cin jarabawar nan.

Ta na nan zaune ta tuna da bata yi isha'i ba, a hanzarce ta fita, ta yi alwala, ta koma dakin, ta hau sallah.

Ta na idar da isha'i ta yi shafa'i da wutiri, sannan ta dora da nafilfilun da bata san adadin su ba, ta na sallah ta na kuka, tare da roqon sauqi akan lamurran da ke faruwa a kowacce sujjada.

Fatan ta Allah ya shirya mata mijin ta, ya kawo qarshen wanan zubar da jinin da ya dauka kamar ba komai ba.

Sai da ta ji idon ta ya mata nauyi ta kasa bude shi sannan ta hakura ta dena sallah, ta kwanta a gefen Lawwalin da ke qasa,kwantar da kan ta tayi a qirjin shi ta yi lufff kamar yaron da ke jin sanyi.

Hawayen ta na diga cikin baccin da ya dauke ta mai nauyin gaske.

Lawwali ne ya bude ido a hankali, jin kamar an danne shi ne ya sanya shi kallon saman qirjin shi, ganin ta ya yi ta haye jikin shi ta yi lufff,hawaye na sauka daga idon ta, duk da cewa bacci take.

Cikin tsananin tausaya mata ya rintse idanun shi da suka kada suka yi jawur.

Ba zai kyale Gwamna Halliru ya qara rayuwar farin ciki ba, in ma ya bar shi ya yi rayuwar farin ciki bai haifu ba cikin asararrun iyaye kamar Dan Talo da Lamishi ba, wanda ke haifawa duniya annoba, kuma su ci gaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali .

Zai hukunta duk wanda ya yi sanadin lalacewar shi, har iyayen nashi, ba zai barsu ba, ya san maganin su, ba dai kudin shi suke so ba? Kuma da shi suke taqama da fadi a gari ba? Zai ga wanda zai dinga basu kudin.

Ya na nan ya na ta tunani, har bacci ya fara kama shi,sannu a hankali ya miqe, tare da Sultana a hannun shi mai lafiya.

Dora ta ya yi saman gado, sannan ya hau, ya rufe su, suka yi baccin su.

Da safe kuwa ya dauki wayar No 5 ya kira gwamna, ta na shiga gwamna ya kece da wata mahaukaciyar dariya, tare da fadin.

"Yaro bai san wuta ba sai ya taka, aza shikai yadda muka sa shi ya zama wani a fagen ta'addanci, ba zamu iya creating wani ba, to gashi yanzu ka ga bayan shi, alqawari na ya...."

"Dad'i na da kai qaramar kwalwa wallah(qaramar kwakwalwa), shin mi yasa ka ke abu kamar wanda be je makaranta ba! Baka tunanin ko na kashe shi wayar shi na hannu na? Tunani ka ke ya kashe ni ya kira ya fadi maka ko? To ka tafka babban kuskure"

Lawwali na fadin haka ya kashe waya, bangaren gwamna Halliru kuwa hankalin shi in ya yi million ya tashi, wani irin tsoro da tashin hankali da damuwar makomar shi ne suka bi suka dabaibaye shi.

Ba shiri ya fara kiraye kirayen waya, akan ya na neman qarin masu tsaron lafiyar shi, da ta iyalin shi.

Hajiya Ikee da ke tsaye ta na so ta ji qarshen Lawwali kuka ta sanya,

"Se na dana fada maka kar a yi haka, yaron nan ba mutunci ne da shi ba, ni kad'ai na san yanda na ji sanda ya shaqe ni, baka taba shiga hannun sa bane, shi ya sa, yanzu Allah kad'ai ya san mi ze wa Sultana da ke hannun shi, Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, mun shiga uku mun lalace"

Kukan ta ne ya jawo hankalin Sultan da ke karyawa ya shiga parlourn, kalaman da ya ji na Hajiya sun juyar masa da kai, waye zai cutar da Sultana?

