kara ta a kunnen shi,

"Ka sakko parlour 'n baqi yanzun nan"

Shi ne kawai abinda ta fadi, cikin rawar murya, aka kashe wayar.

Cikin sauri ya dauki wayoyin shi ya fita, sai da ya wuce parlour biyu kafin ya isa inda take neman shi, ya na bude qofar ya yi turus ya qame,

"Barka da dawowa Excellency ,Bismillah shigo, kai da gidan ka?"

Wani yawu Gwamna Halliru ya hadiya makwat, Allah yake ta roqo ya sa ba wannan bace ranar da tun farko No 1 ya guje musu.

Lawwali ne zaune ya harde kafar shi daya bisan daya, hannun shi daya riqe da bindiga, ya aje wayoyin shi da na No 1 a gefen shi, sai jujjuya bindigar yake, Hajiya Ikee na gurfane kamar me neman gafara,

"Hajiya wai mi na na hakan ga ki ka yi? Na ce miki ki hau kujera, yanzu in Sultana tag-gane ki duqe gaba na ai sai ta hwasa aure na, tunda kin ka shigo ni ke baki baki ki hau kujera, ko sai na taimaka Maki ne"

Gyara bindigar shi ya yi, ya bata rai, da sauri ta miqe ta zauna a kujerar dake daf da wadda gwamna Halliru ya zauna, jikin ta sai rawa yake, a duniya Hajiya Ikee na tsoron mutuwa .

"Lawwali mi na na ka ka yi haka? A gida na za ka fiddo bindiga, ga iyali na? Me ke damun ka?"

"Ni ka ke tambaya me ke damu na? Ashe baka bawa matar ka labari na ba? Ashe baka hwadi mata ko ni wane ne ba? Take ta min wasan yara"

Hajiya Ikee ce ta matsa kusa da Gwamna Halliru, ta na magana kamar me rad'a, kunnuwan Lawwali kuwa a bude suke tsaf dan sauraron ta,

"Ka danna kiran Yaron nan na ka shi taho, shi kawo mana dauki, wajen wanga qaramin dan iskan"

A hanzarce Gwamna ya kalle ta, ya maida kan shi wajen Lawwali, Lawwali ma cikin sauri ya dauke kan shi, kamar be ji me suke fada ba, cikin rad'a Gwamna ya ce ma Hajiya Ikee.

"Lawwali shi na yaro na da ni ka hwada maki,"

Wata 'yar siririyar qara Hajiya Ikee ta saki, ta damqe bakin ta da dika hannayen ta biyu, ta na zaro idanu, domin duk wani labarin ta'addanci da rashin azziqin lawwali ba wanda ba ya riskar ta, wani irin tsoro ne ya sake damqar ta da qarfin gaske,

"Hajiya ni kin ka aikawa 'yan iska su kashe ko? Ni kin ka hana kwana, kin ka b'aci uwa ta da qauna ta gaba garen, Hajiya ke ko san irin laihukkan da kin ka aikata min?"

Da sauri Hajiya ta kada kai, alamar ah ah.

Gwamna Halliru dai ya yi shiru, domin ko ya kirawo jami'an tsaro a kama Lawwali kamar ya yi ihu ne ya yi kirari ya dabawa kan shi wuqa a bainar nasi, in securities ne na gidan kusan rabin su Yaran Lawwali ne, shi ya horar da su, ga dai su nan yanzu sai yanda Oga yace.

Lawwali Wayar shi ya dauka, ya shiga videos ya kunna video Na farko da ya fara yi wa No 1 azaba, ya kunna ya miqa wa Gwamna,

"Ka bi ka ishan da waya tun hwarar sahiya, shi na nit-taho da kai na dan kawo maka wayar da mai wayar dan ka gan shi, gashi ku gani tare, dan Hajiya ta fi gane shin wane ne Lawwali, ya yake maida mutane in an ka ci amana tai"

Sanda Hajiya ta ga yanda ya ke zubawa No 1 ruwan batir a baya, fatar na qonewa kuka Hajiya Ikee ta fashe da shi,kan ta ta hango ana mata wanan izaya, ya zata yi?

