nikai, dama dan in ga kin turo dan karamin bakin nan na ki"

Murguda masa bakin ta yi, ta wuce jikin mota ta na murmushi.

Hajiya Ikee na tsaye a jikin window ta na kallon su, Lawwali ne ya daga kai ya kashe mata ido daya tare da dora yatsun shi biyu a gefen goshin shi, ya yi saluting din ta ya bi sultana, da sauri ta saki labulen ta yi baya.

"Dan banzan Yaron nan dama ya na gani na?"

Hannun ta ta kalla da ya kumbura ta inda ya matsa mata jiyan, ta saka qanqara ta saka ruwan dumi ta gasa har yanzu ciwo yake mata.

Bari zai ci qaniyar shi duk sanda Gwamna Halliru ya dawo daga tafiya, yaron shi zai ara mata a je har gida a kashe mata shi, in ba ya duniyar gaba daya ta ga yanda zai auri sultana.

Bari ma zata yi maganin shi da kan ta ba sai ta jira gwamna ba.

*************************

Sun isa cikin garin Kano da misalin qarfe uku na rana, a unguwar 'Yan kaba anan Lawwali ya sai masu gida mai kyau, da gate, matar Taheer mai suna Fateema nutuniyar kirki ce, ita da mahaifiyar shi,su na ce mata Goggo Larai, sai yaran shi biyu ,Nusaiba da Hamdiyya.

Da addu'a dauke da bakin su ta neman tsari daga sharrin shaidanun aljanu da mutane suka shiga gidan,wata rantsattsiyar mota ce a harabar gidan, Taheer kallon Mubaraka ya yi, ya ce

"Qauna ta wannan  gida da mota hwa duk na ki na"

"Yah Taheer namu dai ba nawa ba, kai din a matsayin yaya ka ke a waje na,dan haka abinda na mallaka namu ne duka"

"Allah shi bani ikon sauke nauyin nan Mubaraka"

Mahaifiyar shi da matar shi suka taya su amsawa da Ameen.

Ko da suka shiga ciki abun ya ba mubaraka mamaki, daga waje gidan bai da wani hatsabibin kyau, amma ta ciki ya qayatar da ita matuqa, bayan sun shiga kantamemen parlour mai dauke da dakuna uku, da kitchen da store akwai wata qaramar qofa, Taheer kiran Mubaraka yayi, ya ce ta bi shi .

Dama ita bata wani zo da kaya ba, dan haka bin shi ta yi ziqau ziqau, su na shiga ta ga babban parlour again, da daki biyu, dakunan ya lalleqa ya na mata bayani, kowanne daki akwai bayi ciki, abinci kuwa Fateema ce za ta dinga dafawa ana kawo mata, Lawwali ya yi hani da babbar murya bai yadda ta yi aiki ba, ya bada umarni a kula da ita ne kawai.

"Yah Taheer ban qi ta taku ba, Amma dan Allah a bani su Hamdiyya su dinga taya Ni kwana tsoro nika ji, kuma dan Allah kar a hana ni aiki, in bana aiki rashin lahiya ni kai, jiki na ciwo yakai,"

Yar dariya ya yi, sanan ya ce,

"To mubaraka, ki zanka gyara bangaren ki, shi kenan?"

"Girki hwa? Ni fa ina son girki Yah Taheer"

Cikin shagwaba ta fadi hakan, murmushi kawai yayi, sannan daga baya ya ce,

"Tau wannan kuma sai na yi wa Fateema magana,dan yanda Oga ya min warning har ita da Goggo sai da an ka yi mata warning, in ta aminceee tau sai ku na yi tare"

"Dan Allah ka hwada mata ba komi, Yah Auwal baya gani, kuma ba zan hwada masa ba"

"Tauu ya yi, bari na tai na samo mana abinci"

"Na gode"

Kallon ta ya yi, ya yi murmushi ya fita.

Ya na fita ta zauna sai hawaye.

