mishi kenan...

"Murad pls take care of her i've an emergency patient to attend now"
Ya faɗa yana ɗan tafiya, kan ma ya ɓace First aid na airport din suka zagaye ta sanin da wadda take tafe, aka ɗan bata taimako kan Murad ya riƙe ta sbd jirin da take ji har suka isa mota, Naina ta cika pim kamar fulawar da aka sakawa yeast duk yadda ta so ya ɗauke ta a motar shi kamar yadda suka zo ya kiya yace asibiti ze yi ta jira Aisha Murad ya sauke su, ganin yadda suka fito ɗaiɗaikun mutane na kara nuna Aishar kamar ya zama musu wani sabon abu ne ganin bafulatana da kayan saƙi a cikin jirgi yasa tayi saurin kwala kiran ƙaninta

"Nameer!"
Tsayawa yayi ta ƙarasa har inda yake
"i would rather follow a taxi than to rode a vehicle again with this gurl"
"amma sis bakya kaunar taxi naga, sannan ai yarinyar nan bata isa ta hana ki shiga motar gidan inlaws ɗinki ba"
Nameer ya faɗa
Tana kwaɓa fuska tace
"gwara min taxi din sau dubu baka ganin yadda duk tayi ta amai ewww, na rasa me ya hau kan dear da ya jajiɓo mana wannan kazantar in taimakonta ze yi yayi mana a chan kawai, mtseww"
Nameer ya saka dariya yana tare musu taxi ya riga ya san sis ɗin tashi da mita sam abu baya wucewa a wurinta barin ma in bata so abun ba, taxi suka shiga tana cigaba da korafinta.

Naina Adam shine sunanta ita ɗin cikakkiyar ƴar kasuwa ce da ta samu shedar kamallah digiri har biyu a harkar kasuwanci, hakan ya bata damar jan ragamar kanfanunnukan mahaifinta da ya kasance hamshakin attajiri a Arewacin Nijeriya, ƙaninta be zaɓi kasuwanci ba kuma su biyu ne kadai Allah ya bashi hakan yasa ta jajirce take kuma kai akan duk wani al'amari na companies ɗin su na *Adams industries* ita ɗin tana da son a san ita wata ce, kaman yadda Allah yayi ta me kyau tana son komai nata ya kasance me kyau kuma na daban ne hakan yasa a koyaushe in ta tuna Emran mai yaƙi take aure se taji kanta yayi sama, kaman duk duniya ba na biyunta.

Naina bata da son mutane ko jansu a jiki a ganinta kowa yayi rayuwarshi yafi, ta tsani talaka bare wani suna wai talauci, ita kanta kawai ta sani se family ɗin ta, sam bata son ganin wani ya raɓe su har familyn mijinta kuwa.

har Nameer ya ajiyeta kofan gida bata daena kananun mita ba ita babban haushin ta yadda yarinyar zata zauna dasu dindindin, ko da ta shiga gidan direct bangarenta tayi ta wuce bayi ta soma da cire kayan nan a cewar ta ya kwashi ƙarnin nono ta zube su cikin laundry bag dake bayin ta isa chan inda aka keɓe don wanka seda ta fara sakin shower ya jiƙe daga kanta har kafafunta a cewarta ɗauraye datti kan ta isa ga jaccuzi ta haɗa ruwa ta shiga tana relaxing, ta jima sossai kan tayi wanka a bayin tayi ta kwalkwale kwalkwalenta su skin care routine da dae sauransu kan ta fito ta sa karamar shirt da wando ta haye gado don baccin huce gajiya..

Tunda suka doshi cikin Layin take ta aikin kallon irin ɓarin kuɗaɗe da aka yi a gidajen da suke zagaye da Layin, babu gidan da zaka kirashi tsoho don kowanne fentinshi na kyalli da ɗaukar idanu, fari tas ɗin gidan da fence ɗin shi be cika tsai ba zagaye da electric wire sbd tsaro gabanshi ɗauke da wasu irin flower masu ɗauke hankali da kawatuwa, gate ɗin shi Black da yaji ado da gold taga Murad yayi horn kaman mintuna biyu taga gate din ya zuge da kanshi a hankali ya siɗaɗa motar ciki, baki sake galala take kallon gidan.

Idan suka shiga birnin yola da Baffanta ta kan ce mishi waenda suke gidajen birni sun ji daaɗi kuma suna aljannar duniya bata san akwai inda ya take waenchan da take santi ba, gidan ba dublex bane flat ne da yake kaman an rakubeshi a dunkule a gefen fankacecen tsakar gidan da yaji ado da flowers daban daban, motoci basu wuci shidda bane a parking lot ɗin sede kowanne ka kalla ka san mota ce da ta amsa sunanta, dubanta Murad yayi ganin yadda take ta kallon cikin gidan da take ta hangen glass yafi ginin dake jiki ta waje yawa, irin glass me garai garai da kana iya hangar wadda ke waje ko yake ciki..