Duk wata wahala No 1 ya sha ya gode Allah,kuma Gwamna da Hajiyar sun gani.

"Ina yarinyar take?"

Cikin matsancin fushi Lawwali ya miqe ya daki glass table din dake center din su, da bakin bindiga ya tarwatse a wajen, qara mai qarfi Hajiya Ikee ta sanya, ta qanqame Gwamna,

"Gwamna Halliru ina mai tabbatar maka da cewa ka tafka babban kure da ka ɗauke min qauna, ka san a wane hali wancan qaramin dan iskan ya jefa ta? Ka san me ya mata!  Ko akwai sa hannun ka a lalata ma qauna ta rayuwa? Akwai sa hannun ka ne!"

Cikin matsanancin tsawa yake maganar shi,wanda ta sanya Hajiya Ikee gama rushewa da matsanancin kuka, wannan shi ake kira da madaki kusa maceci nesan, da ta san wannan shi ne yaron da ake bata labari da bata so ma yi masa iskanci ba, labarin ta'adi da ta'asar shi ba wanda bata ji, ido da ido ne basu taba haduwa ba, da kuma sunan shi, ta san dai kowa Oga yake ce masa  amma bata san shi ne Lawwali ba.

Sultana da ke shiryawa ce ta ji qarar fashewar abu da qarfi, dan guntun tsaki ta ja, sannan tace,

"Masu girkin nan basu rabo da hwashe kwanna, (kwanuka) aiki suke kamar su na aikin hwashe dutsi"

Mai ta hau shafawa ta na tunanin kayan da za ta sanya dan burge masoyin ta, sannan ta na tunanin shin ta masa magana akan abinda ya mata ne jiya? Ko ta bari? Dan gaskiya ita bata son irin soyayyar nan ta zamani a yi ta kiss da sauran irin romace din nan.

A can parlour kuwa Lawwali ya titsiye Gwamna akan sai ya sanar da shi dalilin da ya sa ya sace masa qaunar shi,

"Lawwali baka san me ya hwaru ba, ranar da kun ka kawo mani yaro nan...wani almajiri, har niyyi wani aiki, to qaunar ka ta na gidan nan, ta gane ni, shi na dalilin da ya sa nic-ce a ɗauke ta, kuma ban ce a mata komai mara kyau ba, hasali ma har gida da kuddin da za a zanka sai mata abubuwan more rayuwa sai da na aika wa yaran ka, ban dauke ta da nuhin a cutar da ita ba"

"Me ya sa ba ka hwadi min abinda ke hwaruwa ba? Qauna ta ba mai Surutu bace,ta san aikin duk da nake maka, bana boye mata komi, bata hwasa yi min addu'a ita ko, akan Allah ya shirye ni, ko ta sani ba matsala bane, dan kuwa ba ta hwadi ma kowa, ta san komai, kahin ta gan ka,dan haka yanzu dai ka san ba a yi min ban rama ba ko?"

"Kai wa Allah Lawwali maganar ga ta wuce,"

"Ta wuce? Ashe ma ni ba dan halak bane, shin da na hwadi ma an lalata rayuwar qauna ta ka tambaya ka ji ya take? Saboda bata dame ka ba, kamar yanda lalacewar rayuwa ta bata dame ka ba,to ka sani, abubuwa daya zuwa biyu za ka min dole, in ba ka min ba,.....in baka min ba....ka ga wanan? Sai ya shiga duniya"

Hotuna ne da video da aka dauke su a tare, suna aikata mugayen ayyuka, wanda Gwamna ya yi matuqar mamakin yaushe aka dauka, a take anan, ya qara sallama wa lamarin Lawwali, abun nashi babba ne.

"Yan zu mi ka ka so? Kuddi, kadarori? Ko muqami a gwamnati, dan Allah kar ka tona muna asiri,"

"Kar in tona maka asiri dai, dan kuwa tunda kagga an doka hotuna da video din ga da niyya ka san ina da plans, ba haka nan nike zaune ba, and ko da an kama ni ka sani bani da asarar komi,"

"Lawwali ka sanar da shi abinda ka ka bida, ko mi ne ne zai maka ka ruhwa muna asiri"

"Ba kullum ikirarin in Gwauna yaddawo zai sa yaron shi ya kashe ka, sai na ga bayan ka...tau yanzu ta qare, ni ba na buqatar komi wajen ku a yanzu, amma ban muku alqawarin ba zan nemi wani abu ba a gaba, a yanzu buqatar diyar ku nake baku umarnin ku karba, in ba haka ba....."

