albarka ne a gareshi, idan yaci irin wannan dama se a gidansu to gidansun ba kullum yake samun zuwa ba sbd aiki da kan mishi yawa.

Har suka gama Naina kam bata daena aikawa abincin shi Harara ba, shi kam yayi nak yayi hamdala kan suka wuce dakunansu, wanka yayi ya shirya kwanciya ya kwanta, be damu da duba Naina ba don ya san idan tana da wani bukata zata zo ko kuma shi idan yana bukatarta ya je amma ba kwana suke ɗaki guda ba.

Washegari da safe bayan tayi sallah ta fito kitchen, bata ganinshi bare ta tambayeshi tana tsoron yin abunda basa ci, ita ce ta tattare dining da suka ci abinci jiya taga ya ci sossai kila yana son abubuwan gargajiyan, masa/waina ta fara kokarin haɗawa da Miyar kayan ciki wato offals me daddawa irin na ainihin kauye dahuwar tayi.

Ta soya Masar Dukda ta sha wahala da tandar amma ba laifi yayi kyau sossai Masar, ta shirya a dining taje tayi wanka, doguwar riga ta sanya na Egypt maroon da yaji ado da fararen zare se ta zauna bakin dressing mirror din bayan ta kama gashinta ta fara gyara wurin, ta gyara ɗakin ta share.

Ita dae bata san wa me musu shara ba kuma a koyaushe ta kan ga gidan fess cike da kamshin freshners daban daban sbd da su Naina ke anfani wai bata son warin hayaƙin turaren wuta yana sa ta tari.

Daidai ta fito shima ya fito sanye da kaftan Ash da aka yiwa wani kalar ɗinki irin na zamani, hannun iyakarshi damtsenshi ya bayyana murdewarsu da irin kaurinsu, iyakar rigan cinyar shi, kafafunshi sanye da farin takalma palms masu kyau, hannunshi ɗaure da Black agogo, sajenshi zuwa gashin kanshi se sheki suke suna walwali, cikin seconds ta kare mai kallo kan ta duƙa kaɗan

"Abba ina kwana?"

Yace
"Lafiya..."

Har seda ya isa dining ya zauna yana kallonta har ta ƙaraso kan yace
"ya hannun?"

Ita mancewa take da ƙunan ma sbd ba wani me yawa bane tace
"Yayi sauƙi"

A hankali tayi serving dinshi se kallon kyaun masan yake, ita kuwa mamaki take yadda duk abubuwan da ta girka ze ci amma be taɓa cewa yayi daaɗi ko be yi ba, be taɓa ce mata sannu ba bare ya gode, tura mishi tayi se taga ya janyo spoon a ranta ta raya lallai ba zaka ji daaɗin wainar nan ba tab, ai ita da wuya taci abinci da cokali gani take rage mata daaɗin ze yi.

Zuba nata tayi ta dauka zata juya yace
"Aysher"

Da sauri ta juyo tana amsawa
"Sit, karki sake tashi don muna wuri we are like ur parents"

Kallon abincin tayi ta san matsayin mahaifinta yake amma bazata iya sakewa taci da hannu kaman yadda zata ci a ɗaki ba ko gaban baffanta, zama tayi bayan taje ta wanke hannunta a hankali ta sa ta fara ci, babu wanda ya tanka har suka gama.

"Hanzarta ki sameni mota"
Ya faɗa kan ya miƙe yayi cikin parlor.

Da ɗan sauri sauri ta gama, bata tsaya tattare wurin ba sbd Aunty Asmeey ta fada mata ya tsani jira, gyalen ta ta yafa kawai ta ɗauki takalmi ta fito, gidan gaba ta zauna ya ja motar suka fice.

