Tayi saurin faɗa tana ɗan duƙawa, hannunta ya kalla yace
"Lafiya ya jiki?"
"Da sauƙi Babu komai"
Yana kallon goshinta yace
"kije kitchen ki ɗauki abinci, where is ur uniform kika sa personal?"
"Na jiya ya ɓaci kuma ba zan iya wankewa ba, sauran kuma suna gidan Ammi"
Ta faɗa cikin sanyin muryarta.
Kai ya gyaɗa ya juya ya wuce, fita tayi zuwa kitchen ɗin, doya ce fari ya dafa da faɗi fadi yayi egg sauce.
"Abban nan na nan kaman hawainiya, babu kalar da baya iya zama"
Tayi maganan a fili tana zuba abincin, a nan kitchen ɗin ta zauna ta ci ta koshi kan ta fito parlor tana rike da ruwan faro, se gashi shima ya fito a shirye cikin grey suit da farin ƴar ciki, ba karamin kyau yyi ba, hannunshi riƙe da briefcase ɗayan na ɗan gyara bakin nectie ɗin shi yace
"mu je"
Bayanshi ta bi, yanzu wannan wai har wasan kasa fa yayi da baffanta, to ya aka yi baffanta ya fishi tsufa? Dukda ba wai baffan tsoho bane sede bazaka haɗa shi da Abba ba, komai nashi daban, kai hatta murjewan skin ko Murad dake matashi me jini baze nuna mishi komai ba, da wannan tunani suka mota, ya mata wuta suka fice, be tsaya ko ina ba se harabar makarantar tasu kai tsaye suka dangana da office na principal.
Shi da mahaifin Amina suka samu se wasu authorities na makarantar, a hankali ta kai idanunta kan fuskanshi ya murtuke fuskan alamar ba wasa, hannu ya miƙa musu daya bayan ɗaya kan ya zauna itama ta zauna nan ƙasan rug din kaman yadda Amina ke zaune, mahaifin Mufida da ita ne suka shigo tana sanye da uniform, kaman yadda Amina ke sanye da uniform saɓanin Aysher, daga karshe mahaifin Maryam ne suka shigo a tare, babban ɗan siyasa ne da kowa ya sani me mukami don dasu ake damawa a ƙasar, renon da yayiwa yaranshi shine be san faɗuwa ba a komai yana so su kasance masu nasara hakan ysa yaran basu damu da wa zasu taka ba wurin kaiwa ga nasarar tasu wanda dae dae yake da faɗuwa warwas.
Da Adu'a aka fara kan aka baiwa Aysher damar faɗan duk abunda ya faru, turancinta be nuna ba kaman na su se ta kasa magana, kallon Abban tayi ya gyaɗa mata kai, kokarin soma magana tayi amma da ɗari-ɗari kuma ɗaɗɗaya take fidda kalaman gudun kwafsi, ta kuma yi kokari sossai wadda wasu a ciki ke ganin rigima da iyayi ne yasa take maganan a haka, Maryam V.p ya kalla yace
"Maryam Usman an yi haka?"
Kallon mahaifinta tayi a tsorace ta gyaɗa kai.
"Mufida, Amina Meyasa kuka musgunawa Aisha? Ta muku wani abu ne?"
Principal ya tmbya
Suka girgiza kai
Tsawa v.p academic ya daka musu
"baku da baki ne ana magana kuna kallon mutane?"
"Bata mana komai ba"
Mahaifin Mufida ne yace
"Ashe ke shashace? Yar uwar ki mace mufida ita kika ciwa zarafi? Shine da na tambaye ki kika ce baki san dalilin nema na da makaranta suke ba? Zaki yi bayani"
Mahaifin Amina ma faɗa ya rufe ta dashi sossai kaman ze daketa, shi dae Abba be ce komai ba banda kallonsu da yake.