"Waye zai cutar da sultana? Ku fada min me ke faruwa ne, kwana biyu babu natsuwa a tattare da ku, kun damu da rashin su Sultana, mata da mijin ta a dinga bin diddigin su bai dace ba"

"Dan uban ka Lawwali tsohon dan ta'adda ne ba mutunin kirki ba ne, ya dauke ta ta na can inda ya ke ya na gana mata azaba"

"Ban gane ba? Kun sake sanya ni duhu"

"Kai ba kalar daqiqai ba balle na ce ko takkwalanci(daqiqanci) ke damun ka, shin wane yare ne baka fahimta ba? Lawwali dai dan ta'adda na, ya ha'ince mu, ya auri qaunar ka, ya gudu da ita"

Qaryar da ta yi ta sa gwamna Halliru yin ajiyar zuciya mai qarfi, dan kuwa ta ce ce shi, a yanda ran shi ke tafasa dinnan, abu biyu za ai, ko ya bada amsa daidai, ko ya hasala ya wa Sultan abinda zai zo ya na dana sani da kan shi.

Sultan ne ya kalli Daddyn su cikin damuwa ya ce,

"Daddy u have to call the police and let them know about this, a gaggauta daukan mataki"

Cikin wata kakkausar murya gwamna ya ce,

"Kar wanda ya kuskura ya yi involving hukuma a maganar ga har sai na bada izini"

"But daddy what if suka cutar da Sultana? I can't let anything happen to her,ba zan yahe wa kai na ba in wani abu mummuna ya same ta"

Yanda Sultan yake ji a zuciyar shi, da zai samu ko kukan ne ya yi, kamar yanda Hajiyan su ke yi, da ya ji dadi.

Duk yanda yake tunanin shawo kan Gwamna a hada abun da hukuma ya gagara,qarya kan qarya suka dinga shimfida wa Sultan, daga qarshe suka bashi shawara ya je ya yi ta addu'a har Allah ya dawo da qanwar shi gida lafiya.

Sultan na fita Gwamna ya yi waya, Hajiya Ikee na jin me yake fad'a a wayar ta rikice, ta rude da kuka.

"Me ya kai ka nemo Mubaraka? Ga iyayen shi a gari? Ka rufa muna asiri akan wanda Allah ya lulluba muna, kar ka tone shi,ka sa a kama iyayen shi, ka bar batun yarinyar nan yar ido, yanda yaka son yarinyar nan, ko kan shi ba ya so haka"

"Wanne iyayen nashi za a kama? Yo Allah na tuba ko halbe su zan yi zai damu ne a ka fada Maki? Ke bari ki ji, ba na duba, kuma ba na ganin zuciyar kowa, amma wallah ba wanda yaron nan ya tsana a yanzu duk duniyar ga wanda ya wuce iyaye shi da ni, dan haka bar batun su ma, in na gano qaunar shi na kame ta, zai sako Sultana lahiya"..........

*Hummmm wai haka???*


💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH

PAGE 49:




Gidan talabijin na NTA da ke garin Zamfara ke haska wata gagarumar gobara da wasu ke zargin Bomb aka sanya a wani babban wajen ajiya  na kayyaki kala kala,mallakin gwamnati,kayan sun had'a da, kekunan d'inki, kekunan guragu, shinkafa, man gyada, wake, katifu, da dai abubuwa masu tarin yawa, gwamnati ta danqare su ta ajiye su, saboda zagayowar zabe, sai a yi ta raba wa mabuqata ana neman quri'un su, mutane kuma da yake a matse suke da lalure  laluren duniya, in aka basu sai su karba su na murna, su na ganin an musu wani babban alkhairi ne, ba tare da sun yi tunanin cutar da su ake yi ba a hakan.

Wuta sai ci take an kasa kashe ta, mutane kuwa a hakan suka dinga qoqarin diban kayayyakin abinci, su na guduwa, labari ya kai har gidan Gwamnati, Gwamna Halliru kuwa ba qaramin tashin hankali ya shiga ba, domin wannan ce babbar ma'ajiyar shi,gashi an qona ta, kuma mutane sun samu damar kwasar abinci, da duk wani abu da ya adana domin zabe mai zuwa, gashi mutane sun gano manufar shi ta qanqame kayan more rayuwa a lokacin da ya dace a ce gwamnati na taimakon su, ta saka musu da wahalar da suka sha na zaben ta, ana jiran sai sanda suka matsu da neman abinci a basu.

