ya dinga naushi, sai da ya sumar da shi sannan ya ce a sheqa masa ruwa a dakko shi.

Ba musu haka suka ja shi a qasa kamar buhu, suka wurga a bayan mota, suka rufe gidan suka tafi.

Kowa dai ya san mutum kamar Lawwali zai wahala ace maboya daya gare shi,dan haka daya daga cikin maboyar shi suka nufa, waje ne kamar daji, ba gida gaba ba gida baya, ihun ka banza.

Su na shiga Lawwali ya bada umarnin a daure masa No 1 sama a qasa, sannan a banqara hannayen shi baya a daure.

Cikin abinda bai fi minti goma ba har sun gama.
A wahalce No 1 ke magana, duk qoqarin su na su ji kasawa suka yi, sai da wani a cikin yaran Lawwali ya kasa kunne a bakin shi sannan ya ji me ya ce, dan murmusawa ya yi sannan ya ce,

"Oga ya ce ka kashe shi dan Allah"

Banza Lawwali ya yi da su, ya kammala hada abinda yake haɗawa, ya sa suka juya masa bayan No 1 ya sa a kunna Camera a dauki abinda yake yi.

Ana juya masa bayan nashi ya debi ruwan acid ya kwara masa a bayan, wata iriyar qara da ihu No 1 ya saki, daga baya ya yi shiru, jikin shi ya saki, suma na biyu kenan, jikin No 4 sai rawa yake, tsabar tashin hankali, wannan azabar ya gudar wa kan shi tun asali.

Kamar Lawwali ba zai magana ba, ya duqa ya kama fuskar No 1 ya ce,

"Amma dai ka hi kowa sanin ba aikin Allah muke ba ko? Da aikin Allah muke da masallaci za a same mu, dan haka in ka na ganin ka hwara bautar Allah da gaskiya, daga yanzu tau ka hwara addu'a tsakanin ka da Allah'n shi dau rayuwar ka ka huta,amma da kai, da duk wani mai hannu cikin sace qauna ta, ko wane ne shi,ko uba na na sai na ga bayan shi, ko shi anka bawa mulkin qasa baki daya ba gwamna ba, sai na ga bayan shi , wannan alqawarin Awwal yayan Mubarakaa ne"

Da qarfi ya saki fuskar No 1, jikin shi ya hau lilo a wajen.

Kashe Video akai, ya amshi wayar shi, ya bar wajen, No 4 ya bi shi, cikin matsanancin tsoro,

"Ka shirya komai akan abinda muka yi magana ?"

"Eh...oga...na kammala komi"

"Good, gobe da qarhe shidda na sahe zan same ku a tasha"

"To Oga"

"Kafi kowa sanin hali na in aka ci min amana, kar ka yi wasa da amana ta, rayuwa ta zan dauka na baka, kar ka ci amana ta, Taheer in ka bari quda ya sauka akan Barakana, hummm"

Iya abinda Lawwali ya fada kenan,ya fada mota ya bar wajen.

**************************
Mubaraka bata tashi farkawa ba, sai ukun dare, ko da ta farka a tsaye taga Lawwali ya na kallon ta, hannu ta miqa masa cike da shagwaba, shi kuwa da sauri ya kama, ya zauna a gefen qafar ta, ya kai hannun ta bakin shi ya sumbata.

Murmushi ta yi, sannan ta ce,

"Yah Auwal ina so na ga Ummaana"

Wata tsawa ya daka mata sai da dakin ya amsa, Ita kuwa ta manne da jikin gado tsabar tsoratar da ta yi, nan da nan ta hau kuka, jikin shi ne ya yi sanyi, a hankali ya daidaita nutsuwar  shi,ya zauna gefen ta, ta yi baya, ta na zubar da hawaye,

"Barakana duk irin kewar ki da na yi, ki rasa me zaki fara magana akai, sai mutanen da basu damu da batan ki ba? Mutanen da ba su daina duk wata harkar su ta yau da gobe ba akan batan ki? Barkana Ni kadai ne na damu, Ni kadai ne na ke kasa bacci saboda rashin ki, basu damu dake ba, gobe zaki bar garin nan, ki yi nesa da kowa, ban damu da abinda zai same su ba, ke ce rayuwa ta, kowa ya san da haka,abokan gaba za su iya amfani da ke dan cutar dani, dan Allah kar ki min musu, ki bi duk abinda na ce ki yi, kin sani ba zan cutar da ke ba ko?"

