kanshi tsakankanin wuyanta yace cikin Muryar da ita kanta yaso hautsina ta chan ƙasan maƙoshi
"I'm damn tired love a kula dani"

Tana murmushi ta fara biye mishi nan da nan ta ƙarasa rikita shi don fa shi ta ɓangaren nan be san wasa ba kuma babu sauƙi, seda suka natsu suka yi wanka a tare ya rungume ta suka yi bacci.

Washegari da misalin karfe takwas ya fito a shirye tsab cikin tsadaddiyar gezna me sheƙi navy blue an mata aiki da farin zare gefen hagu da kan aljihu se chan ƙasa gefe da gefen tsagun rigar, hannunshi ɗaure da rolex ɗin shi kafafunshi sanye da wasu half covers na FENDI baƙi sidik se sheki yake hakan ya kara bashi wani kyau da class na musamman, kanshi ba hula don shi ba gwanin saka hula bane, as usual kamshin shi na Khamar lattafa shi ya cike ɗakin da duk wani inda ze ratsa.

Be bi ta kan Naina dake bacci bisa gadonshi ba ya fice tunda yaga yau bata tashi da wuri ba to bazata office bane, kai tsaye ɗakinta yayi yana kara duba agogon hannunshi, knocking yayi ya ɗan tsaya har tazo ta buɗe still kayan jiyan nan ne dae a jikinta cikin harshen fulatanci tace
"Jam bandu na Abba?"
Ya amsa da kalma ɗaya tak kan yace
"je kiyi wanka ki sameni parlor."
Kallon jikinta tayi ita ta san tunda tayi sallah tayi wanka tunda ba baccin safe ta iya ba take zaune shiru shiru har lokacin.

"Nayi"
Tayi saurin faɗa ganin ya juya don komawa parlorn, sake kallonta yayi kan yace
"let's go"
Ta san wannan kam Dukda yadda ya faɗa ɗin da kyar ta gane, da sauri tabi bayan shi tana ɗan kama jelar kitsonta ɗaya tana wasa nashi sbd yadda taji gabaɗaya wurin ya mata faɗi tsabar kwarjininshi tafiyar shi ta zubawa idanu cikin natsuwa da zaati kaman zaki, key ɗin da ya zara ba tare ma da ya duba wace mota bace ya danna ta nuna kanta ya nufeta ya buɗe ya shiga, itama da sauri taje ta buɗe gaban ta shiga ta takure se zazzare idanu take sbd firgici,  a natse yake jan motar suna ratsa tamfatsa tamfatsan gine gine na birnin tarayya har suka sadu da guzabe yayi ta kutsawa zuwa wani tamfatsetsen gida da tun daga waje ta jinjinawa kyau da tsaruwar gidan, ita dae tana maƙale jikin Window tana ta kalle kalle yayinda shi kuwa yake ta aikin amsa calls tana ta mamakin yadda baya gajiya se zuba turanci yake cikin kwarewa, inda Allah ya taimakeshi tented glass ne motar da an yi ta kallon Aysher Indo da kauyancinta.

Gidan sama ne lafiyayyu guda uku a dunkule a wuri guda, gidan bashi da yawan shukoki kaman gidan Abba, amma ya tsaru. Parking yayi ya fito itama tayi saurin fitowa tabi bayanshi, lokaci lokaci sukan haɗu da ma'aikatan gidan suna kai mishi gaisuwa yana amsawa cikin kulawa sbd shi fa yana matukar mutunta ɗan Adam ko yaya yake, dayawa da suke mishi kallon me girman kai sam basu fahimce shi bane da irin tsarin rayuwarshi amma da ka fahimce shi zaka san mutum ne me saukin kai da taimako, ga tausayi ainun.

