ɗin shi, kuma ba da hankali yayi maganar ba bare tayi comprihending, shima cikin turancin yace
"shiga hankalinka ba zan bada aurenta yanzu ba se ta zama cikakkiyar medical doctor sannan"

"Ai se in jira ta, amma dae zaka bani ko babban yaya?"

"In har dae zaka iya jira, but for now ka sahirta mata tayi karatu pls, and wannan zaƙewan bana son shi kaman janyo raini ne da zub da kai pls maintain"

"in Shaa Allah Abban mu"

Murmushi me sauti yayi a hankali yace
"yaushe na zama Abbanka gardi da kai"

Dariya Naufal yayi yace
"Ai babban wa ubane don na kira ka Abba yanzu ba laifi bane"

Girgiza kai kawai yayi yaci gaba da cin abincinshi.

Basu suka bar gidan ba se yamma amma ta ɗan fahimci chanji daga Asma'u da ta tambaye ta se tace mata kanta ne ke ciwo, duk inda ta zauna Naufal na wurin tun bata sakewa har ta fara sakewa suke hira tunda ya iya yaren ta sossai gashi da son wasa da tsokana.

Ko da suka dawo basu wani jira komai ba tunda duk a koshe suke suka wuce ɗaki tayi shirin kwanciya ta kwanta.

Washegari Litinin da safe da ya tashi ya shirya a tsanake, yana fesa turare Naina ta shigo ta mirror ya kalleta ya ɗan sakar mata murmushi tana sanye da suit designer, wando blue me ɗan fadi se farin shirt da ta saka ta ɗaura bakin kyalle haka a wuyanta, bata sa rigar suit din ba se ta yafa shi a duka kafaɗunta, kafafunta baƙin hill ne me tsini sossai haka baƙin jaka ne a hannunta, gyalen kanta da ya bayyana jelar karin gashinta daga gaba har baya zagaye da wuyanta.

A yangance ta ɗan yi hugging nashi tana gaishe shi, cikin kulawa ya amsa yana ƙarasa ɗaura tsadaddiyar agogon shi, a tare suka fito a natse ya kai idanunshi bisa dining ɗin be wani damu ba ganin ba komai ya san she's still a kid ga karatu baya ma so tayi ta stressing kanta, duk a tunanin shi ta wuce don haka ficewa kawai suka yi, a tsakar gida suka haɗu da driver ɗin ta, cikin mamaki Emran ya duba watch ɗin shi Its already 8am, me ya makarar da ita haka?

Juyawa yayi ze koma Naina tace
"Kayi mantuwa ne?"

Girgiza kai yayi ba tare da ya tsaya ba hakan yasa ta bishi, daga parlor ta tsaya tana kallonshi har ya tura kofar Aysher ya shiga bayan knocking da yayi har sau uku...

"Ya ilahil Alameen" ya faɗa kasa ƙasa yana nufan gadon da hanzari ganin tiny body ɗin ta dunkule a wuri guda, sanye take da dogon wandon bacci peach da rigar shi, baka iya ganin fuskanta sbd gashinta da ya hautsine ya baje gabaɗaya a kan fuskan gashi kuma a kife take kwance, daga kallon yadda ta kwanta ɗin da kuma yadda gabaɗaya gadon ya cukwuikuye da alama ba lafiya ba.

"Aysher! Aysher!! Ke Aisha!!!"
Ya jera kiran yana buga pillown da take kai sede bata iya ta amsa ba amma ta ɗan yi motsi alamar tana jinshi, komawa yayi da sauri parlor yana kallon Naina da idanunshin nan yace
"I think yarinyar bata da lafiya please help me ki tayata kimtsawa mu tafi hospital"

Kallonshi take kawai galala kan tace
"am already late ina da meeting da board, bye"
Tana kai nan ta juya ta fice.