Har haushin yanda ake ta masa waya ana sanar da shi abun  jimamin yake, a fusace ya fita daga office din nashi ya na kiran wayar wanda ya bawa aikin bincika masa inda su Mubaraka suke.

An sanar da gwamna Halliru Murtala Gusau, garin da Mubaraka take,amma me ya sa har yanzu ba a gano inda take ba? Duk da cewar Ya sani Kano tinjimin bajimin gari ne, nemo  Mubaraka zai wahala, amma ba zai gaji ba, ba zai huta ba, har sai an same ta.

Bai samu layin wanda yake nema ba, dan haka cikin fushi ya bar gidan gwamnatin gaba daya,ya fada motar shi, ya na ta waya tare da bada umarnin kula da ma'aikatu da duk inda ya kamata a bawa tsaro,masu tsaron lafiyar shi, tuni suka tada motoci, sai gida.

Lawwali bai fito ba sai da ya shirya, kafin sati ya sake zagayowa ya yi wa manyan ma'aikatun gwamnati, da ma'ajiya kala kala,da kadarorin gwamna Halliru barna, kusan wasu abubuwan da gwamnan ya mallaka,ba wanda ya san da su, Lawwali ne kawai ya san ya mallaki wasu kadarorin, tunda shi yake aika,ya sama masa su, ta qarfi da yaji,Lawwali ba qaramin birkitawa gwamnati da hukumar tsaro ta jiha da ta Nigeria gaba daya lissafi ya yi ba, gwamna Halliru ya koma kamar mahaukaci, a yanzu yanda yake ji, bai qi ba kowa ya san me ke faruwa a tsakanin shi da Lawwali da yaran shi ba, amma tsoron shi daya, kar ya aika da jami'an tsaro a buɗe musu wuta kuma Sultana na cikin su, ya zai yi ne.

Sati Uku currr ana abu daya ba d'aga qafa, Sultana ta yi iya bakin kokarin ta dan ganin ta taushi zuciyar Lawwali amma abun ya faskara, daga shi har yaran shi a tunzire suke, ta barauniyar hanya ake shigo musu da makamai daga wasu qasashen,gwamna Halliru ya yi danasanin  damqa masu manyan makamai, domin kuwa ya tabbatar da su ake tarwatsa masu gari, sun bata masa suna a duniyar siyasa, dan ya tabbatar da cewa yanzu mutane na ganin baqin mulkin shi,da su na da yanda za su yi da sun tsige shi.

Ba gwamna Halliru Murtala kadai ba, hatta da Hajiya Ikeeleema bata da ikon shiga manyan taron matan gwamnoni lafiya, ba tare da an yi maganar tabarbarewar mulkin garin nasu na Zamfara ba.

Mummunan labarin neman da gwamna Halliru ke yi wa Mubaraka ya iske kunnen Oga Lawwali, cikin tsananin damuwa da tashin hankali Lawwali ya kira No 4, tare da bashi umarni, duk yanda zai yi, ya yi, ya kawo masa qanwar shi wajen shi cikin qoshin lafiya.

No 4 ya shiga damuwa matuqa, dan kuwa labarin tashin hankali da rashin zaman lafiya da ake ta samu a yankin Zamfara ba boyayye bane, ga shi ba ya so ko da kwarzane ne ya samu Mubraka, dan kuwa a yanzu ya gama tabbatar wa da zuciyar shi ya na tsananin qaunar Mubarakan, tsoron cin amanar Oga ne ya hana shi bayyana mata, da tinanin halin da Fateema za ta shiga in ta ji ya na so ya auri Mubaraka, Taheer No 4 na cikin matsala, ya rasa yanda zai ya cika umarnin oga ba tare da Mubaraka ta samu matsala ba, dan kuwa ya san duk wata hanya da gwamna zai bi dan ganin ya gano su zai bi ta.

