ο»ΏπŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA 2.*πŸ’˜πŸ’˜
*(BOOK 2.)*



*STORY & WRITING...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*Alhamdulillah Allah ya dawo Dani lafiya' masu qorafin Sai ayi hakuri Nima ba haka maso ba' Duk da wasunku sunsan rashin da akamin'*

*Bismilaahir_Rahmaanir_Rahiim*


1️⃣


Haba mana yarinya Se San jikin tsiya mama ta fada tana ture Yasmeen dake kwance bisa cinyanta' qara rungume mama Yasmeen tayi tana turo baki tare da zuba Mata shagwaba tace' mama Allah kaina ke ciwo jinake kama bazan iya rabuwa dake ba mamana ta fada fuskanta dauke da damuwa.

Murmushi me kayatarwa mama tayi tana niyyan Magana daddy ya shigo dakin d sallama Yana cewa' uwar amarya kina inane? ya Zaki zo daki ki kwanta keda 'yarki kubar jama'a''

Sannu da zuwa daddyn Yasmeen mama ta fada tana murmushi' wallahi kaga tin dazu nake fama da ita taqi dagani Se faman shagwaba take kama wacce zatasha nono.

Dariya daddy yayi Yasmeen Ko ta safke Kanta qasa tana murmushi.

Kallan mama daddy yayi yace' hajiya Tashi Yan daurin auren Sunfara shigowa nasan zaku gaisa' dasauri Yasmeen ta tashi tana mejin farin ciki Dan dama abinda takesanji Kenan tin shigowan daddy da dariya ta fita a dakin daddy ya bita da kallan Yana cewa' 'yar lele yau baza'a kula daddy ba?
Murmushi mama tayi tana yafa mayafinta tare da kallan pink shadda dake jikinta tana cewa'hubby duba kaga yadda take neman batamin Kaya kai mashkur ya hadu da aiki' zaro Ido daddy yayi Yana cewa wanne irin aikine haka?
Aiki Dai irin wanda kuke sani kaida ita ' inbadan yanada hakuri ba ai watarana zaneta zeyi idan tace wannan shagwaban zatayi masa' dariya daddy yayi yace' haba dai nima ban zaneniba balle Shi ya tabamin yarinya.

Girgiza kai mama tayi ta Fito a dakin Jin ana buga kofan' tana fitowa taga aunty maryam tsaye jikin kofan' dasauri tace lah aunty maryam kunzo?sannunku da zuwa.

Eh Kya tambaya kinsa mijinki da 'yarki a daki kinbarmu' se faman jiranki muke jama'a duk sun taru' murmushi dauke a fuskan mama tace ayi hakuri aunty kinsan halin Yasmeen wallahi Duk ita ta batamin lokaci.

Uhmn zaku Dena wannan abun daga Ku Har ita' tinda Shi aure ba wasa bane' ita Dai mama batace komai ba tabi Bayan aunty maryam suka fito'
Tinda suka fito'maroka da makida suka fara Mata kirari nan take ta bude jaka tana raba musu kudi.


Jikin Yasmeen a sanyaye ta Shiga cikin dakinta' Bata Ko Kalli su mubeena da zee tare da sauran kawayenta da tin shigowanta suke faman tsokalantaba' kan gadonta Na alfarma ta fada tare da rumgume pillow tana juyi.
Dariya suka sa kafin mubeena ta matsa kusa da ita tana cewa' hy kawata menene abin rumgumar pillow aita pillow ta qare tafada cike sa tsokala.
Dukan wasa Yasmeen ta kai Mata tana cewa' ni da Allah ki kyaleni'wallahi Duk wani iri nakeji kinga tin dazu mashkur ke kirana nakasa dauka.

Wanne irin Abu kikeji haba amarya' ke Duk fa wayan amarya' se ansha manta zee ta fada tana Mata gwalo.

