matan da suka kwamushe, Dan haka yaron shi Mai kula da wajen in baya Nan ya aika, ya kwaso Mata uku su raba abinci, haka kuwa aka Yi, kowa ya ci ya qoshi, daga qarshe Lawwali shi ma ya samu ya ci a nitse.

A wajen ba a Kiran kowa da sunan shi saboda tsaro, Lawwali Oga suke ce Masa direct, daga Mai bi Masa zuwa mutum.biyar da ke qarqashin shi, da Number ake Kiran su.

No 1 shi ne Mai bi ma Lawwali, sai No 2 Mai bi Masa, haka haka, har No 5.

A cikin mutanen da aka kwamushe akwai wadan da iyayen su ko 'yan Uwan su sun zaci sun rasu, domin an amshi kudin fansar su, Kuma an qi maida su gida, sun fi shekara a wajen, sun Saba ma da wajen, wasu Kuma har yanzu ba su Saba ba, Neman duk wata hanya da zata fidda su ta maida su wajen ahalin su suke, musamman manya masu hankali.

Wasu Kuma sabbin zuwa ne, bangaren sabbi daban na tsoffin zuwa ma daban, wasu daga yaran Lawwali sun Yi 'yan Mata a wajen, su na dik wani abu da suka so da su, cikin sauqi, ba tare da sun takura su ba, Lawwali ya San da hakan, Kuma bai Hana ba.

Wajen ya zama kamar prison ga wasu, wasu Kuma kamar unguwa suka je, su na saka ran komawa gida watarana, wasu Kuma kamar gida Suka dauki wajen, kowa da yanda yake ganin wajen.

In ba an samu akasi kamar na yau ba, a wadace suke Koda yaushe da abinci, ruwa da dik abinda suke buqata, wutar lantarki ce kawai babu a wajen.

**********************

Watarana Mubaraka ta dawo daga makaranta, ta gama cire Kaya ta Yi wanka, ta shirya, ta dau abincin ta, ta fara ci, Lawwali  ya shiga kamar kullum ba sallama.

Sanye yake da qananan Kaya kamar ko da yaushe, sun Yi matuqar Masa kyau, zama ya Yi a kusa da ita, suna ma juna murmushi, hannu ya sa ya amshi spoon din ta, ya Yi Loma daya, sannan ya Bata a baki.

"Yah Auwal ni fa ba yarinya bace"

"A waje na ke jaririya ce har yanzu"

Murmushi suka Yi a tare, ledar da ya shiga da ita ya janyo, ya dudduba, wata Yar madaidaiciya ya dakko, ya bude masu, sannan ya ja kujera qarama ya zauna da kyau.

Nama ne gasasshe a ciki, zuba masu ya yi. Saman abincin ya ce su ci,

"Na Yi kewar cin abinci da Kai Yayana"

"Nima haka qanwa ta"

"Amma za mu ragewa su Umma ko?"

"Ga nasu can, wannan namu ne, Ina sane na zo yanzu, na San kin dawo, ko Zaki ci abinci, ko ki na wanka, "

"Sai Kuma gani Ina ma cin abincin, da na qoshi ka kawo da na Yi fushi"

"Ai Ina aiki da lokaci, na san ma baki ci ba"

Sama akai da kwanon, ana masifa.

"Lawwali zaka ci uban ka Wallah ita d'ai ta a gidan da ka bata nama hakan ga Mai yawa?"

Cikin Bata rai Lawwali ya ja ledar gefen shi ya cire wata Leda ya miqawa Lamishi,

"Aje Mana abincin mu, ga naku Nan, Dan mugun kwadai ya maki yawa Lamishi wanga nama da bai da yawa shi na ki ka wa baqin ciki mu ci, Wanda kuka ci gidan Gwauna in an hada da wanga ko rabi be ba,"

"Uban ka ke bamu nama a gidan Gwauna?"

"Lamishi na fada maki ki dena zagi na ko,"

"Mi zaka min Dan uban ka? Waje ka ke Zaki, gida mussa ka ke wallah"

Dariya Mubaraka ta Yi, Dan ita dariya suke Bata, cikin dariya ta ce

"Yah Auwal tsaya biyewa Umma na canye"

Da dariya Shima ya Debi biyu a tare ya sa a bakin shi, Lamishi da ta ga ta na ta masifa Basu kula ta ba, sai kawai ta tafi, ta na tafe ta na laluba ledar, ta na diban naman ta na watsawa a baki, kafin ta raba masu ta ci da yawa.

