idaniyar shi a idon shi ba ba zai ji salama ba, bai san me zai iya aikatawa ba.

Ko da ya isa gida kuwa, ya yi sallama Mai buruji da Kameelu ne suka amsa shi, Kameelu ya tafi da sauri ya na ma yayan nasu sannu da zuwa, ya ga ba walwala a tattare dashi, nan take ya ce,

"Yah Lawwali Mubaraka kuwa bata nan, tun da ta tafi makarantar boko bata dawo ba, wataqila ta wuce islamiyya daga can"

Idanun shi ne suka kada suka yi jawur, cikin d'aga murya yace,

"Miii ! Mi ka ce? Ina ta tai? Yanzu hwa mangariba ake kira, ina ta tsaya?"

Lamishi ce ta fito daga dakin ta, ta tsartar da yawu, ta na saka takalmi ta na daura zani ta ce,

"Ina ko ta tafi banda gantali, na ce kar ta tai makarantar wahalar ga amma sai da tassa qafa ta hita, in ma sace ta ank....."

Wani duka Lawwali ya kai wa randar da ke tsakiyar gidan, sai da ta tarwatse, ruwan cikin ta ya baje a wajen, ba Mai Buruji ba da ta riga ta fara tsorata da yanayin da ya shigo da shi ba, hatta ita 'yar taurin wato Lamishi sai da ta shiga taitayin ta, kameelu kuwa a guje ya bar gidan, cikin hargowa ya kalli Lamishi yace,

"Ina raga maki ne saboda Baraka na, duk wani abu ya same ta, sai na yi ajalin ki"

Yanayin yanda ya yi maganar ya kad'awa Lamishi hanji, a rayuwar ta kafff yau ce rana ta farko da ta ji tsoron d'an nata, ashe kyale ta yake saboda Mubaraka na hana shi, Dan Talo da ya  so shiga gidan dan ganin motar Lawwali ne, ya ji ana tashin hankalin nan, ya koma cikin sanda ba tare da kowa ya ga shigar shi ba, balle fitar shi.

Dakin shi ya shige ya dinga wurgi da duk wani abu da hannun shi ya kai wajen,  tunawa ya yi da ya sai mata waya, kiran wayar ya fara, amma ta na ringing ba a daga ba, wata qara ya saki, sannan ya daki qofar dakin da qafar shi, sai da ta balle tai qasa.

Mai Buruji ta gama shiga tashin hankali ,mayafin ta a hannu ta fice a gidan cikin sanda, ta afka gidan Yabbuga.

Lawwali ne ya sake kiran No Mubaraka aka ce, a kashe take, ihu ya saka, tare da zabura ya fita ya bar dakin , a guje ya ja motar shi ya bar gidan...........

*Mubaraka Allah ya sa ba gidan qawaye ki ka fara bi ba, tunda an fara sa manyan kaya, Lols*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 25:

Ko da ta farfaɗo,kwance ta gan ta a wani gado madaidaici, wanda da alama sabo ne dan katifar shi ma ko leda ba a cire ba, haka aka saka ta, mirror da komai na dakin sabo ne, hatta da fentin dakin, sabo ne, kamar irin dakin sabuwar amaryar nan.

Gefen ta ta kalla, a yayin da ta ji kafar ta ta yi nauyi, Murjanatu ce a hannun ta na hagu, ta danne mata qafa da jikin ta, dayan hannun ta na dama kuwa Saliha ce.

Tunanin baya ta fara yi.

Ta kammala duk wani aikin ta na ranar, ta shirya dan tafiya makarantar boko, Lamishi ta hana ta, ta ce ba inda zata ta zauna ta jire gida, ta yi magiya, ta yi roqo amma inaaa, fafur Lamishi ta ce ta zauna ta jire gida, in ba yawon tazubar zata ba, karatu dai an jima ba aje ba mi za ta gane yanzu?