Lumshe idanunshi yayi ya buɗe kan ya juya ya koma ɗakin hannunshi ya haɗe yana kallonta yana sauke numfashi a hankali hankali, ledojin choculates na diary milk da snacks kusan biyar a zube a gaban gadon, iska ya fesar daga bakinshi kan ya sa hannu ya lalabo wayan shi, kai Tsaye Asma'u ya ƙira ringing biyu ta ɗaga ta gaishe shi cikin girmamawa

"Ki zo mana in baki da class, i need u to help Aysher bata da lafiya"

Tsurawa gaban dressing mirror da take zaune kai idanu tayi kan ta waiga ta kalli ɗakin nata ajiyar zuciya ta sauke kan tace
"Yaya ina school yanzu zan shiga practical kuma a matsayin C.A yake"
Katse kiran kawai yayi ba tare da ya ce komai ba ya sake tsura mata idanu....

*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*

Zaki iya biya ta wannan akawun lamba

3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin

Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰





                         🖤Gureenjoh🖤

RUBUTU A KAN RUWA

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN
         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*

FREE PAGE 10

A hankali ya isa gaban gadon ya tsuguna, hannunshi na dama yayi dropping bisa wuyanta, ɗayan hannun kuma kafaɗarta ya birkitota, hannun dake kafaɗan ya cire ya soma maida gashin kanta baya..

"Ya Salaam" ya faɗa cikin damuwa da alama cikin ciwon nan ta kwana ganin yadda gabaɗaya idanunta suka kumbure tsabar kuka kuma har yanzu hawaye take yi, dama Aysher bata iya ciwo ba se ta gigice ta gigita iyayenta da kuka da raki.

"Aysher!"
Ya kira sunan chan ƙasan makoshi, kokarin buɗe idanun take sede har lokacin hawaye ke zuba, bata ma iya kallonshi sbd idanun babu madubi.
"Me ya faru? Menene matsalar?"
Yayi maganan cikin tsantsar tausayi.

Lip ɗin ta da yayi ja sharrr ta taune tana sake lankwashewa, hannunta ɗaya dake marar ta ya bi da ido.
"Cikin ki ke ciwo?"
Kai ta gyaɗa tana sake fashewa da kuka tana kuma yarfa ɗayan hannunta.

"Me kika ci? Daena kukan nan and talk, me ya janyo ciwon?"
Cikin Muryar kuka tace
"ban sani baa Abbaa"

Sake kallon marar yayi da lokacin ta janye rigar ta ɗaura tafin hannunta bisa marar tana murzawa cikin kuka, kallon fuskanta yayi a matsayin shi na likita kai tsaye ya hasaso abunda ke damunta

"period pain? Dama yana miki ne?"
Sam bata gane me yake nufi ba ta saukar da wuyanta daga tafin hannunshi ta sake kifewa, girgiza kai tayi ita kaɗai ta san me take ji.

Sake juyo ta yayi
"Ki natsu mana ban son rashin hankali, keep quite and tell me dama kina ciwon mara ne yayin al'ada?"

Cikin kuka da ɗan tsoro sbd da ɗan tsawa haɗe da damuwa yayi mata maganan tace
"Ni ban sani ba, ban taɓa yi ba"

Wara idanu yayi
"baki taɓa period ba? Shekarun ki nawa?"

Numfashi taja tana yarfa hannu cikin sakin sabon kuka tace
"wayyoo baffana wayyooo Nene zan mutu, wlh mutuwa zan yi..."

Ganin gabaɗaya ta gama ficewa hayyacinta yasa ya sanya hannu ya sure ta kawai suka fito, drivernta ne ya buɗe mishi mota ya sanya ta, ya bashi umarnin tafiya kawai se gobe in taji sauƙi, da hanzari ya shiga driver seat ya ja motar suka fice.

Har gaban tamfatsetsen building na asibitin nashi da aka rubuta CITY CLINIC a chan tsolon ginin dake nan kaman skyscrapper yayi parking, da gudu security dake tsaye daga bakin enterance ɗin ya je ya buɗe mishi kofa, fitowa yayi ya buɗe bayan ya sake daukar ta ya nufi ciki se bashi hanya ake ana miƙa gaisuwa sede be kula kowa ba.

Katon floor ne dake malale da farin tile daga ka shigo enterance ɗin, chan daga gefe reception ne amma yayi nisa sossai, matattakalai har biyu ne daga nan ƙasa kana iya hangar saman sbd glass ne da shima kaman floor ne, in ka miƙa daga ƙasan akwai elevator wadda kaman har guda biyu ne daban daban, majinyata dake sanye da kayan asibitin ke ɗan kai kawo da en uwansu.

