ce a kitchen nan don in Kaga Naina a kitchen ɗaukar cup ne ko plate se kuma in babu ruwa se a frigde na kitchen.
Har kaman ze wuce zuwa ɗakinshi ya watsa ruwa se kuma ya karkata ya nufi kitchen ɗin, daga bakin kofa ya ja birki ya tsura mata mayun idanunshi yana mamaki ganin yadda take aiki hankali kwance fuskanta cike da annashuwa wadda ze iya cewa banda jiya zuwan Asma'u se kuma yau be taɓa ganin hakan a fuskanta ba.
Riga da wando baby pink na Cotton ne a jikinta, kanta babu dankwali se gashinta da ta kama, fuskarta fayau se murmushi take tana kwashe abunda yafi kyautata zaton ƙosai ne.
Ita kuwa tana cikin aikinta ta soma jin sassanyar kamshi wadda a wurin mutum ɗaya tak ta sanshi na ratsa kofofin hancinta, yatsina fuska tayi to ko don bata san yan birni sossai bane take tunanin shine kaɗai me irin wannan turare? Oho ta taɓe baki tana cigaba da aikinta a hankali taji inuwar mutum gefen ta a razane ta daka tsalle hakan yasa mai fallatsuwa a hannunta, ihu ta tsala tana yarfe hannun idanunta dake nuna firgici zube a kanshi.
Da hanzari ya riƙo hannun yana cewa
"Subhallah! Me hakan? Baki da hankali ne?"
Hawaye ta fara wani na koran wani bata iya ta sake buɗe baki da niyyar magana ba, duba hannun yayi har ya soma tashi sbd jar fatar ta, gishiri ya ɗauka ya zuba mata a wurin yana sake kallon hannun, ya kalleta se Shagwaɓe fuska take..
"Next time idan kin tsorata Naji ko da wasa kin yi ihu i will deal with you, baki san Allah ake ambato ba in an tsorata?"
Yadda ya sauke maganan da natsuwa cikin husky masculine voice nashi yasa ta kau da kai daga kallonshi tace
"in sha Allah zan kiyaye, ina kwana Abba?"
Ya ɗan yi shiru cikin natsuwar shi da kamalar da be ɓoye kanshi ba daga dabi'arshi yace
"Lafiya, me kike yi?"
Se lokacin ta kula da gas dake kunne har man ya fara konewa Allah ma ya sa ta gama se ta kai hannu ta kashe tace
"girki nake"
"wa ya koya miki?"
Ya tsinci kanshi da tambayarta Dukda ya tashi a gidansu yaga kannenshi na girki sede zaman kasashen Turai da ɗabi'ar matarshi yasa yake ganin kowace yarinya ba lalle ta iya girki ba barin ma wannan da bata wuce 16 ba.
Murmushi me sauti tayi wadda baze ce ya taɓa ganin tayi ba tace
"Nene na mana, ai ni tun ina da shekara bakwai take bani girki, ni dae na en gayun nan ne ban iya ba"
Murmushi shima yyi wadda iyaka lebenshi don shi ba ma'abocin dariya bane, murmushin ma ba ko yaushe zaka iya katarin gani a fuskarsa ba, ya kai hannu ya ɗauki kosan ɗaya ya kai baki, lumshe idanunshi yayi ya buɗe yana taunawa a hankali ita kuwa duk ta saki baki da hanci da ido tana kallonshi tana jira yayi compliment, ɗan kallonta yayi se ya yamutsa fuska kaman be yi daaɗi ba, yayi gaba yana taɓe baki ya buɗe jug din ya kalli kunun kan ya juya ya fara tafiya har ya kai kofa ya dakata yace
"lemme fresh up"
Ya fice yana murmushi.
Da gudu taje ta ɗauki kosan ɗaya ta sa a baki tana jujjuya idanu..
"Wallahi yayi daaɗi Abbaaa"
Ta faɗa kaman zata yi kuka.
Hannunta ta duba seda ya tashi dama jikinta bashi da kyau sam akan irin abubuwan nan, a kula ta sa ta kai dining, ta kai jug ɗin ta lura kaman a birni ya zama dole ka kai abinci dining in ka gama ne oho!