Bayan Lawwali ya gama cin abinci da Mubaraka, sai ya Kira ta dakin shi, ta zauna bakin gadon shi, Mai kyau kamar na wata amaryar.

Waya ya zaro ya miqa Mata.

"Ga taki, kin huta da aron ta Lamishi ana zagin ki, za ki iya Kira na duk sanda kk so, zan dinga saka maki Kati akai akai"

Murna a wajen Mubaraka ba a magana, sai dai can qasan ran ta, ta San ba kudin halal bane, har ta gaji da Yi ma Yayan nata nasiha, yanzu Addu'a ta koma Yi masa, ta na fatan watarana Allah ya amsa ya daina aikata dik wani abu Mara kyau.......

Shin ku na ganin wata Rana Lawwali zai daina halayyar shi kuwa?????

A GARIN MU










WRITTEN BY HAERMEEBRAERH








PAGE 8:



Da yamma liss su Yabbuga suka Yi qungiya guda, zuwa gidan sabuwar maqociyar su Lamishi, Yabbuga ita ce a gaba, ita a dole ta San matar gidan.

Sun jima su na buga gidan, har Lamishi ta fara jin haushi ta ce su tafi, amma dake Yabbuga na tsananin son Shiga gidan sai ta ce,

"Ke wataqila kwana takai, ko ta zaga boli, mu jira kadan, ke dus-san ba ta hitowa lokaci guda daga bugun da be hi uku ba,"

Suna tsaka da jayayyar ko su koma ne matar gidan ta bude qofa, Yabbuga washe baki ta Yi, sannan ta kutsa Kai ciki, su Lamishi suka bi bayan ta, sai da Mai gidan ta fara zama sannan Suka zauna.

Gaisawa Suka Yi,Yabbuga ta gabatar da su baki dayan su, matar ta Yi murmushi sannan ta ce,

"Allah sarki ni ko suna na Asshibi, ai na so na shiga wajen ku, sai dai nicce Bari har na idasa gyara waje, har yanzu wajen bai kammalu ba, gashi kin rige ni zuwa, to na gode sosai"

Budar bakin Mai Buruji da ta kalli matar ta ga Yar babba ce, Dan ko za ta girme ta to da kadan ne, sai ta ce.

"Ina Yan yara,"

Cikin jin nauyi matar ta ce,

"Ba yara, ai ni din amarya Nike"

"Amaryaaa"

Suka fadi a tare, sai Kuma Suka yi shiru, abin Sha da Dan motsa baki ta je ta kawo musu, kan ta kawo har sun fara gulmar ta, ta na dawowa Suka Yi shiru.

Lamishi ce ta fara daukan cincin ta Kai bakin ta, Wasa Wasa sai da suka cinye komai suka shanye lemo tass sannan suka Yi hamdala, Suka mata sallama, sannan Suka fita.

Tun daga qofar gidan Suka hau gulmar ta,

"Kee ni na ga duniya, ke gane ta kuwa? Gudan gudan tulluqa, ga ta baqa qirin awar bayan tallen miya,Wai amarya take," Yabbuga ta fada cikin al'ajabi.

"Kee Yabbuga Ina kyautata zaton zaura ta, wallah"

"Lamishi baki da dama wallah, Wai zaura , yo baku gane min hoton mijin ta ba ga giina ta rataye, kyawu nai da gani ya hada dangi da hillani"

"Ohhh wanga Hadi nasu Kam shi ah-hadin Allah, in ba Allah ba wa'iisa yin wanga hadi"

Dariya Suka dinga Yi kamar wasu qananan yara, a qasan bishiyar su suka zauna Suka dora da hirar su.

Hansatu na jin sun fara hira ta San an kafa dandalin munafurcin kenan, tagumin ta ta gyara domin ba ta da lokacin ma saurarar su, tunani ta hau yi game da abinda za ta quqqulla ta dafa ko ta kwadanta masu su ci da daren.