Miqe wa ya yi, ya na bin su da wani irin mummunan kallon da ya sanya Hajiya Ikee matse hannun Gwamna  tare da toshe bakin ta da hannu daya dan kare kukan da ke son ya fito.

Bai ce komai ba bayan kallon daya baza musu ya bi ta hanyar da baqi ke shiga parlour'n ya bar wajen, kafin ya isa bakin motar Sultana ya maida bindigar shi bayan wando, ya mayar da wayoyin shi wandon shi, wayar No 1 kuma a gaban aljihun shi.

Hajiya Ikee kuwa ya na fita ta hau yi wa Gwamna masifa,

"Ashe annubar da ka dakko muna kenan? Yanzu ya zamu yi? Ya zame mana qadangaren bakin tulu, duk ta inda munka yi ba mafita, ka san me yake nufi da biyawa diyar mu buqatar ta? A aura wa Sultana shi fa, ni kuwa ba zan taba bari wannan al'amarin ya hwaru ba, ko zan rasa raina kuwa"..........

*Oga ko zaka dawo ne? Dan bana jin Hajiya ta ji Warning dinnan*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGGE 39:

Tinda ta duba ko ina bata ga iyayen nata ba, kawai se ta karya a gaggauce ta fita, da qudirin in ta dawo za su tattauna akan maganar Auwal din ta.

Tsaye ta gan shi, ya na yarfe hannun shi, jini ta ga ya na zuba, cike da tashin hankali ta kira sunan shi, su na hada ido ya sakar mata murmushin da ke sake nannade zuciyar ta cikin son shi, kashe mata ido daya ya yi, sanan ya ce,

"Ran ki shi dade kin gama mu tai?"

"Me ya sami hannun ka? Ka na zubar da jini! Mu je ciki na sa maka magani,"

Bai mata musu ba, ta kama hannun shi zuwa main parlour din su, su na shiga ta tarar da Sultan na bude qofar dakin shi,ya na fito wa, da alama bai jima da tashi daga bacci ba, shi ma da jinin da ke zuba a hannun Auwal ya yi arba, da hanzari ya qarasa isa gaban su,

"Subhanallah me ya faru haka?"

Hajiya Ikee da Gwamna ne ke tafe, kowannen su zuciya ba dadi, ganin me ke faruwa ne ya sanya su zuwa wajen suma,Hajiya ta tuna ya akai ya samu wannan raunin, sanda ya fasa masu table din su mai kyau da tsada ne ya samu ciwon, kauda kai ta yi ta bata rai, dan ba ta so ma ta kalli jinin da ke diga a saman tsadadden carpet din ta.

"Sultana tai ki dakko fist aid box,yi sauri"

"To Yah Sultan"

Duk ta kidime ta rude, a wajen Lawwali wannan is just a scratch ,amma su a wajen su babban ciwo ne, sai da Sultan ya gama gyara ma Lawwali ciwon sannan Sultana ta kalle shi, cikin kulawa ta ce,

"Gaskiya yau, ba inda zaka, ka zubar da jini da yawa, ka zauna, a samu wasu guards din su kai ni"

"Ba za a yi haka ba Ran ki shi dade, ba damuwa ai an saka min magani, zan iya kai ki"

"Ni dai gaskiya ahhh ahhh, Daddy ka ce wani abu manaa"

Gwamna Halliru ba abinda ya ke da ya wuce kallon ikon Allah ,yaushe Lawwali ya ci shi da yaqi haka?'yar shi har bata iya boye soyayyar shi a gaban su, murmushin gefen baki Lawwali ya yi, ya kafe Gwamna da idanun shi da ke dauke da kallo irin na tsokana.

