baya ba kalar wulaqancin da ban yi wa iyayen yarinyar ga ba, da ita kan ta, amma ka diba ka gani, a yanzu ita ka qoqarin kwantar muna da hankali, saboda halin damuwar da muke ciki,ita ke qoqarin ganin na san wane ne mahalicci na, na shekara d'ai d'ai har shamshin da shidda amma ban iya karanta qur'ani ba na bata rayuwa ta a banza ban san wanene ubangiji na ba, ban taɓa karanta kalma ɗaya ta alqur'ani ba tsabar rashin rabo, boko kuwa ko da baturiyar qasar Amurka sai mun buga, ka diba ka gani, a wata d'aya yarinyar ga ta hwara sawa ina iya karanta wasu kalmomi na larabci, na qara yarda da cewa, kyawun huska, ko wani kyau na halitta, ba shi kad'ai ne kyau ba, kyau shi na cikin kyakkyawan hali da d'abi'a, wanda ya rasa su, komai kyawun huska shi mummuna ne, ina goyon bayan auren ku, dubu bisa dubu ma Sultan, Mubaraka ita ce ta hi dacewa da rayuwar mu baki daya,Allah shi yi muku albarka"
Hannun Hajiya Ikee Sultan ya riqe a nashi gam gam, sannan ya sumbace su, cike da murna, ya dinga godiya,a haka su Sultana suka tadda su, Mubaraka kuwa tun da ta ji Hajiya na yabon ta taso guduwa, amma Sultana ta riqe ta, sai da suka gama, magana sannan Sultanan tai gyaran murya, ta ce,
"Mu shigo an bamu izini? Kar ku ce mun yi maku labe, mun ji shiru ne shi na mun ka taho mu ji ko lahiya?"
"Ku shigo, 'yan sa ido, kun dai taho ku ji mi muka fadi, to kun dai jiya, Hajiya ta amince na auri B love di na"
"Tauuuu mi na na kuma B love?"
"Sultana ba kyau sa ido, ba ruwan ki, ni kadai na san me na ke nufi da hakan,kalla yadda Mubaraka kanta ta baza kunne ta na so ta ji ma'anar B love, ban fad'i to, yarinya rufe kunnuwan,"
Cikin jin kunya ta sa hannayen ta ta rufe fuskar ta, tabbas kuwa ta tsaya ne ta ji me ye ma'anar B love din, kuma ya gano ta.
Juyawa ta yi da sauri za ta fita ta ji ya kira sunan ta, da wata iriyar Muryar da ta sanya ta tsayawa cak ba tare da ta shirya ba, daga Hajiya har Sultana ba wanda ya qara magana, dan su ma za su so jin me Sultan zai fadi da mahimmanci haka, har da sauya murya.
Takawa ya yi zuwa gaban ta, ya tsaya, kallon idon ta yake so ya yi amma ta maida kan ta qasa, kunyar Hajiya take ji, amma ta kula su ba ruwan su,
"Kalle ni Mubaraka,"
Da kyar ta d'aga kai ta kalle shi, idanun su na haduwa da na juna, ta ji kamar an kafe nata, kasa kauda kan ta tayi daga barin kallon shi,
"Mubaraka za ki aure ni? Za ki taimake ni ki tausaya wa Maraya Sultan ki aure shi? Ki sani ba ni da dukiya, ba ni da aikin yi, amma ina tare da dimbin soyayyar ki, wadda na ke jin ta ishe ni qarfin guiwar zama komai da na ke so na zama a rayuwa, da izinin Allah, so Mubaraka za ki aure ni?"
Wasu irin hawayen farin ciki ke mata gudu a kunci sai qaiqayi suke mata, gashi ta kasa daga hannu ta sosa kuncin nata, jikin ta ya mace murus, yau wai ita namiji had'add'e kamar Sultan ke neman aure ta wannan sigar? A gaban mahaifiyar shi, da qanwar shi, ita d'in wace ce? D'iyar tallaka, qanwar tallaka,sannan ita kan ta bata mallaki komai ba, ita ba wani kyau na a zo a taru a sha kallo ba, Sultan ya fita komai, kyawun shi ma abin kallo ne, kyawun shi ma kyakkyawa ne, ga kyawun hali, da d'abi'a, anya bai fi qarfin ta ba, ta sani ba wani namiji da take wa so irin na soyayya bayan shi, amma a yau sai ta ji gaba daya bata cancanci zama matar shi ba.