Hararan zee tayi kafin tace' ni mijina ba jarababbe bane kima dena wannan zancen' hhhhhh suka sa hewa tare da dafawa da junansu' haushine ya isa Yasmeen ta rashi da gudu ta fita a dakin ganin Suna neman sata kuka' dakin mama ta Shiga anan ta kwanta tayi lamo tana tinanin abin kaunarta miji agareta mashkur.


___________


Zaune take a daki ta rasa abinda ke Mata dadi' haka Kawai takejin zuciyanta Na harbawa da sauri da sauri'
Ya Allah nijlah ta furta a fili tare da dafe Kanta tana cewa' Wai meke faru dani' kusan minti shida ta dauka zaune tana nazari' ta Zara a wanne gurbi ya kamata ta ajiye mashkur' lamarinsa da tinaninsa Na damunta musamman a 'yan kwanakin nan Bata da aiki Sena mafarkinshi hannu biyu tasa ta dafe Kanta tanasan yin Kuka sedai Bata ga amfanin yin Hakan ba Dan ita a tinaninta sotake ta manta da wani mashkur ta dauka sabuwar rayuwar data zo Mata sedai Duk da haka takasa samun sukuni Har Seda hawaye masu zafin gaske suka zubomata.
Motsin shigowa dakin da'ake qoqarin yine yasata saurin goge hawayen ta zubama kofa ido.

Mujaheed ne ya shigo fuskansa dauke da murmushi'dubanta ya Shiga yi Yana qoqarin gano damuwa dauke a fuskanta.
Murmushin dole nijlah tayi sabida bataso ya gane wani Abu ya dameta da nacin tambaya' Bata ida tinanin ba Mujaheed ya qaraso saitin inda take.

Kallanta yake cike da tausaya tare da matsananciyar soyayyarta' ganin irin kallan dayake binta dashine yasa nijlah saurin juya masa Baya taba cewa' ni ni.

Dariya yayi ya samu guri kusa da ita ya zauna'
Yaya dai baby? Jikin ne naga kin dawo daki ke daya?
Turo masa Dan qaramin bakinta tayi' kafin tace' ah ah' naji sauqi hutawa Kawai nakesanyi.

Bega munintaba sema wani irin kyau yaga tayi masa nan ya karyar da kai Yana cewa' Nima nagaji kinga semu huta tare Ko babyna?
Zaro Ido nijlah tayi kafin ta murguda masa baki tana cewa' wa ni' Allah babu ruwana kaima ka tafi dakinga kafin aunty husna taganka.

Cike da shagwaba Mujaheed yace'haba baby kin manta gobe e yanzu kinzama mallakina to menene abin gudu ya fada Yana janyota jikinshi.
Lamo nijlah tayi a faffadan qirjinsa tana shaqar dandadan kamshinsa' sedai Duk da haka Bata iya sakewa sosai ba sabida tinanin mashkur daya addabi zuciyanta.

Sun kai minti biyu a haka kafin nijlah tayi qoqarin janye jikinta'
Kallanta Mujaheed yayi yace' baby yanaga Duk jikinki yayi sanyi Ko Dai bakisan aurena Ko Kuma Dan bakiji nace za'ayi wani shagalin biki bane yasa Duk kika lanjaremin.

Girgiza masa kai tayi kafin ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana kallansa tace' haqiqa Mujaheed inasanka some tsanani sedai akwai wani kulli Wanda bansan ta yadda Zan kunce saba' bisa ga wannan dalili yasa' kasa qarawa tayi ta fashe da Kuka.
Dasauri Mujaheed yay Kanta Yana cewa' wannan wanne irin kulli ne? Nijlah kisani ayanzu kin wuci komai kinfi karfin kowa da komai dan Zan iya mallakawa mutum kudi adadin gashin ragumi akanki da Duk Wanda ya tabamin ke' nijlah ki gayamin namiki alqawarin sunce wannan kullin Duk kuwa da girmansa.

