mu shiga,koma menene ku ne kun ka jawo muna, dole a haka zamu shiga mu zauna da koma me ne ne a ciki"

Sultana ta kula da cewa ran Sultan ya fara ɓaci, abinda bai taba yi da iyayen su ba kenan, bayyanar da bacin ran shi irin haka, su kafe ya kafe, dan haka shiga maganar ta yi,

"Hajiya mu shiga sai a nemo mallammai masu ruqiyya su taho su taimaka muna, ko ya ka ce Yah Sultan"

Dauke kan shi ya yi, sannan ya ce,

"Ku shiga ciki, bari na shiga gari na samo malamin da zai zo a hwara tun yanzu, makullan gidan su na cikin safe din Daddy, ki bude ki basuwa in an zo amsa"

"Toh sai ka dawo"

*Ku taimakawa  gwamna Halliru da malami me ruqyaaa*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH

PAGE 60:

Sultan ya yi yawo, iya yawo amma bai samu dacewa da malami ko guda d'aya da zai taimake su ya je ya yi wa Gwamna Halliru ruqiyya ba, wanda suka amince za su je kuma bai gamsu da kalar tasu ruqiyyar ba, dan kuwa cewa suke aljanun yanka suke so a musu su sha jini, za su rabu da shi, (da damar masu cewa su na cire aljanu da yanka, ko kuma aljani ya fadi buqatar shi a masa sanan ya fita, ba rugiyya suke ba, domin ba haka ake ruqiyya ba a sunnar Annabi Muhammad ,bai bamu umarnin yi wa aljani hidima ba, kar fa mu manta Allah ya daukaka mu sama da su, kuma cutar da mu suke saboda ba ma ganin su, amma kuma a dinga musu hidima? Ko a je wajen su neman taimako? Duk wanda yake haka ya sabawa Allah, in bai tuba ba Allah zai kama shi, ko ya azabtar da shi kamar yanda gwamna halliru ke shan wahala a hannun su, ya nemi taimakon su ba na Allah ba, su kuma a yanzu suna azabtar da shi, saboda abinda ya kasance ya na aikatawa).

Da kyar ya samu wani malami guda ɗaya da ya amince zai je ya ga Gwamnan, amma sai da yamma, bayan ya sallami d'aliban shi da ke d'aukan karatu a wajen shi.

Sultan ya koma gida a gajiye, tun daga gate ya ke jiyo kururuwa da ihun gwamnan, gidan shiru, ba wata hayaniya, dan kuwa duk ma'aikatan sun gudu, mai gadi ne guda d'aya kawai ya rage, shi ma dan bashi da wajen zuwa ne, ya sa ya ke zaune a nan din.

Da shigar Sultan gidan, Sultana ta tunkare shi, idanun ta sun yi luhu luhu, saboda kukan da ta sha ta qoshi, ganin mahaifin nasu a cikin mawuyacin halin nan ba qaramin tashin hankali bane a gare ta, ko ba komai, ya gwada masu soyayyar da bata da misali.

"Yah Sultan ya na gan ka kai d'ai? Suman Daddy uku bayan tahiyar ka, na rasa me zan masa ya samu sauqin abinda yake ji"

Kuka ta fashe da shi, saboda tsananin tausayin mahaifin nasu, sultan ne ya kama hannun ta, idanun shi sun yi jajawur, ya ce,

"Mu je ciki, ki dena kukan haka nan, kukan ki ba shi zai bashi lahiya ba,daddy addu'a shi ke buqata, mu tai a samu a kunna karatun Alkur'ani kahin mallam ya taho, dan ba yanzu ne zai taho ba, sai yamma"

Cikin ikon Allah kuwa ana kunna masa karatun Alkur'ani bacci mai dadi ya dauke shi, zama suka yi jingum jingum su na kallon shi, kowannen su da abinda yake saqawa a zuciyar shi.

Hayaniya suka jiyo sosai, daga wajen gate din gidan, a tare suka tashi suka nufi waje, Hajiya babu ko mayafi, daga ita sai leshin jikin ta da d'ankwali, Sultana kuwa tun da suka je bata cire mayafin ta ba, haka suka fita.

