a gidan talabijin n garin Zamfara ,nan da nan kuwa wasu mutanen suka ji qaunar sultana ta shige su, wasu kuma banda zagi da tsinuwa ba abinda suke mata, wasu zagin ta suke da mahaifan ta har su na fadin.

'Dubi kayan jikin su, shi kadai ya isa wani talakan ya ci da kan shi na wata uku, a haka suke son taimakawa'

Kowa da abinda ya ke fadi, domin shi ɗan Adam kayan Allah ne, ba mai iya masa, ba tare da sun san me ne ne a zuciyar ta ba, sun yanke mata hukunci.

Yanda Sultana bata gaji ba haka ma Lawwali bai gaji da ɗaukan ta ba, domin kuwa gwamna da Hajiya Ikee da suka ga abun ba na qare bane, tafiya suka yi, suka bar ta, Sultan ya so zama, Hajiya ta tisa shi a gaba suka koma gida tare.

Mutane kuwa kamar ingizo su ake, qara zuwa wasu suke, su na layi, Ita kuwa miqawa take, cike da farin ciki, da murmushi, da za a bude qirjin ta wataqila hasken dake ciki sai ya kashe na wani ido, saboda tsabar haske, da farin cikin da ke ciki, tabbas dukkan mai bayarwa domin Allah farin ciki ya tabbata a zuciyar shi .

Sun bar wajen da azahar, ba dan sultana  ta so ba, sai dan komai ya qare ne, har da kudin dake jakar ta sai da ta bayar.

Mutane na ta mata addu'a, wasu har ran su, wasu kuma yi kawai suke, a gefe su na zagin ta, da iyayen ta, su na fadin na munafurci ne, dan an kusa zabe ne, ya ke son ya yi amfani da ita, dan ya zarce.

Sultana na ta daga ma wata dattijuwa hannu ta fada motar ta, Lawwali ya mayar ya rufe.

"Ran ki shi dade ina muka nufa?"

"Gida"

Shi ne abinda ta fadi, ta kwantar da kanta a jikin motar, fuskar ta dauke da murmushin da ya kasa gushewa, ko gajiya bata ji a jikin ta, saboda jin dadi.

Lokaci zuwa lokaci Lawwali na satar kallon ta, a duk lokacin da zai dora ido akan fuskar ta, sai ya ji jinin jikin shi ya tsinke, ya qara gudu, ba qaramin kamu son ta ya masa ba.

Har suka isa gida bata daina fara'a ba.

Bude mata motar ya yi, ya tsaya dan ta fita ya rufe, bata san ya na yi ba, dan durqusa wa ya yi daidai kunnen ta kadan ya ce,

"Ran ki shi dade mun iso,"

A firgice ta kalle shi, fuskar shi ta kalla, ta ga ba wani alamar wasa, ko murmushi, sanar da ita kawai ya yi, ya kalli gefe, ajiyar zuciya ta sauke mai qarfi, ta masa godiya zata fita, har ta fara taku za ta shige ta dawo baya, ta kalle shi, shi ma ita ya kalla, idanun su cikin na juna ta ce,

"Sultana,...ka kira Ni da sultana"

Cikin hanzari ta bar wajen, bin ta ya yi da kallo, cikin wani irin yanayi, domin kuwa ta gama kashe masa duk wata laka ta jikin shi .

Jiki ba kwari ya rufe motar ya gyara parking , sannan ya kashe ya tafi gidan shi ,tun a hanya ya kira Mubaraka ya na bata labarin yanda komai ya kasance, ta na ta taya shi farin ciki, ashar din Lamishi ne ya katse mata wayar da take da Yah Auwal din ta.

Komawar su kenan, ta hangi tukunyar tuwon su na zubewa, rude ya tafasa ya malale a qasa.