"Sir in kawo wheelchair?"
Nurse ɗin da ta iso da gudu ta faɗa, girgiza kai kawai yayi ta bishi da sauri ganin yayi elevator alhali emergency ɗin su na daga ɓangaren hagu a First floor ɗin, ita ta danna mishi ya shiga tana shakka shakka sanin halin shi ta tambaye shi wani floor?
"8"
Abunda ya faɗa kenan yana ɗan kallon fuskan Aysher dake kife a kirjin shi jikinta gabaɗaya a sake, likitoci uku ne suka shigo suma da sauri kan ya rufu, kowa so yake ya samu privilagde ɗin ogan nasu sbd mutum ne shi me kirki da sanin ya kamata, ma'aikatan shi suna matukar mutuntashi sbd shima yadda yake mutuntasu, abunda ze sa Kaga ya ɗauki tsatsauran mataki akan ma'aikaci to ba ƙarami bane, kawai dae baya son wasa da aiki in kana so ku shirya ka kasance ka san makamar aikin ka, mata kan mishi kallon marar mutunci da wulakanci sbd yadda baya basu fuskan kawo mishi wargi inda Allah ya tsare shi ma kwarjininshi baya bari mace ta fuskanceshi da wani banzan zance, ko kinyi kokarin yi yana tsura miki mayun idanunshin nan zaki rikice ki rasa abin faɗa a dole suka shafa mishi lafiya.

"Someone should call Dr Hafsa ta sameni a office na now please"
Ya faɗa yana kallon likitocin, a tare suka fiddo waya sede ɗaya ne ya samu ya kira ta.

"Oga needs you in his office now! Its an emergency"
Yana kai nan ya sauke daidai elevatorn ya buɗe kai tsaye ya miƙa doguwar floor ɗin.

"Zaku iya komawa aikinku"
Da sauri ya wuce ya shiga katuwar office nashi me ɗauke da wasu irin office furniture na garari, misalta tsaruwa da fasalin office ɗin ɓata lokaci ne, gabaɗaya asibitin kaman a Turai ba Nijeriya ba, a kan gado dake cikin office ɗin ya shimfideta se murkususu take yi tana kuka a hankali.

Dr Hafsa da kwararriyar gynae ce ta danna door Bell yaje ya buɗe, ta shigo tana miƙa gaisuwa ya nuna mata gadon
"My daughter.. I think she's having cramps matsalar inaga this is her First period gashi ta ja shekaru"

Dr Hafsa da bata yi mamaki ba sbd ana samun irin cases ɗin wata se ta kusa twenty years ma bata fara ba, wasu kuma daga shekara goma kai har me shekara tara ma ita ta taɓa karo da ita a harkarta na gynae, isa gadon tayi ta yaye rigar na Aysher da sauri ya ɗauke kanshi ya koma kujeran shi ya zauna don ya barta tayi aikinta.

Bayan gama observing tace mishi tana zuwa, pharmacy ta wuce ta karbo allurai ta dawo, shi kam yana zaune yana ɗan aiki Dukda ya tsinci kanshi da yawan kallonta kaɗan kaɗan se ya ɗaga idanu ya kalleta, Dr Hafsa na zuwa ta haɗa injections ɗin tayi mata har lokacin jinin be sauƙa ba kawai masifar ciwon marar ne ya hautsina ta..

Seda kuwa ya taso ya taya Dr Hafsa kan aka yi allurar se hawaye take yi.

"Sir da alama this ur daughter sangartacciya ce, ji yadda take ta raki akan M.p da yanzu ta fara shi? Hmm akwai aiki kenan every month!"

Yana kallon fuskan Ayshern ya ɗan yi murmushi kaɗan
"she's in pain ne ba raki bane, now komai ze daidaita kenan?"