Mahaifin Maryam yace
"toh tunda dae abu ya riga ya faru faɗa ko maida zance bashi da amfani ai yara ne, duk shiriritarsu be kamata ana kaiwa zuci ba bare har a kai ga saka hannu jikin ƴar da ba'a san zafinta ba"
Kallon shi Emran yayi se ya ɗan murmusa yace
"daaɗin abun ƴa ai bata fi ƴa ba, tunda kuma babu wanda ze ci kashi a cikinsu ai zancen yara be taso ba, yanzu dae ba wannan ba ina jiran jin an kwatarwa tawa ɗiyar hakkin ta"
Ya faɗa yana directing maganan to principal.
"Bisa laifin da aka same su dashi a gaskiya idan ita bata hakura ba, to hukuncin Maryam shine kora daga makaranta su kuma mufida da Amina za'a basu suspension na sati uku uku"
"saboda kawai faɗan yara? Akan hakan zaku kore ta? Kun ma san wanene ni kuwa da kuke zancen korin ƴa ta daga makaranta?"
"Ko waye kai baka fi karfin doka tayi aiki a kanka ba, penalties din ma yayi sauƙi idan da ta nine we are going to court and they could definately pay a fine or even end up in jail depending yadda shari'a tazo"
Kallon Dr Emran kawai Alhj usman ke yi, yadda yake gayamishi magana kai tsaye yayi matukar bashi mamaki, be gama mamaki ba seda ya ga principal yayi printing expulsion letter yayi signing aka bawa Maryam da ta soma kuka, mufida da Amina kuwa aka basu suspension, ita dae Aisha in ba don mugun kallon da Abban ya mata ba ta so tace ta yafe musu a barsu a makarantarsu tunda ita ta zo ta same su.
Mahaifin Maryam se faɗa yake harda in ya ga dama bazata yi karatu a Nigeria ba ma, makarantar banza makarantar wofi.
Emran dae murmushi ya mishi wanda kai tsaye yake nufin wannan matsalar ka ce...
Murɗawar da mararta yayi ne yasa tayi saurin duƙar da kai tana runtse ido, to fa wannan abu haka ze ta mata? A take gumi ya soma tsatsafo mata a Goshi, ko hakurin da malaman da kuma iyayen mufida da Amina suka yi ta basu ita ba ji take ba, ta de san mahaifin Maryam ya jima da ficewa kuma itama ta bi bayanshi.
Idanunshi ya sakar mata na mintuna kan Tsam ya miƙe
"Allah ya kiyaye gaba, Aysher?"
Ɗagowa tayi idanunta har sun chanza kala
"mu je" ya faɗa chan ƙasan makoshi.
Sallama yayiwa malaman suna ta kara bashi hakuri shi kam hankalin shi na kanta, a dudduke ta isa motan ta haɗa kai da gwiwa.
"Sorry"
Ya faɗa cikin kulawa yana tada motar be tsaya ko ina ba se asibiti, Dr Hafsa ya kira tun kan su isa, a office ɗin shi tayi mata allura, kaman wanchan karon shi ya fita ya nema mata pad, da ya dawo tayi bacci zama suka yi da Dr Hafsa yana tambayarta yadda za'a yi ta samu sauƙi sbd be kamata kowani wata ta sha wannan wahalar ba.
Bayani ta mishi mata kala kala ne, kila in tayi aure ta daena kila kuma in ta haihu, amma saukinta a daena wannan allura tayi ta amfani da lipton me zafi da kayan kamshi da kuma lemon sannan ta koyi amfani da ruwan zafi a mararta daga ta soma jin alama, ya tabbatar mata in ta farka ze tura ta se tayi mata duk bayanin da ya kamata tare da mata godiya, Miƙewa tayi ta fice tana mamakin shi ita bata san haka boss ɗin nasu yake ba sam, ji shi so simple and caring.
Da ta farka yau ma a bayi ta gyara Kanta Allah ma ya sa bata ɓaci ba tukuna, abinci ta gani kan table ta ɗauka ta ci, ta sake kwanciya idanunta na zagaye office ɗin, zuwa yanzu har ta san komai na kan office ɗin sbd yawan zuwa, knocking da aka yi ya sakata Miƙewa taje ta buɗe, Dr Hafsa ce.
