Yah Auwal , shin ka diba yanda kayan  ga sun ka yi ma kyawu? A gaskiya ba da ban ba dan ba sai na ce Aunty Sultana..."

"Shiiii,"

Shi ne abinda Lawwali ya ce, sannan ya wayance,ba ya son No 1 ya San shirin shi, ya jima da sanin No 1 na neman matsayi na musamman wajen Gwamna, so ba zai bari ya ji qudirin shi akan Sultana ba.

Daki suka shiga ya zaunar da ita bakin gado ya ce,

"Barakana ki fada min me ne ne a ran ki, gaba daya bakya farin ciki, murmushi kawai ki ke, amma ba har zuciyar ki ba"

"Yah Auwal ni dai gaskiya ina jin tsoro, in Aunty Sultana bata ji wani abu ba game da yanda ka ke ji fa?"

Da wani ne ya fadi haka ba Mubaraka ba, da ya d'and'ani azabar Lawwali, d'an had'iye bacin ran shi ya yi, ya ce,

"Baraka na ki min addu'a ke baiwar Allah ce, ba ki da laifuka a wajen Allah kamar Ni, ki roqe shi y sanya mata so na, kamar yanda nake son ta,....Baraka kin san matsalar da za a samu ma kuwa?"

Girgiza kai ta yi, zama ya yi a gefen ta, ya ce,

"A binciken da na yi kwanakin baya na gano cewa ba fa wani fita ma take sosai ba,sai ta bushi iska ne ta ce zata siyayya, to yau she zamu zanka haduwa?"

"Inshaa Allahu kar ka damu, ka riqe Allah, ka maida hankali Yah Auwal ka yi tuba na tsakani da Allah, Allah zai taimake ka"

"Amma baraka.."

"Yah Auwal kamar yanda ka yarda in ka  loda harsashi a bindigar ka, ka harba ba abinda zai hana harsashin huda abinda ka harba, to amsa addu'ar Allah a wajen bawan shi da ya yi imani da shi, ya amince Allah ne me yi tafi harsashin bindigar ka"

"To baraka zan dage da roqon Allah"

"Yah Auwal ni na san rabon ka da sallah yanzu an jima, domin sallah na sanya fuskar mumini haske da kyalli, babu wannan a tare da kai, to ta ya ka ke ganin za ta gan ka ta ji ta kamu da son ka? A yanda na ji labari kai din masanin qur'ani ne kafin Lamishi ta kashe maka guiwa ka fara harkar nan, me zai sa ba za ka koma ma abinda ka bari ba?"

Shiru Lawwali ya yi, tunanin baya ya yi, a da kaf makarantar allon Malam Hadi ba ya shi, gashi yanzu ko a hanya in ya je unguwar ba ya gaishe da malam Hadi.

"Baraka dare na yi, muje Mu aje ki gida ko?"

Tashi ta yi, suka fita parlour, tunawa ya yi ko dan ruwa bai ba ta ba, leda ya samu ya cika mata da juices kala kala, da kayan marmari, da dangin biscuits, ya bawa No 1 ya riqe, suka fita .

Har gida suka aje ta za su koma, ta ce,

"Yah Auwal ba za ka sanar da su Baba ci gaban da aka samu ba?"

"Bassu kawai, kuddi kawai suke so ko? To ana kawo masu, ba su damu da me na ke ba, ke kad'ai ce ki ka damu da rayuwa ta, shi ya sa na bawa rayuwar ki mahimmanci kema"

Ya na gama fadi ya daga wa No 1 hannu, ya bashi umarni suka ja suka tafi.

Ta na shiga kuwa ta tadda masifar Lamishi na jiran ta,

"Sannu tinkiya, uwar tinbele, ke san gidan ku amma sai an nemo ki, ina ki ka tafi tun azzufur ba ki gidan ga sai yanzu zaki dawo?"

"Umma Yah Auwal ne fa ya dauken mun ka tai gidan da an ka sai mai, ya nuna min"

"Ga ki uwar shi ko? Shi yasa  nake qara tsanar yarinyar nan fa, d'an nawa guda tilo kin zame mai kamar  uwar shi, ni be kai Ni ba, se ke, bani nan"

Amshe ledar hannun Mubaraka ta yi, ta bubbude, ta ga lemuka da kayan marmari.