Tashi nijlah tayi ta Dan matsa daga kusa dashi tana cewa' Kash Mujaheed abubuwa da yawa kudi basa iya maganinsa Nima Ada nayi wannan tinanin irin Naka a lokacin da naira biyar kemin wahalar samu' Se daga Baya nagane kudi ba komai bane illah wata hanya ta Bata idan har mutum be bisa ta hanyar data dace ba.
Kai nijlah Wai Dan Allah yaushe Zaki sauko kidenamin irin wannan kalaman' kullum baki da aiki saina dagawa kanki hankali' Toni kinga ki yadda a daura auren idan yaso daga Se ayi komai.

Shiru tayi tana kallansa kafin Tayi Magana yayi saurin katseta' kinga nijlah kefa yarinya ce Babu abinda kika sani game da aure kibari adaura auren Na tabbata sekince kinyi auta da ba'a daura mana aure tin tini ba' nizan kula da rayuwarki Zaki Zama tauraruwa cikin dukkan Matan Duniya Zan mallakamiki komai nawa Zan zame Miki mijin tace Se yadda kikayi dani' wallahi shekarunki bazasu sa na wahalar dake ba nidai burina Na mallakeki ki Zama tawa ta Har abada.

Sosai kalamansa suka shigeta Har saida fararen hakoranta suka bayyaba' Duk da gabanta Na faduwa Amma Hakan be hanata amincewa da maganan aurensu ba nan suka zauna Yana Mata Hira masu Dadi tare da Mantar da ita ita din wacece.



_______


Zaune suke a babban falo kowa kagani kasan Yana cikin farin ciki' abincine Kala da Kala iri da iri kowannensu da Wanda ya zuba Duk da ba wani ci suke ba.

Aunty lateefah ce tashigo cikin falon da lemo a hannunta kusa da mummy ta zauna tana cewa' Mummy me zakici a zubamiki kafin anjima gidan ya cika da 'yan biki nasan lokacin Babu abinda Zaki iya chi?
Murmushin kasaita mummy tayi tace'ah ah lateefah ni yau kobanci komai ba cikina ze kasance a koshi sabida na auren da auta macen data dace ba Wanda ya daukomana ba.
Uhmn hakane mummy Wai Haryanzu ba'aga nijlah ba?
Inako za'aganta lateefa aimu wannan ba qaramin farin muka samu ba Dan da tana nan da ba'ayi auren nan ta Dadi ba Dan muddin mashkur Na ganinta baze taba nutsuwa ba.

Dariya lateefa tayi tana cewa' gaskiya ne mummy ni abinda ke bani mamaki Wai ace yarinya qarama kama nijlah Har tasan wani Abu Wai Kishi kai mudai Babu abinda zamuce se godiya ga Allah.

Hakane kinga Tashi gasu Mami sun zo ki kaisu daya falon sabida nan akwai wadanda nake jira.
Dasauri lateefa ta Tashi tana musu sannu da zuwa.


Ango ango kasha kamshi irin wannan daukar wanka haka' murmushi mashkur yay Yana cewa kaga tin dazu nake Kiran mutumiyar Bata amsa ba Ko ina ta aje wayan.

Dariya Nasir yayi yace' kaima kasan Yasmeen da rawan kai Na tabbata tana tare da kawayenta Suna tsara yadda partyn gobe ze kasance.

Eh Kuma hakane Sai kuma yayi tsaki Yana cewa' kasan Allah Nasir naso ace nijlah Na nan za'ayi wannan partyn da Kaya iri daya zamu saka itama tasan tayi aure.

Zaro Ido Ahmad yayi dake zaune gefe besa musu baki ba Se yanzu yace Aiko da ankarma Mata abanza' meyasa Haryanzu ka kasagane haukan kishin Yasmeen Sai kace ba'a gabanka take wasu abubuwan ba?

Yauwa Ahmad gayamasa Dai cewan Nasir Yana mamaki.