Bayan sun tafi, Mubaraka na zaune gidan shiru, kawai sai dabara ta fado mata, ta kuwa sake shirin makaranta, ta dura hijab da niqab din islamiyya, ta dauki kudi cikin wanda Yah Auwal din ta ya bata, shago ta je, ta sai kwado, aka bata mai kyau, me kwari.

Ta na zuwa ta samu ko ina ta rufe, ta sa kwado ta garqame qidan, ta kai wa Yabbuga ajiyar key, ta ce ta yi makaranta .

Da azahar an tashi boko, ta tsaya a makarantar har lokacin islamiyya ya yi, dan ta san bata isa zuwa gidan gwamna ba, Lamishi na can, Auwal na can za su yi rikici a gaban mutane.

Saliha da Murjanatu yaran mutum guda ne, jinin su ya hadu da Mubaraka, kasancewar ta mai qoqari, su kuma su na son mutum me qoqari da kamun kai, (Sai hali ya zo daya ake abota), dan haka suke qawance, boko da islamiyya, su na zaune da iyayen su anan unguwar Tudun Faila.

Sun roqi Mubraka da su tafi gidan su, in za su islamiyya sai su tafi tare .

Haka kuwa aka yi, da misalin qarfe uku, na rana, sun ci abinci sun yi wanka, sun shirya cikin kayan makarantar su, sun sanya niqabin su.

Tafe suke su na hira, suka ji an taka wani wawan birki, a gaban su, kafin su gama tunanin me ya faru, an dauke su cak kamar wasu leda an watsa a mota Bus, ihun su ya qare ne a lokacin da No 4 ya zira hannun shi cikin niqabin su ya shaqa masu wani abu, suka hau bacci.

Tun daga nan suke bacci ba su san a inda suke ba, sai a wannan lokacin da ta farka .

Tashin su Saliha ta yi, ta na qoqarin yin kuka, su na farkawa suka hau ihu, No 4 ne ya bude qofar ya shiga hannun shi dauke da wata qatuwar bindiga ya na muzurai, tare da fadin.

"Ko ku mana shiru ko na tarwatsa kan yarinya,"

Kamar an yi ruwa an dauke, haka suka yi shiru, sun qanqame junan su, su na rawar jiki, No 1 ne ya shiga, fuskar shi a rufe, idanun shi ne kawai a waje, hatta da hannun shi da qafa duk a rufe suke, cikin kakkausar murya ya ce,

"Ke ! Zo nan"

Cikin rashin fahimta Saliha ta miqe ta je, wani mummunan duka ya kai mata sai da ta juya, ta kidime,

"Da ke nake? Ke kuma inna sake kiran ki ba ki zo ba, za ki ga yanda zan lahantar da ke,"

Cikin rawar jiki, Mubaraka ta miqe,dan kuwa ya nuna ta da yatsa, ta san da ita yake tabbas, amma gudun kar ya dake ta ta tsaya daga nesa.

"Ba zaki zo ba kenan?"

Da sauri ta isa gaban shi, ko ina na jikin ta rawa yake, tsabar tsoro,hijabin ta ya cire ya yi wurgi da shi,sannan ya tuge dankwalin ta, gashin ta irin na hausawa mai cika ya kalla, cikar shi da tashon shi sun burge shi,hannu ya kai zai taba, ta yi baya da sauri tare da fadin,

"A'uzu billahi,meye haka ka ke yi, ko baka san haram bane ka taba ni"

Wata iriyar dariya ya kwashe da ita, sannan ya nuna ta da hannun shi manuni, ya ce,

"Ke, ke ce ke fad'in an tabi haramun? Qaunar Lawwali ka batun haramun?"

Hannun shi ya sa gaba daya ya fizgeta ta fada jikin shi da qarfi, qara ta saka, ya kuwa wanke ta da mari se da bakin ta ya fashe, jini ya dinga diga, kuka ta fashe da shi ta na kiran sunan Allah, akan ya kawo masu agaji, Lawwali ne ya fado mata a rai, nan da nan ta kalli bawan Allahn da ya mare ta, kallo ta bishi da shi daga sama har qasa, tabbas shi ne, abokin Yah Auwal, wanda ta ji ya na kira da No 1, cikin rawar murya, ta furta,

"No 1?"

