da akwatinta ta shiga parlorn, zaune Asma'u take tana kallon wani series, ɗan ɗagowa tayi ta kalleta ta maida kanta kan Tv ɗin ta bayan ta amsa sallamar, wani irin sanyi jikin Aysher yayi ta ƙaraso ta zauna tare da cewa
"Aunty Asmy ina yini?"

Ba tare da ta kalleta ba tace
"Lafiya"

Anan Aysher ta ci gaba da zama har tsakiyar ranta bata ji daaɗin hakan ba amma ya zata yi? Bata san wani hanya zata bi wurin fahimtar da ita cewa bazata ma iya auren Naufal ba ko da tana son shi kuwa sbd Auntyn nata ta wuce hakan a wurin ta.

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰



                          🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

FREE PAGE 12



"Asma'u ya zaki barta da kaya anan parlor ko uniform bata cire ba bare ayi zancen cin abinci?"
Ammi dake shigowa ta faɗa.

Miƙewa Asma'u tayi tace
"muje Aysher"
Itama ta miƙe dauke da kayanta suka haura, ɗakin dake gefen nata ta buɗe mata, a tare suka shiga Aysher ta ajiye akwatin tayi saurin Juyowa jin Asma'u na shirin fita tace
"Aunty Asmy!"
Dakatawa tayi ba tare da ta juyo ba, daga bayanta Aysha ta tsaya idanunta na cika da kwalla tace

"Kiyi haƙuri don Allah, ke kaɗai ce nake samun sanyi a wurinki a kab garin nan, kece kika fara amsata da hannu bibbiyu ba tare da kyama ko kyara ba idan kika yi fushi dani kika kyaleni ba zan taɓa jin daaɗi ba, wlh ba abunda kike zato bane tsakanina da Ya Naufal, ko karen hauka ne ya cije ni ba zan iya amsawa wanda kike so da ƙauna soyayya ba ko da kuwa zan mutu ne bare ma wlh babu ko ɗigon son shi a raina, kaman yadda na ɗauki Abbana uba haka dukkanku kuke iyaye a gare ni, don Allah kiyi haƙuri"
Ta karashe da kuka da ta kasa controlling..

Asma'u ma da nata hawayen ya gangara ta runtse idanu tana tuna rashin hankalin da tayi, bata san Meyasa tayi pouring out fushin da ya kamata tayi da Naufal akan Aysher ba tunda shine ya nuna interest a kan Ayshan ba ita ce ta nuna tana yin shi ba, sannan ko da hakan ne ma ita ai me iya sadaukarwa Aysher Naufal ne sbd har ƙasan ranta Allah ya dasa mata kaunar yarinyar..

"Ni ce ya kamata in baki haƙuri Aysher ba ke ba, baki min laifin komai ba, zuciya ne kawai da sheɗan se kuma borin kunyar son maso wani da na jima ina yi ba tare da na san shi ba hakan bace a wurinshi..."
Idanunta dake zubar da kwalla sossai ta ɗaga sama

"ba zan hana ki son shi ba in har dae yana daga cikin irin mazan da kike so da burin aure, don Allah a duk sadda ya kawo miki kokon bararshi ki yi min alfarma kar ki ƙi, dukkanku ina son ku da alkhairi"

Da sauri Aysher ta girgiza kai
"ba zan iya ba, ya ma fi ƙarfina Aunty Asmy, ba fa zan iya ba kiyi hakuri mu bar maganan nan ni karatu zan yi"

Ajiyar zuciya Asma'u ta sauke kan ta juyo tana ɗan murmushin yaƙe
"je kiyi wanka ki sauko ki ci abincin kar Abbanki ya yanka min sammacin barin ɗiyar shi da yunwa"
Murmushi Aysher ta saki cikin jin daaɗi ta fara cire uniform din jikinta.