Dawowa kitchen ɗin tayi ta tattare komai ta ɗauraye abubuwan da tayi anfani dasu, ta kintsa komai a mazauninshi ta fito kenan da niyyan zuwa ɗakinta don yi wanka se gashi ya fito, kamshin shi ya cika parlorn gabaɗaya kananun kaya ne sanye a jikinshi wadda suka matukar amsarshi, yana tafiya cikin natsuwar shi da tsantsar kamala, dining ya nufa ya zauna.
Har tayi kaman zata wuce se ta dawo, zuwa tayi kan dining ɗin ta fara zuzzuba mishi, bayan ta gama ta tura mai, cokali ya ɗauka ya dibi kunun da tunda ya gani yake son sha sbd abunda yake kauna ne yana shirin kaiwa baki yaji an yi sama da cokalin.....
*Littafin rubutu a kan ruwa na kuɗi ne, da Naira 300 kacal zaki ilmantu, faɗakantu ki kuma nishadantu bi'izinillahi*
Zaki iya biya ta wannan akawun lamba
3118518476
First bank
Fatima Muhammad Gurin
Se ki tura shedar biya ta wannan layi
09039206763
In shaa Allah ba zaki yi dana sani ba🥰
🖤Gureenjoh🖤
RUBUTU A KAN RUWA
بسم لله الرحمن الرحيم
FATIMA MUHAMMAD GURIN
(Gureenjo)
ADABI WRITERS ASSOCIATION
Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
*Kowa Ya ga zabuwa..*
*Diddigar ƙaya... Paid*
And now..
*RUBUTU A KAN RUWA*
*Da sunan Allah me rahama me jin ƙai, amincin Allah da rahamarsa su tabbata ga duk wani ɗan uwa/ƴar uwa da ta riski labarin nan a yau, Godiya ta tabbata ga sarkin sammai da ƙassai wanda da ikonsa da buwayarsa ya bani damar sake dawo muku a karo na Goma churrr, duk yanda zan saka muku labarin Rubutu a kan ruwa bana tunanin zaku fahimta se kun baje shi a fai-fai, Allah yayi mana jagora a wannan tafiya*
*SADAUKARWA* wannan littafi gabaɗayanta sadaukarwa ce ga mutane biyu masu dumbin karamci da mutunci.
*AUTAR MANYA*
*ALEESHATULKHAIR*
kun yi min abinda baki baze iya furtawa ba a duniyar rubutu, irin ku kalilan ne masu wankakken zuciya da ƙauna saboda Allah, Allahn da kuka kaunace ni saboda shi shima ya so ku🥺🙏
*Aleesha collection*
''Jira jira jira Lantana Ina za ki na ga ki na sauri haka?"
"a a larai kyale ni yanzu zamanin nan idan kin ga mace ta zauna ita ta so, gidan ALEESHA Collection zani sarin air freshener da turaren wanka da toilet cleaner da shower gel da kayan bacci na yara da na manya na maza da na Mata''
''A a wannan shahararen campany da suke taimakawa mata masu son fara sana'a da kayan kamshi da gyran gida akan farashi mai Kama da kyauta za ki? jirani kawai lantis marainiya 10k dina zan je na ga ko zan samo abin da zan fara maida taro sisi''
Hajiya ta zo ki ji wani zance, ki na son ki fara sana'a ko Kuma har yanzu ba ki gaji da tambayar mai gida ko saurayi kudin biki da na suna yana sha miki kamshi ba, to idan kin shirya nima na shirya tsaf domin ba ki kayana sari akan farashi mai sauki ke ma ki je ki nemi na ki.
Domin neman Karin bayani ku tuntube ni ta number ta Kira ko WhatsApp 09067967944
Sai kun zo
FREE PAGE 8
"What sort of Nonsense is this?"
Ya dakawa Naina tsawa yana kaucewa kunun ya zube a ƙasa instead of jikinshi.
Aysher kam kallon Naina kawai take dake sanye da karamar sky blue nighty da ko cinyarta be gama rufewa ba, yana da tsiririn hannu gashin da babu tantama na doki ne Dukda yadda aka gyara shi aka kalkaleshi don ya zama kaman na mutum hakan be hana shi bayyana ba rabi a zube a kirjinta rabi a bayanta..