"Dan uwar ki bani wayar nan, dama Lawwali ya d'ai sai wayar ga ne, amma na san watarana sai ke yi min ba daidai ba, garin uban ki ka samo shi ko muwa? Mu ka tahiya da zahi, da rani, da damina mu nema, mu kawo a ci ba Dan Talo ba, yanzu da kin ka bari ya tude ki na da abinda zaki dahwa muna? Bani...bani wayar nan, yau sai na liqa Maki kashin wahala (sai ta mata dukan wahala)"

Mubaraka miqa wayar ta yi, ta hau qoqarin guduwa, Mai Buruji na fadin,

"Du Allah dai ki kyale diyar ga Lamishi, dubi fa wanga aiki da tayyi Ita dai, ko ina qal qal qal, dan dai ta tussuwa talge? Ana iya yin wani, ballantana ma ga abinci mun zo da shi"

"To radio uwar zance, tunda niyyi niyyar liqa mata kashin wahala sai na buga in ji dadi, da ki ka hwadin abinci, nan nan wannan mijin naki me mutuwar zuciya mun ka wuce da abukkai nai waje, su na jiran mu kunce su canye"

Wata zabura ta yi da ta sa kajin gidan da Mubaraka, da Mai Buruji tsere, shigar Yabbuga kenan ta ga ana tsere, Mubaraka na ta ihu ta na bada hakuri, Mai Buruji ta maqale qofar dakin ta su na dariya ita da Kameelu, Yabbuga ce ta sheqe da dariya ta ce,

"Yau na ga ikon Allah ma daki kusa, mace ci nesa"

Ai ta na fadin haka zuciyar ta ta tuno mata Lawwali, wani irin tsoro ne ya kama ta, in ya shigo ya ga ana dukan Mubaraka, gaba dayan su sun shiga uku.

Cacima ta kai wa Lamishi ta na son kare Mubaraka daga dukan ta, cikin rashin sa'a Lamishi ta fadi qasa, qafa ta gurde, salati ta zabga, tare da rusa ihu, Dan Talo ne ya keta cikin gidan a guje ya na fadin,

"Mi an kai, wam-mutu? Shin mi na na yah-hwaru wanga salati har garka ana ji"

Ya na cikin maganar ya lura da Lamishi uwar gidan shi a qasa, ga Yabbuga da Mai Buruji na qoqarin daga ta, bayani Yabbuga ta masa daga qarshe ta ce,

"Walle Dan Talo da ta ba Mubaraka kashin wahala Lawwali ya yi ajalin mu har lahira gwanda ta qalle qawahu na baro qohwata na yi jinyar ta, ina nika iyawa da bala'in Lawwali ?"

Har daki suka kai Lamishi ta na ta rusa kuka, mai gyara aka kira ya je ya duba qafar, aka yi addu'o'i aka shafa man shanu da kade, mai gyara ya ce,

"Lamishi ki kula da qahwar ki turmushe na kin kai, kar ki zan ka aikin da zaki wahal da ita, nan da sati kina warkewa, Allah shi bi da lahiya"

(Turmushe, targade)

Lamishi baccin wahala ne ya dauke ta, Mubaraka kuwa ta san ta ja wa kan ta dukan da ita ma in ba ai sa'a ba sai ta kwanta, dan haka kuka ta fara, ta na addu'ar Allah ya mantar da ita me ya faru ya ba wa zuciyar ta hakuri.

Haka Lamishi ta kwana qafa ta yi haushi, ta kumbura,miqo min dakkon kuwa har Dan Talo ranar bata bar shi fita ko ina ba.

Washegari......

*Cassss ga washegari mutuniyar ku 😅*

A GARIN MU




WRITTEN BY HAERMEEBRAEH





PAGE 18:



Washegari da sassafe bayan Mubaraka ta yi sallah, ta ɗora abin karya wa, ta share gidan tsaf, ta wanke bayi, zuwa bakwai da arba'in 7:40am, ta gama komai, wanka ta shiga a gurguje, da niyyar ta shirya ta gudu zuwa makaranta , ba tare da sanin kowa ba.