Bayan tayi wanka ta sauya kaya ta sauƙa ƙasan a nan ta ɗibi abinci ta zauna suna kallon wani hausa film da Asma'un lokaci lokaci su kan yi magana, har bayan la'asar suna nan kaman yadda Aysher bata sallah haka ta lura Asma'un ma, seda Ammi ta zo don shiga kitchen suka miƙe suka bi bayanta, a tare da ita suka yi girkin gida da na Alhaji wadda tuwon dawa ce da Miyar kuka da yaji man shanu, basu bar kitchen ɗin ba se Magrib, duk kowa ɗakinshi yayi, ita kam Aysher tana shiga azkar ta hau yi bayan ta gama ta kwanta cikin tunanin ko su Abba sun isa lafiya? Gashi bata da waya bare ta kirashi taji...

Miƙewa tayi ta fito tana shirin yiwa Asma'u knocking se gata ta fito
"ɗiyarmu ya aka yi ne?"

Cikin jin daaɗin yadda Asma'un ta koma mata kaman da ta ce
"Aunty Asmy ko kin kira Abba kin ji sun isa lafiya?"

Murmushi Asma'u ta saki tace
"sun isa lafiya ya kira Ammi, anjima se in kirashi ku gaisa tunda har kin fara kewar su"
Dariya kawai tayi ba tare da tace komai ba.

"Yauwa ya jikinki? Me yake damun ki daman?"
Asma'u ta faɗa suna sauka downstairs
"ciwon ciki, wlh na ɗauka mutuwa zan yi ai duk son da kika koya min na choculates na hakura dashi na rage sbd Abba ya ce shine ya janyo"

Dariya Asma'u tayi sossai tana cewa
"Allah sarki sannu ko, ba zaki mutu ba in shaa Allah se buruka sun cika, amma dama yana miki ne shan choculates ɗin ya ƙara shi?"

"Ban taɓa yi ba ma se wannan"
Ta faɗa tana jin kunya, da mamaki Asma'u da har ta fara zuba musu abinci ta kalleta lallai tayi delay, parlor suka dawo suka ci abincin a tare suna hira bayan isha suka yi wurin Hajiya ta fi Ammi sakewa da hira anan suka yi ta hirar ruga da abubuwan cikinta wanda duk suka yi kewa.

Misalin karfe tara na dare wayan Hajiya yayi ringing ta ɗaga da sallama se kuma fuskanta ya washe da fara'a tana ambaton sunan Emran
"Alhamdulillah kun sauƙa lafiya dae kam?"

Ta ɗan yi shiru kan tace
"masha Allah, ina Nainan ina mata sannu da hanya"

Shiru ta ɗan yi se ta sake cewa
"gasu nan ma muna ta hira dasu"

"Asma'u karɓi"
Ta faɗa tana miƙawa Asma'un waya.

A ladabce ta gaishe shi, bayan nan ta ɗan yi shiru se kuma lokaci lokaci take cewa to ko in shaa Allahu.
Se kuma ta kalli Aysher don kaman tambayarta yayi.

"Gata nan, dama dazu ta gama tambayata ko mun yi waya kun sauƙa lafiya!"
Ta faɗa tana miƙa mata wayar.

Karɓa tayi cikin yanayin sanyin ta ta saka wayan a kunne tare da sallama, shima ya amsa ba tare da ta bari yayi magana ba ta fara gaisheshi
"Alhamdulillah"
Shine amsar da ya bata se kuma ya ɗaura da
"Ga Asma'u nan duk abunda kike buƙata ki faɗa mata zata kirani ta sanarmin, na manta da safe ban baki pocket money ba na sanya mata a account ɗin ta zata cire ta baki, ayi karatu a kuma kula"

Kanta na ƙasa kaman tana gabanshi tace
"in shaa Allahu, Na gode Allah ya saka da alkhairi Abba ya bada sa'ar abunda aka je nema"

Chan ƙasa ya amsa da Ameen tare da yanke wayar, saukewa tayi ta bi da kallo se ta saki ɗan murmushi kan ta miƙawa Hajiya da suka cigaba da hirarsu da Asma'u.