Cikin murya mai cike da rawa, ta ce,
"Yah Sultan ka dai san kai ba sa'an aure na bane ko? Ka hi ni komi da komi a rayuwa, ba...."
Sultana ce ta katse ta, ta hanyar sanya hannu ta share mata hawayen ta, sannan ta ɗan ja kumatun ta, ta ce,
"Kar na ji kalmar rejection ta fito a bakin ki, zan qi komawa gidan Yayan ki, Hajiya mu basu waje, wataqila kunyar ki taka ji, ke ko kin zauna dirshan ki na kallon su awa ke samu TV"
Dariya sosai Sultan da Mubaraka suke, Mubaraka na dariya hawaye na qara saukar mata, yau rana ce mai cike da farin ciki a wajen ta, ina ma ace Yah Auwal na nan, yaji yanda Namiji kamar Sultan ke bayyana mata ra'ayin shi akan ta.
Bayan fitar su Hajiya Sultan ya sake roqon Mubaraka, akan ta amince da auren shi, dan tura baki ta yi, cikin shagwaba ta ce,
"Ni dai ka dena roqo na haka, dan kuwa ba ni da wani abun baka,mutum guda na zai iya baka amsa, shin zan iya auren ka ko ban iya wa,"
"Ni dai dan Allah kar ki had'a ni da Auwal"
Cike da dariya Mubaraka ta ce,
"Ashe ma ba ka so ka aure ni, wajen shi za ka je wallah, in yace shi na baka niii, to zan aure ka, in yace ba zai..."
"Ya isa haka nan, zan je wajen shi,kuma na tabbata, in da zan je da sadaki na a lokacin zai aura maki ni, "
"Me zai hana ka tai da sadakin gaba ɗaya, domin na mallake ka a matsayin miji na cikin gaggawa"
Yanayin yanda ta yi maganar ya kawar masa da komai, na tunanin ko dai bata yi da shi,zuciya bata da qashi, dan har ya fara tunanin ko Taheer take so, sai ya ji kalamai masu ɗauke da gaskiyar abinda ke zuciyar ta.
Cikin jin kunya ta bar dakin nashi, shi kuma ya bi ta har bakin qofa ya na murmushi, har ta sauka qasa gaba daya bai bar wajen ba, ya na nan tsaye ya na murmishi.
Sultan kuwa bai bata lokaci ba, da daddare ya sha wankan shi, da manyan kaya, ya nufi gidan Lawwali, ya tarar da shi ya na waya da Sultana, sallama ya mata, ya ce zai sake kira ya yi baqo.
Sai da suka gaisa, Lawwali ya sake yi masa ta'aziyya, sannan Sultan ya kalli gidan, ya ga yanda Lawwali ya qayata shi, ya gyara shi, kamar gidan sabuwar amarya.
"Lallai ka na ji da matar ga taka, irin wanga gyara kamar za a kawo maka sabuwar amarya? "
"Ka gyara kalaman ka, dan kuwa Sultana sunan ta kin fi amarya"
Sultan kuwa langwabe kai ya yi, ya yi kalar tausayi, sanan ya ce,
"Allah Sarki,mu gamu mu na son a bamu tamu amaryar amma ba wanda ya damu da halin da muke ciki, har yanzu an kasa gane mun isa aure, a aurar da mu, sai mun aje kunya a gehe mun roqa a muna aure"
Lawwali me zai yi in ba dariya ba, shi ma Sultan d'in dariya ya dinga yi, cikin dariya Lawwali ya ce,
"Yanzu dai ka ce aure ku ke so, kuma maganar neman aure ta kawo ka ko?"