Sai da ta tabbata ta aje ma Lamishi komai na buqata, sannan ta tafi ta sanya uniform ,ta rataya jakar ta, ta na saka takalmin ta ta ji kiran Lamishi, cikin faduwar gaba, tare da saddaqar wa akan ba zata makaranta ba yau ma ta tafi amsa kiran Lamishin,

"Na'am Umma gani"

"Dan uban ki Dan Talo ina kk Shirin tafiya? Kin nakasa ni sannan ki tafi zuwa makaranta? Baki wallah zuwa ko ina, je ki shirya ki bi Mai Buruji,"

Wani irin kuka Mubaraka ta fashe da shi ,a rayuwar ta ta tsani duk abinda zai hada ta da gidan gwamna, kuma ta na hango alamun Lamishi na son ta maida aikin gidan kamar na gado, tunda suna yi itama se ta yi shi.

"Dan soyayyar ki da Annabin rahama Umma kar ki aika ni gidan can, ki barni na tai zuwa makaranta, na kwana biyu ban tai ba, Umma..."

"Ki na ruhwa min baki ko se na fashe shi? ....Mai Buruji...ke Mai Buruji...in ke qare ku tai da wannan lalatacciyar, ta maye gurbi na, kin san sultana ta fara zuwa aiki,"

Mai Buruji da aka kwalawa kira ce ta shiga dakin sannan ta ce,

"Na ko ga Sultana na son Mubaraka, ya kamata mu tafi lokaci na wucewa"

Cikin kuka Mubaraka ta shige gaba, ko uniform din ma qin cirewa ta yi, suka tafi.

Sun isa gidan tara da rabi ta yi, Lawwali na tsaye jikin motar Sultana ya na jiran ta, uniform din nan sun sha guga sai sheqi suke, ga qamshi na tashi a jikin shi, waya yake da No 3 ya na sanar da shi duk abubuwan da suke faruwa, tare da neman sani akan wasu abubuwan da ya kamata su yi, rashin shi a wajen ba shi ke nufin tsayawar ta'addancin su ba, ta waya ya ke sanar da su duk wasu dabaru da makirce makircen nakasa mutane bayin Allah.

Tsayawa ya yi da maganar da yake, a daidai lokacin da mata guda biyu masu matuqar mahimmanci a rayuwar shi suka tsaya a gaban idanun shi.

Sultana ce ta fito cikin simple shigar ta mai kyau, da ɗaukan hankalin mai kallo, a daya gefen Mubaraka ce saye da uniform idanun ta sun yi jawur saboda kuka.

Wayar shi ya soke a aljihu ya nufi Mubaraka, cikin tsananin damuwar da ta bayyana a fuskar shi, jijiyar gefen goshin shi ta fito, cikin Muryar shi ta asalin dan daba ya ce,

"Wane ne? Wane me qarar kwanan ne ya sa ki kuka?"

Hawaye ne suka gangaro mata, Mai Buruji ce ta sakada za ta wuce ya mata wani mugun kallo ta koma ta tsaya cak, tare da fadin,

"Lawwali ina ni ina tabin Mubaraka? Ai ba karen maguzawa na yaccijen ba, walle ba ni ta ba, Lamishi ce ta hana ta zuwa makaranta, tace nan za ta taho, ta yi wa Sultana aiki, jiya ta samu turmushe"(targad'e)

Rintse idon shi ya yi, cikin baqin ciki ya kama hannun Mubaraka, sannan ya kalli Mai Buruji ya ce,

"Ke ki yi wa Sultana aiki, makaranta take so, makaranta zata je, so kuke ta zauna ta zama jahila kamar ni?"

Sultana na tsaye ta na mamakin abubuwan da ta ji kuma ta gani, dama Lawwali dan su Lamishi ne? Sai yanzu da ake magana ta ga kamannin shi da Mubaraka, duk da ba sosai bane, amma akwai kama ta jini, har yanayi ya mata da Lamishin ma.

Waje ya nufa dan sama mata adaidaita sahu duk da ya san hakan zai wahala a irin wannan unguwar, amma ba zai damu da nisan inda zai je ba, dan farin cikin qanwar shi.

Sun dan yi nisa Sultana ta daga murya ta ce,

"Auwal..ku shiga Mota mu aje ta makaranta ,sai mu wuce daga can"

Hanyar mota Sultana ta nufa, su ma suka juya suka koma wajen motar, durqusawa Mubaraka ta yi, ta gaida sultana ta amsa cikin kulawa, bude ma Mubaraka Lawwali ya fara yi, sannan ya zaga zai budewa Sultana, ta daga masa hannu, ta bude da kan ta ta shige .