Ganin tana ta hamma ne ga gobe akwai school yasa suka yiwa hajiyar sallama suka nufi part ɗin Ammi, a hankali Asma'u tace
"Ni kam ɗiyarmu ko kin san idan wannan jinin ya ɗauke akwai wankan da ake yi nashi na daban?"

Kanta ta ɗan sunkuyar kan tace
"Eh Aunty Asma'u an koyar damu a cikin fiqhu"

"Kinga faɗamin yadda ake in ma kin mance wani wuri se in tuna miki don fa Abbanki yace in tabbatar kin iya yadda addini ya koyar"

"innalillahi....Abban ne yace hakan?"
Tayi maganan kaman zata saki kuka wadda ya saka Asma'u kwashewa da dariya, tana ta kwaɓe fuska wai ita kunya ta faɗawa Asma'u yadda ake yin daki daki ta kuwa iya ɗin babu wani kuskure.

"Masha Allah kin yi kokari, yanzu je ki kwanta sbd school kar ki makara Abbanki yace baya son hirar banza da wofi"

Murmushi kawai tayi tace
"Toh se da safe"

"Allah ya bamu alkhairi"

Haka ta cigaba da rayuwa a gidan, zata iya cewa gidan ya fi mata chan gidan sau dubu saboda tana samun yin hira da mutane kuma a sake take babu me mata kallon kyara ko tsangwama se ma janyota jiki, Ammi kullum se ta bata kudin break Dukda ta faɗa mata Abba ya bata kuma suna nan bata kashewa sossai se tace ta kara, idan weekend ne ba zuwa makaranta ta kan raka Asma'u unguwa in zata fita irin wurin Ƙawayenta ko Saloon ko kuma kasuwa, ta fannin girki sossai take sake koyan irin na zamani a gidan sbd in har tana nan bata taɓa zama a yi girki ba ita, tana nan ciki ta kan tambaye su abunda bata sani ba ko bata gane ba.

Ta fannin assignments ma bata wani shan wahala Aunty Asmyn ke koya mata in aka basu, ga Ya Murad da kullum dare tare suke hiransu ya kan kuma sayo musu kayan makulashe su rage dare dashi, bata daddara ba ko in ce ta mance ne oho choculates kam suna sha kaman ba gobe da Asma'u don ita ma gwanar zaƙi ce.

A kwana a tashi seda ta shafe sati uku curr a gidan, har kuma lokacin Su Abban basu dawo ba kuma bata sake waya dashi ba tun wayan da suka yi randa suka isa, yau ya kama Litinin cikin sauri sauri ta sauko sbd letti da ta ɗan yi wurin shiri ta isa gaban dining ta duƙa ta gaida Ammi, fuskanta a sake ta amsa ta tana cewa
"jiya ba kin biye wa Asma'u kuka raba dare kuna hira ba gata chan tana bacci suna hutu ke kin makara zaki je a zane ki a banza"

Kanta ta duƙar tana ɗan murmushi ba tare da tace komai ba
"tashi maza ki ci abinci ki samu ki wuce"

Sharp Sharp ta ci farin doya da kuli da aka yi wadda yaji man hannu da albasa tana ci tana haɗawa da tea bayan ta gama ta miƙe tana rataya school bag tace
"Ammi na tafi"

"Allah ya tsare se kin dawo"

Da gudu gudu ta fice ta shiga mota tana gaida driver ɗin su ya amsa kaman kullum kan suka fice zuwa makarantar.

Yau ake fidda sakamakon kuri'a da aka yi na face of the school, so bayan an yi period uku na farko ba'a sake komawa aji har a tashi, za'a tafi students hall a sanar a kuma ɗauki gwarzuwan hotuna da uniform ɗinta yadda za'a wanke su manya manya a manna a halls da gaban gate din makarantar.