Da sallama iyaka lips ya tura kofar parlorn ya shiga, wata kyakyawar matashiyar yarinya ce ta amsa tana me Miƙewa tsaye
"sannu da zuwa big bro"
"Asma'u ya kike?"
"Lafiya ƙalau big bro"
Murad da shima ya miƙe ya kara so ya miƙa mishi hannu yana cewa
"an tashi lafiya Yaya?"
"Alhamdulillah Ammi fa?"
"tana sama ta haura yin walaha"

Duba time yayi ya gyaɗa kai sbd almost 10 sun bata lokaci a holdup na garin Abuja sannan da nisa tsakaninsu da gidan iyayen nashi be ce komai ba ya nufi saman.

Se a lokacin Murad ya kalli Aysher hannu ya ɗaga mata
"ƴar bororo ashe tare kuke da yaya?"
Murmushin sanayya ta sakar mai tana gaishe shi da fulatanci ya amsa da Hausa, ta gaida Asma'u da taji Abban ya faɗa itama cikin murmushi ta amsa da fulatancin da ta dage take koyo.

"Ya Murad ina kuka samo ta? Ko da ita kuka dawo?"
Asma'un ta faɗa tana sake kallon Aysher da irin kyaunta Dukda har yanzu ba wani girma ne tayi ba don bata da girman jiki, kyau ne dae da gashi masha Allah.
"Ɗiyar Big bro ce ƴar wajen marigayi Ya Isma'il shine Big bro ya ɗauko ta riƙo"
Wani tsalle Asma'un ta daka ta dire
"yeeeyyy yanzu ne zan koyi fulatanci da tushe tunda daga Alhj har Ammi da Hajiya sun ƙi koyamin"

Ita dae Aysher se kallon yadda Asma'un ke murna take, a shekaru zata iya cewa Asma'un nan tayi ishirin amma tana abunta kaman ƴar yarinya, kamu hannun Aysher tayi tace
"ɗiyarmu zo zauna kina ta tsaye nan fa gidan kakanninki ne!"

Da Hausa tayi maganan se Aysher ta ɗan yi murmushi ba tare da ta fahimta ba seda taga tana nuna mata kujera ta zauna
"wani zama zata yi auta? Kin san Big bro sarai karki kaita ta gaida Ammi da Hajiya zauna kiyi ta zuba mata surutu"
Uhmm ta faɗa tana Miƙewa ta rike hannun Aysher suka haura sama, banda kamshi babu abunda gidan ke fitarwa komai kal kal cike da kyau da tsari, ɗakin Ammi suka shiga da sallama.

Tana zaune kan sallaya yana zaune daga gabanta ya tankwashe kafafu ba wani hira suke ba tunda suka gaisa suke zaune haka, Asma'u na shigowa tace
"Ammi kallo ɗiyarmu so masha Allah, Namesake ɗinki ce ma"
Kallon wa ya tambaye ki da Emran ya mata yasa tayi shiru, hannu Ammi ta miƙa mata cikin harshen fulatanci tace
"zo nan ɗiyata, matso"
Zuwa tayi ta kama hannun matar tana yaba kirkin su lallai Abba da matarshi kam nasu kaɗan ne har gwara Abban ma.

Gaishe da Ammi tayi Ammi ta amsa cikin kulawa tana mata gaisuwar mahaifinta ta dinga yi mishi Adu'a Aysher na amsawa.

"I will transfer some token to ur account, anjima ki ɗauke ta ki samar mata gurl stuffs, make sure u get anything in be yi ba just give me a call"
Cikin murna Asma'u ta amsa don ta san zata samu kuɗi, Yayansu be iya aika da kuɗi kaɗan ba sam.

Ammi tace
"Ki kaita su gaisa da Hajiyarku.."

A hankali Emran yace
"Ammi ta fara karyawa pls"
Ya faɗi hakan ne sanin a kauye zuwa yanzu sede abincin rana, shi karan kanshi aure ne ya sabar mishi karyawa a makare da yake gida ko seven baya kaiwa be karya ba.