Sam bata gane inda suka nufa ba har seda ta gansu a gaban gidan su Ammi, farin ciki ne ya lullube ta har tana sakin murmushi me sauti a hankali ya juya ya kalleta, tana ta murmushi kaman wacce duniya ta yiwa daaɗi, bayan yayi parking suka nufi ciki, itace a gaba don ta barshi a mota knocking ta ɗan yi kan ta tura kofar sashin Ammin, sam bata kula ma da mutum ba se ji tayi an ce

"Wowww what a damsel...!"

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰





🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA
 

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

*Aleesha collection*
''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?"
"a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata''
''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis  marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi''
Hajiya ta  zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar  mai gida ko saurayi  kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai  sauki ke ma ki je ki nemi  na ki.
Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944
Sai kun zo

FREE PAGE 9

Shi kam Naufal da kallo ɗaya yarinyar tayi mugun tafiya dashi, ji yayi kab duniya babu macen da ta dace ya mallakawa zuciyar shi kamar wannan yarinya, OMG! Ya ayyana a Ranshi a sadda ta kalleshi da idanunta masu kyau.

"Assalamu Alaikum"
Ta faɗa cikin sanyin muryarta.
Ganin se kallonta yake ya kasa cewa komai yasa cikin hausarta tace
"Ina kwana?"
 
Daga haka bata kara ba tayi sama, a hankali ta tura ɗakin Aunty Asmeey, tana zaune gaban dressing mirror suka haɗa idanu cikin tsananin farin cikin ganinta ta tashi ta rungume ta
"ɗiyarmu kece da safen nan? Tare da wa kuka zo?"

Tana murmushi tace
"Ni da Abba, ina kwana Aunty Asmy?"
"Lafiya ƙalau zo dama neman me tayani zaban kaya nake se gaki Allah ya turo ki, dubamin don Allah wanne ze fi karɓa ta?"

Tana dubawa tace
"zaki fita ne?"
"A'ah ke Ya Naufal ne ya mana surprise visit ze ɗan yi sattuttuka haka tsakani da Allah bana so ya kalleni ba cikin gayu ba, shima irin taste ɗin Abbanki gareshi, yana son gayu"

Murmushi kawai Aysher tayi tana nuna mata wani peach lace me emerald stones yana hade da mayafi emerald tace
"Ina tunanin wannan ze fi karɓarki.."
Ƙarba tayi ta manna da jikinta aiko ya mata kyau ta juyo cikin farin cikin da ya gaza ɓoyuwa a fuskanta tace
"thank you ɗiyarmu bari na shirya"

Shi kuwa Emran har ya nufi bin bayanta se kuma kiran Ahjinsu ya shigo mishi da alama yana son ganinshi ne, don haka se yayi chan ɗin, a ƙayataccen parlorn ya samu Murad da Alhaji suna wani lissafi baje akan hadadiyar rug carpet dake malale a parlorn, Ammi na daga dining a tsaye da alama Abincin Alhajin take haɗawa.

Da sallama ya ƙarasa duk suka amsa ya zauna shima daga ƙasa yace
"Barka da safiya Alhaji"

"yauwa bokan Turai, idanunka kenan?"
Murmushi ya saki yana ɗan shafa keya yace
"Alhaji ina shigowa ai kaine bana samunka"

Alhj yace
"hakkun ai kwanan nan daga ni har Murad bamu zauna ba, wani kamfani ne na saya na sarrafa kaya irin na mata to audugar da muka saya ne ashe ba me kyau aka kawo ba muke ta asara, ina ga zan noma Auduga bana"

"Alhaji ya kamata a huta hakanan jiki da jini"
Murmushi kawai Alhajin yayi dama rikicin su da Emran kenan a kullum, shi dae yana kaunar business ɗin shi baya ji kuma ze iya bari sbd tana da daaɗi neman na kai babu abunda ya kaishi daaɗi da kwanciyar hankali.

