ya ga ba me kallon shi, ya fiddo kudin ya na tafiyar fad'i.

A gaban me gadi ya tsaya, ya dinga juya su, ya na masa kallon raini.

"Kai mai gadi, ka shiga hankalin ka, in ba haka ba, se na sa an kore ka, masu gadi uku na fitar a gidan nan tun sanda ina zama a gidannan, ka tambaya ka ji wane ne Isah direba, tsohon dan iska ne ni, kuma surukin gidannan ne, daga yau na sake zuwa ka min iskanci se ka bar gidan nan, tunda ba gadon tsoho a ciki wajen gina shi"

Me gadi baki ya sake ya na kallon ikon Allah, se da Isah ya maida kudi aljihu, ya gyara tsaf sannan ya bar gidan.

Ko daya isa gidan shi, ya tadda Hansatu na ma yara wanka,ta share gidan fess ko ina qalqal, ta yi wankan ta shar da ita, da kayan da aka bata daga gida, ramar da ta yi ne da baqin da ta yi ne kawai ze nuna halin rayuwar da take ciki.

Murmushi ta mi shi, wanda bata gajiya da yi masa a duk sanda ze fita ya koma gida, dauke kai ya yi, kamar kullum.

Ba sallama ya shige, za ta bi shi ta masa sannu da zuwa ya dakatar da ita cikin daure fuska, komawa ta yi ta ci gaba da yi wa Ahmad wanka, ta na yaqe, abun ya mata zafi sosai, amma ba halin magana.

Se da ya boye kudin shi tass sannan ya dauki dubu talatin ya bar gidan, ta na fada masa ga abinci amma bai kula ba.

Direct wajen yin passport ya je, aka ce gobe ya koma, bai ji dadi ba, haka ya tafi, ya na saman machine suka wuce wani mai saida gasasshiyar kaza,yawun shi ne ya yanko, ai kuwa ba bata lokaci ya ce ma me machine ya juya, Isah kamar abun wasa, ya ce a bashi kaza daya, qosasshiya aka yanka masa ita aka bade ta da yaji, sannan ya ce a bashi rabin kaza again , aka yanka aka sa yaji, ya amsa, shagon kusa da wajen ya je, ya sayi drinks, ya samu wani mai machine din ya nufi gida.

Ya na zuwa ya tadda su a tsakar gida Hansatu na musu karatu, miqa mata ledar kaza ya yi, ya wuce daki, Hansatu da yara na ta murna, su na ta zuba godiya.

Ya na shiga dakin ya bude tashi, sai a lokacin na kula da qatuwar kazar nan ya aje wa kan shi, ya basu rabi, kamar abun wasa, Isah ya sa kazar nan a gaba da ci, bai tashi ba se da ya ci ya taune qashi ya kora da lemo me sanyi, sannan ya saki muguwar gyatsa, ya ce,

"Yauwaaa Allah na gode maka,me ake da talauci? Allah ka nuna min buri na ya cika, kullum se na ci wannan"

Hansatu da yara kuwa na can sun saka barin kaza a gaba, su na ci, su na hamdala ga Ubangijin da ya azurta su da kaza ba tare da sun roqa ba.

Dan sauran lemon Isah ya fito ya miqawa Ahmad ya ce,

"Gashi nan, ba yawa ne da shi ba,...ke kuma in kin gama ki zo ina neman ki"

"To mun gode Allah shi qara budi, Allah shi ruhwa maka asiri duniya da lahira, mun gode,"

"Ameen, ina abinci na? Ko dan kun ci kaza se aka ce miki ba zan ci abinci ba?"

Da sauri ta miqe ta na bashi hakuri, abincin dama da ya rage taliya ce da manja, da dan yaji, har ta na murna in be ci ba da dare ta bawa yaran, tunda komai ya qare, ya siyar.

Ta na bashi kuwa ya zauna a tabarmar da suka tashi, ya cinye tass, ya kora da ruwa.

