dade, baki bacci ba?"

Kallon qur'anin da ta gama karantawa ta yi, ta lumshe idon ta hawaye suka zuba, ta ce,

"Eh ban yi bacci ba, kai me ya hana ka bacci?"

Shiru ya yi, tare da gyara kwanciyar shi, ya lumshe idanun shi ,sanan ya ce,

"Na kasa bacci, ban san me ke damu na ba, Sultana ina da wani babban al'amari a tattare da ni, wanda ni ka jin matuqar tsoro akai"

"Me ne ne wannan al'amarin? Ko zan iya sanin shi?"

Da sauri ya kawar da maganar ta hanyar tashi zaune ya ce,

"Ran ki shi dade, ya kamata ki kwanta ki bacci, akwai gajiya a tattare da ke sosai "

"Humm Auwal kenan, kai a ganin ka zan iya rintsawa? Bayan zuciya ta da ƙwaƙwalwa ta su na hango min abinda ban gani ba? Zuciya ta na hango min kukan yara ƙanana, da mata,da mazaje, zuciya ta na hasko min yanda jini ke malala na dan Adam ba dabba ba,ba tare da haqqin su ba, anya mahaifi na mutum ne kuwa? Anya wadan da suke aikata kashe kashe da zubar da jinin al'umma mutane ne kuwa?anya akwai zuciya a qirazan su kuwa?anya suna tunawa da cewa kamar yanda suke daukan rayukan bayin Allah suma watarana ran su za a dauka? Anya su na sane da cewa akwai wuta akwai aljannah? Anya su na tunawa da cewa su na da mahalicci wato Allah, mai yawan rahama, da kuma yawan azaba? Anyaa????"

*Makaranta Sultana na neman amsa*

A GARIN MU







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH







PAGE 24:






Wata iriyar zufa ce ke karyo mishi, wadda ta sanya shi tunanin anya ya kunna AC ma kuwa, kallon saitin AC din ya yi, ya ga a kunne take, tashi ya yi ya kunna fan, sannan ya koma ya zauna, ya na sauraron yanda Sultana ke karanta masa abubuwan da ko Mubaraka mai yi masa nasiha da wa'azi kullum, bata taɓa fada masa wadannan kalaman masu matuqar taba zuciya ba.

Cikin tsagaita wa da kuka sultana ta ce,

"Allah shi ne mafi sani game da mutanen nan da Daddy ke aiki da su,su ke lahanta mutane, suke kassara su, suke illata su,in masu shiryuwa ne, Allah ya shirye su, in ba masu shiryuwa bane Allah ya musu abinda suke wa bayin shi, "

Shiru Lawwali ya yi, dan bai isa amsa wa da ameen ba, tunda ya san mene ne suke wa yaran wasu, jijiyoyin kan shi ne suka tashi rudu rudu, qit ya kashe wayar,gaba daya ya kashe ta.

Yawo ya fara yi a dakin, me zai sa Sultana ta musu wannan addu'ar , in wani abu ya samu ahalin shi fa? (Na wani bnza na ka dukiya kenan).

Ranar Lawwali bai samu bacci ba sai gaf da suba, bacci kuwa ya sha me kyau, bai tashi ba sai qarfe goma na safiyar ranar.

Sultana kuwa dama ta yi waya NGO akan ba zata je ba, bata jin dad'i, su kula da wajen, da duk wanda ya je neman taimako, abinda ya fi qarfin su su sanar da ita.

Lawwali ma sai da ya tashi ya ga message din ta, ji yayi hankalin shi ya tashi, me ke damun ta? Dole ne ya je ya duba ta.

Wanka ya dauka, ya sanya wasu riga da wando,na shadda sun yi mishi kyau sosai, ba hula, wayar shi da yan kudi, sai makullin mota ya dauka, ya fita, kafin ya je wajen ta, sai da ya shiga gari, ya siyo mata kayan kwalama na Bature, duk ya ma rikice ya rasa me ya kamata ya siya, haka dai ya siyi banza ya siyi wofi ya ja mota sai gidan Gwamna.

