sai dai ta ji maganar shi a bakin mahaifiyar ta, ba komai, za ta bashi mamaki.

Tattare kayan ta yi, ta ware duk wanda ya kamata ta ware, sannan ta kira su Ameena ta deba musu soyayyan naman suka ci, cikin nishadi.

**************************

"Ni fa Sultan ban san me ke faruwa ba, yau kwana biyu kenan, ina kai qawaye na gidan su Sultana Amma ina ganin gidan a ruhe ,shin lahiya? Ko ba kuyin waya ne kaima? Dan ni dai na kira layin ta ba shi shiga"

"Ni ma dai layin nata bai shiga Hajiya, amma na san duk inda take ta na tare da mijin ta, kar ki damu"

Ai sai a wannan lokacin ne hankalin ta ya shiga jikin ta, a zabure ta miqe, ta hau kiran layin Gwamna Halliru, ta kira ya fi sau hudu ana sanar da ita ya na meeting,daga qarshe masifa ta balbale mai amsa wayar ta ce ya kai ma gwamna wayar shi, ba ruwan ta da wani meeting ita.

Yanayin yanda ta daga hankalin ta ya bawa Sultan Mamaki.

Mene ne abun damuwa dan an ce mace na tare da mijin ta ba kwarto ba????......

*Gane min hanya Sultan, wai makaho ya so gulma*


💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH



PAGE 46:


Fitowar gwamna Halliru daga meeting ba wuya, Hajiya Ikee ta sake kiran wayar, da  sauri aka miqa masa ya karba, bayan ya amsa ne ya kara a kunnen shi,jin Muryar Hajiya cikin tashin hankali ne ya sanya shi matsawa daga cikin mutane, ya fara tambayar ta dalilin tashin hankalin ta, Sultan ta kalla wanda ya dauki remote ya na sauya tashoshi hankali kwance, ta ɗan matsa daga inda yake, ta fara magana.

"Sultana fa da wannan shegen yaron ba su gidan su,ni ina jin tsoro musamman tunda ka ga basu fada muna inda su ka tafi ba, Kuma gashi ba a samun ta ga waya"

"Kwarai da gaske yau nake so na tambaye ki ko ku na waya, ban samu dama ba, tunda ban kwana gidan ba, amma abin ya na dauren kai ace ba ta kiran kowa, bari zan bincika in ji, ki kwantar da hankalin ki, kin dai san ba yarinya bace ke, tunani kadan zai sa miki ciwo"

"Wai kai in ba ka fadan baqar magana ba baka jin dadi ko? To ai na san ba yarinya ni ke ba, ba se ka maimaitan ga kunne na ba"

A hasale ta kashe wayar ta koma ta zauna, tunani ya mata yawa, ina su Sultana suka tafi?

Miqewa ta yi ta haye sama, Sultan na bin ta da kallo, tunawa ya yi, me ya sa wai ba zai kira Lawwalin ba, ya ji su na ina?

Gwada layin Lawwali ya dinga yi be samu ba, murmushi kawai ya yi, da dukkan alamu ba sa qasar nan, kallon shi ya ci gaba da yi hankali kwace.

****************************

Hansatu ce ke ta duba kayayyakin da babu a gidan,ta na ta rubuta abinda za ta siyo in ta je kasuwa, gani tayi garin da Hajiya ta haɗa mata, take kunu da shi ya qare, gashi bata san kayan hadin ba, daki ta koma ta dauki wayar ta, ta kira Hajiyan, sai da suka gaisa, sannan ta ce,

"Hajiya kayan hadin garin kunun nan ni ka so ki hwadi min, ya qare, ina so na hada wani"

"Tau ki na ji ba, in kin je kasuwa, ki bidi wajen masu awo, ki siyi, alkama Sa'i guda (kwano daya/mudu daya), ridi rabin sa'i,(kantu) farar shinkafa rabin sa'i , aya irin qananan nan na kunun aya rabin sa'i, sai ki tai wajen masu Islamic chemist, sun fi saida hulba mai kyawu, ki sai hulba mai kyawu roba biyu, ki sai diyan ('ya'yan) habbatussauda, to da kin dawo gida gyara kowannen su za ki yi, ki wanke, ki busar, hulba kuma ki soya ta haka nan, sai ta yi qamshi, sai ki game su, a niqa miki kamar gari, sai ki zanka damawa ki na sha da madara, wannan hadin man shi na nan be qare ba ko?"