Daki ya kira ta, da yammar, ana gab da magariba, Hansatu na ta bashi hakuri akan ya bari a mayi sallah haka Isah ya qi, sai da komai ya yi daidai a tsakanin su sannan ya sa ta hura wuta ta ɗora masa ruwan wanka, dan a cewar shi yin wanka da ruwan sanyi da magariba mura ze saka shi.

Da kyar iccen ya kama, ta samu ta ɗora ruwan ya yi,ta kai masa, itama tayi, ta yi sallah.

Shi kuwa ya na gamawa waje ya yi, ganin shi kuma se sanda Allah ya yi musamman ma da yake jin aljihun shi da nauyi.

Hansatu na shara, ta ji sallamar Yabbuga, watso sharar dakin ta qarasa yi, ledar da Isah yaci kaza ta baje a qasa, ido Yabbuga ta zare waje, tare da sake baki, ta na salati.

"Keeeee waggaa, yanzu kaza kun ka ci shi na ko a qunshe fuffuke a kai min, tau wanda ya ci shi dai, shi dai zai mace, walle a dena rauwwa, yanzu ba daban Allah ya sa na ga kin kunna wuta ba, na zo diban rushi, da ban ko sanin kun ci kaza"

Hansatu mamaki ne ma ya gama qamar da ita a wajen, yanda Yabbuga ta dage ta na magana cikin fad'a ne ya fi bata mamaki, kuma gashi tabbas yawu ya cika mata baki, murmushi ta yi, ta ce,

"Allah shi baki hankuri, dake ba a gidan anka soya ba, balle na ce qamshi ya dame ki, nima yanda kiggane ta haka niggane ta, ya taho mana da ita, amma ki yi hankuri, in ya sake kawowa ina kawo maku"

"Tun da kwadayayya ni ke ko? Yo ce miki niyyi bamu da azziqin cin kaza? Yau na ji zancen yohi"

Yabbuga na diban garwashi ta na Masifa ba a sammata kaza ba.

Hansatu kuwa abun ma ya dena bata mamaki, dariya ta dinga yi, ita da yaran.

***********************

A bangaren Lawwali kuwa............

*Sai gobeeeeee*😅
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻


BY HAERMEEBRAERH


PAGE 27:




Sati biyu ya wuce ba Lawwali ba bayanin shi, ba Sultana kadai ba, hatta da Gwamna Halliru ya fara shiga tashin hankali akan lamarin Lawwali.

Duk wata barna da ta'asa da Lawwali ke aikatawa ta na komawa kunnen Gwamna Halliru, ga zabe ya gabato sauran kwana goma sha uku, lamarin ya tabarbare fiye da tunanin Gwamna, domin kuwa a yanzu Lawwali ko cikin gari bai cika shiga ba, sai jefi jefi dan ya ji halin da ake ciki game da neman qanwar shi da ya sa a yi.

Lawwali ya koma kamar mahauci, akan neman Mubaraka, ya yi kuka har ba iyaka, ya zama kamar wanda ya rasa iyayen shi da dangin shi a dare daya.

Duk wata motar da ta yi tsautsayin bi ta kusa da dajin su, to sunan su matattu, ko kuma ya sa a kame su, ayi ta azabtar wa, ko ya sa a yi ta amsar kudi wajen dangin su, madadin batan Mubraka ya risinar da shi,sai ya sake ruruta masa wutar rashin imani a zuciyar shi.

Sultana kuwa duk ta fige ta rame saboda rashin Lawwali, ko ta je Foundation din ma watarana da kuka take komawa gida, rashin ganin shi a idanun ta ba karamin azabtar da zuciyar ta yake ba.

Duk ta dora laifin akan Hajiya, domin a tunanin ta maganar da Hajiya ta yi ne ya sanya shi yin fushi ya tafi.

