"Aunty Asma'u Don Allah ki koyamin yadda ake anfani da wannan"
Ta Nuna gas ɗin ta faɗa ne sbd ta gaji da cimar da take samu tana missing abubuwan su na ruga kuma shi take so amma bata iya anfani da abun ba tana kuma tsoro shiyasa bata yi kiriniya ba..
"Kinga har na manta kuma wlh Ya Murad ce min yayi in zo in koya miki sbd ki samu abunda zaki ke ci na san matar gidan ba girki ta iya ba, ina ma izzarta ze barta shiga kitchen"
Ita dae Aysher bata ce komai ba.
A hankali Asma'u ke koya mata, kunna gas ita dae taga wani abu kaman bindiga kuma wai ashana se jujjuya shi take, bayan nan ta nuna mata ɗayar da ba se da ashana ake kunna shi ba kana murdawa ze kawo wuta, se suka ɗaura ruwan zafi, locker locker take buɗewa tana nuna mata abubuwa se mamaki take chan tace
"Auntyna yanzu da ba'a dafawa basa ɓaci?"
"Ruɓewa kai sede a zubar, shiyasa lokaci lokaci ze sa a turo ma'aikatan gidanmu su kwashe ya saka sabbi ke farkon auren su fa har shinkafar garar Aunty Naina ya zama gari basu buɗe buhun ba, kina taɓawa ze wargaje sbd ajiya"
Murmushi kawai Aysher tayi amma zuciyarta fal mamaki, shinkafar tuwo suka fitar ba wani tsinta suka wanke suka zuba cikin ruwan da suka ɗaura suka ɗan sa muciya suka juya kan suka rufe, komawa gaban frigde na kitchen ɗin suka yi, Buɗewar ma da yake ba normal bane seda Asma'u ta nuna mata frozen chicken, fish, beef gasu nan birjik se kayan miya babu abunda babu a gyare suke tsab cikin ziplock daban daban sun kankare har dusa dusa suke.
Kaza Asma'u ta fiddo ta sa a cikin bowl da ta sanya Aysher ɗaukowa ta ajiye kan ta zari ziplock ɗaɗɗaya ta dibi kayan miyan da zata buƙata, suka koma gaban blinder wadda na buchimix ne a hankali ta nuna mata yadda ake anfani dashi, ita kuwa tana dauka a kanta tace
"kai na gode Auntyna kinga yanzu zan yi duk abunda na san zan iya ci"
Murmushi Asma'u tayi tace
"kin ma yi kokari ai sati guda kina nan kina ta kame kame duk kin rame".
Dariya Aysher tayi tace
"ba fa kame kame Abba yana kawo min abinci"
"da ke da Abban duk kuna cikin wani hali"
Tayi maganan cikin alhini wadda ya sa Aysher sakin dariya.
Ɗaya frigde din da suka buɗe kayan madara madaran kamfanin Alhaji ne jibge se Aysher taji sha'awar shan nono me ɗauke da dakkere.
"Auntyna akwai turmi kuwa?"
neman turmi suka fara da kyar suka samu, Ayusher ta koma inda taga hatsi a robobi masu kyau ta dibi gero, ta baya suka fita bayan Asma'u ta sa kazar da ta fiddo ta sa mishi spices ta ɗaura kan dayan gas ɗin, ruwa take zubawa kadan kadan cikin geron tana surfa shi har ya surfu, a bakin pampon bayan suka wanke shi tas suka rairaye duk wani ƙasa dake tare dashi, ta ɗan baza shi suka koma kitchen tuwon Asma'u ta bar mata ta tuke ita kuma ta komawa kazar, ta zazzare ƙashin tas kan ta zuba mishi ruwa da manja ta sake wani haɗi da daddawa tayi adjusting seasoning din kan ta rufe ta dawo wurin Aysher tana nuna mata yadda ake kulla tuwo a leda don ta tambaye ta tace duk abincin da ake kawo mata in tuwo ne se ta ganshi a ƙulle a leda ya ake yi? Shine take koya mata.
Bayan sun gama tace
"bari na duba gero na in ya sha in daka"
"kaii wani irin daka kuma ga fa buchimix blender dutse ne kaɗai ba zaki markade a ciki ba, komai yana yi"
Cikin rashin amincewa tace
"dakan hannu ai yafi daaɗi"
Ita dae Asma'u bata ga wani bambanci ba haka ta bita suka koma ba wani yawa kuma abunka da wadda ya riga ya saba a take ta dake shi ya zama gari suka tankade suka koma kitchen.
Lokacin Miyar ta gama nuna yadda ya kamata sbd sirrin kuka na cikin nunar shi, kaɗawa da whisk Asma'u tayi be yi kauri ba yayi daidai se kamshi yake, namar kazar yayi daga daga a cikinshi, ta kwashe a ɗan namiyar kular da suka zuba tuwo.