"Eh Hajiya be qare ba, ko ba man tahwarnuwa (tafarnuwa) da man hulba, da man zaitun, da man hancin kade, (kaninfari) ba? Shi na nan ina yin matsi da shi, kuma na ji sauqin qaiqayin da na ke ji sosai, na ji har da matsi shi na yi Hajiya,"

"Kwarai da gaske shi na da kyawu kwarai wallah, tau yanzu ga wani ki siyo in ki na tahowa, ki siyo man zaitun, da man hulba, ki game su waje guda, ki Zanka shafawa ga maman/nonon ki, shi na da kyau kwarai kwarai,"

"To Hajiya na gode sosai, Allah shi saka maki da alkhairi"

Sallama suka yi, ta kira Ameenah ta ce ta kula da gida,da qannen ta, ta ce ta kulle gidan, in an buga bata leqa ta gan ta ba, kar ta bude ko da ta ji Muryar ta,ta sanar da ita za ta duqar da kanta jikin wata yar bula da ke kofar in suka hada ido to sai ta bude mata.

Ta na fita kuwa Ameenah ta yi kamar yanda Umman su ta ce, Ita kuwa hansatu bakin ta dauke da addu'ar bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala quwwata illa billah ta bar gidan, ta na tafe ta na yin dik wani tasbihi ga Allah da ya fado bakin ta.

Hansatu saboda ta san ta bar yara su kadai bata wani jima ba ta koma.

Sai da ta musu abinci, ta gyara gidan sannan ta samu carrot da cucumber ta goga su a abun goga kubewa, waje mai qanana qananan, sai suka fito kamar an markada su, ruwan ya fito sosai.

Tace ruwan ta yi, ta zuba masa zuma, da lalle, da madara kadan, sai sugar da dan gishiri, sai baking soda da ta siyo, ta fasa kwai guda daya, ta matse lemon zaqi daya, da lemon tsami daya, sai madarar turare mai qamshi, sai kurkur, ta juya sosai sannan ta bi jikin ta duk ta shafa, Ahmad ne ya dinga nuna ya na jin tsoro, ai kuwa ta dinga bin shi, su na ta guje guje da wasa da yaran nata, su na kyalkyala dariya.

Bayan ya yi awa daya ta je ta wanke jikin ta ta yi fesss.

Man carrot din da ta hada sati biyu da suka wuce ta dauko ta ga ya yi yanda ake so, ta tace, ta diga masa madarar turare ta shafe jikin ta da shi, nan da nan ta dau qamshi da kyalli, duk wanda ya san Hansatu a baya, ya gan ta yanzu ba zai tabbatar ta samu sauyi mabayyani, ta hadu ta hadu ta gaji da haduwa, ta cika ta yi bul bul da ita.

(Yanda ake hada man carrot, za ki wanke carrot din ki ki kankare dattin ki goga a abun goge kubewa, ki zuba a mazubi mai murfi, sai ki kwara masa man zaitun/kwakwa ki rufe, duk bayan kwana biyu ki dauko ki juya ki juya,ki mayar ya qara kwana biyu, a haka har sai ya kai sati biyu, zaki tace, ki na shafawa ya na matuqar gyara fata kwarai)

Hansatu dai da yara kullum a cikin gyara gida suke da kan su, ta sanya sabuwar ledar daki, ta sauya zanin gado da labulaye, ta sauya masa food flask ,ta sauya masa jug da spoons,hatta da sleepers sai da ta sauya masa, ta sai masa towel din wanka.