"Daddyyyy ka mishi magana pls, ya ji ciwo a hannun shi fa"

"Amm...uhmmm..Lawwali ina ga ka d'ai zauna, zan samu masu kai ta kawai"

"Ran ka shi dade Sultana ba uwar daki na bace kadai ta nada matsayi mai girman da ba zan iya barin wani abu ya same ta ba, kasan yanzu yanda duniya talalace, kana kauda ido sai ka nemi naka ka rasa,"

Cikin wani irin salo da kwarewa ya yi maganar, Hajiya Ikee da Gwamna sun gane karatun, karr kuma tarr a zuqatan su.

"Sultana kar ki damu, kuje kawai, wa ya fada maki, dan wanga ciwo na damun mazaje? Ai zaman gida se mata"

Har sun kama hanya za su fita Sultana ta koma ciki,cike da dan jin nauyi ta tsaya gaban Daddyn su, tare da kama hannun shi ta ce,

"Daddy, tunda Allah ya dawo da kai lafiya, ga ka ga Hajiya, Yah Sultan da Auwal din kan shi, ka jima ka na min magana akan rashin kula maza da nake, ka na cewa a haka zan yi aure watarana? Tau Daddy yau ina so na sanar da ku cewa na zabi Auwal ya zama abokin rayuwa ta, dan Allah Daddy kar ka ce ah ah, shi nake so, shi nake fatan ya zama abokin rayuwa ta, ba zan iya rayuwa da kowa a matsayin miji ba bayan shi,dan Allah Daddy"

Hajiya Ikee ce ta bude baki za ta yi magana, suka hada ido da Lawwali da ya sunkuyar da kan shi, amma idanun shi na d'age ya na kallon kowa,kallon da ya mata ya yi matuqar shiga kowace kafa ta jikin ta, nan take ta tuna maganar da Gwamna Halliru ya mata a can parlour'n baqi.

'Ke hwaa baki da hankali, sai ki dinga abu babu lisahi,halan baki ga mi ya nuna mana ba, ido da ido kin gan ni sanda na ke duba makaman da za a kai musu daji,tare da ni da su muna hira cikin nishadi, ido da ido kin ganni ina yanka jarirrai har guda ukku (jarirai) kin ga yanda ya ke kisan mutane kamar ya samu kiyashi,amma kin fi so wai har sai asirin mu ya tonu sannan ki nutsu, d'iyar da ki ke taqama taki ce, za ki aurawa shugaban qasa ta san me muke aikatawa sai ta tsane mu,Za ki iya jure tsanar da 'ya' yanmu za su yi mana? In ki na iyawa ni ban iyawa, Sultana ruhi na ce, ba zan taba bari wani abu ya same ta ba, dan su nake duk wanga abu da kika gani, dan na wadata su da dukiya da jin dadin duniya nake abubuwan ga, dan haka in ki ka kuskura ki ka kawo abinda Yaron nan zai bata min suna a duniya, sai na halaka ki da hannu na wallah'

Ihun murnar Sultana ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula, Sultana ce ta saki daddyn ta,ta tafi da gudu kamar wata qaramar yarinya, ta fada jikin Hajiya Ikee, ta ce,

"Hajiya Daddy ya amince, zai aura min Auwal, Hajiya ba ki ce komai ba, kin amince da zabi na?"

Wani abu ne mai daci da maqaqi ya tokare wuyan Hajiya Ikee, har wani d'aci-d'aci take ji a wuyan ta, idanun ta sun qanqance, saboda baqin cikin da ke cin zuciyar ta, amma ba halin bayyanawa, cikin Muryar da kamar shaqe mata wuya akai, ta ce,

"Na amince, Allah ya sanya albarka"

Rungume ta Sultana ta yi, ta na farin ciki sosai, ranta fari tass, kamar madarar shanu, Sultan ma sai wangale baki yake, ya na taya qanwar shi murna.

Dan gyara tsayuwar shi ya yi, ya wani turo qirji gaba, shi a dole ga babban yaya, gyaran murya ya yi, sannan ya ce

"Ban gane ana ta neman izini ba , ba wanda ya nemi nawa?"

