sun fi su yin shiga mai kyau, da tsari, da burgewa.

Sai da aka gama wa mutum uku, sannan aka zo kan su, a lokacin qarfe goma na dare ta gota.

Style kala kala aka dinga nuna musu su kuwa su na kyafewa ana daukan su hoto, style din da suka ga ya sabawa shari'a in ance su yi, sai Sultana ko Lawwali d'aya daga cikin su yaqi.

A haka dai aka gama daukan su hotunan, wasu matasa ne suka gane Sultana, habaa manaa nan da nan waje ya cika da surutai kala kala, wasu na yabon ta, su na ta so a dauke su hoto da ita, wasu kuma na tsangwamar ta saboda mahaifin ta.

Lawwali bai tsaya biye wa shiririta ba, ya ja ta suka tafi gida.

Hajiya ta rude ta rikice da ta ga hotuna, ga su an tura musu ga waya, ga wasu sun taho da su a envelope,kallon Lawwali ta dinga yi daga sama har qasa, ko ba shi da arziki ya na da kyauwun huce takaici.

A cikin daren ta dinga dora hotunan a social media, qawayen ta kawai take jira su ga wannan hotunan, ta ga reaction din su akan mijin Sultanan ta.

Sultana ma ta dora hotunan a social media, musamman Instagram ,ganin yanda suka rude da kallon hotuna kamar basu da lokacin shi ne ya sanya Lawwali yin sallama da Sultan ya tafi gida.

Kayan shi ya cire ya tafi daji, domin ya na da mahimmin abu da ya ke so ya gudanar a can.................

*Biki bidiri buredeee*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 42:


Tokare take jikin gini, kamar wadda aka jingine, ta na ta dariyar yaqe, hannun ta dauke da kwano, shinkafa ce a ciki, ta sha ganyen zogale da quli, tumatur da albasa, da soyayyan mai, abincin da Lamishi ke matuqar so kenan.

"Ko ni mutan gidan ga ba su amsa sallama ne? Sai buga sallama nake tun garka shiru ka ke ji"

Lamishi ce ta fito, sanye da kayan da ta ke gwada wa, in da kudin ka yanzu za ka samu abinda ka ke nema, har sun samu ɗinkin da suka kai, guda bibbiyu, manyan leshi guda biyu atampa manya biyu, kowa d'aid'ai, sun siyo takalma da jakunkuna, sarqoqi da abun hannu, sai sabbin mayafai .

Lamishi ce ta yatsina baki ta ce,

"To wa ya ji ki mu na can mu na harikar azziqi"

"Ai fa, na ga harikar azziqi, mutumi na zai yi aure shi na ko a fad'i min, duk abin da ya faru a baya ai ke san sabanin harshe da haqori ne, to Allah shi sanya alkhairi, ni zan koma, ga gwaben shinkahwa na kawo miki, na san ki na so"

Wangale baki Lamishi ta yi, ta amshe kwano, ta gauraya gaban ta ta afa a baki, dad'in abun ne ya soki kunnen ta sai da ta sosa.

'Yabbuga na ganin haka ta saki jiki ta na zuba, ta ce wannan ta ce wancan, nan dai Lamishi ta manta da komai, suka hau hira akai ta bawa 'Yabbuga labarin abun azziqin da ke ta gudana a gidan.

"To ni dai ba wannan ba, ke dai ga bikin ga da  ya taho a qurarren lokaci, ko tuwahi sabo ban dunka ba, dama ya kai wata guda ne, da na sa Dan Jumma ya sai min Holan ko Suhwa, nima na daura ana bikin Babban d'a"

Dariya suka sanya sukai shewa, tare da tafawa,

"Kar ki damu, ina nan da wata da Hajiya Ikeelima tabban, ke san su irin wannan ba shi gaban su, sai su sa sutura su ɗebe su basuwa kyauta, anjima in sun gane ta ba su ganewa "

'Yabbuga guda ta kama hanci ta zabga, ji take kamar ta jawo goben a d'aura auren,

"Ohhhh Allah na gode maka, ashe da rabon zan daura suhwa a duniyar ga,Allah ya kaimu wannan rana da rai da lahiya"

"Ameeen, ki na da takalme da jikka?"