Ko da ya isa ya tarar da securities da yawa, sanin ko shi waye a wajen gwamna ne ya bashi damar shiga ba tare da wani bincike ba, gwamna Halliru da Hajiya Ikee ba su gida, Sultan ne da Sultana sai masu aiki, ranar Mai buruji da Lamishi duk sun samu zuwa, har a sannan qafar Lamishi bata qarasa warkewa ba, dan haka Sultan ya hana ta yin komai, sai godiya take, ya ce ta ci gaba da turo Mubaraka, ba se ta zo ba, tunda ba lafiya.

Sultana na zaune kusa da Sultan, ya yi tambayar duniya ta qi sanar da shi abinda ke ran ta, saboda ba ta son ya tsani Daddyn su kamar yanda ta tsani ganin shi,ba ta so ta b'ata kowa a rayuwar ta, ta fi so ta fadi alkhairin mutum, in ba ya zama dole se ta fad'i sharrin mutum ba, wannan ba yanda zata yi,balle mahaifin su, bata fatan Sultan ya sani, zuciyar shi zata karye sosai, saboda yanda yake son mahaifin nasu sosai.

Hawaye ta share sannan ta yi murmushin yaqe ta ce,

"Yah Sultan ba abinda ke damu na, ciwon kai ne kawai, in ina da matsala ka sani kai ne mutum na farko a duniya da ke fara ji"

"Haka ne, amma Ni ma kin san na fi kowa sanin ki, ba ciwon kai bane kadai damuwar ki, akwai wani abu da ya ke faruwa, wanda ki ke boye min"

Bude baki ta yi dan yin magana wayar ta ta dau qara, ko da ta ga sunan Auwal, sai ta samu kan ta da jin dad'in hakan,domin a daran jiyan ta yi ta sake gwada kiran shi bai shiga ba, har da safen nan ma ta kira bai shiga ba.

"Assalamu alaikum,"

"Wa'alaikumussalam, Ran ki shi dade ya ki ke? Ya jiki? Ina hwata dai kin samu lahiya ko? Na taho na duba jikin ki, tunda kin ce baki da lahiya"

Miqewa ta yi da sauri ,ta isa gaban window'n da ake hango farfajiyar gidan, ganin shi tayi tsaye da ledar shopping a hannun shi, murmushi ne mai kyau ya kwace mata, ta jingina da ginin wajen, sannan ta ce,

"Lallai ka iya zuwa dubiya, haka ake zuwa dubiya an sha gayu? What if mara lafiyar ta rikice fa?"

Waige waige ya fara ya ga ta ina zai hange ta, bai gani ba,  cikin sa'a ta sake leqa shi suka hada ido, dariyar shi da ke rikita mata kwanya ya saki, sannan ya shafa kan shi, tare da lumshe ido ya sauke su fess akan ta,

Sultan ne ya isa gaban ta, ya harde hannayen shi a qirjin shi, ya na kallon ta da mamaki, dazu fa kuka take.

Su na hada ido, ta bar wajen za ta hau sama, ya riqe hannun ta, a hankali ta ce,

" ka shiga parlour na baqi gani nan zuwa"

Kashewa Lawwali ya yi, ya shiga gidan ya shige har inda aka ce masa, ya zauna zaman jiran ta.

Ita kuwa qoqarin gudu take Sultan ya riqe ta,

"Ina zaki je baki min bayanin sauyawar ki ba a lokaci qanqani? Na fi qarfin awa biyu ina tare da ke, kina ta hawaye, kin kasa fadan komai, yanzu daga amsa waya sai ki fara dariya?"

Shiru Sultana ta yi, dan ko me zai faru ba zata sanar da shi mummunan sirrin mahaifin su ba, gwanda ta tonawa kan ta asiri, akan ta fada masa gaskiya.