Yau ma kamar kullum sun gama gyara gida Hansatu na zaune ta na kallon qaramin madubi, ta na ganin yanda fatar ta ke sheqi, kalar ta mai ruwan cakulan mai duhu na komawa wani ruwan madara mai haɗe da coffee kadan, sai zabga murmushi take, dan ta san ta gama komawa mace mai aji, macen da ta fi qarfin walaqancin namiji, ta kowanne fanni, sauran abu daya take so ya faru, dan ta qara kankaro darajar ta.

A baya rashin kudin gyara jikin ta, da rashin bata abincin da zata ci mai kyau ya gina mata jiki, ta amfana shi ma ya amfana da ita, ya sa duk ta lalace ta kowanne fanni, hatta da gashin ta a da ya lalace, ba wani tsaho ba kyawun gani, dan ko man kitso bata da shi.

Komai nata a lalace a wulaqance, amma a yanzu wannan Hansatun ta daban ce, dan ko a da ba ta yi wannan haduwar ba, a yanzu in Isah ya gan ta ya kuma kusance ta bai sauya hali ba, to ba zai taba sauyawa ba.

Tashi ta yi ta shiga daki, ta dauki turaren musk fari mai kyau din, ta dangwala a hannun ta ta shafa a gaban ta, ta fita wanke hannu, ta tsaya cak, cikin tsananin mamaki, da farin ciki.

Tunawa da abubuwan da Isah ya mata ne ya sanya ta shanye farin cikin ta a cikin ta, ta wuce ta wanke hannun ta, ta koma inda yake a tsaye ya na bin ta da kallon mamaki, shin Hansatu ce ko wata yar uwar su?

Ya na nan tsaye ta isa gaban  shi ta karbi jakar da ke hannun shi, ta bar masa akwatin,

"Sannu da dawowa Baban Ameenah"

Kasa magana ya yi, domin kuwa hatta da Muryar ta in ba ya b'ata ji ba, sai ya ji kamar ta sauya.

Tafe take ta na kada mazaunan ta da suka fito yanzu, ta shige, dakin su ta ajiye kayan, ai ya na ganin ta b'acewa ganin shi ya ture Ahmad da ya qanqame shi ya bi bayan ta.

Ameenah tattara yaran ta yi tace su je dakin su, Ahmad ya so ya mata musu, ta masa tsawa dole ya bita suka tafi dakin su.

Ya na shiga ya ajiye kayan hannun sa, ya nufe ta, kamar yanda ya saba, ba wani wasanni, ba komai, haka zai yi ya tafi, ba ruwan shi da ta samu biyan buqata ko bata samu ba, shi dai zai yi ya tashi.

Dakatar da shi ta yi da hannun ta ta ce,

"Meye hakan? Ah ah malam dakata mana? Daga dawowa ba sannu, ba Allah shi sawaqa, baka san a halin da muke ciki ba, kawai zaka fara qoqarin debe wando! To ka na kuwa maida shi, dan banda ra'ayi"

"Hansatu, Hansatu ni ne fa, ni ne Isah ko baki gane ni ba?"

"In na gane ka kai ka gane ni ne? Haka ka tafi ka bar ni? Ka ga wai shin ma in tambaye ka, dama aure na na bisa kan ka ka tafi ka bar mu ba abincin da zai kai wannan kwanakin da ka dauka,ba kudi, ba kira ka ji lahiyar mu, ba kira ka ji mun ci ko bamu ci ba, wanne hali nake ciki da yara da dakon soyayyar ka, da auren ka me....."

Kuka ne ya kwace mata, mai maqaqi a wuyan ta, bata so yin kuka ba, a yanda ta tsara yi masa, amma ta kasa jurewa.

Barin dakin ta yi gaba daya, ta je ta haɗa masa ruwan wanka, ta dumama miyar da ta dafa musu shinkafa, ta zuba masa komai yanda ya dace, ta zuba soyayyan naman da Hajiya ta aika musu.