"Ina da su, amma tun wanda na ci bikin Kareema ne wallah"

"Kayya, ki ce baki da su kawai"

"Sai goben ki taho akwai wanda zan baki, na Mubaraka ne, Sultana tabbata su,"

Wani tsallan bad'ake 'Yabbuga ta buga ta yi baya, ta ce,

"Yo ance miki kwana na na yaqare da zan saka kayan Mubaraka? Banni na tai bukin ga lahiya mu dawo lahiya, ke san halin Lawwali akan abun Mubaraka, walle ba ze ji nauyin yagan rigar mutunci ba gaban kowa, banni na tai da tsohhin nawwa, ai guntun gatarin ka ya hi sari ka bani"

Dariya Mai Buruji ta ke ta yi, bayan ta dasa kujera a gefen Lamishi ta zauna.

"To bid'i wuri ki zauna in ke qare tsallen, matsoraciya, jiya kuwa yattaho, na san yau ma shi na nan tahe"

Rarraba ido 'Yabbuga ta fara, tuna ranar da ya dawo cikin bacin rai ta yi, ta na baccin wahala, takalmin ta ta shura ta ce,

"Too mutanen ga na yi gida, zan bawa bisashe(awaki/tumaki) ruwan yami, rabon su da ruwa tun jiya"

"Ke dai hwadi gaskiya, dan an ce Lawwali na tahe, shi na ki ka son gudu"

"Ko ni ba haka nan na ba, ai ko Allah sanya alheri ina tsayawa na yi mai, zan dai je ne na ba bisashe ruwa"

"To ya yi, jira na doko miki kayan da za ki saka goben"

Lamishi ce ta shiga ciki, ta dakko atamfar ta bawa 'Yabbuga, kaya ne kamar sababbi fess da su, Godiya ta yi ta yi, ta tafi.

Su kuwa suka ci gaba da shirin kayan zuwa biki, har lalle suka tsara za su daura a daren.

***************************

A gidan gwamna kuwa, ko ina ka wurga ido mutane ne, na birni da na kauye, Sultana ta yi mamakin ganin yawan mutane, ko dan ba a taba aurar da kowa a gidan bane, tunda sukai kudi, mahaifin su ya zama Gwamna dangi suka dena shiga jikin su, saboda tsabar wulaqanci da tozarcin da Hajiya Ikee ke musu, in ka ga ta kula wani a dangi, to fa ya na da maiqo,bata bar dangin ta ba, balle dangin miji, kowa ma tabawa take.

Sai gashi mutane sun yi hakuri da halayyar da ta musu a baya, sun zazzo bikin, domin zumuncin Allah ba dan halin ta ba.

Amarya ta sha gyaran jiki da gyaran gashi, duk inda Sultana ta wuce qamshi ke bin ta,a cikin yan uwan su, har da masu taba jikin ta, dan kawai su ji ya yake, tsabar kyaun da ta musu a ido.

Sultan kuwa na can na hada ma Sultana babban surprise din da ya san in ta gani sai ta yi murna sosai da sosai.

Washe gari kuwa da safe tun safiya ake qawata hall din da za a yi bikin na su, duk wanda ya ga yanda aka qawata wajen zai tabbatar da bikin na manya ne ba na qananan mutane ba.

Amarya da ango kuwa kyawun da suka yi ba mai faduwa ba ne.

Lawwali ba shi da abokan da suka wuce abokan shi na cikin daji, sabbin matasan da suka horar suka bari tsaro da gadin dajin nasu, su No 2, No 3 da no 5 su ne manyan abokan ango.

Da yamma kuwa Mota biyu Lawwali ya aika unguwar su, dan ya san sai su Lamishi sun yi gayya, ai kuwa motocin nan sai da aka cika su taf da mutane.