Bata wani ci abun kirki ba a break sbd har lokacin tana jin cikinta a cike yake daman doya ba dae riƙe ciki ba, kai tsaye daga cafteria hannunta rike da Fanta na gwangwani da ta saya bata ma bude ba aka buga seniors suka fara koran yara zuwa students hall, zama suka yiyyi, malamai biyu ne a stage din mace da namiji, bayan sun zauna suka sake Miƙewa suka miƙa musu gaisuwa, suka amsa Muryar namijin radau sbd shine yake riƙe da mic ɗin, bayan ya basu umarnin zama suka zauna.

Cikin harshen turanci ya fara magana
"kaman yadda kuka sani kuma muka saba, duk farkon session muna yin wannan gasa ta face of school, wannan shekarar ma bata sauya zani ba ranar Juma'a an yi zaɓe mun tara kuri'u na duka Junior and senior section kaman yadda kuka sani babu wanda makaranta ta cire a wannana gaasa ko ɗan js1 ne yaci lallai lallai shi ko ita za'a ba wa, Toh dae Alhamdulillah mun samu mun kirga kuri'u a weekend yau a yanzu kuma zaku ji sakamako"

Kowa sai ya juya ya kalli Maryam dake ta kanainaya Allah kaɗai ya san kuɗin da tayi ta kwasa daga ɗakin daddynta tana zuwa tana kashewa ɗalibai don ta saye su su zaɓe ta, ta saka buri da hope ɗin ta akan wannan karon ma ita ce zata ci babu tantama har ta gama ba za'a tsige hoton ta a fuskan makarantar ba, se murmushi take.

Kashe wutan hall ɗin aka yi aka bar dim Light se na stage kawai, gyaran murya malamar da ta karɓa tayi ta sake gaishe da ɗalibai kan tace
"So the one with the hightest vote among the selected students of year is....!"
Se ta ɗan yi shiru kan da karfi tace
"Aysher Isma'il!!!!"

Sowaa me karfi hall ɗin ya ɗauka a sadda spot Light ya dallare Aysher dake zaune rike da Fanta a hannunta, ita har ga Allah tsorata ma tayi hakan yasa manyan idanunta kara girma da haske se sheki suke yi, Maryam Usman da taji abun kaman sauƙar aradu tayi saurin Miƙewa tsaye tana dafe kirji nasara abu ne me matukar muhimmanci a gareta kaman yadda mahaifinta kan kwaɗaitar mata a koyaushe a komai a kuma ko ina ta kasance me kwato nasara ko ta halin yaya, bata san ta rikice ba seda kawarta mufida Umar ta janyota ta zaunar da ita
"natsu mana baki ga kowa kallonki yake ba?"

Murya na rawa tace
"yarinyar nan tayi nasarar karya min record Mufida I'm screwed daddy ya samu labari kam na gama kaɗewa!"

"Aysher Isma'il come over" da Aunty Doris ke ta maimaitawa ne yasa ta Miƙewa tana sake damke fantar hannunta, hantar cikinta se kaɗawa yake in ta tuna Maryam daga gefe, har ga Allah abunda yasa take bari suke mata abunda suka yi niyya banbancin matsayi ne, su ƴaƴan masu dashi ne ita kuma ba ƴar kowa ba.

Kunna wutan hall ɗin aka yi dallllll a sadda ta hau stage ɗin, Allah ya sa ma ita ɗin me tsabta ce uniform ɗinta kal kal gashi sabo don kwata kwata wata na biyu kenan suke ciki a makarantar don suna shirin 2nd C.A test ne kuma ba ya wuce sati tsakaninshi da revision se exams da compilation, kayanta ya sha karin guga, gashinta dake gyare sbd Saloon da suka je da weekend da Aunty Asmeey se sheki yake gyaran da aka mata wannan karon raba gashin gida biyu aka yi se aka kwantar akan goshinta ya koma baya, yayi lublub tun tana kunyar zuwa makarantar haka har ta saba.

