kallonta ba sede ta ƙasan idanu, dariya ma ta bashi amma da yake shi ba gwanin dariya bane se ya ɗan murmusa ƙasa ta duƙa
"Abba ina yini?"
"Lafiya, ya jiki?"
Ya amsa bayan ya ja lokaci
"Alhamdulillah"
Ta faɗa tana tsugunen
Da hannunshi ya nuna ledar dake zaune a gefen table ɗin nashi yace
"zo ɗauki wannan ki ci"
Miƙewa tayi ta zo ta ɗauka.
"Seat there"
Ya faɗa yana nuna army green ɗin cushions dake daga gaban desk ɗin nashi Dukda akwai tazara kaɗan, wurin taje ta zauna ta fiddo abincin lafiyayyiyar biryani ne da kaza a samanshi, a natse ta soma ci sbd yunwa da dama yake cin cikinta.
Seda ta gama ta maida takeaway ɗin leda taje ta sa a bin da ta gani daga chan kusa da kofa, dawowa tayi ta zauna tana wasa da yatsun hannunta yau tayi missing school ta ayyana a ranta.
Ta jima nan zaune kan taji motsin tashin shi gaban table dake daga tsakiyar kujerun da take kai ya isa ya ɗauki remote ya kunna Tv, kan ya juya zuwa change room ya sake sauya kaya zuwa na theater fitowa yayi yace
"Ki jirani anan, ina da aiki"
"Allah ya bada sa'a"
Ta faɗa tana kallonshi har ya fice, Miƙewa tayi ta fara yawo a office ɗin tana kallo gsky ya mata kyau ainun, jikin Windows taje ta ɗan yaye se ta wara idanunta chabbb ashe a sama sossai take ganin wasu buildings din sun kai na asibitin wasu kuma basu kai ba, ga tituna a shimfide motoci se kai kawo suke, ta jima anan tana jin wayoyin shi dake zube kan desk ɗin shi na ringing sede bata yi gigin zuwa wurin ba ma.
Tana jin kiraye kirayen sallah azahar ta dawo kujeran ta zauna tana kallon Tv, har ta gaji ta kwanta bata yi aune ba bacci ya kwashe ta anan.
*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*
Zaki iya biya ta wannan akawun lamba
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰
🖤Gureenjoh🖤
RUBUTU A KAN RUWA
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*
FREE PAGE 11
Se after 3 ya shigo, a hanzarce ya nufi toilet turus ya ɗan tsaya yana kallon yadda ta shanya kayan baccinta da ta wanke a bayin, ɗan tsiririn tsaki ya ja ya nufi washing handbase ya saba in yayi aiki ya fi ɗaya a rana kan ya iya maida kayan shi se ya watsa ruwa sbd ze yi ta jin ƙarnin jini ne Dukda ko kusa ko alama jinin be taɓa fatar shi ba amma haka kawai ze yi ta jin rashin natsuwa, yau kam dae ba ze iya ba.
Alwala yayi ya fito ya nufi change room ya sauya kaya kan ya matsa inda yake sallah idan be samu jam'i ba ya tayar, bayan ya idar yayi adu'o'inshi kan ya miƙe ya nufi gaban desk ɗin shi missed calls ya samu, na Naina, Asma'u da Naufal se wasu...
Kaman ze kira Nainan se ya tuna yadda tayi biris dashi da safe akan Aysher, ya rasa me ke damunta wannan dae kam kai tsaye za'a ce rashin tausayi da imani, me Aysher tayi mata da zafi da hatta ciwo ma ba za'a ɗaga mai kafa ba?
Asma'u ya ƙira ringing biyu ta ɗaga muryarta da alama tayi kuka ta gaishe shi
"Me ya faru?"
Ya tambaya.
"Babu, Yaya ya jikin Aysher din? Is It serious?"
Muryanta yayi sanyi dayawa kaman ba Asma'u ba, ba don ya yarda da babu komai ba kai ko kiranshi da yaya da tayi ya nuna akwai damuwa yace
"taji sauƙi...."