Sai da ya dauki hanyar makarantar su Mubaraka sanan fushin shi ya fara tafiya, ba zai bari a tauye ta ba, ba zai bari a lalata rayuwar ta a tagayyarar da rayuwar ta kamar yanda aka yi wa tashi ba.

Sultana na kula da yanayin shi, tare da jinjina irin qaunar da yake ma qanwar tashi, ya kuma yi matuqar burge ta, sai ta ga qimar shi da darajar shi a idon ta.

Cikin murya mai taushi Sultana ta ce,

"Ashe Auwal Dan uwan ki ne? ...Auwal ashe ita ce qanwar ka da ka ke fadin ita kadai ke kiran ka da Auwal?"

Wata ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi, tare da sakin murmushin da ya bayyanar da irin son da yake ma qanwar tashi.

"Eh Ran ki shi dade, ita ta qauna ta da nika batu akai jiya"

"Allah Sarki, ashe ku din yaran Lamishi ne, na ji ki na fadin ta samu turmushe, ya yi tsanani ne sosai ?"

Dan bata rai Lawwali ya yi, dan ya qudirta da ya aje Sultana zai je gidan ya tada ma Lamishi da duk wani ragowar hankali da ya rage a jikin ta.

"Eh jiya ta fadi amma da sauqi an gyara mata, an dai ce ta bari har ya warke ne kar qafar ta samu matsala ,"

"Allah Sarki in kin je, ki ce ina diba ta, Allah shi bi da lahiya"

"Ameen, zan hwadi mata"

Burki ya ci a gaban makarantar su Mubaraka, goma har ta yi, ana qoqarin fita break, Mubaraka ta san me yake shirin yi, dan haka da sauri ta fita ta tare shi,

"Yah Auwal kar ka shiga dan Allah, in ma bulala ce za a min, na cancanta, kwana na biyu ban zo ba, yau na je late bai kamata ba, su nada 'yancin yi min komai, malamai na ne, ballantana ma ba zan shiga yanzu ba, saura yan mintuna a tashi break sai na hade da sauran ɗalibai kawai"

Kallon gate din ya yi, ya ga a bude yake, ya kalle ta ya ga ta na murmushi, bai san sanda shi ma murmushi ya kwace masa ba, sai ya nemi baqin cikin da yake ciki ya rasa,ya rasa kalar qaunar da yake ma qanwar shi, niyyar shi ya shiga ya buga masu warning akan kar a taba masa qanwa, amma ta hana.

Dafa kan ta ya yi, sannan ya rungume ta kadan, Sultana da ke kallon su cikin sha'awa da burgewa ce tai saurin daukan su a hoto ta na murmushi, hannu Lawwali ya zira aljihu ya bata dari biyar,sannan ya koma mota, ta na ta daga nasa hannu shi da Sultana ,sultana ma hannu ta daga mata, dauke da murmushi, zai tada motar kenan aka fita break, dan tsayawa ya so yi ya ga shigar Mubaraka, sai kuma ya fasa, ya bata ma Sultana lokaci matuqa ba tare da ya yi tunani Ba, sai a wannan lokacin ya ga tsaurin idon shi .

Hakuri ya dinga bawa Sultana, har sai da ta masa shiru, tunda ta ce ba komai, amma yaqi ya dena bata hakuri.

"Ran ki shi dade kin yi shiru, ko dai ba a yafe min laifi na bane?"

"Wa ya ce maka ka yi lehi? Ai kai lambar yabo ya kamata a baka, a matsayin ka na yayan da ya fi kowanne yaya so da qauna tare da kulawa ga qauna tai, ina ganin soyayya da kusanci na da Sultan amma naku, ya burge ni sosai"

"Koh Ran ki shi dade?ina godiya da yabawa, yabon ki ya fi duk wata lambar yabo ko girma da za a bani, "

Murmushi ta samu kan ta da yi, ba ta sake magana ba har suka isa, shi kuwa leqen ta ta madubi, shi ne ya zama aikin shi .