D'aga kai ta yi a hankali, maganganun shi sun qona ran ta sama da yanda wuta ke qona leda, ta yaya za a ce iyayen ta basu damu da batan ta ba, iyayen ta fa na cikin ta, amma ba abun mamaki bane, ga duk wanda ya san halayyar su.

"Yah Auwal na ji na amince, amma ina neman alfarma"

"Kar ki ce mun zaki je ganin su"

Shiru ta yi ta na kuka a hankali,sautin kukan ta kamar ruwan dalma ake diga masa a tsohon ciwo,

"Ok tau ya isa haka nan, ina kai ki gobe"

"Yah Auwal ina so na ga Aunty Sultana, na yi kewar ta, na san ta damu da bata nako? Har mafalkin ta ni kai"

Murmushi mai sanyi ya yi, wanda shi kan shi bai san ya yi ba, Mubaraka na ganin haka ta tabbata har yanzu akwai soyayya a tsakanin su .

"Tayi kewar ki fiye da yanda baki tsammani, amma lokaci ba zai bari ba, na san yanzu haka ta na sallah, bari na kira na hada ku,gobe da asuba zan kai ki gida, daga nan mu wuce tasha, duk wanda kin ka gani a matsayin wanda zan hada ku, ki yarda da shi, na san ko waye shi,ki yarda da shi,ba zai cutar da ke ba, na sai Maki waya da komai da zaki buqata, na sai gida duk da sunan ki, na sai motar da za a dinga hidima dake makaranta da duk wani abu da zai inganta rayuwar ki Baraka na na yi miki, hankalin ki kawai ni ka so ki kwantar,duk sanda ki ke da buqatar gani na ki hwada min ko a waya ne zaki ganni ke ji?"

Ba abinda take in ba kuka ba, ba ta jin za ta iya jure zama ba shi, amma ba za ta iya masa musu ba.

Da misalin hudu da rabi na asuba ya kira sultana, kamar ya sani kuwa sallah take, sai da ta idar ta kira shi, jin Muryar Mubaraka ba qaramin dad'i abin ya mata ba, ajiye wayar ta yi ta yi sujjadar godiya ga Allah sannan suka hau hira, duk kalar tambayar da Lawwali ya hana ta amsawa bata amsa ba, sai dai ta ce bata sani ba itama.

Biyar saura minti goma suka yi sallama Mubaraka ma ta yi alwala ta yi nafila.

Ta na idarwa Lawwali ya sa ta yi wanka ta ci abinci, sai gidan Alhaji Dan Talo.......

*Ai na manta ashe bai je Makka ba😂😂🤭*


💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻



BY HAERMEEBRAERH



PAGE 36:



Tun sanda Lawwali ya girgide musu qofar ya jingine, har yanzu ba a samu mai zuciyar da ya tsakura daga kudin da Lawwalin ya ke basu ba aka gyara qofar, dan haka yau ma da qafa ya daki qofar ta bude, ta na kaiwa qasa hankulan mutanen gidan da maqotan su duk sai da ya tashi, domin qarar ta yi matuqar tsorata su.

Mubaraka ce ta kalle shi ta kada kai, dan ta gama fuskantar a fusace yake, ba dan ta matsa masa ba ba za su je ba.

A tsaitsaye suka tadda mutan gidan, cikin sallallami da jimamin me ke faruwa, idanun su na sauka akan Mubaraka, murna ta kama su, musamman su Jameelu, wanda sai da suka runtuma a guje wajen ta, za su taba ta Lawwali ya dakatar da su, ba musu suka ci birki.