"Aisha zan tafi"
"Ina zaki tafi?"
Ta faɗa cikin gurɓatacciyar hausar ta, yana mata alama yadda zata gane da kyau..
"Babanmu ni da Ya Emran yana jirana akwai takaddu da zan kai mishi"
"useni ta accam ha ɗo wala mo mi andi, yiwu saare mai bana ha (Ayya karka barni a nan babu wadda na sani, kalli fa gidan kaman a mafarki)"
Ta faɗa idanunta na yin rau rau sam be gane ba shi kam, sede ya fahimci a tsorace take.
"Matar Yaya na ciki, muje in raka ki parlor zaku zauna tare"
Yana maganar ne yana alama da hannu sbd ta fahimta, kai ta gyaɗa Dukda ta kula matar ƴar wulakanci ce, ko da shi ke ba ita kadai ba har mijinta ma ɗan wulakanci ne wannan Murad din ne kawai me kirki, da in ya san baze iya kula da ita ba Meyasa be barta a rugar su ba, tana tunanin ne tana turo ɗan karamin bakin ta Red dashi sharrr.
Seda Murad ya buɗe mata kofa ta shiga rungume da kullin kayanta kan ya juya ya koma da sauri sauri sbd Alhajinsu dake ta kiran shi.

Tsayuwa tayi tana kallon farare sol ɗin sofas ɗin daga gani ba karamin taushi zasu yi ba, komai na parlorn daga fari se lighter Brown wadda ma kaɗan kaɗan ne mixture ɗin, dan kadan gefen gini da aka yi ado dashi se na carpert kaɗan, se na wasu vanity trays parlorn ba wani hayaniya, sallama tayi tayi shiru tun tana tsaye har ta gaji a hankali ta ɗosana ɗuwawunta kan kujerar ai da gudu ta miƙe jin suna shirin burmawa da ita tsabar laushinsu, gefe ta koma ta zauna daga ƙasan farin tiles ɗin tare da zabga tagumi.

Wasa wasa tun tana saƙe-saƙenta har ta koma shiru a hankali ta juye zuwa abun tausayi sbd yunwar da ya fara sasakar cikinta tun safe banda madarar shanu tafasasshe da tasha bata ci komai ba gashi tayi amai, bata ji motsin kowa ba bare ta nemi agaji gashi har duhu ya fara rufuwa bata yi ko sallahr la'asar ba, hawaye ta fara akai akai tana sharewa sbd yadda suke zuba cike da tausayin kanta, me yafi mutuwa ciwo da firgici? Da yanzu suna chan da Baffanta da Nene da kuma zayyad(ƙaninta) suna hirarrakinsu da tsokanar juna cikin raha.

A hankali ta kai kwance akan tiles ɗin da sanyin shi ke ratsa har cikin ƙashinta, jikinta na ɗaukar rawa, tafi awanni biyu cikin wannan hali kan a hankali ta soma jin sassanyar kamshi me ratsa zuciya da sanya natsuwa, kamshin da ta riga ta san me shi a yinin yau kawai sbd yadda yake da masifaffen daaɗi yana shiga hancin ta wadda yayi sanadiyar ƙara murɗawar cikinta da babu komai ciki, sam be kula da mutum a wurin ba sbd rashin hasken parlorn Ƴan kwayayen lantarkin masu kyau dake kunne wutar su ba farare bane wasu kaman Orange kaman Red haka dae wutar ya bada wani colour me duhu duhu haske haske.

Tuntuɓe yaji yayi da kullin kaya chakk ya dakata a saninshi dae a nan kan hanyar babu abunda ze iya cin karo dashi, maida idanunshi yayi kan wurin se yaga kaman mutum a kwance a takure, da sauri ya miƙa hannunshi ya kunna fararen hasken wadda a take ya haske parlorn tarrr kaman rana oily eyes ɗin shi zube a kanta...
"Aysher" ya furta sunan yana duƙawa ganganta
"Ya Salaam"
Ya kara faɗa da deep husky voice nashi
"Me kike yi a nan? Don't tell me tunda kika shigo anan kike zaune?"

Hawaye kawai ta sake farawa bata iya ta amsa shi ba, haka kuma bata iya kallonshi ba hannunshi taji a goshinta da sauri ya janye yana sake ambaton Allah, Ranshi gabaɗaya yayi baki kirin, amma Naina bata da hankali yanzu amanar da ya ɗauko kenan take wulakantawa tun daga yanzu a yau ɗin nan?.