Gyara zama Sultan ya yi ya ce,
"Gaskiyar kenan, ni na rasa iyakar son da Mubaraka ke yi ma, wai na yi na yi ta amsa min buqatar auren ta da na je mata da shi,ta ce sam sai ka amince"
Murmushin jin dadi Lawwali ya yi, sannan ya ce,
"Indai ni ne na amince, na baka goyon baya ka ci gaba da saye zuciyar qauna ta, har sai ta amince ba wani namiji sama da kai a rayuwar ta,"
"Tabdijam, ka dai ce ba wani namiji da zata so da aure sama da ni, amma har duniya ta tashi kaine namijin farko kuma na qarshe da take so, na gode sosai da amincewar ka"
Nan dai suka yi ta hira, Lawwali na bashi labarai akan Mubaraka, abinda take so da wanda bata so, har qaddarar da ta fad'a mata tsakanin ta da No 1,Sultan ya tabbatar masa da cewa, ba namijin da ya dace ya auri Mubaraka sama da shi, ta sanadin Daddyn su haka ta faru, dan haka shi ke da alhakin auren ta, ko da ace ma ba ta sanadin Daddyn su bane, shi dai ya ji ya kuma gani ya na son ta a duk yanda take, ita yake so ba jikin ta ba,shi ma Sultan haka ya dinga fadawa Lawwali abubuwa akan sultana, daga qarshe Lawwali ya kira Mubaraka, ya fada mata amincewar shi, cikin jin kunya ta yi masa godiya.
Lawwali ya bawa Sultan shawara, akan ya tura magabatan shi wajen Baban su, a da ya so shi zai aurar da ita da kan shi,amma ganin mahaifin su na nan da rai, kuma shiriya ta zo masa, ya yi nazari shi ya fi cancanta da ya aurar da diyar shi, sai dai in ya wakilta shi,zai so hakan.
Sallama Sultan ya yi wa Lawwali ya tafi gida.
Ko da ya isa duk sun yi bacci, abinci ya ci, ya je ya kwanta shima, cike da tunanin yanda zai mallaki masoyiyar shi Mubaraka.
*************************
Su Yayah Musah sun sha wahala kwarai kafin Isah ya hakura ya rubuta wa Hansatu saki,dan sai da suka had'a da barazanar za su had'a shi da hukumar qasar, a sanar da duk abinda ya aikata wa matar shi, ya tsorata kwarai dan ya san bai aikata daidai ba,gashi Saudiya ba sa wasa da jinkiri wajen yanke hukunci, Isah na kuka har da majina, ya rubuta wa Hansatu saki d'aya.
A satin suka juyo gida Nigeria Yayah Abdullah murna a qasan ran shi kamar me, amma a fuska ya dinga jimamin lamarin, ya na jaddada rashin adalcin da Isah ya aikata wa Hansatu.
Ko da suka iso gida, Hajiya ta yi farin ciki da samun nasarar raba Hansatun ta da azzalumi Isah, Hansatu kuwa yaqe ta dinga yi, ko ba komai akwai sabo, kuma shi ne uban yaran ta.
Da dare sai da ta ci kuka ta godewa Allah, ta na tsaka da kukan ne ta ga wayar ta ta yi haske, ko da ta duba sai ta ga baquwar lamba, sallama ne kawai sai gaisuwa, da jajanta mata abinda ya faru da ita, mamaki ne ya kama ta, bayan ita da mutan gidan su wa ya san meke faruwa da ita? Lallai lamarin duniyar nan abun tsoro ne labari har ya baza gari.
Ba tare da ta amsa gaisuwar ba ta ajiye wayar, koma waye, ta ji da safe, yanzu dare ya yi.
Tunda Isah ya sawwake wa Hansatu auren wahalar da ta ke fuskanta, duk ta rame, ta zama wata kamar mara lafiya, a so samun ta, ya gyara halayen shi, su ci gaba da zama hakan, sai dai kashhh sanin abubuwan da ya aikata sun ja mishi rabuwa da ita, ba dan an ce sabo turken wawa ba ma, da ko tunanin shi ba zata yi ba, amma ta saba da shi, da halayyar shi, da kuma son shi, su ke wahalar da ita, kafin ta saba da rashin shi zata dau lokaci, wanda bata fatan hakan.