Ɗayan hannunshi cikin aljihu ya nufi gaban kujeran da take ya tsaya yana kallonta ya ƙara da cewa
"bacci ma take"
Ajiyar zuciyar da har seda yaji ta sauke kan tace
"Allah ya bata lafiya"
Daga haka suka yanke wayan.
Kan ya sauke hannunshi kiran Naufal ya shigo dagawa yayi kan yayi magana Naufal ya fara jero mishi tambayoyi
"babban yaya ya jikin Preetty? Maami ke ce min bata ji daaɗi ba naje gidan ma ban samu kowa ba, is it serious? An bata gado ne? In zo asibitin ne?
Idanunshi da ya lumshe ya ware yana ɗan murmushi yace
"taji sauƙi, we are heading home now"
"Toh zan jiraku Yaya"
Daga haka ya sauke wayan, wayan ya ɗan bi da kallo na seconds kaman wayan ya zama baƙon shi kan ya kalleta.
"Aysher"
Ya kira sunan yana ɗan bubbuga jikin kujerar, da alama tana da nauyin bacci. Seda ya kira sau uku kan ta farka, da sauri ta zauna tana gyara rigan jikinta, uncomfortable take jinta barin ma da ta zauna kasancewar ta jima a kwance tana jin yadda jini ke fita mata se taji gabaɗaya ta takure.
"muje gida"
Yana kai nan ya koma ya tattari abunda ze tattara kan ya nufi kofa tana tsaye rike da ledar ta ya buɗe ta bi bayanshi suka fice, bata ga ya sawa kofan kwado ko key ba hakan yasa tayi ta juyawa tana kallon kofan kar dae mancewa yayi, gyara gyalen ta tayi tana kallo ya danna wani abu kaman kofa suka tsaya gaban abun tana daga bayanshi na mintuna kan abun ya dare biyu, shi ya shiga tabi bayanshi cikin tsoron da ya kama ta ta fara kalle kallen cikin elevator ɗin.
Danna wani arrow da ya nuna ƙasa taga yayi, se taga abu ya rufu ya fara motsi da sauri ta rufe idanunta jin jiri na kwasarta baya tayi ta sake dawowa gaba se goshinta ya bugi bayanshi, karamin ƙara ta saki shi kuma yayi hanzarin Juyowa yana riƙe hannunta ganin tayi baya a tsorace zata faɗi.
"Yi haƙuri jiri nake gani"
Ta faɗa cikin diriricewa sbd idanu da ya ɗan tsura mata.
Hannunta da be saki ba ya ɗaura akan wani handle dake gefe da gefe alama na rikewa ne se ta damke ta sake runtse ido jin da gaske jiri take ji.
Har ya tsaya be daena observing ɗinta da ido ba, kofan na buɗuwa yace
"muje"
Se ta buɗe ido ta shiga gaba ganin ya bata hanya, kaman zata kife take tafiya, ga jiri ga kunya sbd gani take kaman kowa ita yake kallo.
Seda yaga zata bi wani hanya kan ya shiga gabanta a tare suka fito ma'aikatan na ta mishi se da safe, motan shi da ya ɗaga a sadda ta fita yaje mall ya sama mata kaya da abinci ya nufa parking lot da nashi ne na musamman ya buɗe ya shiga, tana ɗan kallon kayatuwar harabar asibitin itama ta buɗe gaba ta shiga, a hankali ya ja suka fice daga asibitin se a lokacin ta tuna kayan baccinta dake shanye a office nashi kuma harda inner wear dinta da ta cire, runtse idanunta tayi gashi ba halin ta ce su koma kuma bata da zarrar da zata iya ce mishi gobe ya kawo mata, ina ma ta isa? Amma kuma ya ze yi gobe idan ya je ya gani..
Da wannan sake sake suka isa gida, ita ta soma shiga parlorn se taga Naufal da Naina suna zaune suna kallon Tv lokaci lokaci suna ɗan hira, dama shi mutumin ta ne ta kan sake mishi su yi hira.
"boɗɗi..! Noi a ɓeɗɗi matugo?" (Ya kika kara ji da jiki?)
Ya faɗa yana Miƙewa tsaye ba tare da ya amsa sallamar da tayi ba.