Da sauri No 4 ya fita daga dakin hankalin shi a tashe, zufa na tsattsafowa daga kowacce kafa ta jikin shi,cikin tashin hankali ya kira wayar No 1, shi kuwa ya na ciki ya na ganawa Mubaraka azaba, bai so ta gane shi ba, ya na ganin kiran No 4 ya sake ta ta fad'a cikin su Murjanatu,nan da nan kuwa suka rungume ta, su na lallashi.

Ya na fita No 4 ya ce,

"Dama ka san da qaunar Oga a cikin su? Garin ya ankai muka dakko da qaunar Oga? Ba cewa ka yi wata qaunar abokin ka za mu dauka ba? walle ba ruwa na in oga Lawwali ya gano kai ka ɗauke ta, kar ka kira suna na, ina da iyali, ina da mahaifiya da tai yi min saura, ban shirya mutuwa ba ni da dangi na"

Wata tsawa No 1 ya sake ma No 4,

"Wai kai me ye haka? Kana wani tsoron shi kamar  ba namiji ba? Yanda ya ke jin shi shege ne mu ma muna jin kan mu, kuma ka na ganin da mun tsaya diba wadda nika batu ka na ganin ba za a kama mu ba? Dallah be a man, yanzu ka tai zuwa samo musu abinci mu kulle gida mu koma daji, kahin a kula bamu nan"

No 4 dai bai gama daukan wannan maganganun ba, a mugun tsorace yake, gani yake kamar zai ga Lawwali a gaban shi, cikin rawar jiki ya tafi ya samo masu binci, da ruwa, da duk wani abu da ya kamata su yi amfani da shi, dayan dakin dake can lungun gidan suka maida su, dakin na dauke da bayi, da babban gado, su na wurga su suka rufe gidan, sannan suka tsorata su da fadin akwai masu gadi, in suka ji kwakkwaran motsin su, sun bada umarnin a shiga a harbe su.

Ko da suka fita daga gidan, ina dubawa sai na ga wajen sabuwar unguwa ce,ba gidaje sosai, Bus suka shige suka dauki hanyar da zata sada su da maboyar su.

***********************

Lawwali ya firgice ya haukace wajen neman Mubaraka, tsakanin makarantar su ta boko da islamiyya da unguwar su ya yi zuwa ba iyaka, daga baya gida gidan yan makarantar su ya dinga bi ya na tambayar sanda suka gan ta na qarshe, jikin Lamishi kan ta sai da ya fara sanyi, Dan Talo kuwa ya na can yawon bin abokai, bai san me ke faruwa ba, sai wajejen sha daya da ya dawo ya ji Muryar Lawwali cikin maye ya na ta ashar tare da alwashin in ba a gan ta ba a gobe sai ya yi ajalin Lamishi, mugun bakin ta ne da tsanar da take wa Mubaraka ya ja ta bar gida.

Lamishi fa yanzu tsoron d'an nata ya gama shiga kowacce kafa ta jikin ta, basu taba ganin shi cikin matsanancin hali irin wannan ba, ya farfasa musu abubuwan amfani, ya jiwa kan shi rauni kala kala, ga shi ya kasa kokawa, banda huci ba abinda ya ke fitar wa kamar wani damisa.

Dan Talo qin shiga gidan ya yi, ya labe a waje, (uban banza kenan) jira yake ya samu Lawwali ya shiga dakin shi ya afka gidan, in ya so a nutse ya tambaya ya ji ina Mubarakar ta tafi.

Da misalin sha daya da rabi  na dare Lawwali ya gama yanke shawara, makullin motar shi ya dauka,ya ja qofar shi zai fice, Dan Talo na maqale ya ji motsi, kwanar gidan ya sha a guje, Mai Buruji da Yabbuga na tafe su na tattauna tashin hankalin yau da Lawwali ke ta yi a unguwar, Yabbuga na fadin, da an sha kwana za ta koma, bata fatan had'uwa da shi ya na lafiya ma balle yanzu da yake a fusace.