Ta duba kaff gidan ba wani abu, sai wani tsakin masara da ya Yi qwari, tunani take ta Yi, akan yanda zata sarrafa shi kafin yaran su dawo, ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce,

"Mara shi ba ya hushi, dole ni tai nemo abinda nika ciyar da diya na"

Mayafi ta zara ta duba qafarta, takalmin ta da ke ihun gajiya da taka shi ta kalla, murmushi ta Yi, lokacin da ta tuna sai takalmin da ta so na qasashen turawa shi take sawa qafar, amma yanzu ita ke saka wannan takalmin da ko mai aikin gidan su ya fi qarfin shi.

Tun daga zaure sukai ido hudu da Yabbuga, cikin magana qasa qasa ta sanar da su Lamishi ga Hansatu Nan zuwa, shiru Suka Yi kamar ba su ke gulmar Yahai ba, kasancewar Ta Yahai din Bata samu zuwa dandalin gulmar ba, Yahai na gida ba lafiya.

"Assalamu alaikum, mun wuni lahiya? Ya yarori,"

A tare suka ce,

"Lahiya lumui, ya su Amina,"

"Lahiya lumui suke,....na ji ku na hira na nicce Bari in taho don Allah taimakon Nan dai da kun ka Saba, shi nika bid'a, 'Dan Mai nika so da d'an gishiri ku sammin in dahwa muna abinci kahin su dawo, da swahe ma Basu ci komi ba, Rana ma ta wuce ga dare ya Shiga,"

"Tauuuu, Isa bai gari halan? Irin wanga horon yunwa? Gaskiya bashi kyautawa, wanga zalumci ne wallah, ka bar diya har ukku da mace ba abinci, wanga zalumci na"

"Ke Lamishi Ina ruwan ki? Ba ita tagga tana iyawa ba? Duk wacce ta maishe da namiji uba ai ko ta na macewa marainiya, gashi Nan ta na dandanar azabar namiji, biyayyar da ta ka wa mijin ta, walle ni bani Yi ma nawa, gashi lahiya lau Nike da miji na, ci da Sha da, sutura kuwa wadda manya za su sawa haka nika sa ta,yanzu haka jiya yakkawon naman sanuwa, saboda bani son aiki nan nibbar mai abu nai, shi yayyi muna abinci mun ka ci dazu, komi ya aje muna, duk da qaramin ma'aikaci na, ai maza Zuma na, sai da wuta, wa ka ragawa namiji yanzu?"

"Keee Yabbugaaa raba kan ki da bawa matar mutane irin Wagga shawarar, tauuu, in ki na Bata abinda taka bid'a ki Bata, in baki Yi tau, Dan mu mun Yi nesa da gida"

Bata rai Yabbuga ta Yi, Dan ita ma kayan abincin sun Yi qasa, gashi ta gama yabon miji komai akwai, tashi ta Yi Rai ba dadi, tace wa Hansatu ta bita ciki.

Ko da suka je, wata tsohuwar jarkar manja ta Bata, in an narka be fi a samu dan kadan ba, ta debar Mata uban gishiri kamar auna shi tai Dan yawa, ta debar Mata barkonon da ba a daka ba, ta Bata Maggi biyu.

"Tauu ga su Nan, ki boye dai ba sai sun ga mi nibbaki ba su Yi ta tsintse, tunda ke San dai abin magana bashi musu kadan"

Durqusawa Hansatu ta Yi ta na ta godiya, saboda hakan ai babban taimako ne a wajen ta.

Zata fita ta ga zogale ya Yi fala fala,gwanin sha'awa, roqar shi ta yi, cikin bacin rai Yabbuga ta tsinkar mata kadan ta bata, tare suka fita, Hansatu na boye bubuwan da ta samo a mayafi, Yabbuga na qara kare wa har sai da ta shige gidan ta, sannan ta koma wajen zaman su.

Ta na zama ta dinga lissafin qarya na abinda ta bawa Hansatu, harda cewa ta bata busasshen kihi yara sun ji galmi galmi.

Nan dai sukai ta mata jinjina, ta na basarwa.

Tuno Asshibi ta yi, ta kece da dariya , sannan ta kalli Lamishi ta ce,

"Hummm walle dun-nittina matar can sai dariya ta kammin,( duk na tuna matar nan se dariya ta kama ni) kun ga shegiya baki awat-ta'adin yuqa? (Baki kamar ta'adin Wuqa)"

Dariya sosai su Lamishi suke ta yi.