Tabe baki mashkur yayi a hankali Kuma ya bude baki yace......




Idan Baku mantaba nagayamuku 'yar sadaka book 2 Na kudine Dan haka nakeso kubani hadin kai gurin karanta qarashen wannan labari ta hanyar amana' banaso Duk Wanda ya Biya kudin karatu ya fitarmin dashi idan akayi haka Zan dakata da rubutu' idan kinsan Zaki fitar Ko Zaki siya ki zageni Dan Allah karki siya masoya Kawai nake buqata.


Ga masu San cigaban yar sadaka zasu tuntubeni ta wannan number 09038049272.

200 kachel Zaki Biya ki karanta saina jikuπŸ’˜πŸ’˜ *'YAR SADAKA 2.*πŸ’˜πŸ’˜


*Book 2*


*STORY & WRITING...*
*BY*
*MOMN SULTAN*


*Wannan littafin na kudine ga Mai San cigaban labarin ze iya tuntubata ta wannan number a WhatsApp 09038049272*

*Book 1 free ne.book 2 na kudine' naira Dari biyu 200 kachel Zaki Biya ki karanta masu tinanin karantawa batare da sun siya ba su dena..*


*Free page..*



2️⃣


Tabe baki mashkur yayi a hankali Kuma ya bude baki Yana cewa' tab waza'a Karya Ahmad?badai nijlah ba?
Murmushi Nasir yayi yace' ita mana Ko kana ganin Yasmeen bazata iya aikata hakan ba?.
Murmushin kasaita mashkur yayi sedai bece komai ba sabida sanin halin 'yar mulkin tasa'hannu yasa ya dauka wayarsa dake kan centre table Yana dauka yayi dealing number Yasmeen kafin ta dauka ya Tashi a wurin Yana cewa' minti biyu ina zuwa' beko jira amsar Suba ya fita adakin tare da Kara wayar a kunnansa.

Yasmeen dake kwance a dakin mama Taji ringing wayanta' hannunta tasa ta janyo wayan idonta rufe ta Kara a kunne'daga daya bangaren mashkur yayi sallama.
Dakyar Yasmeen ta iya amshi tare da fadin' baby nah ka Tashi lafiya?
Murmushi mashkur yayi kafin ya amsa mata da'
Inafa lafiya tin safe nake Kiran wayanki baki dauka ba' eyyah baby wallahi kaganni kwance narasa meke damuna Yasmeen ta qare maganar da alamun damuwa.

Shiru mashkur yayi Yana sauraranta Har saida ta Gama Magana kafin ya bude baki a hankali yace' haba Yasmeen Dina meyasa zakimin haka' kinfasan Amana nabaki kanki yayi maganar da murmushi dauke a Saman fuskanshi saika rantse tana kallansa.runtse idanunta tayi tana tinanin irin rayuwar da zatayi a gidan mashkur ba tare da daddy na kusa da itaba' wasu hawaye masu zafi ne suka Sami nasaran gangarowa daga cikin idonta tausayin Kanta ya kamata sedai bazata iya rayuwa ba tare da mashkur ba don haka tayi saurin goge hawayen tana cewa' ah ah baby ba! Babu komai yanzu naji daidai dama rashin jinkane yasa Duk na damuwa.

Dariya mashkur yayi me Sauti Yana cewa' indai nine kinriqa kin sameni' ni nakine ke tawace lokaci kadan ya rage muzama mallakin juna.
Wayan hannunta tayi saurin rumgumewa tanajin saban kaunarsa naqara Shiga cikin zuciya da Duk wani Sako da Lungu Na jikinta.

Jin shirun yayi yawa yasa mashkur Kiran sunanta a hankali' cike da shagwaba ta amsa ta bude baki zatayi Magana Taji an dala Mata duka' dasauri ta juyo taga mubeena Na cewa'
Haba hajiya kin dawo nan kinbar mutane Sai jiranki suke kowa ya Gama shiryawa kema kizo ki chanza wannan kayan Ko kyaji Dadi a jikinki.