"Ni kam zan koma Nene ABBA"
Ta faɗa cikin karyayyiyar muryarta wadda ya saka shi lumshe idanunshi ya buɗe, tana reffering din shi da Abba ne sbd haka Baffansu ke kiranshi a gabansu, ko da Nene ze yi hirarshi ya kan ce Abban yaran nan kaza ko kin san me Abban yara yace? Haka dae so Zayyad da su kan haɗu haka yake kiranshi shiyasa itama ta kira da hakan.

Kallonta kawai yayi be bata amsa ba se ta kara sautin kukanta, dafe goshinshi yayi da tafin hannunshi ya ɗan murza kan ya miƙe tsaye yasa hannu ya dauki kullin kayanta, ɗayan hannunshi kuma ya sanya ya kama nata ya miƙar da ita sbd magana da baze iya yi ba, kaman rakumi da akala haka take binshi suka kutsa cikin gidan zuwa wani parlor se wasu kofofi da dining da aka rufe wurin da labulaye masu haske, komai royals ne anan kam golden da milk da suka haske parlorn, wani kofa daga farko ya buɗe suka shiga ciki, Brown set na Italian bed ne hade da wardrobe din shi da rabi madubi, dressing mirror da shoe rag, a tsakiyar ɗakin ya saki hannunta ya nufi wardrobe ya jefa kayanta ya dawo ya tsaya gabanta duk ya cika mata ido da faɗin kafaɗunshi, tsawon shi da idanun shi masu kaifi dake kanta, so yake yace taje tayi wanka kan ya nemo mata abinci da magani amma maganar na mishi matukar wahala.

Tsaki yaja ya juya ya nufi toilet seda ya buɗe kofa kan ya kalleta ya yafito ta da hannu, a hankali ta fara takowa har ta iso ya wuce ciki ta bishi, da kallo ta bi bayin lallai kam wannan wai makewayi? Ta ayyana a ranta Dukda zafin zazzabin da take ji baki galala take karewa bayin kallo
"Hey!".
Ya faɗa bayan ya ɗauko bucket don ya san ba iya shiga jaccuzi zata yi ba, ba kuma iya anfani da shower zata yi ba,
"This..." Ya nuna blue
"ruwan sanyi ne, but if you turn to this.." Ya mayar Red
"ruwan zafi ne, ki haɗa kiyi taking shower i will be right back"

Daga haka ya fice, ta ƙarasa bakin tap ɗin ta mayar ruwan sanyi tare da sa hannunta se taji sanyi ƙalau, ta mayar jan se taga ruwan zafi na zuba har da turirin hayaƙi dariya ta saki ta ma mance tana jin zazzabi ta fara kalle kalle a fili ta furta
"ko daga ina ake dafa ruwan a sako shi a tiyon nan kuma?"
Bata da me bata amsa haka ta surka tayi wanka ta mayar da kayan da ta cire abunta ta fito a ƙasa ta zauna tana nazarin yadda zata yi sallah se gashi ya buɗe kofa ya shigo da sallama iyakarsa kan lips ɗin shi..

"Abba ina so nayi sallah ban san inda ake kallo ba"
Ta faɗa cikin harshen fulatanci, ɗan kallon kayan sakin da ta sake mayarwa jikinta yayi ya ɗauke kai, ba tare da yayi magana ba ya je wardrobe ya buɗe ya fiddo sallaya ya shimfida daga ɗan gefen ɗakin yana fuskantar gabas ya dawo inda ya ajiye ledojin da ya shigo dashi,

"karki sake zama a ƙasan tiles ɗin nan, wannan ɗakin ki ne as from today, sannan bana so na sake ji kin yi maganar komawa ruga, ni ba karamin mutum bane ba zan ɗauki alkawarin da na san ba zan cika ba, pray, eat and take this medicine ki hau gado ki kwanta..."
Yana kai nan ya juya ze fita da sauri ta miƙe tana karewa ɗakin kallon da yanayin shirun da gidan ya ɗauka, ta fahimce shi sarai sbd da fulatanci yayi maganan hade da turanci kadan kadan so ta gane yana nufin nan ɗin ɗakinta ne kuma ita kadai zata zauna ciki irin wannan shirun da gidan da unguwan ke dashi?

"ABBA"
Chak ya tsaya ya juyo yana kallonta, se ta fara kokarin kuka cikin Muryar kuka tace
"Tso..tsoro nake ji...ni ba zan iya zama ni...ni kaɗai ba..."
Se hawaye sharr, hannunshi ya sa ya murza goshinshi tare da sakin tsiririn tsaki kawai ya juya ya fice.

Sallah tayi tana kuka, ita kam bata kwana ita kadai ba kab rayuwarta ta saba ko yaya kana jin surutun mutane ko makota amma ji nan kaman makabarta? Kuma ta kwana ita kadai? Karar da wannan abu da aka makala a sama kaɗai ya isheta tsoro ga ɗakin kaman lokacin hunturu don sanyi, to ko dai yanayin Rugarsu da nan ɗin daban daban ne? Don ta dae san a kauyensu damina ne.