"Yah Sultan, i am in love, ....i am in love with my driver, amma ban sanar da shi ba, shi ma kuma da alama ya na so na, bai sanar da ni bane kawai, Yah Sultan ina cikin damuwa ne saboda na san ba wanda zai goyan baya a gidan nan,labarin soyayya ta ina hango qarewar shi tun kafin ya fara"

Bilhaqqi yanzu kuma kukan hasashen da ta yi take yi,

"Sultana tabbas zabin ki ba mai karɓuwa bane a wajen su Hajiya da Daddy, amma a waje na karbabbe ne, in dai ki na son shi, ya na son ki, zan tsaya a gefen ki, har sai kun cimma burin ku"

Qanqame hannun shi ta yi cikin nata, tare da fadin,

"Na gode,"

Shafa kan ta ya yi, sanan ya ce,

"Wannan shi ne abinda zan miki, duba da yanda iyayen mu suka maida ni mara mamora a cikin al'umma, ba na aikin komai, ana kulle na kamar mace, ba na baki wata gudunmawa a matsayi na na yayan ki"

"Yah Sultan kar ka ce haka, soyayyar ka a matsayin dan uwana ta wadatar da ni komai,"

Cikin ran ta kuwa cewa ta yi,

'Dole iyayen mu su yi kullen mu, domin sun san me suke aikatawa, su na tsoron kar wani abu ya same mu,'

Sai da ta ɗan gyara fuskar ta ta sanya sutura mai kyau da ta rufe jikin ta sosai, sannan ta isa wajen Lawwali, sassanyan qamshin ta ne ya fara yi masa maraba, kafin kyakkyawar fuskar ta  ta masa sallama.

Sake baki ya yi ya na kallon ta, anya da gaske bata da lafiya? Shi be ga alama ba,

"Kallon nan na ka na neman ya yi min yawa wallah"

"Anya kuwa? Ke taba jin inda wata ya ce wa mutane kallon da suke mishi ya yi yawa?"

"To ai Ni ba wata bace"

"Kin fi kama da wata mai haske shi ya sa na yi misali da wata, sanyin ki kuwa ya fi kama da ruwan qorama, shi ne ba shi cutar da kowa sai amfanarwa"

Kunya ce ta kama ta, tabbas ta gama yarda da cewar, abinda ke zuciyar ta shi ne a zuciyar shi,

"To dubiya kacce ka taho, amma ba ka yi min ya jiki ba"

"Ban ga alamar ciwo a tattare da ke ba, sai ma alamun cikakkiyar lahiya, amma, ya jikin ki? Ina hwatan da sauqi ko?"

"Na ji dama, ciwon da ke jiki na ba a zahiri yake ba, a badini ne, domin kuwa zuciya ta na quna matuqa akan abinda zai iya koma ya  faru da mutanen can, da kuma abinda ka hwaruwa a garin nan, da ma Nigeria baki daya"

"Hummmm"

Shi ne kawai abinda Lawwali ya iya cewa, nan da nan ya tuna addu'ar da ta musu, cikin sauri kar a zurfafa magana ta sake yanko wata addu'ar ta cimmusu baki daya ya ce,

"Ran ki shi dade, ina fatan ban yi karambani ba, na je zan siyo ma mara lahiya kayan dibiya, na rasa mi zan kawowa, na kwaso wadannan"

"Na gode sosai, amma da baka wahal da kan ka ba"

"Babu komi, indai ke ji dad'in kyauta ta, farin ciki na zai qaru"

"Lallai ka yi farin ciki domin kuwa na ji dadin kyautar ka"

Yar dariya suka yi a tare, Lawwali ya shagala da kallon ta suka ji an rangada salati, da sauri sultana ta miqe ta na zare ido, cikin in ina ta hau yi wa Hajiya Ikee Barka da zuwa, wani mugun kallo take bin Lawwali da shi, daga sama har qasa, babban abinda zai ba mai karatu mamaki shi ne, Lawwali dai ba a talauce ya je ba, kayan jikin shi kawai sun tasamma dubu dari,ga tsarabar daya kawo ma Sultana ya kashe 50k, wayar hannun shi abar kallo ce,  ga motar shi can a waje, ko wani dan attajirin sai haka, amma Hajiya Ikee ke masa maqasqancin kallo,

"Ran ki shi dade Barka da War haka,"

Cikin tsawa ta ce

"Dakata min diyan tallaka! Me ya kawo ka har parlourn manyan baqi? Ke Sultana wacce wanga diyan tallakan ya shigo min har nan?"

