da alamar roƙo
"ke rabani da ya Emran, baki san baya son wuce gona da iri a abunda ya shafe shi ba ko? Balle ma ko na kaiki family house Auta bata nan tana school itama"

Bata ji daaɗi ba kuma shirun gidan ne bata so, wani shopping mall suka tsaya a tare suka shiga ya duba mata school bag da sandals da wasu socks duk tayi mamakin kudinsu Dukda kyaunsu kaɗai ya isa ya sa ka san zasu yi tsada ba irin na kauyensu ba, ba'a maganar Rugarsu don ba kasuwa bane dasu a chan, kayan tea ya saya se suka zaga wurin kwanoni waenda yawancin su na fashewa ne a cikin glass glass ya saya mugs guda uku ko wanne da ɗan plate ɗin daurawarshi a kwali aka basu ba wadda ya nuna ɗin ba, se kuma taga ya saya mata bottles har biyu masu kyau pink da blue.

Yana parking gaban wani hadadden gidan abinci ya ce
"Yaya yace baki karya ba in sama miki wani abu yana sauri ne yana da theater da safen, Meyasa ba zaki shiga kitchen ki samarwa kanki abunda zaki ci ba?"
Ya faɗi hakan ne sanin cewa babu wadda be san Naina bata iya komai a harkar kitchen ba, Yayansu kuma ya tsani me aiki kuma haka suke rayuwarsu a cewar shi tunda yana son matarshi ya wadatar ba ruwan kowa da sha'anin gidan shi.

"Abubuwan ne ban iya anfani dasu ba"
Ta faɗa cikin gurɓatacciyar hausar ta.

"Zan faɗawa Auta ta samu lokaci tazo ta kokkoya miki kin ji ƴar Fulani?"
Ya faɗa yana kwashe kayayayyakin tana taya shi da wasu suka yi cikin gida fuskarta dauke da dariyar tsokanarshi.

Har ɗakinta ya ajiye mata kan ya mata sallama ya fice, arranging komai tayi ta kara gyara ɗakin kan ta buɗe abincin da suka saya din shinkafa ce da miya me kaza se plantain, ta ci ta koshi kan ta kwanta ta sha baccin ta, ba ita ta farka ba se azahar tayi sallah ta zauna a wurin babu wani abunda zata yi ga shirun yayi yawa se ta faɗa tunanin Rugarsu da Baffanta Allah sarki duk daaɗin wuri babu kaman gida, kuka tayi tayi kaman wacce aka dake ta seda taji ya isheta kan tayi shiru.

Anan ta kwanta kan sallayar ta sake bacci se la'asar ta farka tayi sallah, tana nan zaune taji knocking.

Miƙewa tayi taje ta buɗe hannunta na ƙasan glasses dinta tana kaikaya idanunta dake radadi sbd kukan da tayi dazu, ganin shine yasa ta gaishe shi ya amsa yana ɗan kallonta har kaman ze yi maganar anan se kuma yace
"zo"

Ya juya tabi bayanshi har cikin parlor, a kujera ya zauna ta samu wuri daga ƙasa ta zauna yace
"ya kuka yi a makarantar?"
Dukda yaji komai daga wurin Murad sede tausayinta ne ya ɗan tsarga mai ganin tayi kuka ya kuma san zama shirun nan ne da bata iya ba yake damunta, zaman gidansu se su, matarshi in ba office ba to bacci shima kuma ba zama yake ba yo to ko zaman ma yake ina ya iya dogon surutu?

Nan ta fara bashi labarin yadda suka yi daga fitar su har dawowarsu harta kara da ko ta ɗauko mai uniform din ya gani? Yace ta bari, suka dan yi shiru kan yace
"me yasa kika yi kuka? An miki wani abu ne?"
Da sauri ta girgiza kai tana mamakin yadda ya sani
"u know ur condition right? Ko kina so ki makance gabaɗaya ki kasa cika burinki da na mahaifinki?"
Nan ma ta girgiza kai da sauri
"words pls"
Tace
"A'a" cikin sanyin murya
"Good kar in kara gani kin yi kuka, karɓi"
Ya faɗa yana miƙo mata bunch daya na 1k Miƙewa tayi taje ta karɓa tana mamakin abunda zata yi dashi.
Shiru yayi na mintuna har kusan biyar kan a hankali kaman me kirgen words yace
"Na sa an saya miki kayan tea ne saboda ki dinga karyawa dashi da safe, kudin nan u should use it kina break dashi a makaranta in ya kare se ki faɗamin"

Jujjuya kuɗin tayi, a Rugarsu in tayi tsanani ne Baffa ya basu Ashirin na break amma ina zata kai wannan ita? Kuma harda in ya kare tayi magana? Godiya tayi mishi sossai da Adu'a ya amsa da "Ameen"
Kan ya miƙe ya nufi ciki har ya kusa barin parlorn ya tsaya tare da Juyowa
"Ki dinga fitowa parlor atleast zaki kalli ko Tv ne"
Har ta gyaɗa kai se kuma ta yi saurin cewa
"Toh"
Ya juya ya shige.