'Yan jarida ne sun kai su takwas a qofar gidan, sai roqon mai gadin suke ya bar su su shiga daukan rahoto.

Su na ganin iyalin gwamnan kuwa suka hau daukan su hoto, tare da qoqarin yi musu tambayoyi, tambayoyin kuwa sun matuqar sanya Sultan da Sultana jin nauyi da kunyar amsa su, tambayoyi ne wanda  da suke tattare da  gaskiya, amma kuma ba za su iya amsa su ba kai tsaye.

Dan haka Sultan ya musu izinin shiga,kamar jira suke, cikin turereniya da rige rige suka shige gidan.

Zama Sultan ya yi a saman kujera da ke a farfajiyar gidan, sannan ya ce,

"Tambayoyin duk da kun ka yi muna, sun nuna cewa wasu daga cikin 'yan jarida musulmai ba su san amfanin aikin jarida ba ga rayuwar su, ta duniya da lahira, domin kuwa da damar su su yad'a labarin da zai jawo su yi suna, ko su samu wata daukaka ta duniya, ko arziqi shi d'ai suke bid'a, ba labaran da za su gyara, kuma su taimaki al'umma ba,misali, yanzu kun taho ku na so ku ji mi na na ya sami tsohon Gwamna, kun taho da list din zargin da mutane ka yi akan shi, me ya sa sanda shi na kan mulki, ba ku zuwa dan taimaka masa wajen yi mishi tambayoyin da za su sa ya yi aiki dole? Ko ku na nufin ba ku da wadannan tambayoyin tun gabanin ciwon shi?

To Bari na baku amsa, amsar da na ke so ku yad'a ta a duniya kowa ya ji, da farko dai dole ne mu san cewa duk abinda ya ke faruwa gare mu a wannan qasa, da wannan yanki,na harikar kidnapping, da kashe kashen rayuka, da sace dukiyoyin al'umma, ba komai ya jawo mana ba, sai sab'awa Allah, daga mu har shugabannin mu, domin kuwa Allah ya ce,

"Wancan ne, haka abin yake, lallai Allah bai kasance yana canza wata ni’ima da ya ni’imta akan wasu mutane ba face har sai sun canza abin da yake cikin rayukansu, kuma lallai Allah mai ji ne, kuma masani.”
(Suratul Anfal: 53)

Kenan mu na da laifi wajen barin tafarkin gaskiya, da annabin mu ya dora mu akai, mun qirqiri sab'on Allah kala kala, a jihar nan ne matasa da basu da ilimi, ba su da aikin yi ke sata, suke shaye shaye, su ke kisan kan mutane, su ke garkuwa da 'yan uwan su mutane, su ke tsafi, suke zina, suke luwadi, suke mad'igo, ba kalar zunubin da ba a aikatawa, to ku na tsammanin Allah ya kauda kai akan abinda ake yi? Ba daban Allah me rahama bane ba ma ku na tunanin yanzu da akwai wata halitta da ta yi saura a duniya?

Allah ya na cewa a cikin qur'ani mai girma

"Ka ce, Shi mai iko ne akan ya aiko da wata azaba a kanku, daga samanku, ko kuma daga karkashin kafafunku, ko kuma ya rarraba ku qungiya-qungiya, kuma ya dandana wa sashen ku masifar sashe (ma’ana: wasun ku su addabi wasu). Ka duba yadda muke sarrafa ayoyi, tsammaninsu suna fahimta.”
(Suratul An’am: 65)

Sannan Allah ya ce,

"Barna (musibu da fitintinu) sun bayyana a cikin qasa da teku (a ko’ina), saboda abin da hannayen mutane suka aikata. Domin Allah (yana nufin) ya d'and'ana masu sashin abin da suka aikata, tsammaninsu za su dawo kan hanya (su daina laifin da suke yi, su tuba).”
(Suratur Rum: 41)

Da Allah ya so da ya halakar da mu gaba daya kamar yanda ya yi wa wanda suka gabace mu, amma ya jinkirta mana ya na nufin Mu tuba, shin baku da labarin al'ummar da ta gabace mu ne? Wadan da Allah ya halaka saboda sun saba masa?Allah ya ce a cikin alqur'ani mai girma.