Kallonshi Ammi tayi ya fuske yana danna wayarshi bata ce komai ba har Asma'u ta fice da Aysher
"yanzu a haka zaka iya riƙe marainiya?"
Ta faɗa tana kallonshi, kanshi ƙasa ya amsa
"Ammi in shaa Allah zan yi kokarin ganin ta koyi girki sbd ta dinga dafawa kanta"

"kai kuma fa? Haka zaka ke zama da yunwa sbd wani tsari naku na banza?"
Shiru yayi ya ma yi mamakin yadda ta iya maganar don ya santa in abunda ya shafe shi ne sede Hajiya ita bata saka kanta sam, yawanci in ze zo sede su gaisa su yi ta zama shiru in ya gaji ya miƙe ya fice.

"Ammi bara na isa wurin Hajiya"
Girgiza kai tayi tace
"a gaishe ta"
Miƙewa yayi ya fice ta bishi da kallo.

A kan carpet ya samu Aysher tana cin jollof Rice da aka yi shi da nama zuku zuku, yayi washar se kamshi yake, Asma'u na zaune tana danna waya yayinda Murad ke kallon Tv
"Murad"
Ta Kira sunan yana dan tsayawa hannunshi ɗaya cikin aljihu
"I will send some token to ur account u should find a very good school within Abuja on monday ka kai yarinyar nan, pls make sure the school is standard nd good"

"Ok sir, in shaa Allah"
Juyawa yayi da nufin tafiya part din Hajiya da sauri Aysher ta saki cokalin ta miƙe don binshi, Asma'u tayi hanzarin katse ta
"zauna Aysher ki ci abincinki ba yanzu zaki tafi ba"
Zama tayi, tsoro take kar ta mishi laifi ta lura magana na mishi wahala, shiyasa yake ta sha ma kowa kamshi yake magana ɗaiɗai kaman me kirge...

Bayan ta gama Asma'u ta sake janta sama zuwa ɗakinta da ya sha kyale kyale komai pink su wallsticker ne su waye ne babu abunda babu, tura ta bayi tayi ta sake wanka ta bata towel bayan ta fito, ta ajiye mata manta ta shafa ta bata turare ta nunnuna mata inda zata fesa bayan ta gama ta ajiye mata wani dogon rigar atmfaarta da yayi mata kaɗan amma tana matukar son atamphar shiyasa take ta ajiyar shi, sakawa tayi masha Allah, da yake beda breast curve irin flay din nan ne se ya mata kyau be Mata wani yawa ba, dankwalin Asma'u ta ɗaura mata ta bata gyale bata iya yafawa ba sun saba yawo haka se gyalen ke ta faɗuwa tana rikowa amma masha Allah tayi kyau abunta.

Gyalen Egyptian Abaya me walwalin dake jikinta Asma'u ta warware ta yafa a kanta ta zari car key ɗin ta, wayanta IPhone 15 pro max dake chargy ta zare tana dagawa fuskanshi ya kunnu zaro idanu tayi tana kallon yawan kudin da Big bro ya saka mata, kai ta gyaɗa tace.
"Ah lallai Big bro an yi ɗiya"

Fitowa suka yi zuwa ɗakin Ammi bata nan, kila ta sauka se suka sauka kawai zuwa kasa, anan suka sameta tana kallon sunnah Tv sallama suka mata tana maimaitawa Asma'u su shiga wurin Hajiya fa kan su bar gidan.

Ɗaya building ɗin suka nufa Aysher bata da magana yayinda Asma'u ke da surutu sede bata iya fulatanci ba hakan ne yasa dole suke tafiyar shiru shiru, Da Sallama suka shiga parlorn wadda shima a tsare yake gwanin kyau da burgewa, wata kyakyawar farar mace ce zaune bisa carpet ta miƙe kafafunta tana ta aikin mita da alama da Abba take sbd ganinshi da Aysher tayi a kwance kan three seater dake facing matar tsawon shi yayima kujerar yawa don haka kafafunshi ya miƙe su a chan saman kujeran ya zubawa matar idanu se kallonta yake, sallamar su ce ya katse ta wadda hakan ya saka shi shima lumshe idanu.

