yake zuwa haka itama in sun fita to tare ne, to Meyasa zasu koma haka da wuri?

"Ɗo you have any plans a Nigeria ne? Mu kara hutawa mana honey?"

Girgiza kai yayi yace
"I've already booked the flights karki manta ni ba ɗan kasuwa bane ni likita ne, me ceton al'umma bani da wani hutun hankali idan har na tuna na bar marasa lafiya da zasu iya bukatata a asibiti bana nan, maybe su zauna cikin ciwo suna jiran zuwana kinga ban kyauta ba in na cigaba da zaman, mu koma mu cigaba da renon cikin a gida"

Bata da ta cewa don ta san shi akan magana ɗaya ko me zata ce yanzu ba sauya ra'ayin shi ze yi ba haka ta miƙe tayi ciki...

On 27 din kuwa karfe tara suka fito a shirye, taxi ne ya ɗauke su ze kaisu airport a maimakon airport din se ta gansu a asibitin da aka mata aikin saka kwayayen hallitarsu.

"Me kuma zamu yi anan Emran?"

"Just wait here ina zuwa"
Yana faɗa be jira cewar ta ba ya fice daga motar ya shiga ciki, bayan mintuna kaman goma se gashi ya fito ya shiga motar suka yi Airport kaman yadda be ce mata komai ba itama bata tambaya ba, karfe 9:50 suka tashi, karfe ɗaya na rana ya musu a Nijeriya, numfashi me nauyi ya sauke a sadda ya shaki iskar ƙasar tashi.

Murad ne ya zo ɗaukan su, cikin farin cikin ganinsu ya shiga gaishe da yayan nashi ya amsa yana tambayar shi su Ammi, itama Naina amsawa tayi ba tare da ta damu da tambayar surukan nata ba, dama bata kiransu zuwa kuwa se idan wani abu ake shima bata wuce awa biyu wai bata son hayaniya zata tarkata ta bar gidan.

Ko da suka isa gidansu ciki tayi ta barshi da Murad suna magana, basu wani jima ba ya mishi sallama ya tafi har ya nufi shiga ciki ya tsaya ya duba agogon hannunshi 1:30 fasa shiga gidan yayi Dukda gajiyar da yake ji a jikinshi, mota kawai ya ɗauka ya fice yana driving cikin natsuwa lokaci lokaci se ya duba agogo har ya isa harabar makarantar.

Ɗaliban dake dan zirga zirga ya zurawa idanu kan ya sauke numfashi ya buɗe motan ya fito, en mata dayawa da kallo suka bishi yana tafiyanshi cikin ginshira da mazantaka dogon bafulani ne sossai har ya ɗan rankwafa, da sauri drivernta ya isa gareshi ya fara kwasar gaisuwa a mutunci ya amsa kan kaman ba ze ce komai ba se kuma yace

"bata fito ba ko?"

"Eh nima nayi mamaki don muna daga cikin na biyu zuwa uku masu fita a makarantar nan da zaran an tashi zaka ganta yanzu kuma har an kusa watsewa gabaɗaya"

"ka je kawai"
Ya faɗa yana nufan ciki ba tare da ya jira amsar drivern ba, wasu en Junior class ne da suke tsaye daga gefe ɗaya tace
"chab yau akwai kura Aisha Isma'il ta doke Maryam Usman hmm"

Ɗayar tace
"Ni tausayinta nake ji yadda Maryam nan suka saka ta a gaba karfi da yaji take rayuwa ita kaɗai a makarantar nan tun da ta shigo bata taɓa sakewa ba"

Wata tace
"ke ai in Maryam Usman ta zama senior kowa a makarantar nan ya shiga uku, ni har tsoron zuwa SS1 nake lokacin na san suna 2"

Duk cikin harshen turanci suke magana, wacce kaman dama ita suke jira da isowarta gangansu kenan tace
"aiko ga ta chan ma sun tare ta bayan halls"

Idanunshi ya bi inda ta nuna da hannu, tun kiran sunan Aisha Isma'il da suka yi be kara gaba ba be kara baya ba, sede ya fiddo wayanshi ya zuba mata idanu yana sauraransu, hanyar da yaga ta nuna ya bi baze ce ga yadda yake ji a lokacin ba se da ya hangi sun ture ta ta faɗi da karfi, runtse idanunshi yayi ya buɗe duk sun sauya gabaɗaya, be yi hanzari wurin nufarsu ba se ya tsaya ya shiga camera ya soma recording ɗin su.

