haka har taji tafara dawowa daidai' amma data tina maganganun Yasmeen sai taji wani irin yar a jikinta ga wani irin faduwar gaba da take.


Tajima zaune kafin ta iya tashi a hankali ta Shiga toilet' alwala tayi ta fito tana dingishi ta shinfida sallaya' dakyar ta iya raka'a daya a tsaye ganin jiri Yana daukanta yasata zauna tayi raka'a dayan a zaune' sosai tayi addu'oin bayan ta idar ta dauki alqur' ani Mai girma tana karantawa' tinda tafara taji wani irin dadi ya rufeta tana murmushi ta rufe alqur'ani Mai girma ta ajiye.

Tunowa tayi da kaka ta zauna tana murmushi tana shafa cikinta' hakan kuwa ya zame Mata kamar ibada a duk lokacin data kebe ita kadai haka zatasa hannu tana shafa cikin tana murmushi' ita kadai tasan irin soyyyar da takewa abinda ke cikin cikin ta' tana zaune taji motsin mutum a bayanta' da sauri ta juyo' ganin Yasmeen tana zubamata murmushi' tare da tahowa tana qarasowa gabanta.

Faduwa gaban nijlah ya cigaba dayi ta kasa cigaba da kallan yasmeen tanaji kamar bazata iya zama guri' daya da ita a halin da ake ciba sabida irin cin mutumcin da mijinsu yayimata..


Yasmeen ta qaraso kusa da nijlah ta zauna tana cewa' kanwata lafiya Baki fito kinci abinci ba?

Yatsina fuska nijlah tayi tana kallan gefe tace' aunty banajin yinwa..


Murmushi Yasmeen tayi cike da kissa tace ke kin Isa ki wahalarmin da yaro ko yarinya tashi Zaki muje kisa wani Abu a cikinki' Allah aunty banajin cin komai.

Niban yadda ba Yasmeen ta fada tana tsareta da Ido.

Tinda kin dage Zan Sha tea shi kadai ma ya isa' tashi Yasmeen tayi tana cewa' ni bacci nakeji yau bazan iya Iran mijinki ba idan ya dawo ki gayamasa Nina kwanta.


Dakyar nijlah ta bude Baki tace sai da safe Nima kwanciya zan' Yasmeen na fita itama nijlah ta Shiga daki' yau ko wanka Bata iya yiba ta cire kayan jikinta ta kwanta kan bed tana tunanin yadda mashkur kesan chanza zaman gidansa ta hanyar wulaqantata.

Har karfe 9 mashkur bai dawo ba haka itama nijlah Bata iya bacci ba har ya shigo cikin dakinta.

Sanye yake da farar jallabiya sai Kofin shayi a hannunsa' tinda ya shigo ta lumshe Ido tana qaremasa kallo harya Samu wuri kusa da qafanta ya zauna' seda ya shanye shayin kafin ya kwantar da kansa a fuskanta ya sakar Mata nauyi Yana shafa cikinta' tayi Kama tana bacci Bata bude idonta harya fara busa Mata iskar bakinsa' ta bude idon tana Masa wani irin kallo Wanda ya kasa gane ma'anarsa' sannu da dawowa tace tana qoqarin juyawa yace'.

Yau kuma bacci wuri kukeji Naga ba kowa a falon ita na Shiga tana bacci kema nazo kinayi?


Nina gajine shiyasa' ita kuma bansan meyasata baccin ba.

Tana gama fada ta tashi tana qoqarin sauka a gadon ya riqeta Yana cewa' Ina kuma za'aje?

Abinci Zan kawo ma ta fada jikinta a sanyaye.

Shafa fuskanta yayi yace' ki kwanta ki huta Ninaci abinci'' zaro Ido nijlah tayi tana kumbura Baki tace' Amma dai' kasan banasan cin abinci waje ko?

Shima kashe Mata Ido yayi ya kumbura Baki kamar yadda tayi yace' niba abinci waje naci ba' naki ne naje da kaina na zuba a kitchen sabida Naga kina bacci.

Murmushi tayi itama ta shafa fuskantashi suka kwanta' duk yadda mashkur yaso jin zumarta yau tayi qima das ta hanashi Koda romance Bata Bari ba haka babu yadda ya iya ya hakuri baccin wahala ya daukeshi.


Washe gari ya shirya ze fita ta rakoshi har falo' nan ta tsaya ya Shiga dakin' Yasmeen domin yayimata sallama sai gasu sun fito tare hannun Yasmeen riqe da sabon wayar da tace mashkur ya saimata.