A ƙasa Aysher ta zube tana kwasar gaisuwa matar ma na da fara'a da son mutane a take ta sake da ita ta fara mata gaisuwar mahaifinta, daga nan Asma'u ta miƙe
"Hajiya bari muje sayayya"
"Toh Allah y tsare se kun dawo"
Kan su amsa wayar Emran ta ɗauki tsuwwa, jin wayar wurin aiki ne ysa ya buɗe idanu ya ɗaga ya kara a kunne, mintuna biyu kan ya sauko da kafafunshi yana furta
"subhallah! On my way pls do the needful, arrange everything in order..."
Yana sauke wayan ya dubi Hajiya
"Hajiya ina da emergency bari naje"
Hajiya tace
"hala lamarin babba ne bokan turai?"
"Accident ne wai rodi ya shiga har cikin left abdominal artery na matar she needs urgent surgery i hope she lives..."
Yana kai nan yayi saurin ficewa tana mishi Adu'a.

Fitowa suka yi, a hankali Aysher ta tambayi Asma'u
"Aunty Asma'u aikin me Abba ke yi?"

Tunani Asma'u ta tafi kan tace
"wai Alhajinmu?"
Girgiza kai Aysher tayi
"A'a Abbana!"
Dariya Asma'u ta saka sossai....

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰



                         🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA


بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

FREE PAGE 4

"Wai Big bro?"
Kai Aysher ta dage daidai suna shiga hadaddiyar SUV lighter brown wadda ya kasance motar Asma'un ce, bayan sun zauna tana yiwa motar key tace
"Ai Big bro babban surgeon ne da ba Nigeria kaɗai ba har ƙasar waje suna matukar ji dashi, duk wani harka da ya shafi tsaga mutum musamman a ciki to ya kware anan, na san Dukda ruga kike kila ba zaki rasa jin CITY CLINIC ba nan ne asibitin shi baya zuwa ko ina banda kasashen waje in kana bukatar aikinshi kayi booking appointment ka zo asibitin shi ya maka aiki, kai ko a Abuja babu asibitin da yake musu aiki, kuma kin san me?"

Ta tambaya tana kallon Aysher da wasu bayanan ta fahimta wasu ko bata fahimta, girgiza kai tayi
"Big bro na da zafi matuka a harkar aiki baya son sakaci da aiki baya yarda ka mishi wasa da aikin hakan ysa duk wadda yake aiki karkashin shi yake taka tsan-tsan da kuskure, sannan sam ba'a tsawwalawa a asibitin yana iya kokari wurin ganin da Talaka da mai kuɗi sun zo asibitin kuma sun ji daaɗi sbd da matukar wuya yayi aiki ba'a samu nasara ba, shiyasa kullum zaki ga yana asibiti ko ya tafi wata ƙasa Dukda tafiye tafiyenshi da sauƙi tunda se ayi booking daga Kasar waje a zo Nigeria yayi aiki a koma"

Ajiyar zuciya Aysher ta sauke a ranta tana ji dama ita ce, wannan shine burinta da na mahaifinta sede tunda ta shigo Abuja ta fara tambayar kanta zata iya kuwa? Har suka isa shopping mall suka yi parking suka fito tunani take yayinda Asma'u ke ta mata surutu wani ta amsa wani tayi murmushi har labarin gidan seda ta bata...

"Kinga Alhajinmu asalinshi haifaffen rugar ku ne, mahaifinshi me kuɗin gaske ne a cikin Fulani sbd ya mallaki dabbobi masu yawan gaske kama daga shanaye, tumaki, akuyoyi, zabi, kaji da dai sauransu, yana da mata har uku da mahaifiyar Alhajinmu itace uwargida amma Alhj shi kaɗai ne ya fita da namiji duk sauran ƴaƴansu mata ne, na biyun tana da yaya mata har biyar, na ukun ƴaƴa matan ta guda biyu se hajiyarsu Alhajinmu dake da guda Alhajinmu da kuma kanwarshi wacce ta rasu da jimawa bayan tayi aure ta haihu shima yana wurin Ammin mu ne da zama tun daga yayenshi har yau.