Murmushin da malaman suke mata da kuma sowar ɗaliban ya bata kwarin gwiwar sakin murmushi me kyau wadda ya bayyana dimples ɗinta duk biyu da fararen hakwaran ta farare suka bayyana, nan me hoton ya matso ya fara ɗaukarta kala kala se murmushi take saki.

Haka taron ya tashi kusan lokacin tashin su so wasu sun fara tafiya wasu ko na ɗan tattaunawa tsakanin juna, a hankali ta ratsa ta bayan classes bayan ta koma ta ɗauki text book ɗinta na physics da ta bari a locker ɗinta, kanta ƙasa take tafiya se ji tayi an bangajeta da karfi ta tafi duk yadda tayi kokarin balancing bata iya tsayawa ba seda ta kai ƙasa hannunta ya saki ƙara sbd faɗi da tayi a kai, glases ɗin ta ya faɗi chan wani waje, idanunta ta runtse da matukar karfi tana jin yadda zafin yake ratsa ilahirin jikinta.

"Dama tun da na ɗaura idanuna a kanki Naji na tsane ki No wonder ashe da dalili ni aka turo ki ki dakushewa rayuwa! Miƙe tsaye in ga abunda kika fini dashi"
Maryam Usman Ta faɗa tana Buge kafafunta dake miƙe da kafanta.

Laluɓe ta fara da hannunta ɗaya a hankali ta soma cewa
"taimakeni da glases ɗina bana iya gani se dashi don Allah"

Dariya suka kwashe dashi su ukun Mufida Umar tace
"Ashe ma makauniya aka baiwa face of school ɗin? Chabbdi yo to ai da sake"

Amina bamanga tace
"dole kuwa asiri ya tonu duk kyaunta in ba ido ai babu kyaun, ke kin tashi ko se mun miki laga laga?"

Hawaye ne ya gangaro daga kurmin idanunta zuwa kan fuskanta
"Me nayi muku don Allah? Me na tsare muku da zafi haka?"

Su kam banda teasing ɗinta da suka fara babu abunda suke, ji da tayi Maryam Usman na cewa
"wannan kike nema makauniya? Gashinan ƙasan kafata zan take shi in ga yadda zaki yi ki tafi gida yau"

"don Allah karki karya min glasses, shine abu na karshe da na mallaka a wannan gari wadda baffana ya saya min da guminshi, ina son abuna karki karyami..."

Kararass haka karan karya glass ɗin ya karade kunnenta idanunta ta runtse tana kokarin isa inda taji karan ta Buge goshinta a jikin wani karfe take shima ya fashe ya fara jini.

A hankali taji an saka hannu biyu a kafaɗunta an ɗago ta, se kawai ta riƙe rigan mutumin da bata tantance waye bane sede yanayin jikin ya tabbatar mata da namiji ne tace cikin rawan lips

"Please help me!"

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰



🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA
 
بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

FREE PAGE 13

*am very busy ayi min uzuri🙏*

Zaune yake a kan three seater kafafunshi a miƙe a ƙasa, Naina na kwance tayi matashin kai da cinyarshi tana bacci cikin natsuwa, operating Phone ɗin shi yake yana wani ɗan research ne ma da wayar, se ya tsaya chak da dannar wayan, a hankali ya fita daga inda yake ya koma calender watan na 25, fita yayi kawai ya shiga App din da yake booking flights a take ya musu booking na me tashi 27 tunda sun riga sun gama duk abunda ya kawo su an yi IVF ɗin kuma komai normal.

IVF shine conception da ake yi a waje a sanyawa mace a mahaifa amma ba da kwayoyin wasu ba da nata da na mijinta hakan kuma ba haramun bane, shafa fuskanta yayi tayi a hankali har ta buɗe idanunta dake cike da bacci ta kalleshi
"Its time for prayer, ki soma shiri zamu wuce jibi da safe"

A hankali ta miƙe zaune sossai take jin daaɗin hutun sbd kulawar da yake bata na musamman ne babu inda
Showing 30001 words to 33000 words out of 38960 words