Turo baki Yasmeen tayi tare da sakin kukan shagwaba tana cewa' baby kaganta ko'
Dasauri mashkur yace wacece haka take tabamin 'yar lele?
Dariya mubeena tayi ta amshe wayan tana cewa' nice nan ango kasha kamshi haka Kawai ka riqe mana amarya dakyar muka gano inda take.

To shikenan gatanan Na Baku aranta kugama Duk abinda kuke anjima kadan zata rakani ankuwa'
Ah inye lallaima angon nan wacce irin anguwace wannan muna tsaka da biki to gaskiya bazamu Baka itaba kabari gobe idan mun kaima ita saita rakaka Duk inda kakeso.

Dariya mashkur yayi yakasa Bata amsa danshi bame San Magana bane' hannu Yasmeen tasa tare da karyar da murya tace pls kawata bani muyi sallama Allah yanzu Zan dawo.

Hhhh kafana kafanki ba inda zani kuyi sallama mu tafi' turo baki Yasmeen tayi tana cewa' baby wannan mayyan tazo anjima mayi waya Ko?
Ok Kawai yace ya katse kiran.

Nan mubeena tasa Yasmeen agaba suka fito' da mama suka hadu a parlon mubeena tace yauwa mama gata Na samomiki ita' shafa kan mubeena mama tayi tana cewa to mu koma dakin kayan Yana can.

A tare suka Shiga dakin aunty Khadijah ta dauko wani gora cike da magani ta miqa Yasmeen tana cewa' amsa ki shanye wannan duka.
Zaro Ido Yasmeen tayi tana cewa aunty dukafa kikace?.

Cikin fada aunty ni kike tambaya' zanci gidanku ki amsa nace' sabida sanin halinta yasa Yasmeen tayi saurin amsa tafara sha tana yatsina fuska' ahaka harta shanye tana hawaye' wasu magungunan ta qaramata ahaka Duk Seda tagama sha tana Kuka tare da Kiran sunan daddy.

Murmushi Khadijah tana cewa' yarinya ana Miki gata kina butsarewa koshi daddyn baze Hana abaki ba kije ki gayamasa.

Turo baki Yasmeen tayi Khadijah na hararanta'nan ta fita tana cewa' Se anyi auren kufi kowa San zuwa turaka tana fita mubeena ta sheqe da dariya tanama Yasmeen gwalo' kwafa Yasmeen tayi Suma suka fita a dakin.

Karfe 7 da rabi mushkur ya dawo gida' alokacin gida yafara watsewa 'yan biki sun tafi Se 'yan uwan mummy da kannanta tare da 'yayanta da sauran surukanta' zaune suke a falo mashkur ya shigo da sallama nan suka fara gaishesa masu tsokala nayi' shidai bece komai ba kansa a qasa yake tambayan aunty lateefah.

Aunty mummy fa?

Kallanshi aunty lateefah tayi tana murmushi kafin tace tana daki itama yanzu ta Gama zancenka' be iya Magana ba ya Shiga dakin.

Mummy naganinsa tafara yimasa kirari' ango kasha kamshi yaran mummy da abba' kaga angon Yasmeen irin wannan kyau da kayi haka tafada tana janyosa jikinta' hannu yasa ya rungume mummy Yana cewa' Mummy nah kema kinyi kyau kama bake ba' murmushi mummy tayi shiko ya narke mata Yana cewa' wallahi Na gaji bakiji jikina ba Sai ciwo yakemin.

Eyyah' sannu yaran kirki' haka taro yake Dan kana Dan karami ake wani abun shiyasa bazaka gane ba Amma yanzu dayazo kanka aika sani.