Hansatu kuwa na can na sarrafa tsakin masara domin yaran ta.

Cikin ikon Allah kuwa sai ga faten tsaki ya samu, wanda za su ci su dan maida yunwar su, cikin murnar samuwar wannan abincin Hansatu ke komai,ta na hamdala ga Allah,ta na kammalawa ta zubawa kowa na shi,ta shiga wanka, ta so ci kafin su dawo,sai ta tuna su da suke yara ma suka hakura da yunwa balle ita?

Da misalin shida na yamma su Amina suka koma gida, murna a wajen Ahmad ba ta faduwa, tun da ya ga murhu ya ga toka,ga guntun icce jiqe ya san an yi dahuwa.

Cike da so da qauna, tare da kulawa ta zuba masu ruwa suka wanke hannayen su, sannan suka fara cin abincin, suna yabawa qoqarin ta.

Bayan sun gama sun sha ruwa, Hansatu ta fara koya masu karatun boko, Amina ta iya rubuta Hausa, turanci kuma ta na ji amma bata iya mayarwa dika, Hansatu ta ga tunda ita ta iya, yaran ta basu samu damar zuwa boko ba, mai zai hana ta koyawa yaran ta a gida?

Su na nan su na bacci Isa ya koma gida a zafafe kamar kullum ya shiga, bai amsa gaisuwar yaran ba balle ta uwar su.

Abincin shi ya jawo, ya zura hannu a aljihun shi ya zaro ledar kifi, dan dari biyu.

Ya juye ciki ya cinye.

Bai tambayi komai game da girkin ba, ya samu ne kawai,kuma ya ci,ya qoshi ya bar kwanon a wajen.

Ahmad ne ya je wajen shi, cikin tsoro, da kuma murnar nuna masa sabuwar kalmar da ya koya, ta Father, wato Baba,

Cikin Bata Rai Isa ya ce,

"Wato Hansatu kin rantse da Allah ke sai raina ya baci ko? Ban hana Maki koyawa yarana karatun nasara ba? Ni da na yi zuwa Sakandire uwar me ya tsinana min,in ba tuqin motar uban ki ba? Ke da ki ka yi zuwa Sakandire yanzu ta amfana da shi ne? Kawo littafin nan"

Amsa ya yi,ji kike kyyyaaaat ya yaga, yaro kuwa ya buga kuka.

Korar shi waje Isa ya yi, sannan ya zauna abinshi ya na hango su,suna jimami, dan sun ji komai,shi kuwa Isa kallon yaran ya yi ya kalli mahaifiyar su, wani irin shu'umin murmushi ya yi, sannan ya furta,

"Allah ya kaimu....."

Me ye a ran ka Isa????
A GARIN MU


WRITTEN BY HAERMEEBRAEH




PAGE 9:







Yau Lamishi ta tashi ba ta jin dadin jikin ta, zazzaɓi ya dame ta, dan haka da Mai Buruji za ta tafi aiki, sai ta ce Mubaraka ba inda zata sai dai ta raka Mai Buruji ta yi mata aikin ta.

Mubaraka bata so ba, domin har ta shirya, ta saka uniform, zata makaranta, duk magiyar da take akan a barta ta je makaranta, Lamishi ta qi, qarshe ma zagi ne da qoqarin kai mata duka ne ya biyo baya, bata da zabin da ya wuce ta bi Mai Buruji, a ranta ta na ta jin haushi rashin Auwal a gida.

Dan Talo ma tirsasa ta ya yi, ya ce sai ta je, wa ya sani ko ita ma a ɗauke ta aiki, hanyar samun su ta qaru.

Sun isa gidan da misalin takwas na safiya, sai da suka sha tambayoyi da kuma neman izinin barin Mubaraka shiga gidan wajen Hajiya Ikee, bayan bayani da Mai Buruji ta mata, dai ta amince, aka bar su su shiga, Mubaraka zuwan ta na farko kenan, dan haka sai kalle kalle take, irin na qauyawan da suka je binni, direct dakin Sultana Mai Buruji ta kai ta, suna tafe ta na sanar da ita duk binda ya kamata ta yi.