*************************

Zaune ya ke ya na jefa soyayyan naman rago a bakin shi, ya na korawa da lemo kwali, in ya cinye ya gutsiri meat pie, Hajiyan Hansatu kuwa na ta zuba godiya da yaba wa surukin nata.

"Dan Allah Hajiya ki dena min godiya haka, ai ke uwa ta ce, musamman ma da ban da kowa ke nake gani na ji dad'i a raina"

"Ai dole na maka godiya Isah, irin wanga kayayyaki kamar dan ni ka tahi Makka, lallai na tafka babban kuskure a baya, da na qi ka, Allah ya bawa d'iya ta mijin maraniya, Allah ya jiqan Alhaji, da ya ga zab'i nai yau,"

Murmushi kawai Isah ke zubawa, cikin sunkuyar da kai ya ce,

"Hajiya ai ni ke da godiya, ba abinda zan ce da Hansatu sai Allah ya mata albarka, Allah kuma ya haɗa ta da dukkan alkhairi duniya da lahira"

Farin cikin da Hajiya ta shiga ba mai faduwa bane,kowacce uwa zata so jin wadannan kalaman a bakin surukin ta, to gashi ita Allah ya jiyar da ita, tun da sauran rayuwar ta.

"Ban ga Yaya ba, ko dai ba shi nan na?"

"Eh shi na office, ai sai yamma zai dawo, wan mata tai yak-kirai tun sahe akwai abinda suke yi"

"Allah Sarki, Allah ya bada sa'a, Allah ya jiqan Alhaji, har na tuna sanda muke tafiya, tun sahe sai dare, ba ya bari na da yunwa, komi yaci shi zai ban, haka zai wuni aiki, rayuwa kenan"

Hira ce sosai ta shaquwa da sabo ke gudana tsakanin Isah da surukar shi, tun sanda ya bar gida nan ya nufa, ya ke ta Suratu, hankalin shi gaba daya ya tattara ya koma gida wajen Hansatu, amma ya fi so sai ta huce ya koma, dan ya san ba ta iya fushi da shi, kamar daga sama ya ji  maganar Hajiya ta ce,

"Ai shawarar da kabban ita na bi, ana nan ana binciken mutanen da sun ka yi kidnapping di na, kuma da alama ana nan ana samun nasara, dan har jami'an tsaro sun Kama yaro guda da an ka had'a baki da shi an ka swace ni"

Wani irin tari Isah yake sakamakon kwarewa da ya yi da lemon da ya daga glass cup ya na korawa, sannu Hajiya ta dinga zuba masa, miqewa ya yi, cikin yaqe, ya ce,

"Allah dai shi tona ma koma waye asiri, bari na tai na ga ta na ta yi min flashing, wataqila suna bidar wani abu"

Murmushi Hajiya ta yi, ta ce ya jira ta kawo masa saqo ya kai mata, ji ya yi kamar ya gudu kan ta dawo, kuka ne kawai Isah be ba, saboda jimawar da Hajiya ta yi.

Kwalin madarar ruwa ta kai masa da galan din zuma, ta ce ya kai ma Hanstu, godiya ya dinga yi, ya na sauri ya bar gidan, mai gadi na gaida shi ko kula shi be ba, da da ne kuwa sai ya tsaya ya masa kurin shi surukin gidan ne.

Ya na fita titi sosai ya lalubi No Laminu, bai dauka ba, ji ya yi kamar ya fashe da kuka dan takaici, in asirin shi ya tonu ai ya kade.

Bari ma, saudiyar nan zai koma zaman Nija be kama shi ba........