"Alhamdulillah wodi dama(da sauƙi)
Ina yini?"
Ta haɗa gabaɗaya sbd ta samu ta wuce ganin Naina da irin kallon da take mata na sama da ƙasa.
"Zauna mana!"
Ya faɗa, a ɗan darare ta zauna a ƙasa tana kau da idanunta daga deadly look da Naina ke mata..
Wani irin abu ne ya tsayawa Naina a wuya yanzu wannan yarinya har she's worth of wearing thomb Brown? Sabon desinge ma da ko ita ta saya ne bata saka ba amma wannan ƴar kauyen ta riga ta sakawa, yanzu ma wai tare suke da mijinta tun safe? Tsaki me karfi taja ganin yadda duk Naufal ya ruɗe a kanta, ga Emran ma da ya shigo se ya samu wuri ya zauna, Miƙewa tayi ta bar parlorn ba tare da ta ko kula gaisuwar da Ayshern ke mata ba.
Naufal ne ya gaida yayan nasu ya amsa mishi yana tambayar su Ammi sbd be shiga ba yau, amsa mishi yayi da suna lafiya suna yiwa Aysher ma sannu da jiki.
Miƙewa yayi yace bari yayi wanka ya shige.
Kaɗan kaɗan take amsa mishi sbd zama da tayi da dare tayi nazari akan chanzawar Asma'u a jiya, ta fara tsoron abunda Naufal ze iya cewa sbd kowa ya zauna da Asma'u ko bata fita fili ta faɗa ba zaka san akwai soyayyar Naufal a ranta gashi shi kuma inda ya dosa daban, sam bazata so ya lalata kyakyawar alaƙarsu ba sbd da ita ne kawai take zama taji daaɗi duk garin na Abuja da ta tsinci kanta ciki babu zato bare tsammani.
Ganin yadda take amsa mishi ne yasa yace
"ko har yanzu jikin ne?"
Kai ta gyaɗa tace
"Ina so ne in ɗan kwanta"
"Toh Allah ya qara sauƙi, zan shigo gobe in duba ki"
Girgiza kai tayi
"Ai gobe zan je school ne"
"har zaki iya zuwa school? Ki huta mana samu ki ƙara samun karfin jikin?"
Nan ma girgiza kai tayi
"Ai da sauƙi in shaa Allah zan iya zuwa"
"to shikenan ko zuwa dare zan shigo, me zan kawo miki? Baki bukatar komai?"
Girgiza kai tayi ba tare da tayi magana ba
"sai gobe ɗin"
Tana kai nan ta nufi ɗakinta, da kallo ya bita har ta shige, yarinyar is just a damsel ya ayyana yana murmushi a bayyane.
Har aka kira la'asar kan Emran ya fito sanye da kananun kaya da alamun yayi wanka ya chanza a tare suka fice masallaci da Naufal, bayan sun dawo be shiga ba ya tafi shi kuma ya dauki mota yaje nema musu abunda zasu ci, har se bayan Magrib ya shigo don ya ratsa wurin friend ɗin shi Sufyan sbd kwana biyu sede suyi waya sam basu samu time na juna ba.
Kai tsaye knock ya mata don ya bata nata ya kuma duba jikinta, buɗewa tayi har lokacin rigan ne jikinta ta gaishe shi ya tambaye ta jiki ta amsa a kunyace, diary milk dake hannunta ya bi da kallo a sadda take karɓan abincin, kaman baze yi magana ba chan ƙasa ƙasa sbd gajiya da yake ji yayi ga kasala dake rufe dashi tun safiyar yace
"Hey in ba so kike duk wata duniya su san kina period ba to ki rage shan wannan zaƙin"
Ya karashe yana nuna choculate ɗin ta idanu...
Ina ƙasa ya buɗe ta shiga..kasa ta sunne kanta be jira amsarta ba ya juya ya tafi gab ze shiga ɗakin Naina ya ɗan saki murmushi da shi kaɗai ya san dalilin abunshi kan ya buɗe kofan ya shiga.