A bincikensu suka samu gammo irin na kaba ɗin nan da Fulani kan yi, kila ma daga cikin kayayyakin kyautar en uwa su na kauye ne suka kawowa matar yayan da alama ko sanin anfanin shi bata yi ba, harda kwarya me ɗan girma da fai-fai da ludayi na asali, wankewa Aysher tayi don duk yayi kura tunda ba anfani ake dashi ba taje ta buɗe frigde se ta tsaya tunani.
Asma'u tace
"matsa je ki murje dakkeren don ni ban iya ba bari na fiddo madarar da naga Ammi na hadawa idan zata yiwa Alhaji kawai dae nashi ba masu sugar bane"
Komawa tayi ga garin geron in ta baɗa ruwa se ta murza ta murza ta ɗaga kwaryar ta kaɗa shi tsakiyar hannunta take yake shure wa a hankali hankali tana fiddawa har ya ƙare, Asma'u se kallon ta take, lallai yarinyar ta samu horo me kyau don tana da tsabta, dama Ammi kan ce mata in ta ganta tayi wani abu Fulani ba'a san su da kazanta ba, bata tabbatar ba se yanzu ji wannan daga Ruga take amma tsabtar ta wanda ma yayi karatu ba lallai yana dashi ba anan, a steamer Asma'u ta saka musu shima tana nuna mata yadda ake har ya dahu, madarar ta zuba kala har uku a cikin kwaryar kan suka zuba dakkeren, Asma'u ta ɗauko kankara ta zuba da sugar kaɗan ta kara flavour ɗan kaɗan take ya bada wani kamshi na musamman.
Se zumudin son sha Aysher ke yi Asma'u ta hanata suka kwashe komai suka kai dining, suka dawo suka gyara kitchen din fes kaman yadda suka same shi, kan suka koma dining din kofi da cokali Aysher ta ɗauka taje ta dibi damammiyar nonon.
"Yanzu ba zaki bari ki fara cin abinci ba?"
Shagwaɓe fuska tayi tace
"Ni dae se na sha damimmayar Nono tukuna in iya cin wani abu, a andi no mi wairi kuje ɗo(kin san yadda nayi kewar abin nan kuwa? Hmmm)
Tana soma zubawa aka dannan door Bell, Asma'u dake cin tuwonta tace
"ɗiyarmu duba kofar nan"
"To Aunty Asmy bari na gama zubawa"
Se dariya Asma'u ke mata kaman ze gudu?
Seda kuwa ta gama zubawa ta sa cokali tayi tasting tana lumshe idanu kan ta nufi kofar rike da kofi da spoon din ta.
A hankali ya fara sauke idanunshi bisa kofin da take ta kaɗa cokali a cikinshi kan ya ɗago zuwa dogon wuyanta dake bayyane, ɗauke idanun yayi ya mayar fuskanta da yayi fayau, murmushi ta sakar mishi a bazata, ɗauke kanshi yayi tare da lasar lip ɗin shi yana jin zazzakar muryarta na cewa
"Abba sannu da dawo..."
Bata ƙarasa ba sbd Naina da ta fito ta bayanshi ta hankade ta a bazata tuni tayi baya zuwa ƙasa kofinta ya hantsila ya zube mata a jiki daga wuyanta zuwa kan kirjinta, sanyin ya ratsa ta wadda a take ta lumshe idanu ta fara hawaye sbd ta matukar firgita.....
*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*
Zaki iya biya ta wannan akawun lamba
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰
🖤Gureenjoh🖤
RUBUTU A KAN RUWA
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*
*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏
*Aleesha collection*
''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?"
"a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata''
''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi''
Hajiya ta zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar mai gida ko saurayi kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai sauki ke ma ki je ki nemi na ki.
Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944
Sai kun zo
FREE PAGE 7
"Naina? Ya subhallah! Are u out of ur sense me wannan?"
Ya faɗa yana shiga cikin parlorn, Asma'u da ta kara so wurin tayi saurin duƙawa tana taɓo Ayshern jin tayi shiru kaman wacce ta suma ko wani abu taji Nainan na cewa
"Yes, am out my sense tunda idanunka sun rufe, yarinya ba gidan ta ba na ubanta ba muzo mu tsaya muna danna door Bell sama da mintuna biyar har ka koma ka ɗauko keys naka daga car da ka bari kan ta wani zo ta buɗe kuma ta tsaya akan hanya, akan dalilin me? Tana da gadon gidan ne ko da kuɗin babanta aka haɗa aka gina?"