Yanzu wannan gidan da ace da kudin halal aka same shi ai mutum ya gama more wa, amma da kudin haramun ne, kwata kwata abun bai burge ta ba, amma ba yanda zata yi, yanzu ta samu dama ne da zata duqufa wajen roqon Allah ya shirya mata yayan ta, ya ganar da shi gaskiya, ya bar mummunar dabi'ar shi, yanzu ba lokacin hutu bane, lokaci ne na ibada.

*************************

Da misalin biyu na dare ya ji motsi ya yi yawa a gidan nashi, kamar ana dira ta katanga, da sauri ya kashe fitilar dakin nashi, tsabar kwarewa da fada da kuma zama cikin shirin ko ta kwana ya san inda komai yake a dakin nashi, cikin sanda ya gama d'aukan duk abinda yake buqata.

Qofar dakin ya bud'e a hankali ya leqa parlour ta jikin glass din window ya ke ganin gilmawar mutane, wani waje ya nufa a cikin duhun ya danna wani makunni kamar makunnin wuta, kujera ya samu ya yi zaman shi.

Daya daga cikin mutum ukun da suka haura gidan na Lawwali ne ya kama hannun qofar, da wani dan qaramin qarfe ya na so ya bude qofar da shi, amma sai ya ji wani irin shocking ya kama shi, ya ja hannun shi ya ja inaa ya maqale, ihu ya dinga zabgawa wanda ya sa abokan aikin nashi tsorata kar a kama su, su ka ruga da gudu suka haura katangar suka bar gidan, Lawwali na jin haka ya miqe ya gyara bindigar shi, ya kunna hasken parlour sannan ya kashe wajen da ya danna dazu. Matashin ya fadi yifff a qasa.

Makulli ya sa ya bude qofar parlour ya shigar da matashin sannan ya rufe qofar ya sake danna abinda ke saka shocking in an taba qofar .

Madara Lawwali ya je ya kawo mai sanyi ya ba matashin ya ce ya shanye.

Kamar wanda yake a yunwace, haka ya dinga diddikar madarar  nan, ya na gamawa Lawwali ya ce,

"Wa ya aiko ku? In ka yi min qarya a maganar farko sai na fasa kan ka,na san wa ya aiko ku, ina dai son ji na daga bakin ka"

Cikin in ina matashin ya ce,

"Matar gwauna Hajiya Ikeeleema ta wallah, dan Allah ka yi min rai, ban san gidan ka na wanga ba, ta dai bamu adireshi na kawai, tace mu kashe duk wanda shike cikin gidan ga, dan Allah...."

"Ya isa haka nan, ba abinda zan maka, na san ba ka san waje na an ka aiko ka ba, tashi ka zauna, ni zan kwanta gobe da sahe kar na tashi na gan ka gida na, zan manta dana tab'a sanin ka,"

"To Oga, ni yanzu ma in ka min izini tafiya zan yi"

Daga kafada Lawwali ya yi, ya ce,

"Wad-da ka ga dama"

Lawwali kashe shocking din ya yi, ya shige dakin shi ya fada gado ta ruf da ciki.

"Mtsss Hajiyar ga qaramar yar tasha ta wallah, diyan ga zata turo min su kashe ni, ni ta hana min kwana, mtssss"

Pillow ya ja ya rufe kan shi, ya na son ya samu bacci kafin safiya..........

*Allah dai ya biya ogaaaaa*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 37:


Duk jikin Lamishi ya yi laushi, bata da burin da ya wuce na ta san a wanne hali Mubaraka take yanzu, shin Lawwali gidan shi ya maida ta ? Ko itama ya tsunduma ta harkar shi?

Bata da amsar tambayar nan, gashi 'yan gulma har sun yad'a komawar Mubaraka, ana ta zuwa barka, da kuma son ganin ta, amma sai dai su yi qarya su ce ta fita da yayan ta wajen 'yan sanda, dan a ji su waye suka sace ta.

Kwana hudu mutane basu daina zuwa jaje ba, har iyayen su Murjanatu sun je, dan a tambayi Mubaraka su waye suka sace su, tunda su sun qi fadi, ko da suka je suma aka ce musu har yau Yayan ta bai maida ta ba.