Ranshi be gama tafasa ba seda yaga ta karya glasses din nan da take ta roƙonsu akan kar su karya mata, maida wayan yayi aljihu ya nufe su daidai tana laluɓen glass ɗin ta Buge goshinta duk yadda yaso ya tare ta kan hakan ya faru be yiwu ba, jikinshi har rawa yake sbd yadda Ranshi yayi masifar ɓaci baze taɓa cewa a rayuwar shi gabaɗaya an taɓa ɓata mishi rai kaman na yau ba...

"Please help me!"
Ta sake maimaitawa tana Laluɓa hannunta me lafiyan ta inda take zaton inuwar mutum ne, hannun da ta faɗi a kai ya kama a hankali ya kurawa idanu daga wrist ɗinta Dukda shi ba likitan ƙashi bane amma ya fahimci babu tantama ta samu gocewar ƙashi a wurin, haƙori ya sa ya taune ƙasan lips ɗin shi ya ɗaga idanu ya kalli fuskanta se jujjuya idanun take jini na bin fuskan nata ta inda goshinta ya fashe.

"Ina ruwanka da sh....."

Wani irin gigitacciyar marin da ya hautsina hangin cikinsu har ita Aysher da bata gani ya sakarwa Maryam, seda ta zube a ƙasa tayi zaman yan bori numfashinta ya bar jikinta na tsawon mintuna kan ta fisgo da karfi har lokacin wasu irin taurari take gani a sama, controlling kanshi yake amma suna so se sun ga ainihin side na Fulaninshi, Ranshi yayi masifar ɓaci da har ji yake in numfashi ya fita daga kirjinshi baya dawowa ya ma kasa magana...

Hannunta me lafiyan yake shirin kamawa tayi saurin ja baya jikinta na rawan tsoronshi don tunda marin ya sauka babu wadda ya iya motsi a cikin su su huɗun...
"Zan tsinka miki mari kika sake matsawa..!"

Ya furta cikin Muryar da ya bayyana tsantsar bacin Ranshi, se a lokacin ta fara analyzing Muryar, Dukda kamshin jini take ji amma hancinta seda ya zuƙo mata kamshin turarensa, gabanta ne ya faɗi, yaushe Abba ya dawo? Cikin rawan murya tace

"A...Abbaa"
Be amsa ba se hannunta da ya riƙe zasu bar wurin ba fa wai don an gama bane rikicin yanzu ya soma, jinin dake zuba mata a Goshi yake son wanke mata.

"Meke faruwa anan ne?"

Principal da suka taho da manyan malaman makarantar ya faɗa, dama a ka'idar makarantar malamai basa tafiya se sun tabbatar da babu dalibin da ya rage a makarantar, kuma se sun yi zagaye sun gama tabbatar da komai intact kan principal ke sallamansu.

Da idanunshi da gabaɗaya suka birkice ya kallesu gabaɗayansu, se kuma ya juya da hannunshi wadda ke free ya nuna su Maryam da har yanzu zaune take a ƙasa mufida da Amina na sangame a tsaye

"you should make sure among them babu wacce ta bar makarantar nan, and you all also"
Yayi maganan kaman yana cikin asibitinshi ne da ya san kowa na karkashin ikonshi, ba neman izini ya basu ba umarni da gargadi ne ke tafe cikin Muryar shi, be sake cewa komai ba ya juya yana riƙe da hannunta gudun kar ta faɗi suka nufi inda ya ajiye motan shi, mazauninshi ya buɗe wato driver seat ya zaunar da ita, ya miƙa hannunshi ya ɗauko savage ya soma goge mata jinin fuskanta da har ya diddiga a uniform ɗinta, ruwa ya sa a tafin hannunshi ya wanke mata fuskan ya fiddo fari kal din hankey ya sa mata a hannunta me lafiya

