 2

"Wuce muje"
Ya faɗa babu alamar wasa a lamarinshi se taji tsoro da shakkarshi fiye da yadda taji na jirgin, Dukda zazzare idanun da take haka ta yi gaba ya tasa keyarta har seat nata, air hotess yayiwa magana akan ta saka mata seatbelt dinta don ko sun nuna yadda ake yi sun kuma faɗa sun bada leaflet a duba wannan yarinya ba lallai ta iya ba, haka ko aka yi ita ta saka mata kan ya koma mazauninshi ya zauna, sam be kula irin maganganun da Naina ke yi ba ko nuna ya ji ma be yi ba bare ya kulata wadda hakan yake kara bakanta ranta ta kuwa ci alwashin yarinyar bazata zauna dasu ba sede ayi wacce za'a yi.

Har jirgin ya sauƙa idanun Aisha a rufe suke ruf babu kalar adu'ar da bata yi ba, numfashinta ma sede ta riƙe na mintuna ta saki ta shaki kaɗan ta sake rikewa tsabar tsoro da firgici da aka sauka kasa takawa tayi sbd jiri, da taimakon wata air hotess ta sauko se kuma amai, kyawawan dogayen yatsunshi ya saka a Goshi ya ɗan murza sbd sarawar da kan nashi yayi, tsiririn tsaki ya ja wadda idan na kula yana daga cikin ɗabi'arshi amma fa shi kuwa duk duniya abunda ya tsana a
Showing 1 words to 3000 words out of 38960 words