sun ƙi sbd yadda hajiyarsu Alhaji bata raga musu ko da wasa suka kama dukuyoyin ƴaƴansu suka cigaba da rayuwar su.

Dawowar Hajiya nan yasa aka saka Big bro karatu yana gama primary Alhj ya fitar dashi waje inda a chan yayi secondary yayi degree na farko da na biyu, shi da Nigeria sede hutu kuma yawanci in ya zo ze je ruga sbd mahaifinki kawai ko yini guda ya kan yi ya dawo, a shekarar gama degreen shi na uku Allah ya karɓi Hajiyar su Alhaji ta aurar da Asma'u da shekaru masu yawa...

Ammi kuwa bayan Ya Salma ta haifi Ya Nurain da Ya Murad, bayan haihuwar ya Murad da jimawa ne aka haifi Ya Naufal wadda mahaifiyarshi ta rasu wurin haihuwarshi se Alhaji ya karbo shi ya baiwa Ammi Dukda Hajiya ya so bawa se ta ƙi sbd Ammi ce kawai mahaifiyarshi ko da take raye ta kuma bada uzurin sashen Ammi ne da yara se ya fi sakewa, a lokacin Big bro na chan Kasar waje yana practical wadda daga nan ne za'a bashi matakin professor a harkar likitanci.

Bayan zuwan Ya Naufal gidanmu da shekaru kusan biyar tukuna aka haifo ni, Alhaji ya mayar min da sunan Asma'u kanwarshi, kowa ji dani yake barin ma Ya Naufal tunda sunan mahaifiyarshi naci Maaama yake kirana yayinda sauran daga me Auta se Big bro da Asma'unshi kai tsaye... Ta faɗa tana ɓata fuska.

Ehen Ya Salma tayi aure tana nan cikin Abuja itama da yaranta, Ya Nurain yana Cyprus tunda ya tafi karatu yaki dawowa sede zuwa ya auri wata baturiya yaransu biyu, kwararre ne a harkar ƙarafuna, Ya Murad na nan da Alhaji shi yake taimaka mishi a komai na companies ɗin su na nan don field ɗin shi kenan se Ya Naufal da yace shi irin aikin Big bro yake so, The young surgeon kaman yadda Big bro yake kiranshi, se Ni ta nuna kanta ina karatun harkar karbar haihuwa da kula da jariri wato unguwar zoma. Toh kinji tarihin gidan Zubair mai yaƙi da iyalanshi".

Tana wannan surutun suna nan suna zagaye ne tana ɗaukan abubuwa yayinda Aysher ke tura chart ɗin, ya cika makil da abubuwa kama daga mayuka, turaruka, gowns, kananun kaya, atampha, laces, shoes da bags.

Aysher na ta murmushi Dukda tana fahimta sbd zallar hausa take yi bata sa turanci se kaɗan kaɗan kuma ta fahimta sossai, Allah sarki hajiya ta ayyana a ranta, irin su Allah yayi musu tanadi me girma ranar gobe.

Wurin biyan kudi suka tsaya Asma'u ta bada Atm card dinta aka cire ko rabin kuɗin da Big bro ya tura mata basu ci ba, komawa Asma'u tayi ta jidi choculates masu yawa aka saka musu a leda daban, daga nan Saloon ta kaita ana ta santin gashinta aka warware aka yi mata gyara na musamman, bata son kitso se aka bar mata kan a haka bayan an gama, daga nan suka yi wurin tailor ɗin Asma'u ta fidda mishi atampha da laces ta bashi kudinshi suka yi akan express ne rana irin ta yau zata dawo ta karɓa ta kai mata gidan Big bro.

Daga nan gida suka dawo a gajiye likis ga yunwa don ma sun yi sallah a Saloon, la'asar da ake kira yanzu kawai suka yi suka nemi abinci Ammi kam tana chan wurin Hajiya don ta kan je a matsayinta na karama su yi hirasu kan ta dawo.

Bayan sun ci abinci suka sake bajewa duk wani abu da suka saya wadda Aysher bata san anfanin shi ba seda Asma'u ta nuna mata, wani shakuwa suka yi na nan take hatta shaving stick seda ta nuna mata yadda ake anfani dashi da cream ɗin veet da ta saya mata na shaving, abu kaɗan se tace
"ɗiyarmu ki dage ki zama yar gayu kika wanku ba karamin gwara kan samari zaki yi ba"

Se Aysher tayi dariya ta ce
"kai Auntyna"
Wannan Auntyna da take faɗa ke fasa kan Asma'u take kara ƙaunarta, se tace
"Ba wannan kaɗai ba ɗiyarmu Big bro baya harka se da Ƴan gayu baki ga Aunty Naina ba? Kaman zata chanza fata sbd kyale kyale da gayu?"