Tana kwance a kan gadonta hannunta na ɗaure a kan goshinta jin motsin shi be sa ta ɗaga kai ta kalleshi ba
"Babe"
Ya faɗa chan ƙasa
A hankali ta ɗaga idanunta ta kalleshi, yana zama gefen ta ya riƙe hannunta yana ɗan shafa bayan a hankali yace
"whats ur problem?"
"Ka daena ɓata bakinka wurin tambayata kaima ka san matsalolina biyu ne daga na wannan shegiyar yarinyar se na haihuwa"
Idanunshi ya lumshe ya sake buɗewa
"Meyasa? Meyasa burin ki ko yaushe ki ɓata min rai Naina? Sau nawa zan gayamiki muhimmancin Isma'il a wurina ne? Why zaki sheganta mishi ƴar da ya haifa ta hanyar aure da sunna?"
Ganin Ranshi ya ɓaci ne yasa ta miƙe zaune se ta takwashe kafa ta kife kanta a kirjin shi
"Am sorry... Ka sanni ban iya ɓoye so ko ƙi ba Emran ban san Meyasa a ko yaushe na kalleta se in ji kaman zan mutu ba"
Sbd sanin yana da bukatarta ne kawai ya sa ya soma shafa bayanta
"hakan babu kyau, bata miki komai ba fa hasali ma tsoron ki take ji ki daure ko ba zaki so ta ba karki ƙi ta, and ban ji daaɗin abunda kika yi ba yau ciwo ai ya wuce gaban wasa kuma kema baki fi karfi Allah ya jarabceki da ciwo ba kina tunanin ita zata iya ganinki ta kyale ki ne? She's just a little girl with a pure heart pls Naina drop all ur dramas i beg u"
Shiru tayi bata iya ta ce mishi komai ba, abincin da ya kawo musu ya sakata ɗauko plates da sauransu suka ci a ɗakin nata, tana ɗan mishi hirar success din ta a company ɗin su da kuma business trip da take son zuwa chan Thailand, se a sannan ya faɗa mata tafiyar su ma ya gama komai its next week monday, sossai tayi farin ciki kila bazata dawo ba se da ciki.
Bayan sun gama yace ta shirya kwanciya ta same shi a ɗaki, Dukda she's not in the mood amma ta san buƙatuwar mijin nata, haka dae ta shirya ta isa ma ta same shi Fitowar shi wanka kenan ɗaure da towel a kugu kayan baccin da be sa ba kenan, ta gurzu har seda yaga ta jiggata ya kyaleta ya kwanta daga gefenta yana runtse idanunshi da sauri ya kuma buɗewa ya ja tsaki tare da dirka ya shige toilet ya sakarwa kanshi ruwan sanyi...
Washegari Aysher bata zauna ba tunda tayi sallah ta fita kitchen doya ta soya se ta mishi miya ya ji albasa sossai, a dining ta shirya tea take son sha, se ta tuna wadda Nene ke yiwa baffa itama kila ya taimakawa cikinta da lokaci lokaci yake ciwo, ruwa ta zuba a tukunya ta ɗibo kayan kamshi ta zuzzuba har da busashen lemon grass da ta samu a kitchen ɗin, ta zuba sugar se ta ɗauko madara cikin na kamfanin Alhaji, evaporated one ne ta zuba a ciki, seda ya dafu kan ta tace ta zuba a flask ta kai dining ɗin ta dibi nata ta koma ɗaki, sauri sauri ta ci ta shiga wanka ta fito ta zo ta shirya cikin uniform ɗinta.
Hannunta rike da socks da take son sawa a mota sbd makarar da tayi ta fito, a dining ta same shi yana zaune yana karyawa hannunshi riƙe da kofin tea din da ta yin yana sha shi anya akwai randa ze daena mamakin hannun yarinyar a girki? Sossai tea ɗin ya mishi daaɗi, har gabanshi ta zo ta duƙa.
"Ina kwana Abba?"
"Lafiya ya jiki?"
"Lafiya ƙalau Naji sauƙi"
"ya daena kwata kwata?"