Cikin kame kame da tura baki Sultana ta ce,

"Hajiya ke san hwa mai tsaron lahiya ta shike, Daddy ne yacce duk inda ni aje qawahu na shi sa na shi, tau yau na ce masa ban zuwa ko ina ban da lahiya, shi ne yazo diba ni, in baki yarda ba ki tambayi daddy shi ne yacce duk inda niyyi shi ma shi yi"

"Akan wanne dalili za a hada ki da wanga gola golan qato? Tau ban yarda ba, ke da gani nai ke san shi na shan wani abu, kuma...."

Cikin jin kunyar kalaman Hajiya Ikee Sultana ta katse ta, dan cin fuska ba shi da dad'i ,tsabar kunyar Lawwali Sultana ta kasa kallon shi.

Lawwali kuwa kawai ayyana irin azabar da zai ganawa Hajiya Ikee yake a duk ranar da tsautsayi ya had'a su, a fuskar shi kuwa murmushi ne bayyane, wanda ba me gane ma'anar shi in ba yaran shi ba, da ace a daji ne yake wannan murmushin to fa tabbas sai ya kai harbi, kad'a kai ya yi, ya ajiye ma Sultana tsarabar ta a gaban ta da kyau da kyau,ya kalle ta ya ga yanda take jin kunyar hada ido da shi, qoqari ya yi suka kalli juna, kashe mata ido daya ya yi, ta kuwa sanya murmushi, tare da rufe fuska, Hajiya Ikee salati ta saki, ta na tafa hannaye, Lawwali kuwa wucewa ya yi tare da fadin,

"Na bar ku Lahiya, Ran ki shi dade "

Ya na fita Hajiya Ikee ta ja Sultana, ta na masifa, tare da fadin, dole a sauya mata driver, bari Daddyn ta ya dawo, kuka kawai Sultana take, ta na bada hakuri, amma haka Hajiya Ikee ta murje idon ta, ta ce sai an sauya mata Lawwali.

************************

Da asuba Mai unguwa ya fita Masallaci, an yi sallah, aka hadu da mutanen unguwa aka sauke qur'ani, aka roqi Allah, akan Allah ya kawo qarshen wannan tashin hankulan da ake ta yi, sannan aka roqi Allah akan ya bayyana Isyaka, Mai Unguwa fadi yake, ya na kumawa,

"Ya Allah ko gawar shi ne Allah ka gwadi mana, mu san ya mutu ne, ya Allah ka bayyana muna da shi lahiya"

Bayan kammala addu'a kowa na tafiya gida ne, wasu da basu samu zuwa har gida jajanta masa ba, suka jajanta masa a nan.

Sai da gari ya dan fara wayewa ya yi sallama da mutane ya dau hanyar gida, a hanya ya gamu da wani daga cikin yaran shi ya na ta gudu, ya na haki, tare da murna, ya na hango baban nasu yaci burki a gaban shi, ya ce,

"Baba ! Baba !! an ga Isyaka, ga shi can gida, kwance jikin Baabaa"

"Alhamdu lilLAAH, Hamdan katheeran, Allah na gode maka,"

'Dan dandamalin wani gida ya hau a gefen hanyar, ya yi sujjadar godiya ga Allah, sannan suka kama hanya, suka nufi gida.

Ko da suka je, ga Isyaka nan, ya yi fururu, kayan shi duqun duqun, jikin shi alamar ya ci duka ya gaji.

Ya na ganin Mahaifin nasu kawai sai ya fashe da kuka, a da kuwa ko kukan ma ya kasa.

Mai Unguwa ma kukan ya fara yi, ya na sake godewa Allah tare da fadin,

"Ba abinda ya fi qarfin Allah, duk abinda Allah ya yi daidai ne, Allah mun gode maka, Allah ka qarawa Annabi daraja da wasila da fadhila, Allah mun gode maka, d'an baba, ya aka yi?"

Ya na cikin kukan ya saki murmushi, hawaye na zuba.