"Emran please! Ni kake faɗawa haka? Why are you eating this? Yaushe ma ka fara cin irin waennan regular foods ɗin kai dake da kyankyami ba ko wani hannu ne ze dafa ya baka ka ci ba?"
Danne fushinshi yake kokarin yi kaman yadda ya saba, tafin hannunshi da ya jike da zufa Dukda Acn parlorn da komai ya kai ya murza goshinshi ya ja tsaki, a lokaci ɗaya ya ɗan ciza harshenshi he looks so cute and charming da fushin..
Shi karan kanshi ya san ba abincin kowa yake iya ci ba but this girl from day one da ya soma ganinta ya tabbatar ko me ta bashi he will not hesitate kuma ya san saboda yana iya cin komai da ya fito daga gidan Isma'il babu tantama ne, so why all the fuss?
"Naina leave my sight, just go"
Ya bata umarni yana me zama ya ɗauki sabon cokali ya bar na ƙasan ya fara shan kununshi, kaman ta makuro shi don haushi juyawa tayi ga Aysher dake tsaye cikin tsoro ta buga mata banzan Harara kan ta wuce kaman iska, kallonshi Aysher tayi cikin mamakin yadda baya tsawaita fushi idan ta fahimce shi, sannan da yayi ta magana gwara yayi shiru, kitchen ta koma ta ɗauko mop ta zo ta gyara wurin kan ta wuce daki be ce mata komai ba.
Bayan tayi wanka ta fito ta zo ta ci nata a nan parlorn tana kallo, har ta gama babu wadda ya fito, Miƙewa tayi ta fito tsakar gidan ta fara ɗan zagaye anan ta ga wani karamin hanya me ɗauke da furanni daban daban masu kyau, hanyar tabi tana mamakin nan ɗin kuma ina ne? A hankali ta bayyana cikin wani lambu me masifaffen kyau bata san sadda ta buɗe baki tana karewa kyaun wurin kallo ba.
Shukoki ne masu kyau da tsari gabaɗaya wurin, kasanshi shimfide da carpet grass, yadda flowers dake wurin suka kawata wurin da kalolinsu kama daga ja, kore, dorawa se taji kaman ta fita daga Kasar ne gabaɗaya, takawa tayi kaɗan idanunta ya gane mata kwantaccen ruwa a cikin wani farin kwami me kalar sararin samaniya, daga gabanshi wani gado ne har guda biyu, gefe chan kuma kujeru ne masu taushi da tebur a tsakiyarshi.
Wurin yayi matukar burgeta ainun, shawagi tayi tayi a wurin tana kallon itacuwa da aka shuka suke fitar da ƴaƴayensu masu burgewa, guiva da yayi yellow kato ta tsinka ta wanke ta soma ci tana ta aikin murmushi, ta jima a wurin sossai don seda taji ana kiran azahar kan ta koma ciki don yin sallah.
Shi kuwa yana tashi daga dining ɗakin Naina yayi, tana lumtse cikin wata lumtsatsiyar cushion nata na ɗakin dake maroon hannunta rike da waya tana dannawa, Bakinta chewing gum ne tana taunawa a hankali, fusge wayar yayi ya wullar kan gadonta yana aika mata wani irin kallo yace
"Naina whats wrong with you? Menene ya hau kanki?"
Kallonshi take tana jin hawaye na cika idanunta ta miƙe tsaye ta nuna shi
"this... You, kaine ke damuna! Emran taya bazan tsani yarinyar nan ba ma for goodness sake? Akan yarinyar nan kuma a gabanta kake ta danganta ni da sunaye kala kala, harda mahaukaciya ka kirani, akan wannan kazama ƴar rugan.."
Idanunshi ya lumshe da karfi se ya buɗe a kanta yana shafa kwantaccen sajenshi kaman wadda ya rasa abun yi se ya taune lip din shi ya saki..
"Taya ba zan dangantaki da irin waenchan sunaye ba? Come back to ur right sense mana! I told u time without number in ba zaki iya taimakona a kanta ba ki fita harkarta, yarinyar nan bata miki komai ba kina aibatata son ranki ina guje miki randa zata iya ramawa bcs zuciya bata da kashi, that time zaki san cewa na gargade ki akan zub da girman ki, yarinya kuma bazata bar gidan nan ba se aure... Shine kaɗai abunda ze fidda ta so pls take a chill pill"
Hawaye ta soma zubarwa wani na bin wani, cikin Muryar kuka tace
"Emran ka daena so na, did you hate me this much?"