Aysher murmushi kawai take tana ayyana yadda zata saje a cikin matasan gayun Abuja, taji daaɗi kwarai zuwanta gidan don da dare da driver ze maida ta harda kwallarta Asma'u tace zasu dinga ziyartar juna kar ta damu, dama bata zuwa gidan ne sbd Aunty Naina se tayi ta dagawa mutane hanci kaman tafi karuna arziki, amma zata ke zuwa sbd Aysher...

Ko da suka iso drivern shi ya taya ta shigar da kayayyakinta har parlor, me gidan na zaune matar kwance kanta akan kafafunshi yana anfani da waya tana ɗan mishi hira jefi jefi, ya sauya kaya zuwa kananu wadda suke matukar amsar shi su ɓoye shekarunshi, da idanu Naina tayi ta bin tulin ledojin har drivern ya gama shigowa dasu kan ta kalli Aysher ta juyo ta kalli Emran

"wannan fa?"
Se a lokacin ya ɗaga kai ya kalli kayan kan ya kalli Aysher da ke gaishesu ya amsa ya maida kanshi kan wayar, ganin babu wadda ya amsata yasa ta miƙe ta nufi kayan tayi ta bubbudewa tana mamaki harda super sheraton zanin da yayi 200k yanzu? Ga egyptian Abayas na 40-40k har kusan bakwai, man shafawa ma kaɗai na CreaVe aka saya mata.

"Emran waennan kaya duk na wannan village girl ɗin?"
In dutse ya tanka to ko Emran ya tamka ko kallon ta be sake yi ba, kokarin tattare kayakin take cikin muryar gargadi yace
"Ki ajiye mata kayanta Naina, wai whats wrong with you ne?"

"Ko de whats wrong with you ba! Taya zaka kashewa wannan yar kauyen wacce ko anfanin kayan bata sani ba irin wannan kuɗi? And ina magana ka ba banza ajiyata a gaban yarinyar salon ta yi ma kanta kallon kan mu ɗaya?"

"Naina! Naina!!" Ya kira sunan yana kallonta, hawaye ta fara tare da zubar da kayan tayi ball dasu ta wuce kaman iska zuwa ɗakinta, idanunshi ya lumshe.

Duƙawa tayi ta tattare kayan ta mayar leda sam bata ji wani haushin matar gidan ba, taji dae rashin daaɗin ganin yadda fuskan Abban nata ta nunawa damuwa, a nan ƙasa ta tsuguna bayan ta gama mayar da kayan leda, sam be san tana wurin ba se chan ya buɗe idanunshi don Miƙewa har ta fara tunanin bacci yayi a hakan ne ko yaya se suka haɗa idanu, saita Muryar shi yayi yace
"Da wani abu ne?"

"A'a, dama zan ce ne na gode Allah ya saka da alkhairi ya kara buɗi"
Da Ameen ya amsa tana nan tsugune kaman ta tambayi wannan matar patient din na dazu se bata yi wannan katsalandan ba taji yace
"se da safe ko?"

Tayi saurin Miƙewa tana cewa
"se da safe"
A hankali tayi ta tattare kayakin har ta shigar, a tsakiyar ɗakin ta zube su kan ta yaye gyalen ta ta isa gaban wardrobe se kallon kanta take tana mamakin wai itace wannan, nace tukuna ma.

A natse tayi ta shirya kayan tana tuna yadda tsarin na Aunty Asma'u yake tana shirya nata tsab se ga ɗakin ya fito kaman na Ƴan mata, tsalle tayi ta faɗa kan gado tana jin daaɗi, ta jima tana juyi kan ta yi toilet ta ajiye kayan wankanta da su shaving stick din, tayi alwala tazo tayi isha'i, zuwa wardrobe tayi ta buɗe tana tuna abunda Asma'u tace
"kin ga anan birni, waennan night wear ake kiransu akwai na matan aure akwai na en mata shiyasa na ɗauka miki riga da wando riga da wando dogaye, da daddare duk kayan dake jikinki zaki cire ki saka su se kin fi jin daaɗi, sannan babu maimaita kaya kina cire na jikinki ki saka shi cikin basket na wanki, in ta kama ma duk dare kan ki kwanta kiyi wanka ki sa turare zaki ji yadda zaki ji daaɗin bacci a wannan rana"

Murmushi tayi ta dauki sabon towel shima seda ta jadadda mata dashi ake wanka in an fito a goge jiki se a shafa mai kan a shanya shi a sa kaya, kayan jikinta ta cire ta haɗa da na saƙinta da ta sanyo a leda ta zuba cikin basket da ta gani irin shi a ɗakin Asma'u na kayan wanki, bayi ta shiga ta farke sabon sosonta ta buɗe shower gel kaman yadda Asma'un ta nuna mata, Allah ma ya sa tana da kwakwalwa bata manta duk zantukan Asma'un ba, wanka tayi da ruwan dumi ta fito ta shafa mai sama sama ta fesa turare kaman yadda ta nuna mata yadda ake sawa tun kan su tafi mall, ta sanya Cotton riga da wandon ta se taji wani daaɗi na ratsa ta, se shakar kamshin jikinta take haka ta kwanta a gadon tare da lumshe idanu bacci me daaɗi ya ɗauke ta...