"To kin gan su mu tafi?"

"Yah Auwal ka bani minti goma dan Allah"

"Whatt? Minti goma? Mi za ki yi halan?"

Takawa ta yi gaban Lamishi da ke ta wangale baki, har cikin tsokar zuciyar ta ta ji dadin ganin 'yar ta ta, haka ma Mai buruji da Dan Talo, amma su na jin tsoron zuwa gare ta ɗan tijarar nasu ya musu rashin mutunci.

"Umma na, na dawo, Alhamdu lilLAAH, Yah Auwal ya kwato mu daga hannun azzaluman da sun ka sace mu ni da su Murjanatu, Ummana na yi kewar ku sosai, duk sanda na tuna ku ina can, sai na ji hankali na ya tashi, sai in dinga hango wa zai dinga miki girki in ba abinci? Wa zai gyara miki daki? Wa zai zanka kai miki ruwan wanka ke da Baba, wa zai zanka shara da wanke-wanke? Ummaa na sai in dinga tuna wa zaki dinga yi wa hwada in ya yi ba daidai ba? Hankali na na tashi inna tuna duk sanda ki ka tashi baki ganni ba wane irin qunci zuciyar ki za ta shiga,.......ashe.....ashe ni damuwar banza nikai, hankalin ku kwance shike da bata na, na so matuqa na ci gaba da zama da ku, domin ko zuciyar ku ba ta so na, ni tawa zuciyar na son ku da qaunar ku, amma a halin yanzu zan bi yaya na, duk inda ya sanya qafa nan zan aje tawa, na gode da zama iyaye da kuka yi a gare ni na tsawon shekaru,za ku ci gaba da kasancewa iyaye na har abada, sai watarana"

Cikin hawayen da ke ta zuba mata ta juya za ta koma wajen Lawwali da zuciyar shi ke ta tafasa, ya na jin zafi da takaicin abinda suke wa Mubaraka duk da ta kasance yarinya mai biyayya, Lamishi kuka take sosai na nadamar abubuwan da ta aikata, amma ba yanda zata yi ta hana Mubaraka bin Lawwali, dan bama ta isa ba, d'an zagi da fadan ma da yake d'aga mata qafa ta na masa yanzu babu dama, ya toshe hanyar su, dan yanzu zai hargitsa musu lissafin gida, juyawa Mubaraka ta yi ta kalli Lamishi da ke kuka qasa qasa, ita da Mai Buruji, sannan ta tsaya ta ce,

"Yauwaa wane suna ma ki ke yawan kira na da shi ? GANTALALLIYA yar iska, da sauran su ko? To ina mai maki bushara da ni din nan, da kike kira da gantalalliya na godewa Allah da ya sa bani na dauki qafafu na na tafi gantali ba, daukata an kai aka kai ni wajen gantalin, me ki ke fata na aikata a wajen Gantali?...."

"Baraka, mu je"

Ba ta yi shiru ba, so take ta bawa Lamishi labarin abinda ya same ta a wajen, amma ba zai iya jure sauraran abinda aka mata ba, jikin shi har rawa yake saboda bacin rai, Lamishi kuwa kuka take bil haqqi, a rayuwar su kaff Mubaraka bata taɓa maidawa wani magana haka ba, me aka mata a can din? Me ya same ta, Lawwali ne ya daka mata tsawa a qoqarin ta na son sai ta qarasa labarin ta, jan hannun ta ya yi ta fuskance shi, su na hada idanu ta sanya kuka sosai, da qarfi ya rungume ta a jikin shi ya na numfashi sosai, dan kuwa shi ma kukan yake ji.