"Kuma da Allah yana kama mutane saboda dukkan abin da suka aikata (na zunubi, kuma ya zamanto baya yafe wani), da bai bar wata dabba ba a bayan kasa. Amma yana jinkirta masu zuwa wani ajalin da aka ambata. Sannan idan ajalinsu yazo, to, lallai Allah ya kasance mai gani ga bayinsa.”
(Suratu Fadir: 45)

Amma sai Allah ya ke hankuri da mu, ya ke yahe muna da mun roqe shi gafara, sannan Allah ya ke jinkirtawa wanda suka qi roqon gafara, dan in sun je gare shi ya musu azaba kwatankwacin abinda suka kasance su na aikatawa, ba dan ba zai iya kama mu ya azabtar da mu a duniya din ba ne.

Da mu da shuwagabannin mu sai mun koma ga Allah za mu ga dadai, an riga an kashe matasan mu, ba ilimi, ba sana'a, ba kasuwanci, zaman banza ya yi yawa, mutum naso ya saka sutura ko ya ci abinci, ko ya samu abun hawa ba shi da ikon yin hakan, in ba shi da cikakken imani sai ya je zuwa neman kuddi ta kowacce hanya, me kyau da mara kyau.

Ina mana nasiha mu ji tsoron Allah a duk abinda muke aikatawa, akan duk wani muqami komai qanqantar shi da Allah ya bamu, saboda wasun mu daidai da muqamin kwasar tutu mutum ya samu, buri nai shi cutawa na qasa da shi,ba tausayi, a tsakanin mu, ba soyayya a tsakanin mu, balle jin qai.

Ina fatan na amsa dukkan tambayoyin ku a wannan jawabi nawa, mu ahalin Gwamna Halliru Murtala Gusau, mu na roqar mishi yafiya daga wajen mutanen da ya yi wa mulki ba daidai ba, mu na roqon ku da ku yafe masa, domin Allah, kar ku diba abinda ya shiga tsakanin ku da shi na rashin adalci ko kyautatawa, ku dubi Allah ku yafe masa"

Duk dauriya irin ta Sultan a daidai wannan gabar sai da ya fashe da kuka, saboda ya sani, ba lallai ne mutane su yafe wa mahaifin nasu ba, sannan in masu redio da talabijin sun saurara ko kuma sun kalla, to wanda suke a qarqashin mulkin shi da ba su da kafar sadarwar fa? Wanda suka mutu fa? Wanda shi ya kashe su da hannun shi fa? Ta yaya za su yafe masa bayan ba su da rayuwa.

Kukan shi ne ya tsananta, har ya sanya 'yan jaridan da kan su suka janye abun maganar daga gare shi, sun zo da niyyar tozarta gwamnan, sai gashi sun samu nagartaccen d'an shi ya musu bayani, da nasiha mai ratsa zuciya.

Haka suka tafi jiki ba kwari.

Masu karbar makullan gidajen da Sultan din ya bayar sun sallama sun karba sun yi godiya sosai, sannan su ka tafi.

Har qarfe biyar ba malam ba bayanin malam, Sultan da sultana su ne suka yi alwala, suka ce wa Hajiya ma ta yi alwala, suka dauki qur'anan su suka yi ta karantawa, Gwamna ne ya farka da wani irin ihu, mai cike da razananniyar qara, wanda ya sanya Hajiya Ikee da Sultana miqewa suka buya a bayan Sultan a guje, sai makyarkyata suke, shi kan shi ba dan qarfin imani ba da ba zai iya zama a wajen ba, guduwa zai yi.

Jijjiga jikin Gwamna ya dinga yi, Sultan kuwa na ci gaba da karanto ayoyin da ya san ana ruqya da su, bai daina jijjigar ba har sai da ya fado qasa, duk jikin shi ya nannade, musamman qafafun shi, idanun shi sun qara fitowa kamar wanda ake turo su ake musu hayaqin barkono tsabar ja da suka yi.