Cikin girmamawa ta gaisheta don ko ba'a faɗa ba Dr Hafsa zata iya haifar ta, dubata tayi ta bata shawarwari masu yawa kan ta fice Aisha na mata godiya, se after asr ya dawo da alama duk ya gaji, sannu ta mishi se kuma ta miƙe Tsam ganin ya zauna a cikin kujerun taje wurin frigde ta ɗauko mai ruwa da cup daga kan frigde din.
A hankali ta zuba ruwan kan ta mika mai cup din, ta san dae haka Nene ke yiwa baffa idan ya dawo a gajiye da ruwan sanyi take soma tarbarshi wanda basa rabo dashi a randar ƙasar su, karɓa yayi ya shanye ta kara mishi ya sake shanyewa yana lumshe idanu jin sanyin ruwan na ratsa shi.
"Thanks" ya ce bayan ya miƙa mata kofin, ta mayar.
Miƙewa yayi ya shiga ya sauya kaya ya fito suka fice a tare, gidan Alhj suka yi yana parking Asma'u na parking.
Da gudu ta zo ta rungume shi
"oyoyo Big bro"
"ya school?"
Ya faɗa yana rabata da jikinshi.
"Fin.... Aisha me ya sameki? A ina kika ji ciwo kuma yaushe?"
Ganin Aisha ya katse mata maganan da take shirin faɗa, da sauri taje ta kamata suka yi ciki tana kwala Kiran Ammi, girgiza kai yayi kan ya nufi sashen Hajiya..
*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*
Zaki iya biya ta wannan akawun lamba
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰
🖤Gureenjoh🖤
RUBUTU A KAN RUWA
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*
LAST FREE PAGE
Ba karamin zagi su Maryam suka sha wurin Asma'u ba se dariya Aisha ke yi, Ammi kam banda Allah ya tsare gaba bata sake cewa komai ba, Wata kyakyawar mace da tayi kama da Abbanta sossai ta gani tana saukowa daga stairs hannunta riƙe da wata karamar fine girl, fuskanta ɗauke da murmushi take cewa
"Auta ke da waye kuma tun daga sama nake jiyo Muryar ki?".
Dama ya ya nan ta fara faɗa mata abunda ya faru kaman tana wurin, seda ta gama Aysher ta gaisheta ta amsa cikin kulawa tace
"Amma Aysher be kamata kina fuskantar irin wannan abu ki ƙi magana ba, duk haka ta faru ki faɗa a ɗau mataki da wuri kin ji?"
Kai ta gyaɗa, Asma'u ta dora mata da cewa wannan din itace Aunty Salma ƴaƴan ta biyar, Aunty salma na da kirki sossai sede Aisha ta lura bata da surutu kaman Aunty Asmeey tana nan so quite kaman Abba ne, a tare suka cigaba da hirarrakinsu bayan Aysher ta karɓi yarinyar me suna Hibba da hannu ɗaya yarinyar kuwa ta sake suna ta ɗan wasa, har Magrib suka tashi suka yi sallah suka dawo parlorn tana mamakin rashin shigowan Abba, se after isha suna cin abinci tsakar parlorn ya shigo da sallama.
Duk suka amsa, a ƙasa ya zauna chan gefe kusa da kafafun Ammi yana gaisheta, seda ta ɗan muskuta kan ta amsa da kalma ɗaya, Aunty salma ce ta gaishe shi ya amsa yana tambayarta yara, Asma'u ta gaishe shi ta ɗaura da
"A zuba maka abinci Big bro?"
Girgiza kai kawai yayi, ya jima zaune parlorn sede yayi operating waya ko ya amsa call be cewa ba'a ce mishi se lokaci lokaci salma ke ɗan mishi magana wanda yake amsawa ɗai-ɗai, Ammi kuwa ganin ya ƙi tashi yasa ta miƙe abinta tana cewa Aisha
"kin tabbatar kin haɗa komai a akwatin ki ko? Kar ki mance wani abin"
"Eh Ammi na haɗa"
"to ki tabbatar kan ku tafi kin shigo akwai sakon da zan baki"
Tana kai nan ta dubi salma
"ke kuma kwana zaki yi ne kam?"