Dasauri nijlah ta dauke kanta tana jin yadda wani irin zazzafan kishi na taso mata' harta juya zata koma daki ta fasa ta dawo kusa dashi ta riqe hannunsa Shima hannunta ya riqe gam Yana tambayanta"


Ya akayi my sugar?

Ko jikin ne?

Girgiza masa kai' tayi tana nuna wayar hannun Yasmeen' menene ki bude Baki kimin magana idan haihuwane na sani ya fada maganan cike da damuwa.


A hankali nijlah tace' ya mashkur kace zaka saimin waya kuma baka siyamin ba sai gashi ka cikowa aunty leda da kayan ciki harda sabon waya' shine nace Zan tambaya nawa ko mantawa kayi' kuma kace Wai kazar........

Wayar hannun Yasmeen ce ta Fadi qasa ta raga raga Yasmeen bata damu da faduwan wayan ba ta bude Baki zatayi magana mashkur ka dakatar da ita ta hanyar tambaya nijlah.

Ita Yasmeen ta gayamiki Nina saimata sabon waya da Kaya?

Eh nijlah tace tanasanjin amsar dazai Bata yayinda Yasmeen tayi tsuru tsuru da ita tana mamakin iskanci da iya shege da nijlah tayi agabanta.

Mashkur beyi magana ba ya ajiye jakar hannunsa ya dauki car key dinshi ya fita cikin sauri' Yana fita nijlah tayi saurin komawa dakinta ta bar Yasmeen tsaye cikin mamaki.


Mintuna 30 da fitarsa sai gashi ya dawo hannunsa riqe da qaton keda' ciki harda sabon waya Mai shegen tsada Wanda yafi na hannun Yasmeen' a falo ya tsaya hannunsa riqe da ledan ya Shiga kwala musu kira'

Yasmeen' nijlah kuzo" dasauri Yasmeen ta fito tana rausaya tace' baby lfy kakemana irin wannan Kiran?

Be amsataba har saida nijlah ta qaraso tana dingisa qafa sabida nauyin da jikinta yayi ya miqa Mata ledan hannunsa' Amma tayi ta Shiga bude ledan.

Yasmeen ta daskare a tsaya ga haushin fashewan wayanta ga kuma ita be Bata ledan ba' ranta a bace tace'

Baby ni Ina nawa ledan?

Ina wacce kikace na Baki?

Cike da borin kunya Yasmeen tace' ni baka kawomin wani leda ba' kuma ita munafukar data gayama ai' dasauri mashkur ya daga hannu ze saukemata nijlah tayi saurin riqe hannunta tana cewa'

Ah ah ya mashkur kada ka soma' dacan baka sa hannunka a jikin aunty ba sai yanzu yanzun ma sabida ni' to banyadda da wannan kuma hakan daya faru na gane ba Kai ka siya kayan ba' ta fadane sabida kawai ta hadamu kuma danasan hakane wallahi bazan tambayeka ba' Amma kayi hakuri Dan Allah maganan ya qare.


Sai ta juya inda Yasmeen ke tsaye ta riqe hannunta tana hawaye tace' aunty kema kiyi hakuri niban.... Ture ta Yasmeen tayi mashkur yayi saurin tarota ta fada jikinsa.


Baki da hankali Zaki tureta' ko bakiga halinda take ciki ba' kece da laifi Amma Dan bakar zuciya Zaki tana Baki hakuri kina neman illatamin ita?

Kuka Yasmeen ta sa ta tafi dakinta da gudu' nan ya saki tsaki ya Kira mummy a waya Yana gayamata' murmushi mummy tayi ta bashi hakuri Amma duk da haka be hakura ba saida ya Kira mama ya gayamata duk irin abinda ke faruwa

Ajiyar zuciya mama ta sauke tace' yanzu kana Ina?

Ina gida yanzu nakesan fita' toka jira yanzu zanzo gidan.

Bakinsa na rawa yace' mama basai kinzo ba ko a waya kika Mata magana ya isa' ka jirani kawai tace' ta Shiga dakin daddy' tana Shiga ta fito drive ya dauketa suka fita.

Zaune ta Samu Yasmeen a daki tana katsa waya' Yasmeen na ganin mama tayi baya da sauri gabanta na faduwa' binta mama tayi har saida suka Kai jikin bango mama ta riqo kunnan Yasmeen da hannu biyu tana cewa' yaushe kika dawo da wannan mugun halin naki? Koke ba'agayamiki magana kiji?