"share fuskan"

A hankali ta share, duk gashin gaban goshinta ya sake mammanewa, hannu ya sa a aljihu ya ciro wani Brown cover na glass me azababben kyau ya buɗe, se ga rantsatsen glass kwance a ciki frame ɗin Light peach ne da fari fari yayi matukar kyau ya fiddo ya sanya mata a ido, lokaci ɗaya fuskanshi ya bayyana mata tar seda ta tsorata ganin yadda fuskar nan tashi ke a ɗaure, Dukda yadda yake ji ya ga kyaun da glass ɗin yayi mata dama kuma ya raya hakan sbd a wani shopping da suka fita da Naina ya ga frame ɗin ɗauke da lence ɗin shi sede ba medicated ba, be bari Naina ta ga sadda ya saya ba sbd ya san fitinarta, asibitin ya kai da yake ranar da ya kaita asibiti tana mp ya ga number ɗin lens din nata so kawai faɗa musu yayi ga abunda yake so a yanka a sa a frame ɗin.

A yau da zasu taho ya tsaya asibitin ya karɓa ya sa a aljihu shine be cire ba se yanzu.

"Why??"
Ya tambaya yana kallonta da idanunshin nan da be ɓoye zafin da zuciyarshi ke ciki ba.

Muryarta na rawa idanunta na sake cika da hawaye tace
"Kayi haƙuri Abba, tsoro na ji... Ina tsoron kar daga zuwana in fara baka matsala da ciwon kai, sannan su ɗin sun fi ƙarfina in ka duba tazarar matsayi dake tsakanin....."

"Enough pls!"
Ya faɗa da ɗan tsawa, da sauri ta matsa baya hawayen da suka cika idanunta suka soma gangara, hannunshi ya sa ya murza goshinshi tare da sakin dogon tsaki me sauti.

Ji yake kaman ya mammaketa itama ko ze huce kaɗan.
"Me kike nufi? Da nace zan zama tamkar mahaifi a gare ki na karɓi amanar ki kina tunanin akwai wani wadda ze iya sake ɗaga miki yatsa in kyale? Karki kuskura ki sake haɗa matsayin ki da na yaran nan saboda ko ta ina basu kai ki ba bare su kamo ki har su zarta ki"

Cije lip dinshi na kasa yayi.
"Next time irin haka ta faru baki faɗamin ba har na gane ke zan soma sassaɓawa.. Mu je"
Ya juya, da sauri ta fito ta rufe motar jikinta har rawan tsoro yake yadda yake faɗan kaman ze maretan itama.

"Show me the principal's office"
Yace yana kallonta, da yatsa tayi saurin nuna mishi arean yayi gaba ta bishi a baya idanunta cike da tsoron abunda ze faru.

Kaman yadda ya faɗa ɗin kuwa suna nan zazzaune suna jiranshi don tambayar duniya sun yiwa su Maryam babu wacce ta iya cewa komai, tsoro ne da razani cike da idanunsu, rashin gaskiya baro baro ya bayyana a fuskokinsu.

"Ta ina zamu fara? Ku zan yi ƙara ko iyayensu?"
Yayi maganan daga tsaye ba tare da ya zauna ba cikin harshen turanci.

"Yallaɓai da dae ka zauna mun ji Duka sides of the story sbd har yanzu mu bamu san Meke faruwa ba, su kuma basu ce komai ba"
V.p ya faɗa cike da girmamawa da suke dashi ga guardians din students nasu.

Zama yayi HM ya ɗauko mai ruwan sanyi a frigde ɗin Principal ɗin ya bashi, karɓa yayi ya sha sossai kan ya ajiye, a natse ya faɗa musu duk abunda ya faru ya kuma fiddo video din a matsayin shaida, gabaɗayansu sun girgiza sam basu san abu haka na faruwa a cikin makarantar ba, hakuri suka soma bashi a take yace be san shi ba, ya birkice musu da kyar ya hakura gobe a dawo in yaso za'a kira iyayensu se a haɗu gabaɗaya.