Ta gwada No shi ya fi sau shurin masaqi amma ta qi shiga, kullum sanar da ita ake a kashe wayar take, ta yi kuka ta godewa Allah, ta yi sallah ta yi addu'a akan Allah ya dawo mata da shi in da alkhairi, in babu Allah ya sa mata hakuri da dangana, hakan da ta yi ne ya sa ta ɗan samu sauqi kadan a ran ta, har ta ci gaba da aikin alkhairin da ta sa wa ran ta.

Shiru shirun ta, da rashin shiga mutane da take ya bawa Gwamna damar yada abubuwan da take na alkhairi a gidajen talabijin da rediyo, da duk wata kafar sadarwa, mutane kuwa na ta yabawa, wasu na qara neman taimako a wajen ta, ita kuwa hakan na mata dadi, ganin aikin da take ya na ta bunqasa.

In ta na aikin ta na samun nutsuwa da kwanciyar hankali,da ta dawo gida komai sai ya kwance mata ,ba abinda take gani a idon ta in ba Lawwali ba, tsayuwar shi a jikin mota, da murmushin shi mai sauti, yanayin yanda yake kafe ta da ido, ya na kallon ta, sai ta ji kamar a wannan lokacin ya ke kallon nata, har lumshe ido take, watarana ta yi murmushi in ta tuna, watarana ta fashe da kuka.

An shiga sati na Uku Lawwali be bayyana ba, sai wata safiyar Lahadi, ya shiga gari, direct wajen aski ya nufa,a ka yi masa aski me kyau, aka masa gyaran qafafu da hannuwa, sannan ya sayi turaruka, da kayan abinci ya nufi gidan shi,ko da ya shiga gidan duk ya yi qura, kallon ko ina ya yi, cikin sanyin jiki ya ajiye ledojin hannun shi ya kalli ko ina, wasu irin zaratan hawaye ne masu zafi suka dinga zubar masa.

Mubaraka ce ke masha shara, in ta biyo shi, ta yi wanka ya maida ta gida, ko gyaran da akai wa gidan na qarshe ita ta masa, har ta dinga mishi fadan ta ajiye wani flower vase a tsakiyar table, ta koma ta gan shi a qasa, ya kama kunnen shi ya na bata hakuri, ta na ta tura baki ta na shagwaba, ta ce ta hakura kar ya sake, ta mayar ta gyara komai, ta yi wanka ya maida ta gida, ya na gama tunawa ya sanya wani irin kuka mai ban tausayi, sannan ya ce,

"Barakana ina kin ka tai na? Wanne hali ki ke ciki? Kin ci abinci? Kin yi wanka kuwa? A wanne irin waje ki ke kwana? Barakana, ki yafe wa yayan ki, na kasa kare ki, na kasa nemo ki, baraka na ki dawo gare Ni, ke ce sanyin idaniya ta, na rabu da Sultana duk da son da nake mata, na kasa cire ta a zuciya ta, dan Allah ki dawo ki taya Ni neman soyayyar ta, ba zan iya ba Ni dai,ke Ni ka jira ki sa Sultana ta so ni, Barakaaaa"

Kuka ya dunqule a waje guda ya na yi, kamar qaramin yaro, ya na son dika qannen shi, amma mubaraka ta daban ce, ita kadai ce ke son shi, ita ke kula da shi, ita kadai ta damu da rayuwar shi, tun ya na da burin ya dawo na gari, har ya kangare, ba wanda ya damu da wace iriyar rayuwa yake ciki, kudi kawai iyayen shi suka sanya a gaba, yau kuwa zai kai musu kudin da zai haukata su, amma sai suma sun bayyana masa Barakan shi, ko ya sawa kudin fetur a gaban su ya qona, hakan sai ya fi masu ciwo sama da yanda yake ji a ran shi.

A haukace ya debi kudin da ya koma da su, masu dimbin yawa a jaka, ya zari makullin motar shi, da wayar shi da ya bari a gidan, bai je ko ina da ita ba, motar shi duk ta yi qura.