Juyawa tayi kan Aysher da Asma'u ta ɗago ta, tana aika mata wani banzan kallo tace
"Mayya kawai"
Daga haka ta ja tsaki tayi wucewarta
Dafe goshinshi yayi ya ɗan murza kan ya ja tsaki, idanunshi akan Aysher da ta share hawayen fuskanta ya ɗan kalli wuyanta da duk Damammiyar nonon ya ɓata ya ɗauke kai yace
"Je ki wanke jikinki"
Asma'u haushi ne ya zo mata har wuya, shikenan abunda ze ce? Ji fa maganganun da matarshi ta gama faɗa, dama sun san ba iya tsawatar mata yake ba amma kuma ai wannan wulakanci ne, cikin Muryar kuka Aysher tace
"Kayi haƙuri"
Kan ta juya ta nufi ɗakin ta, tausayinta ne ya kama Asma'u, ita ya kamata a ba hakuri amma shi take bai wa.
Ɗauke idanunshi yayi daga kallonta bayan ta rufe kofar ya sauke kan nonon dake zube yace
"Ammi ne ta aiko ki dashi?"
Ta san yadda yake matukar so, kuma duk sadda ze shiga gida se ya sha na Alhaji idan Ammi tayi, kusan abunda kaɗai yake sha a kofar Ammi kenan don na Hajiya baya mishi daaɗin na Ammi.
"Aysher ce tayi"
Sake kallon Nonon yayi se ya nufi dining inda yaga kwanoni.
Asma'u kuma ta soma gyara wurin, bubbude kulolin yayi, baze iya cewa ga sadda yaga kuloli haka akan dining ɗin gidanshi ba, kai be ma taɓa gani ba sbd abubuwan da yake dafawa daga kwai, doya, dankali se ɗan spaghetti su kuma daga tukunya se plate ne, amarcinsu ma ba a Nigeria suka ci ba shiyasa ba'a aiko musu da abinci ba, sannan Asma'u ma baze ce ta taɓa zuwa gidan nashi tayi ko mintuna goma bane ze iya kirga sau nawa tazo amma yanzu yadda ya gantan nan ya san ta jima kuma me yiwuwa ita tayi girkin.
Dama yunwa yake ji banda coffee daya sha a office tun safe be ci komai ba gashi yanzu almost to 3, don yana sauƙa Juma'a Naina ta kirashi akan motar ta ya tsaya shine ya biya ya ɗauko ta suka barwa machanic motar.
Zama yayi yana jiran Asma'u, bayan ta gama gyara wurin tazo ta soma zuba mishi abincin, a ranta tana raya eh ai mune kake yiwa muzurai, idan kaganmu a wuri ko Hajiya sede tayi serving naka amma idan bama nan kana iya shiga kitchen ka girka ka kaiwa wata katuwa har kan gado, kaman ta ja tsaki amma ta san halin shi baya so kwata kwata a ja mishi tsaki nace Toh wanzami baya son jarfa akwai wadda yskai shi jan tsaki kuwa? Ai ko tsaka ya sara mishi.
Nonon ta zuba mai a wani bowl me garai garai ta tura mishi ta zauna ta cigaba da cin abincinta, a nan ne ta gaishe shi ya amsa yana cin abincin da cokali.
"Tun yaushe kike nan?"
"Tun 12:30 nazo, na kawowa Aysher ɗinkunanta shine ta roƙi na koya mata anfani da abubuwan kitchen nan"
Kai ya gyaɗa, tuwon ya ture Dukda yayi daaɗi sossai ya janyo bowl din ya fara shan furar, wow ko na Ammi se haka ko da shike baze yi mamaki ba Fulanin ruga ce.
"Aysher kam lafiya? Duk zumudin shan Nonon kuma ya tafi ne?"
Ta faɗa tana Miƙewa bayan ta gama cin abincin jin shiru shiru Ayshern bata fito ba.
Ya shanye wadda ta saka mishi har ya kara be ce mata komai ba har ta wuce ɗakin Ayshern, a kwance ta sameta sanye da plain riga Onion Colour har ƙasa, daidai cikinta ya kama se ya sake daga kasa.
"Aysher kwanciya kika yi? Abincin fa?"
"He'i am Aunty Asmy(ya isheni)"
"wani irin ya isheki me kika ci da ze ishe ki? Tashi oya mu wuce ki ci abinci"
Duk yadda ta so ƙi haka Asma'u ta sakata a gaba se tace tana tsoron ta sake laifi bazata fita ba se duk sun shige.
Taɓe baki Asma'u tayi ta fice taje ta zuba mata abincin ta sake zuba mata furar yana kallonta be ce komai ba ta wuce zuwa ɗakin Ayshern.