Su Aunty Asma'u, Khadeeja Katuru, Halima (Maman yayana),Khadeeja Jabo, Eeshaa, Maman Jasrah,Aunty Rumma,Ameena Saudia, Su uwar gida Sarautar mata Iyar Ilham, Ashwal, Mom Sawwama, Maman Husnah,Maman Muhseenah,Mum Basheer, kai da dukkan mutanen group din A GARIN MU, sai da suka samu mota guda ta kwashe su zuwa event center din nan.

Amarya Sultana kuwa a zaton ta tunda bata da qawaye Lawwali ne kawai zai je su tafi, sai ta ga an kawo motoci da yawa, da damar su gilashin su baqi ne, har wadda akai wa decoration wato ta amarya da ango, a tunanin ta sauran motocin da ke take musu baya securites ne a cikin su, haka ta shiga motar cike da son ganin irin kwalliyar da angon ta ya yi.

Lawwali ma Allah Allah yake ta qarasa shiga motar ya qarewa kwalliyar da ya hango ta baqin gilashin motar kallo.

Ana budewa qamshin su ya qauraya da na juna, kasa lumshe idanun su suka yi, saboda yanda suke kallon juna.

Kowannen su na godiya ga Allah, da ya haɗa shi da abokin rayuwa kyakkyawa kamar dan uwan shi.

Hawayen farin ciki ne suka fara sauka daga idanun Sultana, tissue lawwali ya miqa hannu gaban mota ya zaro, ya fara goge mata hawayen ta, duk abinnan da suke, masu video da hotuna na ta dauka.

Mai hoto guda daya aka samu ya zauna a gaban motar, da ya ga sun yi abinda ya burge shi sai kuji kyasss kyarasss ya dauki hoto.

A hankali motocin ke tafiya, har suka isa wajen event din, wani irin kidan waqar Hamisu breaker aka saki da ya yi wa amare, Lawwali ne ya fara fita, ya zagaya, ya budewa Sultana mota, ta fita, hannun ta na cikin nashi, kan ta a qasa, ta fara takawa, duqawa ya yi kadan ya mata rad'a a kunne, daga kai ta yi, a lokaci daya ta fashe da wani irin kukan farin ciki, hannun ta ta sanya bakin ta ta na zubar da hawayen farin ciki, ba kowa ta gani ba illa qawayen ta da suka yi karatu da ga na nan gida Nigeria har turawa na can qasar waje, sai tsirarun abokan Sultana da Sultan din kan shi, sun yi ankon baby pink din wani tsadadden material, larabawa da hausawan mu na nan sun yi rolling kan su da mayafai masu adon duwatsu.

Turawan cikin su kuwa an musu dinki daidai da yanayin su, an gyara gashin nan sai sheqi yake, an ci dogayen takalma masu tsini.

Yau kwanan su biyu a Nigeria, Sultan ne ya gayyace su, tare da tsara komai da ya kamata, duk da cewa a qurarran lokaci ne ya samu nasarar tsara abubuwan yanda ya kamata, a hotel din City king hotel Gusau, ya musu masauki.

Nan da nan kuwa suka dinga zuwa daya bayan daya suna gaisawa da Sultana, ana rungume rungume ,da sumbace sumbace irin na gaisuwar mutanen qasashen turawa.

Sai da suka gama tsaf ta taka zuwa gaban Sultan,ta rungume shi da kyau, ta na kuka tare da yi masa godiya.

Share mata hawaye ya dinga yi, ya na girgiza mata kai, shiru ta yi, ta na murmushi, basu shiga main wajen taron ba, sai da suka je wani daki a hotel din da ake taron, aka gyara mata kwalliyar ta, sannan qawaye suka fara shiga aka sanya amarya da ango a tsakiya, ana tafe  Hamisu breaker na waqe su.

Ranar su 'Yabbuga an yi ciniki, dan duk kudin da iska tai gangancin kawo shi wajen zaman su, to fa b'atan dabo yake, ba a sake ganin shi .

Biki ya yi biki, Hajiya Ikee da qawayen ta, sun samu abinda suke so, an ci, an sha, an raqashe, an watsa kudi,su Asshibi, sai kallon turawa ake ana musu hoto, Mai Buruji da Lamishi kuwa sai fad'i ake wa mutanen unguwa ana tinqahon bikin d'an su ake.