Shagwaɓe fuska ta ɗan yi uwa me daaɗi
"Da se na fi kowa farin ciki wlh Ammi, Ammi kora ta ma kike? Zan tafi to amma babansu ne ze zo ya ɗauke ni"
Harara Ammi ta zabga mata tana cewa
"Ai kin san mu bama son namu iyayen muka barsu muka dawo gidan babanku da zama"
Asma'u da Aisha se dariya suke yayinda ita salma ta kara narke fuska, ita Kam Ammi tayi sama abinta.
A hankali ya maida kanshi kan wayanshi ya ɗan Tsurawa wayan idanu ba tare da yana yin komai ba, in da sabo ya ci ace ya saba sede ya rasa me yasa yake jin shi out cast idan Ammi na mishi haka, babu abunda ya fi tsana a al'ada irin wannan a rayuwar shi kuma ba ze lamunci ayiwa ɗan shi ba capital No.
Miƙewa yayi kawai fuskanshi sam ba walwala se ma sake tamketa da yayi.
"Se da safe Yaya"
Salma ta faɗa don ta san ba dawowa ze yi ba, da sauri Aysher ta miƙe ta haura seda ta shiga tayiwa Ammi sallama ta bata snacks da ta sa aka mata sbd zaman gidan Emran se da shiri da wasu designers Abaya guda biyu, sossai tayi mata godiya kan ta fito ta shiga ɗakinta ta janyo trolley dinta, Asma'u ta miƙe ta taya ta suka saukar zuwa mota, da gudu taje tayiwa Hajiya sallama sbd kar ta ajiye shi ta dawo, yana zaune ciki Asma'u ce ta sa a akwatin a boot, juyawa tayi wurin Hibba tana ce mata
"byebye baby"
Ba se yarinya ta soma miƙa mata hannu tana kuka ba, duk dariya suka yi Aunty salma na cewa
"wannan kam se ki sami lokaci Asma'u ta kawo min ke ki mana yini tunda jinin ku ya gama haɗuwa da Hibba uwar Ƴan kyuiyan duk duniya"
Tana buɗe motan ta cewa Asma'u
"Eyyaaa Aunty Asmy ko ban je ba watarana ki karɓota ki kawomin ita?"
Harara Asma'u ta zabga mata tana cewa a nawa? Duk dariya suka yi ta shiga motar tana ɗaga musu hannu, daidaita zamanta tayi ganin sun hau titi sossai, gabaɗaya se motar be yi mata daaɗi ba Dukda ta san Abban ba ma'abocin sakin fuska bane sede da kallo ɗaya a yanzu zaka san akwai abunda ya taɓa Ranshi har suka isa gida babu wanda ya tanka se sautin karatu dake tashi kasa ƙasa..
A tsakiyar parlor suka samu Naina tana kai kawo ganinsu tare yasa ta ja ta tsaya, tana sanye da doguwar riga baƙa shara shara da alama tana hutu ne sbd abun cikinta.
"Emran ina kuka fito?"
Tayi tambayar tana tsatsaresu da idanu, ita fa ba wawuya bace kuma auren soyayya suka yi da mijinta ba haɗi ba, kuma ta san kishi taya za'ayi wannan ƴar kauyen take zama gaban motar da ta saba zama cikin har tana haɗa kafada da mijinta?
"What sort of question is this? Ashe kece mijin..."
"Dole zaka ce haka, wlh dole zaka ce hakan saboda kun san baku kulla gaskiya ba, sau nawa kuna fita ku yini tare? Dabba ka maida ni ko ban san me nake yi ba? Ko jiya tare kuka yini wallahi yau se kun faɗa min me kuke kullawa.."