A zaune ta tarar da Sultana ta na karanta qur'ani, sai ta ji wani irin dad'i ya kama ta, durqusa wa ta yi ta gaishe ta cikin girmamawa ,itama ta amsa, bayani ta sake mata, cikin murmushi Sultana ta ce,

"Ai kuwa ga kamannin ku nan sun fito ke da Umman naki, Bismillah in kin wanke toilete zaki gyaran nan, sannan ki dan wanken wadannan kayan"

"To inshaa Allahu,"

Bayi ta je ta wanke tass, ta na yi ta na mamakin irin haduwar wajen,kayan bayin da ta gani a wata roba ta dauka ta duba an aje komai, amma ita da za a barta da hannu za ta wanke su, ba sai an wani sanya a washing machine ba.

Ko da ta fita gani ta yi Sultana ta koma saman sallaya ta bar mata gadon ta gyara, ai kuwa cikin azama ta fara gyarawa.

Karatun da Sultana take Yi itama ta fara bi, dan shiru Sultana ta Yi, cikin murmushi mai sauti,take bin Mubaraka da kallo, sai ta ji yarinyar ta shiga ran ta,

"Masha Allah, Mubaraka ko? Ashe ke din hafiza ce,masha Allah Muryar ki na da dadin karatu, izun ki nawa?"

"Na sauke Aunty sultana ,Amma ba a Mana bikin sauka ba, na gode da yaba min,"

Har ran ta ta ji dadin yabawar da Sultana ta Mata, ta so samun wannan yabon wajen iyayen ta, amma ina, ba su san mahimmancin karatun qur'ani ba su, balle su yaba.

A haka ta gama gyara dakin suna karatu ita da Sultana, cikin nishadi, sai Sultana ta ji kamar ta jima da sanin Mubaraka, yarinyar ta shiga ranta cikin lokaci qanqani, sai take jin ta kamar a mkaranta take, da ta gama aikin ta ma, hira suka dan yi, anan Sultana ta ke jin wasu labaran da bata ji dad'in su ba, game da rayuwar Mubaraka, ta na son karatu, iyayen ba su damu ba, a nan ne ta ji kwadayin son shiga cikin gari,ta na son ta je ta ga yanda mutane suke rayuwa a cikin unguwanni, da kewaye, amma ta san zai wahala ta samu hakan.

Daga baya Mubaraka Neman izinin zuwa wankin ta yi, sai da ta sake zuwa wajen Mai Buruji ta nuna mata wajen, dan yanayin kyaun gidan na ruda ta, ta manta hanyar zuwa wajen da ake wankin, har tunanin yanda za ta koma wajen Sultana ma take.

Yawo take a gidan Dan ganin ya gidan ya ke,ta na tafe ta na qarewa qayataccen gidan kallo, ta na jinjina lamari irin na masu kud'i, cikin murmushi ta ayyana a ran ta

'Dole gida ya had'u ya tsaru, gidan gwamna guda'

Tunanin ta ya tsaya cak a daidai sanda ta shiga wata farfajiya, a hankali take jiyo kukan qaramin yaro, ta na tafe, har ta kai saitin inda kukan ke fitowa, ta na saurarawa sai ta ji ya na fad'in,

" Dan Allah ku kyale ni da zafi, wayyoo na Shiga uku"

Wani gini ta gani, an dan kebance shi daga jikin ginin babban gidan, dan haka can ta nufa, rasa ta inda za ta leqa ta Yi, saboda ya nayin gidan ba qaramin gini aka Masa ba ta yanda zata samu damar leqawa ta ga me ke faruwa.

Wankin da ta je shanyawa ta maida hankali wajen shanyawa , ta shanya biyu ta samu gefe ta zauna zaman jira riqe da bokoti, da kuma sabuwar wayar ta da earpiece da Lawwali ya siya mata, ta tabbata koma su wane za su fito, to kuwa zata jira,hannun ta ta sanya qasan rigar ta ta zaro wayar ta da earpiece din ta, ta danna a kunnen ta ta rage qirar'ar da ta kunna sosai, hankalin ta tashe, ta rasa me akewa yaron da ta ji ya na ihu, ji take kamar ta fada dakin ko da za a
Showing 9001 words to 12000 words out of 150481 words