Kuka Yasmeen ta saki tana Bata hakuri" ba hakuri Zaki bani ba halinki Zaki chanza' ko laifi yayi danya Bata nata ledan dake ya Riga Baki tin tini?

Shiru Yasmeen tayi mama ta dauketa da mari tana cewa' ki bani amsa Mara mutumci Wanda batasan daidai ba' yanzu da yarinyar Bata tambaya nata ledan ba da shikenan kin hada gagarumin fada a rasa inda matsalan yake.

Cikin kuka Yasmeen tace' mama Dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan qara ba' karya kike mama ta fada tana kaimata wani marin' mashkur ne ya shigo da sauri nijlah nabin bayanshi.

Yana Shiga Yasmeen ta tayi saurin dawowa bayanshi tana kuka' ran mama a bace tace' Dan gidanku kibashi hakuri kuma idan kika qara hada wani Abu saina batamiki.

Hakuri mashkur yaba mama Yana Mai jin haushin dukan' yace' Kinga abinda kikaja ko? Wallahi banaso mama taba tamin ke ya fada Yana shafa fuskanta' nijlah ta riqe hannunta tana cewa' sannu aunty Kuma bakai ka gayama mama ba zakace haka muba ruwanmu dakai nijlah ta fada tana janye Yasmeen zuwa jikinta.

Mamaki mama tayi ta tsaya tana kallan yadda yasmeen ta riqe nijlah' gwanin sha'awa.

Mama tace' yanzu ke haka bai fimiki ba' Kuna zaune lfy Zaki tsiro da wani tsirfa'

ta daina mashkur ya fada Yana kallan Mama Allah yasa mama fada tana daukan jakanta'

Nina tafi Allah yasa daga wannan zuwan bazan qara zuwa yimiki fada ba' shiru Yasmeen tayi Yana qara riqe hannun mashkur' ya bude Ido Yana kallanta a hankali yace' Baki amsa ba.


To kawai tace tana shinshigewa jikinsa'

Har mota suka rakata' Basu dawo ciki ba saida sukaga tafiyanta' suna dawowa mashkur yayi murmushi Yana kallan yasmeen' a kunyace Yasmeen ta juya zata Shiga daki' yayi saurin janyota jikinsa ya sakar Mata murmushi Yana Jan hancinta yace' babyna kina birgeni' inajin dadin yadda kike tafiyar da rayuwanki' ta bude Ido tana kallansa cike da mamaki ya daga Mata gira Yana cigaba da cewa' babyna kina da saurin amsar laifinki Baki da daurin kai' sedai kina da saurin daukar zuga' na tabbata wasu ke zugamin ke.

Girgiza masa kai tayi ya juya' Yana kallan nijlah data zaune kan daya daga cikin kujerun ta zuba kayan daya kawomata Ido ganin yadda ya kureta da Ido tayi saurin cewa' ka Bata kayan ni saina amsa wayan.

Murmushi yayi yace' ah ah ki riqe itama nata Yana mota nayi hakane sabida na kawo karshen irin wannan abun.

Key motarsa ya miqa nijlah Yana cewa' jeki dauko Mata nata' dasauri Yasmeen ta amshe key tace' zauna ki huta tana fama da kanta zaka sata aiki' dariya mashkur yayi yabi bayana Yasmeen tana dauka ya Shiga motan ya tafi sabida makara dayayi bai iya komawa ciki ba.


Washe gari sun tashi Kama babu abinda ya faru haka rayuwarsu ta cigaba aminci haryafi nada' yau tinda suka tashi nijlah ke jin ciwan Mara da baya sedai taqi fada tana qoqarin dannewa har saida taji abin yayi yawa ta tashi dakyar ta Shiga dakin Yasmeen tana yarfe hannu' Yasmeen na kwance tayi saurin tashi tana cewa' kanwata lafiya.

Dakyar nijlah ta iya cewa' aunty bayana cikina Dan Allah ki taimakamin' da gudu yasmeen ta tashi ta Kira mashkur a waya' kafin yazo har tafara galabaita suka sata a mota suka tafi hospital' Basu fi minti 10 da zuwa ba Allah ya sauketa lafiya ta Samu Diya mace.

Sosai sukayi murna yarinya tayi Kama da babanta' babu wani Abu data dauko na Nijlah' hakan ba qaramin farin ciki yasa mashkur ba harya zauna Yana tsokalan nijlah abinka da yarinta ta zauna tana kuka' mummy ce ta koreshi tana rarrashinta' sedai kowa ya zo sai yace' da mashkur take Kama.