Kishiyar Baabaar Isyaka ce ta zo, ta ce,

"Tau ga ruwan wanka can na sauke taso ki je ki  wanke shi ya  ji dad'in jiki shi"

Godiya Baabaar Isyaka ta mata, ta kinkime shi ko nauyin shi bata ji,su ka nufi bayi, riga ta fara cire masa, ta fara qoqarin cire masa wando, ihu ya sanya, ya na fizge fizge, kamar mai jinnu, tare da fadin

"Ba na sooo, kar ka taba ni, ba na sooo wayyooo Allah na da zahi, zahi nika ji wallah, wayyoooo a taimaka min...."

Kuka sosai Baabaar shi ke yi, ta fita da gudu, zata kira taimako, ta tadda Mai unguwa da kishiyar ta da wasu daga yaran gidan a bakin qofar bayin, da kyar a ka samu ta nutsu, ta yi bayani, dakko shi akai waje, aka cire wandon, juya bayan shi Mai unguwa ya yi, wani wari ya ji ya na fita daga bayan yaron nashi, su na daga shi aka duba sosai, an fafake ma yaro baya, jini da wani ruwa mai danqo danqo ke zuba, ga wari, ihu da kururwar mata da yaran gidan ne ya cika ko ina na gidan, Mai unguwa kuwa suman tsaye ya yi, hawaye na bin kuncin shi, zuciyar shi ta yi mugun qunci, ta yi baqiqqirin,

"Wa ya yi maka wannan mummunan al'amari Isyaka? Wa ye ya bata maka rayuwa Isyaka? Wa ye ya zalunce mu? Ya aikata abinda Allah da Manzon shi ya yi hani da shi, ya tsine wa masu yi, da wanda aka musu, Allah ya na fushi da masu wannan mummunar dabi'ar da ko dabbobi ba sa aikata wannan alfashar,wa ye ya ci amanar mu? Waye shi ? Waye ya ci amanar mu?"

Babban dan Mai unguwa ne ya kama Isyaka daga hannun mahaifin nasu, ya aje saman tabarma, sannan ya ja hannun baban nasu suka koma gefe, ya zaunar da shi saman kujerar shi ta tsakar gida, ya na jin ya zauna, ya dafe goshin shi, ya fashe da wani irin kuka, mai ciwo.

Gaba daya gidan ya rikice, da sassafiyar har maqota sun ji koke koken sun shigo, kafin ka ce kwabo, labari ya baza unguwa.

Wasu da ke a social media kuwa har sun fara yadawa, tare da ɗaukan hoton Isyaka ba da izinin iyayen shi ba, ba da sanin shi ba.

Gani suka yi kukan ba zai kai su ba, uwar gidan Mai unguwa ce ta dauke shi, ta na kuka ya na kuka, ta wanke shi tass, ya suma ya kai sau uku kan a gama, saboda ciwon da ke jikin shi.

Ranar ahalin Mai unguwa ba mai maganar karyawar safe ma balle na rana, kowa hankalin shi a tashe yake, bayan sun gama shirya yaron, Liman ya yi sallama da Mai Unguwa.

Ko da ya je, suka gaisa ya jajanta abinda matan shi suka je suka bashi labari,  sai ya bada shawara akai yaro asibiti, sannan a kai ma yan sanda rahoto.

Haka kuwa akayi ,a police station an yi ma Isyaka tambayar duniya bai san su waye suka dauke shi ba, bai ma san sanda aka dauke shi ba,sannan  aka maida shi, (sharrin asiri,wasu masu aikata hakan su na sihiri,domin in b asihiri ba ba yanda za a yi wasu abubuwan su faru, se kuma son zuciya da rashin tsoron Allah, Allah ya ma na tsari da mugun ji mugun gani, mugun aiki)

Ba yanda suka iya, daga qarshe dai aka ce za a yi bincike, wanda zai wahala ayi din,cases irin wannan sun fi dari a wajen yan sandan,ba kan shi farau ba,an dad'e ana yi ba a bi ma mutane haqqin su, domin wasu masu bin haqqin ma suke kwace haqqin, asibitin aka wuce da shi, nan ma sai da aka sha fama kafin a samu bashi gado.

**********************

Lawwali na fita daga gidan su Sultana unguwar iyayen shi ya nufa, domin yanda ran shi ke tafasa da kalaman Hajiya Ikee, in bai dora sanyin
Showing 42001 words to 45000 words out of 150481 words