Inda ya saba cin abinci nan ta aje masa, ta shige cikin yaran ta, ta kwanta ta juya musu baya, su ma shiru suka yi kamar ruwa ya ci su.

Isah kuwa wanka ya je ya yi, dan yanzu zaman Saudiya ya sa ya fara tsafta, ya na komawa ya ga abinci ya dauka ya ci, har lumshe ido yake, ya yi kewar abincin ta mai dadi .

Bayan ya gama ne dabara ta zo masa, murmushi ya yi, ya kwalawa Ameenah kira, da ta je ya ce ta kira masa Umman su

Ya san ba zata qi ba, dan a halayyar ta ya jima da sanin ,ba ta son yaran su na gane rashin jituwar su.

Ai kuwa Ameenah ta isar da saqon gyatumi, ina nan tsaye ina jira na ji shin Hansatu zata je ta wa Isah Barka da dawowa mai kyau ko kuwa??????

*Mutanen kwarai me kuke gani? Zata biye masa nee ko kuwa?*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH


PAGE 47:


Hansatu na nan kwance ta na jin yanda ake dambe tsakanin soyayyar Isah da tsanar shi a cikin zuciya da ruhin ta.

Ameenah ce ta shiga ,cikin ladabi ta ce,

"Umma na fada maki fa Baba ya ce na kire ki tun dazu amma ba ki je ba, kar shi yi fada fa"

Ita kan ta ta yi mamakin rashin zuwan shi ya fara sababi, amma bari ta je ko dan kar ta sawa yaran ta tunanin rashin kunya a zuciyar su, hakan zai yi matuqar tasiri wajen d'arsa musu tunani kala kala akan qin zuwan nata.

Bismillah ta yi, ta sauka daga katifar su, ta gyara rigar ta, sannan ta tafi.

Ta na shiga ta gan shi,kwance, alamar jiran ta yake, har yanzu zuciya da ruhin ta ba su tsaida hukunci akan abu d'aya ba, shin za su ci gaba da son Isah da daraja shi kamar da, ko za su tsane shi ne da nuna masa tsantsar qiyayya?

Ta na nan tsaye ta ji Muryar shi,

"Wai ke me ke damun ki ne? Ko kin zama kurma ne kuma makauniya? Ba ki ga kiran da nake miki bane ki ke a tsaye?"

Wani baqin ciki ne ya tokare mata wuya, a yanda take jin ta, yanzu ta wuce wadda namiji zai nema a haka, ita mace ce da namiji zai bi, zai nunawa tsananin maitar shi da kwadayin shi,wadda za a nema da soyayya, da wasanni,ba wai a neme ta kamar ana neman akuya ba.

Wani tunani ne ya shigi zuciyar ta nan take, fita ta yi, ta zuba abinci da nama, ta kai wa Ameenah ta ce,

"Ameenatu zo ku kai wa Mama 'Yabbuga, ku zauna can kar ku je ko ina, zan zo da kai na na taho da ku,"

"To Ummaa"

Cikin zumudi da son yawo Bilkisu ta sanya hijabin ta, dan sun jima rabon da su fita waje, ko za su fita sai da Ummaan su.

Su na tafiya ta saka sakata, ta koma dakin da Isah ke kwance ya na ci gaba da jiran Hansatu, ya fara quluwa da sabon abinda take masa, ta na shiga ta tura qofa ta rufe window, duk qoqari na na dauko rahoto ya gagara.

Ba su suka bude qofar nan ba sai bayan awanni biyu cur, tashin kuka nake ji, ina kasa kunne sai na ji ashe ba mutum daya ke kukan ba, cike da Mamaki na leqa, Isah na gani durqushe gaban Hansatu ya na kuka har da majina, ya na roqon ta bai qoshi ba kar ta masa haka.