************************
Yau Mubaraka ke so ta koma gidan su, Sultana da Sultan sai lallaba ta suke akan ta yi zaman ta,ta qi sam,ta ce ya kamata taje ta ga halin da iyayen ta ke ciki, mussamman tunda ta jima ba ta gidan .
Hajiya Ikee ta yi ta mata godiya, da za ta tafi ta rasa me zata bawa Mubaraka, Mubaraka ta fahimci hakan, dan haka ta cewa Hajiya,ta sa mata albarka kawai, ya ishe ta, shi ne babban kyautar da ta ke so ta mata, albarka kuwa Hajiya ta saka mata, suka raka ta har bakin gate, Lawwali na mota ya na jiran ta.
Su na had'a ido da Sultana ya marairaice fuska, shi adole ya na so ta tausaya masa ta koma haka, ba ya so ya furta, tunda ta yi babban rashi, ba zai so a ga rashin hakurin shi ba, bayan Mubaraka ta shiga Mota ne, Hajiya Ikee ta ce,
"Allah shi kiyaye, muna godiya,kwarai kwarai, Allah shi yi muku albarka, Auwal in ka kai ta gida, ka biyo ka dauki matar ka ku wuce haka nan, Allah shi bada lada, Allah ya jiqan Daddyn su, rashi dai an riga an yi shi, ba a zauna ba ba tare da an koma zaman aure ba, zaman ya isa haka nan, gani ga Sultan babu komi, da ka Kaita ka dawo ku tahi"
"Ni fa ba yanzu zan koma ba"
Da sauri Lawwali da ke ta murna ya kalle ta, cike da mamakin yanda ta ke qin komawa qarfi da yaji, ga mamakin shi kuwa sai ya ga su na ta mishi dariya, dama wasa ta ke,
"Auuuu zolaya ta ki ke ko? Ke dau bashi wallah"
Jan motar shi ya yi, ya bar su nan tsaye su na mi shi dariya, Mubaraka ma dariya take.
Kamar yanda Hajiya ta alqawarta kuwa, haka ya je da dare ya dauki Sultana, wadda ta sha gayu kamar amaryar da za a kai dakin miji, sai qamshi take zubawa, ta yi haske,ta ciko sosai, har Lawwali na mamakin qibar da ta yi, ita da take cikin jimamin rashin mahaifin ta.
Sultana kuwa ta matsu su je gida ta masa babban albishir.
Ko da suka isa gidan,ta yi matuqar farin cikin ganin yanda ya gyara gidan sosai,kamar baquwa haka ya dinga shiga da ita sashe sashe na gidan,ta na gani.
A dakin su suka tsaya, ta na tsaye ta na kalle kalle ya dauke ta, qara ta saki saboda matse mata ciki da ya yi, da sauri ya ajiye ta, cike da shagwaba ta kai masa dukan wasa a qirji, ya tare hannun ta, ya na bata hakuri,
"Ko dake ni za ki bawa hankuri, kin ji baya na, awa zai qalle, ke yi nauyi yanzu mi ki ke ci ne haka?"
"Ba dole na yi nauyi ba, tunda ka min babbar ajiya,"
Cikin rashin fahimta ya ce,
"Shin ajiyar mi na yi maki kamar wani maye? "
Ta na wani irin kyakkyawan murmushi ta kama hannun shi ta ɗora a saman cikin ta, ta na shafawa, tare da cizon leben bakin ta na qasa,
"Ga ajiyar nan, ita ta ke sani cin abinci sosai, har na yi qiba,"
Lawwali wata iriyar zabura ya yi, ya yi baya, ya na toshe bakin shi da hannayen shi dika biyun, murna ce sosai da bata iya boyuwa a saman fuskar shi, Ita kuwa bin shi ta yi ta fada jikin shi,ya kuwa rungume ta ya na sumbatar ta ko ta ina, su nata dariya, a hankali ya kai bakin shi kunnen ta ya ce,
"Na gode Sultyna, Allah shi yi miki albarka, da ke da abinda ke cikin ki, Allah ya sauke ki lahiya, ya bani ikon kula da ku, Allah ya raya mana Muhammad, in mace ce kuwa Ayshaa nika so a sanya mata"
"Ameen ya Allah miji na, kuma uban yara na,Sunan mahaifan ka ne?"