"Uhumm uwar kwad'ayi, wanga lemon wahala da ya had'o ki da shi fa? Ina lehin yar kaza ko balangu, ah ah, an hada mu da kayan ruwa mu sha mu yi ta hitsarin wahala ko?"

Dariya Jameelu ya kece da ita, dan shi a duniya fadan Lamishi na bashi dariya,

"Jameelu ka kiyaye ni, ina fada kana dariya zan yanka maka mari se kayi hitsarin wahala"

Haba me Jameelu zai yi ba dariya ba, a guje ya bar gidan, dan ta na iya yan ka masa marin wahalar da ta furta .

Juyawa ta yi kan Mubaraka ta ɗora daga inda ta tsaya ta ga wayam.

Ci gaba tai da masifa, ta na bude robar lemukan ta na kurba, ta na ware masu tsami a gefe, masu zaqin a gefe.

***********************

Mota ce madaidaiciya a qofar gidan Isa, driver na zaune ya na jira, Hansatu kuwa na ciki ta rikice, ta rasa ma kayan da za ta sanyawa yaran ta, kowanne ta dakko ya na da matsala ,ba ta san kayan yaran ta sun lalace ba haka sai yau, ita kan ta atampar da ke jikin ta ta ji jiki, wata baiwar Allah ce a nan layin nasu take bata tsofaffin kayan ta da na yaran ta, ita ta bata atampar ta kusan shekara biyu ta na dirzar ta.

Cire tunanin komai ta yi aran ta, ta saka masu jemammun kayan suka fita, kallon Isa ta yi, cike da mamaki, tun da Isan na da kaya masu kyau,amma ya saka wasu tsofaffin kayan shi sun kode kwarai, musamman ta saman bayan shi ,

"Kun shirya? Mu je mun bar bawan Allah na ta jira"

Kalaman shi ma na yau abun mamaki ne,

A gaban mota Isa ya zauna, Hansatu da yara suka shiga baya.

Driver tuqa mota ya yi, suka fara tafiya .

Yabbuga na zaune a qasan bishiyar su ita da matar Yahai, sun ga wucewar su Hansatu.

"Ke ji Isa wani kaya da ya saka"

Dariya suka kece da ita, Matar Yahai ta ce,

"Ina za su haka?"

"Jiya da dare na ji Isa na fadin sai sun je, ko ta na so ko bata so, ita ko ta na ta magiya akan kar su tai, tau qarshe sai da ya buga ke san jakki ba shi jin dumi sai bugu"(kin san jaki baya jin magana se an dake shi)

Dariya suka sake sanyawa, Dan jumma ne ya fita daga gida za shi masallaci, ran nan baqiqqirin, ya na gida ta fita zaman gulma, ko abinci da kan shi ya diba a tukunya, tsabar gulma na cin ta, ta gama girkin bata kwashe ba ta bari a tukunya, dik ya danqare.

"In kin gama dumin sai a tai zuwa sallah ko?"

Gaba ya yi bai jira ta cewar ta ba.

**********************

A gaban kantamemen gate din na gidan su Hansatu motar ta tsaya,wani irin kuka ne mai tuquqi ya tasowa Hansatu ,rabon ta da gidan tun wani zuwa da su Amina suka yi, ta je dakko su, lokacin Ahmad na qarami sosai,ba kalar wulaqancin da masu gadi ba su mata ba, saboda sabbi ne ba su san ta ba, kuma yayan ta da ya fita a wulaqance ya kora yaran, ko ciki ba a bari ta shiga ba.

"Ah ah hito mana"

Fita ta yi, ta na share hawaye, an sauya fentin gidan, gidan ya sauya kamar ba shi ba, kalle kalle ta fara, qofar shiga gidan ta kalla, hawaye ne suka zuba mata tunawa da mahaifin ta da ta yi.

A kunne ya rada mata,

"Ki na barin wannan  iskancin ko sai na ci maki mutunci"

Da sauri ta hau goge idanun ta, yayan ta da ya fito kuwa a zaton shi wata kalma mai dadi aka fada mata, ta daina kuka.