Ya na shiga ya fitar da ita, ya koma ya kulle gidan, ya na qoqarin fita daga layin, motoci guda biyu da ke kai Sultana Foundation a yanzu su ka shiga unguwar suma,kamar an ce ta daga kai, Lawwali ta gani fuskar shi ba walwala, idanun shi jawur kamar ba shi ba, ya na tsula gudu,gashi duk ya yi duhu,

"Auwal? Dama Auwal na nan? Shi ne ya daina zuwa? Driver bi motar Auwal duk inda ya yi,"

"Tau Ran ki shi dade"

Dayar motar masu tsaron lafiyar ta na ganin an juya suma suka bi su, ta waya ta sanar da su me ke faruwa, kwantar da hankalin su suka yi suka bi su a baya.

Saboda damuwar da Lawwali ke ciki, be ma kula ana bin shi ba, har sai da ya shiga unguwar su, ya tsaya a qofar gidan su, sannan ya kula da motocin Sultana.

Wani irin yanayi ne mara fassaruwa ya shige shi, kewa ne, tsantsar soyayya ce, da kuma neman taimakon ta, duk sun had'u sun game masa waje daya.

Ita kuwa bata san sanda hawaye ke gudu a fuskar ta ba, ga alama nan, Lawwali na shaye shaye, amma bata duban wannan, domin dama dan Adam tara yake, be cika goma ba, ita dai a kowanne hali yake ta na son shi, ita kadai ta san ya take ji.

A hankali suke takawa zuwa ga junan su, Sultana ji ta yi kamar ta kwantar da kan ta a faffadan qirjin shi, ko abinda take ji zai ragu, Lawwali ji ya ke kamar ya isa ya rungume ta, ta shafa kan shi da siraran yatsun ta, tare da fada masa cewar 'Komai zai wuce, zai yi daidai' a cikin kunnen shi.

Sun jima su na kallon juna kafin Sultana ta yi qarfin halin cewa,

"Why? Me yasa? Me ya sa za ka tafi a lokacin da zuciya ta, ta amince, ta yarda, ta kuma gamsu da ta kamu da matsanancin ciwon son ka? Me ya sa ka tafi, a lokacin da nake tsananin buqatar ka, ka kuwa san ya nake ji a nan dina? (Ta sanya hannu, ta nuna saitin zuciyar ta, cikin kuka,) ba zaka gane ba, saboda baka san me ne ne soyayya ba ga dukkan alamu,"

Cikin sauri ya dakatar da ita, dan kalaman ta na sake harzuqa zuciyar shi, ta na hango masa mugunta kala kala.

Cikin cije lebunan shi a cikin bakin shi ya shafa kan shi, da hannu daya, sannan ya ce,

"Sultana, ba ke dai ka jin duk abinda kin ka lissahwa ba, ni ma ina ji dika, wataqila har da dori ma, amma sultana ba ke d'aya zuciya ta ke so ba, qauna ta ita ce rayuwa ta, ban da komai banda kowa sama da ita,ita kad'ai ce gata na a duk qasar ga, ba mai so na tsakani da Allah, sama da ita, a yanzu haka ji na nake kamar duk duniya sun juyan baya, ni kadai ne, ban da kowa banda komai,"

"Wait a minute,me ya samu Mubaraka?"

A cikin tashin hankali Sultana ta masa wannan tambayar, a cikin qasa da minti bakwai ya bayyana mata me ya faru dangane da batan ta,da kuma irin neman da yake mata, bai samu ba.

Cikin kuka Sultana ta juya ta rufe bakin ta, ta jima a haka ta na kuka, Lawwali ma ji ya ke kamar ya yi kukan, sai daga baya  ta juya gare shi, ta na share hawayen ta, motar ta ta fara budewa zata shiga,sannan ta ce,

"Mu je gida Daddy na nan yau, mu sanar da shi,a sanya neman ta, duk inda ta shiga, i love her, she is a gud gurl, I can't let anything happen to her, she is like a sister to me, mu je gida Auwal, maza shiga mota mu je,"

Kallon gidan su ya yi, cikin takaici, ya na jiyo muryoyin mata ana ta zabga hira, ya ji haushi da be shiga ya tarwatsa su ba, qanwar shi ta bata amma suke hira haka ana dariya har waje ana ji, ya so ya shiga ya gan su, da duk sai ya musu rashin mutunci d'aya bayan d'ayan su, amma ba komai next time.