A guje suka ga Dan Talo, su ma diba suka yi a guje Yabbuga ta yarda yar kwabirar wayar ta rakani kashi, sai ihu take ta na kiran Dan Jumma tare da zagin shi ta na fadin ya na sane ya qi raka su.

Dan Talo ya riga su fad'awa gidan su Yabbuga, dafe da qirji suka same shi ya na maida numfashi, Dan Jumma ne ya fito a tsorace ya na tambayar waye.

"Mi na na kun ka shigon gida haka  a guje kamar wad'anda aka biyo? Yaqi akai halan?"

"Yaqi ake amma a gida na, wannan shegiyar yarinyar ce ta tafi yawo, bata dawo ba, ta ja muna bala'i, hatta da gambun gidan nan bai tsira ba, sai da Yaron nan ya ɗebe shi yau, komi ya hwashe ya lalata, na jiyo ya na fadawa Lamishi gobe in ba a ga Mubaraka ba sai ya yi jalin ta, ban ko wallah shiga shi gama da ni"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, anya Dan Talo kun yi addu'a kuwa? Yaro awa diyan shedannu? Bashi jin maganar kowa sai dai a ji tashi?"

"Ke Yabbuga shige ciki, kai kuma, dan Allah ka kama matar ka ku tafi gida, kuma da ka ke fad'in Mubaraka ta tahi yawo, ka hini sanin halin ta, iya sani na da ita ba za ai mata shaidar yawo ba, yarinya ce me hankali ,ko tunanin wani abun ne ya same ta baku yi, ku kam Allah ya yi muku sauqi, (gyara tsayuwar shi Ɗan jumma ya yi, ya na kada hannu, ya ce) zan ruhe gida"

Cikin sanyin jiki Mai buruji ta bi Dan Talo da jiki ya wa sanyi, sai yanzu maganar batan Mubarakan ya fara shigar shi, tabbas ita ba me yawo bace, kawai dai yawan fad'a da Lamishi ke yi ne ya sa shi ma yake fada.

Su na shan kwana suka tsaya cak, sai da suka tabbatar motar Lawwali bata nan, suka qarasa.

Su na shiga suka ga Lamishi na hada kayan ta, cikin tashin hankali, Dan Talo na tsaye a bakin qofar shiga dakin ya ce,

"Ke kuma mi na na ki ka yi haka? Ina zaki da wanga tsohon dare?"

"Gidan iyaye na zan tafi, tunda d'an da na haifa da ciki na ya ce  sai ya yi ajali na akan qaunar shi, diyar da ni na haihe ta da ciki na, wanga wanne irin bala'i na? Ka dai san yadda Yaron nan shike ko?"

"Tau in kin tai can an ce maki barin ki zai? Kin ga kin ja musu musiba, gwanda ki zauna, gobe mu tai bid'ar ta gaba dayan mu, ki yi tunani dai"

Shiru ta yi, ta na nazari,to ina Mubaraka ta tai? Ita din ba me yawo ba ce, (sai yanzu ta san ba me yawo bace, duk sunayen da take kiran ta da su).

***********************

A hargitse ya shiga dajin, kowa ya san Oga ba lafiya a daren,dan haka kowa ya nutsu, No 1 da sauran yaran shi na kusa ne suka bi shi a baya, dakin da suke ajiye mutanen da suka sato, 'yan uwan su sun kasa biyan kudin fansa ya shiga ,firfito da su ya sa aka dinga yi, sai da ya fidda wajen mutum biyar sannan ya jera su a filin wajen, idanun shi kadai abin tsoro ne, bindigar da aka cika da harsashi ya karba ya dinga kai musu harbi, sai da ya harbe su tass, sannan ya koma dakin shi da ke wajen, ma'ajiyar giyar shi ya je ya bude,ya jima kwarai  rabon shi da shan giya ,dakko kwalba ɗaya ya yi, ya kafa kai, bai aje ba sai da ya sha ta kusan rabi, wata iriyar razananniyar qara ya saki, ya buga kwalbar a qasa, wannan qarar ta firgita No 4 ba kadan ba, hankalin shi ya yi bala'in tashi, tsoro ya hana shi tunanin mafita.