Ciki suka shiga............

A GARIN MU




WRITTEN BY HAERMEEBRAEH




PAGE 15






Masha Allah, shi ne kawai abinda Musulmin kwarai zai ce in ya ga abinda ya masa kyau, ko ba mutum bane, ko da waje ne, ko tufafi, ko abun hawa, indai ya maka kyau ,to ka ce masha Allah, shi ne abinda Hansatu ta fadi a qasan ran ta, an gyara gidan su sosai ,ya yi kyau kamar ba shi ba.

Mahaifiyar ta na zaune a daya daga cikin kujeru na alfarma, ganin su Hansatu ne ya sanya ta miqewa tsaye, ta na murmishi, hannu ta bude mata, Hansatu kuwa ta na isa sai ta durqusa a qasa ta hau kuka, kuka ne da duk mai raunin zuciya ya kalla sai ya koka, mahaifiyar ta ma kan ta hawaye ta ke,

"Hajiya ku yafe min, na aikata babban kuskure akan so, na qi bin umarnin ku, Hajiya dan Allah ki yafe min, daga yanzu ba zan sake tsallake maganar ku ba"

"Hafsat ta shi kin ga yaran ki na kuka, tashi na yafe maku , da ke da mijin ki, qaddarar samun wadannan kyawawan yaran ne ta raba ki da mu, mun godewa Allah da ya sanya ta hanyar aure kuka same su, ba ta hanyar banza ba, mu ma muna da laifi, da mun hakura mun bi me kuke so da haka bata faru ba, da ace ke din baki samu kyakkyawar tarbiyya ba, da lalacewa zaki, tunda ki ka tafi ban qara yin lafiya ba, hawan jini ya kama Ni, saboda yawan tunani, amma alhamdu lilLAAH daga ranar da na je na gan ki, zuwa yanzu n fara samun lafiya a jiki na, dan haka daga yanzu ke da iyalin ki, ba mu yi muku shamaki da ko ina ba na gidan nan"

Isa ne ya zube guiwa bibbiyu ya na godiya, tare da matso kwallar dole,

"Hajiya mun gode da yafe mana da kuka yi, Allah ya qara girma da daukaka, Allah ya qara arziki, mun gode"

Murmushi Hajiya ta yi, Yayah'n Hansatu ne ya daga Isa daga durquson da ya yi, shi kuma ya na ta wani sunne kai, kamar na Allah, yaran shi na ta bin shi da kallon mamaki.

"Mun zama daya yanzu, ka daina godiyar nan haka"

Kwalawa matar shi kira ya yi, mai suna Aziza, ta kuwa taho cikin izza da mulki, kamar wata sarauniyar gaske, sai buda hanci take, ta na rufewa, ita a dole ga matar mai kuddi.

"Haba Baby wanga wane irin kira na? Me ne ne?"

"Qauna ta Hafsat da na ke fada maki? Ita ce ta zo,"

Wani kallo ta bi Hansatu da shi daga sama har qasa, tabbas ga kamanni nan, amma wannan wacce irin shiga ce a jikin ta? "

"Wagga d'in ita ce qaunar ka?"

"Eh ita ce, tai ki sa a kawo masu abincii da an ka tanada domin su"

"Ni fa na mance ban ce a yi wani abinci na musamman ba, amma dai an yi na dare, a wajen su kuwa na san zai zama kamar na ranar sallah, ina zuwa"

Daga Hajiya har Yayahn ba wanda ya tanka, kunya ce ma ta kama su, suka hau yi ma su Amina wasa, murmushin yaqe Hansatu kawai take yi, lallai matar yayan ta batta da mutunci da dukkan alamu.