Tana ɗaura mata drip tace
"Yeah, in shaa Allah daga ruwan nan ya kare ina ga komai ze yi daidai dole ne ta samu irin wannan cramps sbd rashin farawa da wuri, ze iya yiwuwa ta samu wani watan ze iya kuma yiwuwa cramps ɗin na farko ne kawai, amma please ta rage shan zaƙi sbd gudun irin wannan wahala"

Kai ya gyaɗa a ƙasa ƙasa yace
"thanks"

Juyawa tayi ta fice tana mamakin ganin yadda duk ya damu, se kuma tana mamakin ta yadda Wannan ɗin ta zama ƴar shi, gyaɗa kai tayi
"ze iya yiwuwa don prof ba karamin yaro bane kawai jikinshi ne Allah ya halliceshi me kyau, sannan ma family ɗin shi da abunda ya shafe shi to him are confidential don baya taɓa magana akan family, ko matarshi bana tunanin akwai wadda ya santa"

Ta ida maganar tana zama a kujeranta.
"Amma fa yarinyar tashi kyakyawa ce shi ta biyo ga dukkan alama"

Ni dae nace aiki ya sameki Dr Hafsa.

A chan office nashi kuwa ya jima yana aikinshi don har drip ya kare bata farka ba yaje ya cire mata baccin da bata samu daren jiya ba take yi peacefully, yana da aiki a lokacin so change room ya shiga ya sauya kayanshi zuwa blue riga me karamin hannu da wando wadda yayi matukar amsarshi, hular ya riƙe a hannu tare da face mask ya tako ya fice zuwa theater, ya shafe awa uku cur kan ya fito daga nan bakin kofan ya cire rigan da ya ɗaura a saman blue kayan me kaman leda tare da handsglove da facemask duk ya zuba a cikin kwandon shara kan ya wuce kai tsaye zuwa office ɗin shi...

Ita kuwa cikin bacci tayi ta jin wani abu na sauƙa mata me lema lema wadda yayi making ɗinta uncomfortable, juyi tayi a hankali ta soma buɗe idanunta da suka yi nauyi sossai, bata iya kallon komai se farin haske me surkin duhu, a hankali ta fara laluɓe se ta fahimci kaman ba a gadonta bane...

"Akwai mutum a nan don Allah?"
Ta faɗa a ɗan tsorace, shiru ta sake maimaitawa shiru..

Zaune ta miƙe a tsorace jikinta na rawa ta sake maimaitawa
"wayyoo baffana...!"

Buɗe kofan da aka yi ya sakata firgita ta koma baya tana sake laluɓe cikin rawan lips take cewa
"wa...waye? Pls help me bana ganin komai.."

A wurin ya tsaya yana kallonta fuskanshi with blank expression changing room ɗin shi ya nufa ba tare da ya ce komai ba, a cikin aljihun trauser suit ɗin shi ya fiddo glases din ta da har ya nufi barin ɗakinta da ita a hannu ya tuna ya koma ya ɗauka a bed side, fitowa yayi kai tsaye ya nufe ta..

Ƙamshin turaren shi ne ya sa ta natsu daga birkicewar da tayi ta zata ita kaɗai ce, hawayen fuskanta ta share cikin rawan voice tace
"A...bb...a"
Be yi magana ba seda ya sanya mata glases ɗin da kanshi idanunshi a fuskanta yace
"ya cikin? Ya daena ciwo?"

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke se yanzu taji daidai ganin tana kallon komai rass, se kuma lokacin ta tuna da cewa tana ciwon ciki, da sauri ta matsa tana kallon inda ta zauna jin da gaske lema ne a ƙasanta a tare suka sauke idanunsu kan ɗan jinin da ya ɓata wurin kaman kiftawar ido ta koma da sauri ta sake zama a wurin tana sunne kai ƙasa cikin tsantsar kunya ji take ina ma ƙasa ya tsage ta shige da wannan abun kunya..

"Wait here ina zuwa"
Yana kai nan ya koma change room ya chanza zuwa navy blue suites da ya zo dasu ya zo ya fice daga office ɗin har lokacin kanta a sunkuye.