In ya ce ze sanar da gaskiya,ya san bai tsira ba, in ya bari har Lawwali ya gano da kan shi nan ma bai tsira ba, ya zai yi??????

*Ina nissani?*

[6/21, 5:15 PM] HAERMEEBRAERH ❤️: 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻



BY HAERMEEBRAERH



PAGE 27:





Sati biyu ya wuce ba Lawwali ba bayanin shi, ba Sultana kadai ba, hatta da Gwamna Halliru ya fara shiga tashin hankali akan lamarin Lawwali.

Duk wata barna da ta'asa da Lawwali ke aikatawa ta na komawa kunnen Gwamna Halliru, ga zabe ya gabato sauran kwana goma sha uku, lamarin ya tabarbare fiye da tunanin Gwamna, domin kuwa a yanzu Lawwali ko cikin gari bai cika shiga ba, sai jefi jefi dan ya ji halin da ake ciki game da neman qanwar shi da ya sa a yi.

Lawwali ya koma kamar mahauci, akan neman Mubaraka, ya yi kuka har ba iyaka, ya zama kamar wanda ya rasa iyayen shi da dangin shi a dare daya.

Duk wata motar da ta yi tsautsayin bi ta kusa da dajin su, to sunan su matattu, ko kuma ya sa a kame su, ayi ta azabtar wa, ko ya sa a yi ta amsar kudi wajen dangin su, madadin batan Mubraka ya risinar da shi,sai ya sake ruruta masa wutar rashin imani a zuciyar shi.

Sultana kuwa duk ta fige ta rame saboda rashin Lawwali, ko ta je Foundation din ma watarana da kuka take komawa gida, rashin ganin shi a idanun ta ba karamin azabtar da zuciyar ta yake ba.

Duk ta dora laifin akan Hajiya, domin a tunanin ta maganar da Hajiya ta yi ne ya sanya shi yin fushi ya tafi.

Ta gwada No shi ya fi sau shurin masaqi amma ta qi shiga, kullum sanar da ita ake a kashe wayar take, ta yi kuka ta godewa Allah, ta yi sallah ta yi addu'a akan Allah ya dawo mata da shi in da alkhairi, in babu Allah ya sa mata hakuri da dangana, hakan da ta yi ne ya sa ta ɗan samu sauqi kadan a ran ta, har ta ci gaba da aikin alkhairin da ta sa wa ran ta.

Shiru shirun ta, da rashin shiga mutane da take ya bawa Gwamna damar yada abubuwan da take na alkhairi a gidajen talabijin da rediyo, da duk wata kafar sadarwa, mutane kuwa na ta yabawa, wasu na qara neman taimako a wajen ta, ita kuwa hakan na mata dadi, ganin aikin da take ya na ta bunqasa.

In ta na aikin ta na samun nutsuwa da kwanciyar hankali,da ta dawo gida komai sai ya kwance mata ,ba abinda take gani a idon ta in ba Lawwali ba, tsayuwar shi a jikin mota, da murmushin shi mai sauti, yanayin yanda yake kafe ta da ido, ya na kallon ta, sai ta ji kamar a wannan lokacin ya ke kallon nata, har lumshe ido take, watarana ta yi murmushi in ta tuna, watarana ta fashe da kuka.

An shiga sati na Uku Lawwali be bayyana ba, sai wata safiyar Lahadi, ya shiga gari, direct wajen aski ya nufa,a ka yi masa aski me kyau, aka masa gyaran qafafu da hannuwa, sannan ya sayi turaruka, da kayan abinci ya nufi gidan shi,ko da ya shiga gidan duk ya yi qura, kallon ko ina ya yi, cikin sanyin jiki ya ajiye ledojin hannun shi ya kalli ko ina, wasu irin zaratan hawaye ne masu zafi
Showing 45001 words to 48000 words out of 150481 words