Lawwali kuwa can qasan ran shi kewar Mubarakan shi yake, ana hidimar bikin shi amma bata nan, da gwamna bai mishi abinda ya masa ba da tuni, auren nan, da zuciya daya za a yi shi, ba wata boyayyar manufa, da tuni masoyiyar shi, kuma qanwar shi abar qaunar shi na wajen, in ma ya kyale gwamna bai rama abinda ya masa ba a rayuwa ai bai cika dan halak ba.........

*Wai ni dan Allah ba za a hakura da wannan daukan fansa bane??*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH

PAGE 43:



An tashi taro lafiya, babu wani wanda ya tafi da qorafin bai samu abun biki ba, ko bai ci ya qoshi ba.

Bangaren su Lamishi kuwa ta so su gaisa da Hajiya Ikee da qawayen ta, ko dan ta qara kankaro wa kan ta aji da mutunci, wajen mutanen unguwar su, amma haka Hajiya Ikee ta dauke kai, ta na yatsina ta ce musu ta na zuwa, ko da ta tafi sallama tai ta yi da qawayen ta da suke komawa gidajen su, ta na gama sallamar su, ta tafi ta ta motar, aka ja ta sai gida.

Haka su Lamishi suka gaji da jira suma aka kwashe su sai gida, Sultana ranar a hotel din da qawayen ta suke ta kwana, duk da Lawwali ya so ya maida ta gida,amma ta nuna masa rashin dacewar hakan, tunda dan ita suka zo.

Ai kuwa kwana suka yi su na hira, suka ci suka sha, suka yi games kala kala, irin na al'adun wasu qasashen.

Basu suka kwanta bacci ba sai bayan sun yi sallar asuba, su na idarwa kuwa suka hau baccin gajiya.

Sha daya na rana suka tashi, suka hau wanka, da shirin tafiya gidan Gwamna, yau za a Daura auren Sultana da Lawwali, masu gyaran jiki da kwalliya sun hallara, nan da nan amarya da qawayen ta suka sha gayu, ankon purple din yadi suka sanya, amarya ta saka nata kalar golden da milk, qamshi sai tashi yake ko ta ina, in ka kalli wannan sai ka ga kamar tafi kowa kyau a wajen, da ka kalli 'yar uwar ta sai ka ga ta doke ta farkon kyau , kowacce na ji da kyau, aji, ilimi, da gayu.

Manyan motocin da suka je daukan su abun kallo ne, cike da nutsuwa ake tuqa su har zuwa gidan Gwamna halliru, tin daga farkon layin unguwar har qarshen shi motoci ne, na alfarma, matan manya ne danqam a cikin gidan, wasu daga wasu garuruwan suka zo, wasu a cikin garin suke.

Amarya na shiga gidan hankali ya koma kan ta da qawayen ta, Sultana ta gode ma Sultan a ran ta ya fi sau a qirga, ba dan shi ba da sai dai ta yi ta yawo ba qawaye, da kuwa abun bai yi armashi ba.

Bayan an yi sallar azahar ne aka daura auren Auwal da Sultana a Central mosque, da ke cikin garin na Gusau, a kan sadaki Naira dubu dari biyar, lokacin da Dan Talo ya ga Uban kudin da Lawwali ya damqa masa a hannun shi ya ce na sadaki ne, ji ya yi kamar ya suma dan takaici, a cewar shi wannan qarawa mai qarfi qarfi ne ai.

Haka dai ba dan ya so ba ya bada sadakin nan.

Kowa ka gani cikin farin ciki yake, Lawwali kuwa ba a magana, bakin shi ya qi rufuwa, sai doka murmushi yake, daga qasan zuciyar shi, ya na jin wani irin dadi mara misaltusa, kwanciyar hankali da nutsuwa ta baibaye shi.

Bangaren gwamna Halliru kuwa, zuciyar shi baqiqqirin haka yake jin ta, amma haka yake ta murmushi da dariyar dole, ga mutanen da suka halarci daurin auren.