Basu suka fito ba se dab magarib da Asma'u zata wuce, kaman kar ta tafi haka Aysher taji don sun sha hira har class na fulatanci suka yi, ita kuma Asma'u ta koya mata assignments dinta na biology da physics, har mota ta raka ta, dubawa tayi ta ɗauko choculates ta mika mata tace
"ɗiyarmu a sha wannan kuma kar ayi kuka"
Dariya Aysher ta saki itama Asma'u tayi dariya tana cewa
"ko kefa da kin yi wani kicin kicin da fuska, yauwa ga Big bro din nan ma"
Ta faɗa tana kallon shi yana tahowa da alama yayi alwala don gyara hannun tsadaddiyar shadda dake jikinshi yake.
"Dama tafiya zaki yi ba sallama?"
Ya faɗa yana kallon Asma'un.
"Big bro na kira line naka be shiga ba, ɗiyarmu kuma na tsoron matar Abbanta ta ƙi zuwa ta maka magana"
Kallon Aysher yayi da kyawawan idanunshi masu girma da suke a lumshe, ta bata fuska sbd abunda Asma'u ke cewa kaman zata yi kuka, ya maida kallonshi kan Asma'u yace
"ke kuma da yake gidan baƙon ki ne ko?"
Ya ƙarasa yana mika mata bunch din 1k yace
"Ki gaida su Ammi"
Tunda ya faɗi hakan ta san yau kila be samu ya shiga gidan bane, godiya ta mishi ya wuce abunshi. Aysher na riƙe da choculates ɗin ta har Asma'u ta fice kan ta dawo ta shige ɗakinta.
Washegari da wuri ta tashi sbd dokin yin girki, dama haka take inde zata yi girki tayi ta ɗoki kenan, kitchen ta wuce bayan tayi brush tana nazarin abunda zata girka, tas ta bubbude lockers din ta ja baya har da sa hannu a haba tana gyara glass dinta da ya karawa fuskarta kyau.
Cikin sassanyar muryarta tace
"Ina son kunu amma ba kamu, ko nayi Basise ne?"
Basise wani nauyin kunu ne da mutanen yola ko Taraba ke yi da danyen shinkafa na tuwo, kai ta gyaɗa cike da gamsuwa ta dibi gyaɗa markadadde daga gani ta san markaden yola ne sbd sune suke yinshi yayi tililis mai ya kwanta me yawa a samanshi kaman kayi ta lasa kuma duk jimawar da ze yi baya lalacewa sbd wannan mai kuma an soya gyaɗar sama sama.
Tacewa tayi ta zuba a tukunya, a wurin kunna gas din kuwa seda aka yi da gaske sbd tsoro irin nata, bayan ta kunna ta ɗaura tukunyar taje ta dibi shinkafa rabin cup ta wanke ta ajiye, tsamiya ta jiƙa a cup kan ta fara tunanin mahaɗar kunun nata, nan ta yanke yin ƙosai, wake ta diba ta surfe ta wanke ta haɗa da atturugu da albasa ta sa a buchimix blender din da Antynta ta tabbatar mata komai yana nikawa, a take ta markade yayi tilis ta juye a roba, da gudu ta koma wurin gyadarta ganin ya kusa zuba ta juye shinkafar ta tsaya tayi ta motsawa na mintuna kan ta ajiye ludayin ta koma ta buga kosan sossai.
Tana yi tana dawowa ta duba kunun seda shinkafar ya nuna tilis ta kashe gas ɗin kan ta zuba ruwan tsamiyarta ta ta kara juyawa ta zuba sugar ta sauke, a wani madaidaicin jug me garai garai ta juye sbd shi baya son flask ze dafu sossai yayi kauri shiyasa ta barshi a jug, komawa tayi ta fara suyan ƙosan cikin annashuwa take komai.
Iskar bakin shi yake hurawa wadda ke fitowa da zufa sbd gudun da yake yi na motsa jiki, wuyanshi maƙale da karamin towel, daga kanshi head Phone ne me kyau, riga marar hannu ne jikinsa wadda ya fidda murdaddun damatsansa alamar be ɗauki motsa jiki da wasa ba, dogon wandon Puma ne jikinshi se rufaffun takalma duka baƙake, sun yi nasarar fito da kyakyawar skin ɗin sa fari kal, kwantaccen sajenshi se digar zufa suke har cikin tattausan gashin kansa duk da haka wani masifaffen kamshi yake fitarwa..
Tsagaita jogging ɗin yayi ya buɗe parlorn ya shiga, ko kan ya kai tsakiya ya tsaya chak yana nazarin kamshin da ya cike parlorn wadda babu tantama daga kitchen yake fitowa, ko ba'a faɗa ba ya san Aysher
Showing 15001 words to 18000 words out of 38960 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6 Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13