Haka tayi Sallar a tsorace ta dawo ta zauna ta buɗe abincin, kura mishi idanu tayi ganin abubuwa daban daban gauraye da shinkafa gashi yayi kalar ɗorawa, se dankwaleliyar kaza a saman shi, kazar ta cire ta sa a murfi ta fara aikin tsince su carrot ɗin tana ayyana ko basu sani bane suka saka ko sun cuce Abban ba tare da ya buɗe ba suka saka mishi abubuwa har da ganye, ko karas bata gane ba sbd bata ci ba kuma bata saba ganin an yanka shi haka ba, bare su peas, green beans, baked beans, cucumber.
Hanta kawai ta bari da shinkafar wadda hakan ya ɗauke ta sama da mintuna ashirin kan ta soma cin ɗan shinkafar da ta rage ta haɗa da kaza, Admiral A ya siya mata hakan yasa ta shanye tas sbd gardin nono da kuma kamshin shi da take ji, maganin da ya ajiye ta dauka ta sha se taji ta rasss se a lokacin ta tuna tsoronta ta soma zazzare idanu, gadon ta hau tunda yace kar ya kara ganinta a ƙasa ta dunkule tana mamakin wannan sanyi, neman zazzabin da ya rufeta dazu tayi ta rasa a take bacci yayi awon gaba da ita tana ta santin laushin gadon da pillown ga kamshi..

Bayan ya gama duk abunda ya san al'adarshi ce har ya kwanta se kuma ya miƙe ya yaye White duvet me taushi da ya shige ya sauka, a hankali cikin salon takunshi ya isa wani karamin drawer ya janyo ya fiddo wata karamar woofer me kaman Apple yana fidda blue light a ɗakin ya kunna akwai memory me full qur'an ciki ya kai baqara cikin kira'ar shuraim ya rage sauti ya fito, seda yayi knocking tukuna ya tura ya shiga tana chan dukunkune yaje ya ajiye bedside har ya juya kuma ya sake dawowa, ita kam kaman ƴa take a wurinshi ze kula da ita kaman yadda mahaifinta ze kula da ita har ranar da Allah ze fiddo mata miji tayi aure kaman yadda yayi alkawari don haka ze yi kokarin ganin ya rage miskilancinshi ya bata kulawa kamar yadda ze yiwa ƴaƴanshi idan ya haifa, duvet ya janyo ya rufe ta kan ya juya ya fita ya ja mata kofa.

Idanunshi ya ɗan sakar mata na mintuna biyu daga inda take tsaye riƙe da kugu ya zagaye ta ya nufi ɗakinshi.
"Emran me kake yi a ɗakin yarinyar nan? Meyasa ma ka ajiye ta anan din alhali akwai Boys quater?" Chak ya tsaya...


*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba
6039380652
Keystone bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰



🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA
 

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

FREE PAGE 3

"Naina!"
Ya faɗa cikin Muryar gargaɗi ta san shi in akwai abunda yayi mugun tsana a ɗabi'arta shine mummunar fassara da kuma mitar ta, ita kishi kishi dae na banza da wofi, cigaba da tafiyar shi yayi kawai se yaji ta rushe da kuka, abunda yake saurin tsinka shi kenan baya so sam, Juyowa yayi ya dawo da baya ya sanya hannu kawai ya ɗauke ta suka nufi ɗakinshi a tare ba tare da ya ce da ita uffan ba.
Kan gadon shi ya shimfiɗe ta kan ya bita ya matse a tsakanin hannunshi cikin kunnenta ya fara raɗa mata...

"Kin dae san duk abunda ze sa ni hayaniya da ɗaga murya ba son shi nake ba, why a kullum burin ki kiga mun yi faɗa hun?"
Narkewa ta sake yi a cikin jikinshi ita ta san kayanta da yadda ya iya ririta mace in yana yi dake, shiyasa take mugun kishin ganin wata mace ta raɓe shi kar ya sakar mata romon soyayyarshi garɗinta yasa ta raba su
"Amma dear ai ni aka ɓatawa dole nayi magana aure fa muke da ni da kai, be kamata in zaka kawo wata ta zauna karkashin kulwarmu ka kasa shawartata ba, gashi yanzu da daren nan Kaje har ɗakinta alhali dae ka san ba muharramarka bace"

"dake da gidan duk mallaki nane a tunanina ina da iko da ku duka, taimako nake shirin yi da aikin lada idan har ba zaki taimakeni akai ba please do not involve ur self, case closed."
Kara shige wa jikinta yayi yana saka
Showing 3001 words to 6000 words out of 38960 words