Basu bar asibiti ba sai bayan sallar magrib suna zuwa gida mummy tace' Yasmeen tayiwa Mai jego farfesun kaji' ba musu Yasmeen ta Shiga kitchen ta fara hada kayan sedai ta fara wanke kaji taji wani irin qarni ya bugi hancinta' take amai ya fara taso Mata tana dannewa' qara tasowa yayi ta Koma daki da gudu ta fada toilet tana kwarara amai' mashkur dake kwance a dakinta ya tashi Yana Mata sannu harta gyara jikinta' tambayoyi ya Shiga yimata taqi bashi amsa ganin haka ya fara zargin abinda yake gani a tattare da ita' tashi yayi ya daukomata mayafi Yana cewa' tashi muje hospital a dubamin ke.


Ni ah ah ka inda zanje' nasamu sauqi' ki tashi nace' haka zakita zama da ciwo.


Murmushi Yasmeen tayi tana cewa' nidai ka bari ba yanzu ba' Ido ya zubamata Yana cewa'ciki ne ko?

Ni uhmn uhmn' Allah shine mashkur ya fada Yana janyota jikinshi'


Ni Dan Allah karka fada kaga yadda mummy ta takurawa kanta akan cikin nijlah shiyasa na boye nawa Kai ma banso ka gane ba.

Hannu mashkur ya daga sama Yana godewa Allah.


Ranar suna yarinya taci sunan mummy (hauwa'u) ana kiranta ikram.

Sosai gurin taro ya cika da jama'a kaka da tawagarta' kawayen nijlah ma saida suka zo sabida' aunty husna tayi kuka sosai har saida nijlah ta tayata' tana cewa' aunty ki kwantar da hankalinki indai na haifi namiji sunan ya mujaheed zansa dariya husna tayi suna cigaba da amsar Baki hidaya ma ba'a barta a bayana tayi nata gayyana haka akayi taro kowa ya watse.


Watan ikran hudu Yasmeen ta haifi yaranta namiji aka sama sunan daddy.

Sosai suke qoqarin fidda haqqin junansu ta hanyar yiwa juna adalci tare da yin uzuri a duk lokacin da wani yayi ba daidai ba tsakaninsu.

Ikram nada shekara biyu nijlah ta Samu wani ciki se dai bamai fallasa bane Kama na ikram.


Bayan wata Tara ta haifi yaranta namiji' ansamasa sunan mujaheed suna kiransa da annur.


Sosai rayuwa ta musu dadi' suna zaune cikin soyayya da kaunar juna' mashkur ya zama babban mutum yana kasuwancinsa Allah na qara budamasa.


Alhamdulillah' godiya ta tabbata ga Allah Mai kowa Mai komai daya Baki ikon kammala wannan dogon labari Mai suna a sama' kuskuren danayi Allah ka yafemin' fadakarwa dake ciki ya Allah ka bamu ikon yin amfani da ita.


*Ina godiya ga wadanda sukasa mahaifina cikin addu'arsu nagode sosai Allah ya saka muku da alkairi' Allah yajiqanshi da Rahama da sauran musulmai Baki daya*

*Godiya gami da jinjina a gareku masoyana bisa ga yadda kukayi hakuri Dani kuka cigaba da bibiyar labarin 'yar sadaka har yazo karshe*

*Jinjina gareku masoya labarin 'yar sadaka wadanda suka siya labarina Ina qara jinjina muku sedai inaso ku riqe amana Dan Allah kada ku fitarmin da labari*


*Gaisuwarki ta dabance kawa kuma aminiya' alkairin Allah ya kaimiki har inda kike' Ina godiya sosai da kaunar da kike nunamin' duk da kwana biyu andena Hawa on sabida ni lolxx*


*Masu jiran a gama abaku ku karanta ku sani ba haqqinku bane' haqqin mutane dayawa ne idan Kunga Zaku iya dauka akanku gashinan' masu juyamin labarin suna maidashi audio kuma ku kiyaye' idan kunne yaji....*



Nagode nagode Nagode

sai Allah ya sake hadamu a sabon littafinq Mai suna.........Shima book 1 free ne.
Momn sultan ce

AMEENA 24 HOUR'S HAUSA NOVEL DOCUMENT for more information contact on +234 0714979567
WhatsApp ONLY

Showing 63001 words to 65321 words out of 65321 words