Kafin wani lokaci qanqani an cika dinning table da abinci kala kala, qamshin shi ya sanya yunwar cikin su motsawa, ta yanda har ana iya jiyo kukan yunwar ta na neman agaji, cikin wasa Hajiya ta ce,

"Wayyyooo wayyoo ni yunwa taa, yi hakuri bari kuka haka nan, yanzun ga zan baki abinci ki tafi"

Dariya su Ahmad sukai ta yi, ta na riqe da hannun Bilkisu da Ahmad Amina na biye da ita suka zauna a kan kujerun table din, plates ta sawa kowa a gaban shi, ta na tambayar su me za su ci, da sauri Hansatu ta isa ta karba ta na zuba masu hawaye na zubar mata, mahaifin ta ta tuna, a baya in ta na zuba masa abinci, ya na mata wasa, tare da sanya mata albarka.

Dafa kan ta Hajiya ta yi ta ce,

"Allah ya miki albarka, ki kasance cikin farin ciki har qarshen rayuwar ki"

"Ameeen Hajiya ta"

Isa ya gama qulewa, sun tafi sun bar shi, yunwa sai narkar masa da tumbi take, ko ta ma waiga ta kalle shi, balle ya mata alama, kwafa ya yi a hankali, sannan ya furta,

"Za mu je gida ne"

Yayah ne ya kama hannun shi, ya ce,

"Suruki na mu je mu ci abinci,"

A zaqe Isa ya miqe, ya na zama kuwa, kazar da ke gaban Hansatu ce ta tsone masa ido, to ta riga ta san halin gogan nata, dauka ta yi ta mayar plate din gaban shi, da murmushin yaqe,

"Ah ah, Hafsat ci naki mana, ga wani nan zuba masa,"

Isa maida hannun shi baya ya yi, da har zai kaiwa kazar damqa, hansatu da ta san halin mijin ta, cika masa plate ta yi d kyau, kusan duk abinda ke kan table din sai da ta sa masa,ba kunya ba tsoro, ba godiya haka ya fara ci, su Amina sun jima da fara cin abincin su.

Shiru ka ke ji, banda qarar cokula da taunar Isa ba ka jin komai, hakan kuwa ba qaramin bata ran Aziza ya yi ba, cin abinci kamar wani akuya, dan tsaki ta ja, sannan ta ce,

"Haka ka ke cin abinci?"

Kafe Isa ta yi da ido, ta na yatsina fuska, cike da nuna kyankyamin shi, dan murmushin yaqe ya sakar mata, ya ci gaba da cin abincin shi, da qarfi ta daki table din, sai da yaran suka razana, ta ja kujera baya, ta bar wajen.

Ta na tafe ta na masifa da harshen turanci.

"Ku yi hakuri da halin Azizah, in baki manta ba, akwai wanda muka zaba Maki ki aura a baya, qanwar shi ce, yanzu haka su na da hannun jari mafi yawa a kamfanin mu, yayan nata ke riqe da kamfanin, mutumin kirki ne matuqa, amma Aziza dake renon qasar waje ce, tarbiyyar ta da tamu ta bambamta, a haka ta fara barin wasu munanan halayen mutanen can, ku ci abincin ku, ku rabu da ita, a qasan ran ta, mutuniyar kirki ce, ba ko da yaushe take haka ba"

"Ba bu komai Hajiya,Allah ya sa ta gyara halayen ta gaba daya, domin ku ci gaba da jin dadin zama da ita"

"Ameeen" shi ne abinda yayan ta ya riga kowa fadi, ya na mutuwar son Aziza, amma halayen ta na baqanta ran shi.

Bayan kammala cin abincin su ne, Bilkisu ta ga Hajiya ta goge bakin ta da tissue ta ɗora a kan ragowar abincin ta, ga qashin da ta ci ta tauna duk ta zuba a sauran abincin, tashi ta yi tsam ta dauke, sannan ta kalli Hansatu ta ce,

"Umma ai dai ba kyau wulakanta abinci ko? Hajiya ki dena bata abincin da kika rage, kar watarana ki rasa abinda za ki ci, Umma bari na samo leda mu qulle sauran mun dumama gobe"

Kunya ce ta kama Hansatu matuqa, Hajiya kuwa da Yayah yi sukai kamar ba su ji me Bilkisu ta ce ba, kwashe wanda suka zuba a saman plate din suka yi kawai, suka tara a wani empty mazubi dake wajen,

"In Allah ya yarda daga yau ba zaku sake zama da yunwa ba kunji?"