Sultana da Hajiya Ikee ba abinda suke Banda kuka, dan ko addu'ar ma sun kasa.

Yau ace mutum mai cike da isa da izza kamar gwamna Halliru ne a nannade kamar wata igiya, su na cikin haka, Gwamna ya fara motsa baki ya na so ya yi magana, Sultan bai tsaya ba, karatu kawai yake ya na kumawa, Hajiya Ikee ko qiftawa ba ta yi saboda kallon shi, a ina ya iya wanan karatun? Da yaushe ya iya wannan karatu mai dad'in sauraro haka?

"Za mu sha jiniiii ! A bamu jinii ! Mu na so mu sha jinin d'an tayi !"

Abinda Gwamna Halliru ke ta nanatawa kenan, kamar karatu, duk wani yunkuri na Sultan akan ya ga lamarin ya lafa, ya zo da sauqi inaaa ba wani sauqi, sai ma qara tunzura su da yake, suna jin zafi da qonewar da suke amma ba za su fita ba saboda taurin kai.

A hankali tsoron da Sultana take ji ya fara tafiya, matsawa ta yi dan ta zauna, ta taimaka wa Sultan su ci gaba da karatun tare, ta ga Daddyn su na bin ta da wani irin kallo, ya na murmushi, sai dad'i ya kama ta, a zaton ta lafiya ce ta samu, a nannad'en da yake ya fara matsawa kusa da ita, hannu ta kai zata kama nashi hannun, kamar daga sama ta ji an ce,

"Kar ki taba shi, tashi daga wajen, Hajiya ku shiga daga ciki, ku bar mu, da izinin Allah, Allah zai bashi lafiya"

Sultana ta so yin gardama, amma ta tashi ba dan ta so ba, wani ihu gwamna ya saki, ya na fadin,

"Za mu sha jiniii, za mu sha jiniii jinin d'an tayii ! Za mu sha jiniiin d'an tayin can !"

Kallon su gaba daya ya koma kan Sultana da ke kallon hannun gwamna Halliru, wanda ya daga yatsan shi manuni, ya na nuna cikin ta, da sauri ta kama cikin ta ta na shafawa, cike da tsoro Hajiya Ikee ta ja ta jikin ta ta rungume, nan da nan kuwa suka bar wajen, Malamin da ya yi alqawarin zuwa ne, ya kunce jakar da ya zo da ita, ya daukko wani ruwan da ya yi wa addu'a, ya dauko wasu mayuka na korar shaidanun aljanu, shafawa Gwamna su ya yi, sannan ya fara karatu shima ya na watsa masa wannan ruwan.

Azaba ta yi azaba, gumurzu ya yi gumurzu, Gwamna ya gaji da tumurmusa shi da suke yi, amma ba shi da ikon hanawa, a can cikin ran shi ya yi dana sanin fara siyasa, ya yi dana sanin sanyawa zuciyar shi son abun duniya, amma ba shi da damar hana duk abinda ke faruwa, a can qasan ran nashi ya ke addu'a, Allah ya dau ran shi ya huta, hawaye ne ke gangare masa, ya na bin Sultan da kallo, malamin ne ya ke magana, dan yanda ya ga jikin shi ya saki, da alama sun jigata kwarai,sun qoqqone, shi ya sa jikin su ya saki.

"Ran ka shi dade, Ranka shi dade Halliru,"

"Ba za mu tab'a rabuwa da shi ba, sai dai ku kashe mu tare da shi,"

"Haka kun ka ce? To kuwa za mu yi addu'a Allah ya dauki rayuwar ku, ku ku mace ku bar shi"

"Allah ma ba zai bar mutum kamar Halliru ya ci gaba da rayuwa a doron qasa ba, ka kuwa san wane ne Halliru? Ka san me ya aikata a doron qasa? Ka na da la...."