Sake matsawa tayi tana kallon jinin a ranta tace oh na shiga uku shi kuma wannan abu da tonon asiri ya zo, wayyooo Allahna ya zanyi da wannan kayan kunyar...?
Tun tana da shekara goma sha biyu take jin wasu daga cikin Ƙawayenta kan yi labarin al'ada al'ada kan aka zo ma aka yi musu a fiqhu a islamiyya, kan ta isa sha huɗu kusan duka Ƙawayenta kowa na yi se ita, tun bata damu ba har ta fara damuwa har ma Nene seda tayi magana akan hakan duk alkunyar ɗiyar fari da take mata, amma da tayiwa baffa magana yace kar ta damu ze zo ne in lokacin yayi se yanzu da take sha shidda, tuna irin azabar ciwon da ta sha daga jiya zuwa safiya yau tayi a fili cikin Murya kaman me fashewa da kuka tace
"na shiga uku yanzu ko wani wata haka zan yi wannan ciwo??"

Ƙarewa office ɗin kallo ta soma yi, gaskiya bata taɓa ganin office me tsaruwar wannan da kyau ba, komai a kimtse a killace, a hankali ta sauƙa tana sake kallon gadon bedsheets din da yake fari sol ta cire ta nufi wani kofa da adu'ar Allah yasa toilet ne, tana buɗewa kuwa taga bayi ne, shimfide da fari sol ɗin tile se kamshin freshner yake fitarwa, da sauri ta shiga tayi ta dube dube kan ta samu liquid soap dashi tayi anfani ta wanke bedsheet din ta shanya, daga tsaye da take taji jini na gangara a jikinta alamun fa jinin ta na flooding sossai, hannu ta ɗaura a kai

"Ya zanyi yanzu???"
Tayi maganan kaman zata yi kuka, knocking ɗin kofan toilet din taji a anyi da hanzari ta ɗaga kai tana kallon kofan gabanta na faɗuwa ta kalli kafafunta jinin har ya kai nan.

Muryar mace taji tana cewa
"Aysher ki buɗe zan baki abunda zaki kimtsa jikinki ne"
Ajiyar zuciya ta sauke kan ta nufi kofan ta buɗe.

Dr Hafsa ce wacce tana haurowa ne don duba Aysher din se ta gamu da Emran, leda ɗaya daga cikin ledojin hannun shi ya miƙa mata yana ce mata
"pls help her doctor"

Karɓa tayi cikin murmushi tace
"patient ɗita ce sir ba se ka rokeni ba"

A tare suka shigo ganin bata gadon ne yasa Dr Hafsa isa bayin.

Shiga ciki tayi tana kallon yadda jinin ya ɗan ɗidɗisa a ƙasa
"sannu ya jikin?"

Kanta ta sunkuyar tace
"da sauƙi ina kwana?"

"Yini dae yanzu ai sha biyu ya wuce"
Tayi maganan tana fidda pad ɗaya daga cikin roll ɗin shidda da ya saya da wasu panties da suke cikin leda set guda tace
"kin iya anfani da wannan?"

Kai ta girgiza, a natse likitar ta nuna mata
"amma kiyi wanka tukuna ga wannan kaya ne"

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke Dukda kunyar dake dawainiya da ita tace
"Na gode"
Fita Drn tayi yayinda ita kuma cikin kunyar kanta ta cire kayanta ta watsa ruwa, share bayin tayi tayi mopping ya bushe yadda ta same shi bayan ta saka pant dake ɗauke da pad ɗin, seda ta gama ta warware doguwar riga fari da milk stones da ya saya mata, rigan yayi bala'in yi mata kyau, daga ɗan karamin waist ɗinta a kame kasa kuma ya buɗu amma ba chan ba, dogon hannu yake dashi.

Gashinta take son kamawa amma babu abun kamawan hakan yasa ta ɗauki tsiririn ɗan kwalin da be wani rufe kanta sossai ba ta saka, kallon kanta tayi a madubin bayin tayi kyau sede kam se taga kaman Naina sbd irin shiganta ne hakan, kila taste ɗin matarshi kawai ya sani ta ayyana, amma ita kam ina kunya ze barta ta ratsa mutane haka?

Ɗaukar ledar pad da panties din tayi ta nufi kofa gabanta na faɗuwa, yanzu in yana nan ya zata yi? Da wani ido zata kalleshi? A hankali ta murda handle ɗin ta fito.

Yana zaune gaban desk ɗin shi yana duba system, da ƙadan da kadan tayi ta matsowa kaman me tsoron taka ƙasa duk bata san ma tun fitowarta yake
Showing 24001 words to 27000 words out of 38960 words