Bude mata qofar yayi, sannan ya take mata baya har office din ta, akwai mutanen da ta kula da su a jiya da ta ke bada taimakon nan, yau ma sun zo, su na ganin ta suka taso, fess da su,da alama mutane ne masu ilimi.

Har office suka je, Lawwali ne ya gabatar mata da su, domin ya san su, suma 'yan gwagwarmayar siyasar mahaifin ta ne, amma su mutane ne masu gaskiya da amana, gwamna na amfani da su in ya na son isar da saqon addini, ko kuma saqo wajen mutanen kirki, dan ya siye zuciyar mutane a ce shi din na Allah ne.

Ya rasa dama aikin da zai basu tun kafuwar gwamnatin shi, kullum suka je neman aiki hakuri yake basu, bude wannan NGO ya taimake shi sosai, dan haka ya ce su zo su taya sultana aikin.

Sultana ta ji dadin ganin su sosai , dan haka ba bata lokaci ta tattauna da su, ta kuma zabawa kowa bangaren da ya dace da shi .

Da taimakon su ta fara kasafin yanda zata gudanar da qungiyar, aiki ya sha kanta, da wannan damar Lawwali ya samu, ya tafi gida ba tare da sanin ta ba.

Ko da ya isa ya wuce Yabbuga a qofar gidan Asshibi, ta qurawa motar shi ido ta na son tai gulma dan bata gane motar waye ba,idon su karaf ya fada a na junan su, rakubewa ta yi a jikin ginin gidan Asshibi ta na salatin da ko iyawa ba ta gama yi ba,

Lawwali da ya san yanda Yabbuga ke mugun tsoron shi ne ya ci wani wawan burki dan nesa da su, ta na ganin haka, sai ta yi zaton baya ze yi ya je wajen su, bangaje Asshibi ta yi, ta afka gidan ta, ta na salati, ko ina na jikin ta rawa yake, Lawwali kuwa me zai banda dariya,qarasa wa ya yi gidan su,ya bude ya shige .

Lamishi na ta baccin ta hankali kwance.

A tsaye ya tsaya mata, ya ce

"Lamishi...Lamishi, shin kwana ki kai ko mi?"

Bude ido ta yi, tare da qanqance su, tsaki ta doka sannan ta ce,

"Sannu uba na, nicce sannu ubana, lalatacce tambadadde fado min a kai za ka yi? Ka tsaya min a ka kamar za ka hwado?"

"Ba wannan ya kawo ni ba, Barakana ba zata yi bautar gidan Gwauna ba,in ki na bari har ki ji sauqi tau, in baki bari ki hakura da aikin, ai dama kun tsufa barin ku kawai sun kai dan an saba, amma me kuke in kun tai?"

Kofin da ke gefen ta ta dauka ta maka masa a guiwa, ko gezau be ba, yo wace wahala ce shi be sha ba,

"Ka hwa rammin Lawwali, (ka fa raina ni Lawwali) in ce ga abinda za ai ka ce ah ah? Za ta dawo ta samen tunda ta kai qarata wajen ubana"

"Ni dai na fada maki, bata koma zuwa aiki wani gida, sai da son ran ta"

"Ka san bana jin magana, se ka buga zan gane me ka ke cewa ubana...kuma wane irin kaya ne na gani jikin ka? Jahili dai ka ke balle in ce ko aiki ka samu na taimakon qasa"

Ran shi ya yi mummunan baci da kalmar Jahili data jefe shi da ita, ba dan ya na musun shi din jahili bane, amma su waye silar zaman shi Jahilin?

Wani mugun kallo ya wurga mata, sannan ya sa kai ya bar gidan.

Zagin dai da ta saba, wanda shi ne ya dauki kaso saba'in na lalacewar shi, shi ta dinga qunduma masa, ta na maimaitawa, tare da fadin Mubaraka za ta same ta, su a dole qungiyar 'yan hadin kai, to duk abin su ita ta haife su, sai ta
Showing 27001 words to 30000 words out of 150481 words