Lawwali ne ya duqa cikin wasa, da dariya, ya ce,

"Ran Babban yaya shi dade, a mana ahuwa, ina neman izinin auren Sultana a hannun ka"

Cikin dake wa, Sultan ya dafa kan Lawwali, ya ce,

"Na baka izinin auren qauna ta, Allah ya muku albarka,"

Dariya sosai Sultana take, Lawwali na taya ta, Sultan ma cikin dariya ya dafa kafadar Lawwali ya ce,

"Congratulations man,Allah ya sa ayi da mu"

"Thanks bro, ameen, bari mu tai, lokaci na tahiya"

"Yau ba za mu zauna mu yi murnar wannan rana ba?"

Cikin shagwaba Sultana ta fadi hakan, ta na dan noqe kafada, ba qaramin kyau ta wa Lawwali ba, iyayen ta kuwa a zuciyar su sai suka gan ta, kamar yar qaramar yarinyar su, da suke matuqar lele, da qauna a zuqatan su.

Sultan ne ya kama kumatun ta, cikin sigar wasa ya ce,

"Ohhh Baby Sulty za ta zama babbaaa, ki tafi NGO din ki, ki gode Allah ma ki na da abun yi, unlike me, sai dai a dahwa a bani na ci, na kwanta, da jikin qiba gare ni, da na fi wata mata da aka kira da Hameedan Hamma (Lols)"

Dariya sosai Sultana ta yi, amma abu daya na d'an damun zuciyar ta, kallon kallon da ke tsakanin iyayen ta da Lawwali, da kuma rashin fara'ar su, da walwalar su, a wajen ta wannan babban abun farin ciki ne, da sauri ta kawar da tunanin komai, da ta tuna dalilin da ya sa iyayen ta ba su cikin farin ciki sosai,Lawwali talaka ne, kuma driver, sun amince ne kawai saboda farin cikin ta, babu komai, hakan ma sun taimaki rayuwar ta ai, ta na godiya.

Sallama suka ma iyayen na su suka tafi, ko da ya je bude mata mota da sauri ta bude, ta ce ta gode, ya kula da hannun shi, ba dan ya ce ba komai ba ma, yau ba inda za su.

Zuciyar su fari tasss suka isa, Lawwali kan shi jin amincewar su Hajiya Ikee ya ke a matsayin wata babbar nasara da ya taba samu a rayuwar shi,duk da dai har yanzu auren Sultana ya na nan a matsayin auren daukar fansa a zuciyar shi, (zan so ganin anyaa Oga zai cika wannan alqawari da ya daukar wa kan shi? Sultana ce fa).

************************

Kwanan su Hansatu uku ba wuta, saboda NEPA sun yanke musu wuta, sakamakon rashin biyan kudin da ba su yi ba, wayar ta babu caji, sai dai ta kai gidan 'Yabbuga, daga kaiwa jiya, yau an kai 'Yabbuga ta fara masifar za a dame ta da saka cire din caji, ba aikin ta ba kenan, kar su dame ta.

Dan haka Hansatu da kan ta, ta saka Hijabi ta kai wayar ta gidan Asshibi, dan sun dan saba yanzu, su na dan ziyarar junan su.

Ta tarar da Mijin Asshibi zai fita, suka gaisa, ta tambaye shi ko Asshibi na nan ta kawo caji ne, ya tabbatar mata da cewar ta na ciki, ya fice abin shi.

Ya na shiga Mota ya danna kiran Isah, bayan sun gaisa, ya tambaye shi ya Makkan, Isah ya kalli kayan abincin da ke gaban shi, ya shafa tumbin shi da ya fara ajiye wa ya ce,

"Laminu Makka ta yi, ka ci ka sha ka kwanta ka yi bacci, ba me tashin ka,in kuwa ka na da suruka kamar tawa ko ba ka sana'a zaka warwasa Alhaji"

"Shegen kaya, ka na can ka na tatsar surukar ka a nan"

"Bari kawai Laminu, shekaran jiya ni ce mata an kwace sauran goro da ni tai da shi, ta tausaya min sosai, ta aikon
Showing 81001 words to 84000 words out of 150481 words