Maida Mubaraka gefe ya yi, ya kalli iyayen nashi ya ce,

"Wannan kukan munafurci  na ku kai wallah, ai murna za kuyi ku taka rawa, abinda kuke so, ya samu diyar ku, kullum fatan ki ta yi yawo ko? Ta yi gantali, ke kin san ma'anar Gantali kuwa? Ki ke hada d'iyar ki ta cikin ki da wannan mummunar kalma? Kin yi kuskure matuqa, ga gangali nan ki na gani, ko da shi ke ke rayuwar da muke ciki bata dame ki ba, ba a maganar mijin ku (subhallah mahaifin shi ya ke kira da mijin su) shi dai gashi nan ne d'ai, a dahwa a bashi ya ci shi kwanta da ku, ku haihwa, ya shiga gari ya yi hira da abukkai shi dawo, shi ci abinci, shi tai yawo, shin baka gajiya da aiki guda yau da gobe ba wani sabon abu da zaka qirqira da zai amfane ka da iyalin ka? Ko ni da nike wannan harka watarana gajiya nikai, to yanzu burin ku ya cika, kun haifi kalar diyan da kuka so, sai ku yi ta kuri a unguwa, mu tai, lokaci na tahiya"

Har sun kai soro ya koma ciki, a fusace ya debi dika kudin aljihun shi ya watsa musu, ya daki bokitin da ake dama kunu a gidan, ya ce,

"Gashi nan, ga abinda kun ka fifita sama da jini da tsokar ku,...ohh yi hankuri na hwashe muku bokiti, ku sai wani"

A tsaye a bakin mota ya tadda Mubaraka ta na rizgar kuka, al'ajabin iyaye kamar su Dan Talo take yi, wai wasu mutanen a duniya me suka dauki aure ne? Mai suka dauki samar da zuri'a ne, shin sun cancanta ma su zama iyaye?

Ba su bar wajen ba sai da Lawwali ya lallashe ta, ya bata baki sosai, da yi mata nuni da rayuwar da yake mata fata a gaban rayuwar ta.

Cikin gidan Dan Talo kuwa bayan tafiyar su Mubaraka, Lamishi d'aki ta shiga ta ci gaba da kuka, tare da danasanin abubuwan da ta dinga aikatawa, ba abinda ke mata gizo sama da kalaman Mubaraka na qarshe, shin me ya same ta?

Mai Buruji kuwa tattare kudaden ta yi tsaf, ta na gamawa Dan Talo ya je gaban ta, ya ce,

"Bakkani su nan (bani su nan)"

Wani kallon tara saura kwata ta masa, sannan ta ce,

"Me ya sa da ina tattarawa baka taya ni ba, sai da niqqare, zaka ce na baka? Tau ban basuwa, yaya zan bawa"

Cikin kad'a kai, da kyacci (qwafa)ya bar gidan, domin kuwa haske ya bayyana sosai, kowa na ganin kowa, gari ya washe.

A tasha kuwa Mubaraka kuka ta sanya ta na tirjewa akan ba zata bi su No 4 ba, tun Lawwali na lallashi har ta suqurar da shi ya hau fada,

"Gidan uban wa za ki zauna in baki bi su ba? Waje na? Rayuwar ki ta zauna cikin hatsari? Na rasa nutsuwa ta? Ko na kasa aiwatar da ayyuka na na yau da gobe, ko kuma wajen wadancan mutanen ki ke son komawa(iyayen su ya ke nufi).

Ita dai ta yi dif hawaye na zuba, ganin yanda take a tsorace ne ya sanya shi jan ta gefe ya daga kan ta, ya na share mata hawaye, sannan ya rungume ta, kukan ta ne ya qaru, ita dai da zai taimake ta, da ya barta a duk inda ya ke, bata son barin garin, musamman da No 4.

"Baraka na ki saurare ni da kyau ki ji, Taheer ba zai taba cin amana ta ba, na san inda zaku zauna, na san komai game da rayuwar shi, ba zai cutar da ke a kan sanin shi ba, ko wancan bai san ke za a dauka ba , sanda ya sani lokaci ya qure, na yarda da Taheer kamar yanda na yarda da kai na, dan Allah kar ki qi binai, hankali na zai hi kwanci in ki na can,ke ga shi na da iyali, ba shi d'ai na ba, ga mahaifiya tai, ga mata tai,ga diya nai, ba ke dai ta ba hwa"

Ita dai jin shi kawai take, ta hakura zata bi su,amma ba dan zuciyar ta na so ba.