Bata tashi ba se ta fara kallon tvn, tana nan zaune har aka magarib ta miƙe kenan don shiga ɗaki shima ya fito ba tare da yayi magana ba ya fice da alama masallaci za shi, ita ɗaki ta wuce taje tayi alwala tazo ta yi sallah anan ta zauna har aka yi isha ta gabatar kan tayi shirin kwanciya, choculates taci ta sha ruwa tayi baccin ta abunta.

Da sassafe ta gama shirin ta saide ta kasa fita a haka barin ma gashinta dake reto a bayanta wani iri take ji Dukda nata socks ɗin yana da kauri sossai kuma har gwiwarta, wardrobe din ta ta buɗe ta duba hula fari ta cusa gashinta a ciki se ya zamana gaban goshinta ya ɗan fito gashin ya kwanta a wurin yayi lub, fitowa tayi bayan ta sha tea, a parlor ta same shi yana tsaye Naina na tsaye daga gefenshi sanye cikin wasu peach suits na mata da yayi matukar amsar ta kanta karamin gyale ne ta ɗan yafa, takalmin kafanta kuwa ya kai 5inches a tsawo White kaman yadda gyalen kanta ma White ne haka fashion ear rings din ta ma White ne, wow matar ba laifi ta iya ɗaukar wanka ta ayyana a ranta kan ta gaishe su cikin girmamawa, shine kaɗai ya amsa Naina kam ko ta tanka.

Ɗan kallonta yayi from head to toe, Naina ma ta kare mata kallo tana ayyana yadda uniform ɗin ya karɓi yarinyar yayi mata kyau ainun, ɗauke kanshi yayi yace
"kin karya?"
"Eh na sha tea"
"akwai driver a waje he will drop u"

Da sauri ta fice bayan tace mishi ta gode sbd mugun kallon da Naina ke aika mata, tsaki taja tace
"Don Allah dae akan maganan mu pls pls"
"kin san dae ba zan bar aiki in tafi wata kasa na tsawon kwanaki ba ko?"
"Sbd buƙatuwar mu zaka iya mana, its something that would help us all"
Ɗan pecking goshinta yayi yana sa hannu a kumatunta ya ɗan shafa tare da jan iska yana sanya lip din shi na ƙasa a baki na seconds kan ya saki yace
"Babe lets talk in mun dawo Ok?"

Idanunta da ta ɗan lumshe ta buɗe tare da gyaɗa kai ya riko hannunta suka fito, har lokacin su Aysher basu tafi ba, tsayawa yayi yana tambayar drivern ya? Yace yana sa ruwa ne a motan kaman ze yi maganan Meyasa be yi da wuri ba kuma se ya fasa ya juya ga Naina da ta kalli motar da ya bayar don kai yarinyar makaranta na seconds wata Camry ce 2020 edition, ɗauke kai tayi ta buɗe tsadaddiyar motar ta ta shiga tana daga mishi hannu seda yaga fitan ta kan shima ya shiga nashi Black BMW a kusan tare motocinsu ya fice.

Ko da suka isa makarantar godiya ta yiwa drivern tayi office na principal kaman yadda ya faɗa mata a jiya in ta zo nan zata je, ta gaishe shi ya amsa, kan ya kira wata malama a waya cikin mintuna ta zo yace
"Miss Veronica this is ur New student Aysher Isma'il pls introduce her to the class"

"Ok sir" ta faɗa kan ta dubi Aysher tace su tafi, a baya ta bita har ajin nasu single single seat ne a ajin amma suna da ɗan yawa don zasu iya yin ashirin da biyar, a gaban class ɗin ta tsaya suka miƙe suka gaishe ta bayan ta amsa ta basu izinin zama suka zauna kan ta faɗa musu ta kawo musu sabuwar class memeber ne hope zasu karbeta hannu bibbiyu, suka amsa kan tace Aisha ta gaya musu sunanta da kanta, tana ɗan ɗari-ɗari ta faɗa, seat ta nuna mata daga gefen Windows amma be mannu da Windows ba sbd wucewan malami tace ga seat ɗinta ta zauna, zuwa tayi ta ajiye Jakarta ta zauna nervously.