Murad ne ya gaida yayan ya amsa cikin kulawa, daidai Ammi ta kawo shiryayyen tray da abun karyawar Alhajin irin na masu ciwon siga, a ladabce ya gaida mahaifiyar tashi ta amsa ba tare da ta bashi attension ba, har ta juya se kuma tace
"in kana buƙatar kari se ka ƙarasa dining ɗin"

Girgiza kai yayi kaman tana kallonshi yace
"Alhamdulillah! Na karya a gida"
Maganar seda ya sa ta ɗan juyo ta kalleshi, ya fahimci ma'anar kallon Se kawai ya mata murmushi.

"Shiga ciki Likita ka ɗauko aid box ɗina ka zo ka gwada sugar da hawan jinin nan ban san wanne ne ya min yawa ba kwanan nan se in ta jin jiri da ciwon kai"

Marairaicewa Alhjn yayi yace
"Alhaji ba ka gani ba? Yanzu jikinka na bukatar hutu, Don Allah kayi kokari ka barwa Murad wannan aiki yanzu"

Cikin fara'a da alama dabi'arshi ce yce
"Imrana kenan ai idan lokacin barin yayi za'a bari ne!"

Miƙewa yayi ba tare da ya sake cewa komai ba ya nufi ɗakin Alhajin nasu anan ya ɗauko First aid ya zo ya mishi gwaje gwaje sugar din ne yayi rising don haka ya mishi allura, da kanshi ya haɗawa Alhajin tea wadda komai nashi na masu diabetes ne, anan ya zauna Murad ze cigaba da lissafe lissafen ya watsa mishi Harara wadda ya saka shi shirun dole, Ammi kuwa na zaune gefe tana kallonsu.

Naufal ne yayi sallama ya shigo parlorn.
"Babban yaya"
Ya kira Emran yana sakin murmushin jin daaɗin ganinshi.
"The young surgeon yaushe a ƙasar?"
Ya faɗa cikin murmushi sbd Naufal mutumin shi ne sossai da sossai.

"Ka ganshi nan wlh muma se ganinshi muka yi jiya ya diro mana ba notice"
Alhaji ya faɗa, dariya Naufal yayi ga dukkan alama shi mutum ne me raha da faram faram.

"Ammin mu yanzu naga wata yarinya ta shiga side dinki, yaushe kika samo wata ƴar ban sani ba?"

Ammi tana kallonshi tace
"Anya Naufal? Asma'u ce kaɗai a sashen nan ko dae nayi bakuwa ne bayan fita ta"

Yace
"kai A'ah Ammi wannan bata yi yanayi da bakuwa ba, se nine ma tayiwa kallon baƙo tana gaisheni ta haura upstairs se surutun su na tsinta da Mami"
Haka yake kiran Asma'u don baya iya kiran sunan mahaifiyar tashi kai tsaye.

Ganin suna ta wahalar da shari'a ne yasa Emran dake ɗan danna waya yace
"Aysher ce"

"Au ashe tare kuka zo da ƴar fullo tamu"
Murad ya faɗa, Ammi kam bata ce komai ba se Naufal ne yace
"wacece ita Murad?"

"Me damuwanka da sanin wacece"
Xe yi magana Ammi tace
"ɗiyar yayanku ce"

Ze sake magana Emran yace
"kai kuje chan parlorn sashen ku ko na Ammi kuyi wannan dogon surutun baku san Alhaji ba daaɗi yake ji bane?"

Shiru duk suka yi kan suka miƙe suka fice, Alhaji yace
"ka korar min yara ai se ka min hirar..."

Ammi ta saki murmushi me sauti tana kallonsu
"yi dariyarki Ammin su, ai yau se ya buɗe wannan baki da ba ya doguwar magana ya min hira tunda ya kori masu tayani hirar"
Murmushi me sauti kawai Emran ke saki yana ɗan shafa kai a tsanake cikin natsuwa yace
"Ai Alhaji ba surutu kake buƙata yanzu ba hutu ne, ka samu ka ci abinci ka ɗan kwanta"

"Mahaifiyarka ke ce min ka ɗauko ɗiyar sama'ila, to Allah ubangiji ya tayaka riƙonta, ya dafa maka wajen tarbiyartar da ita, Allah yaji kan mahaifinta"

Da "Ameen" ya amsa a natse, hirar komawa yayi tsakanin Alhaji Da Ammi na irin karamcin Isma'il da iya mu'amalarshi, shi kam sede ya kallesu ya ɗan yi murmushi.