Lawwali na tsaye ya na ganin yanda Mubaraka ke share hawaye, daga musu hannu ya yi sanda motar su ta tashi.

Cikin tsananin hawaye ya juya ya nufi motar shi, tunda yake a rayuwar shi yau ce rana ta farko da ya yi addu'a ya roqi Allah wani abu da kyakkyawar zuciya.

"Ya Allah ka kare min qauna ta, Allah ka san wad-da ni ka son ta, Allah duk inda take ka zama gatan ta ba na kusa balle na bata kariya, Allah ka kare min ita, kai na mai kare bayin ka a duk inda suke, Mubaraka bata da lehin komi, Allah ka sani komai ke faruwa laihi na ne, kar ka hukunta qauna ta da lehi na"

Ya jima zaune a motar idanun shi sun yi jawur saboda kuka, time ya kalla ya ga bakwai da rabi, cikin sauri ya nufi gida kafin ya isa takwas ta wuce, wanka ya fada, ya yi a gaggauce, ya na shiryawa wayar shi na ringing bai dauka ba dan ya san ko waye.

Sai da ya gama shiri tsaf, ya ci abinci sannan ya fesa turarukan shi masu qamshi mai dad'i, sannan ya samu yaran shi da ke gidan ya sallame su, tare da basu umarnin komawa can sansanin su.

Ya na tafiya kan ya isa gidan Gwamna ya yi waya da wanda ya bawa tsaron No 1 ya ji ya suke, sun sanar da shi duk irin abinda ya ce su yi ba wanda ba su aikata ba, ya na nan ya na jin jiki, murmushin jin dadi ya yi, sannan ya kashe wayar shi.

Ran shi fess ya shiga gidan, a qalla ya sauke manyan nauyin da suke kan shi, saura na gaba.

A tsaye ya gan ta, ta na ta safa da marwa, hankalin ta a tashe, siririyar dariya ya saki, dan kuwa ya san sai ta masa shagwabar ta, akan dad'ewar da ya yi, ta bayan ta ya ja ya tsaya, tare da kama kunnuwan shi, qamshin shi ne ya sanya ta tsayawa cak dan kuwa ta san ya iso kenan.

Cike da shawagabar kuwa ta juya, ta langwabe kan ta gefe daya, ta na kallon shi da wani irin sassanyan kallon da ya sa jikin shi mutuwa.

"Me ya sa ka ke min haka? Ka na so zuciya ta ta buga ko?"

"Tabdi, ashe dama zuciyar ki bata bugawa? To da inji ne a jikin ki ki ke amfani da shi?"

Cikin kama haba da kallon ta a karkace yake maganar, hakan da ya yi ba karamin dariya ya sanya ta ba,ai kuwa dariya ta dinga yi, shi ma ya na taya ta,  kallon yanda fuskar ta ke sheqi da walqiya yake ta yi, a hankali ya furta,

"Sultana ke kyakkyawa ce, fuskar ki na sheqi kamar hasken farin wata, zan so ki kasace cikin hwarin ciki har qarshen rayuwar ki"

A hankali ta daina dariyar ta ɗan sunkuyar da kan ta, ta na murmushi,

"Ameeen Allah ya sa, amma ka dena zuga kyau na, duk yadda  ka ke ganin kyau na, naka ya wuce nawa,"

Kama baki ya sake yi, sanan ya ce,

"Ran ki shi dade mu bar wagga magana, namiji ina yaga kyawu? Namiji iri na dan talakawa taya zai zama mai kyau?kyau ai shi na wajen ku diyan masu kuddi, mai da sabulu da komi da kuka amfani da shi daban ne da namu,"

Ran Sultana ya baci da kalaman shi, ya kuma kula da hakan, dan haka sassanyar dariya ya yi, ya ce

"Yi hankuri wasa ta
Showing 72001 words to 75000 words out of 150481 words