Daga makarantar asibiti ya nufa da ita, Dr Safwan ya kira wanda shine yake kula da duk abunda ya shafi harkar ƙashi a asibitin ya tabbatar mai yana office kai tsaye nan suka yada zango, da sauri ya miƙe tsaye ganin shugabansu ne da kanshi a cikin office ɗin nashi yau Dukda ya kan yi ziyarar bazata sbd masu wasa da aiki amma Dukda haka ya ɗan tsorata kaɗan don ya san prof Emran bashi da sauƙi.

"Sir ai da ka kira ni se in sameka ka zo nan da kan ka?"

"Dr daughter na ce ta samu ɗan problem a hannu nake so ka duba mata"
Yayi maganan yana zama.

Daga tsayen da take ta gaishe da Dr Safwan ɗin tana kallon kwarangwal dake jejjere daban daban a kan desk ɗin nashi.
Amsawa yayi yana zagayawa ya isa gareta
"mu ga hannun?"

Miƙa mishi tayi ya duba, Dukda yayi tunanin gaucewar ƙashin ne amma sbd gudun laifi yasa ya kaita wurin xray yayi mata cikin minti biyar ya fito ya duba, aiko dae gocewar ne ze yi gyara.

"Zaki ɗan daure don ze miki zafi"

Kanta ta gyaɗa duk tsoro ya cika ranta, runtse idanu tayi da karfi jin ya fara kokarin gyarawa seda kuwa tayi kuka, likitan na murmushi yace
"babba dake ɗan wannan kike yiwa kuka?"

"Allah ba ɗa bane Dr."
Bata san ta faɗi hakan ba ma, tana kallon hannun  a lokaci ɗaya tana share hawayen fuskanta, har ya zagaye da farin bandage bayan ya shafa wani abu kaman mai, kallon Abban nata tayi idanunshi na kan wayanshi, be ɗago ba seda Dr Safwan yace
"ranka ya dade an gama, ba wani abu in shaa Allah"

Tsam ya miƙe yana mika mishi hannu
"thank you Dr"
Yana faɗan haka ya juya ya fice tabi bayanshi, office nashi ya shiga ta bishi anan ya fidda First aid yayi mata dressing na goshinta, in ya kawo Cotton me ɗauke da spirit ya ɗan manna tace "shhhh" se ya dankara mata Harara haka zata tsaya sbd tsoro har suka gama.

Lokacin har an yi la'asar seda yaje yayi sallah a masallacin asibitin kan ya dawo suka tafi, yunwa take ji kaman taci babu, tana Allah allah ya tsaya ya saya musu don ta san kila yanzu kam gidanshi suka nufa ba gidan Alhj ba, kaman kuwa ya ji ya tsaya restuarant ya saya musu abinci, har sun bar wurin ma Naina ta kirashi, da Bluetooth na motan ya amsa cikin Muryar shin nan yace

"ya aka yi ne?"
"Ƙalau hun, ina kayi haka tunda muka dawo baka shiga ko cikin gida ba"

"nace ya aka yi?"
Ya sake maimaita maganan shi na fari ba tare da ya bata amsar tambayar tata ba.

"Eyyaaa in zaka dawo yanzu pls baby na craving KFC kitchen ka biya ka samo min"

Sun kusa isa ma a sadda tayi kiran amma be ce komai ba bayan Ok, ya juya akalar motan ɗan kallonshi Aysher tayi yunwa take ji wlh, gashi yanzu yamma ya soman nan holdup na garin in ya rikesu taya zasu koma har ta ci abinci ta cire wannan uniform da take ji ya takurata, baki ta ɗan turo tana sake kallonshi se suka haɗa idanu...