Labari ya fara sauya salo, wasu na ganin ko yayan ta ya aurar da ita ne? Wasu na ganin qarya ne dama ba a gan ta ba, aka ce an gan ta,wasu na ganin tsoro ne ya sanya aka boye ta, kowa dai da abinda ya dasa a zuciyar shi, yake gani kuma shi ne daidai(haka halin dan Adam yake, sai ya sa maka maganar da ba ita ce a zuciyar ka ba a bakin shi)

Mai Buruji ta shawarci Lamishi da komawa wajen aiki, tunda dai an ga Mubaraka, yanzu zama shirun zai sa mata kadaici.

Haka kuwa aka yi, wata ranar Litinin da sassafe, suka shirya, suka dauki hanyar gidan gwamna Halliru, adaidaita na aje su, suka hango Lawwali tafe, zai je gidan shi ma.

Lamishi bata taɓa tsayawa ta masa irin wannan  kallon ba, kallon uwa da d'a, kullum kallon wani abu mara daraja da amfani, take masa, da ace tun sanda ya na da halin kirki take masa kalar wannan kallon, wataqila da Allah ya tallafa mata sun zama kamar sauran yara na gari.

Ciki suka shiga suka jira zuwan shi.

Ko da ya zo yi ya yi kamar bai gan su ba, Mai Buruji ce ta ce,

"Lawwali Barka da swahiya,"

Ko kallon inda take bai ba, ya je ya jingina da motar Sultana, Lamishi kuwa bata yi fushi ba, bin shi tayi, ta hade hannayen ta ta na wasa da su, ta ce,

"Yayan Mub...."

"Kar ki sake ki ambaci sunan ta abakin ki, zan manta ba a gida muke ba na karta Maki rashin mutunci,me ki ke so? Kuddi na ki ka bida?"

Wasu hawaye ne masu dumin gaske suka zuba mata, da hanzarin ta sa hannu ta share su,

"Uhmm dama cewa na yi, ku na tare da ita ne? Na ga baka maishe ta gida ba tun sanda ka kawo ta mun ka gane ta"

"Ban yi niyyar maishe ta gidan ba, kuma ba amfanin ki san inda take, ko akwai? Ke dai san ni ba zan cutar da ita ba, ke kuma fa? Duk duniya ta shaida ke ki na iya kashe ta ma da hannun ki, tunda kin ka kashe ta da bakin ki"

Ita kan ta ta na mamakin yanda maganganun Lawwali ke qona zuciyar ta, ta ya uwa za ta kashe dan ta? Duk da ta sani bata kyauta ba matuqa, amma ba za ta iya kashe Mubaraka ba, jinin ta ce.

Murmushin mugunta Hajiya Ikee ta yi, a daidai lokacin da ta saki labulen d'akin ta, ta d'auki dan kwalin ta ta d'aure kan ta da kyau, ta fita daga d'akin ta, sauka take a matattakalar benen, cikin sauri, dan bata son Lamishi ta bar wajen, bata isa ba.

Ta na fita kuwa Lamishi na isa bakin qofar shiga cikin gidan, dan gudanar da aikin ta, Mai Buruji ma ta wuce nata aikin.

Da sauri Lamishi ta yi baya, tare da duqar da kan ta, ta hau gaishe da Hajiya Ikee, cikin tsawa da hargowa Hajiya Ikee ta bangaje Lamishi ta fadi qasa, sannan ta ce,

"Keeee! Mahaukaciya, daqiqiya, mai warin talauci, halan baki gani ne? Ko kuwa hayaqin icce ya makantar maki da ijiya? (Idanu)"

Mamaki ne mai girma a zuciyar Lamishi, ta san Hajiya Ikee bata da mutunci, amma haka bai taba shiga tsakanin su ba, duk kalar rashin mutuncin da take musu baya wuce akan aikin su, su na gyarawa ta bata, ko in Sultana na musu magana ta yi ta hantarar Sultanan ta na hana ta magana da masu aiki, amma wannan bangazar da zagin rashin mutuncin daga ina?