Basu fi awa a sashen ba sbd kwanciya da Alhaji ya shiga yayi suka fito, tafe suke a tare da Ammi duk yadda ta so shiru ta kasa se cewa tayi
"Yanzu kam kana samun karyawa kan ka fita aikin kenan?"

Ɗan kallonta yayi cikin natsuwa yace
"Eh yarinyar nan Aisha na kokari, kusan duk abubuwan da nake so na gargajiya ta iya su"

Murmushi Ammi tayi cikin disappointment ba wai bata yi murna da taimakawa ɗan ta da Aysher ta fara daga zuwanta ba, kawai tana jin takaicin yadda Naina bata san girma da darajar miji bane, bata san sirrin dake cikin yiwa miji hidima bane daga nan duniya har lahira.
Har suka isa sashen ta basu sake magana ba, a kan Dining suka samu Murad yayinda Naufal ke zaune kan kujera yana kallo hannunshi rike da Orange juice yana sha.

Haurawa Ammi tayi yayinda shi kam ya zauna yana yiwa Naufal da ya bashi hankalinshi Ƴan tambayoyi wadda yawanci akan aikinsu ne don in har Kaga yana dogon magana akan aiki ne.

A hankali Ammi ta tura kofan Asmeey da har yanzu bata gama shiri ba se wani rawar kai take tace
"Toh sarkin zakwaɗi se ina?"

Tura baki tayi tace
"Ammi mutum ba ze yi wanka ba se ze fita?"

Girgiza kai Ammi tayi ba tare da tace mata komai ba ta maida kanta kan Aysher da tayi saurin zamowa daga bakin gadon tana gaisheta, cikin kulawa ta amsa tana sake kallonta to idan wannan ƴar yarinyar zata iya shiga kitchen tayi girki me ze haka Naina dake da kusan ashirin da takwas shiga kitchen fisabilillahi?

Kau da tunanin tayi ta nufi ɗakinta don gabatar da salatul duha ɗin ta.

"Zo mu je"
Asmeey ta faɗa bayan ta gama duk wani shirinta.

"A'a Aunty Asmeey ni ina nan"

"ba zaki shiga ki gaida Hajiya bane?"

Miƙewa tayi jin hakan ta gyara yafin gyalen dake ta zamewa sbd ba saka shi suke a ruga ba, dama baffanta ke sakata sa hula dole in ba haka ba gyalen a kwankwaso za'a ɗaura shi.

A hankali suke saukowa wadda karar saukowan ya fusge hankalin jama'ar parlorn banda Emran dake amsa call, Naufal kam babu inda idanunshi suka sauka se a kanta, Allah ya sani shi kam ya gani kuma yana so, Asma'u ta ƙarasa ta zauna ganganshi ta fara mishi surutu yayinda hankalinshi da natsuwarshi ke kan Aysher da ta samu wuri daga ƙasa ta zauna tana ɗan murmushi.

"Mi hofni ma boɗɗi"(Na gaishe ki pretty)
A tare Emran, Aysher da Asma'u suka kalleshi ita dae Asma'u ta san me boɗɗi ke nufi tunda tana tsinta, yayinda Emran hakan ya ɗan bashi mamaki, ita kuwa Aysher murmushi ta saki jin yana jin yaren ta sossai, kara gaishe shi tayi se ya fara mata tambayoyi akan Rugarsu.

Hirar da ta kwana biyu bata yi ba ta sake suke tayi da fulatanci, Asma'u da take kallon wannan ta kuma kallo wanchan ne tace
"Wallahi wannan abunda kuke yin ba kyau, taya zaku zauna cikinmu kuyi ta yaren da bama ji?"