Kama ta yayi, suka zauna a bakin gadon su, ya ci gaba da shafa cikin nata, da in ba an fadi ta na dauke da ciki ba ma, ba mai ganewa,
"Ahh Ahh, ina son sunan Muhammad ne saboda ina fatan Allah ya sa ya yi koyi da Annabi Muhammad, in mace ta kuwa, ina so ta yi koyi da Nana A'ishah, domin kuwa yanzu ba ni da abin kalla in na zauna ni kadai ga YouTube sai wa'azi , da duk wani abu da nissan zai amfane ni, anan na ke jin tarihin su,"
Sultana ta ji dadi matuqa,cikin murmushin da ta kula ya qi barin fuskar shi tun da ya fara maganar Annabin rahama, ta fara kissing din shi, sannan ta ce,
"Ya kamata na baka tukuicin amfani da lokacin ka akan abinda ya dace"
Juya ta ya yi, ya kwanta a saman ta, ya na kallon cikin idon ta, fuskar su dauke da fara'a ya ce,
"Ya kamata na baki tukuicin kular min da ajiyar da na baki, sannan ki karbi hukuncin qin sanar da ni da wuri da baki yi ba"
Cizo ya kai mata a wuya, na wasa,daga nan na ga ya fara......sai na gudu, saboda an hana ni sa ayis a gidan mutane.....
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 63
A rumfar Dan Talo ya tsaida motar shi, Lawwali har qasa ya durqusa ya gaida mahaifin shi,cikin jin nauyin haka Dan Talo ya amsa, dan bai saba ba, shi kan shi Lawwalin be saba ba, ganin Mubaraka na yi ne ko da yaushe, ya sanya shi yi a yau.
Abokan Dan Talo da ke zaune a rumfar sai mamaki suke, daya bayan daya suka dinga zamewa su na barin wajen,hira suka dan tab'a, Lawwali na tambayar shi yanayin kasuwancin,
"Kassuwa dai gata mun godewa Allah, tafi zaman banza, ka ga ana samun na cefane,ga kuma hirar dai ana yi, abukkai na na zuwa kullum muna hirar mu, "
"Da kyau, Allah shi taimaka, ai dama shi rai dangin goro ne,ya na bidar damshi,"
"Haka nan na, ka ga ban samu na koma gidan rasuwar nan ba gashi har an yi arba'in,Allah shi jiqan gwamna"
"Ameen, ai ba komi,ga Barakana nan, ta je, ta zauna musu, ai ta wakilce mu dika,barakana shiga gida,gani nan zuwa"
Amsawa ta yi da "to" sannan ta shige ta bar su, anan Lawwali ke sanar da Dan Talo abinda ke faruwa tsakanin Mubaraka da Sultan, ya yi farin ciki sosai, sannan ya amince Lawwali ya zama waliyyin ta, Lawwali ya yi ta godiya dan kuwa dama yana son hakan.
"Amma fa nan za su zo, tambaya, dan zan so koma me za a yi ya zama an yi shi a nan gidan, nan ne tushen mu, da nan muke taqama,"
Dan Talo wani irin abu ya ji mai sanyi na kwaranya a zuciyar shi,ba ilimin addini, balle ya godewa Allah akan ni'imar da ya mishi, haka dai ya ke ta jin daɗin shi, a zuciyar shi, har suka gama magana Lawwali ya shiga ciki.
Ya tarar da Matar Yahai na ta bada labarin abinda ya faru da mijin Asshibi da Hansatu, sai zaqewa take da qarin gishiri, su na hada ido da Lawwali wai ita wayayyiya, a dole ba ta tsoron shi, ta ce,
"Ango ka sha qamshi"
Daga mata hannu ya yi, sannan ya ce,
"Sannu, sannu uwar gulai uwar munahurci, watakam waccan qandarabushe munahikar lungun ta dena zuwa, ke kin karbe ta ko? To ki
Showing 138001 words to 141000 words out of 150481 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47 Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51