Cikin awa ɗaya da rabi da tayi a ajin malamai uku sun shiga sun fita, maths, biology da kuma physics bata wani fahimci abunda suka yi din ba don fa ba'a fara term din da ita ba so an ɗan wuce ta amma dae ta maida hankali, tana nan zaune bayan shuɗewar awa da rabin tana ta kallon dalibai dake shiga da fice ana ta hidiman break, wasu yan mata uku suka zo suka tsaya a kanta, ɗaya na gefe tace
"Ina faɗa miki yanzu duk ajin nan zasu daena ganin kyaunki se na wannan, Allah ya sa ma bata da ilimi don Abun se ya miki yawa, har muka kare jenior ba'a samu wacce ta fiki kyau ba se anan?"

Ɗaya dake ɗayan gefen kaman tana cikin alhini tace
"hmmm akwai aiki Maryam"
"ya isheni haka!"
Ta daka tsawa cikin masifa tana sake karewa Aysher kallo cikin tsananin jin haushi.

Ita dae kallonsu kawai take har suka tafi fuu, me abun fushi don wani ya fi ka kyau kuma Allah na? Ta tambayi kanta sede babu me bata amsa, Miƙewa tayi ta fice daga class ɗin a hanya ta tsayar da wata tana mata tambay la da Hausa, yarinyar tace cikin harshen turanci
"in an kama ki kina hausa u r dead"
Hannunta ta ja ta kaita cafteria ta saki ta juya ta tafi.

Meatpie ɗaya ta saya da Nutri milk bata kashe dari bakwai me kyau ba ta ajiye chanjin ta ci ta sha kan tayi class ganin an buga yara na ta gudu don shiga azuzuwansu, Miss Veronica ce ta shigo.

Har ta fara english se wadda aka kira Maryam dazu ta ɗaga hannu, Miss vero ta bata damar magana
"Miss vero ina ba'a amince da saka komai a kai ba a wannan makaranta?"

"Yes dear"
Miss vero ta amsa
"then Miss is that girl different? Me ma sunanta Aysher Abi Fatima?"
Tayi maganan cikin izgili.
Miss vero ta dubi Aysher tace ta cire abun kantan, zaro ido tayi se tayi ta yawo kai banza a makarantar??
"I Said remove the cap in ur head Aysher.."

Duk aka zuba mata idanu ganin ta fara hawaye se Maryam da kawayenta ko in ce yan gidan ta suka kwashe da dariya har da tafawa...

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰



                         🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA


بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*

*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏

*Aleesha collection*
''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?"
"a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata''
''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi''
Hajiya ta zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar mai gida ko saurayi kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai sauki ke ma ki je ki nemi na ki.
Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944
Sai kun zo

FREE PAGE 6

A hankali ta kai hannunta ta fara zame hular sbd kama kanta da yayi garin zarewa ta haɗa har da ƴar karamar ribbon da ta kama gashin dashi tuni gashinta ya baje yana yauƙi shi kaɗai kaman haɗin baki Ƴan ajin suka yi ihun
"wooooow"
Da sauri Aysher ta zare ribbon din ta sake fara kokarin kama gashin idanunta cike da hawaye, Maryam dake kallonta ranta ya sake baƙi kirin ina ma ace yarinyar bata da gashi da sun sha dariya, ta tsani competition se gashi ta samu wacce daga zuwanta ta tsole mata idanu, makarantar suna da wani ɗabi'u na turawa kaman contesting na model of the school, face of the school, festivals, field trip da dai sauransu.
Su kan zabi face of school ko model ne daga js 1 har Ss3 za'a fidda mutum ɗaɗɗaya, in an samu six a cikin wannan six ɗinne za'a fidda ɗaya ayi mata picture da uniform kala kala a mammana a duk hallway na makarantar, ita ce wannan kambu ke hannunta be taɓa fita ba amma ga dukkan alama wannan yarinyar zata kawo mata cikas cikin al'amura yadda take ganinta wata goddess of beauty.

Ita dai Aysher tana nan zaune tana kallon malamai don kallo zata ce sbd yadda gabaɗaya take tsarge ba wani mai da hankali take ba har aka tashi karfe ɗaya da minti ashirin, cafteria ta koma ta sake sayan snacks ta nufi inda aka tanada don ajiye motoci a nan ta samu driver ɗin da ya kawota ta buɗe ta shiga tana gaishe shi, shima gaishe ta yayi suka nufi gida.