Gwalo ya juya ya mata yana dariya yace
"In kin yi zuciya ki koya. Ko Boɗɗi?"
Ya juyo yana tambayar Aysher, tana dariya ta gyaɗa kai daidai zata sake magana suka haɗa idanu sbd ɗagowa da yayi hakan yasa tayi shiru.

Tsam ya miƙe ya fice daga parlorn ba tare da yace uffan ba, nan Naufal ya dawo hirar shi da Aysher tana amsawa, a hankali Asma'u da ta kura mishi idanu ta fara jin wani abu kaman haushi ko rashin jin daaɗi cikin zuciyarta, irin kallon da yake yiwa Aysher ya sha bambam da irin kallon da yake mata, tana da wayewa sannan tana da sani akan menene soyayya idan bata yi kuskure ba kaman Naufal na shirin kwarewa wannan yarinya ne, wani irin mummunan faɗuwa gabanta yayi a take yanayinta ya fara sauyawa..

Tsam Aysher ta miƙe tana ce mishi su yi hirar su da Aunty Asmeey tana zuwa, kitchen ta wuce me aikinsu ta samu ta fara ɗaura abun rana nan ta tsare ta da tambaya da kuma kula akan irin girkin na birni a tare suka yi suka gama, daga nan ɗayar zata kai na sashen Hajiya kaman yadda suke yi se ta bita ta baya suka bi zuwa sashen na Hajiya.

A tsakar parlor suka sameta zaune yayinda Emran ke kwance bisa dogon kujera sambal idanunshi a lumshe kaman me bacci, cikin sakin fuska Hajiya tace
"Ah me sunan Hajiya kece tafe da abincin?"

Tana ɗan murmushi ta tsuguna kasa tace
"tare da harira muke to zamu shigo nan se aka yi kiranta ta koma, ina kwana Hajiya?"
Cikin harshen fulatanci suke maganar

"jam ko ɗume noi school a ɗo habda kam?"(Lafiya ƙalau ya makaranta Fatan ana dagewa kam)
Cikin murmushi da bata daena ba tace
"Alhamdulillah"
Miƙewa tayi ta isa dining ta ajiye abincin hannunta, har ta juyo se Hajiya tace
"war wannu Abba ma ɗo yamdu ɗo tun nane o yiɗi nyamugo bo mi anda ko haɗi mo"(zo ki sakawa Abban kin nan abincin nan tun dazu yake son ci amma na rasa me ya hanashi).

Karasawa tayi ganganshi ta tsuguna cikin sanyin murya tace
"Sannu da hutawa Abba"
Be tanka ba, ta buɗe abincin cikin natsuwa ta saka ta janyo table ƙarami ta ɗaura mishi akai, ta juya zata fice ya kira sunanta.

"Zauna ki zuba ki ci"
Ya faɗa ba tare da ya buɗe idanunshi ba.

Kaman ta ce mai zata koma taci a wurin Ammi se kuma ta zauna, ta zuba ta fara ci jefi jefi suna hira da Hajiya, Miƙewa yayi zaune ya sanya spoon ya fara cin nashi sam be sa musu baki a hirar tasu ba.

Naufal ne ya shigo idanunshi akanta
"ke kuma daga bari kije ki zo se ki yi ɓatan dabo?"

"Ya Naufal ai na tsaya taya su harira girki ne"

Zama yayi gefen Emran yana cewa
"eyeee yau muna da cin daaɗi kenan tunda kin sa hannayenki masu albarka"

"Naufal pls in surutu ya kawo ka bama buƙata"

Cikin harshen turanci yace
"Afuwan Babban yaya ni kaina bana sanin ina sakin zance Allah yarinyar nan ta ruɗa ni za'a bani ita???"

Kallonta Emran yayi sede ya fahimci bata gane abunda Naufal ke fada ba sbd accent
Showing 21001 words to 24000 words out of 38960 words