Kwafa ya yi, ya shige motar shi, ya bi ta su Sultana.

*************************

Gwamna Halliru na ganawa da su No 1 da 4, su na tattaunawa akan yanda Lawwali ya haukace.

Sultana ta je za ta shiga parlour wasu masu tsaron wajen ne suka dakatar da ita, tare da sanar da ita cewar Gwamna ya ce kar a bawa Kowa damar shiga, sai da izinin shi, d'aya daga cikin su ta kalla tace,

"Ka je ka sanar da shi ni ce, na ke son magana da shi, ya na da mahimmanci na gan shi yanzu"

Har security din zai tafi, Lawwali ya qarasa shiga wajen, su na hada ido, security ya ja baya, tare da fadin,

"Ran ka ya dade Oga, Barka da zuwa"

"Gwauna hwa? "

"Shi na ciki Oga"

Mamaki ne danqare a cikin Sultana, an hana ta shiga amma an budewa Lawwali  ya shige,me kenan? Lawwali ya fi ta matsayi a gidan Uban ta kenan?

Ko da suka shiga shiru wajen ya dauka, ba No 4 da ake tausa ba, ana nuna masa ba abinda Lawwali zai yi, as long as bai gane ina qanwar shi take ba, har Gwamnan kan shi sai da hankalin shi ya tashi ainun.

Cikin rawar murya, No 4 ya ce,

"O....ogaa, kai ne da rana haka?"

Lawwali ko kallon No 4 be ba, ya samu kujera ya zauna, tare da harde qafa,No 1 ne ya je ya tsaya a daf da shi,hakan kamar girmamawa ne a gare shi, No1 na ta hararar No 4 tare da yi masa nunin ya nutsu, Sultana kuwa mamakin abinda take gani ya fi qarfin ta, waje ta samu ta tsaya, ta na kallon yanda mahaifin ta ya yi lakwas a gaban Lawwali, bai magana ba akan zaman da Lawwali ya yi a gaban shi .

"Oga har yanzu fa shiru,yanzu haka mun kawo maganar ne wajen Excelency saboda a bamu taimako"

"Mu ma abinda ya kawo mu kenan,na yi iya qoqari na na kasa, ina neman taimako a hukumance, a bido min qauna ta, in ba haka ba,....."

Shiru ya yi, ya taune leben bakin shi na qasa, tare da dukan tafin qafar shi da ya dora a saman dayar qafar tashi.

"Ah ah Sultana, mik-kawo ki nan?"

"Tare muke,"

"Ban gane tare kuke ba, qaqa an kai kuke tare?"

"Dad Mubaraka ce ba a gani ba, kusan sati Uku yanzu, shi ne na rako shi neman taimako wajen ka, amma yanzu na kula is like, ni anka rako, ko wani zai iya min bayani akan abubuwan da nake gani a yanzu?"

Da sauri gwamna ya zari wayar shi, ya kira Head quarter na yan sanda, ya fara bada report din batan Mubaraka, Sultana tuni ta manta da tambayar da take yi, ita da Lawwali sun bawa Gwamna hankulan su.

Wayar aka bawa Lawwali ya yi kwatancen ta,da bayanin ranar da suka nemeta suka rasa, tare da alqawarin ze tura hotunan ta.

Godiya ya miqe sosai ya na wa gwamna, Sultana ma haka.

Gwamna na son bin su ya ji dalilin da ya sa suke a tare, kuma ya na son magana da su No 1, dan haka sai da ya bari su Lawwali sun fita, sannan ya qara jaddada musu su yi taka tsantsan ta yanda asirin su ba zai tonu ba, domin in Lawwali ya san sun sace qanwar shi, har shi kan shi ba
Showing 51001 words to 54000 words out of 150481 words