"Ran ki shi dade ki yi min ahuwa, ban gan ki ba"

Sai da Hajiya Ikee ta kalli inda Lawwali ke tsaye, sannan ta ce,

"Ina hwa zaki ganni ana Allah Allah a shigo AC, a yi aiki a saci abinda aka sata a tai gida, tau bari ki jiya, daga yau, duk na qara diba abu ban gani ba, sai nasa an daure min keyya, da shegiyar kishiyar can taki, da duk wani dangi naki, barauniyar banza barauniyar yohi"

Wani irin tashin hankali ne ya shiga Lamishi, a barta da rashin mutunci, da rashin ragawa kowa, gulma da munahurci,amma banda sata, sataa, ita Lamishi ake zargi da Sata? Wai me ke faruwa ne yau? Ko dan dai ta jima bata zo bane?

"Ran ki shi dad'e ki yi min ahuwa, diya ta ce ta bace, ba mu gane ta ba, sai kwanan nan, shi yasa bana zuwa, na aiko Mai Buruji ta sanar da ku,"

Sultana da ta fito ta ga Lamishi a qasa, a wulaqance, sai ta ji ran ta ya ɓaci, ko da ba mahaifiyar Auwal bace, bai kamata a yi wa mace mai shekaru haka ba,da hanzari, ta d'aga Lamishi ta na kad'e mata jiki, kallon motar ta tayi, ta ga Lawwali na tsaye ya na jiran ta, ko kallon wajen ma baya yi, alamu sun nuna kamar ma baya wajen, ballantana ya san me ake aikatawa, daidai da kwayar zarra ba bu digon baqin ciki a fuskar shi.

Ran Sultana ya baci da hakan kuwa matuqa, ya na tsaye ake wulaqanta mahaifiyar shi? Wane irin yaro ne shi? Kafin ta gama tunanin ta taji Muryar mahaifiyar ta na fadin,

"Aka neme ta anka rasa ko ta bi duniya? Zamani ne na in talauci ya wa mutum yawa shi hwara biyar samari, dan su samu kuddi"

Kusan a tare suka kalli Lawwali, kowannen su da abinda yake saqawa a cikin zuciyar shi, Hajiya Ikee ba karamin kaduwa hanjin cikin ta suka yi ba, da ganin yanayin fuskar shi, wani irin gurnani ya saki kamar wani zaki, da sauri ya zagaya ya bude mota, tare da yi wa sultana alama da su tafi.

Kamar wadda ya yi wa magani, haka ta bi umarnin shi zungui zungui ta fada mota, da wani irin gudu ya bar gidan,tsoro ne da tashin hankali a bayyane a fuskar Sultana, wannan wanne irin gudu yake da ita.

Bangaren Lamishi kuwa sai ta ji wani sanyi ya mamaye ta, ta tabbata Hajiya Ikee bata zagi banza ba, ko bai rama dan ita ba, sai ya dau mataki dan qanwar shi, qarasa miqewa ta yi ta na murmushi, ta tsaya sosai, ta na jiran Hajiya ta matsa, ta shiga ta hau aikin ta.

Hajiya Ikee kuwa, ji ta yi qirjin ta na bugawa da sauri da sauri, idanun Lawwali kawai take hangowa, tafe take zuwa daki, ba tare da ta san sanda ta fara tafiyar ba.

Tunani take mai zurfi, game da abinda ya faru, zama ta yi a bakin gado, ta na nazari, cikin murmushi ta miqe, ta ce,

"Wato duk wanda ka son ya sami nasara akan ka Lawwali, shi tabi qaunar ka, da kyau"

Hannayen ta biyu ta tafa, cikin jin dadi, tare da ganin ta samo babbar hanyar da za ta yi maganin Lawwali.

Lamishi kuwa, ko da ta shiga dakin Sultana Dan gyarawa, sai ta ga babu datti, kuma Mai Buruji ta tabbatar mata da cewar ba mai zuwa gyaran dakin ta, tun bayan batan Mubaraka, da alama da kan ta take gyarawa,duk da cewa akwai masu aiki sosai a gidan, wanki ne dai gashi nan, ta tara mai mugun yawa, sake dan gyara abinda ba a gyara ba ta yi, ta debi wankin, ta tafi wajen yin wanki.