"Dan Allah Hansatu ki barni na qara ko sau guda ne,"

Hawayen ta ta share, ta d'auki sabon towel din ta, ta daura, ta kalle shi, sannan ta ce,

"Ka san kuwa da yaya na taushi zuciya ta ka yi har so biyu? To Bari na fada maka wani abu da ban so fada maka ba, a baya ina maka son da tunda nake ban taba jin ko ganin macen da ke son mijin ta ba kwatankwacin yanda ni ka son ka, ban ta ba ji ko ganin macen da ke wa mijin ta biyayya ba kamar yanda ni ka ma, ba dan ban san darajar kaina ba, sai dan tsananin son da nake maka, ka san mi? Abun haushi abun takaici, wannan son har yanzu ya na nan, amma wani sabon al'amari ya shiga son, tsanar ka ta gauraya da soyayyar ka a zuciya ta, na rasa wanda zan dauka, na amsa kiran ka ne kawai, saboda ni bautar Allah nake a zaman mu, ba bautar ka ba ISAH, (cikin sauri ya kalle ta, domin bata taɓa kiran sunan shi ba, tun bayan auren su) da bautar ka nike da na sa qafa ta na shure ka, na yi fatali da kai, na tofa maka yawu ga huskar ka, dan qasqantar da kai, da bautar ka nike ba bautar Allah ba, da yanzu ina gidan mu, ba zan zauna da namijin da ba shi ganin daraja ta ba, da qima ta, da mutunci na ba, da bautar ka nike da kafin ka dawo na bar gidan nan, kar ka yi zaton wai dan na samu iyaye na sun amshe ni ne yanzu,na gwammace ni da d'iya na mu kwana a titi da mu ci gaba da zama da kai,.... amma....amma ba zaman kaina nake ba, har yanzu kai miji na ne, kuma qarqashin ka nake, sannan bautar Allah na ke, bai cin haka nan,....da zan biye wa zuciya ta, da zan biye wa zuciya ta Isa,......"

Kasa qarasa kalaman ta tayi,saboda ba zasu fad'u ba, abubuwan da ta ke da qudirin yi mishi a zuciyar ta su na da yawa, tsoron fushin Allah akan ta ne kawai ya mata katanga da aikata su, komai bawa zai yi, kar ya tuna kan shi, ya tuna mahaliccin shi, kafin ya aikata komai, shin Allah ya yarda da abinda zai aikata ko bai yarda ba?

Wankan ta ta je tayi, ta sake yin na sabulun da ta yi wa hade haden kayan gyaran jiki, da turaruka masu qamshi.

Ta koma d'akin dan shirya wa, a nan durqushe inda ta fita ta bar Isah ya na nan, bai motsa ba, ran shi a matuqar bace ya ke, amma ko karen hauka ne ya cije shi, ba zai iya mata komai ba, ko da da harara ne, dan a yanzu bai san iya ina Hansatu ta tsaya ba, bai san me ne ne akan ta ba, kwarjinin da ta masa ba zai bar shi aikata mata komai ba, wannan shi ake kira aji, Hansatu ta kankaro ajin da Isah na matuqar shakkar ya kusance ta da rainin wayo, dandana masa kan ta da ta yi, ya sake birkita masa kai, ko da farkon auren su bai samu abinda ya samu ba a yanzu daga gare ta, wannan Hansatun kamar an sauya masa sabuwa ne.

Bata kula shi ba, haka ta gama shirya wa, yamma ta yi sosai, dan an kusan kiran sallah ma, ta sanya sabon takalmin ta da sabon mayafin ta da ya yi kala da riga da skirt din da ta sanya na qananan kaya ta fita zuwa gidan 'Yabbuga, Hansatu fa jama'a ta koma Hafsatu, gaba daya ta sauya ta kowane bangare.

Sallama ta yi, ta gaishe da 'Yabbuga da ke zaune a qule gaban yaran, sai zabga tsaki take.

Mamakin ganin bacin rai kwance a fuskar 'Yabbuga ne ya kama Hansatu, cikin mamakin ta ke tambayar ta me ya faru.

"Hummm
Showing 99001 words to 102000 words out of 150481 words