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba
0545475847
Gt bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰



                          🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

FREE PAGE 14

*Albishirinku💃 Toh gobe Free Page ze ƙare in shaa Allahu wacce bata saya ba kuma tana son jin yadda zata kaya a gidan Abba se ta garzayo ta saya*

"Raki kam kin ƙware a kai amma baki iya kwatan kanki a faɗa ba, ɗauki abincin ki ci"
Ya faɗa a fuske kaman ba shi yayi maganan ba.
Murmushi ta saki tana mamakin hallayyar Abban nata, kaman me gani har hanji, juyawa tayi ta ɗauko, tint ne motar kuma ba zata iya hakuri har su koma ba ga holdups ya fara, abincinta take ci hankalin ta kwance sbd ko ta inda take ma Abban baya kallo se waya da ya kan amsa, kan su je KFC ta gama ledar na ajiye kan kafafunta, seda ya buɗe motan ya fita kan ya miƙa hannu ya ɗauki ledan ya rufe motar tana kallonshi ya cillar a bin kan yayi ciki, wani murmushin ta kuma saki.

Babu wanda ya sake magana har suka iso gida, shi ya kwashi ledojin don tayi niyyar ɗauka ya hanata, da sallama ta shiga parlorn Naina tayi saurin tasowa sede ganin Aysher ne yasa ta dakata tana kallonta sama da kasa, ita har ga Allah ta ma mance da wanzuwar yarinyar

"Ina yini Aunty Naina? Kun dawo lafiya?"
Ta faɗa cikin girmamawa.

Tsaki ta ɗan ja kan tace
"lfy" shima sbd zura mata idanu da Emran yayi ne, ledojin ta karɓa don tana ji kaman ana yasa a cikinta, be zauna ba yabi bayan Aysher don shiga ɗakinshi ya watsa ruwa kan Magrib, daidai zata shiga ɗaki yace

"Yau 27 in case kin ji wani ciwo makamancin na wanchan watan don't seat alone by yourself in pain, hope am clear?".

Da sauri ta amsa kanta ƙasa ta kuma shige daki lokaci ɗaya, a jikin kofa ta tsaya ita har ta ma mance wlh cikin dabara ta zare uniform din ta ta shiga wanka sauri sauri sbd sallahn da bata yi ba, Sharp Sharp ta fito tayi rama Sallar da ake binta anan ta kwanta sbd ta gaji sossai, bata wani jima ba aka yi Magrib ta miƙe ta gabatar ta ɗan yi karatun alqur'ani yau ko malaminta kila ya zo ya gaji da zama ya tafi be ganta ba, bayan tayi isha ta miƙe ta ɗan saka turare kan ta zura kayan bacci, farin doguwar riga wacce tsawon ta daidai sharabarta be ida isa idon sawu ba ta kwanta...

Washegari da safe seda ta shiga bayin ta ga uniform ɗin ta a bucket bazata iya wankewa ba sbd hannunta kuma bata da wani a gidan yana gidan Ammi, alwala tayi ta zo tayi Sallar asuba sbd yunwar da take ji ta haɗa tea ta sha da biscuit, bayan ta gama taje tayi wanka ta zo ta shirya cikin riga A shape na atampha da ya mugun amsar ta, bazata iya dauri ba ko gashin bata sake taje shi ba sbd hannunta ta ɗauko gyale da ya shiga da kayan ta yafa daga kanta, zama tayi tana tunanin abunda ka iya faruwa a makaranta yau sbd ta lura Abba bashi da sauƙi sam idan ranshi ya ɓaci...

Jiya sossai ya tuna mata da baffanta, duk sanyinshi a kan yaranshi shi wuta ne, Dukda be san komai ba ya kare ta ya bata goyon baya, hannunta ta sa ta shafa glasses din da yayi mata kyau a ido sossai tana ɗan murmushi lallai Abba na da taste me kyau kaman ya san zata buƙata a lokacin ya taho dashi shi da be taɓa ma zuwa makarantar ba ma...

Kanta ta sunkuyar tuna abunda ya faɗa na karshe kan ta shiga ɗaki, ko date ɗin watanta be mance ba, kunyar hakan ya lullube ta...

Knocking da aka yi ne ya sakata saurin Miƙewa taje ta buɗe kofan, yana tsaye hannunshi ɗaya a aljihun three quater fari sol dake jikinshi ya hadata da baƙar shirt marar nauyi.
"Ina kwana
Showing 33001 words to 36000 words out of 38960 words