Lawwali ne ya ja abokan shi gefe ya ce musu,

"To an daura auren hwa, daga yanzu zuwa kowane lokaci wasan zai fara"

"To Oga, muna maka fatan alkhairi"

"Godiya ni ke, da irin jajircewar ku, da tsaya min bisa gaskiya da amana, sai na taho"

Sallama suka mishi, suka koma inda suka fi wayo, masu iyalin cikin su, sai da suka leqa iyalin su, da iyayen su, sannan suka tafi daji.

*************************

Gidan Alhaji Dan Talo mutane ne danqam,Lawwali ya saki bakin aljihu, sai wadaqa ake da abinci da abun sha, Hajiya aunty 'Yabbuga su ne akan abinci, sai abinda tace a zuba, a gefe kuwa Kareema 'yar ta ta zo itama, sai ta debi kaji, da drinks ta boye a zani, ta wurga mata, ita kuma Kareema ta dauke ta kai gida, in ta juye ta koma, haka suka dinga yi, sai da 'Yabbuga ta tara naman kaza me yawa da snarks da drinks .

Kusan duk wanda ya zo daga kan 'yan uwan Lamishi da Mai Buruji, da Dan Talo sai da suka yi ta tambayar Mubaraka, Lamishi ba ta da amsar bayarwa, dan haka sai ta shashantar da maganar, Mai Buruji ce ta qirqiri karya ta ce Yayan ta ya kai ta karatu qasar waje,shi ya sa ba a gan ta ba.

Ba qaramin dad'in wannan qaryar Lamishi ta ji ba, sai ta ji ta qara son kishiyar ta ta, Dan kuwa Mai Buruji abokiyar zama ce ta gari.

Lawwali ya sanar da su, ba sai sun je daukan amarya ba, shi da kan shi zai dau amaryar shi, su yi bikin su kawai anan.

****************************

Kamar yanda al'adar amare take, yin kuka a duk sanda za a kai yarinya dakin mijin ta, Sultana ma, ba a barta a baya ba, daga ita har Gwamna Halliru kuka suke, Hajiya Ikee kuwa idon ta kyamas ba alamar hawaye, sai dariya take musu, Gwamna Halliru na matuqar ji da Sultana, gashi ya zama dole a gare shi ya hannun ta ta zuwa ga Lawwali, Lawwali da kanshi ya je daukan amarya, ko aboki daya bai raka shi ba, Hajiya Ikee ta tanadi wanda za su raka amarya dakin ta, ba su da wani yawa.

Da kyar Sultan ya samu ya banbare Sultana daga jikin Gwamna Halliru, ya na kuka, itama ta na kuka, haka Sultan ya damqa ta a hannun Lawwali, wanda ya ke jin zuciyar shi ta karye matuqa.

Anya zai iya bada auren Mubaraka kuwa? Wani iri yake ji a zuciyar shi na rauni, wanda ya sanya shi zubar hawaye, bashi da abinda yake so sama da mubaraka a rayuwar shi, nisan da ta mishi ba qaramin qona zuciyar shi yake ba, kallon gwamna Halliru yayi, cikin tsananin takaici da tsana ba dan shi ba, da tini da Mubaraka a wajen.

Da sauri ya ja Sultana suka shige motar da ya zo da ita.

Hajiya Ikee sai da ta ga Sultana a mota ta tabbata tafiya zata yi, sannan ta ji hawaye na gangare mata, daga musu hannu mutane suka dinga yi, mota biyar ne suka dafe musu baya, dan raka amarya dakin mijin ta.

Gidan da Lawwali ke da zama suka nufa, gidan ya sha gyara, an qawata shi sosai da sosai .

Lawwali qin bude motar ya yi, ya ce ma driver ya sanar da su, su shiga su ga gida, in sun gama su tafi, da kan shi zai shigar da amaryar shi.

Dariya mutane suka dinga yi, su na ganin he is very romantic, qawayen ta dik sun mata sallama, kuma sun shiga sun ga waje, sun yaba, mota suka koma aka maida su hotel din da suka sauka, washegari kowa zata koma garin su da qasar su.

Sai da wajen ya rage daga Sultana sai
Showing 90001 words to 93000 words out of 150481 words