Rikitattun idanunshi ya zuba mata, she knows baya son kuka, kukan ma daga macen da yake so sannan kuma shine silar zubar hawayen, amma Meyasa ta kasa fahimtar shi?
Ganin tana shirin kaiwa ƙasan tiles da kukan da ya kwace mata yasa yayi hanzarin janyota jikinsa, kuka take tayi kaman an mata wani abun a zo a gani.
"Please stop it Naina, ki daena bana so"
"abunda kake so kenan Emran, kana dae sane da cewa bani da wani farin ciki a cikin zuri'arka se naka, yanzu kaima ka fara tsanata ko don ban haihu bane? Ko sbd ban haihu bane yasa bani da power a gidana?"
Ajiyar zuciya me karfi ya sauke, hakane ya rasa me yasa family dinshi basa son ta ba kuma sa janta a jiki, amma shi kam yana son kayarshi kuma ai ya san haihuwa na Allah ne tunda dukkansu lafiyansu ƙalau.
"Ban tsaneki ba Naina, ba zan iya tsanarki ba ke fa sirrina ce taya zan fara tsanar sirrina huhnn?"
Haka ya lalace a rarrashinta sede duk yadda ta fito mishi inde kan maganar Aysher ne ze kauce sbd babu dalilin da ze sa ya biye mata ya butulcewa abokinshi tun na yaranta, bata huce ba seda ya amince zasu tafi New York a mata IVF, zasu gwada sa'arsu akan hakan kuma su gani.
Fitowa yayi daga ɗakinta bayan ya tura ta bayi tayi wanka, alwala yayi sbd azahar da ake ta kira ya fice, bayan ya dawo ɗakinshi ya wuce sbd baya jin fita a lokacin har ya kwanta ya lumshe ido se ya tuna ƙunan da tayi dazu, Miƙewa yayi ya duba ointment ya fito ya mata knocking, jin shiru yasa ya tura bata ciki, ya duba kitchen bata nan, fitowa yayi ya fara dube dube a tsakar gidan nan ma bata nan, kuma ya san ba iya fita zata yi ba, garden ya nufa tun daga nesa ya hango ta a kujerar dake bakin ruwan riƙe da alqur'ani tana karantawa cikin sanyin murya da natsuwa.
Ajiyar zuciya ya sauke kan ya nufeta ko sau ɗaya be ɗauke idanu daga kallonta ba, tana sanye da doguwar riga sky blue and White se ɗan baby hijab shima sky blue ya mata kyau sossai barin ma da garin yayi lublub alamar hadari hadari.
Karatunta take a natse idan tayi tayi se ta rufe qur'ani tayi da kai, ta sake komawa farko ta haɗa, tana cikin bitarta se haddar ya gudu mata, shiru tayi tana son tunawa se ta ɗauko se ta chanza ayar zuwa wani chan daban, a hankali taji sautin shi yana ɗaga mata, waiwayowa tayi se suka haɗa idanu, karamin murmushi tayi kan tace
"Na gode"
Be ce komai ba ya zauna a ɗaya kujerar dake facing nata, se ta gyara zamanta tana maida dukkan kafafunta dake maƙale a saman kujeran ƙasa.
Ganin tayi shiru yasa yace
"ƙarasa haddarki"
Cigaba da karatun tayi shi kuwa yana dannar waya, idan tayi ɓata kuma ze gyara mata har ta kamallah.
"Muga hannun?"
Yayi magana kaman me tambayarta.
Qur'anin ta ajiye akan cinyarta ta wara hannunta cikin rashin fahimtar shi, shi kuwa ointment ɗin ya buɗe ya ɗan matse a hannunshi na dama ya ajiye se ya miƙa mata tafin hannunshi na hagu.
Zara zaran yatsunshi dake ɗauke da zoben azurfa me kyalli ta kalla, kan cikin ɗan faɗuwar gaba da ya risketa ta ɗaura tafin hannunta na dama bisa tattausan tafin hannun nasa, a tare suka lumshe idanu suka buɗe, yatsunta ya zubawa idanu yayinda ita kuwa idanunta ke bisa kwantaccen sajenshi da ya matukar ƙawata fuskarshi ya mugun amsarshi.