Daga kai yaran sukai suna kallon Uncle din nasu cikin farin ciki.

Basu suka fara shirin komawa gidan su ba, sai bayan isha'i,Hajiya ta haɗa masu ashirin ta arziki,dan kuwa sai da bayan mota ya qi rufuwa.

Kayan sawa ne, na Hansatu da yaran, da na Isa kan shi, Isa kuwa bayan sabbi shi da Hansatu har da kwance na Yayah da Aziza da Hajiya suka samu, yaran ne kawai aka sai masu sabbi tun kan su je.

Har qofar gida motar ta tsaya, Yabbuga na jin qarar mota ta diba da gudu ta labe a zaure, ta na leqen su, Dan Jumma kuwa mamaki ya gama kashe shi,gulmar ta ta har ta kai, su na tsaka da hirar su ta zabura ta yi waje haka?

Sai da ta gama ganin kayan da Isa ya shigar shi da Hansatu sannan ta koma ta labe a katanga, daidai inda ta kan ji maganar su, ta na tsaye ta ji maganar Isa,

"Bubbude mu ga meye a ciki, dan iskanci shi ne dazu ku ka tafi cin abinci kuka bar ni zaune ga dan iska, na je gidan su Mata ta cin azziqi ko?"

"Ka yi hakuri ba haka bane"

"Dalla Malama bude naga me aka saka a ciki,"

Ganin abun azziqin ne ya yi yawa, nan da nan ya fara washe baki, ya na zuba, har zama ya samu waje ya yi, ya na ma Hansatu hira, mamaki ya gama kashe ta.

Ranar Isa sai da ya gwada mata soyayyar da suka dade ba su yi irin ta ba.

Ta ji dadin hakan matuqa, addu'a ta dinga yi Allah ya tabbatar da su cikin azziqi mai albarka.

Yabbuga kuwa ta nade komai jira take washe gari ta yi ta guntsawa qawayen ta na gulma, duk yanda ta so ta yi maganar abu da Dan jumma ya qi bata hadin kai, tai ta Masifa ita daya, har bacci ya dauke ta.........

Sai mu jira uwar gulma ta tashi daga kwana😅

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻




WRITTEN BY HAERMEEBRAERH




PAGE 16:

Da misalin 8:12am, Yabbuga na tsaye a qofar dakin Hansatu, riqe da jug din da ta ciko shi da wani tsinkakken kunun da ta tsulawa ruwan zafi, sai sallama take wage baki ta na dokawa, Isah ne ya fito ya na miqa, rigar shi a kafada, ko kauda ido Yabbuga ba ta yi ba, ta fara gaida shi ,

"Ango na Hansatu, an kwan lahiya?"

"Lahiya lau, qaqa an kayi yau kittaho gidan ga da swahiya haka?"

"Ohhh ni Yabbugan Dan jumma abin arziqi dai be amshi kare ba, wagga tambaya awab-ba a son zuwa na?"

"Ni ban ce ba, na ga dai ba ki saba taho wa da sahe ba, Ni rabo na ma da na gane ki gidan ga na mance"

Sai a sannan kunya ta kama Yabbuga.

"Yo jiya ina zaune na kunna gidan redio nijji Mallam na wa'azi akan zama da maqwacci lhiya, shi na nicce bari mu gyara, rayuwar ga ba tabbas"

Isah dai kurkure bakin shi ya yi, ya fice.

Hansatu ce ta qarasa fita tsakar gidan, dan dama ta na tsaye, ta nutsu ta yi shiru ne kar a ce kuma ta yi laifi.

"Barka da sahiya Yabbuga,"

"Barka dai Hansuwa, shin ina 'yan yara ban gane su ba"

"Su na ciki, karatu Ni ka masu, ke san abinda ya hwaru, ina tsoron barin su sake hita,kuma dama basu zuwa boko, to mu na karatu a gida "

"Allah Sarki, tauu ga wanga nikkawo musu, a gasa hanji, ko da dai na ga jiya kun tai gari a mota,"

Cikin dariyar son jin gulma ta yi maganar, Hansatu murmushi ta yi ya
Showing 21001 words to 24000 words out of 150481 words