"Ba na son sanin wane ne shi, ina roqon ku ta girma da azziqi, ku rabu da shi, kahin Allah ya ci gaba da qona ku,ta sanadin ayoyin shi da muke karantawa, don kuwa duk mun ka fara ba mu bari sai kun mace, maqiya Allah"

"Sai dai ka kashe mu, amma ba inda za mu, kuma sai mun sha jini, dan lokacin da yake bamu jini ya gota"

Sultan ne ya miqe cikin tashin hankali ya ce,

"Malam jinin shi suke zuqa, in suka sha jinin shi yanzu ba wanda za a qara masa zai iya rasa ran shi"

Kallon shi sosai Malam Ya yi, ya kalli gwamna da ya fara shure shure, qafafun shi na miqewa daga nannadewar da ya yi.

Sultan ne ya ta fi da gudu ya na qoqarin rungume gwamna Halliru, Malam kuwa na ci gaba da karatun Alqur'ani, tare da yarfa masa ruwan da aka yi wa ayoyin ruqya, jikin gwamna Halliru sai makyarkyata yake, ya na jijjiga da qarfi, jini ne ya fara fita ta hancin shi, idanun shi sun kada sun yi jawur.

Hankalin Sultan ya gama kaiwa qololuwa wajen tashi,

"Daddyyy, Daddy, kalle ni, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, ya Allah ka kawo mana agaji, Daddyyy ! Daddyy Please open ur eyes, Dad.."

A hankali jikin gwamna ya sake, kan shi ya fad'a qirjin Sultan, wani irin kuka mai cin rai Sultan ya sake,ya jima ya na kukan kamar zai shide Malam kuwa samun waje ya yi ya zauna ya na ta tasbihi ga Allah, duk abinda Allah ya yi shi ne daidai.

Kukan Sultan ya yi yawa, ta yanda har sama su Hajiya Ikee na jiyowa, a tare suka sauka qasa ita da Sultana, ganin abinda ke faruwa ne ya sanya Hajiya yanke jiki za ta fadi, Sultana ta taro ta, tare da cewa,

"Hajiya mu godewa Allah, tunda ya samu kwana, (bacci) mu isa, sannun ku Malam, Allah shi bada lada, mun gode,Yah Sultan ba kuka za ka yi ba, mu godewa Allah, tunda ya samu bacci , yanzu Mom ke fad'an ba su kwana, mu tai mu yi sallah mangariba ta yi"

Da qarfi Sultan ya ce,

"Wai ke ba ki da idanu ne? Daddy is gone, he is dead, ya mutu, ya rasu,"

Idanun ta ne suka cika da hawaye, ta fara kada kai, ta na so ta yi dariya, ta na kuma so ta yi kuka,

"Wasa ka ke yi ko? Daddy ba zai mutu ba, daddy bai mutu ba"

Da gudu ta sake Hajiya Ikee ta qarasa faduwa hannun kujera ta yi kan mahaifin nasu, da ya sake jiki, a jikin Sultan, jijjiga shi ta fara ta na kiran sunan shi, cike da kidimewa, gaba daya yau ilimin su, da tunanin su ya gushe (Allah kar ka gusar mana da hankalin mu, a lokacin da muke da tsananin buqatar shi, Allah kar ka sa mu
aikata abu da jahilci a lokacin da muke tsananin buqatar aiki da ilimi) wani irin kuka Sultana take mai tsananin ban tausayi, tare da surutan da basu kamata ba ace musulmi na gari ya na furta su, a lokacin da ya yi rashin wani nashi .

Mutuwar ta gigita kowa, Malam dai tun da ya zauna ya ke kallon kowannen su, tausayin su ya cika masa zuciya, ya san a wannan yanayin da suke ciki, wa'azi ko nasihar ma ba za su ji ba, a hankali ya fara furta

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,"

Tun ya na yi a hankali har ya fara da qarfi, sai a wannan lokacin ne hankalin su ya fara dawowa jikin su, suka fara furtawa su ma, su na kuka su na maimaita wa.

Cikin qanqanin lokaci Sultan ya fara waya, ya na sanar da dangin mahaifin nashi na nesa da na kusa, har da dangin Hajiya Ikee, hankalin shi bai kawo ba ya kira Lawwali ya sanar da shi.

Har sai da aka wanke Gwamna Halliru, aka kai shi makwancin shi na gaskiya a wannan lokacin, sai bayan sun
Showing 132001 words to 135000 words out of 150481 words