A hankali ya shafa mata ointment ɗin bisa ɗan ƙunar kan ya saki hannun ya ja da baya, daidai lokacin aka kira la'asar, dukkansu Miƙewa suka yi sede ita taja ta tsaya shi kuma ya fice daga wurin..
Bayan tayi sallah ta chanza hijab zuwa dogo kan ta fito zuwa ɗan hut ɗin da suke karatu ciki, a shimfide yake da tattausar darduma da tuntu irin na gidan sarauta, daidai malamin ya shigo ta zauna ta bashi hadda ya kara mata, suka yi hadith da take kan ya mata sallama ya tafi, ɗaki ta koma tana tunanin abunda zata girka musu da dare don matar gidan kam taga fitan ta tun suna karatu cikin wani rantsatsen paper lace da aka mata dinkin doguwar riga, karamin gyale a kafaɗarta se gashinta da ta zubo shi har baya wadda na ƙari ne.
Tunawa da taga bishiyar zogale a garden din yasa ta maida karamin hijab ɗin ta tayi waje, cirowa tayi Allah ma ya sa bashi da tsawo da se ta nemi abin cirewar, kitchen ta dawo ta dibi shinkafa ta ɓarza ta wanke ta ciro dankwalelen kaza daga frigde, a tsanake ta haɗa dambunta me rai Allah ma ya sa ta iya anfani da steamer sbd dakkere da suka yi a ciki ranar da Asma'u, a hankali kamshin ke ratsa kitchen ɗin, bayan ta gama ta zuba a foodflask se ta fara yiwa kazar nan haɗin gashi irin na tukunya wadda ba'a raba asalin Fulani dashi idan har a ruga yake, sam bata wani san anfani da oven ba don haka a tukunyar ƙasa tayi gashinta dake ta zuba kamshi ta saka a kula daban, tattare kitchen ɗin tayi ta wanke abubuwan da ta ɓata kan ta kai abincin dining area.
Komawa ɗaki tayi ta gabatar da Magrib da aka kira, karatunta ta ɗan yi bita har aka kira Isha tayi sallah da azkar kan ta fito don ɗiban abinci, har tayi serving kanta ta zauna a dining ɗin se gashi nan ya shigo parlorn bakinshi ɗauke da sallama iyaka lips ɗin shi, bayanshi Naina ce riƙe da leda me tambarin gidan abinci.
Dukkansu Dining ɗin suka kalla sbd motsi da tayi na kokarin tashi ta koma ɗaki don gujewa haddasa rikici a tsakaninsu, plate ɗin hannunta ya ɗan kalla kan ya kalli dining ɗin, Naina tayi saurin cewa
"Kaga na biya Fav restuarant ɗinka na samar maka favorite food naka gwara ka ci tun da zafin shi"
A hankali yace
"I think am not eating that.."
"Toh me zaka ci? Da safe ma fa wani jagwalgwalo kaci"
Murmushi yayi yace
"ke kika ɗauke shi haka Babe, but trust me yana riƙe ciki sossai ba abunda ya kai abincin gargajiya gamsarwa".
Daga haka ya isa dining ɗin ya buɗe flaskes ɗin don tuni ta tsufa a ɗakinta bayan tace musu sannu da dawowa.
Har mamakin yadda yarinyar nan ta iya girki yake, ze iya cewa kusan sabon abu ne a wurinshi kuma ba sabo ba tunda ba yau ya fara zuwa ruga ba yana kallo ana aurar da yara a 12/13yrs kuma su yi girki na ban mamaki kai ko mahaifiyarta ze iya tuna a sadda Isma'il ya aure ta bata wuce 14 ba ake ta cewa ma ta tsufa a gidansu idan tayi girki duk yaje ya dinga yabon girkin kenan.
Naina da ta biyo shi ta zauna ta fidda abincinta daga leda ta fara ci, shi kam zuba dambun yayi da kazan dayawa ya zauna ya ci sossai, shi ze iya cewa zuwan Aysher ai
Showing 18001 words to 21000 words out of 38960 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7 Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13