Uhmn mummy Kenan kullum kallan yaro kikemin ni Allah babban ne' mashkur ya qare maganar cike da shagwaba.
Eh yanzu Kam ka girma auta sema kafara haifamana Yara kaima ka Zama baba' rufe Ido yayi Dan kunya mummy tace'
To abinci fa nasan bakaci komai ba kunacan Kuna shirye shiryen gobe' eh mummy dama naje police station Akan maganan nijlah Naga abun Sai gaba yake mummy haryanzu Bata dawo ba.

Kai kayimin shiru uban 'yan nacin tsiya Wai dama haryanzu Baka manta da wannan aljanar ba?to wallahi ka kiyayeni idan ba haka ba Zan sabar ma.
Cikin sanyin jiki mashkur ya qara rungumeta Yana cewa mummy kiyi hakuri bazan iya mantawa da nijlah ba, Duk wani bugun zuciyana ita yake ambato ta Zama jini da tsoka a jikina bantaba tinanin haka nake santaba Se yanzu da Bata tare Dani.

Sassauta murya mummy tayi tana rarrashinsa' haba auta kada ka Bata wannan lokacin me dubbin tarihi a rayuwanka da wannan tinanin naka'ka kwantar da hankalinka in Dai Mata kakeso gashinan an daura aurenka da Yasmeen Na tabbata zata maye dukkan gurbin da nijlah ta mamaye Naga ma itace zabinka ta farko to meyasa kakesan zubda soyayyarku ka kaita can wata ruga inda kafi kowa sanin natsani wurin kai sunan fulani ma banisan ji balle harna hada jini dasu' Dan Allah mashkur ka bar batin nijlah bari Na Har abada.

Dasauri mashkur ya dago kai Yana kallan mummy sedai ganin hawaye a fuskanta yasashi saurin sa hannu Yana goge mata' dakyar ya iya bude bakinsa daya masa nauyi yace'
Mummy kiyi hakuri ki gafarceni wallahi ba'asan Raina nake zancen nijlah a gabanki ba zuciyatace Bata iya jurewa sabida ita din haqqinta a wuyana ya rataya gashi Bata tare dani'Amma daga yau Zan kiyaye indai sunanta zesa ki zubda hawayenki.

Baqaramin Dadi mummy Taji ba anan itama ta rungumeshi tana samasa albarka' shiyasa nakesanka Dana Allah yayima albarka yabaku Zaman lafiya Kaji Dana.

Da kyar ya iya amsata da ameen Dan zuciyarsa da hankalinsa Naga nijlah a wannan lokacin' yinkurawa yayi ze Tashi mummy ta rigasa tana cewa' tsaya Kaci abinci nasan kana fita baci zakayi ba.

Be musaba ya zauna Yana shafa fuskanshi' ahaka Har mummy ta fita ta dawo hannunta dauke da plate'fatan dankali ne Sai kunun gyada' Zama yayi yanacin abincin kama yanacin magani ahaka yaci da dan yawa sabida yanajin yinwa sosai' Yana gamawa ya Tashi Yana cewa' mummy saida safe nizan wuce dakina.

To auta kayi bacci lafiya' Allah yasa mashkur yace harya kai bakin kofa Mummy tace lah auta kaga Na Manta idan kunyi waya da diyar tawa kace ina gaisheta' Yana murmushi ya amsa da to.

Yana Shiga dakinsa ya kulle Ko ina kafin ya Shiga wanka Bayan ya fito ya dauko wayansa dake kashe ya kunna' Yana kunnawa Kiran Nasir Na shigowa cikin wayan' dauka mashkur yayi ya Kara kunne Yana sauraransa duk da yasan fada Nasir zeyi.

Haba Malam menene kakeyi haka Ko bakajin dadine?
Nasir me kagani? mashkur ya tambaya kamar besan abinda ke faruwa ba.

Yanzu ka kyauta Kenan katafi kabarmu muna cikin taro' Dan kaifa suka
Showing 1 words to 3000 words out of 65321 words