Sai da ta gama aikin cikin gidan sannan ta tafi wajen su Mai Buruji, nan ta labartawa Mai Buruji duk abinda ya faru, dariya Mai Buruji ta dinga yi, daga qarshe ta ce,

"Aiko yau ta kai qarshen iskanci, da wulaqanta tallaka, kee Yaya watarana ma haihuwar dan iska na da rana, dan ko walle na sani Lawwali ba shi barin wanda duk ya ɓaci (zagi) qauna tai, ko da ke ta kuwa, balle wata can,"

"Bari ke dai,shi ne na ka wa dariya nima, yo Allah na tuba zagi ko ga unguwa sha nai mukai kullum, abu d'aya ya yi min ciwo da ta ce muna mata sata,na san banda halin kwarai, amma hwa bana sata bana maita,"

Haka sukai ta hira a tsakanin su, su na aikin su.

Bangaren Lawwali da Sultana kuwa, duk yanda ta so ta yi magana, ko da kalmar bada hakuri ne kuwa, ya gagara, saboda yanda Oga ya daure fuska abun ba a cewa komai, banda tafasa ba abinda zuciyar shi take yi, har shi za a zagarwa qauna? Yarinyar da yake jin ta kamar tsoka daya a miya? Duk wanda ya zage ta, ko ya taba ta, ji yake kamar ya soka mishi kibiya a idanun shi, ya na matuqar jin ciwo ya ga wani na zaluntar Mubaraka.

Hajiya Ikee da ta san tanadin da yake mata da bata taba masa qanwa ba, abinda ya wa Lamishi ya bata ran shi, domin kuwa Uwa uwa ce, amma da ya tuna shegen kwadayi da son abin duniyar su ya ja musu walaqanci,dan ba shi da tabbas akan abinda Hajiya ikee ta fadi, na suna sata, duk wani mai son abun duniya in ya samu na wani, zai iya sata,dan haka  sai ya dauke kai ya dena kallon su, amma duk abinda take fada a kunnen shi, kuma tabbas ta dauki bashin da ba zata iya biya ba.

Tsaye take a daya bangaren, ta kasa tafiya ta na so ta masa magana, duk ya bi ya hade gabas da yammar fuskar shi, ya qi sakin ta, zagayawa ta yi saitin inda yake zaune ta duqar da kan ta, wani irin qamshi ya ji ya shaqa mai kwantar da hankali, bai gama shaqar qashim ba Muryar ta mai sanyi da kwantar da hankali ta daki kunnen shi, sai da tsigar jikin shi ta miqe,

"Auwalll.."

Rintse idon shi ya yi, da suka yi jawur, dan bacin rai, ya wara su a kan ta, maganar da ta kwaso a bakin ta take so ta yi, tini ta maqale a maqoshin ta, cikin sauri ta bar wajen, ta shiga office din ta, ta jima a zaune kafin nutsuwa ta same ta.

Lawwali kuwa wajen ya bari, bai tsaya ko ina ba sai wajen da ake horar da No 1, zaune ya gan shi, an bashi abinci da ruwa, Lawwali ya san mene ne yunwa, a lokacin baya can kafin tsohon Gwamna Lamido da suka kashe ya ja shi jiki, sai su kwana su yini basu ci ba, wannan dalilin ne ya sanya, ba ya qaunar barin duk wani wanda ke qarqashin shi da yunwa ko da kuwa kai mai laifi ne a wajen shi, qiyyyar No 1 da ke ran shi bata hana ana bashi abinci sau uku a rana ba, kuma abinci mai rai da lafiya.

Ya na zuwa danqar wuyan No 1 ya yi, ya danna a cikin doya da kwan da yake ci, sannan ya dago kan shi ya dinga falla masa mari,

"Duk a dalilin ka ne, a sanadin ka ne qauna ta ta samu mummunan tabo, da baka sace ta ba, da ba mai yi mata kallon 'yar iska, da baka sace ta ba, da har yanzu martabar ta da qimar ta na nan a idon mutane, yarinya ce mai daraja, yarinya ce kamila,ba ta da laifin kowa akan ta,
Showing 75001 words to 78000 words out of 150481 words