Be bi ta kan Naina ba ya wuce ɗakinshi yayi shirin kwanciya ya kwanta abun shi.

Hawaye take tsakanin ta da Allah
"Mommy wai kinga abubuwan da yake yiwa yarinyar nan? Ni abubuwan ma basu dameni ba, ya kaita duk inda ze kaita sannan ya mata na tsani yarinyar ba tare da na san dalili ba"

"wai yaushe kika zama haka ne? Ina ke kika gaya min yadda ya dinga lallaba ki akan in ba zaki taimake shi akan yarinyar ba ki fita harkar ta? Wannan abunda kike yin shi ze sa ta raina ki, ki kama kanki a matsayinki na me ilimi kuma matar gida, tun yaushe baki maida ita ƴar aikin da ya ƙi samar miki ba!"

Shiru tayi tana nazarin maganan maman tata, hakane kuma fa, kuma ta san fushinshi bashi da kyau shiyasa be cika yi ba don in ya birkice kaman wadda ya sha shaferin Fulani, zata fita harkar yarinyar ta kama abunda ke gabanta tunda ta riga ta zame mata ƙashin wuya.

Sun ɗan kara tattaunawa da mommy kan ta miƙe tayi wanka ta shirya cikin wasu sexy nighties ta nufi ɗakinshi don bashi hakuri irin ta masoya, ta san kayanta cikin lokaci kankani ta samu ta saukar da fushin suka sha baccinsu ita kanta ta san mijinta na son ta to me na wani damun kanta akan yar kauye?....

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰



🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA


بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

Jira jira jira lanta Ina Zaki Naga kina sauri aa larai kyale ni yanxu zamanin idan kin ga mace ta zauna ita taso gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata Aa wanan shaharren campany da suke taimakawa Mata masu son Fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida Akan farashi me Kama da kyauta Zaki jiran ki kawai lantis inda da wata yar marainiya 10k din zanje Naga ko zan samo abun da zan Fara Mai da taro sisi
So kike ki Fara sana'a ko Kuma har yanxu baki gaji da tambayar megida kudin biki da na suna Yana Sha Miki kamshi ba to idan kin shirya Nima na shirya tsab domin baki kayana sari akan farashi sauki kema kiji ki nime naki
Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944

Sai kunzo

*FREE PAGE 5

Washegari da wuri ta tashi sede bata yi wanka ba, ta gaji da zaman ta dubo choculates da Asma'u ta jida mata ta fara sha, jin daaɗin su ya sa tayi ta shan abunta har taji ya isheta, ƙishi take ji don haka ta miƙe ba tare da ta damu da neman dankwali ba gashinta se rito yake daga tsakiya da aka mata parking ta fito, blue Cotton nighties din nata se ya mata kyau kaman ƴar baby, fuskanta banda farin glass dinta babu komai, a hankali ta nufi inda tafi tunanin kitchen ne jin gidan yayi shiru sossai.

Tana sa kanta ta tsaya chak tana karewa bayanshi kallo, bata shiga mamaki ba seda ta fahimci me yake yi, girki fa yake yi kaman, baki ta saki tana kara zura idanu don tantancewa ina namiji ina girki? Ta ayyana tana kama haɓa, shi kam be ma san da mutum ba, yana sanye da farin karamar shirt da ya kama shi ya fidda kakkarfar surarshi da three quater Black me aljihuna dayawa, ya gama soya irish yana soya kwai gefe kuma ruwan zafi na tafasa a kettle.

Tunani take ta shiga ne ko ta koma kuma kishin ruwa take ji, ita dae wannan abun kunya ne namiji a kitchen abunda bata taɓa gani bane a gidansu, bata tunanin ko ruwan zafi baffanta ya iya dafawa, to ina matar gidan? Ta tambayi kanta, tana shirin juyawa ya juyo se suka haɗa idanu...