*Yayah Isah namu na mudunci😂*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 50:


A cikin daren Isah ya je gidan Laminu, Asshibi na ta mitar an hana su sakewa da mijin ta, ya fita tun safe, sai daren ya dawo, hakuri Laminu ya bata ya sanya rigar shi ya bude gate ya fita, Isah ya gani tsaye cikin tsananin damuwa, da tashin hankali, murmushi ya yi, ya ce wa Isah,

"Na san me ya kawo ka, kwantar da hankalin ka, magana ta qare dazu da rana, na aika wani yaro da maganin kusa (bera) an sa mishi ga abincin da an ka kai, ya ci ya mutu, sai in ga me bada shaida"

Wata iriyar ajiyar zuciya Isah ya sauke, tare da sakin kwalin madarar a qasa, ya rungume Laminu, ya na murna,

"Kai sake ni menene haka, sai an gan mu a ce 'yan iska muke, kai jaye"

Tura Isah baya Laminu ya yi, ya na waige waige, cikin jin dad'i Isah ke bawa Laminu labarin yanda ya san an kama yaron nasu, Laminu ya ce,

"To rudewar da kayi na yasa bata idasa baka labari ba, da ta baka, da ka gane cewar an kashe shi , ko kuma ba a sanar da ita ya mace ba"

"Kaiii Laminu amma kai shege ne"

"Ahafff hauka nike da zan bari asiri na shi tonu? Kai fa ba dan garin nan bane ba, ka na iya guduwa ko baka da iyaye a Kano ,ni kuwa uwaye na da uwayen matata nan suke"

Hira suka dan taba Laminu ya ce shi zai shiga matar shi na can na jiran shi, Isah ma murmushin da bai taba kalar shi ba a rayuwar shi ya yi, tare da cewa,

"Ni ma tun dazu take min waya, bari na je gida"

Sallama suka yi, kowa ya kama hanyar shi.

Ko da Isah ya isa gidan, ya tarar da shi kamar kullum, a share, a tsaftace, abincin shi na wajen da aka saba aje masa, har da sabuwar tabarma.

Komai da yake buqata ya same shi har da qari ma, amma fa Hansatu ce kawai bai gani ba kamar yanda ta saba, ko qarfe nawa ze kai a waje, ta na nan ta na jiran shi.

Ko daya leqa dakin da kyau kwance ya gan ta, sanye da wata iriyar rigar bacci mai daukan hankali, sake leqa wa ya yi shin Hansatu ce ko wace ce? Kafff rayuwar su bata taɓa sanya rigar bacci ba, tunda ya aure ta ba ko lefe, balle ya ce ya saka a ciki.

Baccin ta take cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, Isah kuwa hankalin shi in ya fi cikin unguwar ya tashi.

Cike da damuwa ya zauna bakin gadon, ya kai hannu zai tashe ta, da sauri ya janye, dan bai san da me zata farka ba, rashin sanin meye a zuciyar ta na sa Isah damuwa, da dakatar da shi akan abinda ya so aikatawa.

Ya kai qarfe goma da minti sha daya ya na ta kai komo, tsakanin daki da parlour, motsin shi ya yi yawa, har ya hana ta bacci, da wata iriyar miqa ta tashi, wadda ta sanya Isah kai mata runguma, turashi baya ta yi, sannan ta ce,

"Meye haka? Bacci fa ni kai, duk ka ishen da motsi, mi ka ke bid'a wanda ban aje maka ba? Ko kuwa kwanan da nikai ka ke baqin ciki na yi duk da wuni da na yi aiki?"

Zama Isah ya yi a bakin gadon, ya na kama wandon shi, jijiyoyin kan shi har sun bayyana rud'u rud'u,

"Dan Allah Hansatu ki taimaka min, ni ba ni buqatar komi sai ke, na qoshi da abincin ma ni, ki taimaka min"

Tashi ta yi, ta na wata iriyar tafiya da ni kaina sai da na yi mamakin shin anya Hansatun Isah ce? Ko kuwa Hafsatun Hajiya ce?

Hijabin ta ta zira ta fita waje, fitsari ta yi, ta wanke bakin ta, dan ta yi bacci ta ji ya sauya mata, sai da ta wanke fuskar ta sannan ta koma d'akin, Isah ta gani cikin mawuyacin halin da ba zata iya kauda kai ba, ko ba dan shi ba, dan tsoron fushin da Allah da Mala'iku za su yi da ita, ta sani duk matar da mijin ta ya neme ta a shimfida
Showing 105001 words to 108000 words out of 150481 words