"Abunda jakar kwakwalwanki ya faɗa miki shi muke yi, Wallahi Naina ki kiyaye ni nayi iya lallaɓakin da zan yi and i will not take it lightly kika ce zaki tsallake iyakarki"
A tsorace Aisha ke kallon su ganin tana kokarin haddasa fitina a tsakanin ma'auratan hawaye ne ke bin fuskanta sam bata gane abunda Nainar take nufi dasu ba, wace kuma irin macece zata tsaya sa'insa da mijinta murya a sama?
"Ni kake kira jaka imran? Ni Naina kake cewa jaka akan wannan banza kazamar ballazar? Wallahi zan yi ajalin yarinyar nan yau se in ga karshen karuwanci da mij..."
Marin da ya ɗauke ta dashi a bazata ne ya ɗauke maganar dib sbd gigita da tayi bata san ta kai ƙasa ba, bata ji a kab rayuwarta an taɓa kai hannu jikinta se a yau... Gabaɗaya bata gani daidai haka bata ji daidai
Ɗagowa tayi cikin matsanancin rawar murya ta ce
"N...ni ka mara? A kan w..wannan"
Ta karashe tana nuna Aisha da gabaɗaya hannayenta ke kan Bakinta idanunta gabaɗaya sun firfito cike da tsoro da firgita, daga Abban har Naina babu wanda fuskanshi ke da daaɗin kallo a cikinsu
"zan iya miki fiye da haka tun da kin ce baki san abunda zaki ke furtawa a kaina ba Naina, sanin kanki ne ni ba mazinaci ba ne ko a da ban yi zina ba bare yanzu, idan kwakwalwarki ta sake kimtsa miki abu a gaba ki tauna kan ki furta min don wlh ba zan ɗauki wannan raini da rashin kunyar ba"
Tsam ta miƙe tana jin mararta na Murɗawa da karfi kan Aisha tayi
"Wallahi wallahi na rantse da Allah se nayi ajalin ƴar iskar yarinyar nan..jaka sakarya wacce uwarta ta wofintar da rayuwarta saboda dukiya, dabbar da ko a me sharar takalmi na ba zan ɗauke ta ba"
Haukacewa tayi ta soma fashe fashe a parlorn duk abunda ta samu se ta wurga wa Aisha, da sauri ya janyo hannunta ya tura ta ɗakinta a rikice ta zube a wurin ta fashe da matsanancin kuka, Me ke shirin faruwa? Saboda maraici ne duk hakan? Ashe ta kai abun wulakantawa haka a idanun Naina?
Ita kam seda tayi son ranta da tsine tsine babu abunda bata faɗa ba yana tsaye ya harde hannu yana kallonta, duk haukar ta tsoron shi take hakan yasa bata yi kanshi ba, ta fashe da tsananin kuka daga karshe tare da zarrar keyn motarta ta fice be ce mata ci kanki ba, se jajayen idanunsa da ya runtse da karfi...
Tana tuƙi tana kuka har ta isa gidansu a parlor ta samu iyayenta kawai ta zube jikin Dad dinta tana kuka me gunji an yi mata abunda ba'a taɓa mata ba a rayuwa, ita Emran ya mara akan wanchan karuwar yarinyar.
A rikice suka rufu suna tambayarta me ya sameta? Me aka mata har Nameer da Shigowar shi kenan yaga parking nata da yadda tayi cikin gida da gudu, mararta dake ciwo ta dafe ta ɗago tana kallon mahaifinta, a razane ya ɗaura tafin hannunshi samar fuskanta
"wa ya mare ki Naina?" Tambayar se ya sake hasala ta ta sake fashewa da kuka irin wanda bata taba yi ba.
"Wayyo cikina Daddy, mommy cikina zan mutu"
A take suka sake rikicewa basu ankara ba se jini da suka ga yana malala daga jikinta, kan kace me jikin ya rikice se ta koma yaraf ta sume, da gudu Nameer yayi mota da ita iyayensu suka rufa musu baya se asibiti...
Danƙari! Aisha kina ruwa tsundum...
*To fa anan free Page ya kare, mallaki naki ki ji ya zata kaya a gidan Abba*

Showing 36001 words to 38960 words out of 38960 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13