Ya tambaya kai ta gyaɗa ba tare da ta ɗago ba, yace
"to Alhamdulillah, Allah ya tsare"
Ta miƙe ta fice bata ga motar Naina ba alamun ta riga su wucewa ne ta shiga wadda ke kaita driver ya ja ya wuce.
A ranar da ya fita ya je gida ya sa me aikin Hajiya zuwa kasuwa da driver aka sake siyayya me yawa aka kai gidan nashi, ko da Aysher ta dawo ta gani ta ji daaɗi don akwai ganyayyaki har da kubewa, wanda zata sa a frigde ta sa kubewa kuwa ta sa a kwando ta ajiye waje sbd in an sa a frigde yana baki, tun daga ranar har satin ya kare tayi abinci kala kala wadda sossai Yake jin daaɗinsu, ita ba wai tana yi don burge shi bane kawai tana yi sbd tana ganin hakan ne ya kamata bazata zauna yana dafawa ko kullum yana zuwa saya ba tunda komai a kwai ba babu ba...
A ɓangaren makaranta babu abunda ya sauya daga yadda su Maryam ke treating dinta bata iya ta faɗawa kowa ba kuma, amma tana kokari wurin karatu sossai, ta ɓangaren Naufal kullum se ya zo da dare wani lokaci ma a gidan yake cin abinci, ran juma'a aka neme su a school dole ta sa ya juya Asabar duk yadda ya so ya saya mata waya ko gaisawa su ke yi Emran yace be amince ba waya ba yanzu ba, ita kuwa Naina babu abunda ya chanza daga kiyayyar da take yi mata sbd, ko zasu haɗu sau nawa baya hana Aysher gaisheta amma bazata amsa ba, ko kallon abincin da take dafawa bata yi idan Emran baze iya zuwa saya mata ba se tayi order ko ta fita taje ta sayo, ƙaninta Nameer shima tun da yazo ya ga yadda tashi ɗaya yar fullon da suka zo da ita ake ta musu dariya a jirgi ta sauya ya fara nuna yana ciki Dukda Addar tashi kai tsaye ta nuna bata amince ba kuma a shirye take ta haɗa shi da iyayen su hakan be hana shi zuwa sa'i sa'i ba...
Yau Lahadi bayan ta gama girkinta na dare da tayi tuwon shinkafa da Miyar danyen kifi ta shirya dining, ta zo zata wuce da nata ya dakatar da ita hakan yasa ta samu wuri ta tsuguna a gefenshi, idanunshi ya cire daga system da yake operating tun bayan la'asar a wurin yace
"gobe in shaa Allah zamu yi tafiya da Naina"
Da sauri ta kalleshi se ta duƙar da kai tana wasa da hannunta ganin shima ita ɗin yake kallo
"ba barinki zamu yi anan ba, ki haɗa kayan ki gobe da safe ki sa a mota idan driver ya koma daukar ƙi gida chan ze kaiki har se mun dawo in shaa Allah"
Ajiyar zuciya ta sauke dama har ta fara tunanin ta yadda zata zauna a wannan gida ita kaɗai, a hankali tace
"Toh in shaa Allah zan yi hakan Abba, Allah ya tsare muku hanya ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya"
Murmushi me kyau yayi mata wadda seda gabanta ya faɗi ba tare da ya amsa a bayyane ba, ta miƙe ta shige ɗakinta.
Washegari da safe bayan ta gama abin kari ta shirya ta janyo akwatin da ta haɗa duk abunda ta san zata buƙata ta janyo ta fito, yana zaune dining ta duƙa ta gaishe shi, cikin kulawa ya amsa ya kara da
"Babu abunda kike buƙata?"
Kai ta girgiza yace
"karɓi"
Kuɗi ne, ta miƙe ta karɓa tare da mishi godiya
"se mun dawo ko?"
Ya faɗa yana kallon fuskanta ta sake musu Adu'ar sauƙa lafiya kan ta janye akwatin ta fice...
Kaman yadda ya faɗa driver gidan Alhj ke kaita bayan an tashi kenan sun tafi ɗin already,
Showing 27001 words to 30000 words out of 38960 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10 Chapter 11Chapter 12Chapter 13