A jikinshi yaji kaman mutum na tsaye wurin hakan ya saka shi Juyowa se ya kalleta, ya ɗan yi mamakin sauyin da ta samu a kwana biyu kacal da Shigowar tata birni, a ladabce ta gaishe shi ya amsa yana cewa

"yunwa ko? Breakfast is ready"
Ji tayi wani sabon kunya ya rufeta, ina ma da ta iya anfani da waennan abubuwan nasu kuma ta iya girkin en gayu? Ina zata bar Abbanta a kitchen yana musu girki suna mata?

"A'a diyam mi ho'ata (ruwa zan ɗauka ne)"
Frigde ya nuna mata ta ƙarasa ta ɗauka se taji ya ce.
"Wait"
Dakatawa tayi, ya haɗa mata tea ya daura a gefen tray da ya ɗauko ɗan ƙarami gefe ne dauke da irish da kwai da ya soya se ya zuba mata ketch up daga gefe incase bata iya taci ba zata barshi a wurin, ya riƙo trayn yazo ya mika mata.

Karɓa tayi bayan ta ajiye ruwan da ta dauka a kai
"Na gode"
Ta faɗa tana me ficewa sum sum sum Allah ya gani bata ji daaɗi ba.

Daki ta shiga ta ajiye trayn ta fara ci kuma yayi daaɗi sede shayin ya mata kauri kuma ita kam be ji sugar ba se gardin madara, haka dae ta shanye ta kuma cinye abincin tass yayi daaɗi, trayn ta dauka ta kai kitchen babu kowa yanzu hakan yasa taje ta wanke ta mammayar inda taga en uwansu kan ta koma ɗakin ta tayi wanka, riga er kanti ta saka baƙi me dogon hannu ta koma gado ta kwanta..

Haka ta yini shiru shiru se chan around 3 yayi mata knocking ta tashi taje ta buɗe leda ya miƙa mata ta karɓa tayi godiya, abinci ne a ciki kala biyu kila har na dare, taliyar taci ta bar tuwo da Miyar egusi da yaji naman se chan anjima ta sake kwanciya, sallah kaɗai ke dagata shirun ya mata yawa, haka dae ta kai dare taci tuwon ta fiddo abubuwan ta zuba cikin dustbin na kitchen ba kowa ta ɗauki ruwa ta koma ɗaki.

Washegari monday tana sane da yau ne Murad ze kaita makaranta da wuri ta tashi ta shirya ta sa Abayarta guda ɗaya colour purple da ado sossai White ya mata kyau sossai, ta yafa gyalen kan gashinta da ta taje ta sake kamawa yadda taga sun mata a Saloon, ta samu wuri ta zauna tana jiran tsammani. Bata jima da zama ba kuwa taji an mata knocking

Da sauri ta isa kofar ta buɗe se ta saki murmushi ganin Murad ta gaishe shi shima ya amsa yana me tsokanarta ina kayan saƙinta ko yanzu kan mage ya waye? Ta bashi Amsa da ko yanzu zata iya sakata ta shiga ko'ina ai ba'a gudun asali, murmushi yayi suka fito a tare bata haɗu da duka ahalin gidan ba suka fice.

Ko da ganin irin tsaruwar ginin makarantar ma ta san ba makarantan wasa bane ba kuma na yaran talaka bane don da alama ze yi kuɗi motoci kawai take gani manya manya ana tsayarwa yara suna fita maza da mata suna shiga, yanayin uniform din ya ɗan sa ta rage marmarin nata, Maza kam nasu yayi don dogon wando ne ruwan toka se farin shirt da jacket me ɗan kauri kaman suit amma akwai ratsin ruwan tokar daga wuya da kuma hannu, nectie ɗaure daga ƙasan jacket din se tambarin makarantar daga kan jacket din, amma matan kam skirt ne shima ruwan toka me tattara iyakarshi gwiwa se farin riga da jacket ɗin, wasu socks ɗin su ya haura har saman gwiwa yayinda wasu socks ɗin su iyakarshi idon sawu kuma kawunansu babu dankwali dukkansu.

A baya take binshi har office na principal suka shiga cikin harshen turanci suka gaisa ya mishi bayanin kawo sabuwar daliba, duk wani abu daya kamata a take ya biya mata, aka kira wani malami yazo ya mata interview
"ba laifi yarinyar tana da kokari sede akwai matsalan magana da turanci da kuma dae waenda ba za'a a rasa ba, za'a barta SS1 ɗin amma a shawarce a kara mata da lesson teacher da ze na taimakonta a karatun"
Malamin ya faɗa bayan tambayoyi da yayi ta mata wasu ta amsa wasu kuma bata sani ba.

Godiya Murad yayi mishi aka kawo mata uniform da littatafanta suka fito, a mota ta dubeshi tace
"Yaya ka kaini wurin Aunty Asma'u"
Ta faɗi hakan tana kallonshi
Showing 9001 words to 12000 words out of 38960 words