Kakanmu Dukda be yi boko ba sede yayi sha'awar ɗan shi kwalli ɗaya tal yayi hakan yasa tun da Alhajinmu yayi wayau ya kai shi cikin birnin yola inda anan yayi karatu tun daga farko har ya kamallah jami'a ya karanci business, bayan bautar Kasar shi a wani company a Kano se suka riƙe shi a matsayin sun bashi aiki sede yaje ruga ya dawo, bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana aikin suka maida shi Abuja a wannan komawanshi da New appointment na promotion babanshi yayi mishi aure inda ya aura mishi Hajiyarmu ya dawo da ita Abuja.

Sun ɗauki tsawon lokaci da Hajiya bata haihu ba wadda hakan ya kawo mata tsana a familyn mijin ta yadda bata isa taje ruga ta dawo cikin natsuwa ba, barin ma hajiyar Alhaji bata iya ɓoye ƙin ta Sam a ranta, daga karshe ta ba Alhaji umarnin kara aure, mahaifinshi be ja ba sbd a lokacin ma ba wani lafiya ta ishe shi ba, shi kam ya san iya biyayya Hajiya wacce ainihin sunanta Zaliha tana yi mishi, zaman su bata taɓa saɓa mishi ba wannan rashin haihuwa kuwa ya san daga Allah ne in lokaci yayi zata haihu saide hajiyar shi ta kasa fahimta, dole a wani zuwa da yayi suka tafi wurin dukiyar Alhaji dake chan wani ruga daban ya Ga Ammin mu ya yaba.

Kama kama aka ɗaura auren su da Ammi, Hajiya tayi namijin kokari a zaman su sbd kowa ya sani muddin Kaga gida zaman lafiya ya mishi karanci mafarin uwargida ce kaman yadda idan Kaga yayi kyau to duk uwargida ce, ta riƙe girmanta ta kyautatawa Ammi fiye da tunaninki, ta janyo ta a jiki Dukda irin gargadin da dangin Alhajinmu suka dinga yiwa Ammi, itama dake ba me son fitina bace ta rungume kishiyar ta suke wanzar da zaman lafiya me girma a tsakaninsu.

Ammi bata shekara ba ta haifi Big bro, a sunan Big bro babu irin cin kashin da ba'a yiwa Hajiya ba wadda har Ammi seda ta taya ta kokawa don haka se ta sakarwa hajiyar ragamar Big bro ta ɗauke idanunta kwata kwata a kanshi kullum in zasu je ruga to mitar hajiyarsu Alhaji shine yadda Aka bar Emran hannun kishiyar uwa, lokacin yayenshi tasa dole aka kai mata shi, mafarin amintarsu da mahaifinki kenan, sun taso tare a ruga don kama kama seda Emran ya shafe sama da shekaru huɗu a ruga yana rayuwa dasu sbd kawai a nesanta shi da Hajiya, a cikin wannan shekarun ne Allah yayiwa Alhajinsu Alhajinmu rasuwa, an raba gado an ba kowa nashi sbd yawan na Alhaji se ya fara wani tunani akai.

Wasu ya sayar a lokacin shanu na da daraja sossai ya dawo Abuja ya samu fili ya fara gina campany na kanshi, wasa wasa se ga Alhaji ya tashi da ma'aikata babba ta yadda aka koma aka kwaso mishi dabobbinshi yayi paultry farm daga karshen companyn ya dibi ma'aikata da kwararrun turawa aka fara sarrafa madarar shanu, zuwa youghut, su madarar gari, su fresh milk da dai sauransu, hatta kyankyashar kaji da waye waye duk ana yi, bunkasar companyn yasa ya sake buɗe wata inda ake sarrafa fatun dabbobin zuwa abubuwa dayawa takalma, jakunkuna, da dai sauransu.

A zaman Big bro a ruga kar kice da son iyayenshi kawai ba yadda suka iya ne don Ammi har ta sake haihuwar Ya Salma har ma an sakata play class Big bro be fara makaranta ba, da kyar da suɗin Goshi Alhaji ya lallaba mahaifiyarshi suka dawo Abuja ya sama musu gida na musamman ita da Asma'u kanwarshi da naci sunanta bayan rasuwar ta, sauran matan kam
Showing 6001 words to 9000 words out of 38960 words