Se dare ya kawo mata abinci tayi godiya, haka rayuwarta ya cigaba da tafiya abunda ya chanza shine zuwan malamin dake mata islamic da yamma hakan ya rage mata kaɗaici, kuma ba laifi tana kokarin ganin tayi picking karatun, kan sati ya ƙare ta ɗan yi rama sbd matsalar Maryam ta zame mata bully, har aikenta suke cikin izgili da raini, har wani tsoron Maryam din ne ya shige ta na masifa ko muryarta taji se jikinta ya hau rawa, hakan ya samu tasiri ne sanin cewa duk wadda ta gani a makarantar ta san ɗan wani ne saɓanin ita da alfarma taci har Allah ya kawota nan ɗin, sannan tana da zurfin ciki shiyasa bazata iya faɗawa kowa ba to yo ko ta so faɗa din ma wa zata sanarwa? Babu.

Yau Jumma'a tunda suka tashi daga school ta dawo gidan tana kwance idanunta a lumshe ko uniform bata cire ba, banda hawaye babu abunda take sbd irin fusgan gashinta da su Maryam suka dinga yi a chan baya wurin garbage na makarantar, ta aike ta shawarma taje ta kawo shine wai Meyasa ta sayi me Sausage bata san bata ci ba, suka dinga gayamata maganganu marasa daaɗi har da fisge mata gashi, wani irin sarawa kanta ke yi..

Buɗe kofar ɗakin taji an yi da sauri ta share hawayenta tare da Miƙewa zaune, a take ta saki murmushi ta sauƙa da wuri taje ta rungume Asma'u
"Aunty Asmy sannu da zuwa"

"yauwa ɗiyarmu, me ya faru na ganki so silent haka? Yanzu ko uniform baki cire ba tunda kika dawo?"
Asma'u ta faɗa tana zama bakin gadon ta ɗakin kal kal, itama zama tayi tana cewa a hankali cikin hausarta
"Kaina ne ke ciwo shine na ɗan kwanta ko ze lafa"

"sannu ɗiyarmu, baki sha magani ba?"

Kai ta gyaɗa ina zata ga wani magani yau kwananta uku daga matar har mijin bata sanya kowa a ido ba, driver ɗin dake kaita school dae kan kawo mata abincin dare bata san wa yake sanya shi ba.

"Akwai firt aid a kitchen ai muje ki sha maza... Tsaya ma ke ga fa dinkunan ki nan ya gama kinga yadda suka yi kyau?"
Ta faɗa tana fiddo kayayyakin daga cikin leda, da sauri Aysher ta fara dagawa tana yaba kyaun su gaskiya yayi kokari, wani batik Red nd peach ta ɗaga ya zuba mata adon Red lace a jiki sannan an yi mata tail kaman me zuwa dinner haka, fitted ne ya mugun yi mata kyau tace

"kai Auntyna bari nayi wanka na sa wannan gaskiya ya min kyau"
Dariya Asma'u tayi tace
"ciwon kai har ya ware kenan ana ta santin kaya"
Murmushi kawai tayi ta shige toilet wanka tayi tana feeling sulɓin skin ɗin ta sbd yadda take samun kulawa na Mayuka da abubuwan wanka, ramarta kuwa bayanna kyaun surarta ya kara, hancin ta ya kara tsawo idanunta suka kara girma, a gaban madubi ta zauna tana shafa ƙasan gashinta da scalp din yayi Red sbd fusgan da ya sha.

Wani abu me zafi ta haɗiye kan ta shafa mai tana kallon Asma'u dake zaune tana ta dannan waya, bayan ta gama ta fesa turare ta ɗauki rigar ta saka wow wow wow, ita kanta ta yaba da yadda yayi mata mugun kyau, barin ma da ta kama gashinta sako sako ta ɗaura dankwalin daga gaban gashin baya da gaban goshinta dake kwance lublub ya bayyana.

"Auntyna!"
Ta Kira Asma'u da hankalinta ke kan waya, ɗagowa tayi se ta zaro idanu
"wooooow i got a fine daughter, ke kinga yadda ya miki kyau? Yanzu muje ki sha magani"
Miƙewa tayi suka fito suka shiga kitchen, First aid ta ɗauko ta duba pcm ta bata ta kuma ce mata ko gaba zata ji wani ciwo akwai magani anan
Showing 12001 words to 15000 words out of 38960 words